Littafan Hausa Novels

Duhun Zuciya Sarkakiya Hausa Novel Complete

Written by Hausa_Novels

Duhun Zuciya Sarkakiya Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

Duhun Zuciya Sarkakiya Hausa Novel Complete

Bismillahi Rahman Rahim.

 

DUHUN ZUCIYA 2021

 

SHAFI NA ƊAYA

 

Pharty BB

Wattpad PhartyBB

 

 

‘Ina ma ni ce a wannan yanayi da lokacin? Ina ma duniyata zai canza zuwa ga mafarkina? Duhun da yake kewaye ya gushe ya zamto haske. Koyaushe zan samu haske? Wa zai cire ni daga duhun da yake lulluɓe da zuciyata?

Tsawon lokaci hasken cikin rayuwata ya gushe. Ko wacce rana ina tsumayin wanda zai haskaka duniyata.’

 

“Radiyya! Radiyya!!”

 

Sunan da ya shiga kunnuwanta cike da karaɗi da amo ya sa ta dawowa daga duniyar tunanin da ta tsunduma kanta.

Firgigit Radiyya ta amsa tana duban wacce ta ƙirata tare da faɗin.

“Ki ka ce me?”

 

Ba ta damu da yanayin da take ciki ba. Kullum uzurinta shi ne a gaba da rayuwar wani. Ba ta duba da rayuwar wani na kusa balle ta fahimci halin da ya ke ciki.

Mugun kallo take watsa mata, duk da ta sunkuyar kanta ƙasa balle ta hango.

 

Kalmar da ya fara fitowa daga bakinta shi ne.

 

“Ubanki na ce! Kin saka mini ido kamar mayya! Cinye ni za ki yi?”

 

Kai Radiyya ta girgiza tana matsawa baya don kar ta taɓa lafiyar jikinta, tasan zai iya biyowa baya bayan zagi.

Waye Mijina Hausa Novel Complete

“Ƙarfe biyu ki tabbatar kina ƙofar makarantar su Walid, kar ki yarda ki bar mini yaro yana jira. Sannan Uncle Nasir zai dawo ƙarfe uku ki ba shi abinci, na tafi gidan sunan Farida, zan kai ƙarfe shida ko bayan magriba Uncle Nasir zai ɗauko ni.”

 

Daga haka ba ta jira ko Radiyya ta ƙara magana ɗaya ba ta ɗauki jakarta ta fice a falon.

A sanyaye Radiyya ta miƙe ta koma ɗakinta har da saka mukulli a ƙofar, bakin katifarta a saman gado ta zauna tana zuba tagumi, a hankali wasu siraran hawaye masu zafi suka zubo mata, nata rayuwar take tunawa da babu jiƙo balle samun ƴan ci.

Gajiya ta yi da zaman ta zame ta kwanta nan ƙasa ɗakin don jiran lokaci ya yi, ta riga ta gama ayyukanta na safe da rana gaba ɗaya na gidan, babu abin da ya rage sai abubuwan da ba za a rasa ba.

Barci ya fara fisgarta ta ji bugun ƙofa tare da ƙiran sunanta a hankali kamar koyaushe, a firgice ta miƙe tana tattaro hijabinta ta miƙe tsaye cikin mugun kiɗimewa, jin muryar mai ƙiran ya haddasa mata tsoro bayan wanda kullum take ciki.

 

Daga can waje ta ji an dakata da bugun ƙofar a hankali aka ce.

 

“Buɗe ƙofar Radiyya, don Allah ki buɗe mini ƙofar nan yau kaɗai.”

 

“Bazan buɗe ba.”

Ta samu kanta da faɗa cikin kukan da ya ke neman kwace mata, kafin ta ƙara sauraran maganar da zai biyo baya da gudu ta kwasa ta shiga cikin bathroom(bangida) ta kulle kanta. Tana jin ana buga ƙofar da ƙarfi wanda dai dai yake bugun da bugun zuciyarta.

Kuka ta fashe da shi tana durƙushewa nan ƙasar bangidan.

 

‘Ina zan sa ka rayuwata da wannan masifar!”

 

Ta furta haka cikin kuka tamkar wani take faɗawa abun da ya ke faruwa da ita a kowane rana, cikin firgici da tsoro take.

Kuka ta ci gaba da yi na tsawon lokaci har ta ji an daina bugun ƙofar, a hankali ta miƙe ta nufi wajen wanke baki, fuskarta ta wanke sannan ta fito cikin sanɗa a bangidan, numfashi ta sauƙe ganin babu kowa kuma da alama an bar ƙofar ɗakin, kasa zama ta yi saman gadon a hankali ta sulale ta zauna tana jingina jikinta jikin gadon tare da ɗaura kanta saman katifar da yake kewaye saman gadon. Idanuwanta ta lumshe wanda suka bawa siraran hawayen da ya taru damar zuba bisa kyakkyawar fuskarta. Ba ta damu ta share su ba domin a kowacce rana tana zubar da irin su babu adadi.

Rayuwarta kawai take tunawa da irin yanayin da ta tsinci kanta a matsayinta na ƴa mace mai ƙarancin shekaru. Ba ta da inuwar da za tasa kanta domin samun sauƙi daga zafin da take ji, kullum gani take tamkar rayuwarta a juye yake tafiya, ba ta da gabas balle yamma, duhu ne kewaye a zuciyarta da babu haske ko kaɗan wanda zai haskaka mata samun mafita ko hanya, ire ren tunanin da ta ke jefa kanta a ciki kullum da zaran ta samu kaɗaicewa ita ɗaya.

Alarm ɗin da ya buga ne ya sata firgita a mugun tsorace, kyawawan idanunta farare ta fara zarewa tare da jujjuya kanta tana neman inda ta ji ƙarar, can ƙarshen gado ta hango, da sauri ta miƙe ta isa gurin tana ɗauka, kashewa ta yi kafin ta duba lokaci ta ga ɗaya har ya kusa gotawa, a hanzarce ta buɗe dirowar gefen gadon ta ɗauki ƙaramar jakanta da kuɗi yake ciki ta doshi ƙofar fita, sai da ta murɗa hannun ƙofar ta tuna dalilin da ya sa ta kulle, tsoro ne ya ƙara ziyartan zuciyarta ta dakata, ga

lokaci yana tafiya, ta kusa mintuna biyar tsaye tana karanta duk addu’ar da ya zo bakinta na neman tsari da sharrin mutun da shaiɗan, wani sanyi da ƙarfin guiwa ne ya ratsata kafin ta buɗe ƙofar a hankali ta leƙa kanta cikin falon, babu kowa hakan ya sa ta fice da sauri a ɗakin ta sawa ƙofarta mukulli, tana sawa ta juya ta nufi hanyar fita a falon.

Ta isa tsakiyar falon ta ji maganar da ya kusa sa ta yin tuntuɓe tsabar tsorata.

 

“Ina za ki je?”

 

Shi ne kalmar da ya fito daga bakin wanda yake kwance saman doguwar kujeran falon, idan ba ka iso wajen ba ba za ka san yana kwance ba ko ka lura da shi ba.

Gaba ɗaya jikin Radiyya rawa kawai ya hau yi ta juya suka haɗa ido, da sauri ta yi ƙasa da kanta cikin rawar murya ta ce.

“Zan je in ɗauko Walid ne daga makaranta.”

 

“Ya yi kyau.”

Ya faɗa daga kwancen da yake.

Tana ganin haka ta fita da sauri har ƙafafunta suna harɗewa.

 

 

Tana fita adaidaita sahu ta tsayar ya kaita har ƙofar makarantar, bayan ya sauƙeta ta roƙeshi ya jirata zai mayar da ita, ya yarda hakan yasa da sauri ta fita ta shiga cikin makarantar, bayan ta sanar ta zo ɗaukar yaro ne suka yarda don sun saba ganin tana kawo sa wani lokaci kuma tana zuwa ɗaukar sa. Bayan sun bata izini ta shiga ciki ta samu an tashi yara ƙanana da ake tashi sha biyu da rabi, gurin yaran ta nufa tana raba idanu inda za ta hangosa. Yaron yana daga gefe yana ganinta ya kwaso jakarsa da lunch box nasa ya nufa wajenta da sauri. Sai lokacin ta hangosa ta sakar masa murmushinta mai kya, yana isowa ta karɓi lunch box ɗin ta kama hannunsa suka nufi hanyar fita.

 

“Anti na ɗauka yau kin manta da ni.”

 

Girgiza kai ta yi ta dubesa ta ga ita yake kallo, har lokacin murmushi bai gushe a fuskarta ba ta ce.

“Ni na isa na manta da yarona, wani ɗan aiki na yi.”

 

Daga haka suka fita suna hira sama sama har zuwa wajen da mai adaidata inda ya yi fakin yana jiranta, ciki suka shiga ya ja suna barin gurin. Har ƙofar gida ya sauƙeta ta sallamesa tana masa godiya sannan suka shiga cikin gidan. Babu kowa a falon, hakan ya bawa Radiyya damar jin wani sanyi har ba ta san lokacin da ta sauƙe ajiyar zuciya ba. Kai tsaye ɗakinta ɗakin yaron masu gidan da suke rayuwa tare su biyun suka nufa, ƙofar ta buɗe suka shiga ciki, wanka ta masa ta canza masa kaya, ganin lokacin sallar azahar ya yi ta ɗaura alwala shi ma ta nuna masa ya yi suka fito suka gabatar da sallah sannan suka fito falon zuwa madafa.

Indomie ta dafa masa cikin sauri ta haɗa ta ba shi ya hau ci.

 

“Kar faɗawa Mimi ban ba ka abinci da wuri ba ka ji yarona.”

 

Kai ya ɗaga mata, ta shafa kansa ta bar gurin cikin sauri ta hau haɗawa Uncle Nasir nasa abincin da ba ta samu yi ba ɗazu. Haka suke yi idan ya kasance ita ɗaya ce a gidan, har sai ta ɗauko sa ko Uncle Nasir ya ɗauko sa take samun sakewa a gidan, ta dafa masa nasa abincin cikin sauri sannan ta dafawa mutanen gidan.

Shi ne garkuwarta a gidan, shi yasa take son sa tana ba shi dukkan kulawa da gujewa abin da zai sa ya yi nisa da ita, idan kuma Aunti Mimi tana nan to tana samun sakewa nan ma.

 

Tana tunane tunane ta gama girkin wajen ƙarfe uku saura, tana kammalawa ta haɗa abin da ta yi amfani da shi ta wanke ta kimtsa madafar, abincin Uncle Nasir kuma ta jera masa a dinning table. Sai da ta tabbatar komai tsaf kafin ta deɓi nata abincin ta wuce ɗaki ita da Walid sannan ta hau ci, nan Walid ya nemi ƙari ta tura masa sauran akan ya cinye duk da ba ta ƙoshi ba, jagwalgwalawa kawai ya yi yace ya ƙoshi, dole ta haƙura ta ɗauke plate ɗin ta kai kitchen don wankewa.

Tana cikin ɗaurayewa ta ji sallamar da duk lokacin da ya ratsa dodon kunnenta sai ya haifar mata da bugun zuciya da rawar jiki.

Ba ta san ta saki plate ɗin ba sai da ƙarar faduwar sa ya dawo da ita hankalinta ta duba ta ga ya fashe, baya ta ja a tsorace ta rasa abun yi, ta kalli ƙofa ta kalli plate ɗin.

 

 

Jin motsi da ƙarar fashewar abu a cikin madafa shi ya hanasa ƙarasawa ƙofar ɗakinsa da ya nufa ya dawo baya ya nufi madafa, tsaye ya ganta duk ta ruɗe.

