Littafan Hausa Novels

Dr Saif Complete Hausa Novel

Dr Saif
Written by Hausa_Novels

Dr Saif Complete Hausa Novel

 

 

 

 

 

 

 

DR. SAIF*
_(return)_

©Ummu Hanan.

Bismillahir Rahmanir Raheem

Haske writer’s associated
(Home of expert & perfect writer’s).💡

A hankali had’add’iyar motar tayi parking a harabar hospital d’in kusa da jerin gwanon motocin dake parke a wajen.
K’ok’arta ki fito Ayshaa kinji?, Naji wata murya ta fad’a daga cikin motar, “Aunt Salma bazan iyaba fa” wata siririyar muryar mace ta fad’a cikin shagwa6a, “daurewa dai zakiyi meye amfanin zuwa asibitin?.
Mintuna kadan wata matashiyar mace ta fito riqe da wata matashiyar budurwa dabazata haura sha bakwai ba kyakkyawace sosai kamar su d’aya da matar da alamu yayarta ce,

Tarairayota jikinta ta qara yi tana d’an murmushi gamida girgiza kai ganin yadda d’an zazza6i kad’an ta zauna sai shasshake mata take.

Kai tsaye office d’in babban likitan suka nufa bawani layi sosai daga Wanda ke ciki saikuma wasu mutum biyu masu jira, layi sukabi suma gaba d’aya Ayshaa ta kanannad’e Aunt Salma ta hanata motsin kirki sai faman 6ata fuska take kamar mai shirin sakin kuka.

Wad’anda suka shiga d’in basu wani jimaba suka fito sukuma suka shiga.
Had’add’en office ne daya wadatu da kayan zamani da ake qawata ofisoshi dasu sanyin A.C da qamshin air freshener da kuma na mamallakin mai office d’inne suka cakud’a suka bayar da wani irin daddad’an qamshi mai sanyaya rai da yanayi mai dad’i.

Matar Aljan Hausa Novel Complete

Idona ne ya sauka kan mai office d’in, fatabarakallahu ahsanul qaleeqeen, kalmar dana ambata kenan cikin raina saboda had’uwar mutumin tun daga zaunen zaka fahimci cewar giant ne ALLAH ya azurtashi da wani irin sirrin kyau mai d’aukar hankalin jama’a.
Idanunshi a lumshe suke ya dafe kanshi da hannu d’aya d’ayan kuma ya d’orashi kan table d’in gabanshi riqe da pen sosai yayi relaxing kan kujerar dayake zaune, a hasashena dai bazai wuce 31 zuwa 32 ba.
Sallamarsu ce tasa yad’an bud’e ido kad’an ya kallesu ya qara mayarwa ya rufe.

Duk da halin da Ayshaa ke ciki bai hanata ta6e baki ba, da jan k’aramin tsaki a ciki, Tunda suka zauna baice uffan ba haka suma basuce komiba bakajin komi sai sautin karatun Al’qur’ani mai girma daya kunna a wayarshi k’ira’ar khusary cikin k’arshen suratul baqrah kad’an kad’an sautin ke fita ta yadda idan baka kasa kunne sosai ba bata yadda zakaji.
Tuni Ayshaa tafara gunguni tanajan k’ananun tsaki, duk abinda take kuma yana kallonta ta qasan idonshi da tsakin datake masa.

Dr Saif

Ganin shirun yana neman yin yawa yasa Aunt Salma ta bud’e baki zata fara magana, sai a lokacin ya d’ago ya zauna sosai kan kujerar tare da ware manyan idanunshi yana d’aga mata hannu alamun tayi shiru.
Shirun tayi kuwa cikeda mamakin irin Dr’n da ALLAH ya had’asu dashi yau, Ayshaa kam tuni ta shaq’a sosai jitake tamkar ta tashi ta shaq’o wuyanshi dan yadda ya raina musu hankali.
Kamar wanda akayiwa dole kokuma mai ciwon baki yace
“Ko zaki iya barina da patient d’in?”
Kamar wata doluwa Aunt Salma ta kad’a kai tana k’ok’arin raba jikinta dana Ayshaa databi ta kanainayeta, kamar zata saki kuka take fad’in
“Haba Aunt Salma bazan iya zama bafa”, k’ok’arta dai little sis” Aunt Salma ta fad’a tana shafa kanta gamida ficewa.
Shirun ne dai ya qara ratsa wajen dan ba wanda ya q’ara ko tari cikinsu saima wani aiki daya tsira a laptop d’insa bayan ya saka suratul Ali imraan dan suratul baqrahn harta q’are.

Yana ganinta ta gefen ido sai faman lallanqwashewa take alamun zaman ya gundureta, Itakam Ayshaa ta d’au alq’awarin indai bashi ya fara tambayar ta abinda yake damunta ba bazata fara masa magana ba tunda shine likita shiya dace ya fara tambayar ta damuwarta.
Shima a nashi b’angaren hakanne indai bata fad’a masa damuwarta ba shikam bazai tambayeta ba dan yaga alamun yarinyar y’ar rainin hankali ce (Saif bakada gaskiya fa😹😃).
Wani dogon tsaki taja ta miq’e ta fice daga office d’in bayan ta jefa masa wata muguwar harara.
A hankali ya sauke idanunshi daga kanta bayan ta fice ya tsurawa table d’in gabanshi ido “wai yarinyar nan kuwa tasan wanda takewa tsaki? Kokuwa batasan yadda ya tsani tsaki bane? (Ina zata sani🤨). ALLAH ya q’ara had’ashi da ita kuwa san tayi masa tsaki.

A reception ta samu Aunt Salma tana zaman jiranta, da sauri ta tashi ta tareta tana tambayar ta lafiya? Ganin yanayin yadda ta fito office d’in
“Wlhi Aunt mutumin nan mugun d’an rainin wayone” ta fad’a tare da hararar inda office d’in yake.

“Tunda dai ya dubaki ai shikenan naga alamun shi ai d’an jida kaine” Aunt Salma ta fad’a tare da jan hannunta, baki ta turo tace
“Nifa bai dubani ba, bai tambayeni abinda ke damuna ba nima kuma ban masa bayani ba
“Wato kowa yanaji da kanshi ko? idan shi bazaiyi magana ba ke bazakiyi ba?”
Baki ta tunzuro gaba tace
“Amma Aunt Salma shi….”dallah wuce muje malama”, Aunt Salma ta katseta tana hararar ta.
Gaba tayi bakinta a d’ane tanajin tamkar ta koma ta gaggaya masa magana d’an rainin wayo kawai.
Da hanzari isah direba ya taso yana fad’in
“Kun fito Hajia?”
“Eh amma bata samu ganin Dr ba kaimu wani asibitin”.
Aunt Salma ta bashi amsa tana shigewa motar batare data jira ya bud’e mataba.
Ayshaan ma shigar tayi shima ya zagaya cikin rawar jiki ya shiga ya tada motar suka fice daga cikin hospital d’in.
★★★
Bai q’ara duba kowaba ya had’a nashi ya nashi yabar asibitin yatafi gida.
Sallama yayi cikin wani qaton parlour dayasha q’awa kala kala na ababen more rayuwa.
Matashiyar budurwa ce y’ar kimanin 18yrs a zaune tana game a wayarta, kamarsu d’aya saidai ita tana da d’an duhun fata kad’an kuma yafita dogon hanci.
“Sannu da zuwa Yaya” ta fad’a bayan ta amsa sallamar tana cigaba da game d’inta dan tasan bama lallai ya amsaba.
A ciki ya amsa yana tambayar ta Mamie”
“Yanzu ta haura upstairs” tabashi amsa.
Kan cushion ya zube yana sauke numfashi, har ynxn tsakin da marar kunyar yarinyar nan tayi masa bai bar sukar ransa ba, yayi dana sanin barinta ta tafi batare daya d’au mataki a kanta na jiyake tamkar ya dawo da hannun agogo baya.
“A ah ikon ALLAH tunanin me Saifu yakene haka?”
Ya tsinkayi muryar Mamie tana masa magana, murmushi ya d’anyi yana shafa sumar kanshi mai laushi.
“Gajiya ko?” Ta tambayeshi tana murmushi.
“Gajiyar ma akwaita Mamie ga yunwa tun breakfast fa”
To kaje kayi wanka kafin Imaan takawo maka abincin”.
Car key d’insa ya d’auka da manyan wayoyinshi guda biyu ya miq’e tsaye.
“Kaga daka aje iyali duk wad’annan abubuwan saidai kazo ka tarar da komi ready”
Mamie za’ayine fa ina lalubawa bansamu bane har ynx”
Baki ta ta6e tace
“Uhmm nagaji da gafara sa banga q’aho ba, ALLAH dai ya nunamin ranar da zanga matar Saifu inga wace kalace da tsawon shekaru ake lalubota”
Dariya Imaan tasaka tana toshe bakinta da hannunta, harara ya zabga mata tayi hanzariin daidaita fuskarta.
“Vry soon Mamie insha ALLAH” ya fad’i a hankali yana barin parlourn.

