Littafan Hausa Novels

DijanGala Hausa Novel Complete

Yadda Ake Rikita Maigida Yayin Kwanciya
Written by Hausa_Novels

Dijan Gala Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

DIJANGALA

 

 

 

Page 1

 

 

Musty tsaye gaban mirrow yana taje gashin kansa da comb, wayarsa ne yayi kara alamun kira yana shugowa, ya kalli allon wayar “Sweet Hamra” a rubuce, murmushi yayi sai da wayar ya gama ringing sannan ya dauki wayar ya kirata, bayan ta amsa ya kara wayar a kunne

 

“Love ya kike?

 

Ta bangaranta murmushi tayi, kwance take kan gado cikin nishadi tana dan juye juye

 

Baby kun taso ne?

 

“A’a bamu taso ba, amma yanzu haka ma na gama shiri, yanzu zan fita mu tafi Airport”

 

To Allah ya kawo min kai lafiya

 

“Amin love”

 

Aje wayan yayi gefe ya dauki comb ya cigaba da gyaran kanshi, bayan ya gama yaje ya zauna bakin gado, akwai wani karamin tabir a gabanshi dake dauke da farantin silver, tabar wiwi ne duk an gama nade su, ya dauki daya ya kunna ya fara zuga yana fitar da hayaki

Kishiyar Kabila Hausa Novel Complete

 

“Ta bangaran Hamra tashi tayi daga kan gado ta fito, falo ta shugo wani kamshi ya tare ta, komai tsaf tsaf a falon, kitchen ta nufa ta samu Mummy da masu aiki na sarrafa kayen shaye shaye da ciye ciye, hakan na faruwa a duk lokacin da Mustapha zai dawo

 

“Mummy sannu da aiki”

 

“Yauwa Hamrah”

 

“Yanzu muka gama waya da Ya Mustapha, wai yanzu zasu tafi Airport”

 

“Nima ban dade da gama waya dashi ba”

 

“Mummy bari naje nayi wanka na shirya kafin ya iso”

 

“Ya kamata”

 

Hamrah ta fita, Mummy ta cigaba da ayyukanta

 

 

 

Dije na cikin daki tana bachci kamar a mafarki taji karan jirgi, a gigice ta farka tayi waje da gudu,

 

Inna na tsakar gida tana gyarar shinkafa ta ga Dije ta fito da gudu, bata yi mamaki ba don tasan soyayyar dake tsakanin Dije da jirgin sama, Inna ta cigaba da gyarar shinkafanta

 

Tsayawa Dije tayi jikin ginin kasa, tana kallan jirgin tana murmushi cikin nishadi can kuma ta daga hannu tana ma jirgin Bye bye

 

Inna ta kalli Dije “idan kin gama kizo kije ki debo mana ruwan aiki”

 

Dije ta turo baki “Ni Inna wallahi na gaji, ni kadai zan yita aiki a gidan nan”

 

“Lallai kuwa Dije wallahi idan baki debo ruwa ba a gidan nan, babu ke babu cin Shinkafa da wake dake kan wuta”

 

Dije ta zaro ido ‘Inna da gaske shinkafa da wake zaki dafa”

 

“Tsaya a nan kar ki tai ki debo ruwa ki gani”

 

“Inna wallahi zanje”

 

Dije zuwa tayi ta dauki tayarta da abin garawa, sannan ta dauki roban debo ruwa

 

“Kar dai kije ki fasa min roba”

 

Dije ta fita da gudu tana gara tayarta cikin kwarewa

 

Da fitar Dije bata tsaya ko ina ba sai wajen me sayar da wainar fulawa, zama tayi kan roban a gaban me wainar fulawan

 

“Bani na goma”

 

Ina kgudunta, “Bashi zaki bani”

 

“Ummana ta hanani bayar da bashi”

 

Satar idonta Dije tayi tasa hannu ta kwashe Wainar fulawan, sannan ta dauki roban ta da tayarta da abin garawa

 

“Laaa Dije dawo min da wainar fulawa na”

 

Dije bata kulata ba ta cigaba da gudunta, sai da tayi nisa sannan ta tsaya ta fara cin wainar fulawa, bayan ta gama taje bohol inda ake diban ruwa, ta tarar da layi sosai amma bata ranta tayi taje ta cire roban dake gaba ta saka nata, babu wanda ya iya magana don sanin halinta

