Littafan Hausa Novels

Duniya Hausa Novel Complete

Written by Hausa_Novels

Duniya Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Duniya Hausa Novel Complete

Page 2

 

London;Tite Street

10:am

 

Ganin yadda suke zaune su hudu,suna cin abinci cikin farinciki ya nuna cewa sudin yan’uwane, Wanda yake nuna karfin jini dake yawo a tsakanin su, suna cikin haka ne waya me kiran iPhone14 yafara buzzing alamar Kiran waya ya shigo, wata kyakyawa matashiya ce ta dauki phone tace Abby, Granny ce, tana fadin haka yay saurin picking call cike da ladabi, saide yadda fuskarsa yay looking Yanzu da babbanci da sanda ya amsa wayar, salati Ya dingayi yana hawaye, cikin tashin hankali suka Mike sukayo kansa “Abby, Honey” mai yafaru?

 

Mai Martaba is gone Amina, ya tafi ba tare dana sake sashi a idona ba,wanda aka Kira Abby yay maganar cikin damuwa.

 

Ammy tace “Inna lillahi wa ina ilaihi rajiun, Yanzu shikenan Papa ya rasu? Mu da muke shirin Komawa gida next week? Mayar da dubanta zuwa ga Ali, wanda tasan mutuwar zai gigita shi duba da yadda suka shaku da kakan nasa, koh kwakwaran motsi Ali ya kasa yi,he just can’t believe that his best friend is gone forever..

Rafeeq Hausa Novel Complete

Da kyar Ali ya iya furta Inna lillahi wa ina ilaihi rajiun but Abby ai ba agaya mana cewa baida lafiya ba,saide kawai muji mutuwar sa? No, no it can’t be….

 

Cikin kuka kanwar sa Maryam ta rugume shi tana kuka tace, Blood hakuri zamuyi,janye jikin sa daga gareta yayi, yabar dining area ya wuce dakinsa direct, shifa abin na daure mai kai 6hours ago su kayi waya da papa and he sounds good..! Sai Yanzu kawai a kirasa ace masa wai ya rasu?

 

Jin ana knocking yasa ya mike ya nufa Door din, budewa kofar yay while turning away, Baby ? Ammy ta kirashi dashi cikin tausayawa.. Baby juyo ka kalleni.. ”

 

Juyowa yayi yana kallon mahyfiyarsa, idonsa yayi mugun yin ja ba alamar hawaye koh daya a idonsa, Ammyn ban yarda ba,maybe dogon Suma Papa yayi ba mutuwa ba,

 

Haba Baby? Wannan Wacce irin magana kk yi?saikace ba Muslim ba? Karfa ka manta dacewa “Kullu nafsin za’ikatul maut” inda lokaci yayi dole mu amsa Kiran UBANGIJI mu, so kasa ALLAH a ranka in shaa ALLAH zaka ji saukin abun, sannan ka shirya Kayanka gobe by 7am in shaa ALLAH muna Zaria,inda ka gama shiryawa saika fito mu wuce airport… Tana fadin haka ta fice daga dakin,

 

Scattering well black curly hair insa yayi, yana jin radadi da zafin abin..fadawa toilet yayo, yay abinda zai yi yafito, yafara setting traveling bag insa,

 

Next Morning

Karfe 8 yay masu a zazzau..palace din makir yake da Manya da kananu mutane,cikin Manya mutane, akwai shugaban kasa, gwamnoni da sauran su, ba tare da bata lokaci ba aka fara hada hadan kai Mai Martaba izuwa gidansa na gaskiya,

 

Da Karfe 11 har andawo daga makabarta, ana amsa gaisuwa, Shikam Ali Guests house ya nufa, sabida zazzabi da ya rufe sa,ba yajin zai iya zaman cikin mutane,hawaye yakeyi na tuna wayan da sukayi da Papa jiya..

 

“Papa yace Takwara ya kamata ace ka dawo gida kayi aure, tunda kaga mahyfinka bason dawowa gida yakeyi ba, Kai nasan inda kayi aure Annan zaka zauna kana kulawa dani ko Takwara..?