*DR. SAIF*
©Ummu Hanan

Bismillahir Rahmanir Raheem

Haske writer’s associated
(Home of expert & perfect writer’s)

Free page
No 2….

K’arfe 9:15 ya shigo parlourn gidan sanye yake cikin wasu riga da wando marasa nauyi farar riga da red color d’in wando,anja adon dogayen layika a gefe da gefen wandon da farin zare hular sanyi ce a kanshi mai laushi white an rubuta MY MAN agaban hular sai farin slipper dake sanye a k’afarshi mai taushin tsiya sai zuba daddad’an qamshi yake.
Kai tsaye upstairs ya nufa wajen Mamie yana stairs na farko yana shirin taka na biyu ya hango Daddy da Mamie zasu sauko downstairs da alamu rakiya tayo masa, da saurinsa ya juya zai fece kafin Daddyn ya hangoshi saidai ya makara dan daf dazai fice ya tsinkayi muryar Daddyn yana fad’in
“Karka sake ka fita ka makaro nariga na ganka”
Cak ya tsaya tare da runtse idanunshi yana dafe goshinshi q’asa q’asa ya furta
“Oh my gosh, dama bai fitaba?”
A sanyaye ya koma bakin stairs d’in ya tsaya tare da sunkuyar dakai.
“Barka da safia” ya fad’a bayan sun sauko har lokacin bai kallesu ba
“Barka dai uban y’an shiririta”Daddy ya fad’a yana kallonshi a kaikaice,ya d’ora da fad’in
“Wato Saifu idan ka sake ka shiga hannuna wllhy bazakaji da dad’i ba wato wasan b’uya ma ka fara dani ko, nagaji da nanata magana d’aya kusan shekara d’aya muna abu d’aya dakai, to anzo ga6ar da haqurina yazo karshe kaji na fad’a maka”
Kanshi a q’asa a hankali yace
“Ayi haquri insha ALLAH za’a duba”
“Okay bakama fara dubawar ba kenan?, rasa amsar bayarwa yayi still dai kanshi na q’asa sai faman susar k’eya yake.
Kai Daddy ya kad’a yace
“Good hakan yayi maka kyau” ya ka’rasa maganar tare da nufar k’ofar fita.
ALLAH ya kiyaye sukayi masa ya amsa tareda ficewa.
Marairaicewa yayi ya kalli Mamie zaiyi magana, bata kulashi ba ta nufi ainahin cikin parlourn kan cushion ta zauna, bin bayanta yayi ya zauna kusa da k’afafunta tareda kamo hannuwanta ya riq’e cikin nashi
“Dan ALLAH Mamie ku k’ara hakuri insha ALLAH nan bada jimawa ba komi zai zama labari”.
“Ah to gara dai kayiwa kanka fad’a dai fisabilillahi ace kusan shekara d’aya muna magana d’aya dakai nagaji da gafara sa banga q’aho ba, ALLAH ya azurtaka da komi na rayuwa amma ajiye mace ya gagareka ga sadeeq nan da mahfooz (causin brothers d’insa) duk sunyi aure harda albarkar y’ay’a ga kuma Sameer nan k’aninka ne amma har ansa date d’in aurensa kai kana zaune wai ko bakada lafiya ne?”
Fuska ya b’ata sosai kamar zaiyi kuka yace
“Mamie please ki daina wannan maganar dan ALLAH”.
Baki Mamie ta ta6e tace
“Ah ah to aida gaskiya ta, cikin y’an uwa ma ga y’an mata nan dayawa masu sonka ga yaran k’awayena da abokan Daddyn ka amma ka shafawa idonka toka kak’i saurararsu saboda ALLAH fa”.
“Ni Mamie duk basu yimin ba wllhy”.
Rank’washi Mamie ta sakar masa a kanshi tace
“Ai kaji matsalarka Abbana”.
Wajen ya dafe da hannunshi kamar zaiyi kuka yace
” Da zafi fa Mamie”(uhm sai an fita ai tawa mutane muzurai).
Dariya Mamie ta d’anyi tana miq’ewa tsaye tace
“Bari in koma sama dan ALLAH ka daure dai babana a k’ok’arta a samo mana suruka”.
Shima d’in tsayen ya miq’e yana fad’in
“Insha ALLAH Mamienah”.
Daga nan ta haura upstairs shikuma ya shige part d’inshi.

WANENE SAIF???
Saifuddeen Sadeeq Matawalle wanda abokansa ke masa lak’abi da S.S Matawalle d’ane a gurin Alh Abubakar Sadeeq Matawalle babban d’an siyasane daya riq’e muq’amai da dama a cikin gwamnati inda daga baya yabar harkar ya komawa kasuwanci inda yake da manya manyan kamfanoni a fad’in Nigeria suna zaune a garin Abuja matarshi d’aya Hajia Hafsat babbar likitace a babban asibitin Abujan macece mai mutunci da kirki da sanin yakamata, yaransu uku kawai Aisha ce ta farko sai Saif data bawa kusan shekara takwas daga nan sai Zainab (imaan) data kasance y’ar auta inda tazararsu da Saif shekara goma dan har sun fitar da samun wata haihuwar kamar yadda suka fitar bayan haihuwar Aisha,cikin ikon ALLAH kuma aka samu cikinta.
Aisha tayi aure anan cikin garin Abujan tanada yara uku kauthar,hibbah,

 

*DR.SAIF*

©️Oum Hanan

Bismillahir Rahmanir Raheem

Haske writer’s association
(Home of expert & perfect writer’s).

Free page
No 3…

Aisha tana aure a nan cikin garin Abujan tanada yara uku kauthar hibbah sai d’an jaririn datake goyo areef.
Imaan tana shekarar ta tafarko a higher level.