 

Wani dan matashi kasa hakuri yayi sai da yayi magana

 

“Dije gaskiya ba zai yuhu ba sai kin cire roban ki”

 

Dije ta galla masa harara “to idan ka isa ka cire min roba mu gani”

 

Sa hannu yayi ya janye roban Dije dai dai lokacin ta dauki katon dutse ta biga masa a kai, ihu yayi tuni jini ya fara fita daga kansa, tsorata tayi da sauri ta dauki roban ta da tayarta da abin kadawa ta ci kafa

 

Bata tsaya ko ina ba sai wani wurin dibar ruwa, nan ma akwai layi, hankalin ta kaiwa yayi wurin wani dan matashi da yake dauke da gwafa a hannunsa, tana kallan yadda yake sa dutse a gwafa yana harbawa, karasawa tayi wurinsa

 

“sannu ko”

 

“Yauwa sannu”

 

Ina son wannan abin (ta nuna gwafa) ka bani kyauta

 

“Taya zan baki kyauta nima ina da bukatarsa”

 

Don Allah ka bani,

 

“Sai dai ki siya”

 

Ta sosa kai tana tunani

 

“Sai dai na baka wannan roban” (ta nuna masa roban da tazo dibar ruwa dashi)

 

ya tsaya yana kallan roban

 

“To shikenan ga gwafar, bani roban”

 

Ta mika masa roban ta amshi gwafar juyawa tayi cikin farin ciki ta wuce

 

 

 

Hamrah ta gama shirinta tsaf cikin wani atamfa riga da siket, tayi kyau sosai, ta shafa turaruka sun kai kala goma, bayan ta gama ta fito falo taga Mum da Dad tsaye, Mum na gyara ma Dad zaman Necktie

 

Murmushi Hamrah tayi don ba sabon abu bane, in dai Mum da Dad ne soyayyarsu a fili ne kuma koda yaushe cikin yinsa suke yi

 

Mum ta kalli Hamrah “wow irin wannan kyau haka my dear”

 

Hamra ta ce Mum ai ban kaiki kyau ba, a kullum kina kara zama Yarinya ce

 

Dad ya ce kuma fa haka ne, sai yasa har yau na kasa kara aure

 

Mum ta watsa masa harara cikin wasa, wayar Dad ne ya shiga ringing, bai dauka ba saboda babu suna

 

“Daddy kiranka fa ake yi”

 

Share kawai babu suna

 

A karo na biyu kira ya shugo wayarsa ya duba allon wayar “NEXT KING”

 

Murmushi ya baiyana a fuskarsa

 

“Yaron mu ne”

 

Mum da Hamrah duk murmushi suka yi

 

Amsa kiran yayi ya kara a kunne

 

“Hello My Dear Son”

 

Shuru yayi yana sauraren dayan bangaren, tashin hankali ya baiyana a fuskarsa hakkun, Mum da Hamrah sun kula da tashin hankalin da yake ciki,

 

“Ok, I am coming” (ya katse wayan)

 

Dad meke faruwa ( a rikice Mum tayi tambayar)

 

Kwantar da hankalin ki bari na je na dawo koma miye ne zaki ji

 

Mum zata kara magana ya katse ta “I am sorry, don’t say anything, bari naje na dawo kawai

 

Dad ya fita suka bishi da kallo

 

Allah yasa dai lafiya, gabana ya fara fadi (Hamra ta fada jiki a sanyaye)

 

 

Nima gabana fadi yake yi (mum ta fada)

 

Dad direct Airport ya wuce, yana isa ya shiga private Jet sai America

 

 

 

Dije na tafiya ta hango wani manomi a gonarsa yana noma, daukar dutse tayi tasa a gwafa ta harbi mutumin a baya a rikice ya waigo, Dije ya gani, cin kafa tayi, gaskiya Dije ta kware a gudu, ba’a cin mata idan ana tsere

 

Manomin ransa ya bace sosai “zan kamaki watarana, sai kin raina kanki”

 

Ya koma ya cigaba da nomansa

 

Dad hankalin shi a tashe ya shiga cikin Asbitin, sannan aka nuna masa dakin jinyar da Mustapha yake ciki

 

