Dua The Hated Girl Hausa Novel
DU’A*(The hated girl)
By
*Jiddarhtulkhair*
“`This book is gonna be my first so any kind of suggestions highlights of mistakes from my readers are most welcomed“`
~Note: wannan littafin ba pure Hausa bane~
Dafatan zakuyi supporting dina Thank you
*In shaa Allah I won’t let my readers down*
*Thanks much for reading this book*
I seek Allah’s guidance in writing this book Allah yasa karna kauce hanya, sannan ya amfani al’umma masu irin halin
Bismillahir Rahmanir Raheem
Tattalin So Hausa Novel Complete
*CHAPTER 1*
Around 4:30am mummy ce tashigo dakin su Dua without second thought ta wasa ma Dua ruwan sanyi tana masifa, Dua she wakeup in panic tafara ba mummy hakuri “Am sorry mummy am so sorry pardon me I beg you pardon me,”
hakan bashi yasa mummy ta sassautawa Dua masifan da takeyi mata ba saying “you have to finish all the works before 6:00am”
Dua da rawar murya tace “in shaa Allah mummy” Amrah tanajinsu tasake jan duvet dinta tacigaba da baccin ta
Mummy na fita Dua tashiga toilet tayi Alwala tafito tafara nafila sannan tayi asuba da ta idar ne tafara rokon Allah tana kuka “ya Allah please help me out, I’m clueless Allah,” tana idarwa tafita kasa without waking Amrah up
Duk da suna da housemaid hakan besa mummy yima Dua sassauci wajanyin aikin gida ba, tana fita tasamu fatima me musu aiki “Good morning sister fatima”
” morning Dua how have you been?”
I’m fine sister fatima”
“Masha Allah then” daganan Dua suka fara shara tare har saida suka gama everything before 6:30am tayi arranging breakfast dinsu a dining table sannan taje tayi alerting mummy akan sun gama
Sama tawuce direct tasamu Already Amrah ta shirya toilet tawuce Amrah tabita da kallon banza sannan taja saki tace “villager” sarai Dua tajita but tayi kamar bataji taba after Dua tafito a wanka itama shirin schl tayi sannan tawuce dining room Dan suyi breakfast tana zuwa Already daddy shima yafito har kasa ta durkusa sannan tace “Good morning father” kallon ta yayi from head to toe sannan ya yamutsa fuska yace “morning” hakan be dameta ba inda sabo tasa ba but deep down her abun na mugun damunta mummy ma yamutsa fuska tayi, guri tasamu tazauna sannan tafara breakfast koda Amrah tafito A tsaye ta gyaishe da parents din nata kowa ya amsa mata fuska asake itama breakfast din tazauna ta fara, Daddy ne yayi braking silent dinda “you 2 you have to finish in 10minutes time so don’t waste my time” haka sukayi sauri sauri suka gama breakfast din sannan sukayima mummy sallama suka fita parking space Dua batayi attempting shiga gaban mota ba dan tasan batada wannan right din Amrah ce tazo tashige gaban motan daddy yakaisu har school gate sannan yayi dropping dinsu
Amrah nashiga school direct wajan friends dinta ta wuce su uku ne firdausi da rumaisa daman su ba karatune ya damesu ba kawae dai kabarsu da wayewa da daukan wanka suna ji da kansu sbd iyayensu nada kudi, hakan yasa suke ganin sunfi kowa.
