Dakika Biyar Hausa Novel Complete
DAƘIƘA BIYAR
_MALLAKAR_
*SAJIDA NIGER*
*Da sunan Allah mai rahama mai jin ƙai*
_1_
*Garabasa , garabasa, dole na gwongwajemu ai, in sha Allah daga yanzu har zuwa na rufe free page daga bakin page 10 diu mai so ya garzayo ya biya dari ukunsa, ta hanyar transfer ko katin MTN, account number 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank sai ki bani shedar biyan ta wannan number +22793811618, idan kuwa katin ne shima ka turon hoton ta number +22793811618, MUTANENA na NIJAR ga naku, katin Sahelcom ko ta airtel ta dala daro, watau 500 francs, sai ku karkare ku turon hoton ta wannan number da take tawa +22793811618, sai kun zo
Zan rayu da kai Hausa Novel Complete
Su biyar ne a zagaye da shi, ko na ce a zazzaune suna kallon in da yake zaune saman kujera mai zaman mutum d’aya irin ta manyan office, hannayansa a cikin juna yana kallon takardar dake gabansa mai son saka shi daria, da kuma son saka shi amai.
A nutse ya d’auke idanuwansa ya d’ora a kan manyan ma’aikatan dake k’asa da shi su biyar cif, a cikinsu d’aya tak ne ya girma, hud’un nan harda wanda ya kai haihuwarsa , sai dai lamari na aikin gwamnati ya saka dole zasu yi masa biyayya a matsayinsa na babbansu.
Takardar ya turo gaban mai bi masa a girman kujera , sai kuma ya kalli wanda ya girma a haife, wanda suke kamanni irin na k’arfin jini, kana ganinsa gan’nin farko zaka iya kiransa da Ɗan uwansa. Hannunsa mai d’auke da agogo, k’irar kampanin *CHOPARD CARATS* wacce a k’iyasin kud’inta million ashirin da biyar ce Euro, <<the watch is so majestic, so elegant, so classy, so luxurious>> balle da ta hau saman tsintsiyar hannunsa mai d’auke da gashi mai ruwan maroon haka kad’an irin gargasar nan dake zaunawa a jikin wasu yaren, bama irin larabawa, fulani, buzaye, dai da sauransu.
Kamar zai yi furuci ne da goggagan turanci irin wanda a k’asar turawa kawai zaka iya jinsa, sai ko a TV, sai gashi ya bud’e bakinsa, da muryarsa mai tafiyar da yannayin halitar jikinsa, watau ELEGANY Voice, ROCK voice ya ce” Abin mamaki, a wannan takardar harda saka hannunka?”
A hankali wanda ya yi nuni ya yiwa maganar ya sadda kansa cike da jin nauyi, baki ya tab’e ya kalli sauran ma’aikatan, da yannayi na Expression din fuskarsa ya ce” Sorry fa, ban fad’i haka dan na raina maku ba, na yi mamaki ne a matsayinsa na jinin AHMAD SULAIMANE yana saka hannu a tab’argazar tabbatar tallafi wajen sake rugujewar tarbiyar y’a’yanmu a garin da ya riga ya rasa banban gurno na tarbiyyar wasu yaren, ta hanyar yin riko da al’adun wasu masu jan kunnayen da Ba da dabi’a!…”
Ya ajiye maganarsa hankali kwance, sannan ya bud’e computer da ya rufe sakamakon shigowarsu cikin gaggawa , tsari irin na wanda ya lak’anci abin, ya dadannata sannan ya rufe ya mik’a hannu ya d’auki rigar suit d’insa ya ratayata a tsintsiyar hannunsa, da d’ayan hannun kuwa ya sake gyara zaman yar k’aramar bindigarsa mai ruwan zeba ya lab’eta da kyau ya zagayo hankali kwomance da niyyar fita ya bar masu office d’in, idan ya so in sun gama sa rufe, wanda haka d’in ma magana ce mai girma ya dank’ara masu.
Da girmamawa sosai, Général ya dube shi,muryarsa a tausashe ya ce” MARÉCHAL, ka yi hakuri idan mun b’ata maka, ka san daga ina wannan order d’in ya zo, yau kusan sati biyu kenan ana jiran saka hannunka, ka sani, muma abin ba dad’i zai yi mana ba, tab’arb’arewar y’a’yanmu a cikin gari yana damunmu, balle an yi masu dalilin maida hankali da yi hankali kwonce suna da masu basu tsaro sai ya ya kennan? Sai dai ka san shi umarni umarni ne, kamar yadda kana bamu umarni babu ja ba tsayawa muke aikatawa.”