Tsayawa yayi cak yana kallan Mustapha dake kwance baya motsi, an dasa wasu na’urori suna aiki a jikinshi suna taimaka masa, da alamu ya samu karaya da dama a jikinsa, sannan ga tarin bandeji da aka zagaye kanshi dashi

 

“Inna lillahi wa inna ilaihir raji un, my Son kaine haka”

 

Kasa jurewa Dad yayi, kuka ya subuce masa, wayarsa ce ya shiga ringing ya kalli allon wayar “First lady” a rubuce

 

Ya amsa ya manna a kunne

 

“Hello”

 

Jin muryarsa yasa ta kara rikicewa

 

“Please Daddy what is going on”

 

(Dad bakinshi na rawa) babu komai, ki kwantar da hankalin ki

 

“Hankalina ba zai taba kwanciya ba har sai nasan halin da ake ciki, idan ka boye min wani abu shi zai sani a damiwa”

 

Dad ya fashe da kuka, hankalin ta ya kara tashi

 

Na shiga uku, meke faruwa ne?

 

“Danmu ya samu hatsari”

 

Inna lillahi wa inna ilaihir raji un ta fada (ta fashe da kuka)

 

“Mu gode Allah, kaf jirgin shi kadai ya rayu, yanzu haka ina tare dashi”

 

Ina son magana dashi (ta fada cikin muryar kuka)

 

“Bai farfado ba”

 

“Ba zan iya hakuri ba, yanzu zan biyo jirgi na taho”

 

Ba sai kin taho ba

 

“Daddy I can’t, gani nan zuwa kawai”

 

Ta katse wayar ta kalli Hamra da tunda ta fara wayar suna tare, a rikice ta kalli Mum

 

Mum Yayana yayi hatsari ko? Ta fada bakinta na rawa

 

“Ki kwantar da hankalin ki ai yana da ransa yanzu ma can zan tafi”

 

Mum mu tafi tare Hamra ta fada tana hawaye

 

To shikenan, jeki shirya

 

Hamrah ta wuce dakinta, Mum itama ta wuce dakinta, bada dadewa ba duk suka dawo a shirye, Mum ta tara ma’aikatan gidan tayi musu sallama da shaida musu su kula da gida, bayan nan suka wuce Airport, bada dadewa ba jirgi ya tashi sai America

 

 

 

Dije tana tafiya tana gara tayarta, sai da tazo wurin Baba me gyaren Radio sannan ta tsaya, karasawa tayi wurinsa

 

“Baba ina wuni”

 

Ya kalleta yayi murmushi “yau kuma Dije babu sallama”

 

“Na manta ne”

 

“To Dije ya akayi ne? ”

 

“Nazo ne kasa min wannan wakar nan”

 

“Wanne kenan? ”

 

“Ka manta, wanda ake cewa *Dijangala ta mai gari, ba auran talaka ba*

 

Baba yayi dariya sosai

 

“Dije kenan Dije Matar manya”

 

“Baba dagaske ni matar manya ce

 

“Insha Allah”

 

“Baba sai yasa ban taba yin saurayi ba, ina jiran wanda ya dace dani yazo, ina jin dadin yadda kullum kake kirana matan manya, kuma ni ina ji a Jikina ni matar manya ce, amma baba kasan banda yawan surutu, surutu na kad……. Baba ya dakatar da ita

 

“Maganar a isa haka Dije”

 

“To kunna min wakar Baba”

 

Baba ya dakko karamar wayarsa, da botiran duk sun kode, ya kunna wakar da Dije take so, amsar wayar tayi ta manna a kunnanta tana murna, bin wakar take yi, da wakar ya kai karshe ya shiga wani sai ta dawowa Baba dashi

 

“Ka kara samin naji”

 

Baba ya amsa ya kara sa mata wakar, ta amsa ta cigaba da saurara tana nishadi

 

Inna zaune tsakar gida tai tagumi tana jiran Dije, Aisha ce ta shugo cikin sallama, Inna ta amsa sallamar

 

“Sannu da gida Inna”

 

“Yauwa Aisha, kin ganin min Dije? ”

 

“A’a Inna ban ganta ba”

 

“Oh ni, tuntuni fa na aike ta debo ruwa babu ita babu labari”

 

“Inna bari naje na debo miki”

 

Aisha ta aje Jakarta ta dauki roba ta fita, Inna ta rike kai cike da takaicin

 

“Allah ka nuna min ranar da Dije zata yi hankali”

 

Bata gama rufe baki ba Mai Wainar fulawa ta shugo tare da mamanta, Inna na ganinsu gabanta ya fadi, jikinta ya bata Dije ta ja mata magana

 

Sannunku Inna ta fada tana mikewa

 

Maman mai wainar fulawa ta fara masifa

 

“Kar kice mana sannu, ya yarinyarki zata addabemu a gari, kullum idan yarinyata na sana’a sai tazo ta diba ta tafi, wannan rayuwa ce?