Saif yayi gaba d’aya karatun shine a k’asar Egypt tun daga matakin secondary school har zuwa masters degree inda ya karanchi medicine dan tun yana k’aramin shi yake sha’awar irin aikin Mamien shi kodan ya taimakawa k’asarshi da y’an uwanshi musulmi, Daddyn shi yaso ya ya karanchi harkar zane amma ganin inda hankalinshi yafi karkata yasa ya k’yaleshi yabishi da addu’ar samun nasara, b’angaren ilmin addini ma ba laifi yana dashi dai dai gwargwado ya sauke Al’qur’ani mai girma da sauran littattafai tun kafin tafiyarshi Egypt.
Mutum ne shi mai k’wazo da jarumta a aikinshi da duk wani abu dayasa a gaba, hakan yasa bayan yasamu shaidar shi ta zama babban likita dactocin q’asar sukaso riq’eshi yayi aiki dasu shikuma ya k’ek’asa k’asa yak’i yarda dan acewarshi k’asarshi da mutanen cikinta yayiwa karatun shi, saidai yayi musu zaman 1yr kafin yadawo cikeda d’imbin nasarori da tarin yabo daga inda yabaro.
Tun kafin yadawo Daddy ya gina masa k’aton asibiti a matsayin gift d’inshi aka zuba ingantattun kayan aiki da k’wararrun ma’aikata.
Yana dawowa kuwa ya fara aiki, sosai asibitin ya samu karb’uwa gurin al’umma talaka da mai kud’i, talaka yana sonshi ne dan sauk’in asibitin dan basu tsawwala ba yayin da masu kud’i suke sonshi saboda kwarewar ma’aikatan asibitin.

Tun bayan dawowarshi da y’an y’an watanni Daddy ya tuntub’eshi da maganar aure, saiya kawo masa uzurin baisamu yarinyar datayi masa ba a lokacin.
Daddyn ya karb’i uzurin nashi bai takura masaba yace dai yayi k’ok’ari ya nemo wadda yakeso.
Tun daga lokacin Daddy da Mamie suka fara takura masa da maganar aure ganin bai k’ara tayar da maganar ba sam bai d’auki batun da wani muhimmanci ba, Mamie kam kullum addu’a take binshi da ita a cewarta taga kamar tsoron matan ma yake.

Miskili kafi mahaukaci ban haushi taken da kakarsa kemasa kenan Hajjah wadda ta haifi Daddyn shi, wataran suyi dad’i wataran arabu baram baram shida ita😄.

Ta bakin na Hajjahn kuwa Saif miskili ne na bada labari sosai magana kemasa wahala baida fara’a sam kullum fuskar nan tashi a cunkushe ko murmushi saita k’ure yakeyi tun Mamie namasa fad’a harta gaji ta daina danta lura abin a jininsa yake.

Imaan tana son taga ta sake da yayanta suna hira da wasa da dariya saidai ba damar hakan dan bata samu fuskaba shiyasa idan taje gidajen friends d’inta sai taita sha’awar su idan taga yadda suke sakewa da yayyinsu suna wasa da dariya saitaji dama itace gashi batada abokiyar hira saidai Mamie in Mamien bata nan kuwa saidai waya inta gaji tayi barci shiyasa bini bini tana gidan Aunt Aisha har gara yanzu data fara d’aukar lecture kullum tana busy karatun yakan d’auke mata hankali.

Mutum ne mai tsafta da son gayu kullum tsaf tsaf yana fitar da daddad’an qamshi.
Wannan kenan.

 

WACECE AYSHAA???
Ayshaa Thabit Mohammad d’iyace ga fitaccen d’an kasuwar nan Alh Thabit Mohammad, ba inda harkokin kasuwancin shi basu kaishi anan suka had’u da Alh Abubakar Sadeeq Matawalle suka k’ullah amintaka da juna saidai ba wanda yasan iyalin wani acikinsu, sai matan da suka had’a suke gaisawa ta waya yana zaune a garin kano da iyalanshi
Yaransu biyar duk mata ALLAH bai basu namiji ba.
Haleemah, Safiyyah, Salma, Fateemah sai Ayshaa y’ar auta, tagama secondary school d’inta inda kafin a samar mata jami’a tajewa Aunt Salma hutu dan suna d’asawa sosai da ita, duk sunyi aure, Haleemah da Safiyyah suna aure anan garin kano sai Fateemah dake aure a bauchi sai kuma Salma dake Abuja.
ALLAH ya azurtata da kyakkyawar sura da kyan diri komi dai Masha ALLAH.
Tanada surutu kuma matsiwaciya ce ammafa idan aka tab’ota😃.

★★★
Back to story…

“Aunt Salma kayan makeup d’ina fa sunyi k’asa wllhy” Ayshaa ta fad’a tana kallon Aunt Salma dake gyarawa Ikraam gashinta tanasa mata beats.
Harara Aunt Salman ta jefa mata tace
“Sai kace wata gwanar makeup d’in ko an siyo miki ma ai barinsu kike baki using dasu.
Shagwa6ewa tayi tace
“ALLAH Aunt Salma turarukana sunyi k’asa fa”.
Shiru Aunt Salma tayi kafin tace
“ALLAH ya taimakeki akwai turarena daya k’are nakeso asiyomin inajin dad’in amfani dashi.
Tsaye ta miq’e tana fad’in
“Toh yaushe zanje inyi shopping d’in Aunt?”.
“After asr sai isah ya kaiki”, ta amsa mata.

“Yawwa my Auntynah” ta fad’a tare da bata peck a gefen kuncinta tare da nufar bedroom d’inta da d’an gudunta kamar wata karamar yarinya🙄.
Da kallo kawai Aunt Salma tabita tayi murmushi gamida girgiza kai tana cigaba da abinda take.

★★
5:13pm ta fito parlourn sanye cikin arebian abayah blue black datasha adon manyan flowers whit color a gaban rigar tayi rolling da mayafin abayar kalar rigar, whit plat shoes tasaka da y’ar k’aramar purse riq’e a hannunta sai wayarta dake riq’e a d’aya hannun data d’aura bak’in agogo.
Farar powder kawai ta shafa a farar fuskarta sai whitlips da kwalli data zizara a idanunta wanda suka k’ara fito mata da kyakkyawar fuskar tata sai zuba kamshin humrah take.

Ganin Aunt Salman bata parlourn yasa kai tsaye ta nufi bedroom d’in Aunt’n, ta shiga da sallamarta, a gaban mirror ta sameta ta fito wanka tana shafa lotion, bakin gado ta zauna tace
“Aunt na shirya”
“Okay d’auko min purse d’ina a wardrobe”
D’aukowar tayi ta miq’a mata ta ciro kud’i tabata tare da nuna mata kwalbar turaren dazata siyo mata.
Sallama tayi mata ta fice.

Parking sukayi a bakin q’aton mall d’in kusa da wata bak’ar mota duk gilasanta tinted ne an bud’e k’ofar driver side mamallakin motar ya zuro k’afarshi d’aya waje sanye cikin bak’in covershoe kamar yadda wandonshi ya kasance bak’i sosai takalmin ya haska farar k’afar.
Ta gefen motar tazo ta wuce ta shiga cikin mall d’in.

Cosmetics side ta nufa ta fara duddubawa tana zab’ar wanda takeso tunawa tayi da saq’on turaren Aunt Salma data bata sanin halinta na mantuwa yasa ta fara duddubawa ko zata ganshi anan ganin bata samu anan ba yasa ta fara baza ido wasu wuraren, can ta hangoshi cikin tulin wasu turarukan wajen ta nufa idanunta akan turaren ba zato taji tayi karo da mutum purse d’inta ta fad’i k’asa shima wanda sukayi karon man gashin dake hannunshi ya sub’uce k’asa.
A tare suka sunkuya batare da sun kalli junaba shi yakai hannu kan purse d’in ita kuma takai kan sportin waves d’in dake kusa da ita suka d’ago a tare da niyyar bawa juna haquri idanunsu suka sarq’e cikin na junah…
Mrs Salees Mu’az.