 

Murmushi Ali yayi yace Papa kenan? Dan yaro dani ne kk wani Kiran min aure? Ina laifi kace min nadawo Zaria nai aiki tunda na kammala karatuna?saina fi kulawa dakai harta abinci nizan dinga baka.. ”

 

“A’ah Takwara, nide nafison kayi auren ka dawo kusa dani, ga ka ga iyalinka, nasan zan samu kulawa Sosai…

 

Ali yace aiko Papa zaka mutu banzo ba kenan, don ni aure baya gabana Sam, ban ma da budurwa balle in fara tunanin wanni abu wai shi aure…

 

Papa yace Yanzu kana numfi at your age bani da suruka? Takwara how old are you now?

 

Ali yace 27 Papa, Papa kabar magana Auren nan kawai muyi hiran mu, tunda jibi ne convocation na, zan tattaro su Abby muzo maka Hutu yadda we’ll not get tired of each others company koh ya kace Old Man?

 

Papa yace Hmmmm Takwara kenan haryanzu dai baka bar wannan halin na tsoran mutane ba koh? To muna gama wayar nan zankira kanina nace masa ya nema maka auren cousin inka Khadijah…Papa na fadi haka Ali Ya yanke Kira, sabida inda akwai abinda yafi tsana so far a rayuwansa shine Aure.. Baya tunanin zai taba yin Aure a rayuwansa sabida dalilai Biyu, dalilin farkon wannan ya kasance sirrin sa, dalili na Biyu bai son takura sabida shidin ya kasance solitary confinement..bacin iyayensa da Papa bai sakin jiki da mutane, koh a gidane yafi son ya zauna shi daya.. A hankali yace Papa I’ll miss you so much, ALLAH ya jikan ka da rahama amin.

 

 

*TASLEEM(TALATUWA

 

Jin tayi ana horn Aman sai ta cigaba da tafiyar ta hankali kwance..

MEEMsALY ? MEEMsALY ? Jin yana Binta yasa ta jiyo lafiya malam?

Oh oh You? We met again tafada tana murmushi kafin Hali..

 

NIMRAH right? So it’s you? Ya fada yana murmushi..

 

Yes. What are you doing here or don’t tell me that you also live here? Ta fada cike da dan tsoro..

 

Nope. I came to pick up my girlfriend but here I am, stock up coz I don’t even know where she lives and her line is not going through..

 

Ayyah so sorry about that tafada trying to walk away…

 

Kema Annan kk? Ya fada yana biye da ita,

 

Nope ina Danraka ne ba kowa a gidan shine Nace bara na zauna da neighbor na tunda cikin Daren yau in shaa ALLAH za a bude portal ina Gama registration zan wuce Umrah tare da family na,

 

OK. Hope dai baki daura mata nauyi ba? Yayi magana showing concern..

 

Nauyi kuma?

 

Yace Yes. Inda babu damuwa I can accommodate you in a more comfortable and safe apartment Nimrah?

 

No Thanks. sabida Dad na ya kirata yace ta kula Dani harna Gama komai tunda ita Masters takeyi ta fini sannin kan garin..

 

OK cool. Toh Yanzu ina zaki?

 

Bakin titi zan amsa Abu a mota ne kasan dazun ban samu naje shikan ba tayi magana while walking away..

 

OK.. Toh can I have your digits sabida kamar ku daya da girlfriend na voice naki da kiban kawai ya babbanta bansa koh Don Jilbab dake jikin ki bane Nimrah?

 

Murmushi tayi kafin tace wai dagaske kk yi ina Kama da ita?

 

Yes. Shiga Car mana sai nakai ki bakin titi inda zaki amsa sakon..

 

No I’m fine.. Zanje a kafa kusa ne fa, ba wani nisa daga nan tayi magana cikin dan tsoro..

 

Koh dai tsoro na kk ji?

 

A’ah walhy?

 

Toh shigo man, don bazan so nabar kyakkyawar yarinya tayi yawo cikin Rana nan ba…

 

Murmushi tayi kafin tace OK..ya bude mata ta shiga,mika mata phone insa yayi, yace Kinga ta nan kamar ku daya kamar yan biyu walhy kuna kama..

