Littafan Hausa Novels

Dan Tijarar Siriki Hausa Novel Complete

Yadda Ake Rikita Maigida Yayin Kwanciya
Written by Hausa_Novels

Dan Tijarar Siriki Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

DAN TIJARAR SIRIKI

 

 

 

“`Salon na daban ne wannan Karon gajeran labari ne ma ciki da nishadi don ku masoyana masoyana littafina.“`

 

 

 

 

 

“`Ina ma kowa barka da sallah Allah ya amsa ibadun mu ya ya yafe mana zunuban mu ya gafarta mana ya kuma maimaita mana shekaru masu yawa masu albarka amin.“`

 

 

 

“`Wannan shafin na masoyana na ne a duk in daku ina kaunarku alkhairi Allah ya kai muku irin su HAWANCY WANNAN KANWAR KIRKI CE, UMMEE ABDUL KEMA INA KAUNARKI CIKIN RAINA, MAMAN ABDUL KEMA HAR KULLUM MUNA TARE, ZAYNAB ABU MARKA KEMA KAUNARKI BA ZATA KIRGUBA CIKIN RAINA DOMIN KINA BAN NISHADI KWARAI, TAKWARATA WATO KHADIJA KEMA INA KAUNRKI SOSAI KAI KUNA DA YAWA FA INA SONKU DUKA WALLAHI ALLAH YA HADAMU HAR A ALJANNA`

 

 

“` JIN JINA GA YAN KUNGIYATA INA MATUKAR ALFAHARI KASANCEWA CIKIN KU IRIN SU IYAR NUSY IYAR AMSAD IYAR ARIFU ALKHAIRI ALLAH YA KAIMU KU HAR GADON BARCINKU

 

 

 

“`KAWAR KIRKI INA MATUKAR SONKI A CIKIN RAINA WATO OUM SHARIFA SOYAYYARKI DABAN TAKE WAJENA“`

 

 

 

 

 

 

“`Bismillahir rahmanir rahim“`

 

 

“`Page 1“`

 

 

.Adama! Adama!! Adama!!! Kiran malam tsalha kamar za a tashi kiyama ya ke Mata, cikin sauri tare da gyara d’aurin dankwalin da ke Kan ta fito bakin ta d’auke da masifa tace”Haba malam wannan wani irin kira ne kamar na ci bashi banki ko nayi sata”? Kallon banza ya bita dashi tare da cewa”Uban wa yace ki bar mardiya tayi zancen da wannan ce shegen yaron mai kama da busasshen kifi”? Ya tambaya cike da masifa tamkar ana kun burashi,” Ubana, malam mai yakuwa yace in barta tayi zance da shi”. Ta bashi amsa itama cike da masifa.

Ban Dace Dashi Ba Hausa Novel Complete

 

Karb’e zancen yayi tare da gyara tsayuwarsa yace ” Wallahi Adama ki fita idona ba na hanaki bar min ya’ya suna zance da masu warin talauci ba? Nace ba na hana ba, saboda kunnen kashi gareki ba kiji ko?” To wallahi yau sai na lahana wannan shegen mai masifar naci kamar bakin talauci”. Yana fad’ar haka ya shiga dube duben a bun duka. Kallon sa Adama tayi tare da sakin mugun tsaki ” mtseeeeeeeewwwwww! Sannan tace” Wallahi malam ina rabaka da dukan sirikan ka wai kai abun kunya bai dameka bane?” “Bai dameni ba ,nace Adama nace bai dameni ba ,yo ni abun kunya ai gaba na bashi ba baya ba”. Ya bata amsa lokacin da ya dauki wani katon itace ya yi waje.

 

 

 

 

Adama baki takama tare da cewa” Allah ya had’aka da mai ma mugun duka ko banza kai ma ka ji yadda mutane keji, ace mutum sai TIJARAR masifa shi bai son talauci wai hmmmm talle kema audi gori “.mtseeeeeewww ta kuma jan tsaki ta shige daki.

 

 

 

Aliyu manne jikin katangar gidan su mardiya ya dage yana ta zuba uban kalaman kauna mardiya kuwa sai dariya take saboda irin shaukin da zuciyar take Mata.

 

 

 

Fakam fakam fakam Malam Tsalha ya taho wajen, ba su san da zuwan sa ba sai dai ji kake Timmmmmmm! Malam tsalha ya bugama Aliyu itace a wuya take kuwa ya baje wajen ya suma. Ihu da kururuwa Mardiya ta saki tare da ware muryar ta da karfi tace” Wayyyo Allah Baba ka kashe min Aliyu ” .Ko a jikin malam tsalha illa ma kallon ta da yayi yace ” zaki bar wajen nan ko kema sai na jirga miki itacen kin baje nan wajen shegiya mai zuciyar talauci”.