Radiyya da tsayuwarsa nan bakin ƙofar ya haifar mata da wani mugun tsoro ta nemi kaiwa ƙasa tana durƙusar da guiwarta saman fasashshun plate ɗin da suka fashe, zafin da ta ji ya ratsata yasa ta sakin ƙaramar ƙarar azaba.

Tsaki ya buga ya nufi gurinta ya tsaya saman kanta, curewa guri ɗaya ta yi jikinta gaba ɗaya rawa yake yayinda bakinta yake rawa ta kasa furta ko kalma ɗaya. Ta tsani su keɓe su biyun, tana tsoron keɓewar su kamar yadda take tsoron ajalinta, cutarwa ne a tare da shi a kodayaushe.

 

“Me kuma aka miki na kuka? Ko kin ji ciwo ne? Wannan shegen tsoron naki watarana sai na canza miki kamanni.”

 

Girgiza kanta kawai take alamar babu komai, har lokacin hawaye take zubarwa da za ta rantse bata san yaushe suka fara zuba ba, idan zai canza mata kammani ya fiye mata komai akan abin da yake bibiyarta da shi.

Tsugunnawa ya yi saman ƙafafunsa daf da ita har tana jin hucin numfashinsa. Ƙoƙarin ja baya take inda motsi kaɗan ta yi sai fasashshun plate ɗin sun kurje jikinta.

Yana ganin haka yasa hannayensa a kafaɗunta ya matso da ita kusa da shi, sai lokacin ta samu damar sakin kuka mai ƙarfi tana ƙoƙarin fisge jikinta.

 

“Don Allah Uncle ka bar ni…”

Ta faɗa cikin kuka da azabar zafin da yake ratsa ƙafafunta, wannan zafin duk da haka ya fiye mata akan wanda zai jefata ciki.

 

“Me yasa ki ke tsoro na Radiyya.”

Ya faɗa yana kai hannunshi saman kyakkyawar fuskarta don share mata hawaye.

Ya tsani ganin su, sai dai kullum shi ne dalilin zubar su.

 

Fuskarta ta kawar gefe ganin abin da yake shirin yi mata ta ce.

“Walid yana nan, zai iya shigowa koyaushe.”

 

Jin haka ya sa shi sakinta ya miƙe, wani tsakin ya ja a karo na biyu ya nufi ƙofar fita yana faɗin.

“Ki tabbatar kin kimtsa gurin kuma kin kimtsa kan ki kafin ki bar nan. Abinci na ina jiranki a falo idan kin gama.”

 

Radiyya ta kai tsawon mintuna tana kuka kafin ta miƙe da ƙyar, tana ɗingisa ƙafarta da ya fi jin ciwo ta ɗauki tsintsiya da abun kwashe shara ta kwashe fasashshun plate ɗin sannan ta goge gurin, sai da ta wanke fuskarta ta fita kitchen a ɗin, a saman dinning ta hangosa yana zaune, yi ta yi tamkar ba ta gansa ba nufi ɗaki da sauri cike da tsoro, tsawan da ya daka mata ya sa ta dakatawa da tafiyar tuni jikinta ya hau ɓari.

 

 

 

“Kin san ke nake jira!”

 

Haka a tsorace ta dawo baya tana ɗingisa ƙafarta zuwa wajensa, ba ta yarda ta kallesa ba ko haɗa ido da shi ba ta hau zuba masa abincin.

Duk yana lura da ita hatta yadda jikinta yake rawa ya bayyana a hannunta da take amfani da shi wajen zuba masa.

 

“Kin ji ciwo ne?”

 

Ta ji tambayar, sai lokacin ta ɗago kai suka haɗa ido ta ga ya tsareta da mayun idanuwansa masu tsorata ta, da sauri ta yi ƙasa da kanta tana girgizawa lokaci ɗaya.

 

“Inga ƙafar.”

 

Ya faɗa mata yana ƙoƙarin kai hannu zai kamo hannunta ya zaunarta, tana ganin haka tamkar tasan shirinsa ta zille ta yi baya, harara ya watsa mata tamkar tana kallonsa.

 

“Zan ɓata miki rai fa yarinyar nan, zo ki nuna mini ƙafar ko sai na miki ta ƙarfi.”

 

“Ni ban ji wani ciwo ba, zafi yake kuma ya daina.”

 

Radiyya ta ce tana share hawayenta tare da ƙara yin baya, kafin ya ƙara wani maganar ta bar gurin cikin sauri ta nufi ɗakinta, mukulli ta sawa kofarta tamkar koyaushe, sai lokacin ta ji sanyi, cikin ɗakin ta kalla daga tsayen da take a bakin ƙofa, can ta hango Walid kwance yana barci saman gado, bathroom ta wuce kai tsaye ta cire skirt ɗin jikinta, guiwarta ta duba ta ga ya ji ciwo har da jini, gurin ta wanke da ruwan dettol duk da tana jin zafi haka ta daure, bayan ta gama ta ɗaura alwala ta fito ta canza kaya zuwa doguwar riga don za ta fi jin daɗin sa, sallah ta gabatar ta lallaɓa ta hau saman gadon gefen Walid ta kwanta, aikinta ta fara wato tunani, a haka har bata san barci ya ɗauke ta ba.

 

 

Bata san an yi sallar magriba ba sai Walid da ya farka ya hau tashinta, a firgice ta farka ganin Walid ne ya sa ta jin nutsuwa sai kuma ta ga lokaci ya ja.

 

“Anyi sallah ne?”

 

Ta tambayesa ya ɗaga mata kai ya ƙara da faɗin.

 

“Daddy ya shigo ki na barci har ya gyara miki kwanciya, ya tafi ɗauko Mimi a unguwa.”

 

Fararen idanunta ta zaro tana kallon yaron jin maganar da ya faɗa na farko, cikin inda inda ta nuna kanta.

“Ka ce ya shigo har ya gyara mini kwanciya, to waya buɗe ƙofar?”

 

“Ni ne na buɗe na fita wajensa sai muka shigo tare mu duba kin tashi, shi ne ya ga kin kwanta ba daidai ba ya gyara miki kwanciya.”

 

“Ya isa Walid! Kar ka ƙara buɗe ƙofar idan ina barci, ka tashe ni in buɗe maka ka ji don Allah.”

Ta ƙarashe maganar cike da alamar roƙo tamkar yaron ɗan shekaru shida zai fahimci yanayin da ta ke jin kanta.

 

Kai kawai ya ɗaga mata wanda Radiyya ba ta ƙara dubansa ba ta miƙe ta shiga bathroom, sai da ta yi kuka son ranta don baƙin cikin taɓata da ya yi kafin ta ɗauro alwala ta fito, cikin gaggawa ta yi sallar ta fita zuwa kitchen, abincin dare ta ɗaura mai saurin dahuwa, tana kwashewa a food flask mata da mijin suka yi sallama.

Walid da yake falo da gudu ya nufe su suna rige rigen ɗauka, Uncle Nasir ne ya yi nasarar ɗaukar sa suka ƙarasa cikin falon suna dariya gwanin sha’awa.

Radiyya ba ta fito ba sai da ta gama kwashewa ta ɗauka ta fita zuwa dinning ta ajiye sannan ta ƙarasa cikin falon, gefe ta durƙushe da ƙyar saman guiwarta mai ciwo tana yi wa Aunti Mimi sannu da dawowa.

 

“Yawwa Radiyya.”

 

Ta amsa da shi ta juya zuwa ga mijinta da yaronta, jiki a sanyaye Radiyya ta miƙe ta koma kitchen don ƙarasa sauran aiki, tattarewa ta yi ta gyara ta kimtsa ta fito don tafiya ɗakinta, babu kowa a falon alama sun shiga ɗaki, ita ma ɗakinta ta shiga ta kwanta, wayarta Nokia ta jawo tana latsawa. Ba ta da abokin hira ko abin karantawa balle ya ɗebe mata kewa, tunani shi ne abokin rayuwarta sai kuka da tsoro da suka zamto makusantanta na kusa.

Tana nan haka aka fara ƙiraye ƙirayen sallar isha’i ta tashi ta gabatar, tana cikin lazimi Walid ya shigo da gudu.

 

“Aunti ki zo in ji Mimi.”

 

Miƙewa ta yi tana riƙe da hannun yaron suka fita tare zuwa falon, saman dinning ta same su zaune kusa da juna.

Cikin siririyar muryarta ta yi musu sallama, Uncle Nasir ne kaɗai ya amsa ya mata kallo ɗaya ya ɗauke kai, Aunti Mimi harara ta watsa mata tana faɗin.

 

“Uwar me ki ke yi a ɗakin nan! Ke wace irin yarinya ce koyaushe sai an ƙira ki idan lokacin cin abinci ya yi. Radiyya ki kiyaye ni, ki kiyaye ranar da za ki shiga hannuna.”

 

Hawayen da yake ƙoƙarin zubo mata ta share cikin rawar murya ta ce.

“Ki yi hakuri Aunti, sallah na yi.”

 

Tsaki ta buga tana nuna mata saman dinning ɗin.

“Zuba mana abinci maza ki bar gurin nan, kar ki cika mini kunne da wannan banzan kukan ki da ba ya ƙarewa.”

 

Cikin sauri ta isa gurin ta zuba musu daidai yadda suke buƙata, tana ƙoƙarin barin gurin ta ji Uncle Nasir ya ce.

“Ke fa? Haka za ki zauna ko kin ci ne?”

 

“Na ƙoshi.”

 

Ta faɗa tana yin gaba, cikin sauri Aunti Mimi ta miƙe ta cafkota ta baya tana juyo da ita, kafin Radiyya tayi wani yunƙurin ta kwasheta da mari ta hau duka. Duk ƙoƙarin Radiyya ta ƙwaci kanta ta kasa, Walid na gefe yana kukan ta daina dukar masa Aunti, amma ina Aunti Mimi tamkar ta samu jaka haka ta dinga jibgarta, kuma dama idan ta fara sai ta ga dama take barinta.

Uncle Nasir da ya ga abun bana ƙarewa bane ya miƙe ya riƙo hannun Aunti Mimi da ƙarfi.

 

“Kashe ta za ki yi Mimi? Budurwa ƴar shekaru ashirin za ki daka? Idan ta miki laifi kamata ya yi ki mata faɗa ba duka ba.”

 

Cikin masifa Aunti Mimi ta dubi Radiyya da take kuka don ta bugu ba kaɗan ba ta ce.

“Kana gani ana mata magana tamkar sa’anninta ne suke mata, sam ba ta ji. Kuma idan ba ta nutsu ba watarana sai na karyata a gidan nan.”

 

Kallon Radiyya ya yi Uncle Nasir ya ce.

“Ta shi ki tafi ɗakin ki kin ji.”

 

Babu musu ta miƙe da ƙyar ta nufi ɗaki, saman gado ta faɗa tana fashewa da kuka. Tuni Walid ya bi bayanta ya faɗa jikinta suka ci gaba da kukan tare, ta kasa lallashin kanta balle shi, ta kowanne ɓangare ba ta samun sanyi.

….

 

Da ƙyar Uncle Nasir ya lallaɓa Aunti Mimi ta ci abinci ta wuce ɗakinta, yana ganin ta wuce ya ɗauki nasa abincin ya ƙara akai ya nufi ɗakin Radiyya, har bakin gadon ya ƙarasa ya zauna ya ajiye abincin saman bedside drower. Kallon su ya ke Walid tuni ya yi barci sai Radiyya da ta bawa ƙofar baya wanda hakan ya sa ba ta ji shigowarsa ba, hannunshi ya kai saman kugunta ya ɗaura tare da ƙiran sunanta.

 

“Radiyyatu.”