 

Ware Manya idanuwa ta waje tayi,”wai naga ita tayi piercing nose and tasa nose ring and me I don’t do makeup

 

Yes. She’s too exposed and naughty Ina tunanin ma zaki girmeta sabida she’s just 16 but very Smart,

 

Really? I think wannan makeup yake sata looking older than her age Tasleem tayi magana trying to deviate from the talk..

 

Nope koh a haka kasan yarinya ce but tana da mugun wayo Sosai ina tunanin ma tafi ki wayo

 

Really?

 

Sosai ma kuwa amma ni kuma kallon ta kawai nakeyi ina tara ta ina jira tazo hanuna Hmmmm rannan sai na fanshe kudina, don wuni zanyi akanta..

 

Tasleem ji tayi gabanta ya fadi yace rass,da kyar ta iya hadiye wani abu mai daci kafin tace, ban gane ba? I thought she’s your girlfriend?

 

Yes. But she thinks she’s playing me?

 

How?

Ehm Ehm kasan ba nisa crossing zanyi kawai ka sauke ni anan..

 

Haba mana tayaya zan bar kyakkyawa yarinya kamar ki ta tsalleke titi? bara muje daman ni zango zanyi inda nayi Uturn sai najiye ki

 

OK.

 

Fara driving yayi yana Uturn yasa luck a mota sai gudu yakeyi kamar wanda ake binsa, ganin haka yasa tace

 

Malam lafiya kuwa Ka sauke ni please ina zaka kaini? Dama saida sis Maryam tace kar in kula kowa Ashe abinda take warning ina akai kenan

 

Hmmm MEEMsALY you think you can full me right? Tunda muka hadu a kasuwa nasan kece amma tunda you’re good at playing games Nace Oya let’s go na biki har kofar gidan nan dana ganki,na tambaya masu dinki a shops dake jikin gidan, sukace sunan ki TALATU kuma nan ba Layin ku bane kinzo wajan kawar ki ce nikuma Nace sai naga gudun ruwanki shiyasa nai ta zaman jiranki har kk fito…

Gashi Yanzu kinzo hanuna hahaha harda sani a blacklist koh irin an wanki Gara koh? Toh sisi na bazai yi ciwo ba TALATU saina fanshi kudina

 

Are you stupid like are you alright upstairs? Kai kasan TALATU da kk magana sabida ni ban Sansu ba nide ka sauke ni kafin inyi ma abinda har ka mutu bazaka manta dashi ba tafada tana kokarin bude kofar?

 

Hahaha ya Kyalkyalce da dariya yace ina jira toh..

 

Dauko wayar tayi zatayi dialing kawai ya kwace

 

Yaci gaba da driving da speed bai tsaya koh ina ba, sai Gest inn dake GRA

 

Ganin an shiga da ita ciki ta dinga rusa kuka tana rokansa Don ALLAH bawan ALLAH bansa wacece MEEMsALY ba koh TALATU nasan Kama mukeyi Don ALLAH karkayi min Haka

 

Zaki fito ne koko sai na dauko ki

 

Ganin bata da niyya fitowa ya bude kofar zai riko ta

 

Toh ka tsaya man zan fito da kaina ta fada tana kuka mai cin rai…

 

Karfa ki batamin lokaci yamma nayi zan wuce aiki..

 

Don ALLAH kayi hakuri walhy bani bace

 

Mtchews…! Saiki gayawa wanda kk Raina amma bani ba.

 

Toh gayamin nawa ne kudin Naka na biyaka sai na tafi Dukda dai bani ce naci ma kudin ba..”

 

Hahhah Rainin sense ba kudin nake so ba jikin ki nake so maza ki fito yarinya yau zaki san da cewa kin hadu da maye..

 

Ganin baida niyya compromising with her yasa kawai ta….