 

 

 

Wani ihun Mardiya ta kuma saki da karfi tare da cewa ” Wallahi babu inda zani sai dai nima ka kashen…………ai bata gama rufe baki ba ya yo kanta aguje tini ta cika bujen ta da iska tayi gida tana burarin ihu kamar Wanda aka aika ma uwarta ta mutu.

 

 

 

” Shegiya da kin tsaya kema da na bugeki in buge banza mai gadon talauci so kike duk mu taru mu kare a talauci ni daku to Wallahi Baku isa ba babu ko babu auren talaka, tinda ni nazo a talaka to ku dai bazaku auri talaka ba yawwa”. Shi kadai yake San batunsa yana kallon Aliyu dake kwance yashe akasa.

 

 

 

Ihun da burarin mardiya ya fito da Adama daga cikin daki da sauri har ta na buge goshi,zama mardiya tayi a kasa tana ta tumamin tare da kara bude kakkyawam bakinta tana ihu hade da share majina,kallo Adama ta bita dashi tare da kama habarta tace”Wai wannan wani irin masifa ce dan Allah?” Uba tijara ya’ya kuma shigen rigima da koke koke, ga bakin talauci duk ya ishemu da wanne mutum zai ji dan Allah”? “”Ke mardiya wai uban me aka miki kike wannan ihun kamar Tsalha ne ya mutu?” Adama ta tambaya har yanzu idon ta na kallon mardiya dake kuma share hawaye da majina.

 

 

 

Ihun ta ta cigaba batare da ta bata amsa ba, tare da kara watsa kafarta alamar birgima kamar ba budurwa ba,Uban dundu Adama ta zuba Mata tare da cewa” Wallahi idan baki min shiru ba sai na ci ubanki yau ni naga mugun abu wai menene”? Jin zafin dundu da Adama tayi Mata yasa ta guntse kukan tare da nuna hanya tana bude baki tace” Ba …….ba …baba ne ya dake Aliyu kilama ya kashe shi “? Tana fada ta kuma kurma wani ihun.

 

 

 

Adama jin haka ta zabura tai waje tana salati gaf da zata fita sukai karo da malam tsalha yana shigowa, ” Gidan uban wa zaki ki ka fito kamar wata motar diban yashi?” Ya tambaya yana kare Mata kallo. Itama kallonsa tayi tare da cewa” Cewa akai kayi kisan kai shiyasa na fito dan ingani yadda in munje kotu zan bada shaida” ta fada hade da gatsene fuska.

 

 

 

“Sannu uwar gulum to matsa ki ban hanya tin kafin kema in bugeki in kinje lahirar kya ji dadin ba da shaida munafuka”Malam Tsalha ya fada ya na kokarin ture Adama dake kokarin fita.

Da sauri ta matsa domin da gaske yake.

 

 

 

Shigewa ya yi ciki har yanzu Mardiya na zaune wajen da Adama ta barta tana share hawaye, kanta malam tsalha yayi a fusace tare da kai Mata duka yace” Shegiya wadda bata son arziki idan ban da abunki baki ganki bane? Kyakkaywa dake son kowa kin Wanda ya rasa, ba gidan nan ya kamata a haifeki ba, amma kika zo a nan amma sabida dodewar basira kike so ki mutu cikin talauci”. To ba dani ba tun wuri ki rabu da aliyu bai da komi sai karin boko, da shegen karyar turanci to magafal ma yaci ubansa nagaya miki”.

 

 

 

Tinda ya fara maganar batace kala ba ilah ma cigaba da kukanta da tayi, Adama ce ta shigo tace ” Wai kai malam dan Allah ina ruwanka ne da soyayyar su? Su fa yaran yanzu soyayya ke gaban su ba kudi ba ka kyaleta dan Allah”.

 

 

 

 

A fusace malam tsalha ya juyo tare da kallon Adama yace”Ashe kece mai mun bakin ciki ban sani ba?” To Wallahi ki kiyayeni tun wuri na gaya miki”. Sai ya yi fuuuuuuuuuu ya bar gidan.

 

 

 

 

 

Aliyu da ke kwance kasa har yanzu bai farfado ba saboda ba karamin duka malam tsalha ya masa ba, Abokin sa ne Habu mai rake ya biyo ta hanyar ya ganshi da sauri ya zo wajen yana daga shi tare da kiran sunan sa” Aliyu! Aliyu!! Amma shiru ba amsa sabarsa ya yi a kafada ,yayi gidansu da shi cikin rudewa.

