Littafan Hausa Novels

Darasi Hausa Novel Complete

Written by Hausa_Novels

Darasi Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

DARASI

 

 

BOOK 1

 

Rabiatu Bashir

Ummu maher(miss green)

 

 

 

 

*@Wattpad link*

 

.

 

 

 

*@Arewa book link*

 

.

 

 

 

Tsokaci:ban yadda wani ko wata yayi amfani da wannan littafin ba wajen canza wani abu ba,wannan littafin mallaki na ne a kiyaye doka ce.

 

 

 

 

 

Bismillahir-Rahmanir_Rahim.

 

 

*_My parents_*

 

01

 

 

…….”Wai ni indo me kika dauki kanki ne da ban isa in gaya miki magana kiji ba,kullum sai kin dorawa wannan yarinyar tallah saboda me zaki ringa kokarin keta duk wata doka da zan saka agidannan?”.

 

 

“Mlm bafa ka isa ka hanani dorawa wannan yarinyar tallah ba tunda ba kaine kake daukar dawainiyar ta ba,matukar kanason in daina dora mata to kadinga kula da komai nata ciki harda ciyar damu dukkanmu”,tana kaiwa nan tayi tafiyarta tana yan kunkuni da karfi.

 

 

Shiru Mlm yayi ya goge wata kwalla da ta zubo masa a Idanunsa.

 

Talla ne akan Fahima itama tana goge hawayen daya cika mata kurmin idanunta sannan ta shigo gidan,ta karaso inda mahaifinta yake ta ce”Baba don Allah kayi hakuri ka daina biyewa Amma saboda ranka zai dinga baci ni kuma banason abinda zai bata maka rai don Allah kayi hakuri”.

 

 

shafa kan kyakkyawar yarinyar yayi sannan yace”Fahima Allah yayi miki albarka kinji,kema Allah yabaki masu yi miki biyayya kinji”.

 

Cikin tausayin mahaifina na ce”Amin Baba”.

 

Ina tafe ina waiwayen mahaifina da ya kasa fita har yanzu yana nan wajen dana barshi,haushin mahaifiyata ya kara ninkuwa acikin zuciyata,da wannan tunanin na karasa shiga cikin gidan.

 

 

“Ke!”

 

Da sauri na kalli Amma wacce ta kasance mahaifiyata sannan ta ce”Saboda kinyi tsiyar taki kin zubarmin da kudi shine ko sallama ba zakiyi min ba kawai sai ki shigo gida kina neman fadamin kan tukunyar girki ki jazamin siyan maganin da ban shirya ba”.

 

Fareedah Nabeel Hausa Novel Complete

Kallon mahaifiyata nayi wadda na mayar kamar tv tun shigowa cikin gidan,wato ita babu ruwanta da konewa ta ita kudinta ne ya dameta,Amma kenan ita babu ruwanta kudinta kawai ta saka a gabanta.

 

Jiki na a sanyaye na shige cikin dan rubabban dakinmu wanda kana ganin ginin gidan kasan tsohon ginin ne,runtse idanuna nayi na kalli silin din dakin ina tunanin rayuwar da mahaifana suke yi,kwatata Amma wato mahaifiyata bata mutunta mahaifina kullum cikin fada da gaya mishi bakaken maganganu kawai don bashi da kudi,ina cikin tunanin Kannena suka shigo dakin da na ke,Khalil,sai nusaiba,da Haruna,kannena ukune kacal don Amma tun kan Harun tace ta daina haihuwa da babanmu wai ta gaji da haihuwa ba’a yi mata ragon suna,don haka yanzu shekarun Harun Biyar Amman Amma ta daina Haihuwa,hatta Harun Amma Bata ji kunyar Dora masa talla ba,duk kannena suna talla,kowa da Safiya tayi zai tafi nashi tallan.

 

 

 

Muryar Nusaiba ce naji tana cewa,Anty Fahima wannan mutumin nan da kika hanani zuwa wajenshi,shine yau ya kirawoni wai inzo zai Bani alewa shine ni kuma na gudu.

