Littafan Hausa Novels

Daulatul Arab Hausa Novel Complete

Written by Hausa_Novels

Daulatul Arab Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

DAULATUL ARAB

 

 

 

MANAZARTA WRITES ASSOCIATION

 

 

 

STORY AND WRITING

ZAINAB AHMED YUSUF HAƊAJA

MRS

Abdussalam

 

 

WhatsApp number

+218917586263

 

 

 

WANNAN BOOK TUNDAGA FARKONSA HAR,KARSHEN SA SADAUKARWA NE AGAREKU

MASOYANA

 

 

PAGE 1️⃣➡️2️⃣

 

Bismillah

 

 

 

Danno hancin motarshi yayi kan titi gudu yake ba kakkautawa hakan yasa duk wani mai motar daya hangeshi kokari yake yabashi hanya ya wuce

 

 

” FERAS yakamata ka rage gudun motarnan haka kasanfa layin babban masallaci zamubi kuma gashi kaware kiɗa bayan sallar azahar ake yanzu

Sanin Gaibu Hausa Novel Complete

 

Wanda aka kira da suna FERAS ne naga ya kunna sigari ya kalli abokin nasa yace

 

” to shek yasir mai zai hana na saukeka a masallacin ayi sallar dakai

 

” gaskiya FERAS bakada dama ina ni ina yin sallah koka manta jiya nasha giya kaga kuwa nida sallah sai nan da kwana Arba,in

 

 

Wani murmushi FERAS yasaki yace “tunda kuwa kasan sallah ta haramta agaremu muda muke shan giya karka kara yimin korafi akan tukina, ” ok shikkenan naji yanzu dai muyi sauri mukarasa inda zamu kafin lokaci ya kure mana

 

 

Nan suka cigaba da tsula gudu abinsu suna busa sigari ga tashin kiɗa duk inda suka gifta sai kaji kanka kamar ya tsage saboda karar kidan

 

 

Feras ne ya hangi wata jar mota a gaban sa kowa yana matsa masa ya huce amma motar taki matsawa hakan yasa feras cikin fishi da hassala ya karawa motarsa gudu ya daki wannan jar motar

 

 

Gaba ɗaya robar bayan jar motar yacire hakan yasa mai jar motar fitowa cikin bacin rai danganin wanda ya masa wannan ɗanyen aikin

 

Shima feras futowa yayi yanufo mai jar motar yana zuwa yaga wani dattijo ne yake jan motar

 

cukume shi feras yayi kan kace kwabo ji kake tass feras ya ɗauke dattijon nan da mari hakanne yajawo hankalin jama,ar gurin kansu

 

Cikin ruwan masifa da bala,i feras yake magana

 

” uban wanene ya ɗaure maka gindi a kasarnan da har zaka gogarmin motata to wallahi sai ka karbi mukullin kaje ka sauyomin wata inba hakaba ka kare rayuwar ka agidan kaso

 

Dattijon nan yanajin haka ya fashe da kuka ya tsugunna yadafa kafafun feras yace

 

” dan Allah yallabai kaimin rai kataimake ni taya mai motar milion 20 zai iya biyan mai motar milion 100 na zubda girmana yallabai na dafa kafafun ka kataimaka min kayafemin

 

 

Duk da gurin ya ciki da mutane ƴan kallo amma babu wanda ya iya magana acikinsu bare susa baki feras ya yi hakuri saboda kaf titin babu wanda baisan feras ba dakuma goyan bayan da yake dashi uwa uba ga ɗinbin dukiya kamar baza a mutuba

 

Cikin isa da izza haɗi da alfahari da girman kai feras yaɗago yana watsawa mutanan gurin wani wula kantaccen kallo yace

 

” kai dattijo babu wata mota data isa ta gogi tawa kuma tacigaba da moruwa dan haka indai kanaso na yafe maka saikun haɗu kaida waɗan nan mutsiyatan karnukan kun ragargaje motar ka

 

 