 

A mugun tsorace Radiyya ta juya kaɗan ya rage ta buge Walid don har ya motsa, bai cire hannunsa ba sai ma ƙoƙarin jawota jikinsa ya ke alamar rarrashi. Cikin rawar jiki Radiyya ta buge hannunsa tana ja baya, kafin yace wani abun ta sauƙa a gadon ta shige bathroom.

Tsaki Uncle Nasir ya buga ya miƙe ya fita a ɗakin cike da jin haushin ta, sam ta kasa sakin jiki da shi, duk yadda zai yi ya yi ta ƙi, abin har ya fara ishansa.

 

 

Radiyya lokacin ta kasa kuka, yawun bakinta da ruwan hawayenta ya kafe kaf, zama ta yi cikin bathroom ɗin tsawon mintuna, sai da ta tabbatar ya fice wajen mintuna goma kafin ta yi wanka da ruwan zafi wanda ta ji daɗinsa ta fito, kayan barci ta saka ta fesa turare sama sama, ƙofar ɗakin ta kulle ta bar mukullin jiki yadda babu yadda zai buɗe ta waje, sannan ta hau gadon, sai lokacin ta lura da abincin da ya kawo mata, ba ta bi ta kansa ba ta kashe wutar ɗakin ta kwanta gefen Walid, a tsorace da tunane tunane haka barci ya kwasheta.

 

 

Washegarin da asuba da ta farka ba ta koma ba, kafin mutanen gidan su farka ta yi shara ta goge falon ta yi wanke wankenta, fara ƙoƙarin haɗa breakfast Walid ya farka, sai da ta gama wajen bakwai da rabi ta masa wanka ta shiryasa cikin kayan makaranta sannan suka fito falon, abinci ta zuba masa ya ci ta ɗauki lunch box nasa suka fita ganin har lokacin iyayensa ba su farka ba balle du kaishi makaranta, kuma zai makara, shi yasa duk wata Uncle Nasir yake bata kuɗi don zirga-zirgar kai Walid da ɗaukosa wani lokaci.

 

 

Takwas da wani abu ta dawo gidan ta samu sun farka suna breakfast, har ƙasa ta durƙusa ta gaishe su, Uncle Nasir ne kawai ya amsa mata ta miƙe za ta wuce ɗakinta ta ji Aunti Mimi ta ce.

 

“Idan kin gama ki shirya da azahar Uncle Nasir zai zo za ku fita kasuwa.”

 

Cak Radiyya ta tsaya don jin maganar ta yi tamkar an buga mata guduma a tsakiyar kanta.

 

….

 

#vote

#comment

#share

DUHUN ZUCIYA

 

Shafi Na Biyu

 

Pharty BB

Wattpad PhartyBB

 

 

Tsoron nan da take ciki kullum shi ya ziyarci kwanyarta yayinda tashin hankali ya biyo baya, kallon su ta yi ƙoƙarin yi sai dai babu wanda hankalin sa yake gareta balle ya fahimci halin da take ciki, ita kaɗai ta damu da damuwarta da hatsarin da rayuwarta yake shirin faɗawa.

A sanyaye ta ja ƙafafunta zuwa cikin ɗakinta, ta rasa wani irin tunani za ta yi, tasan duk shirin Uncle ne da Aunti Mimi ba ta gano hakan ba, ba tasan yaushe za ta fuskanci halin da take ciki ba, ko ta samu ta sassauta mata nata matsin lambar, ta barta ta ji da ɗayan ɓangaren. Yaushe ita tana matar gidan amma sai ita za ta masa rakiya kasuwa.

‘To me zan masa?’

Ta tambayi kanta tana zama bakin gado tare da rafka tagumi. Tana tsoron keɓewarsu su biyun har cikin ranta, tsoron abin da zai je ya dawo take domin tasan ita za a cuta.

 

Kwala mata ƙiran da Aunti Mimi ta yi ya sa ta zabura ta miƙe da sauri ta fita tana amsawa. Samu ta yi ita ɗaya ce Uncle ya fita a falon.

 

“Ga ni Aunti.”

Radiyya ta faɗa yayin da take durƙusawa ƙasa.

 

“Ki gyara saman dinning ɗin sai ki ɗaura abinci mai sauƙi don ki yi ki gama ki shirya, kar ya zo ya yi ta jiranki na sanki da sanyin jiki.”

 

To Radiyya ta amsa da shi tana miƙewa. Tamkar yadda ta buƙata haka ta tattare gurin ta kai kitchen, sai lokacin ta yi breakfast kafin ta fara aikin. Guraren sha biyu da rabi ta gama komai tsaf ta wuce ɗakinta, wanka ta yi ta ɗaura alwala ta fito, doguwar riga ta saka da babban hijab har ƙasa, mai kawai ta shafa sai turare kaɗan marar ƙarfi ta feshe jikinta da shi, ba ta yi wani kwalliya ba bayan haka, don tsoron abin da zai faru take idan suka zamto su biyu ne. Sallah ta fara gabatarwa bayan ta idar ta fito falon, a daidai lokacin Aunti Mimi ta fito cikin shirin fita.

Kallo ɗaya ta yi wa Radiyya ta ɗauke kanta.

 

“Zan je ɗauko Walid a makaranta, idan Uncle ya zo ku tafi kawai.”

 

Da tana da halin magana da ta yi, roko ɗaya kaɗai za ta yi gareta, su fasa fita tare ko a fasa wannan tafiyar ita da Uncle Nasir. Kai kawai Radiyya ta ɗaga tana faɗin.

“To a dawo lafiya.”

 

Ba ta gama sauraronta ba tasa kai ta fita. Kasa zaune da tsaye Radiyya ta yi ta fara zagaye falon, ƙarshe ta ɗaura hannu saman kanta ta fashe da kuka, nan ƙasan falon ta durƙushe ta ci gaba da kukanta son ranta. Hanyar da za ta kufce masa take nema domin tseratar da rayuwarta.

Ta jima haka kafin ta miƙe tsaye da sauri ta fita a falon. Ba za ta iya jira ya dawo ya sameta ita ɗaya ba.

Bakin baranda ta zauna tana zabga tagumi ta zubawa ƙofar shigowa gidan ido.

Mintuna goma da zamanta aka danna horn, da sauri Mai Gadi ya fito a ɗakinsa ya buɗe get ɗin, motar Uncle Nasir ya danno kai ciki. Da Radiyya ya fara tozali, ta cikin motar suka haɗa ido Radiyya tayi saurin sunkuyar kanta ƙasa. Ya yi mamakin ganinta a waje zaune sai kuma tunanin Mimi ta fita ya sa shi buga tsaki.

Bayan ya kashe motar ya fito ya doshi gurinta, Radiyya na ganin haka amma ta ƙi tashi ta ƙara raɓewa jikin gini. Kusa da ita ya tsaya daf yana binta da kallo kafin ya ce.

 

“Tashi mu shiga ciki.”

 

Girgiza kai ta yi kanta a ƙasa har lokacin tana wasa da kyawawan yatsun hannunta, yayinda zuciyarta yake bugawa tamkar zai fado kirjinta.

 

“Nan ma ya isa.”

Ta furta tana tsoron abin da zai faru.

Bai ji haushin me ta faɗa ba, ya ƙara sassauta murya.

 

“Jira na kawai za ki yi na shirya idan na ci abinci sai mu tafi, na fiki son fitar mu tare Radiyyatu.”

 

Jin maganar sa na ƙarshe ya sata dubansa idanunta har sun kawo hawaye, wani irin kallon yake mata fuskarsa ɗauke da murmushi, ba ta san hawayen sun zubo ba sai ji tayi abu me ɗumi yana bin kumatunta, ba ta damu ta duba menene ba ta ce.

“Zan jira ka anan.”

 

“Shikenan, amma ki bar kukan nan.”

 

Yana faɗar haka ya wuce ciki, Radiyya ba ta daina zubar da hawaye ba har Uncle Nasir ya ɗauki tsawon mintuna talatin ya fito cikin shirin ƙananan kaya. Duba ɗaya ya mata ya ɗauke kansa ya nufi inda ya ajiye motarsa. Cikin sanyi jiki ta miƙe ta bi bayansa, motar ta buɗe ta shiga kamar yadda ta ga ya mata alama. Bayan ta zauna ta rufe ƙofar ya yi ribas ya danna horn Mai Gadi ya fito ya buɗe masa get ya fita, dai-dai lokacin Aunti Mimi ta iso a cikin nata motar. Tsayawa ya yi yana sanar da ita yanzu za su dawo ba za su jima ba, kai ta ɗaga tana ƙoƙarin yin gaba Walid ya saka kuka sai yabi su, duk yadda suka so ya yi shuru ƙi ya yi. Ganin haka Radiyya ta dubi Aunti Mimi.

 

“Aunti ki barshi mu tafi tin da ba jimawa za mu yi ba.”

 

Wani kallo Uncle Nasir ya watsa mata ta yi saurin rufe bakinta tana yin ƙasa da kanta. Juyawa ya yi ya kalli Aunti Mimi da ta rasa ya za ta yi, tsaki ya buga ya ce mata.

“Barshi ya zo.”

 

“Da kayan makarantar?”

 

“Babu komai.”

 

Dole ta buɗe masa ya fito ya zagaya wajen Radiyya, tana ganin haka ta buɗe masa ya shiga ya zauna saman cinyarta, sallama ya yi wa Aunti Mimi kafin ya ja motar. Suna cikin tafiya Uncle Nasir ya dube su suna magana ƙasa ƙasa.

 

“Ki na ganin kin kuɓuta ne? Sam ban yi niya ba ne don ina da hanyoyi da dama da zan yi amfani da su, kawai dai na fi son yardar ki.”

 

Radiyya da tasan da ita yake maganar ta ƙara ƙanƙame Walid tana karanto addu’o’in da duk ya zo zuciyarta na neman tsari daga sharrin sa. Ya saba ire-iren waɗannan maganganun idan su biyun ne, tasan da ƙarfi ne da tuni ya nuna mata.

Da ma yasan ba za ta tanka ba kamar kullum, haka yasa ya yi shuru ya ci gaba da tuƙi. A babban shago da ake ji da shi a garin ya tsaya ya fita, ita ma fitowa suka yi da Walid suka bi bayansa.

A ciki suka same sa zaune suna gaisawa da mutumin gurin, gefe suka tsaya, ganin haka ya mata alama da hannun ta ƙaraso wajen su. Ba ta kalli ko inda suke ba kanta a ƙasa ta ƙarasa wajen.

 

“Ki ɗauki duk abin da ki ka san ana buƙata na kayan azumi, ki ɗauki komai uku.”

 

To ta amsa da shi ta nufi wajen ajiye basket ta ɗauka ta fara zagaye cikin shagon da yake ɗauke da komai. Kayan shayi da duk tasan ana buƙata na azumi ta ɗauka, sai kayan abinci irin ƙanana, kamar yadda ya faɗa komai uku uku ta ɗauka. Walid yana biye da ita tana yi yana mata surutu. Bayan ta gama ɗauka ta kai gurin su, dubawa Uncle Nasir ya yi ya kalli mai shagon.

 

“A ƙara wasu abubuwan da kuma kayan abinci shinkafa da mai da macaroni da sauran su.”

 

Cikin umarni Mai Shagon ya ƙira yaran shagon sa aka ɗauka aka kai masa mota. Kuɗin su ya biya su har da ƙari, Mai Shagon yana ta murna, shi yasa yake son zuwansa siyayya shagon.

Bayan an gama suka musu sallama suka tafi, gida suka nufa kai tsaye.