 

Kallon yarinyar na Shiga yi hawayen tausayin yarinyar suka Shiga zarya a idanuna,”Anty kuka kike don Allah ki daina kuka idan kina kuka Nima zanyi”.

 

 

“Ba kuka na ke ba y’ar kanwata,ki gayawa Amma wannan maganar kinji,don ba’asan zuciyarshi ba “.

 

 

“Wallahi Anty Amma ba zata yarda ba dukana za tayi rannan ba na Gaya mata ba,shine tace wai k’arya nake kuma wai Kada na sake in gayawa kowa,idan ba haka ba zata zaneni”.

 

 

“Amma n ce tace Miki haka”?.

 

“Eh wallahi Anty haka tace wai ko ke da Baba Kada na Gaya muku idan ba haka ba zata k’unani in mutu”.

 

 

Rungume Yarinyar nayi ina sheshshekar kukan tausayin Nusaiba Yarinyar da Bata fi shekara8 ba Amman har wani Dan iskan ya Fara hakar rayuwarta,gaskiya ya Zama dole asan abin yi,don tasan halin Amma ko don cinikin da Nusaiba ta ke mata zata iya barin Yarinyar har aje a lalata mata rayuwa a banza.

 

 

 

Da daddare muna zaune muna cin tuwon Dare Amma kuma taje barkar haihuwar kawarta,na kalli Mahaifina da yake ta cin tuwonsa cikin farin ciki,na ce”Baba inason zamuyi magana ne”?.

 

 

“Ina Jin ki Fahima”.

 

 

“Baba daman Akan Nusaiba ne,wai kullum ta dauki talla sai wani ya kirawota shagonsa wai zai Bata alewa,da ta fadamin sai nace mata ta dinga guduwa,shine yau ma mutumin ya Kara tare ta”,na Fadi hakan ina sheshshekar kuka,don a rayuwata ina matukar son kannena musamman Nusaiba.

 

 

Shiru Baba ya yi min baice komai ba ya sha ruwan Dana debo masa ya wanke hannunsa ya saka ta kalminsa ya fita.

 

Wata kwalla ce ta sauka akan fuskata,to me hakan yake nufi?shima Baba ya Fara bin goyon bayan Amma ne ko me?ai Naga koda na fada masa ya nuna damuwarsa tunda yarsa ce Amman me yasa baiyi wani Abu ba?,duk ni kadai nake wannan surutun daga bisa ni,kuma na koma cikin dakinmu zuciyata babu dadi.

 

 

Cikin dare na jiyo hayaniyar Iyayenmu,Baba na yana cewa Amma”Wallahi duk ranar da kika Kara dorawa Nusaiba talla to a bakin aurenki,shasha wacce Bata San inda yake mata zafi ba,kowa yana tattalin nashi yayan Amman ke Banda ke,saboda wani dalili mara tushe da kike tutiya dashi,iya abinda naji Kenan daga nan Mahaifina Bai Kara magana ba sai Amma ce naji ta bude kofar gida ta fita a cikin wannan Daren, Mahaifina ya biyo ta yana Kiran sunanta.

 

 

 

Wani kuka ne ya kufcemin a shekaruna wadanda Basu Gaza 14, ba Amman babu abinda bana ganewa a game da Zaman Iyaye na.

 

 

Da k’er Baba na ya shawo Kan Amma ta dawo tana ta sababin fadanta,wai wallahi ita ba zata Kara dorawa Nusaiba talla ba Amman fa ya dinga Nemo abinci a gida.

 

 

“Eh naji Insha Allah Zan dinga nemowa da dai a lalatamin rayuwar Y’aya na”.

 

To daga haka kuma ban karajin bakinsu ba,Baba ya rufe kofar ya shigo ya kwanta.

 

Sai da na Dade banyi bacci ba daga Baya baccin ya daukeni,ina tuna caftar Baba da Amma don Baba na a rayuwarshi ya tsani b’acin ran Amma yanzu zakiji sunyi fada an jima zasu shirya.