 

 

 

Duniya

 

Page 3

 

Ganin baida niyya compromising with her yasa ta fito tana kurma Uban ihu,gani ga securities agun amma basu ce kala ba,yasa ta tadinga kurma Uban ihu tana birgima a kasa, a fusace ya duka da niyyan daukan ta sai yaji murya daga saman kansa yana cewa, let go off her.A fusace ya dago da niyyan wanke Wanda yayi mai magana da mari sai kawai ya sauke hanunsa kasa, don ganin uniform Men dake bayansa, daya daga cikin uniform men yace Meyafaru ne Baiwar ALLAH ? Tasleem dake kwance a kasa tayi saurin dagowa tana kallon wannan young, handsome and sexy guy da ya kure ta da kallo,tayi saurin mikewa ta koma bayansa cike da tsoro tace Don ALLAH ka taimake ni zai kashe ni,

 

Guy din yace hey! Calm down gayamin abinda yafaru..? A hankali tafara bashi labarin tundaga kasuwa harzuwa iya yanzu tanayi tana kuka…maida dubansa izuwa Yasir yayi, yace meyasa kk son zubar da mutunci ka? Ace ma eh da gaske itace MEEMsALY so sai kayi mata ta karfi koh mai? kafin ya sake mayar da dubansa gareta yace daga ina ya dauko ki?

 

Daga Samaru,ya kwace min kome nawa tayi magana cikin shagwabe… Alama yayi wa security guard insa da ya amso mata kayan ta,

A zuciye Yasir Ya nufa motar yana tunanin ya zaiyi da yarinya don baze taba barin ta tafi scot free ba,dauko jakanta ya mika mata, ta amsa da sauri tana sauke nauniyar ajiyan zuciya..

 

Mayar da dubansa yay izuwa gunta yace ga driver na,zai mayar dake.

 

Thank you sir, ALLAH ya saka da alkhairi ta juya ta watsa ma Yasir harara ta bi bayan Dss da akace zai kaita gida…Shima ya shige nasa car din tare da escorts insa suka bar haraban guests house din..

 

Hankali kwance ta zauna a mazauni owners seat tana murmushi, tace I can’t wait to see their faces inda suka ga na fito a motar, shegu kawai sa’idawa banza, da wannan tunani suka issa gidan su Meems tace ma driver nan zaka sauke ni, samari layi sakin baki sukai suna kallon ta,tace driver ka sauko don Allah kafini tsawo ka dubamin wanca mota tayi pointing inda masu zaman banza suke, suna ganin Dss ya sauko suka tsare a guje, kyalkyacewa tayi da dariya tayi masa godiya kafin ta shige ciki, da sallama ta issa cikin gidan su Meems durkusawa tayi ta gaida Ummah, kafin tace ummah Maimuna fa?

Ummah tace tana daki tana shirin zuwa islamiya, kefa? yau ba zaki bane?

 

Tasleem tace zani Ummah ai hijabin na gun Maimuna dazun nazo nayi guga kuna gun Aiki…ummah bara na shiga ciki na same ta, da sauri ta nufa dakin Meems, suna hada ido suka kwashe da dariya, tace Talatu baki da dama..

“A’ah Maimuna karki kuma in ba so kk ajimu dake ba.. ”

 

Ya hakuri K’awa, yanzu dai karasa min naji, nan take Tasleem ta bata labarin suka ci dariya harda kaiwa kasa,Meems tace dazun Inno ta aiko wai ya batun wara?

 

Kinji manta da batun wara bara muyi sallah mu wuce islamiya, kafin wannan Maye ya isheni da kira… ”

 

Tasleem yanzu Mal Nazeefi shine Maye? Banza Tasleem tayi mata ta nufa toilet tayo alwala ta fito tayi sallah suna idarwa, taci abinci kafin suka dauki hanya zuwa islamiya, tunda ga nesa ta hango Mal Nazeefi dake ta fama murmushi a dalilin hango su da yayi…

 

Suna zuwa kusa dashi suka gaishe shi kafin suka wuce cikin makaranta… Zama sukayi gu daya har lokacin koyarwa yayi Malam Nazeefi ya shigo, Wanda ya kasance malamin Fiqh,gaba daya hankalin kowa ya karkata izuwa gun malam amma banda Tasleem dake fama tauna chew gum…

 

Jin an tabo ta yasa ta jiyo tana kallon Hauwa tace lafiya zaki kaimin Uban duka? Hauwa tace malam ne ke miki magana, toh sai akace ki dake ni?zako kici nakashi yarinya bara atashi, ganin gaba daya suna niman tayar da hayaniya ya kira dukkansu da suzo, Hauwa ne tafara mikewa kafin Tasleem ta mike taja hijabin yadda nonuwata suka tsaya cak dasu, tana wani karkade karkade tuni ya sunkuyar da kansa,yan aji suka kwashe da dariya,

 

Tsawa ya dakka masu kafin ya umurce su dasu zube a kasa, maida dubansa yay gun Tasleem dake fama bangare bangare yace baki ji abinda nace ba kenan?