Suna isa Radiyya ta yi saurin fita tare da Walid, da kallo ya bita har ta shiga falon, fitowa shi ma ya yi ya shiga cikin falon, Aunti Mimi ya samu kaɗai a falon, tuni Radiyya da Walid sun wuce ɗaki.

Abinci yasa ta kawo masa, tana ta faɗa me yasa Radiyya ba ta ba shi ba tun dawowarsa da farko, nan ya nuna mata shi ya so hakan.

 

Radiyya wanka ta yi wa Walid ta canza masa kaya kafin su fito a falon suka same su zaune, wajen dinning suka nufa ta zuba musu abinci ta zauna suka ci. Bayan sun gama ta tattare wajen ta kai kitchen, da ta ajiye ta fito ta samu Walid yana wajen iyayensa suna hira. Ɗakinta ta wuce ta kwanta don huta gajiya, tuni barci ya kwasheta ta manta ba ta rufe ƙofa ba kuma tasan ba zai zo mata ba yanzu saboda idon mutane.

Barci take mai daɗi hankali kwance, bata san inda kanta yake ba.

Wannan lokaci shi ya ba shi nasarar shigowa cikin ɗakin bayan Aunti Mimi ta ɗauki Walid sun fita zuwa gidan su kai musu kayan azumi.

Yadda ya sameta kwance ta yi ɗaiɗaiya tana barci shi yafi komai masa kyau, saman gadon ya ƙarasa ya zauna yana zubawa kyakkyawar fuskarta ido.

Radiyya kyakkyawar budurwa wacce take cikin ganiyar kuruciya, fara ce ba sosai ba, tana da kyakkyawar sura da zubin halitta da Allah ya bata, wannan yasa kullum tana cikin hijabi.

Sannu a hankali ya bita da kallo har zuwa saman kugunta da yafi komai burgeshi a jikinta, take shaiɗan ya ci gaba da buga masa gangarsa bai san lokacin da ya kai hannu ya fara shafarta ba tare da kwanciya ya rumgumeta.

Cikin barci Radiyya ta ji hakan, da farko ta ɗauka cikin mafarki ne tamkar yadda ta saba idan ta farka ta ga ƙarya ne, sai dai wannan lokacin ta ji abin na ci gaba har ana ƙoƙarin juyata a zare hijabin jikinta, duk da idanuwanta a rufe yake haka ta fara kokuwar kwatar kanta, ganin abun na ci gaba yasa ta buɗe ido ta ga zahiri ne ba mafarki ba. A mugun tsorace ta yi ihu, babu shiri ya rufe mata baki da hannunsa.

 

“Ki mini shuru, yau rana ɗaya ki bar ni in ɗanɗani zumarki Radiyyatu, zan ba ki ko nawa ne, zan miki gata da duk abin da ƴa mace take buƙata.”

 

Ya faɗa yana ƙara rumgumeta iya ƙarfinsa. Kuka Radiyya ta fashe da shi kafin ta samu nasarar cizon tafin hannunsa da ya rufe mata baki, babu shiri ya zare hannunsa yana yarfewa don cizon ya shige sa, hakan shi yabawa Radiyya damar ture sa iya ƙarfinta, bai yi zaton hakan ba dole ya yi tangal tangal zai faɗi ƙasa ya ga tana ƙoƙarin guduwa mafakarta wato bathroom, cikin zafin nama ya fizgo hijabinta ya wurgata saman gado tare da bin bayanta, ihu ta saka tana kuka tana roƙarsa ya rabu da ita.

 

“Don Allah Uncle ka rabu da ni, duk matan duniyar nan sai ni ɗaya, me na maka? Me na tare maka? Abin da ka ke ƙoƙarin aikawata gare ni haramci ne fa mafi muni, kar ka manta matsayin mijin yar uwata ka ke, wacce muke uwa ɗaya uba ɗaya.”

 

Bakinta ya buge, ya fara kokuwar cire mata hijabinta da ta cukwuikuye ta hanasa rawar gaban hantsi da shi.

 

“Ke kaɗai Radiyya nake buƙata. Mintuna ba zai wuce uku ba zan yi in gama. So nake in ji naki ni’imar, nasan za ki fi Mimi.”

 

Girgiza kai ta yi tana kuka tare da ƙanƙame jikinta. Addu’a take akan Allah ya kawo wani abun da zai dakatar da shi daga niyar sa akanta.

Duk roƙon duniyar nan ya yi Radiyya ta ƙi barinsa ya yi mu’amala da ita. Cikin jin haushi ya fizgota ya watsa mata mari tare da tureta ta buge kanta a kan gadon, wani azabebben ƙara ta sake tana fashewa da kuka. Ko kula da halin da ya barta bai yi ba yasa kai ya fice a ɗakin.

Radiyya na ganin haka ta lallaɓa ta sawa kofarta mukulli, anan bakin kofar ta durƙushe tana kuka.

Wani irin masifa ne yake faruwa da rayuwarta, mijin yar uwarta ya dinga nemanta ta ƙarfi. Wa za ta faɗawa ya yarda da hakan?

Dukkan su fuskar muminai yake nuna musu balle su yarda cewa shi ɗin zai aikata haka gareta. Ƙarshema tasan zaginta za su yi su ce sharri ta masa. Aunti Mimi fa tasan ranar kasheta ne kaɗai ba za ta yi ba.

 

Ba ta san lokaci yaja ba sai da ta ji hayaniyar Walid, agogo ta kalla ta ga kusan ƙarfe huɗu, cikin sanyi jiki ta miƙe a gurin tana ƙoƙarin barin gurin ta ji Walid ya buga ƙofar yana ƙiran sunanta, fuskarta ta goge da hijabinta ta kimtsa kanta kafin ta buɗe, rumgumeta ya yi yana murna.

 

“Aunti mun je gidan Umma tana tambayarki, ta bani zogale.”

 

Hawaye ne ya cika idanuwan Radiyya ta yi saurin ƙoƙarin hanasu zuba ta shafa kan Walid.

“Ya yi kyau, bari inyi sallah.”

 

Sakinta ya yi ta wuce bathroom, tana shiga ta jingina jikin ƙofar ta fashe da kuka.

 

“Allah ka nema mini mafita a wannan baƙin duhuwar rayuwar da nake ciki.”

Ta faɗi haka tana share hawayenta

Sai da ta yi kuka mai isarta ta ɗauro alwala ta fito, ba ta samu Walid a ɗakin ba, ta gabatar da sallah kafin ta fita waje, duk suna zaune a falon, ba ta kalle su ba ta fara ƙoƙarin wucewa kitchen Aunti Mimi ta ƙirata.

 

“Ke zo ga shi Umma ta ce na kawo miki.”

 

Baya ta dawo ta ɗauki ledar da ta nuna mata ta wuce da shi kitchen, tana shiga ta buɗe, kayan ci ne na gargajiya su tsamiyan biri da taura da aduwa, tattarawa tayi ta mayar ledar ta ajiye sannan ta hau yin aikinta. Abincin dare ta yi ta kwashe ta jera saman dinning ta wuce ɗakinta, sai da aka yi sallar isha’i ta yi sannan ta fito jin hayaniyar su kafin ta ci duka irin na jiya, samun su tayi saman dinning ta ƙarasa ta zuba musu ta ɗebi nata ta bar gurin, babu wanda ya ce mata ci kanki.

Har ƙarfe goman dare tana jiran zuwan Walid shuru bai zo ba, hakan yasa ta zauna jikin gadon ta jinginar da kanta tana jiransa akan idan ya shigo ta kulle ɗakin kar ya zo ya yi ta bugawa ta yi barci, tun tana ƙoƙarin kokuwa da barcin da yake son kwasarta har yayi nasarar saceta ta kifa kanta kan katifa, jikinta a jingine da gadon.

 

 

Suna gama cin abincin ya miƙe, da kallo Aunti Mimi ta bisa.

“Kana bukatar wani abu ne?”

 

“Juice zan ɗauko.”

 

Ya ce ya wuce Kitchen kafin ta ƙara wani maganar, abincinta ta ci gaba da ci.

Can ya fito riƙe da kwalin 5alive da cup ya tsiyaya yana sha, na goran ya ajiye saman dinning ya ci gaba da shan na kofin hannunsa, tas ya shanye sannan ya zuba ya miƙawa Walid, babu musu yaron ya karɓa ya hau sha, ganin haka Aunti Mimi ta ɗauke na kwalin.

 

“Ni ma zan sha tun da abin son kai ne.”

 

Murmushin gefen baki Uncle Nasir ya yi ya ce.

“Da kinyi hakuri zan ba ki rabon ki.”

 

Ba ta kulasa ba ta kafa baki ta hau sha, murmushi kawai Uncle Nasir ya yi ya miƙe.

“Idan kun gama na shiga ciki.”

 

Daga haka ya wuce ɗaki ya yi shirin barci, ya ɗauki kusan mintuna sha biyar ganin shuru ya fito falon, samun su ya yi duk sunyi barci a saman kujerun falon, Aunti Mimi ya fara ɗauka ya kai bedroom ya kwantar ya dawo ya ɗauki Walid ya kai ya kwantar gefenta, sannan ya kashe wutar ɗakin ya kulle ɗakin da mukulli, yasan sai nan da awanni biyar cib maganin barcin da ya zuba a juice ɗin zai sake su, kafin nan yana da ishashshen lokaci da zai ishesa ya yi komai.

Wutar falon ya kashe ya nufi ɗakin Radiyya, yau ko ta ƙarfi sai ya nemeta sai dai duk abin da zai faru ya faru, tsoron sa ɗaya dama ya nuna mata ƙarfi ta ji ciwo asirinsa ya tonu, amma idan ta ba shi haɗin kai a hankali zai bi da ita.

 

….

 

#vote

#comment

 

DUHUN ZUCIYA

 

Shafi Na Uku

 

Pharty BB

Wattpad PhartyBB

 

Murɗa hannun ƙofar ya yi tare da turawa lokaci guda, buɗewa ƙofar ya yi, wutar lantarkin ɗakin a kunne hakan shi ya ba shi damar hangota zaune a ƙasa ta ba ƙofar baya, kanta ta kwantar a kan gadon, duk zaton sa idonta biyu. Ƙofar ɗakin ya tura a hankali ya shiga sannan ya kulle har da sa mukulli.

 

‘Yau ƙudiri na zai cika.’

Ya faɗa a ransa yana dumfararta cikin takun da babu sauti, har ya isa wajenta ya durƙusa saman guiwowinsa ba ta motsa ba. Leƙa fuskarta ya yi ya ga idonta rufe, anan ya ga barci take a hakan, murmushi ya yi ya miƙe tsaye, sai kuma ya duƙa ya ɗagota sama don kwantar da ita saman gado.

 

Wannan motsi da taɓata da aka yi shi ya farkar Radiyya daga barcin da ya kwasheta.

 

“Walid!”

 

Ta furta duk tsammaninta shi ne, sai kuma ta ji ana shirin yin sama da ita alamar ɗauka, ba ta faɗi abin da zai fito daga bakinta ba ta ji an kwantar da ita bisa gado.

‘Mutum ɗaya ne zai min haka.’

Zuciyarta ya sanar mata da wannan saƙon. Take wani mugun tsoro ya ziyarci zuciyarta da ilahirin jikinta gaba ɗaya. Idanuwanta ta buɗe fes bisa fuskarshi, hasken lantarki ɗakin shi ya ba ta damar ganin shi.

 

Murmushi ya sakar mata, tare da ɗaura hannu ɗaya saman fuskarta ya shafa.

 

“Kyakkyawa.”

Ya furta yana ƙoƙarin yin ƙasa da hannunsa zuwa wuyarta zai zare hijabin jikinta, kuma ya cukwuikuyeta ya hanata motsin kirki.