 

 

 

 

****************

 

Wani kyakkyawan gida na hango me kyau da kuma tsari,colour din Gidan fari ne k’al,tun daga bakin kofar Gidan sojoji ne fal tsaye da bindigunsu sun sai ta gabas dasu,a cikin gidan kuwa wasu flowers ne masu kyau koraye da kuma pink sun haska gefe2 Gidan tsakiyar kuwa yaji wani rantsatstsan interlock me matukar kyau,gida babban gida Wanda idan Ka shige Shi ma sai kayi 2hour ba kaje wani wajen ba.

 

 

Wow Kada dai na Gama cikaku da surutu kyaun wannan Gidan sai Wanda ya gani,don Gidan Yadda kukasan white House na America.

 

Wata mata na hango zaune a wata farar kujera wacce ta gaji da haduwa a garden din Gidan matar ba zata wuce 35 ba,tana waya da wata tana cewa”Falmata wallahi abinnan yana damun kwakwalwata, Haihuwa na ke son Samu ko ta halin kaka,wajen da kika rakani rannan nake son ki sake rakani,zanzo Maiduguri gobe ki rakani,don Yallabai Baya nan sai nan da kwana 3 zai dawo.

 

Daga cen b’an garen Falmata tace”oky ranki ya dad’e ina jiran zuwanki,yawwa ni kuwa kin Samu kinje Yola din kuwa wajen Maman Yallabai Ammar?”.

 

 

“Banje ba kuma bazan je,don wallahi na rantse Miki da Allah abinda matarnan tayi min Nima saina Rama,don tana tutiya d’anta ne ni kuma ina tutiya da mijina ne”.

 

“Hhh mutuniya ta Kenan shiyyasa na ke son ki,kiji dadinki matar Yallabai,Insha Allah sai kin haifi magajin Gidan Yallabai Ammar”.

 

Wata dariya Sakinat tayi sannan ta ce”ai ni wando Ce dai dai nake da k’ugun kowa”itama dariya Falmata tayi sannan tace”to ina jiran zuwanki don akwai Wanda mukayi alkawarin fita dashi.

 

Suna Gama wayar ta shigo cikin sashenta Wanda fadin iya haduwarsa ma b’ata Baki ne,har zata Shiga dakinta sai kuma ta dawo sannan ta nufi wajen wani kyakkyawan hoton wani matashi Wanda ya saka kakinsa na soja,yayi bala’in kyau sai Ka kasa gane Balarabe ne ko kuwa wani half-caste ne,don yana da wani irin sirrin kyau na ban mamaki.

 

 

Shafa hoton Sakinat tayi sannan tace”ilove u mijina inason Ka da yawa”.

 

Ganganci ne mace ta rabe Ka,na sani ko ban sani ba ciki kuwa harda wacce ta kawoka duniya,don ni kadai a kayi Ka General Ammar Muhammad Lamido ina matukar so da kaunarka,dafatan Ka wayi gari lfy tana fadin hakan tayiwa hoton kiss ta shige daki abinta,tana kulla Yadda za tayi don itama taga ta ajje kwanta a acikin wannan babbar gonar.

 

 

 

 

 

 

Ammar yana zaune cikin k’aya taccen office dinsa Wanda ya gaji da haduwa,kyakkyawan matashi ne wanda ya gaji da haduwa cikin kayansa na kaki,ya d’aga kansa yana wani tunani,Anya kuwa yana yiwa kansa da mahaifiyarsa adalci kuwa,rabonsa daya saka k’afafunsa a Yola yau shekara 5 Kenan fa,yaso ace kafin wannan tafiyar da ta kamasa zuwa kasar Tunesia yaso yaje,Amman ya dauki alkawari Insha Allah idan ya dawo zai je,ya share wata kwalla da ta cika mishi idonsa,yana cikin tunanin yaji k’arar wayarsa Wanda yasan ba kowa bane illa matarsa Sakinat don ita kadai ce ta ke da numbersa.

 

“Ranka ya dad’e dafatan kana lfy,Allah ya Kara maka lfy,Allah ya Kara mana dank’on soyayya Amin,shima amsawar yayi da Amin.