 

*DR. SAIF*

©Oum Hanan

Bismillahir Rahmanir Raheem

Haske writer’s association
(Home of expert & perfect writer’s).💡

Free page
No 4…

Zaku biya kud’inku ta wannan account number d’in
0781515544 ibrahim sani Access Bank.
Sai kuyi screenshot na payment dinku ta wannan number
09133396869
Kokuma katin waya na MTN ta wannan number dake sama.
Masu son shiga grup sai suyimin magana ta number dake sama
200 kacal ba yawa😃😝.
Saina jiku🥰😍🤝🏻

 

Baki bud’e kowa ke kallon wanda ke gabanshi tuni fuskar kowa ta canza, especially Saif da dama kullum fuskar a cunkushe take saiya k’ara murtuke ta sam ba alamun rahma a cikinta.

“Mutane saikace makafi, suna ganin mutum bazasu iya kaucewa ba”. Ayshaa ta fad’a tana jan tsaki tare da warce purse d’inta dake hannunshi ta dangwarar da man gashin dake hannunta a q’asa ta miq’e da niyyar barin wajen.

Sosai ranshi ya b’aci idanunshi har sun fara kad’awa.
“Wani tsakin kuma dai again?”.
Ya fad’a cikin ranshi tare da miq’ewa cikin wani irin zafin nama.
Ba zato taji an turata wani d’an corridor daba komi a wajen, bayanta ya bigi bangon wajen.
“Ochhh”ta fad’a a hankali tana runtse idanunta saboda azabar zafin daya ratsa k’ashin bayan nata ta saki purse d’in hannunta q’asa.

A zafafe yake tunkarota da wani irin taku cikin ranshi yana ayyana irin punishment d’in dazai bawa mara kunyar yarinyar.
Wani masifaffen tsoro ne ya ziyarci zuciyar Ayshaa gabanta banda fad’uwa ba abinda yake amma tak’i barin tsoron ya bayyana a kan fuskarta harda k’arfin halin jefa masa harara nan kuwa k’irjinta kamar ya faso ya fito saboda tsoronshi, innalillahi kawai take ambata saboda batasan irin hukuncin dazai yanke mata ba kuma da ganinshi ba imani zaiyi ba.

Daf dazai k’arasa wajenta zuciyarshi tagama ayyana masa irin hukuncin dazai yanke mata dan haka yana zuwa baiyi wata wataba yasa hannu ya fisgota da uban k’arfi ta fad’a k’irjinshi hannu yasa ya d’ago fuskarta ta k’arfin tsiya.
Ganin abinda yake shirin yi yasa gabanta yayi mummunan fad’uwa ta shiga kakkauda fuska tana k’ok’arin tureshi saidai ko gezau baiyiba tamkar wani dutse yabi duk ya cumimiyeta.
Ganin ba iya k’wacewa zatayi ba yasa ta datse bakinta b’am, ganin haka yasa yasaka lallausan hannunshi guda d’aya ya toshe mata hanci ta yadda bata da damar shaq’ar numfashi.
Tuni numfashin Ayshaa ya fara kaikawo bai samu hanyar fitaba ganin haka yasa dolenta ta bude bakinta tuni ya shigar da nashi bakin cikin nata(wuuuuu Saif😲😳🤨 dama irin hukuncin kenan🙄).
Wani mulmulallen abune ya tsayawa Ayshaa a maq’ogoronta tsabar bak’in ciki.
Wani mahaukacin kiss ya shiga yimata tamkar zai cinye bakin gaba d’ayanshi kala kalar mugunta ya dinga yimata a cikin bakin, tun tana k’ok’arin tureshi harta sadaq’ar tai laq’was a k’irjinshi tana shan nau’ikan azaba a cikin baki😥😀.

Sai daya d’auki mintuna yana gana mata axaba sannan ya saketa ya k’ara turata baya yabar wajen cikin sassarfa.
Duk yadda taso riq’e kukanta hakan ya gagara nan ta sulale k’asa tasaki wani irin kuka mai cin rai wata tsanarshi na ratsata sosai abinda yayi mata yayi mugun tsaya mata a rai ashe banda wulak’anci har iskanci ya iya kenan?”.

Sai data dad’e tana zaune tana sharb’ar kukanta, kuma har lokacin ko mutum d’aya bai gifta ta wajen ba.
Purse d’inta kawai ta d’auka batabi takan body spray guda biyu data fara d’auka ba ta fice tana share hawaye.
Duk yadda isah ya dinga tambayar ta abinda ya faru k’in tanka mata yayi har suka k’arasa gida ta fice da sauri har tana had’awa da d’an gudu ta shige gidan, da kallon mamaki isah ya bita yana mamakin abinda ya faru da ita yaga dai k’alau suka fita da ita kuma harta shiga store d’in baiga wani canji a fuskarta ba, to ALLAH kad’ai yasa meya sameta.

Kan cinyar Aunt Salma ta zube tana k’ara sakin wani kukan, d’agota Aunt Salma tayi a rikice tana tambayar ta da lafiya?”
K’in amsa ta tayi ta cigaba da kukanta , da k’yar Aunt Salma ta rarrasheta gabanta sai fad’uwa yake tana tunanin abinda yasamu y’ar k’anwar tata.

“Tell me little sis meya faru haka?”. Aunt Salma ta fad’a tana k’ara share mata hawaye.

Sai dataja majina sannan tace
“Aunt wani ne mukayi karo dashi a mall d’in”.
Sakin baki kawai Aunt Salma tayi tana kallon Ayshaan da mamakin tab’ararta.
Tsaki ta d’anyi kafin tace
“Amma kedai Ayshaa anyi shagwa6a66iya wllhy, yanzu dan kunyi karo da wani shine abin kuka dan tsabar shiririta?”

”Aunt zafi fa naji q’aton kai gareshi fa,tace tana turo baki.
Dariya Aunt Salma tayi tace
“Kodai ke kikeda raki?, Tab’arar autanci kawai ke aiki dake, ALLAH ya kyauta miki ni d’agani inje inyi aikin gabana.
Tashin tayi ta figi purse d’inta ta wuce bedroom d’inta.

Purse d’in ta jefa kan gado ta fige gyalen datayi rolling shima ta jefa kan bed tabi bayansu jagwaf ta kwanta ruf da ciki, ganota kawai take wannan mugun Dr’n yana kissing d’inta wani bak’in cikin na k’ara shigar ta, kamar wadda aka zabura ta tashi da sauri ta shige toilet bayan ta zame abayar jikinta.
Wanka tayi ta matsa maclain a brush ta fara dirzar bakinta.
Tsaye tayi gaban mirror’n toilet d’in tana kallon bakinta dayai wani irin jawur ya d’an d’aga kad’an
Hannu takai kan lips d’in tana shafawa a hankali saboda irin zafin dayake mata.
“ALLAH ya isana ban yafeba wllhy mugu kawai”, ta k’arasa maganar tana share wasu hawayen dasuka taho mata.
Fitowa tayi ta nemi wata doguwar riga marar nauyi tasa ta kwanta saidai duk juyin dazatayi saita shaq’i mayen turarenshi mai sassanyan qamshi daya cika dakin nata wanda yake jikin doguwar rigar data cire duk yabi ya cika d’akin, saboda irin kokawar dasuka sha yasa rigar tasamu rabonta sosai.
A fusace ta diro daga gadon ta dauki rigar ta cumimiyeta ta jefa wardrobe (kamar ita tayi laifin😹).