 

Fassara tashin hankali da Radiyya take ciki abu ne mai wuya a lokacin. Ji ta yi duniyarta da komai nata ya tsaya, kukan ma ta kasa sai bugun da zuciyarta yake tamkar zai faso kirjinta, magana kam yawun bakinta ya kafe balle ta samu furta wani abin.

Shurunta shi ya ba Uncle Nasir damar ci gaba da abin da yake mata, juyata ya fara son ransa har ya samu nasarar zare mata hijabi, da kallo ya bi kyakkyawar surar jikinta da shi, nan shaiɗan ya ci gaba da buga masa gangarsa.

Radiyya tana ji sannan tana gani ana neman rabata da mutuncinta da darajarta na ƴa mace, abu mafi ƙima a tare da ita, za ta rasa shi ta hanya mafi muni. Dukkan wani guntun ƙarfinta da jarumta ta tattaro ta sa hannuunta biyu ta ture sa, baya ya yi babu shiri don bai tsammaci haka ba. Ganin haka ta sake saka ƙafar damarta ta bugeshi inda ya sauka gefen cikinsa na hagu. Babu shiri Uncle Nasir ya saki ƙara tare da dafe cikin yana yin baya.

Hakan ya ba Radiyya damar miƙewa ta kwasa a guje sai bathroom,  mukulli tasa tana jingina jikin ƙofar. Zuciyarta ta dafe tana sauƙe numfashi domin wannan karon hawayen ya ƙi zuwa mata, kuka take son yi ko za ta ji sauƙin abin da take ji, tsoro da tashin hankali ya hanata tabuƙa komai, ganin abin Uncle Nasir take ya fara wuce rashin tausayi sai dai rashin tsoron Allah. Ba ta san lokacin da ta sulale ta zauna daɓas a ƙasa ba.

 

 

Iya wahala ya wahala don bai taɓa tsammanin haka daga gurinta ba, cikinsa riƙewa ya yi sosai sai fitar da numfashi yake yana haɗa zufa. Sai da ya samu nutsuwar hankali ya lura da Radiyya ta jima da barin gurin, tsaki ya buga ya miƙe da ƙyar yana dafe cikinsa ya fita, nan saman kujerun falon ya zube yanata juyi har barcin wahala ya kwashesa a gurin.

 

 

Radiyya wani abu mai suna barci ranar ba ta yi ba, yadda ta ga dare haka ta ga wayewar asuba, tana jin ƙiraye-ƙirayen sallar assalatu a hankali ta miƙe daga zaunen da take a rakuɓe. Alwala ta yi, ba ta yarda ta fito ba sai da ta leƙa ta tabbatar babu kowa ɗakin, dama tasan zuwa war haka ya fita. Cikin sauri ta fito ta nufi ƙofar ɗakin ta kulle da mukulli, sai lokacin ta ɗan ji nutsuwa ya shigeta. Hjabi ta ɗauka ta fara nafila, har aka fara sallar asuba sannan ta gabatar, ta jima tana addu’a akan Allah ya kawo mata mafita a rayuwarta sannan ta shafa.

Sai da haske ya fara haskaka ɗakin alamar rana yana fitowa kafin ta fita falon a tsorace, babu kowa ciki, hakan ya ba Radiyya damar fara gabatar da aikinta. Tana cikin haɗa breakfast Walid ya fito cikin kayan barci, kasancewar weekend ne babu makaranta kuma iyayen ba su yi ƙoƙarin sa shi makarantar islamiyya ba.

 

Rumgumeta ya yinta baya yana faɗin.

 

“Aunti jiya wajen Mimi na kwana.”

 

Juyowa ta yi da murmushinta mai kyau tana kallonsa ta ce.

“Babu komai. Ka tashi lafiya?”

 

“Lafiya lau. Sai dai Daddy babu lafiya, yana kwance tun safe.”

 

Dum zuciyar Radiyya ya buga jin ya ambaci rashin lafiya ga mahaifinsa.

‘Kar ya zamto dalilinta ya ji wani ciwon!”

Ta faɗa a ranta cikin tsoro. Sakin Walid ta yi ba ta ce komai ba ta juya jiki a sanyaye, aikinta ta ci gaba da yi duk da maganar da ya faɗa mata ya ƙi barin ranta. Haka ta daure ta gama, bayan ta gama ta ja Walid zuwa ɗaki, ta masa wanka ta canza masa kaya sannan tayi suka fito, har za ta wuce dinning ta ji dai gwara ta leƙa ta gaishe sa kafin Aunti Mimi ta mata rashin mutunci. Tana riƙe da hannun Walid suka yi sallama a ƙofar ɗakin Aunti Mimi. Amsawa ta yi tana basu izinin shiga kafin suka shiga, can gefe Radiyya ta rakuɓe tana durƙusawa har ƙasa ta gaisheta tana tambayar mai jiki.

 

Sai lokacin Uncle Nasir ya buɗe ido ya kalli Radiyya, ido suka haɗa ta yi saurin yin ƙasa da kanta zuciyarta na bugawa.

 

“Zo nan Radiyya.”

 

Uncle Nasir ya faɗa ƙasa ƙasa. Radiyya yi ta yi tamkar ba ta ji ba ta ci gaba da wasa da gefen hijabinta, kuma ta kasa tashi. Tsawar da Aunti Mimi ta daka mata ya sa ta miƙewa babu shiri.

 

“Don ubanki ba ƙiranki yake ba! Ke wai wace irin yarinya ce?”

 

Idanun Radiyya cike da hawaye ta kasa barin su su zubo don gudun yin wani laifi, haka tamkar mai taka wuta ta dinga jefa ƙafafunta har ta isa bakin gadon da yake kwance, tana ƙoƙarin durƙusawa ƙasa ya mata nuni da ta zauna bakin gadon.

Kallon shi ta yi ta ga ya zuba mata mayun idanuwansa, kanta ta sunkuyar ƙasa tana girgizawa duk lokaci ɗaya alamar a’a ta durƙusa ƙasa saman gwuiwarta.

Aunti Mimi ya kalla da ta mayar da hankalinta kan Walid, ɗauke kai ya yi ya kalli Radiyya murya ƙasa ƙasa ya ce.

 

“Ki sani kin ci bashi Radiyya, zan rama, kuma zan yi ko ta ƙarfi.”

 

Da sauri Radiyya ta kallesa ya ɗauke kansa tamkar ba shi ya yi maganar ba, hawayen da take ɓoyewa ne suka zubo bisa kumatunta, cikin sauri ta goge su ta miƙe tana fita a ɗakin, ɗakinta ta wuce tana kukan da ya samu ƙwace mata. Saman gado ta faɗa ta fara sosai.

‘Wani irin mutum ne Uncle Nasir! ba ya nufi na da komai sai sharri!’

 

Kuka Radiyya ta yi son ranta kusan mintuna kafin ta miƙe zumbur, gurin kayanta ta nufa ta dinga ciro duk wanda tasan zai mata amfani ta tusa a babban jaka, tsaf ta gama shiryawa, ta riga ta aminta da shawarar da zuciyarta ya ba ta. Gefe ta ajiye bayan ta gama.

Tana zaune har kusan ƙarfe sha ɗaya, babu wanda ya damu da cinta da shanta a gidan, babu wanda ya nemi ba’asin zamanta na tsawon lokaci a ɗaki, yunwar cikinta ya sa ta fitowa zuwa falon, babu kowa ta tarar. Har ta nufi dinning da sauri kuma ta koma ɗakinta ganin ta samu damar da take jinkirin zuwanshi, jakan kayanta ta ɗauka ta fito cikin sanɗa har ta samu nasarar fita zuwa get. A hankali tasa hannu ta fara ƙoƙarin buɗe ƙofar jikin get ɗin.

 

“Waye nan?”

Faɗin Mai Gadi yana fitowa daga ɗakinsa jin motsi.

 

Maganarsa ba ƙaramin tsorata Radiyya ya yi ba, juyawa ta yi da sauri ta ganshi tsaye. Cikin rikicewa da ƙyar ta lalibo ta haɗa daidaitacciyar magana ta ce.

“Aike na aka yi.”

 

“Waye? Alhaji ya hana ni in buɗe miki ƙofa, don haka ki koma ciki, idan ya fito na tambayesa ya amince sai ki fito in buɗe miki.”

 

Kurr cikin Rabi’atu ya bada ƙara jin abin da Mai Gadi ya faɗa, wato kulleta zai fara yi domin ya samu damar cutarta. Take dabara ya faɗo mata, ta ƙirƙiro murmushin dole don kar ganota ta ce.

“Tare da Walid za mu fita, kuma ba zai yi sauri ba shine zan tafi kawai, wallahi ba zan jima ba, kasan dai duk inda na je ina dawowa.”

 

Kamar bai yarda da ita ba, don daren jiya Uncle Nasir ya hanasa akan yana barinta fita, hatta zuwa kai Walid makaranta da ɗaukowa ya ce zai fara yi da kansa, don haka kar ya yarda ya barta ta fita.

Yanayin da fuskarta ya nuna ya hango kamar tana buƙatar fitar. Take wani zargi ya ɗarsu a zuciyarsa ya dubeta.

 

“To wannan jakar fa?”

 

“Kaya ne zan kai aike.”

Ta faɗa cikin sauri ganin kamar ya fara yarda da ita.

 

“Ki yi haƙuri ki koma ciki, bazan iya saɓa umarnin Alhaji ba.”

Daga haka ya matsa ya mayar sakatar da ta cire ya koma saman farin roba ya zauna.

 

Cikin sanyin jiki Radiyya ta ja ƙafarta ta koma cikin falon, har lokacin falon babu kowa, cikin sassarfa ta wuce ɗakinta ta kulle kanta, yunwar ma ta daina ji tsabar haushi. Zama ta yi ta zuba tagumi tana maganar zuci.

 

‘Yaushe zan samu farin ciki? Tsawon lokaci farin cikina ya gushe. Ba zan kwana na tashi ban zubar da hawaye ba, babu ranar da ba ya wucewa ban shiga yanayi na firgici da tsoro ba. Duk abin da yake min yanzu kuma zai kulle ni tamkar akuyar gidan shi.’

 

Tsanar sa ne ya linku cikin ranta banda wanda akwai shi dama, tsana mafi yawa ta ji take masa.

 

 

A hankali ya saki labulen windown yana sakin shu’umin murmushi, dama ya san hakan zai faru shi ya sa ya yi wa tufkar hanci tun wuri.

Aunti Mimi dai da idanu ta bisa bayan fitowarta daga bathroom ta gama haɗa masa ruwan wanka, yanzu ta barshi kwance ta shiga bathroom, kuma ta fito ta ganshi tsaye jikin window.

 

“Na gama haɗa ruwan.”

 

Ta sanar masa tana nufan wardrobe don ciro masa kaya.

 

“Thanks.”

Ya faɗa ya wuce cikin bathroom don yin wanka jin ciwon cikin ya lafa.

 

 

Har wajen ƙarfe sha biyu Radiyya ganin yunwa na neman halakata ya sa ta fitowa zuwa falo, wajen dinning ta nufa ta hau tattare gurin, ta gyara sannan ta yi breakfast ta hau girkin rana. Abinci mai sauƙi ta dafa musu ta jera ta deɓi nata ta wuce ɗakinta, kulle ƙofar tayi kamar koyaushe.

 

Har daren ba ta ƙara saka kowa a idanuwanta ba hatta Walid, sai dai ta ji motsi a falon wanda ta tabbatar na Aunti Mimi ne a cewarta tana jinyar mijinta.

Ƙarfe goma aka ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin, ta tsorata da jin hakan, amma dole ta miƙe ta nufi baƙin ƙofar ta tsaya.