 

 

nan dai suka Bata lokaci suna soyewarsa da sahibarsa Sakinat.

 

 

 

*UMMU MAHER ce*

DARASI

 

 

BOOK 1

 

Rabiatu Bashir

Ummu maher(miss green)

 

 

*@Wattpad link*

 

.

 

 

*@Arewa book link*

 

.

 

 

*SIRRINKI*

Ki zami mai yi wa mijinki biyayya yin hakan zaisa ki rabauta duniya da lahira

 

 

 

02

 

……yana Gama waya da Matarsa Sakinat ya d’aga wayarsa ya Kara a kunnensa cikin nutsuwa shiru sukayi gaba kidayansu sanin halin Ammar,Amir ya ce”Kai fa haka kake Ammar Amman sai Ka bugowa mutum waya Ka yi shiru”?.

 

 

Shirun Ammar ya k’ara yiwa Amininsa Amir Wanda yanzu ya ke a America da Matarsa da yayansa 4,Gajiya Amir yayi sannan ya ce”Ammar lafiya me ya faru?cikin damuwa Amir yake fadar hakan don yana matukar Jin tausayin abokinsa Ammar don ya hadu da shu’umar mata,baiyi tsammani ba yaji Ammar ya ce”so na ke Ka turomin da number Umma”!.

 

Mamaki da wasu hawaye ne suka Fara zubowa a fuskar Amir, bakinsa yana kakkarwa ya ce”yanzu Ammar number mahaifiyarka karasa acikin wayarka? abin ya daure min Kai”.

 

“Don Allah Amir Ka tausayamin Ka turomin number Umma,na kasance cikin bakin ciki, kwakwalwata tana gab da tarwatsewa kunnuwa na suna yimin kuwwar muryar Umma na,ina San inji Muryar Umma na”,sai wasu hawaye masu zafi suka zubo masa.

 

 

Kashe wayar Amir ya yi hawaye yana fitowa a idanuwansa ya saka handcachiep dinsa ya goge hawayen da ya zubo masa,ya Danna message ya Nemo number Umma yana kuka ya turawa Ammar number.

 

 

Tunda Amir ya kashe wayar Ammar ya tashi tsaye a office dinsa ya buga tebur idanuwansa sukayi jawur sosai kamar garwashi,allurar Soja ta tashi,gashin jikinsa ya Fara mimmik’ewa,ya Rasa abinda yasa duk wata mace in dai ba Sakinat ba,Baya taba ganinta da gashi ciki kuwa harda Mahaifiyarsa wato Umma,wacce take matukar sonshi da k’aunarsa itace ta dauki nauyin karatunsa tun kafin ya Zama wani Abu ta shige mishi a gaba ya zamo abinda ya Zama tun bayan rasuwar Mahaifinsa,yana cikin wannan tunanin Yaji k’arar shigowar sako,da sauri ya dauka yana sharce wata uwar zufar da ta zubo masa,hannunsa yana kakkarwa ya dauka ya duba number Umma ya kirawo Hannunsa sai k’erma ya ke.

 

 

 

Wayar tana hannun Khalisat wato kanwar Ammar,tana Assignment an Kira yafi sau 3 taki dagawa sai tsaki take tana cewa”gaskiya ko waye wannan ya iya nacin jaraba”,ta Fadi hakan cikin yaran Fillo wato fulatanci,sai da wayar ta kusa tsinkewa sannan ta d’aga cikin dakusasshiyar murya tace”waye”?.

 

 

“Common ki kawai wa Umma stupid!”.

 

 

Da sauri jikinta ya Fara kakkarwa don tabbas ta gane muryar yayanta,hawaye suka Fara zubo mata da sauri ta haye step,tana kwalawa Umma Kira wacce alokacin ta ke sallar duha,wato sallar walaha, Khalisat cikin kuka ta ce Umma ya Yaya Ammar a waya”!.

 

 

Lokaci daya Umma taji kanta ya Shiga sarawa sosai,zuciyarta taji tana bugawa ta saka hannunta ta danne saitin zuciyarta daya tsananta buga mata.