Saidai kuma wata sabuwa inji y’an caca qamshin mouth fresh d’in daya fesa ya addabi bakinta duk da brush d’in datayi hakan baisa ta daina jin kamshin ba a bakinta.
“Maye kawai”.
Ta furta hakan tana turo baki gamida lumshe ido tanason yin barchi…
Mrs Salees Mu’az.

 

*DR.SAIF*

©Oum Hanan

Bismillahir Rahmanir Raheem

Haske writer’s association
(Home of expert & perfect writer’s).💡

Last free page
No 5…

Ga mai buk’atar cigaban book d’in nan zai tura 200 ta wannan number asusun
0781515544
Screenshot na payment kuma ta wannan number
09133396869
Ko kuma katin waya na MTN 200 a wannan number dake sama.
Ga masu son shiga grup sai sumin magana duka dai ta wannan number.
Saina jiku😍🤝🏻.

Kai tsaye gida ya wuce ranshi a b’ace yarasa minene had’inshi da yarinyar, tsaki yaita faman jerawa har ya isa gidan.
Daga yadda ya dinga matsa horn d’in a zafafe ya tabbatarwa da baba maigadi ba lafiya,dan haka cikin rawar jiki ya bud’e gate d’in ya shiga da motar.
Hannu kawai ya d’aga masa lokacin dayake masa sannu da zuwa dukda dai dama bawani sakar musu yakeyi ba amma yana tsayawa suna d’an gaisawa sama sama yaukam ko saurararshi baiba ya wuce yanada tabbacin tab’oshi akayi daga waje.

Imaan kawai ya tarar a parlour tana duba handout.
“Sannu da zuwa Yaya”, ta fad’a tana binshi da kallo.
Uffan baice mataba ya nufi side d’inshi. “ALLAH ya shirya matar mutumin nan ta shiga uku wllhy” ta fad’a q’asa q’asa tana tab’e baki.
“Ke kuma kedawa?” Mamie da saukowarta kenan taji tana magana k’asa k’asa.
Baki ta turo tace
Mamie nida Yah Saifu mana ya shigo ina masa sannu da zuwa ko kallon inda nake baiyiba bare ya tankamin”.
Murmushi Mamie tayi tana d’an girgiza kai tace
“Oh Imaan inda sabo fa yaci ace kin saba da halin Abbana a gidan nan”.
Kamar zatayi kuka tace
“ALLAH Mamie banajin dad’i ace niban isa in zauna da d’an uwana muyi hiraba yaji damuwata ba muyi shawara a tsakaninmu”.
“Toh yazaki? Haka yayi shi sai haquri”.

Tun kafin ya shiga bedroom d’in nashi ya cire suit d’in ya fara b’alle bottom d’in shirt d’in ta ciki yana shiga ya jefasu kan sofa ya zame wandon bayan ya cire takalmin ya rage dagashi sai boxer da singlet farare ya shige toilet.
Shower ya sakarwa kanshi ruwan sanyin ya shiga ratsashi, idanunshi a rufe yake hango kissing d’in dayayiwa yarinyar duk da yayine dan punishment d’inta hakan bai hanashi shiga wani irin yanayi ba a lokacin kasancewar hakan bai tab’a faruwa dashi ba a tsawon rayuwarshi.

Sai daya dad’e a cikin ruwan kafin yayi off yasaka bathrobe ya fito da dan k’aramin towel yana goge sumarshi.
Shima d’in sosai kayan jikinshi suka samu tsarabar humrahr Ayshaan mai d’an banzan qamshin dad’i dan haka tuni dakin ya dauka, tsaki yayi ya yayibi kayan ya jefa a wardrobe(irin yadda Ayshaa tayi🤣).
“Mayyar yarinya kawai, mara kunya” yace yana wurgi da towel d’in, bathrobe d’in ya cire ya ciro jeans blue da da red shirt long sleeve yasa ya fesa zaunannen turarenshi.
Parlour ya fito wajen Mamie sai cika yake yana batsewa.
Duk dai tasaba ganinshi cukulen hakan bai hana ta tambayeshi lafiya ba?”
“Nothing Mamie”.
Ya amsa mata tareda miq’ewa ya k’ara yimata sallama ya fice.

Gidan mutuniyar tasa ya nufa Hajjah, 2dys bai samu ya lek’ata ba.

A parlour ya sameta ta k’urawa k’atuwar plasma d’in dake jikin bango ido tana kallon sunnah TV taci medical glass, tsaf tsaf da ita kamar koyaushe taci atamfarta mai kyau da tsada ta kafa d’aurinsu irin na tsaffi sai tashin qamshin turaren wuta parlourn yake.
Ciki ciki yayi sallama ya shiga.
Itama d’in a ciki ta amsa sallamar tare da juyar dakai tana tab’e baki,(rabuwarsu ta k’arshe da fad’a suka rabu shiyasa baikoma ba kuma sai ranar😀🤣).

Shima d’in kujera yasamu ya zauna bai mata magana ba(kamar dole😃😃).
Ganin yak’i yimata magana wajen mintuna takwas yasa ta
Had’e rai sosai ta kalli sashin dayake yanata latse latsen waya tace
“Tashi ka barmin gidana, miskilin banza miskilin wofi ka wani shigomin saq’am saq’am dakai ko magana bakaimin ba dogon banza kawai”.
Dariyarshi yaita k’ok’arin had’iyewa dan indai tace masa dogon banzan nan to yakaita maq’ura.

Fuskarshi ya daidaita dan karma yayi dariyar yace
Kaji min tsohuwa,aiba gidanki bane”, har lokacin kanshi na q’asa yana typing a wayarshi.
La’ilaha illallahu Muhammadan rasulullahi wato kace gori kazo yimin dama? To ai dad’in abin d’ana ne ya ginamin mara mutunci kawai”.
Ganin yadda ta daddage tana ta fad’a yasa ya ajiye wayar yataso yadawo kusa da ita yana murmushi ya kamo hannuwanta yana fad’in
“Haba My dear Hajjahnah kefa wani lokacin bakisan wasa ba nifa wasa nake miki”.
Kafin tace wani abu wata budurwa ta fito daga bedroom d’in Hajjahn tanada k’iba sosai kuma gajeriyace bata cika tsayiba.
Tuni y’ar fara’ar dake kan Saif ta b’ace saboda ganinta.
Itakam wani kyakkyawan murmushi tasaki tasaki ajiyar zuciya tana lumshe ido tare da bud’ewa a kanshi.
“Yah Saifu” ta ambata tana wani ma’qe murya tare da zama kusa dashi a hannun kujera.
“Ya kike?” Haka kawai ya fad’a tare da miq’ewa ya d’auki wayarshi ya fice ko sallama ma baiyiwa Hajjahn ba.

Baki sake duk suka bishi da kallo.
”ALLAH ya baka lafiya toh” Hajjah tace tana kyab’e baki, mutum saikace mai jinnu? Yanzun nan ka ganshi fuskar da d’an rahma anjima kuma ya tamketa tam toh ALLAH dai ya sauk’a”.