Idasa fitowar ya yi ya k’araso inda yake tsaye, sai da ya tsaya a gabansa ta yadda ya sake gannin tsayinsa da nasa ba d’aya ba, duda shekarun da ya bashi na haihuwa bai hanna shi nuna masa idan shi shekaru ya bashi, shi a takardar nan ce ya riga ya sha gabansa,
A dake,muryarsa na amsa amo mai k’arfin mak’ogwaro ya ce”SO WHAT?”
Da sauri General ya d’an ja baya ya d’ora hannunsa gaban goshinsa yana sara masa, da yar gaggawar maganarsa irin yadda yake yi ya furta” I’m sorry Sir!”
Hak’orinsa ya d’an dantse yana yi masu kallon k’asa k’asa…Gaba d’aya yanzun kowa ya zama baya son rigima, sai a ringa baya baya da masifa, bayan du jaraba dai sai dai a kashe ka, mutuwa kuwa ai kowama yi zai yi, shi bai ga abin tsoro a mutuwa ba gaskiya!
A kausashe yana dubansu ya ce” Ban ce ba zan saka hannu ba, but ina buk’atar lokaci dan na sake bin lungu, lungu na sake karantar haukan yan matan garin nan da kuma k’arfin decision d’in nan, idan na ga ba zan iya saka hannu ba kawai kunna iya zartar da aiki da ita a haka, dan babu d’an Adam d’in da zai saka ni yiwa kaina k’ofa a gidan wuta!”
Yana idasawa ya fice d’in ya barsu a nan, sakatariyarsa na ganin fitowarsa ta mik’e tana sara masa had’i da yi masa fatan sauka lafiya, dan ba zata ce masa mu kwana lafiya ba, kowani lokaci ana iya ganin dawowarsa, ya ga damar dare ya tsala ya zo ya fita da patrouille, ko kuma sai an sakankance ya zo ya fita da kansa bakin babbar hanyar TILABERY hanyar da yan ta’ada ke d’an gabatar da d’an sakin jikinsu dan morewa.
K’arar rufo k’ofar , sai da ya saka S FULANI rintse ido, domin kamar a kansa aka buga K’ofar, Attahir ne ya dira hannayensa a saman table din dake ajiye yana kallonsu ya ce” Kuma kun sani, ba zai tab’ a saka hannu a wannan takardar ba, kuma idan muka kai cen wajen yallaɓai babu yadda ya iya da shi, wannan abu ne na ra’ayi,yace baya ra’ayin bada tallafi a haka, bai dace mu ce zamu had’u mu zo mu same shi ba, yana bamu girmanmu, mun sani sarai yana girmamam furfurarmu, ya kamata mu iya kanmu, mu kiyaye haye masa, mu da kanmu dan bamu da karfin kiyawa a zauna lafiyar ne irin nasa, da na rantse maku ba zan saka hannuna a cikin rakardar ba yan mata karfin idan sunna so su yi yawo da pant a cikin gari ba, wai du wanda ya zage su, ko ya nunasu, balle ace ya taba su muna nan zamu kama mutun, mu aikawa alkali shi, a yanke masa hukunci mai tsanani, me kennan muke son yi? Bayan rikicewar al’umarmu ta yanzu, basa gidan Tiktok, basa gidan Instagram, basa nan basa cen, sunna yadd’a kalar tasu bad’alar ta hanyar cutar kansu da kansu a matsayin wayewa sai mu k’ara rik’e masu mara taf dan su baje kolin rashin da’arsu hankali kwonce? Sunnan K’ASAR MU K’ASAR MUSULMAI!, zamu yi abinda a *DAKIKA BIYAR* zamu halaka kawunnanmu, MARCHAL yana da damar k’iyawa, ya k’iya mu kaita hakanan ina rok’on ku.”
Wanda yake christan cikinsu , wato JOEL ne ya d’auki magana yana fadin” Ko mu Christian, ba zamu so irin tab’arb’arewar y’ayanmu ta yanzu ta nin’ninku ba, but kowa yana da zabin yadda zai tafiyar da rayuwarsa ai, mu a adininmu ba takura shi yasa adininmu ya fi dad’i sosai.”