 

Khalisat tasan za’ayi haka Amman sai ta goge hawayenta ta ce”Umma ki daga wayar nan kiji me zaice Miki,ki ajje fushinki a gefe ki janyo danki a jikinki don Allah”.

 

Hannun Umma yana k’erma ta saka hannunta ta amshi wayar,sai dai ta kasa saka wayar a kunnenta.

 

Yaron da ta keso ta ke k’aunarsa Amman yau an wayi gari ya wofantar da ita,ya guje ta tamkar wata mujiya,idan Bata manta ba yau tsahon shekara 5 rabon da ta saka Ammar a idaniyarta balle har ya bugo mata waya.

 

 

Duk abinda a keyi Ammar yana Ji,kuma yana jiyo kukan Amminsa,hankalinsa ya tashi jijiyoyin kansa suka tashi sosai ya dafe kansa yana kuka.

 

 

Da sauri Khalisat ta saka wayar a handsfree don Umma taji muryar d’anta sosai,ai kuwa tana saka muryar taji Ammar yana cewa.

 

“Ammina”!

 

Sai kuka yaci k’arfin Ammar wani amai ya taho masa,ya ajje wayar ya ringa kwarara amai kamar me yaron ciki,ta cen bangaren Umma tana Jin Ammar ya Fara amai,hankalinta ya tashi ta Fara Kiran sunansa tana cewa”Ammar don Allah Kada Ka saka kanka cikin wani Hali Nima Ka sakani,don Allah kayi magana inji Muryar Ka”.

 

Itama anan kukan yaci k’arfinta ta yarda wayar tana matsanancin Kuka,Khalisat ma hawayen ta ke tana sharewa Umma hawayen sannan tana bubbuga bayan Umman kamar k’aramar yarinya.

 

 

 

 

 

Kiran wayar Ammar Khalisat ta ringa yi Amman Bai daga ba,k’arshe ma taji an kashe wayar,hankalinta ya tashi ta Rasa Yadda zatayi gashi,ga Umma ciwon zuciyarta ya tashi da k’er ta Samu ta balli maganinta ta Bata ta Samu bacci,gashi kuma Yaya Ammar shima yana cikin wani Hali.

 

 

Kifa kanta tayi tana kuka me tsuma zuciya,tana kuka tana cewa”Anty Sakinat Baki kyauta mana ba kin rabamu da sanyin idaniyarmu,kin raba D’a da uwa,kin raba soyayya me k’arfi,Why me yasa kika yi mana haka?Meye ribarki?”.

 

Nan dai Khalisat ta ringa surutai marasa Kan gado,daga Baya ta tashi ta yi alwala ta Fara sallar Nafila tana kuka tana rokon Allah subhanahu wata’ala ya kawo musu sauki da haske cikin wannan lamarin.

 

 

 

 

 

 

************

“Wallahi Fahima Kada ki sake ki dauki tallannan ki zubarmin da kudi,kika yarda kika zubarmin da kudina ranar saina ci ubanki a Gidanan”.

 

 

“Na gode”

 

Na ji muryar Baba ya fito daga ban d’aki ya cigaba da cewa”Fahima Kada ki Dade kina zuwa idan kiga babu ciniki ki dawo”.

 

Cikin sassanyar Murya ta na ce”Insha Allah Baba bazan dad’e ba”.

 

Na dauki tallan na tafi ina tunanin Hali irin na Amma,ita dai zata Samu kud’i babu ruwanta da matsala,ko da hakan yana barazanar lalacewar rayuwar y’ayanta.

 

 

Yauma banyi wani cinkin kirki ba na taho gida saboda ƴan garuwar da muke siyarwa duk sun tafi gida don haka yanzu babu ciniki,gaba yana dukan 3 na taho gida don nasan yau Amma Bala’in ta akan babanmu zai ƙare.