 

 

 

Mahaifar Aliyu zaune tana tankade, ta ga an shigo dashi cikin sauri ta Mike tare da rudewa bakin ta har rawa yake wajen tambayar me ya faru.

 

 

 

Habu ne ya kwantar dashi Kan tabarmar da Innar Aliyu ta tashi sannan yace” Nima hanya ta biyo dani wajen gidansu mardiya nan na tsincesshi Kwance a kasa”. Ya fada yana mai duba aliyun da yafara motsa kansa.

 

 

 

 

Da sauri ya yace ” Inna Aliyu ya farka” da sauri Inna ta kai dubanta kan Aliyu ta re da sauke ajiyar zuciya.

 

 

 

Dafe kansa Aliyu yayi tare da kokarin tashi Habu ne ya taimaka masa ya jingina da katangar dakin, sannan ya kalleshi yace” Wai me ya faru nagan ka kwance a kasa”? Dan ya mutsa fuska Aliyu ya yi cikin jin zafin da wuyan sa yake masa yace ” Hmmmm ni da baban Mardiya ne fa”.

 

 

 

Mtseeeeeeeeeeeewwww! Habu ya ja uban tsaki tare da tashi daga Kan tabarmar yace ” Kada ka rabu da mardiya in ka mutu wani ya aureta, kan me zaka dinga wahala akan yarinyar da ubanta bai sonka?”. Inna sai anjima” yana fadar haka ya kwashe sudedden silifas dinsa ya fita daga

 

 

 

DAN TIJARAR SIRIKI

 

( “` gajeran labari“`)

 

 

 

 

“` written by mamashu “`😘😘😘

 

 

 

“` Bismillahir rahmanir rahim “`

 

 

 

“`Page 2“`

 

 

…………✍✍✍Malam tsalha sauri kawai yake faram faram kamar Wanda zai tashi sama sai tashin kura yake , gidan su Aliyu ya nufa, bayan ya fito daga gida bai ganshi ba.

 

 

” Malam tsalha Malam Tsalha!” Malam Barau ya ke kwad’a ma Tsalha Kira Wanda tsabar balain da ke cinsa bai ya ji bare gani, kara bud’e muryarsa Malam Barau ya yi ” Malam Tsalhaaaaaaaaa”. Wani uban burki Malam Tsalha ya ja kamar tsohowar roka tare da juyowa ya kalli mai kiransa.

 

 

 

Ganin Malam Barau yasa ya kara tamke fuska kamar saniya yace ” Nifa ban cika son Kira daga matsiyata ba, mene zaka dinga kwala min Kira da wannan farar yammar dan Allah “? Ya fada fuskarsa babu alamar faraa.

 

 

 

 

Murmushin takaici malam barau ya yi sannan yace” Gani nayi ai tsiya da tsiya ce ta hadu, ai ba laifi bane dan an gaisa ko?” ” Dakata malam cewar Malam Tsalha sannan ya cigaba ” Ni Wallahi da arzikina domin Allah ya ban ya’ya kyawawa kaga kuwa Allah yaban arziki, kai dai ne ka ke fama da tsiyarka dan haka kira kanka matsiyaci ba ni ba”.

 

 

 

Dariya Malam Barau ya yi sannan yace” To naji ni matsiyaci kai mai arziki ko?” Murmushi Malam Tsalha ya saki sannan yace” Yanzu na ji batu”. ” Ina zaka kaike wannan saurin da yamma lisss haka?” Malam Barau ya tambya yana kallonsa.

 

 

 

” Gidan su shegen yaron nan Aliyu zani kai kashedi kan yarabu da yar wajena Mardiya ya ga yarinya kalan madara da bounrvita kalan shan AC ya keso ya lalata Mata jiki da busasshen jikinsa, to Wallahi ba dani za ai wannan iskancin ba dan haka tun wuri zan ma tufkar hanci ya’ yana yan habuja ne ba yan nan ba aheee”. Ya ba Malam Barau amsa yana mai kara kallon hanya.

 

 

 

“Ha………….”maganar ta katse daga bakin Malam Barau ganin malam Tsalha ya falfala a guje ya nufi wani saurayi, shima binsa ya yi aguje dan ganin me yasa shi gudu.

 

 

 

Habu mai rake da ya fito gidan su Aliyu cike da takaici sai ji ya yi rammmmmmmm an shak’e masa wuya cikin nishin wahala yace” Kaiiiiii wayyyooooo dan Allah sakeni me namaka malam?”. Jin murya bata Aliyu ba yasa Malam Tsalha ya d’an saki wuyan sa tare da kallon sa yace ” Abokin shege ai shege ne dan haka kaima zan baka kashedi, Ka gayama wannan shegen abokin naka ya rabu da yata tin kafin na muku wulakanci na gaya ma”.