Su dukansu hud’un kallonsa suke har ya dire ayarsa, ajiyar zuciya COMMANDANT AMIR AHMAD SULAIMANE ya yi yana dubansa shima, murmushi ya yi kawai yana girgiza kansa ya k’araso inda yake tsaye, hannunsa ya d’ora ya daka a gefen kafad’arsa kad’an ya ce” Ba’a halice mu dan mu zo mu ji dadin rayuwarmu ba!, A sanina, an halicemu ne dan mu bautawa wanda ya halicemu,……mu kuma ka ga yadda muke kallon namu adinin, kuma mun yarda da haka……, Kun ga ni fa ko a haka na yi iya yina, kyalenin nan da ya yi na rantse bai kyale ni ba, ina nan ina jiran sakamakona dan kar ku manta bayan boss dina a nan, yayana ne a gida!, Komai zai iya faruwa, magariba na shigowa zan je na samu jam’i sannan na wuce gida.”
Daga karshe dai kowa haka ya kama gabansa, abinda suka zo da shi din basu samu ba suka koma da takardar da nufin zasu kaita haka idan aka kwana biyu ya masu shiru, suma sun san abu ne mai wahala, yawanci abinda ya sa ake kai ruwa rana da shi kennan, inda yake da k’arfi daya ne tak, gurbin da yake kai a yanzu ba siyasa ce ta d’orashi ba, a buga a buga a yi k’asa, a yi sama sai dai a dawo a sasanta yadda za’a fahimci juna, ama ba dai a yi masa barazanar za’a cire shi daga kujerarsa idan bai yi biyaya ba, powernsa tana sama da ta mai gidansa, wanda siyasa ta d’ora a kujerarsa, dole zasu je a sannu dan su ci gaba da gaisawa koda hali na kujera ya juye da d’aya.
Sakatariyarsa na tsaye ne a kofar office din sai da kowa ya fito ta shiga ta sake duba komai yadda yake sannan ta rufo kofar ta koma bakin aikinta, dan ita ba zata tashi da wuri ba yau, akoy aiyukan da zata yi masu yawan gaske, mijintama yau ba zai sauka da wuri ba dan sun fita dauko wani mai laifi idan sun tashi sai su yi tafiyarsu gida tare.
A hankali yake tukinsa, har ya k’arasa anguwar mahaifansa, wa’inda ya kwana biyu cif bai lek’o su ba, bai k’arasa gidan direct ba sai da ya biya ta wata majalisar samarin anguwa ya ajiye motarsa daga nesa kadan dan baya so ya karaso daf da su wani ya nemi guduwa, harka ce ta samari idan wane yana jin magana wane baya ji, sai hakuri da addu’a kawai, shi kuma yana shiga cikinsu ne dan a nan yana k’ara samun ilimi na matasanmu.
Saukarsa kawai suka gani a gabansu, hakan ya sa Yusuf mik’ewa tsaye a ba zata yana kallonsa, sai kuma ya koma da sauri da idanuwansa yana yiwa Bashir ido kan maganar da suke yi, lokaci d’aya kuma suka ringa yi masa sannu da zuwa kusan du aka nemi tashi a bashi abin zama.
Murmushi ya yi ya zauna saman kujera yana gyara zamansa da kyau ya kalli Yusuf, wanda shine uban dabar ya ce” Baba zan samu shayin kuwa?”
Yusuf ya wani dan duk’ar da kai ya ce” Sai oga, shayi kai akoyshi oga, bari na ziga maka shi.”
Daga haka ya yi shiru, haka wajenma gaba daya tarin samarin ya d’auki shiru kamar ba kowa, har sai da aka zuba masa shayin nan ya amsa ya sha sannan ya mik’e yana murmushi ya d’aga masu hannu ya masu salama ya k’arasa cen wajen motarsa ya bud’e ya shige ya tafi.
Wata wawuyar ajiyar zuciya Abbas ya sauke yana d’aga yar yatsarsa da ya murje sigarin da yake busawa da ita ya talabe hab’arsa da hannayensa bibbiyu ya ce” Baba dama oga na kawo ziyara nan har na zo da wannan askin na kuma kunna sigari?”