 

Jikin Inna a sanyaye ta ce don Allah kiyi hakuri in Allah ya yarda ba zai kara faruwa ba

 

“Gwara dai ki dauki mataki wallahi idan ba haka ba zan dauki mataki da kaina

 

“To a daiyi hakuri”

 

Bata gama rufe baki ba, wanda Dije ta fasawa kai ya shugo

 

Inna na ganinshi zuciyarta ya bada wani kara

 

“Na shiga uku, Bawan Allah kaima Dije ce ko? ”

 

To waye idan ba Dije ba ya fada cikin bacin rai ya cigaba, “wallahi ba don ke ba a garin nan da tuni mun dade da batar da Dije”

 

Don Allah kuyi hakuri, zan dauki mataki a kanta sosai, insha Allahu hakan ba zai kara faruwa ba

 

Dije ce ta shugo da gudu tana kada tayanta, tsayawa tayi cak tana kallansu, juyawa tayi a hankali zata fita, Inna ta dakatar da ita

 

“Idan kika sa kafa kika fita saina yi mugun bata miki rai”

 

Dije ta juyo cikin fushi

 

“Nifa sharri suka zo suyi min”

 

“Au kin tabbatar min ma da kinyi musu laifi kenan”

 

“Nifa banyi musu laifi ba”

 

“To meyasa kika tsargu? ”

 

Shuru Dije tayi tana harare harare da murguda baki

 

Inna ta kallesu “don Allah kuyi hakuri”

 

Maman mai wainar fulawa ta ce Da haihuwar wani dan gwara barinsa, ta ja hannun yerta suka fita

 

Wanda Dije ta fasawa kai kallan Dije yayi ya ce wallahi kina cin albarkacin mahaifiyarki, amma mu hadu a karo na biyu ki ga ikon Allah

 

Murguda masa baki tayi ya fita yabar gidan

 

Inna ta kalli Dije “ina robar ruwan?

 

Bakin Dije ya fara rawa, gwafar hannunta ta kalla sannan ta kalli Inna

 

“Inna naga mabukaci na bashi saraka”

 

Inna ta zaro ido gami da bude baki ta ce Roba na?

 

 

 

Mum da Hamrah hankalinsu ya tashi sanadiyar halin da suka sami Mustapha a ciki, sunyi kuka harya ishe su, haka suka cigaba da jinyar Mustapha

 

 

*BAYAN WATA UKU*

 

Mustapha kwance kan gadon jinya, ciwukan jikinsa duk sun warke gabadaya, sai dai wani abu daya tun daya farka baiyiwa kowa magana ba sai dai yana ta kallansu daya bayan daya

 

Dad yaje ya samu Likita a Office, Likita ya shiga yiwa Dad bayanin halin da Mustapha yake ciki

 

“Mustapha ya samu matsala a kwakwalwarsa, tunaninsa ya koma baya, zai dinga tuna abubuwan da suka faru yana karami, zai dinga tsoro yana razana, watarana zai dinga abu kamar yaro”

 

Dad ya zaro ido cike da tsoro, “me za’a yi akai, ko nawa zan bayar indai har zai samu lafiya”

 

Likita ya girgiza kai “Da akwai abinda za’a iya yi akai da anyi tuntuni, amma wannan nalurar da yake ciki bana din din din bane, a kowani lokaci zai iya dawowa dai dai, akwai magungunar da zan baku da zasu taimaka masa wurin dawowa da tunaninsa”

 

“Inna lillahi wa inna ilaihir raji un………..

 

“Mustapha kwance kan gado a dakin jinya yana kallan Mummy da Hamrah, Hamrah taje bakin gadon da Mustapha yake ta zauna tana masa wani kallo na soyayya”

 

Baby ka yi min magana mana (ta fada a shagwabe)

 

Ya tsura mata ido

 

Dad ne ya bude kofa ya shugo jiki a sanyaye, Mum ta karasa wurinshi da sauri

 

“Ya kuka yi da Doctor?”