 

 

 

Cikin wahalar ruk’on da Malam Tsalha ya yi wa Habu, Habun yace” Wai ni dan Allah ina ruwana ni ba ni ke zuwa wajen yar ka ba dan Allah ka sakeni”. Kamar zai yi kuka yake maganar.

 

 

 

Sakin sa ya yi tare da kallon sa yace ” Wallahi ka gayama abokinka matuk’ar ya kuma takowa kofar gidana da nufin zuwa wajen ya’ta to aradun Allah sai na kiyama ya fishi jin dadi”.

 

 

 

 

Malam Barau da ke tsaye yana kallon ikon Allah yace ” Wai kai Tsalha naga kai ma duk uwar d’arin ce ko? Amma ka bi ka matsa ma mutane naga kai ma ai talakan ne kuma babu alamar za kai kud’in m………….” fasssssssssssssssss! Ji kake malam tsalha ya wanke fuskar Malam Barau da Mari dole maganar ta tsya iya bakinsa.

 

 

 

Malam Barau cikin jin zafin marin ya rungumi malam tsalha suka fara kokowa wajen, Habu mai rake ya shiga ihun neman taimakon rabo domin wajen babu mutane sosai ga duhun magariba ya yi ganin babu Wanda ya zo ya shiga kokarin rabasu, kokowa Suke iya karfinsu kamar ba dattijai ba, Habu sai nishi yake dukkansu ba kadan bane irin mazan ne masu kiba, ganin ba zai iya ba ya sulale ya bar su nan ya gudu dama bai gama farfadowa daga shakar Malam Tsalha ba.

 

 

 

 

Naushi malam barau ya tafka wa Malam Tsalha a ido, ihu ya saki mai karfi tare da sakin Malam Barau ya shiga laluben hanya dan bakaramin zafin dukan yaji ba. Sannan ya shiga surfa ashar yana zagin Barau ta uwa ta uba.

 

 

 

Malam Barau ya shiga daria tare da cewa” Hoooooooo talakan banza talakan wofi na fada kayi abun da zakai”.

 

 

 

 

Cije yatsa Malam Tsalha ya yi cike da bakin cikin kiransa talaka ga azabar zafin da idonsa ke masa ga bai ganin hanya dole ya dinga lalube ya yi hanyar gidansa amma zuciyarsa fal bakin ciki kuma cike da alwashin cin mutunci da zai wa Barau na kiransa talaka.

 

 

 

 

 

Yana zuwa kofar gidan sa me zai gani Aisha ce ke zance da wani dan acaba take zuciyarsa ta kuma hasala rasa me zai dauka ya yi ,tsugunawa ya yi ya kwashi kasa ya yi kansu a guje.

 

 

 

 

Watsa musu kasar ya yi tare da duro ashar mummuna ya watsa ma Aisha da saurayin sannan ya yi kan Aisha da duka. Kwasa tayi cikin gida a guje.

 

 

 

 

Malam Tsalha ya kalli mataccen machine din da Sale ya zo dashi ya sa kafa ya dake shi take kuwa wani gefe ajike ya balle, sannan ya yasa karfinsa ya dauki mashin din ya wurga ma Sale dake chan nesa da shi ya yi cikin gida a fusace.

 

 

 

 

 

Aisha da gudu ta shiga gida Adama zaune ita da Mardiya Maryam kuma na wajen murhu tana hada wuta hayaki duk yacika gidan sai ga Aisha aguje ta tsallake su tayi cikin daki, a tsorace suka mike suna shirin shigewa daki sai ga malam tsalha nan ya shigo yana shigowa hayaki ya cika masa ido, kallon wajen murhun ya yi tare da sa kafa ya yi fatali da ruwan da Maryam ta dora a kan murhu sannan ya bude murya ya ce ” Wallahi duk sai na ci uban ku shegu marasa mutunci in banda iskanci taya za ku dinga kula matsiyata wai so kuke in mutu a talauci ne?, to Wallahi na rantse da Allah ba ku isa ba, ku ba ku isa ku sani mutuwar wahala ba na mutu gawata ma a rasa mai kaita”.

 

 

 

 

Adama dake kallon sa shekeke tace” Wallahi na zata tashin kiyama ce tazo? Yoooo kan ya ya sun yi gadon uban su ai ba laifi bane , baka ji mai hausawa suka ce ba Kyan da ai ya gaji ubansa” Dan haka gado suk…………..Adammmmmmmma! Malam Tsalha ya fada da karfi lokacin da idon sa ya kuma kankacewa da masifa.

About the author

Hausa_Novels

Leave a Comment