 

“Waye ne!”

Ta tambaya a ɗan tsorace.

 

“Ubanki ne, za ki buɗe ƙofar.”

 

Ta ji muryar Aunti Mimi. Cikin rawar jiki ta buɗe tana yin gefe, tasan za ta iya kai mata duka. Harara ta watsa mata ta ce.

“Ki zo ki ɗauki Walid ya yi barci.”

 

Tana faɗar haka ta bar gurin, da sauri Radiyya ta bi bayanta har zuwa ɗakinta, Uncle Nasir baya nan hakan ya bata damar nutsuwa ta ɗauki yaron, tana shirin fita a ɗakin ya shigo, da sauri ta ba shi guri ya wuce kafin ta fice da sauri zuwa ɗakinta.

Bayan ta kwantar Walid ta kulle ƙofar ɗakin, bathroom ta wuce ta ɗaura alwala ta fara nafila don neman mafita ma rayuwarta. Har ƙarfe biyun dare ta kasa barci, ganin babu komai babu kuma wani motsin ya sa ta kwanta nan saman darduma, tuni barci ya ɗauketa.

Ƙiran sallar farko a kunnenta, ta farka da sauri, alwala ta shiga ta yi ta fito ta yi sallah a gaggauce jin masallacin da yake gefen su sun kusa idarwa. Tana idarwa ta ɗauki jakar kayanta da ƙaramin jakarta ta nufi ƙofa, a hankali ta buɗe ƙofar ɗakin ta leƙa kanta ta ga wutar falon a kashe da duhu falon, cikin sanɗa ta fita har zuwa bakin ƙofar falon ta cire lock ta buɗe, fit ta fice har zuwa get din inda ta ci sa’a a buɗe Mai Gadi ya tafi sallah, shi ya sa ta yi dabaran fita da asubahi kafin ya dawo.

Cikin sauri ta fice a gidan tamkar za ta tashi sama, tafiya kawai take babu ji babu gani burinta ta ganta inda take son zuwa, har gari ya fara haske Radiyya tana tafiya har rana ya fito mutane suka fara fitowa. Unguwar da take son zuwa nisa ne da shi kuma sam tunanin hawa abu bai zo ranta ba. Ƙarfe bakwai da mintuna ya sameta ƙofar gidan da take son zuwa duk ta gaji ta galabaita.

Tsayawa ta yi ta kasa shiga cikin gidan, tunaninta ɗaya idan aka tambayi dalilinta na zuwa, sannan wani irin rayuwa za ta fara gudanar a gidan idan har sun karɓeta.

 

Hayaniyar da ta ji yana tasowa a cikin gidan ya sa ta shiga da sauri babu shiri. Hango matan gidan biyu ta yi suna cacar baki. Gefe ta rakube tana kallon su inda suke surfawa junan su zagi tamkar yara ƙanana duk sun hargitsa gidan. Ganin suna shirin kaiwa juna bugu kuma babu mai musu magana ya sa Radiyya sakin jakar hannunta ta yi gurin da sauri.

 

“Don Allah Umma ki bari, ki yi haƙuri.”

 

Tace tana kamo hannun mahaifiyarta.

Umma masifa ya cinye idonta ta nuna amarya Zulaiha da yatsa.

“Zan canza miki kamanni Zuhaila, albarkacin Malam ki ke ci wallahi, da na jima da koya miki hankali na rantse.”

 

Zulaiha da take baƙin ƙofar ɗakinta ta riƙe kugu tana jijjiga.

 

“Idan kin fasa Zuhra! Ƙarya na yi ne? Ƙarya na yi ba a yawon ta zubar ki haife su ba, ko akwai wanda ya taɓa kallon uban su, ko kika sanar cewa ga ubansu nan.”

 

“Ubanki ne ubansu Zulaiha, da shi nayi yawon ta zubar ya mini ciki na haifesu.”

Umma ta ce tana ƙoƙarin yin kan Zulaiha cikin tsananin ɓacin rai.

 

Radiyya baƙin ciki ne ya ziyarci zuciyarta, wannan rashin hankali da su ke gwadawa juna yafi ƙarfin ƙwaƙwalwarta, da girman su da hankalin su ga yara duk sun kewaye su suna kallo. Tunanin da ta tafi na wucen gadi shi ya ba Umma damar kwatar hannunta ta yi kan Zulaiha. Ihun da ta ji shi ya dawo da ita hankalinta ta kai dubanta gurin, Umma ta hango ta hau kan Zuhaila da duka, suna kokuwa yaran Zulaiha na ƙoƙarin kwatar mahaifiyar su hannun Umma.

Cikin zafin nama Radiyya ta yi gurin, ta fara ƙoƙarin ɗago Umma tare da ba ta haƙuri.

 

“Umma don Allah ki yi haƙuri, wannan ba girmanku ba ne wallahi.”

 

Hankaɗata Umma ta yi cikin masifar da ya rufe idanunta.

“Ki bar ni da ita Radiyya, sai na koya mata hankali yau.”

 

Zulaiha da ta ci wuya duk da haka bakinta bai mutu ba, tana ƙoƙarin kwatar kanta ta ce.

“Ƙarya aka yi ne, idan wasu sun ji tsoron faɗa miki ni na faɗa. Ta je yawon ta zubar an dawo da shegu.”

 

“Don Allah Aunti amarya ki daina faɗar haka, Umma don Allah kibyi haƙuri, da girmanku bai kamata ba.”

Faɗin Radiyya tana kuka, maganganun Amarya Zulaiha ba su dameta ba don sam ba ta fahimce su ba.

Ganin sun kasa rabuwa yasa Radiyya tashi daga durƙushen da take ta nufi ɗakin Uwargidan Malam. Daga bakin ƙofar ta tsaya cikin kuka ta ce.

 

“Inna ki fito ki musu magana don Allah su rabu da juna.”

 

“Idan sun ga dama su cinye junan su.”

Inna ta faɗa daga cikin ɗakin. Fitinar su ya isheta.

 

Jin abin da ta fada da sauri Radiyya ta bar gurin, dama ba ta sa ran za ta yi magana ba. Wajen su ta koma tana roƙar su akan su rabu. Ƴan matan gidan wasu na dariya.

 

“Kai kai kai menene haka!”

 

Suka tsinci muryar Malam da tun shigowarsa daga zaure yake jin hayaniya, sai da ya shigo idonsa ya gane masa abin da ke faruwa. Cikin sauri ya ƙarasa wajen yana ɗago Umma saman Zuhaila da ta yi kaca kaca da ƙasa, kanta ya yi buzu buzu ya ɗebe ƙasa.

Bayan Malam ya yi nasarar raba su ya ɗago Zulaiha, yana duban kowa ransa a ɓace ya ce.

 

“Kowa ya nutsu, me ya ke faruwa haka. Zuhra lafiyarki? Matar nawa za ki danne haka kina jibga kamar jaka.”

 

Zuhaila da ta ji mijinta ya hau Umma da faɗa ta fashe da kuka tana karkaɗe ƙasar jikinta.

“Malam tun safe take zagina.”

 

“Ku same ni a ɗakina dukkan ku. Har ke Radiyya.”

 

Daga haka ya wuce ya bar gurin. Umma juyawa ta yi ita ma ta bar gurin ko a jikinta. Radiyya hawayenta ta share ta je ta ɗauki jakar kayanta ta nufi ɗan ƙaramin ɗakin da Umma take, tana ƙoƙarin shiga Umma ta fito, harara ta watsa mata ta wuce, cikin sanyin jiki Radiyya ta shiga cikin ɗakin da babu komai sai ƴar katifa da taburma a shimfiɗe, gefe wajen kayan Umma ne cikin akwatuna. Gurin ta ajiye nata jakar kayan ta fita a ɗakin don amsa ƙiran Malam.

Malam, Inna Saudatu, Zuhaila da Umma ta samu a falon, sallama ta yi Malam kaɗai ya amsa, ta shiga ta samu guri ta zauna. Shuru ɗakin ya ɗauka ta ji Malam ya ƙira sunanta yana karawa da faɗin.

 

“Radiyya yaushe ki ka zo? Sannan me ya faru tsakanin Zuhra da Zulaiha?”

 

Kanta ta sunkuyar ƙasa murya ƙasa ƙasa ta ce.

“Yanzu na zo, na shigo na tarar Umma da Aunti amarya suna cacar baki, duk yadda na so su rabu sun ƙi.”

 

“Kenan babu abin da ki ka ji na farkon faɗar?”

 

Kai ta ɗaga har ila lokacin kanta a ƙasa. Duban matansa ya yi ya ce.

“Kul kar na ƙara ji ko gani wani faɗar ya taso a cikin gidan nan. Zuhra ke ce babba. Zulaiha ki ba ta girmanta, duk ba zan so na ɓata muku rai ba. Saudatu duk kin fi su, amma ki na zauna ki na ji ana wannan faɗar.”

 

“Au laifi za ka ɗaura min?”

Faɗin Inna Saudatu cikin faɗa.

 

“Ba haka ba ne, ya kamata ki musu magana idan su na haka.”

 

Ba ta tanka masa ba ta juyar kanta tana gunguni. Doguwar tsaki Umma ta ja tsabar takaicin ganin sam ba ya iya mata faɗa. Malam Baba Ƙarami da kamar ruwa ya cinyesa ya ce.

 

“Za ku iya tafiya, ke Zuhra da Radiyya ku zauna.”

 

Cikin fushi Zulaiha da Inna Saudatu suka fice a ɗakin. Kallon Radiyya ya yi da kanta yake ƙasa.

 

“Me ya kawoki gida? Ba shekaran jiya yayarki ta zo ba.”

 

Shuru Radiyya ta kasa amsa tambayoyin da ba ta da amsar su.

 

….

 

#votes

#comments

#keeplove

 

DUHUN ZUCIYA

 

Babi NA Huɗu

 

Pharty BB

Wattpad PhartyBB

 

Ruwan hawaye ne ya taru a idanuwan Radiyya, dama ta san da ƙyar su yarda da barinta ta zauna. Ba ta da amsar da zata ba su, tsoron sanar da gaskiya take su ƙi yarda.

Sauƙar dukan da ta ji a haɓarta ya sa ta dawowa daga duniyar da ta faɗa.

 

“Don ubanki ba tambayar ki ake ba! Me ya kawo ki?”

Faɗin Umma a zafafe, sanyin halin Radiyya yana ba ta haushi, sam yarinyar ba ta da zafi kamar ita ko Mimi.

 

Radiyya hawayen da suka zubo mata a fuska tasa hannu ta share, cikin rawar murya ta ce.

“Baba zan zauna ne anan in yi azumi.”

 

“Ita Auntinki ta yarda ne? Ko Nasir ɗin?”

Baba Ƙarami ya sake mata wani tambayar.

 

Girgiza kai ta yi wani hawayen yana zuba mata, wannan lokacin ba ta share ba ta ce.

“Ni kawai na zo ne. Don Allah kar ku ce in koma, ku barni na zauna tare da ku.”

Ta ƙarasa maganar cike da alamar roƙo. Idan suka ce ta koma gidan nan mai cike da duhun da ya shafi zuciyarta tabbas za ayi ɗayan biyu.

 

Umma da ta hasala ta nuna Radiyya da yatsa.

 

“To don ubanki sai kin koma yanzu ba gobe ba. Ina zan iya miki ga ni ga ke.”

 

Fashewa da kuka Radiyya ta yi ta rarrafa wajen Baba Ƙarami.

“Don Allah Baba ka sa baki Umma ta barni na zauna anan.”

 

“Kin san zaman gidan nan Radiyya?”