 

Shuru Dad yayi yana kallan Mustapha

 

“Zuwa gobe zamu koma gida”

 

“Taya zamu yi mu koma yaronmu bai samu lafiya ba”

 

Dad ya shiga yin magana cikin takaici “warkewarsa ba yanzu ba”

 

Ta kalleshi cikin tsoro “ban gane warkewarsa ba yanzu ba”

 

“Doctor ya tabbatar min daya samu matsala a kwakwalwarsa, tunaninsa ya dawo baya, sai din ga yawan jin tsoro da saurin razana, watara zai rika yin abu kamar yaro”

 

Mum ta zaro ido gami da dafe kirji

 

“Na shiga uku”

 

Hamra ta tashi daga inda take tazo wurin Dad

 

Bakinta na rawa ta ce Dad yanzu mene ne mafita, ba za’a iya masa magani ba?

 

“Nalurar bana din din din bane ya tabbatar min a kowani lokaci zai iya dawowa hankalinsa, ta hanyar tunawa da wani abu daya faru dashi, kuma ya bani magungunar da zai dinga masa amfani dashi zasu taimaka masa sosai

 

Mum ta shiga yin kuka “Allah sarki my son”

 

Itama Hamra kuka ta fara yi, babu mai rarrashin daya daga cikinsu

 

Grandma ce ta budo kofa ta shugo hankalin ta a tashe, Hamrah taje da gudu ta rungume ta tana kuka

 

“Grandma” Mustapha ya furta

 

Duk kallansu ya koma kanshi

 

Hamrah ta ce laaaa yayi magana

 

Duk suka zo wurinshi suka kewaye shi suna kiran sunanshi

 

“Grandma ina chocolate dina? ”

 

Shuru Grandma tayi tana tunani a zuciyarta, “rabon dana sayawa Mustapha Chocolate tun yana primary, to make faruwa yanzu? a zahiri kuwa cewa tayi karka damu zan saya maka da yawa kasha a koshi”

 

“Sannan Grandma ina son Ball, ki saya min”

 

Zaro ido tayi ta kalli Dad “meke faruwa da Yaron nan?”

 

Dad ya ce Doctor ya tabbatar da tunaninsa ya koma baya, zai dinga yi kamar yaro

 

Grandma ta ce na shiga uku, yanzu miye abin yi

 

Karku damu zai samu lafiya, jarabtace ta samemu

 

Mustapha ya kalli Grandma “Grandma ina fushi da Dad da Mum sun san bana son allura, amma suna gani Doctor keyi min”

 

Grandma ta zauna gefensa ta rungumosa jikinta

 

“Kayi hakuri ba’a fushi da iyaye, tunda nazo kaga koda yaushe muna tare”

 

“Dad ya ce gobe ma zamu koma gida”

 

Grandma ta ce da yafi dai, ina son aje ayi masa maganin gargajiya

 

Dad ya kalleta, “haba Mama wani gargajiya kuma, Doctor ya bada magungunar da za’a rika masa amfani dasu ba sai an hada da wani ba

 

Grandma ta ce to shikenan, hakanma yayi

 

“Ina jin yunwa” Mustapha ya fada

 

Mum tayi farin ciki da ganin yadda Mustapha ke magana tsabanin baya “zaka sha shayi”

 

“A’a ni cornflakes zan sha”

 

“To shikenan bari na hada maka”

 

Mum taje hadawa Mustapha cornflakes, Grandma na aikin yi mishi tatsuniya, Hamrah da Dad nata gefe suna kallanshi, Mum tazo da cornflakes ta tsaya ta dayan gefenshi tana bashi cornflakes a baki yana sha

 

 

 

Dije sanye take da kayan islamiyyata turo baki tayi “ni Inna gaskiya na gaji da zuwa wani Islamiyya, sai ayi ta cin zalun mutane

 

Inna ta kalleta “ai kuwa ko mutuwa zaki yi sai kin tafi makaranta yau, haba Dije kin ki boko kin ki islamiyya, wannan wane irin rayuwa ce”

 

“To ba sai nayi aure ba”

 

“Wa kike tunanin zai aureki a garin nan, tunda nake ban taba ganin wani yazo wurinki zance ba, mazan garinma tsoronki suke yi”