D’an murmushi Safnah tayi dan tasan ganinta ne yasa ya fita.
ALLAH ya gani tana matuk’ar k’aunar Saif kuma tanaji cikin ranta zata iya komiye dan taga ta mallakeshi tun tana yarinyar ta ta taso da sonshi ta ginu ta rayu akan k’aunar shi kuma tanajin babu abinda zai mata katanga dashi.
Safnah d’iyar yayar Daddyn Saif ce suna zaune a garin kaduna tayi karatu har zuwa matakin degree daga nan tasamu aiki a gidan radio dayake ta karanci aikin jarida ne.
Y’ar gayu ce sosai akwai kuma d’aukan wanka, itace y’a ta biyu a gurin Hajia safina sai k’annenta uku mata biyu namiji d’aya.
Yanzu ma takanas ta d’auki hutu a gurin aikinta duk dan saboda Saif d’in.
”Hajjah zanzo inje can gidan Daddyn”.
Safnah ta fad’a tana kallon Hajjah.
“Ai saiki ta zuwa dama ai nasan abinda yakawo ki garin nan shikuma wanda kike danshi baisan kinayi ba”. Hajjah tace tana miq’ewa tsaye ta shige d’aki.
“Koma dai meye naji kuma nagani, zan kuma dauki duk wasu tarin k’alubale indai akan Yah Saifu ne”.
Ta k’arasa maganar tana miq’ewa ta shiga d’akin datake sauka idan tazo.


Cikin y’an kwanakin sam Aunt Salma bata samun zama saboda bikin sister’n mijinta da za’ayi sai shirye shiryen biki sukeyi.

Yau alhamis ta kasance ranar kamu, ba yadda Aunt Salma batayi da Ayshaa ba akan ta shirya suje k’ememe tace ita bazata ba dataga zata matsa mata kuwa tace kanta ke ciwo,dolenta ta k’yaleta.
Ita kuwa Ayshaa hayaniyace kawai bataso shiyasa tak’i zuwan.
Haka Aunt Salma suka shirya itada Ikraam suka tafi suka barta ita kadai a gidan.
Wanka ta k’ara yi ta d’an murza mai sama sama ta bud’e wardrobe da niyyar d’aukar kaya idanunta suka sauka kan doguwar rigar data saka ranar dataje shopping, siririn tsaki taja tare da janyo rigar taji waiko har yanzun akwai k’amshin turaren ajiki, aikuwa tana kaita wajen hancinta taji k’amshin ya bugeta.
“Da k’yar idan mutumin nan ba maye bane” ta k’arasa maganar tana sakin wani tsakin gami da wurga rigar inda ta d’auko ta d’auki wata armless pich color tasa tasaka hula tabi gab’ob’inta da body spray ta k’ara kwanciya tare da janyo wayarta ta kira Ammi sukasha hirarsu.

Imaan ce da Safnah zaune a parlour suna hira.
Cikin takunshi na nutsuwa da mazantaka ta k’akk’arfan namiji majiyin k’arfi ya shigo main parlour din.
Sanye yake cikin 3qtr na farin wando da green d’in riga mai yankakken hannu k’aramin towel ne rataye a kafad’arshi hannunshi riq’e da ruwan Swan k’aramar roba sai d’ayan hannun dayake amsa waya, ga dukkan alamu dai daga gym yake dan har lokacin da ragowar gumi a fuskarshi duk daya goge.
Sallama kawai yayi a ciki dan ba wanda yaji sallamar ma.
Bai kalli ko sashin dasuke ba ya wuce.
Safnah da tunda ya shigo parlourn idanunta suke kanshi tamkar zasu fad’o tsabar kallo, gaskiya ne tasan idan tayi gamdakatar da mallakar Saif tasan ta tserewa sa’a namijine d’aya da d’aya a hakan ji take tamkar ta tashi ta rungumeshi taji d’umin jikinshi ta shaq’i mayen turarenshi dayake sakata cikin wani mood mai wuyar fassara, tasan kuma hakan bamai yiwuwa bane dan ko hannunshi tayi gigin tab’awa to ranar ta bani da masifarshi da bala’i dan akwai ranar datayi hugging d’inshi ranar har marinta saida yayi shiyasa nesa nesa dai.
Imaan dama tunda ta d’ago ta kalleshi ta maida kanta k’asa ta cigaba da chatting d’inta.
Wajen TV stand ya tsaya ya d’ora robar ruwan akai yana cigaba da wayarshi da sam ba’a jin miyake cewa.

Tuni Imaan ta tashi tabar parlourn Safnah data k’urawa bayanshi ido ta kasa jurewa a hankali ta tashi ta nufeshi ta zare towel d’in gabanta sai fad’uwa yake.
Kamar daga sama yaji kamar ana tab’a gefen fuskarshi, juyowa yayi yaga waye yayi arba da Safnah hankalinta gaba d’aya yana kan lallausan sajenshi, towel d’in ya warce yana binta da wani irin mugun kallo tuni jikinta ya fara rawa.
“I will call you later” ya fad’a da sauri yana katse wayar.
“Mahaukaciyar inace ke? Ban hanaki tab’amin jiki ba? Idan kika kuskura hakan ta k’ara faruwa zan baki mamaki”, ya ka’rasa maganar yana nunata da d’an yatsansa yabar wajen a fusace.

K’walla ce takawo idanunta tasa bayan hannunta ta share.
“Bazata gajiya ba, da haka har zuwa lokacin da hak’anta zai cimma ruwa.

Friday.
Ranar ake dinner d’in farida k’anwar Kabeer mijin Aunt Salma.
Da farko nok’ewa tasoyi dan batayi niyyar zuwa ba Aunt Salma tace sam bata isaba dolenta taje.
Haka nan badan ranta yasoba ta shirya cikin lace silver color da adon golden na flowers da aka mammana duwatsu doguwar riga mai rafa daga k’asa ta bud’e sosai saman kuma ya tsuke sosai rigar tayi mata kyau ta fitar da shape d’inta, ture kaga tsiya kawai tayi da d’ankwalin lace d’in ta yafa k’aramin Vail silver ta d’aura silver agogo sai jewelry d’in datayi amfani dasu duk silver ne, kyau kam tayishi Masha ALLAH duk da bawata kwalliya a fuskar powder ce kawai da lipstick da kwalli kamar yadda ta saba, tamkar ka sace ka fece🤣 sai zabga k’amshi take wayarta kawai ta d’auka ta zura plat shoes ta fito.

Gidansu Kabeer d’in suka nufa daga can zasu wuce Hall d’in da ake dinner.

Sai wajen 7:45pm sannan aka fara tattafiya dan har taso ta koma gida wai tafasa zuwa saida Aunt Salma tayi mata jan ido sannan ta haqura.

Hall d’in cike yake da mutane tako ina.
Amarya tasha kyau sosai itada angonta.
Nan aka fara gabatar da dinner.
Gaba d’aya zaman wajen gundurar Ayshaa yayi taita sakin k’ananun tsaki tana yamutsa fuska, duk yadda taso tafiya kuma Aunt Salma ta hanata dole sai lokacin da aka tashi.
Sai wajen k’arfe 11:22pm sannan aka tashi.
Ganin Aunt Salma ta tsaya wajen wasu friends d’inta yasa tayi gaba dan tagaji da tsayuwar.
A hankali cikin nutsuwa take takawa ta shiga duddubawa amma bataga motar gidan ba, kiran Aunt Salma tayi ta fad’a mata tace ta fita daga can waje isahn bai shigo cikin Hall d’in ba.
Takawa ta farayi a hankali kamar wadda ke tsoron taka k’asa.