Gaba ɗaya wajan babu wanda bai girgizaba amma kowa yasan wannan shine zabi mafi sauki dan idan ba hakaba ta tsoho tagama karewa shima tsohon a karan kansa ya yarda daya salwantar da motar tasa indai feras zai kyaleshi

 

Juyawa dattijon yayi ya kalli jama,ar dake gurin yana zubar da hawayen bakin ciki yace “ya ku ƴan uwana kuzo ku taimaka min wajan ciki sharaɗin yallabai

 

 

Duk gurin babu wanda bai tausayawa dattijon nan ba amma shikwa feras ko a jikinshi haka ya zauna saman motar sa ya kunna taba yana sha har suka gama filla filla da wannan motar tukunna yaja motarsa suka tafi

 

 

( WANNAN KENAN )

 

 

 

” Baba baba ka dakata nace maka

 

Cikin sanyin jiki mutumin ya juyo ya kalleta zuciyarsa cike da tsoran ƴar tasa yace ” naam FAHDA,

 

Tana karasowa ta cukumi kwalar baban nata tace

 

” wallahi kai mugune azzalumi shekarata 30 duk nazama uwar mata babu aure duk lokajin da miji ya fitomin sai kace ba yanzu zaka aurar dani ba to yanzu ankai ga ko samarin dazasuce sunasona ma babu duk sun gudu saboda gani suke natsufa bazasu iya aurena ba shiyasa yanzu nazo koka ne meni dakanka kabiyamin bukatata kokuma kafita kanemo duk wanda zai sadu dani ayau ɗinan

 

 

Gaba ɗaya baban nata yarikice jiki na rawa yake cewa ” innalillahi wa inna,ilaihir raju,un duniya ina zaki damu wai yanzu fahda ina matsayin mahaifinki kice na nemeki na shiga uku ni jabir yau naga ta kaina….

 

” dakata dallah malam niba wani surutu nace kamin ba zabi nabaka kuma yazama dole ka aiwatar da ɗaya daga ciki

 

” fahda kisaurareni kiji ni ima matsayin mahaifinki bazan iya aikata fasukanci dake ba amma zanje na nemomiki wanda ya dace

 

 

Cikin damuwa baban nata yayi wannan maganar sannan yaja motarsa yafice,

 

Wani masana yanufa dan nemowa ƴarsa mai biya mata bukata yayi sa,a duk ga bakaken mutanenan birjik sunata aiyukansu parking ɗin motar sa yayi sannan yakarasa da sallama abakinsa

 

Gabaɗaya ƴan,samarin suka amsa masa bayan sun gaisa suke tambayarsa wane aiki yakeso amasa

 

Ɗan jim kaɗan tsohonnan yayi yakare musu kallo cen ya hangi wani matashin saurayi baki mai yalwa taccen kirji kana ganinsa kasan lafiyayyene sannan yace wa saurayin yazo

 

Cikin harshen larabci tsohon yace ” yaro inaso muje dakai gidana akwai wani kaya da zaka kwashemin ni nakasa kwashewa kasan jikin tsufa

 

 

Murmushi saurayin yayi sannan yace ” babu matsala baba muje na kwashe maka , yauwa nagode yaro

 

 

 

Fahda tana kwance akan gadonta taji shigowar motar mahaifinta cikin sauri da zumuɗi tasoma leke ta windo, gani tai yazo dawani bakin saurayi kai kana ganinsa kasan maji karfine wani uban tsalle ta daka cikin murna tafara cire kayan dake jikinta

 

 

 

A bangaran baban nata kuwa suna sauka daga motar yace wa saurayin ” yauwa sadik nan ne gidan nawa kashiga ciki zakaga kayan a parlor nibari na fara gyara maka inda zaka zuba kayan

 

 

To sadik yabi tsohon nan dashi yashiga cikin makeken parlorn gidan,

 

Yana shiga yaji wani daddaɗan kamshin turare yadaki hancinsa wata ajiyar zuciya yasaki saka makon wani sanyi mukaiyub dayaji yana ratsashi karab yaji anja ƙofar tawaje ana samata mukulli

 