Kunkune ta fara yi kafin ta zube a kasa, cigaba da koyarwa yay, saida ya gama ya kalla Hauwa yace ta koma ita kuma Tasleem ta bisa office, yana gaba tana biye dashi amma wanni irin tafiya takeyi na shakiyanci, yan aji suka kwashe da dariya..har suka isa office ta durkushe a gabansa..

 

Yanzu Talatu abinda kk yi ya dace?

 

Cikin shagwaba da girgiza girgize tace Mam Nazeef wai menayi ma? Kulum Saika bani punishment a islamiya, can kuma ka lalabo kazo tadi..

 

Kasa kallonta yayi, sabida ALLAH kadai yasan wana irin hali yake shiga Inda tana wannan shagwaban..shikin sarkewar murya yace ki koma anjima zan zo gidan.komawa aji tayi, bayan antashi islamiya ta jira fitowar Hauwa bata ganta ba, daga karshe hakura tayi,ta wuce gida..

Da sallama ta shigo wanni kwakwararan gida, Wanda ba plaster bale cement, tun daga nesa ta hango Inno a bakin Murhu tana fama da hayaki,d’aga murya tayi tace Inawuni Inno..

 

Wata mata ce ta juyo wacce baza ta wuce shekarun 65 a duniya ba,tace sai Yanzu Talatuwa? Lafiya kk kuwa?

Turo baki Tasleem tayi tace, Talatuwa kuma saikace wata talge ba dadin ji…?

Yo kajimin Yar banza yarinya, Wato abinda ake fadi a layi gaskiya ne, to Dan dan ubanki inda nakiraki karki amsa, gayamin daga inda kk?

kunkune tayi kafin tace, cikin makaranta na shiga, da ganan na biya gidan su Maimuna muka wuce islamiya..

 

Ayo ai nadauka baki je islamiyar bane, to maza kije kici abinci ki shiryo ki fita tuyan..

Kai Inno, nide nagaji wallah ki bari sai gobe man, tafada tana zunguro baki..

Anqi a bari din,kajimin yar banza Kai?bayn kinsa tara kudi mukeyi sabida walimar saukar ki, Inda baki je ba Ina zamu samu dubu goma da zamu bada?

 

ALLAH zai… Bata bari ta karasa ba ta bita da muchiya, da gudu Tasleem ta shige daki tana fasa ihu, kamar Wacce ake ma duka…

 

*Muhammad Ali*

Some days later

Yau ake kwana uku,Mai Martaba inda aka nema Kowa da kowa ya kasance a Fadar yau za raba gado da kuma sanni magajin Sarki..

 

Shi Abban Ali Wanda ya kasance shine ɗa nafari a yara maza,Abban Ali, shine na goma a yaran Mai Martaba amma Nafarko kuma nakarshe agun Amaryasa Rukayya Wacce tana hyhuwar sa ALLAH ya dauki ranta, shiyasa Mai Martaba Eng Muhammad Ali Hammajo,ya daurawa Abubakar son Duniya, koh kuka yaji Abubakar nayi,sai yaji ransa ya sosu,wanda haka ya jawo ma Abubakar bakin jini agun sauran matar Mai Martaba,Da har suka fara kokarin ganin sun raba Abubakar da mahyfinsa,wannan dalilin yasa Mai Martaba ya dauke Abubakar daga masauratan izuwa Jihar jalingo a sirrince gun dagin mahyfiyar Abubakar, tunda Abubakar yabar masauratan bai sake dawowa ba sai bayan da yayi aure,har Matarsa Amina ta Kai watan hyhuwa, Wanda Al’ada ne in jikan fari ne ya kasance an birne cibiyar sa a cikin Masauratan…”