Ita kuma Dua hanyar class tawuce zata shiga knn taji ance “Hey friend” kobata juya ba tasan best friend dinta Ayesha ce, da smiling face tajuya sukayi hugging juna Ayesha ce ta fahimci kamar tana cikin damuwa tace “Dua what’s wrong? you look so pale” Dua da fuskar tausayi tace “Ayesha When will my family start loving me? What did I do to them, they hate me and they don’t love me at all why why please? What did I does to them for deserving such punishment?” Takarasa maganan tana me fashewa da kuka sosai dakyar Ayesha ta lallabeta har tayi shiru
Subject Teacher sune ya basu Test dama Dua talented ce itada Ayesha suka fara test dinsu hankali kwance dansu question din yamusu sauki Amrah yadda taga sun gama da wuri har sunyi submitting shiyasa tayima Dua magana da ido Akan tayi mata, ita kuma tafara yiwa Amrah knn akace *submit* hakan yasa kawae tayi mata submitting din without fishing the test hakan yasa da test result yafito Dua da Ayesha suna da 20/20 Amrah kuma 15/20 Amrah taringa zagin Dua ita kuma bata tanka taba
Har aka tashi driver yazo daukansu suna isa gida suka tarar da parents dinsu a parlor nan Amrah tasa kuka wae Dua tamata mugunta tahada karya da gaskiya tafada sukuma dake bason Dua suke ba nan suka ringa zagin Dua mummy kam harda dukanta tayita kuka tanajin duk duniya kowama ya tsaneta kuma babu Wanda zai sota tunda ko agida batada maisonta except her best friend Ayesha
*shin mummy da daddy sune parents din Dua*?
*Meyasa suka tsane Dua*?
_Dan samun amsoshin tambayoyin ku kubiyoni a next chapter_
JazakAllah khair for reading this book
Keep reading .
Remember me in your prayer🙏🏿
*By jiddarhtulkhair*
*08110615256*
*DU’A*(The hated girl)
By
*jiddarhtulkhair*✍️
*CHAPTER 2*
*FLASHBACK*
Alhaji Muhammad Usman shine mahaifin su Du’a
Assalinsa bafulatanin tafawa balewa ne dake jihar Bauchi, su biyune agun mahaifansu, shida kanwarsa hibbah dake aure a london,
Alhaji Muhammad usman gogoggon dan Boko ne yayi karatunsa a *TAFEs university* dake kasar Australia inda yayi karatunsa a fannin marketing
Lokacin graduating dinsa ne suka hadu da matarsa Hajiya Zahra, lokacin sunje taya uncle dinta murnan kammala masters degree dinsa.
Tun daga lokacin suka kulla soyayya , inda magana yayi nisa
Hajiya Zahra ‘ya daya tilo ga iyayenta ita assalinta yar rimi ce dake jihar kaduna, ta taso cikin so da kulawa, iyayenta assalin masu kudine,
Tayi karatunta a *Stanford university* dake America inda ta karanta English literature, shiyasa tasamu karancin tarbiya musamma yanayin environment dinda take karatu
Itade bawata kyakkyawa bace Amma tana danata kyaun daidai misali…
Bayan bikinsu Alhaji Muhammad Usman da matarsa Zahra ya tattara nasa danasa yakoma Abuja anan yake kasuwancinsa har Allah yabuda masa..
2years to their weeding matarsa Zahra ta haifi danta Aryan inda yasamu so da kulawa agun iyayensa hatta hibbah saida tazo sunan Aryan,
Lokacin da Aryan ya cika 2 years, Awannan shekaranne Alhaji Muhammad Usman da babban Abokinsa Alhaji Abubakar tukur suka samu riba sosae aka kasuwancin su dake suna International trade ne daga nan shikenan kullum suna cikin kudi” hakan yasa Alhaji Abubakar bama Abokinsa shawarar suringa ziyaran gidan marayu suna tallafa musu,.
Hakan kuwa sukayi, azuwansu ta farko ne yaga wata kyakkyawar budurwa da bazata wuce 18years ba tunda yaganta yaji yana sonta musamman dayaji Nanny’s din wajan kowa yana yabawa da iliminta da hankalinta..
Hakan yasa bayan ya koma gida yaji shi lalle inbe aureta ba akwai problem, daga nanne without second thought yaje neman aurenta” Alokacin da Aneesa taji cewa wani yazo aurenta da farko taki Amma caregiver dinsu taringa bata shawara akan zata samu ‘yancinta hakan yasa Aneesa ta yarda..
_kada ku manta wannan flashback ne so ba lalle mutafi deep down ba, kawai dai ku fahimci relationship dake sakanin kowa acikinsu_
*Ya zahra zataji idan taji zaiyi aure*?