Tana tafe tana masifa ita kad’ai cikin ranta na abinda yasa isahn bai shigo cikiba dan tafiyar akwai d’an tazara kafin a fita waje kasancewar babban hall ne.
Wani santsi ne taji ya kwasheta da batasan ko meyeba, ido ta runtse sosai tana kiran sunayen UBANGIJI gashi babu d’an abinda zata kama ta riq’e, gaba d’aya ta gama sakankancewa sai takai q’asa amma saita tsinci kanta bisa wani faffad’an k’irji.
“Alhmdllh” ta furta can k’asan ranta jin batakai ga k’asan ba, amma kuma waye haka ya tareta? K’amshin turaren jikinsu ne ya had’u a lokacin ya bada wani kalar qamshi mai masifar dad’i😌.
Yana ganin ta gama daidaita ta yadda koya saketa bazata fad’i ba ya tureta daga k’irjinshi.
A hankali murya q’asa q’asa tamkar mai rad’a yace
“Nonsense”
Kamar walk’iya yabar wajen, sai qamshin turarenshi dayabar mata.

“Nonsense?” Ta k’ara maimaita kalmar cikin al’ajabi, kaji wani d’an rainin hankali wayace ya taimaketa? Zaizo yana fad’a mata magana, sosai kanta ya kulle jin irin k’amshin turaren wannan mugun Dr’n to kodai shine? Ta jefawa kanta tambayar, “No impossible mezai kawoshi gurin nan?, Mutum da garinsu kice maizai kawoshi?
Koma dai meye damuwarshi ce ba tata ba sai data d’an jima a wajen tana ta kallon hanyar dayabi kamar zata k’ara ganinshi sannan ta tafi…
Mrs Salees Mu’az😍

 

*DR.SAIF*

©Oum Hanan

Bismillahir Rahmanir Raheem

Haske writer’s association
(Home of expert & perfect writer’s).💡

Ga masu buk’atar cigaban wannan book d’in zasu tura 200 ta wannan account number
0781515544
Ibrahim sani Access Bank.
Shaidar biyanki ta wannan number
09133396869
Ko kuma katin waya na MTN ta wannan number dake sama
Ga masu son shiga grup sai suyimin magana duka ta wannan number dake a sama.
🥰😍🤝🏻.

No 6…

Suna komawa toilet ta shiga tayi wanka kota warware gajiya dan tib’is take jinta.
Tana fitowa ta zura dress night riga da wando light purple ta kwanta.
Asubah tagari
Mutuniyar Saif😀.

★★★
K’arfe bakwai da y’an mintuna ya fito cikin shirin fita.
Yau shigar hausawa yayi maroon d’in shadda gezner sai maik’o take da k’yalli, ya kafa hula zannah kalar shaddar wrist d’inshi d’aure da bak’in agogo na fata daya haska farin hannunshi sai bak’in takalmi half cover da yasaka sosai yayi kyau kayan sunyi matuk’ar amsarshi kasancewar bai cika mu’amala da manyan kayaba shiyasa duk lokacin dayasa yakeyin kyau sosai.

Safnah kawai ya tarar a parlourn kamar mayyah😄 sarai kuma yasan dalilin zaman nata saboda dashine.
“Wow wow” kalmar data dinga ambata kenan cikin ranta lokacin data ganshi ba k’aramin tafiya da imaninta yayi ba taji tamkar taje gareshi.
“Good morning Yah Saif” tace cikin kashe murya tana wani fari da idanuwa.
Baima kalleta ba bare yasan anayi
“Morning” kawai yace mata ya stairs jin kamar ta biyoshi yasa ya juya ya zabga mata harara tare da cewa
“Ina zaki?”
Dabarbancewa tayi ta rasa abinda zatace masa karshe dai tace
“Zanje gaida Mamie ne Yah Saif”
“Meyasa tun d’azu bakije ba? C’mon friend b’acemin dagani”.
Juyawa tayi kamar zatayi kuka ta koma parlourn ta zauna.
Tsaki yaja ya cigaba da taka stairs d’in cikin nutsuwa.

Knocking yayi a k’ofar bedroom d’in Mamie’n ta bashi iznin shiga.
A hankali ya murd’a handle d’in k’ofar ya shiga, a zaune ya sameta kan sofa tana karanta hisnul muslim har k’asa ya durk’usa ya gaisheta ta amsa tareda yimasa addu’a kamar yadda ta saba.
Sallama yayi mata tabishi da fatan nasara a aikinshi.
Har yakai bakin k’ofa tayi kiranshi ya dawo, littafin ta ajiye tare da maida dukkan hankalinta kanshi tace
“Babana ina maganar mu ta kwana ne, har yanzu banji ka k’ara cewa komiba?”
Kai ya sunkuyar tare da sa hannu ya turo hular gaban goshi ya shiga shafa k’eya.
“Ahmm Mamie, d’agowa yayi ya kalleta yaga yadda ta tsura masa ido saiya kasa cigaba da maganar dama kuma ba abin fad’ar.
Kai ta kad’a tace
“Alamu sun nuna har yanzu bakayi wani motsi bako?”
“Ai Mamie….”dakatamin ai me?” Mamien ta katseshi
“Munyi waya da Daddynku d’azun nan(yayi tafiya ne Mexico), yabani saq’o in fad’a maka kafin yadawo ka tabbatar kana da abinda zaka fad’a masa in kuma ba hakaba shi yana da abinda zai fad’a maka”.
“Mamie saura fa one week yadawo for God sake taya zan nemi mata cikin sati d’aya” yayi maganar kamar mai shirin kuka.
“Kaci gidanku” Mamie data rasa abin fad’a dan takaici ta sakar masa dak’uwa😄
“Inace fin shekara muna fama dakai?,to nidai y’ar saq’o ce kuma na isar tashi kaje ALLAH ya kiyaye”.
Da “Aameen” ya amsa ya tashi ya fita.

Har lokacin Safnah na parlourn, tana ganinshi kuwa ta miq’e
“Yah Saifu” tamkar kurma haka ya wuceta ya fita daga parlourn.
K’ugu ta kama da duka hannayenta tana kad’a kai kamar k’adangaruwa lallai taga alamun saita tashi tsaye a kanshi yanada taurin kai dana zuciya wannan abinda take bazai kaita ko inaba zata tafi amma zata dawo da shirinta dolene ta mallaki Saif a matsayin mijinta.

Yana shirin tashi daga aiki Mukhtar yayi sallama office d’in ya shigo.
Mukhtar abokinsa ne da suka had’u a Egypt lokacin dayaje karatu, tun dai baya kulashi harya fara biyawa ta kanshi saboda ganin yanada hankali kuma yanayin abinda yakaishi q’asar, sosai suka qulla abokantaka kuma akayi sa’a shima d’an Abuja ne shikuma engineering ya karanta, yanada surutu sosai abinda ke had’asu fad’a kenan da Saif idan ya isheshi da magana shima bashida auren yanadai niyyah.
“Mr Man harka tashi kenan?”
“Eh” kawai yace masa yana cigaba da zura laptop d’inshi a jaka.
“Muje kawai to ka saukeni”
“Saboda kai bakada motar ne ko yaya?”
“Wllhy yanzun nan nataho da ita ta lalacemin a hanya na kira bakanike za’a gyara”.