 

Tun daga soro na kejin hayaniyar atika mai kayan gonjo da amma ana ta hira ana shewa,sam ban son matar Ƙwata2 saboda Atika duk wani rashin mutunci itace ta ke koyawa amma shi,ko kallon Atika banyi ba nayi hanyar ɗakinmu tare da yiwa Amma sannu da gida,ko amsamin bata yiba sai kallon kayan tallan kaina ta ke tana hararata,jikina ya hau rawa don idan nayi sa’a ne ma zai tsaya a zagi don nasan har duka sai ta yi.

 

 

“Ke zo nan don ƙaniyarki”.

da sauri naje har ina haɗa hanya don tsoron Amma na ke ji kamar mala’ikan mutuwa.

 

“Yanzu ita Atikan itace abin wulaƙantawa a wajenki?idan Adama ƙanwar ubanki ce zakiyi mata haka?tsugunna ki gaisheta kafin inci ubanki la’ada waje don bazan zuba miki ido kina rashin mutuncin da kika dama ba.

 

“Hmm Amma dama kin ƙeleta yaran yanzu ai sai a hankali ballantana ma idan suka ga sun fara tashen balaga sai kaga abubuwa kala2”.

 

“haba Atika ba tashen balaga ba Allah yasa tashen tsuntsaye ne wallahi ni babu ruwana dukan kawo wuƙa zanyi mata, daman ga haushin ubansu ina fama dashi ayi namiji kamar mai zuciyar karya baya ajje komai sai yawon ƙasan bishiya daga wannan ta tafi ya koma wancan inuwa.”

 

 

zuciya ta ce naji tana ta tafarfasa kamar zata ƙone don naƙi jinin a zagar min uba abin yana taɓa min zuciyata sosai.

 

 

Ina cikin wannan tunanin sai kuwa naji Atika tana cewa”ni wallahi Amma dama birni kika bayar da wannan yarinyar aka kaita aiki da mun huta da ganinta tsogai2 tana yawo a gari.

 

 

Saurin ɗago kaina nayi jin maganarta wai a kaini aiki?

 

 

 

 

*ummu maher ce*

*DARASI!!

 

 

BOOK 1

 

Rabiatu Bashir

Ummu maher(miss green)

 

 

*@Wattpad link*

 

.

 

 

*@Arewa book link*

 

.

 

 

*SIRRINKI

 

Yin tsarki da ganyen magarya yana taimakawa wajen kashe Ƙwayoyin cuta musamman lokacin gama al’ada.

—————————–

03

 

.. . . . . .”Wallahi Amma ni babu wani gidan aiki da za’a kaini ina jin fa yadda ake bada labarin duk yaron da aka kaishi aiki yanke kanshi ƴan birni suke su cinye namanshi har da romanshi”.

 

“Ai wallahi ƙaryarki kuwa ki zauna min a gida muna haɗa kafaɗa da ke a cikin gidannan dolen ki tafiya birni kije ki nemo mana kuɗi wallahi,kullum mu kenan cikin talauci ke ko kunya ma bakyaji kullum kina yawo da wannan koɗaɗɗan zanin”.

 

Kuka ne ya kufcemin na fita waje zuwa gidan kaka ta wacce ta haifi mahaifiyata,ina zuwa gidan na tarar da ita a bakon murhun ƙasa zata ɗora sanwar dare,na fashe mata da kuka sosai harda majina.

 

“Ke ƴar nan lafiyarki kuwa kika shigo min gida kina sharce hanci kamar wata tatsitsiyar yarinya”?.

 

“ba Amma bace ita da Atika wai birni zasu kaini aikin wanke2 da shara,ni kuma wallahi ba zanje ba.”

 

“yanzu Amma son kuɗin nata har ya kai ta kaiki birni aiki? ni wallahi spn kuɗin yarinyar yana bani mamaki,don kawai Allah ya jarabci mahaifinki shikkenan sai ta shiga yawon neman kuɗi kamar wata wacce ta fito a turu,”maza tashi ki share hawayenki insha Allah babu wanda zai kaiki aikatau kinji”.

 

sai da daddare sannan na koma gida amman a wannan lokacin Nusaiba ta dawo daga tallan kayan miya,tsaye nayi ina kallon ikon jalla mai duka,na kirawo sunanta da Ƙarfi har sai da ta tsorata.