*shin Dua da amrah mamansu daya*, *Aryan fa*?
*shin waye ne mahaifiyar Dua acikinsu*?
“`Kyautar 1GB ga duk wacca ta bada amsa daidai“`
*By jiddarhtulkhair*
*08110615256*
*DU’A*(The hated girl)🧕
By
*jiddarhtulkhair*✍️
*CHAPTER 3*
Zahra hankalinta yayi dubu dataji wai mijinta zai Kara aure hankanne yasa kullum suke cikin rashin fahimta dukda yana iya bakin kokarinsa naganin sun daidai ta,
Daga baya ne dai tadan kwantar da hankalinta tunda taji cewa ashe ‘yar gidan marayu zai aura, wato hakan na nufin yarinyar ilimi zero, kwalliya zero, kyau zero, iya girki zero, everything zero ai abunma da sauki, tunda mijinta ya kwallafa ran saiya Kara aure gwamma aneesan da wata, hakan kadae zai bata damar cutar da ita cikin ruwan sanyi.
After bikin Alhaji Muhammad da Aneesa tasamu kulawa da soyayya wajan mijinta, Ananne ma ya maida Zahra makaranta inda taje *school of nursing* Wannan kulawanne yasa hankalin zahra dubu tashi dan haka ta kudurta cewa saitaga bayanta.
2 years later Zahra ta haifi ‘yarta Wato Amrah after 4 month saiga Aneesa ma ta haifi ‘yarta Wato Dua, Dua tun tana jaririya tayi Wani irin farin jini gun mutane harta hibbah saeda tazo sunan Dua ita da yarta Fatrisha
Nanne Zahra takara tabbatar da Aneesa da yarta sunfita farin jini.
Awajan Alhaji Muhammad kuma yana kokarin yin Adalci asakanin matansa amma deep down him yafison Aneesa saboda tasan yadda zata zauna dashi cikin ladabi gata da hakuri.
Dua nada 1 year ne arzikin Alhaji Muhammad yafara baya baya, lokacin da takai 5 years ne yasamu kariyar arziki Wanda hakan yajawo ma Aneesa da yarta bakin jini gun mijinta, maganar zahra akullum shine”Ai daman Aneesa nada farar kafa kuma tun lokacin bikin tasan da hakan dan kartayi magana ace kishine”, shi kuma tun baya yarda harya fara yarda saboda duk lokacin da ya kwana a dakin zahra toh tabbas a ranan sai yayi asaran Wani Abu.
Hakan bakaramin damun aneesa yakeyi ba amma ta daure ta cigaba da ibadan ta kuma kullum burinta tabawa yarta tarbiyya da isheshshen ilimi hakan yasa kullum tana cikin yimata lesson,.
Dan aikin data samu a privacy health care dashi take yima Dua hidima dashi
Friend din Zahra ce humairah, tazo taringa zuga zahra hakan yasa suka Kara kaifin shirinsu akan Aneesa
Aneesa takamu da breast cancer Wanda hakan yasake jamata bakin jini gun mijinta akan yaji tausayinta sai yake Kara jin tsanarta; saboda a ganinsa saboda ita yasamu kariyar arziki yanzu kuma ga ciwonta yasashi kashe mata kudin wajan nema mata lafia.
Wata rana jikinta yafara damunta dan haka fatima ce tarakata asibity, akayi admitting dinta
Lokacin da Aneesa take Asibity Daddy ko zuwa kanta bai tabayi ba,.
Dua kuwa kullum cikin kuka takeyi garashin lafiyan mummyn ta ga kuma Azaban da take fuskanta gunsu Amrah.
Ahaka har mummyn Dua tafara samun sauki aka sallame su.
Kuyi min hakuri naga korafinku akan nakara yawan chapter din, in shaa Allah next zan Kara long typing
_Karku manta a flash back muke har ynx but munkusan gamawa just one page yarage mana_
*By jiddarhtulkhair*
*09061648106*
[…] Dua The Hated Girl Hausa Novel […]