Tambayar da Kawu ya mata kenan ganin tamkar tafi son hakan. Ga inda za ta ci mai kyau, ta sha mai kyau, ta kwana a guri mai kyau, amma ta zaɓi tahowa inda ci ma yana gagaran su balle wasu abubuwan.

 

Umma jin abin da ya faɗa ya sa ta ƙara hasala ta kalli Baba Ƙarami ta ce.

“Ba za ta zauna ba fa Malam.”

 

Radiyya cikin kukan da take jin zafinsa har cikin ranta ta ce.

“Umma zan riƙe kai na, idan dai don ci da sha ne. Ku bani gurin kwana kawai ya wadatar.”

 

“Tashi ki j Radiyyae.”

Faɗin Baba Ƙarami ya dubi Umma da ta haɗa rai sosai. Cikin lallami ya ce.

 

“Ki barta ta zauna a gurinki Zuhra tun da ta amince. Abinci ba zai gagari a bata ba idan an dafa, sauraran abubuwan kuwa ta iya wa kanta, idan kuma za ki iya mata to shikenan. Ita kuma Mimin idan ta biyo sawu sai a sanar mata, daga nan mu ji dalilin tahowarta tun da ta ƙi sanar mana.”

 

Umma ba ta jira mai zai ƙara ba ta fice ranta ɓace. Ɗaki kai tsaye ta wuce ta samu Radiyya zaune ta buga uban tagumi. Daga alama tunanin sabuwar rayuwa da za ta fara take. Gida mai cike da mutane kala-kala, kowa rayuwarsa yake da yaransa, tsakanin su da Mai Gidan ciyarwa, shi ma sai ya nemo da ƙyar a sana’arsa na Dukanci. Shi ya sa a gidan kowa rabi shi yake rike da kansa da yaransa.

 

Ko kulata Umma ba tayi ba, aikin da za ta yi na wanki ta tattaro ta watsawa Radiyya a fuska. A firgice ta ankara da haka, sai lokacin ta dawo hankalinta ta fara tattare kayan tana kallon Umma da take kunce bakin ɗaurin zanin jikinta, duk ya mutu ya tsufa. Tana kallo ta ciro canji canji na kuɗi da idan aka haɗa ba zai wuce dubu ɗaya ba, ɗari biyu ta ware ciki ta mayar sauran ta kulle sannan ta kalli Radiyya da take ta kallon mahaifiyar nata.

 

“Ga shi ki siyo omo da sabulu na ɗari da hamsin, ki zo ki min wanki tun da Allah ya kawoki.”

 

Babu musu Radiyya tasa hannu ta karɓi kuɗin da Umma take miƙa mata, sannan ta miƙe tsaye. Har ta kai bakin ƙofa ta tsaya, sai dai ta kasa faɗin abun da ke ranta har sai da Umma ta tambayeta.

 

“Lafiya kuwa?”

 

“Umma ban yi karin kumullo ba.”

A tsorace Radiyya ta faɗin hakan, don ba ta san mai zai biyo baya ba.

 

Murmushin ƙyeta Umma ta yi ta ce.

 

“Ai kuwa babu komai, sai dai ki jira na rana idan sun girka su tsakura miki. Ke da kanki ki ka yarda za ki riƙe kanki fa Radiyya, tun yanzu kin fara nema ina ga gaba? Idan akwai canji a wajenki ki siya wani abun, domin ni ma bani da komai.”

 

A sanyaye Radiyya ta dawo baya ta buɗe jakanta, ƙaramar fos nata ta ɗauka ta fita gaba ɗaya a ɗakin. Umma duk tana binta da kallo, bayan fitarta ta buga tsaki ta miƙe, sam yarinyar ta kasa wayewa irin na yaran zamani.

 

 

A shagon bakin titi Radiyya ta siyo sabulu da omo, tare da ƙosai da bireda na Naira ɗari ta kamo hanyar gida. Tana tafiya tana tunanin sabuwar rayuwar da za ta fara gudanarwa, fatanta da addu’arta Allah ya sa Uncle Nasir ko Aunti Mimi idan sun biyo sawu kar ace ta koma. Da wannan tunanin ta isa gida, kowa harkar gabansa yake a gidan, ɗakin Umma ta wuce ta samu ba ta ciki kuma ba ta filin gida. Zama ta yi ta ci abin da ta siyo, bayan ta gama ta miƙe ta tattari kayan wankin ta fita dashi, bakin rijiya ta ajiye ta ɗauko bokati da baho ta ɗebe ruwa ta fara wankin, babu wanda ya mata magana haka ita ma ta mayar da hankali a aikinta.

Tana cikin yin wankin ta yi rabi Umma ta yi sallama ta shigo, kai tsaye wajen Radiyya ta yi ta tsaya saman kanta.

 

“Sannu da dawowa Umma.”

Faɗin Radiyya bayan ta ɗago ta dubi Umma, ta sunkuya ta ci gaba da aikinta.

Kai Umma ta ɗaga ta wuce ɗaki don hutawa, kitso maƙota ta shiga yi. Sana’arta kenan wanda da shi ta riƙe kanta a gidan, sai abin da Uncle Nasir ya aiko musu na kayan abinci ko Mimi ta ba ta kyauta.

 

….

 

Tsaf Radiyya ta zage ta yi wa Umma wanki ta shanya wajen ƙarfe goma da rabi, tana cikin tattare gurin ta ji sallamar da ya sa zuciyarta bugawa har kanta ya sara. Sallamar Aunti Mimi kenan tare da shigowa cikin gidan lokaci ɗaya, wacce ta hango tsaye ya sa ta yin kanta a masifance.

 

“Radiyya ba ki da hankali ashe? Yaushe za ki daina sani magana? Ki sa kafa ki taho babu sanarwa, bayan haka me aka miki?”

 

Radiyya dai ta kasa magana domin ta san ko mutuwa za ta yi tana faɗar dalilinta, ba za su yarda da abin da ya sa ta barin gidan ba. Shi ya sa ta nemi ta ɓoye. Kan Radiyya a ƙasa, jikinta ya fara rawa, don ba ƙaramin aikin Aunti Mimi ba ne ta ce za ta bugeta, don ma ta lura yau ƴan faɗan basa kanta sosai.

Ganin Radiyya ta yi shuru ya sa Mimi wucewa ciki ta barta tsaye, idan ta ci gaba da mata shuru za ta iya bugunta, ko yanzu don Uncle Nasir ya roƙeta kar ta yarda ta taɓa lafiyarta ne, da babu abin da zai hanata dukarta.

 

Shigar Mimi ciki samun Umma ta yi a ɗaki, bayan sun gaisa Umma take sanar mata da zuwan Radiyya babu sanarwa, kuma babu kwakkwaran dalili zuwanta.

Girgiza kai Mimi ta yi cike da jin haushin Radiyya, idan ta koma gida tare da Radiyya abin da zai hanata dukarta babu shi sai Allah, a zahiri tsaki ta buga tana kallon Umma ta ce.

 

“Umma ban san dalilin zuwanta ba, hasali ma ba mu da labari, farkawa na yi naga babu ita a gidan, sanin babu inda za ta je yasa na ƙi zuwa da safe. Amma yanzu ta zo maza mu koma, Baban Walid duk ya fini shiga damuwa Umma, ko yanzu dalilin sa ya sa ni zuwa.”

 

Umma bayan ta gama sauraronta ta girgiza kai tana faɗin.

“Na rasa gane wace irin yarinya ce Radiyya. Ta sanar da mu tana son yin azumi a gida ne, ban goyi bayan zamanta nan ba ko don irin rayuwar da ake gudanarwa a gidan, kowa ta kansa yake, don haka asirinta a rufe ta zo ku koma. Amma da sharaɗi.”

 

“Sharaɗi kuma Umma? Sharaɗin me?”

Tambayar da Mimi ta yi wa Umma cike da mamakin kalamanta yau akan Radiyya.

 

A hankali ta ja ƙafafunta tana ja baya, maganganun su ɗaya bayan ɗaya su na ratsa dodon kunnenta. Ba ta san ta iso bakin baranda ba sai ji ta yi ƙafarta ɗaya ya zame, babu shiri ta kai ƙasa tana zubewa. Ƙarar faduwar ta ya sa mutanen gidan kallonta har da masu ƙoƙarin tambayarta lafiya.

 

“Wannan yarinyar anya ba ta da aljanu? Dubi tana faɗuwa ita ɗaya.”

 

Faɗin Inna Saudatu tana gyaran hatsi, da alamar na tuwon dare ne tun da an kusa gama na rana.

Amarya Zulaiha da take bakin ƙofar ɗakin girki mai cike da hayaki da zafi tamkar gidan birede, duk ta haɗa zufa sai maiƙo take. Bakin zaninta tasa ta share gumin da yake zubo mata tana faɗin.

 

“Ga alamu kuwa, abin ka da ƴar mahaukaciya.”

 

Dariya mutanen gida suka saka jin abin da Zulaiha da ta faɗa akan Umma. Radiyya da sauri ta miƙe kafin su ƙara wani maganar, a dalilinta ana ciwa mahaifiyarta fuska. Ƙofar gida ta nufa ta tsaya a soro tana jin dariyar su, fashewa da kuka ta yi ta haɗa kanta da gini.

‘Ina zan saka rayuwata da raina na ji sanyi? Ina zan samu inuwa na fake daga wannan ƙunar rana da nake ji a kowanne lokaci? Kullum zuciyata da rayuwata ƙara duhuwa yake daga lamarin mutanen duniya.’

Tunawa da abin da kunnuwanta ya jiyo mata a ɗakin ya sa ta sake fashewa da wani kukan. Rayuwa inuwa ɗaya da Uncle Nasir da Aunti Mimi, abu ne mafi wuya da wahala a rayuwarta kuma.

 

“Waye a nan?”

Ta ji murya saman kanta, da sauri ta juya ta ga Baba ne, duk da ta shaida muryarsa da ya yi maganar amma hakan bai hanata tsoro ba, hawayenta ta share ta sunkuyar kanta ƙasa.

 

“Babu komai Baba.”

Ta faɗa a sanyaye tana goge fuskarta.

 

Bai yarda ba ya sake cewa.

 

“To me ki ke anan? Sannan kukan me ki ke Radiyya?”

 

“Babu..”

Ta faɗa ta kasa ƙarasa maganar ganin irin kallon da yake mata.

 

“Biyo ni cikin gidan.”

 

Daga haka ya yi gaba ya barta nan tsaye. Radiyya kamar ta kurma ihu, tsoronta ɗaya kar ya sanar da Umma, sannan kar ya yarda da batun komawarta gidan Aunti Mimi. Kamar ba za tabi shi ba haka ta ja ƙafafunta a sanyaye ta yi cikin gidan.

A ƙofar ɗakin Umma ta hangosa tsaye da alama magana suke da Umma da Mimi, ƙin ƙarasawa ta yi wajen ta tsaya. Wajen mintunansa goma a ƙofar sannan ya bar gurin ya nufi ɗakinsa, Radiyya na tsaye wajen kowa na bin ta da kallo, mutanen gidan har sun fara amincewa lallai yarinyar nan ba ita ɗaya ba ce.

 

“Ke ki je in ji Baba.”

Radiyya ta samu saƙon ƙira a bakin ƴar amarya, daga haka yarinyar ta bar gurin.

A sanyaye Radiyya ta nufi ɗakin, a ƙofa ta yi sallama ya ba ta izinin shiga, tare da sallama ta shiga, shi ɗaya ne ciki sai Amarya Zulaiha ita ce da girki. A nan bakin ƙofar ta zauna tana faɗin.

 

“Kawu ga ni.”

 

Kai ya jinjina ya dubi Zulaiha da ta ƙi barin ɗakin, don duk ta ji mai zai faru.