 

“Daga ina ki ke Nusaiba”?.

 

“Yaya daga talla na ke,ban siyar da wuri bane shine wani mutumi yanzu ya siye duka yace gobe idan na ɗakko in kawo mishi wani kango zai siye duka,kinga na huta da dukan Amma”.

 

Ƙwalla ce mai zafi ta zubo daga ƙwarmin idanuna na ce”Nusaiba daga yau ba zaki sake talla a gidannan ba wallahi”,ina faɗar hakan naja hannunta tana wai gawa ko zata ga Amma don dukkanmu tsoranta muke sosai.

 

Gidan Inna na kaita inda na baro yanzu, har ta ja ƙofarta za ta rufe sai ta ganmu ni da Nusaiba mamaki ya hanata magana amman fuskarta fal ta ke da mamakin ganinmu.

 

 

“Inna don Allah don Annabi ga Nusaiba nan ta dawo wajenki da zama,saboda zamanta wajen Amma babban hatsari ne babba”,na fashe da kuka Inna tana rarrashi na.

 

 

Nan na ƙwashe duk abinda ya faru tun daga farkon tallan Nusaiba har kawo yanzu,shiru Inna tayi tana tunanin hali irin na ƴarta wato Amaturrahman.

 

 

A yanzu hankalina ya ƙwanta sosai don riƙon Nusaiba ya koma gun Inna har ta saka ta a makarantar islamiya da ta boko,sai dai fa har yanzu aƙwai sauran Rina a kaba don yanzu Amma ta ƙara ƙaimi wajen kaini aika tau daman ga haushin na kai Nusaiba gidan Inna wai tunda ni ce na kaita dole yanzu in dinga yin tallan Nusaiba na kayan miya,da yamma kuma tallan taliya da mai da yaji,babu yadda na iya dole ne inyi abinda Amma tace don ni a yanzu daɗi na ke ji da riƙon Nusaiba ya koma gun Inna.

 

 

 

*** *** ***

 

Jirgin ƙarfe 10 ya hayo daga Tunesia zuwa Abuja,kana ganin yadda ya ke tafiya kasan bashi da cikkakiyar lafiya ajikinsa,don Ammar fari ne daman ƙal mai matsaicin jiki don haka duk wanda ya sanshi zai tabbatar da tabbas ba lafiya ya ke,motoci ne sun kai biyar suka zo tararshi a Airport ɗin suka shiga daskarewa suna sarawa ogansu wato general Ammar.

 

 

Kai tsaye ɓangarensa ya nufa sakamakon da sashen Sakinat ya ke fara zuwa amman yau sashensa ya nufa,babu wanda ya faɗawa zuwanshi Nigeria hatta da aminansa basu san da maganar dawowarsa ba.

 

Sai da daddare bayan yasha baccinsa tare da mafarkin aminsa,ya fito zuwa sashen Sakinat tsit kamar babu kowa sai masu aikinta suna ta kai kawo,da Lantana ya fara haɗuwa sabuwar mai aikin da ta yi,ta durƙusa har ƙasa tana gaisheshi cikin girmamawa ya amsa ba tare da ya kalli inda ta ke ba,sai jin muryarta yaji tana cewa”ranka ya daɗe ai Hajiyar bata nan yau kwananta 4 kenan”.

 

 

Cak yaja ya tsaya sai a lokacin ya jiyo,Lanta ta haɗiyi wani yawu ‘maƙut’ don tsabar tsoronsa da ta ke yi,ƙyaunsa da ƙwarjininsa yana ƙara ninkuwa a azuciyarta.

 

“Kika ce ta yi tafiya?”.

 

“eh yallaɓai” ta faɗi hakan cikin tsoro da fargaba.