 

“Basa zuwa wurina saboda ni matar manya ce, niba sa’arsu bace, Baba me gyaren Radio ya fada min ni matar manya ce, kuma yana samin wakar *Dijangala ta mai gari, ba auran talaka ba* kinga kenan niba matar talaka bace”

 

“Na gaji da wannan surutun naki, fita ki tafi”

 

Tura baki Dije tayi ta je zata dauki taya Inna ta dakatar da ita

 

“Makaranta zaki tai da taya? Baki isa ba, maza ajje ki tafi”

 

Dije ta fita tana maganganu “ni gaskiya an cika takura min”

 

Inna ta bita da kallo “Allah ya shiryeki Dije”

 

 

 

 

Dije na tafiya da sauri tana hadawa da gudu, don ita Dije a ka’ida bata iya tafiya normal ba, tana isa islamiyya, sai data tsinci duwatsu sannan ta shiga cikin aji babu sallama ta zauna, Malam ya tsaya yana kallanta

 

“Dije anya ke mutum ce”

 

“Malam daga zuwana kuma me nayi? ”

 

“Au bama kisan me kika yi ba?”

 

“To tashi ki fitar min daga aji”

 

Tashi tayi tana yayyatsine fuska, sai da taje kofar aji, ta saka dutse a gwafa ta harbawa Malam, Allah yaso bai sameshi ba, bata jira wata wata ba ta ruga a guje

 

Malam ya bita da kallo “mara mutuncin kawai, da kin tsaya mana, da dutsen nan ya same ni wallahi da da saina miki rashin mutunci

 

Ya cigaba da koyar da dalibai

 

 

 

 

WAIWAYE ADON TAFIYA

 

Alhaji Matawalle babban dan kasuwa ne kuma mai fada aji, cikakken dan karamar hukumar Gwarzo ne dake garin kano matarsa daya Hajiya Sa’adatu ita kuma bafulatana ce ta garin Azare dake garin Bauchi, yaransu biyu wato Sulaiman da Salman, Sulaiman ya gaji mahaifinsa a fannin kasuwanci sosai shi kuma Salman Likita ne, yafi mai da hankali a aikinsa, Sulaiman yazo ya yi aure, ya samu mata a karamar hukumar Hadeja dake Jigawa, Sunanta Hafsat, bada dadewa ba ta samu ciki ta haifi da namiji da ya ci suna Mustapha, bata Kara samun ciki ba sai bayan shekara uku, cikin yazo da matsala hakan yasa aka cire cikin, tun daga wannan lokacin bata kara samun ciki ba

 

Hafsat marainiya ce, iyayenta sun rasu tun tana karama, ta tashi a hannun yayarta Ramatu, babu gatan da Ramatu bata bawa Hafsat ba, ta tsaya mata akan karatun boko da islamiyya, ta tashi cikin wayewa da yenci, lokaci daya suka hadu da Sulaiman suka kulla soyayya har ya kai ga yin aure

 

Yaran Rahmatu biyar, Babban cikinsu Mahmud sai Haruna sai Fatima sai Aisha, autarsu ita ce Khadija, wachcha ake kira da Dijangala, dukka yaranta sunyi aure, Aisha da Dije kadai suka rage, kuma yaranta gabadaya suna yin makaranta har matakin Jami’ar amma banda Dije da ko primary ta gagara tsayawa tayi, hakama fannin islamiyya taki yi, sam sam Dije ta tsani karatu

 

Salman kanin Sulaiman shima yazo yayi aure, yer Mubi ya aura na garin Adamawa sunanta Halima, bada dadewa ba ta samu ciki ta haifi yerta d ta ci suna Hamrah lokacin Mustapha nada shekara goma a duniya

 

Mustapha ya tashi cikin soyayyar yer uwarsa Hamra ko kadan baya son abinda zai taba ta, Tun Hamrah na karama yayenta suka rasu a hatsarin mota daga Adamawa zuwa kano, bada dadewa ba Alh Matawalle shima ya rasu

 

Mustapha da Hamrah suna girma suna kara shakuwa da junansu, har shakuwarsu ya koma soyayya tun suna boyewa har yazo ya baiyana

 