Cikin Ikohn ALLAH, ALLAH ya sauke ta lafiya ta samu Danta kyakyawa mai kama da ita, Wanda itama ta kasance yar Fulani Gembu, dake jihar Jalingo, sai ka rantse kace sudin ba yan Nigeria bane tsabar kyawun halitta su.. ”

 

Mai Martaba da kansa yace a sa ma dan sunan sa, Wanda hakan yakara sa bakin jini Abubakar ya karu a zukatar matan Mai Martaban,especially Killishi Wacce Abin yafiwa ciwo takasa dane Zuciyar ta, Wanda yasa taje ta same Mai Martaba da maganar, tace yanzu fisblh abinda kayi ya dace? Saikace Abubakar ne kadai danka? Ka dauki son duniya ka daura mai? koh akansa aka fara hyfa ma jika namiji da zaka sa me Sunanka?

 

Hajara karki manta dacewa Abubakar ya kasance shine Da’na nafari a wannan masauratan wanda nake sa ran bayan bani shi zai gajeni…”

Ya gaje fa kace? ka ko San abinda kk fadi kuwa? nice fa uwargida dole wanda zai gaje ka ya kasance daga guna, sannan da kk fadin haka shidin me ya sani game da sarauta? Hamza tun yana karami ake koya me mulki da sarauta…

Mai Martaba yace Hamza bashine da’na nafari ba don haka bashine magajina ba, sannan magana sa suna danayi, Eh nayi ne sabida haka nake so, zaki iya tafiya kuma banso nasake jin kin kara kawomin irin wannan maganar…

 

Har Amina tayi jego ta gama bamai zuwa gunta sai kuyangu ta, daga karshe dai barin kasar sukayi a dalilin aikin da Abubakar ya samu acan kasar UK..

**

Dawowa cikin labarin, kowa ya hallara a fadar banda Ali dake guess house, sabida shi irin mutum ne Wanda in hayaniya yay mai yawa sai yakama zazzabi… Batare da bata lokaci ba akayi abinda za ayi inda akace A. M Abubakar ne Magajin Sarki, ana fadin haka Hajara da yaranta sukayo kansa suna nuna farinciki su, sukam sauran zama sukayi suna kallon Ikohn ALLAH.. Cikin kanne Mai Martaba wani yace bazan mu tashi daganan ba, batare da cikishe wasiyar da wanmu yabar mana ba, wai ina Ali yake?

 

Abby yace he’s down shiyasa baizo ba..

Toh shikenan ina Khadijat ? Nasan kuna da labarin kome tunda a ranan da Mai Martaba ya kirani a ranan na isar da sakon, Toh Mai Martaba yace a hada Auren Ali da Khadeejat yar gidan Hamza nan bada jimawa ba,

Sunkuyar dakai Khadijat tayi, Tana murmushi tabbas ba wanda zai ki namiji kamar Ali, she can’t wait to get married to him..

 

Not edited

09074267236

Thanks

Duniya

 

 

Page 4

 

Mahyfiyar Ali bataso ba, amma ya ta iya? Aikin gama ya gama, Kawu Garba ne ya dube Abby da Ammy yace sai ku sanar dashi cewa an tsaida ranan bikin su a ranan bikin nadin sabon Sarki…

Su Khadijat murna har baka, cikin kunya ta rugume Gimbiya Hajara wato kakarta tana murmushi,aka rufe taron da adu’a…

 

Ammy tana Komawa daki ta kira Ali a waya,bugu daya ya amsa bata tare da bata lokaci ba ta bukace ganin sa b4 8pm, amsawa yayi da toh kafin ta yanke Kiran…

8pm yayi mai a Part din Abby, kowa yagansa yasan yana cikin damuwa, cikin girmamawa da biyaya ya gaishe da iyayensa kafin ya zauna kusa da kanwarsa Maryam, Maryam tace blood azubo ma abinci? Girgiza kai yayi alamar A’ah,

 

Abby yayi gyaran voice kafin yace son ALLAH da yayi mu yafi mu sonsa shiyasa ya amshe ransa. kuka,tunanin bashine Mai Martaba yake bukata ba,adu’a shine abinda yake bukata.Yanzu ba wannan ba nasan kana da labarin Khadijat..