 

“Amarya ba ni guri mintuna biyu.”

 

Ta ji haushin hakan don ta so jin maganar da zai faɗawa Radiyya, idan marar daɗi ne ta samu abin gorantawa Umma. Fuuu ta miƙe ta fice har tana take ƙafar Radiyya da take bakin ƙofa. Bayan fitarta Baba ya mayar da hankalinsa kan Radiyya da take murza yatsun ƙafarta.

 

“Radiyyatun Mardiyya!”

 

Ya ƙirata da sunanta gaba ɗaya da ya haddasawa Radiyya bugun zuciya, tsoro ya cikata, ta riga ta sadaƙar cewa zai yi ta koma gidan da take gani tamkar kabarinta ne. Gida ne mai cike da azzalumai, wanda basu damu da ciwon wani ba sai nasu, masu son kai, wanda suke son ɓata mata rayuwa.

 

“Radiyya!”

Baba ya faɗa a tsawace da ya firgitar da Radiyya ta dawo hankalinta ta kalleshi.

 

“Na’am Baba.”

 

“Ina hankalinki ina ƙiranki?”

 

“Ka yi haƙuri.”

 

Ta faɗa a sanyaye, ta haƙura ta saka a ranta za ta koma, ko me zai faru ya faru, sai dai za ta yi ta ƙoƙarin kare mutuncinta sai inda ƙarfinta ya ƙare.

 

Cikin kwantar da hankali tare da lallashi Baba yana duban Radiyya da kanta yake ƙasa ya ce.

“Radiyya ki faɗa min me yasa ki ka bar gidan yayarki, ba da saninta ba ko Nasir?”

 

‘Tirƙashi!’ Radiyya ta faɗa a ranta domin ba ta da amsar bayarwa gareshi, ba za ta taɓa faɗar gaskiya ba haka kawai take ji, ba za su taɓa yarda da ita ba.

 

“Ke nake saurara Radiyya. Ki sani Nasiru yana taimaka mana sanin kan ki ne, bayan haka ke ma jin daɗinki yana gidan. Sai dai kin zaɓi ki dawo nan inda ni kai na da taimakon Yayuna nake wasu abubuwan, sai sana’ata da ba samu, bani da sana’ar kirki balle riƙe gida. Amma bazan takura miki ba kamar yadda na ce, idan za ki riƙe kan ki da wasu abubuwan, ni bazan hanaki gurin kwana ba, ɗakin Zuhra ya ishe ku ke da ita, abin da aka dafa shi za ki ci idan sun ba ki, idan ba su bayar ba ki hakura.”

 

Rana na farko Radiyya ta cire tsoro ganin ta samu zaɓi gurin kawunta, hakan yana nufin duk hukuncin da ta yanke zai karɓa, a sanyaye ta ce.

“Baba na maka alƙawarin ba zan taɓa tambayarka wani abu ba, idan an bani zan karɓa idan ba a bani ba, ba bazan tambaya ba. Na amince zan zauna a haka.”

 

Shuru ya yi kamar ba zai ce komai ba, can ya numfasa yana kallonta ya ce.

“To wai me Mimi da Nasiru suka miki? Ko tana musguna miki ne? Tun fara tasowarki fa ki ke gurinta sai yanzu rana ɗaya ki ce a a.”

 

Da sauri Radiyya ta girgiza kai.

“A’a Baba ko ɗaya, kawai na fi son zama kusa da Umma ne yanzu.”

 

“Kafin ki yi aure ko?”

 

Da sauri Radiyya ta girgiza kai tana jin kunya. Murmushi Baba ya yi dama don ya tsokaneta ya faɗi hakan ganin duk ta takura.

 

“Shikenan Radiyya, Allah ya ba ni ikon ko da ciyar da kune ku ci ku ƙoshi. Idan kin je ki turo mini Umma da Mimi mu yi magana.”

 

“Ameen Baba, na gode sosai.”

 

Radiyya ta faɗa farin ciki na lulluɓeta. Tabbas wannan ranar farin cikinta ne, ji ta yi ko wani baƙin ciki da duhun da zuciyarta yake ciki ya fara yayewa. Fatanta ɗaya Aunti Mimi da Umma su yarda kamar yadda Kawu ya yarda.

Tana fita ɗakin Umma ta nufa ta samu sai hira suke da Mimi, gefe ta zauna da ƙyar a tsorace, ta gaisheta da Aunti Mimi da ta aika mata saƙon harara. A da dare Radiyya ta ce.

 

“Umma, Baba yana ƙiran ku.”

 

“Munafuka me ki ka faɗa masa?”

Mimi ta faɗa cike da jin haushinta.

 

Girgiza kai Radiyya ta yi da sauri.

“Babu komai wallahi.”

 

Umma da ta miƙe tana nufan ƙofar fita ta ce.

“Biyo ni Mimi mu je mu ji me zai faɗa kuma.”

 

Mimi kamar ta make Radiyya ta miƙe ta fice fuu. Girgiza kai Radiyya ta yi tana addu’a akan Allah ya sa kar su matsawa Baba ya ce ta koma, wannan baƙin gidan me cike da duhu.

Ta jima zaune tana saƙa da warwara kafin da ƙarfi ta ga an ɗago labulen ƙofar ta ɗaga kai. Mimi ce tsaye fuskarta tamkar hadirin da ya haɗo daga gabas ya dumfari yamma. Babu shiri ta sunkuyar kanta ƙasa zuciyarta yana bugawa.

 

“Munafuka dole ki sunkuyar da kai ƙasa. Kin haɗa ƙarya da gaskiya kin sa Baba yace za ki zauna anan ko? To ki zauna wahala ma kaɗai ya ishe ki, gidan da abinci ma yana gagar su balle wasu abubuwan rayuwa. Amma ki sani ina zaune ni Maimuna za ki zo ku same ni Radiyya. Banza wacce ba ta san alheri ba.”

 

Daga haka Mimi ta sake labulen ta fice cikin ɓacin rai. Dogon numfashi Radiyya ta sauƙe, ko kwana za ta yi tana zaginta ba zai dameta ba akan ta koma gidanta. Hannunta ta ɗaga sama alamar addu’a, da fara’a a fuskarta da ya ƙara ƙawata kyakkyawar fuskarta ta ce.

“Allah na gode maka daga kuɓutar da ni a wannan gida da sharrin wannan bawanka, Allah ka ƙara kareni da kariyarka, ka bani abin da zan riƙe kaina ni da mahaifiyata.”

 

Tana gama addu’ar ta shafa. Misalta farin cikin da take ciki abu ne kaɗan.

‘Tun asali me ya hanani zuwa gida idan nasan lokaci ɗaya za a karɓi zuwana.’

Ta tambayi kanta.

Tana nan zaune Umma ta dawo ɗakin, kallo ɗaya ta mata ta watsar.

 

“Tun da kin zaɓi zama a wannan baƙin gidan, kin zaɓi mu jera da ke a ɗaki ɗaya, asirinki a rufe muna samu dalilin ku. Amma babu komai kan ki ki ka wa, domin dalilinki ba zai fasa alherinsa ba Radiyya, ƴar uwarki yake aure ba ke ba balle ki mana baƙin ciki.”

 

Radiyya kanta a ƙasa tana jin Umma sai faɗa take, ta inda take shiga ba tanan take fita ba, ita kam ta gwammace komai za ta faɗa ta faɗa mata da rayuwa inuwa ɗaya da su, ko yagan naman jikinta za ta yi kowacce rana ita ce mahaifiyarta, kuma yafi mata akan ta rasa mutuncinta ta hanya mafi muni. Umma ta yi faɗa ta gaji ta fice a ɗakin ta barta zaune.

Har dare maganar kirki bai haɗa su ba. Da daren Inna Saudatu da ta gama girki ta zubawa Umma, aka ci sa’a ta ƙara malmala ɗaya na Radiyya, don Baba ya sanar musu za ta zauna zuwa bayan sallah ta koma, ta zo azumi. A gidan raba abinci ake ba a ci tare, kowacce da yaranta, hakan yafi musu zaman lafiya a faɗin su.

 

Haka Radiyya ta fara gudanar da sabuwar rayuwa a gidan, babu mai shiga harkar wani, tsakanin mutanen gidan baƙar magana, gwara yaran su suna jituwa akan matan gidan. Ba ta shiga harkar su kullum tana ɗaki, yarinya ɗaya ce mai kirkir cikin su ta lura wato Amrah. Tsakanin ta da Umma sai hantara da aiki.

Da safe za ta share tsakar gidan, ƴan matan su yi wanke wanke, da yamma za ta yi wanke wanke su share tsakar gida, duk wacce mahaifiyarta take girki ta tayata aiki. Baba ya ji daɗin ganin Radiyya ta sake tana taya yaran gidan aiki. Umma ta yi faɗar ta gaji ta rabu da ita.

 

***

 

A hankali ya karkato da kan motarsa ya shigo layin, layin masu kuɗi ne sosai a unguwar wanda ake ji da su, gidaje ne reras kamar wanda aka zana aka ajiye tsabar kyau da haɗuwa, tsantsan kuɗi aka zuba aka gina gidajen. Da kallo yake bin gine ginen yana tuna shuɗadden lokacin da ya wuce. Tsawon shekaru ashirin kenan, amma hanyar har yanzu bai ɓace masa ba, sai ma samun cigaba da aka yi. Sannu a hankali yake tafiya cikin baƙar motarsa da yasha tinted. Sanye yake da riga t-shirt da baƙin wando jeans, baki ne wanda fatar jikinsa ya murje don hutu da jin daɗi, kallo ɗaya za ka masa ka hango hakan, sai dai fuskar sa haɗe yake tamkar wanda aka aiko masa da saƙon mutuwarsa.

A haka ya ci gaba da tuƙi har zuwa ƙofar wani gida mai kyau babba cikin jerin kyawawan gidajen. Idanuwansa ya rufe ya yi baya tare da kwantar da kansa saman kujera. Kokuwa yake da zuciyarsa, tun a gida yake hakan, da ƙyar ya ɗaure ya taho har zuwa nan, amma sai ji ya yi yanzu ba zai iya ba, zai iya aikata komai idan suka yi ido biyu da juna, tsawon shekaru ashirin ya kauracewa abin da zai haɗa su, ya datse ko wacce hanyar haɗuwar su.

Ƙarar wayarsa ne ya sa shi buɗe idanuwansa da suka fara canza launi, hannu ya kai ya ɗauki wayar da yake ajiye a majiyar cikin motar, ganin me ƙiran kamar ba zai ɗauka ba can ya ɗaure ya ɗauka.

 

“Hajiya!”

 

Ya faɗa a sanyaye ta ɓangarensa yana jiran ya ji me za ta faɗa.

 

“Ka taho?”

 

Hannu ya kai ya shafa gashin kansa ya lumshe ido ya buɗe.

“Ina ƙofar gida.”

 

“Ka daure ka shigo Rashad kar ka koma.”

Ta faɗa da alamar roƙo a nata ɓangarenta.

 

“Hajiya ba zan iya ba.”

Ya faɗa bai jira me za ta sake cewa ba ya zare wayar ya kashe ya wurga saman kujeran gefensa. Da mugun gudu ya ja motar yana barin ƙofar gidan tare da ficewa a unguwar gaba ɗaya, yana ji wayar yana ta ƙara alamar ƙira ya ƙi ɗauka, sai gudu yake shararawa a titi.

 

‘Bazan ƙara taka ƙafana gidan da aka gina da haram ba. Wannan alƙawari na ɗaukarwa kaina.’

Furucin da ya furta kenan tsawon shekaru ashirin.

 

About the author

Hausa_Novels

Leave a Comment