Tun Mustapha na karami yake mutuwar son kwallan kafa, ganin yadda yake son kwallan kafa yasa Dad ya kaishi makarantar kwallan kafa dake America, a kwana a tashi Mustapha ya zama shahararren dan kwallan kafa da duniya tasan da zamansa, ko karamin yaro ka tambayeshi *Musty Sule* ya san wa kake magana, kwarjini, daukaka da farin jini suka kara baiyana a fuskar Mustapha, kowa burinsa ya hadu da Musty Sule, a Nigeria kuwa ba karamin ji dashi ake yi ba, yayi mugun sunan da ba’a taba tsammani ba

 

Mustapha baya neman mata ko kadan kuma baya wasa da sallah, ko miye yake yi idan yaji kiran sallah ya barshi kenan, sai dai abu daya daya shiga zuciyarsa sosai shine tabar wiwi, yana bala’in son tabar wiwi, kuma a koda yaushe zaka sameshi yana sha

 

Mustapha da Dijangala basa shiri ko kadan, Dije na mugun jin tsoron Mustapha dalilin takura mata da yake yi kuma ko kadan baya mata da sauri, shi kuwa Mustapha a zahiri tsananta yayi saboda shi gaskiya baya son kazanta, ita kuwa Dije tana kaiwa wata daya bata yi wanka ba, sam sam Dije bata son wanka

 

 

Watarana Mum da Mustapha suka shugo Hadeja, Inna tayi farin ciki da ganinsu, Mum tayiwa Inna albishiri akan ta biya mata saudiya wannan shine karo na uku da Inna zata je Saudiya, Inna tayi farin ciki sosai

 

Mum ta tambayi Dije don tunda tazo bata ganta ba

 

Inna ta ce da ita karan kanta bata san inda Dije tayi ba

 

Mustapha gajiya yayi da zama ya ce bari yaje ya zagaya gari ya dawo, ya fita ya je wurin motar da suka zo dashi, ya bude ya shiga, babu wanda zai ganshi don motan na dauke da bakin gilashine, ko kadan ba’a ganin wanda yake ciki, sai dai na ciki ya gano na waje

 

Ya ja motar ya tafi

 

 

Dije gara tayarta take yi cikin nishadi can ta hango wani makaho yana tafiya yana daddogara sanda, tafiya ta fara yi a hankali tayi sanda sanda taje ta gefen makahon, wani bakin motane yazo wucewa ya tsaya sanadiyar ganin Dije

 

Dije sawa makahon kafa tayi ya fadi kasa sosai, saita fashe da dariya don sosai abin yayi mata sugar, Tsohon ya tashi da sauri fadi yake “wani dan banzan ne” Dije tayi sauri ta dauke sandarsa

 

Mustapha ne ya fito daga motarsa cikin fushi, Dije na ganinshi ta rikice

 

“Yau na shiga uku”

 

Ya watsa mata mugun kallo “baki shiga ba, za dai ki shiga”

 

Juyawa tayi zata gudu ya dakatar da ita, “Wallahi idan kika kuskura kika kara wani taku daya saina lahira ya fiki kwanciyar hankali

 

Dije ta mikawa makahon sandarsa

 

“Baba kayi hakuri kuskure ne”

 

makahon amsar sandansa yayi ya ce Allah ya shiryeki sannan yayi wucewarsa

 

“Don Allah Yaya kayi hakuri ba zan kara ba”

 

“Idan kika kara bani hakuri saina saba miki”

 

Karasawa yayi wajen motarsa ya bude booth

 

“Oya zoki shiga”

 

Zaro idanu tayi

 

“Yaya ni akuya ce? ”

 

“Ai akuyama ya fiki daraja, da shine a seat zan saka shi”

 

“Don Allah kayi hakuri”

 

“Na ce zan saba miki idan kika kara bani hakuri, kawai kizo ki shiga”

 

Cikin tsoro tazo wurin motan, turo baki tayi sannan ta shiga, rufeta yayi sannan yaje ya shiga motar ya ja ya tafi, bai tsaya ko’ina ba sai kofar gidansu Dije, ya fito daga mota yazo ya budeta, tana shirin guduwa ya damko ta

 

“Ina wasa dake zaki gudu? ”

 

“Kayi min rai Yaya”

 

“Ke wallahi saina hukuntaki, ba dukanki zanyi ba, tsallan kwado kawai zaki yi”

 

“Tsallan kwado kuma, ni kwado ce da zanyi tsallan kwado”