 

Cike da mamaki ya dago, yana kallon Abby, kafin yace Abby Wacce Khadijat?

 

Abby yace Khadijat nawa ka sani? Idan kuma akwai wata Khadijat daka sani apart from Khadijat Abbanka Hamza sai ka gayamin..

 

Ali yace Abby me ya same ta? Ya fada out of curiosity..

 

Kamar yadda Mai Martaba ya fada Haka zai kasance, kashirya aurenka nan da wata Biyu, Abby na fadi haka ya mike yabar parlor…

 

Ali is outta words and finding it hard to believe, Ammy tazo ta dafa shi tace son, ka kwantar da hankalin ka, ka cika wasiyar kakan ka, please accept this as your faith kayi biyaya..

 

Ammy ban shirya yin aure Yanzu ba, besides banda niyyar yin aure Don ALLAH kice Abby ya janye wanna batun.. Please Ammy abeg of you, yafada maganar kamar zai yi kuka..

 

Haba Ali? Me acikin aure da baka so eh? Besides yarinya she’s young, beautiful and amazing lady..bata da makusa koh kadan, make some time with her and get to know her Son..

 

Ammy a halin da nake ciki yanzu bazan iya yin aure ba, inama ace Inada daman fada maki cewa aure zai iya zama babba barazana agareni?duk wannan maganar da Zuciyar sa yakeyi, kafin yace Ammy Don ALLAH ku janye maganar auren nan…

 

Haba Aliyu? Yanzu sakayar da zakayi wa kakar naka kenan? Ina kaunar da kk nuna mai? Haba Aliyu kayi hakuri ka aureta kacika Final wish Papa.. Jeka ALLAH yay ma albarka ta fada tana shafa fuskarsa kafin ta mike tabar parlor, daman maryam tuni tabar masu parlor sai bayan sun Gama ta fito ta same shi absentminded sabida ta kirashi yafi sau uku amma be amsa ba, sai can ya dago fuskarsa nan tasa kamar besan wanni abu dariya ba.. Mikewa yayi without saying anything yabar palace din gabadaya..

 

 

 

Farin Hijab roba roba ne ajikinta wanda yake nuna kome na jikinta zaune take gaban Murhu awaranta, ga mutane cike a bench suna jiran a sallamae su..

 

Wanni ne ya zo gun tare da wata sunyi zunbi students tana ganin su, taja hijab gaban goshin ta, tace you welcome how do you want your wara? With sauce or pepper?

 

Da mamaki suke kallonta jin tayi turanci, saurayin yace give me 300 wara with pepper, budurwa tace mine with sauce but I’m so surprised like are you in school?

 

Tasleem ta girgiza kai ba tace kome ba don batason dogon bayani daze sa su bukace Ganin fuskarta, fara sallamar wanda suke kan benchi tayi,sukam students zama sukayi suna labarin new iPhone da ya shigo,

Budurwa tace now you’ll see Temi with this latest iPhone, that girl ehn she’s something else.. See Colins I don’t think she came from a wealthy family…

 

Wanda aka Kira da Colins ya kwashe da dariya yace Jay you’re jealous of her.. Kema from her dressing and everything zaki gane cewa iyayenta nada kudi, ke koh shoes inta kade ya isa yasa ki gane suna da kudi..

 

Karya ne colins, Temi na runs girl, dafa a hostel take yanzu fa cemin akayi ta kama gidan that’s worth 400k..zai magana kenan Tasleem ta miko masu package din awara daman haka takeyi Inda yan makaranta ne sai tasa masu a roban takeaway inda yan unguwa ne sai tasa masu a Leda, 1k suka bata sannan suka bar mata change din.

Bayan sun tafi ne ta buga Uban salati, tabbas zama bai gani ba, “harta ma takalmi ma sai Ansa ma ido? Ah gaskiya dole na nema kudi bare mu da zamu faculty of Life science inda akace yan gayu da masu kudi sunfi yawa zuwa bikin suhailat ya kamani kam dole nayi anko wata kila na hadu da wasu hot guys” Kiran sunan ta da Mal Nazeef yay ya dawo da ita daga duniyar tunanin ta,

 

Barka da zuwa Mam Nazeef tayi magana cikin shagwaba..