Juyawa yayi yana cewa ” baba lafiya naga kana kulleni kabuɗe ƙofar mai namaka ko kuwa saceni zakai

 

Sadik yana cikin wannan maganar yaji sautin takalmi ana saukowa daga bene ji kake kwas kwas kwas, juyawa yayi dan ganin mai saukowa ga mamakinsa wata matashiyar balarabiya yagani kyakkyawa

 

Da sauri yasa tafin hannuwan sa ya runtsa idanunsa dan ganinta yayi tsirara haihuwar uwarta babu komai ajikinta sai wani shegen takalmi mai tsini

 

 

Da murmushi a fuska kar fahda ta karaso kusa da sadik ta dafashi cikin siririyar muryarta mai ɗaukar hankali tace

 

” marhabtin marhabtin ya helwa (barka da zuwa ya kyakkyawa)

 

 

 

Dare ya tsala tundaga farkon layin har karshensa babu kowa sai sukaɗai da uban gaiyarsu gabaɗaya layin ya turnuke da warin kayen shaye shaye kala kala

 

Makota sunkasa bacci saka makon karar kidan da yake tashi a unguwar wanda inda sabo sun saba duk ranar Al,hamis haka FERAS yake gayyato abokansa suzo suyi parking ɗin motocinsu suciki layin masu shaye shaye sunayi masu shangiya sunayi

 

 

Daga gidansu FERAS kuwa kaninsa shek,ali yakasa bacci saboda sababin yayan nasa na duk ranar Al,hamis hakan yasashi ɗaukar Al,qurAni yafara karantawa

 

Karatun ma kinyuwa yayi gaba ɗaya karar kiɗan da shewarsu FERAS ta hanashi jin kunne hakan yasashi tashi ya nufi waje dan yiwa yayan nasa magana

 

A babban parlorn gidan ya tadda Ammen su da sauran kannansa suna kallo

 

” aa shek, ina zaka fita haka a darannan ?

 

” Ammee inaso zanje nayiwa FERAS magana yarage kiɗannan wallahi na kasa bacci kuma ko karatun ma yaki yuwuwa

 

” lallai shek,Ali kanaso kajawowa kanka sababin FERAS muma nan dakake gani kasa baccin mukai shiyasa muka kunna kallo kuma kojin abinda ake cewama bamayi kawai muna kallon fuskar talbiziyon ne

 

” Ammee ai bada rigima zanje masaba kawai inaso na lallaba shi ya rage karar kiɗan

 

 

To shikkenan Ammee tabi shek,Ali dashi yakama hanya yafice yana jin kirjinshi na dukan uku uku

 

 

Tunkan yakarasa wajansu yafara sallama duk da yasan bazasu amsa masa ba harsaida yakai wajan oga kwata kwata kafin shek,ali yayi magana FERAS yace

 

” aa barka dazuwa ustaz shek,ali ya kokaima kazo ayi shagalin da kaine ?

 

” lahla ya ɗan,uwana dama nazone na faɗa maka dan Allah idan da hali kataimaka mana kaɗan rage karar kiɗannan kasan yanzu dare ya tsala karfe uku kuma inada yakini a unguwarnan bama manya ba ko jinjiri bazai iya yin bacci ba koga hayaniyar ku kadai barekuma kidan

 

 

Lokaci ɗaya fuskar FERAS ta cenza izuwa kalar hassala yaɗaga ruwan giyar dayake hannunsa ya tuttulawa shek,ali akansa nan da nan abokan FERAS suka fara shewa suna tafawa feras

 

” wato kai shek,ali har iskancin naka yakai kazo kace zaka faɗamin abinda ya kamata ni sa,ankane yaushe aka haifeka wato saboda kazama limamin babban masallaci shine kake kallon kowa daidai dashi kake ko ?

 

 

 

 

 

Wannan sabon book ne Akwai darusa dayawa acikinsa idan naga ruwan comment ɗinku zamu iya cigaba da gashi

 

ZAINAB AHMED YUSUF HAƊAJA

About the author

Hausa_Novels

Leave a Comment