 

“To yau kin zama kwado sai ki fara irin tsallan da kwado yake yi”

 

Turo baki tayi alamun ba za tayi ba, zare belt dinsa Mustapha yayi, tana ganin haka ta tsorata ta fara tsalle kamar kwado

 

Mai awarar fulawa tazo wucewa ta tsaya tana kallan Dije tana mata dariya, Dije haushi ya cikata ta kunduma mata zagi

 

“Sai na ci ubanki, shegiya kawai, bari na kamaki”

 

“Au a gabana kike zagi”

 

“To ai ba kai na zaga ba”

 

“Laifinki ya karu”

 

“To kai baka ga dariya take min ba”

 

“Ni ina ruwana, ai kina cikin punishment ne, laifinki ya karu”

 

Dije ta fashe da kuka, tana tsalle tana kuka

 

Ranar Dije taji jiki sai da Mum ta kwace ta a hannun Mustapha, har gashin kafa sai da tayi mata, Inna kuwa dadi taji, don karan kanta Inna tasha fada da ana canza yaro da tuni ta canza Dije

 

Haka Dije ta kasance cikin takura har Saida Mum da Mustapha suka bar garin sannan suka samu sa’ida

 

 

Bayan Hamrah ta gama karatunta a fannin Likitanci aka saka ranar auransu da Mustapha, sunyi farin ciki sosai don ba su da wani buri daya wuce su kasance da junansu, bikinsu ya rage saura sati biyu Mustapha ya samu wannan hatsarin, dalilin dakatar da bikin kenan aka shiga yin jinya

 

“Su Dad sun dawo gida Nigeria suna cigaba da jinyar Mustapha, Mustapha shiga dakinsa yayi ya tsaya yana kallan dakin, ji yayi an rungumoshi ta baya, a razane ya juyo gami da sa karamin ihu, Hamrah ya gani tana masa murmushi, shagwabe fuska yayi

 

“Ke kina bani tsoro ko”

 

Yatsine fuska tayi “yaya kaifa ba yaro bane, you have to know”

 

Rungumarsa tayi tana kokarin kissing dinshi yasa karfinsa ya ture ta gefe

 

“Saina fadawa Grandma kina min iskanci”

 

“Bata rai tayi wannan wane irin sakarci ne, gaskiya ba zan iya ba”

 

Dogon tsaki taja ta fita daga dakin, dakinta ta wuce ta zauna bakin gado tana tunani a zuciyarta

 

“Har yaushe Mustapha zai warke, da ganin alamu ba zai taba warkewa ba, gaskiya ni ba zan iya ba, dole nasan abin yi”

 

Mustapha ya fito falo ya zauna kusa da Grandma

 

“Ban ga kayan wasa na ba, kuma Banga kwallona ba”

 

Grandma tai masa murmushi “Bari na aika a sayo maka kayan wasa iri iri”

 

“Grandma harda kayan kwallo za’a saya min”

 

“Karka damu duk za’a saya maka”

 

“Jibi zan tafi Hadeja bikin Aisha” Mum ta fada tana kallan Dad

 

“Bikin har yazo ne? ”

 

“Eh”

 

“To Allah ya kaimu”

 

“Amin”

 

“Ya maganar auran Mustapha da Hamrah?” Grandma ta tambaya

 

Dad ya ce za’a daura sati na sama

 

Hamrah data shugo falon yanzu ta tsaya cak, gabanta na fadi, Grandma ta kalleta

 

“Hamrah lafiya”

 

A shagwabe Hamrah ta karaso “Ni Dad kada ayi auran nan”

 

Kowa ya zaro ido yana kallanta Dad ya tambayeta dalili, ta ce masa tafi son sai Mustapha ya samu lafiya, Dad baya son takura mata, ya ce to shikenan amma Mum bata ji dadi a zuciyarta ba, haka suka cigaba da tattaunawa

 

 

Taku har kullum Maryam M. Hasheem (M. Jaruma ce)

 

Complete document naira dari uku ne N300, ki tura zuwa wannan account din 0440617768, Maryam Mohammed. GT bank, sai ki tura shaidar biya ta wannan layin 09049493054, idan kuma Katin waya ne, sai ki tura Katin Airtel ta wannan layin 09049493054, Nagode.

About the author

Hausa_Novels

Leave a Comment