Tafe suke a motar Mukhtar duk ya cika Saif da surutu yana bashi labarin yarinyar dayake so
“Oh my God Mukhtar wllhy ka isheni kaina harya fara ciwo” Saif ya fad’a yana dafe goshinshi.
Dariya Mukhtar ya d’anyi yace
“Wai dan ALLAH kai sai yaushe zaka fito mana da girlfriend ne musha biki?”
Tsaki Saif yayi yace
“D’an iska maganar ka kenan dama ta aure gara ma dai kayi mu huta “.
“Toh kaiya gani mr man? Aure ai abin sone”.
Shiru Saif ya d’anyi tunawa da yayi da abinda Mamie tace Daddy yace a fad’a masa.
“Yadai?”
Mukhtar yayi tambayar yana kallonshi.
K’aramin tsaki ya saki ya d’an shafi gefen girarshi yace
“Yanzu haka fa case d’in da muke da maigida(Daddy) kenan ya uzzuramin da maganar aure wllhy d’azu Mamie tacemin yace kafin yadawo in tabbatar nasamu yarinyar danake so inba hakaba shi yanada wadda zai had’ani”
“Das vry good, Daddy ya burgeni sosai fa” Mukhtar yace yana dariya.
Harara saif ya jefa masa bai daice komiba ya cigaba da tuk’inshi.
“Haba mutum yana fama da cuta yayi aure ya huta yak’i, gara suyi maka hakan ai”.
“Cutar uban me nake da ita?”
Saif yace yana masa wani irin kallo.

Dariyar shak’iyanci Mukhtar ya saki yace
“Man mubar maganar nan kawai amma nina sani kanada buk’atar mace a kusa dakai”.
“Nina fad’a maka haka munafuki?”
”Baka fad’a ba amma nina sani ai sau nawa ina kamaka kana shan lemon….bugu ya kaiwa bakinshi yai saurin kaucewa yana dariya.
K’wafa yayi yace
“Zanci ubanka ne vry soon wllhy”.
Shidai Mukhtar dariya kawai yake masa.

★★★
7dys After.
Week end ne ranar dan haka har wajen tara da rabi yana barci.
Ringtone d’in wayarshi dake kan bed side drawer ne ya katse masa barcin, hannu yasa ya janyo wayar yana sakin d’an tsaki.

Tuni ya wartsake sosai ganin sunan Dad dake yawo saman screen d’in, kwananshi d’aya da dawowa kenan kuma yasan maganar da za’ayi masa.
A sanyaye ya tashi ya zura ash color d’in jallabiyyah saman boxer’n dake jikinshi ya zura slipper white ya d’auki wayarshi ya fita.

Suna zaune a parlour suna jiranshi, tun dayaga Daddy ya d’ora k’afa d’aya kan d’aya yana girgizasu yasan ba za’a raga masaba🤣 danko sallamarshi sai Mamie ce ta amsa.

Kusa da k’afafun Daddyn ya zauna yana satar kallon Daddyn gaba d’aya ya gama tsarguwa.

“Barkanku da safiya”, yace kanshi a q’asa.
Ba wanda ya amsa sai sunanshi da Daddyn ya kira.
A hankali ya amsa tareda d’agowa ya kalleshi.
“Yanzu Saifu ka kyautawa kanka ka kyauta mana kenan?”
Yawu ya had’iya ya k’ara k’asa dakai yace
“Daddy kayi hakur….”stop” Daddy ya katseshi a zafafe, lallai yasan daddy yakai maqura.
“Ina tarbiyyah da ilmin addinin da muka baka? Banyi zaton haka daga gareka ba Saifu.
Sosai kan Saif ya kulle dajin maganganun Daddy sunsha bambam da maganar auren dayake masa kafin yagama tunanin yaji abinda yasa kanshi yayi wani irin mugun sarawa
“Wace yarinyace aka ganku da ita a shopping mall kana kissing d’inta???”
A razane ya d’ago ya zubawa Daddy idanunshi yanajin wata irin fargaba da fad’uwar gaba.
Kan Mamie ya maida idanunshi itama yaga fuskar nan tata a had’e ba alamun fara’a.
“Innalillahi wa inna ilaihi rajioun” ya ambata cikin ranshi yana dafe goshinshi saboda irin sarawar da kanshi keyi.
“Tambayar kafa nakeyi Saifu” muryar Daddyn ta katseshi daga duniyar rud’anin daya tafi.
“Muna jinka”
Mamie tace a hasale.
Sam saiya rasa abinda zai fad’ar gaba d’aya kanshi ya kulle da wannan lamarin.
“Okay tunda bakada abin fad’a ni ina dashi, inaso ka bud’e kunnenka sosai kajini wannan yarinyar da aka ganku tare zansa a bincikomin gidansu zamuje muyi magana dole zaka aureta dan bazaka b’ata mata rayuwa a banza ba kuma cikin 2months nakeso ayi komi a gama understand?”
Cikin kid’ima ya bud’e baki yace
“Wllhy Daddy abinda kake zat…..”banason wani dogon magana dole ayi abinda nace ka riga da ka b’ata min suna hankalinka ya kwanta” daga haka ya tashi ya fice gaba d’aya daga gidan.
Wajen Mamie ya rarrafa ya kamo hannuwanta ya zuba mata idanunshi da suka sauya launi lokaci d’aya girgiza mata kai ya shiga yi yarasa mema zai fad’a mata.
“Wllhy kabani kunya Saifu yaushe kazama haka?”

“Wllhy Mamie kinji na rantse miki sam abinda kuke zato bashi bane kun bani tarbiyyah mai kyau taya zan aikata abinda kuke zargi a kaina, ko a lokacin danayi zaman k’asar waje ban aikata wannan mummunar d’abi’ar ba bare yanzu dana dawo gida gaban idanunku Mamie please kiyi tunani fa” ya k’arasa fad’a yana k’ara damk’e hannunta sosai jijiyoyin kanshi duk sun tashi rad’a rad’a.

“Toh idan ba haka bane yane Saifu?, Tabbas ance an ganka da yarinya a shopping mall”.
“Mamie nifa….”kayi kissing d’inta ko bakayi ba?” Mamie ta katseshi, bai saba yiwa Mamie k’arya ba hakan yasa duk ya dabarbance.
“Mamie punishment d’inta fa nayi bawai da wani niyyah nayi ba”.
“Punishment kamar yaya?” Mamie ta tambaya.
“Mamie yarinyar ne batada kunya an tab’a kaita hospital d’ina in dubata tayimin tsaki kuma muka had’u a Mall nan ma tayimin tsakin kuma Mamie kinsan banason ana min tsaki shine nikuma nayi…..shiru yayi ya kasa k’arasawa sai sosa kai yake.

Harara ta zabga masa tace
“Shine da sakarci da wauta kayi kissing d’inta? Haka ake horon?.
Baki ya d’an turo yace
“Ni Mamie narasa me zanyi mata ne”.
Tsaki tayi tace
”Toh kajawa kanka ai”.
Dan ALLAH kiyi wani abu akai Mamie please help me”.
Kai ta girgiza tace
”Karma kasani a ciki kasani sarai idan yayi magana baya canjawa dan haka kayi addu’a kawai ALLAH yasa hakan yazama alkhairi”.
Ji yayi tamkar ya d’ora hannu bisa kanshi yayita ihu ko zasu fahimci halin dayake ciki.
A nan ta tashi ta barshi yanata saq’e saq’en zuci, zaici uwar yarinyar nan kuwa😳.

About the author

Hausa_Novels

Leave a Comment