 

Wucewarsa ya yi sama bai ƙara bi takanta ba,har ya zaro wayarsa zai kirawo ta sai kuma ya fasa ya sakko zuwa ɓangarensa yana tunanin hali irin na Sakinat,a shekara 8 ɗin da sukayi da Aure zai iya ƙirga sau nawa Sakinat ta tambayesa zuwa unguwa duk sanda ta yi niyya kawai tafiyarta ta ke yi,har zuwa wasu ƙasashen ma,a kullum tambayar kansa ya ke me yasa duk abinda Sakinat ta ke yi mai bai taɓa tsawatar mata ba duk da yana da matuƙar zuciya amma ta zama ta banza,duk izzar da ya ke da ita in dai ya shigo gida ko baya tsoron Allah to ya zama dole ya zama bawan Sakinat don mugun tsoronta ya ke.

 

Sakinat ce zaune gaban boka tsidau tana cewa”boka so na ke nima in haihu ko ta halin ƘaƘa ne don ba zan yadda wannan dukiyar da na ke gani ta tafi a tutar babu ba,ayi duk abinda za’ayi ko nawa ne zan biya matuƙar dai nima zan samu abinda na keso.”

 

wa wa keken bakinsa ya buɗe ya ce”ni boka tsidau na yi miki alƙawarin haihuwa a gidan multibuloniya Ammar,akwai abinda zamuyi miki matuƙar kika yi to tabbas za ki samu Haihuwa don haka ki saka aranki ma kin samu”. sai ya bushe da wata irin dariya mara daɗin sauraro.

 

“Tashi ki biyoni kin samu Haihuwa kin gama”.

 

dariya ce ta kama ƙawar Sakinat wato Falmata don tasan abinda bin boka tsidau ya ke nufi,ɗan jiyowa Sakinat ta yi ta kalli ƙawarta da ayar tambaya a bakinta sai dai babu ikon yin maganar don boka tsidau tuni ya yi gaba cen ƙarshen dutsen inda wata ƴar ƙaramar bukka ta ke.

 

Wa iya zubillah wannan boka aranar sai da sukayi alfasha da Sakinat kuma ya tabbatar mata cewa buƙatar ta kamar ta biya ne.

Masha Allah Ammar shirye ya ke cikin wata tsadaddiyar shaddarsa ruwan arsh ya gyara gashin kansa wanda ya ƙwanta luf luf irin na asalin fulanin usul,fatarnan sai walƙiya ta ke yasha agogonsa na rolex ya yi matuƙar ƙyau,wani irin nishaɗi ya ke ji don ayau zai ga Amminsa bayan shekara 5cif ba tare da sun haɗuba.

 

Yana shiga motar dieban yaja sauran motocin suka biyosa ya rufe idanunsa kamar mai jin bacci daman kuma aƙidarsa ce kuma haka Allah ya halicce sa baya mintina ba tare da ya yi hakan ba,hakan baƙaramin ƙara masa ƙyau ya ke ba,ga waɗanda basu sanshi ba sai suce iyayi ne.

 

 

 

 

Wata muguwar harara Sakinat ta bugawa ƙawarta Falmata ta ce”gaskiya Falmata baki da mutunci da ki ka haɗani da wannan bokan gashi yanzu ya haɗa jiki dani in banda wari da hamami babu abinda ya ke,ni wallahi Allah ya isa kawai kuma yanzu ba sai

Anjima ba Zamu je hospital a dubani”.

Dariya Falmata ta yi bata ce komai ba suka cigaba da tafiyarsu har suka kai bakin titi suka tari mota suka tafi,duk jikin Sakinat ciwo kawai ya ke.

 

Ko da aka duba ta lafiya ƙlau babu wata cuta sai anan taji wani babban abu ya wuce a maƙogoranta ta amshi ruwan sanyi ta kora,suka hau mota Falmata ta wuce gida ita kuma Sakinat ta wuce Adamawa wajen mahaaifinta.

 

 

 

Jiniya ce ta cika titin baki ɗaya ko da ba’a gaya maka ba kasan wani mai babban muƙami ne zai wuce don haka sai matsawa a ke.

 

 

Salati Sakinat ta yi ganin motocin mijinta G.A M wato general Ammar Muhammad.

 

 

 

About the author

Hausa_Novels

Leave a Comment