Barka dai hoorun enn, ya fada yana murmushi..

 

Haba dai Mam Nazeef? Wane ni da wannan suna? Ta fadi magana tana dan cokaro dan bakin ta…

 

Hmmm Talatu kenan, bakisan irin baiwar da ALLAH yay miki bane shiyasa kk fadin haka, nide burina na malleke ki a matsayin mata..

 

Murmushi tayi kafin tace ALLAH koh? Yace Eh Sosai ma hoorun enn, Yanzu dai ba wannan ba Mam Nazeef, tayi magana tana dan sunkuyar dakai kasa,

 

Toh menene fada inji hoorun enn, cikin shagwaba tace dama maganar walimar saukana kasan dai bamu da karfin siyan rago da biyan kudin sauka..

 

Kekam bana gayamik cewa na biya miki ba? Sannan kuma nace zan aiko da kaji biyar na makaranta

 

Cikin shagwaba tace Mam Nazeef baze issa ba fa, abokanai na yan areas zasu zo kuma yakamata na karamasu, ka hadamin da dubu goma man.. ”

 

Gaskiya Talatu banda kudi Shima wannan dubu ashirin adashe na shiga sabida ke, kinga inda na biya kudin sauka 10k Saura 10k shine na kajin.. Zatayi magana kenan wata bakar mota tayi horn, cikin kwarkwasa da kisisina ta mike tafara takawa wanni yaga yanda take tafiya zaka rantse kace tafi karfin shekarun ta,

Sauke glass din motar Alhji yayi ta sunkuyar dakai tace ina wuni Alhajee, na nawa za akawo ma? Tande baki yayi kamar wani tsohon Maye yace Talatu koh? Murmushi tayi tace eh to, Talatu ce…

 

Talatu Inajin dadin waranki, Gaskiya koh naci bai isana shine nace why not gobe by 10am kizo guests house ina kiyimin na kamar dubu goma,

 

Zaro da Manya idanuwa ta waje tayi tace Alhajee dubu 20 fa kace? Kaikam mai za kayi da wara na dubu 20?

 

Talatu kenan, bawai ina numfi waran dubu 20 zakiyi min ba, A’ah kawai kudin aikin waran ne dubu 20,Inda kin rena ne sai na kara maki..

 

Murmushi tayi tace toh Yanzu ya kk so ayi? Amma kamata yayi ka bayar da kudin in yaso sai nazo maka dashi can na soya…

 

ciro da bundles 200 guda daya,ga kuma complimentary card na sai ki kirani dashi, saida ta waiga taga Mam Nazeef baya kallonta tayi saurin amshewa ta cusa a hijab kafin tace Alhajee Nagode saide banda waya,

 

Ya salam yarinya wayeyya kamar ki ace baki da waya? Toh inda kinzo zamuyi magana wayar, amma Yanzu ki nema Waya sai ki kirani,

Toh Alhaji bara azubo ma waran tana fadin haka ta juya tana tafiya, Alhajee kam suma zaune yayi yana mamakin yadda yarinya nan take da cikar hallita,kuma daga Ganin ta danya ce shakaf, gobe zansha romo harda luguda don yarinya zata kawo wuta.. Kyalkyalce da dariya yayi yace zanta shanawa da ita harna kwashe gara.

 

Talatu kam kwashe sauran waran tayi ta packaging mai, Mam Nazeef yace dukka ya siye?

Murmushi tayi tace walhy kuwa kulum in yazo na dubu yake siya tana fadin haka ta kai mai motar da yazo amsa sai ya hada da hanun ta yana lashe baki kamar he’s craving for something.. Saurin Janye hanunta tayi tace sai nazo Alhajee..

 

Murmushi yayi yace toh Talatu, sai kinzo koh yay magana yana kashe mata ido yana Jan motar ta saki baki tace…..

 

09074267236

MissDmk✍🏻

Thanks

About the author

Hausa_Novels

Leave a Comment