Yusuf ya saki daria yana kallonsa ya ce” Kai baba yanzu fa ka gama cewa kai shege ne, ina cewa yanzu ka gama d’udd’urawa masu kaki ashariya kace kai ba dai mutun ba sai dai Allah?”
Abbas ya yi dariar shima yana mayar da kwalin sigarinsa cikin aljihun wandonsa ya mike yana gyara takalminsa k’ato mai nauyi ya ce” To kun ji, ni kam na k’ara gaba, kai in ba wulak’anci ba Baba ta yaya zaka had’a karnukan sojoji da ubansu? Mutumen nan fa baya duka kwata kwata, ni da idona na ga ya mari kannin matarsa ya summa, uban wa ya aikeni wasa da numfashi? Ce maka na yi ina fafatawa da k’annanun karnukan ba wai SULAIMANA ba , na fasa kawai sai kum faso.”
Kusan d’aid’aikun yan jagaliyar watsewa suka yi, dan sun gani sarai ciki ya shige, yana anguwar , ba zasu d’auki kasadar d’ora daba a wajen ba yau, dan komai na iya faruwa ciki harda ya tub’eka ya zaneka tasss yace baya son rashin kunya kuma babu abinda ubanka ko babarka zasu yi, hasalima ce masa suke Yah SAYYADI.
A nutse yake tafia cikin babban filin gidansu, jifa jifan yakan had’u da samarin gidan, su gaishe shi da girmamawa sannan su wuce bayan ya amsa masu ta hanyar basu hannu, sannan ya d’an ja ya tsaya yana k’are maka kallo, hakan ke saka su saurin sadda kai su ringa kame kame kamar sun aikata laifi, bayan shi ba Dukansu yake yi ba, babu wanda zai ce ga ranar da ya saka hannu ya dake shi a gidan nan, ama sun fi jin tsoronsa tamkar ransu fiye da wanda yake da masifar maganar da dukansu kamar zai kashe su da zarar sun yi laifi.
A kofar falon mahaifinsa ya ja ya tsaya yana dan sake gyara shigarsa, ya sani ne koda ABAH bai ce komai ba sai ya bishi da kallon an yi girman wofi saboda shigarsa
Da wannan ya yi dan murmushi ya kama abin bud’ewar ya shige yar k’ofar farko sannan ya dannan abin budewa ya ja ya tsaya, ya san za’a haska fuskarsa ta camera kafin ya samu shiga
Minti biyu tsakani jar wutar ta bada blue, hakan ya saka shi murdawa ya shiga , a nutse ya cire takalman kafafuwansa yana dan satar kallon Mahaifinsa dake zaune saman kujera zaman mutun biyu yana murmushi yana fad’in” Marhababika Abahna.”
Dan murmushi ya yi yana tsayen nan har amaryar Docter Ahmad SULAIMANE ta shinfid’a sabuwar darduma a saman lalausan cafet din dake malale mai kyan gaske da tsafta tana murmushi da zumbulelen hijabinta tana nuna masa tare da fadin” Babangida barka da zuwa, Bismillah Abah.”
Murmushi ya sake yi ya k’arasa a nutse ya hau saman dardumar dake daf da kaffafuwan mahaifinsa, ya sada kansa sosai a tausashe ya mika hannayensa biyu dan amsar na mahaifinsa dake miko masa ya ce” Barka da hutawa ABAH, yaya ibada?”
Musabaha suka yi mahaifinsa na kallon agogon hannunsa har suka gama ya zauna a nan kusa da kaffafuwan nasa ya dauki kaffafuwan ya dora saman wandonsa a hankali yana dan murzawa yana jin muryar mahaifinsa a tausashe ya ce” Yaya iyali?, Yaya fama da jama’a?”
Murmushi ya yi kasa kasa ya ce” Alhamdulilah…”
Sai kuma ya dago yana kallon fuskar mahaifinsa mai dauke da furfura fara kal a gemunsa baki daya, sai tsili tsilin bakin gashi ya ce ” Yaushe rabon Docter da zuwa gidan nan?”
Kin bashi amsa Docter Ahmad ya yi ta hanyar kamo wata maganar ya ce” Abahna, na tambayeka iyali baka ce komai ba?”
Aunty amarya ce ta yi murmushi bayan ta zuba masa ruwa a kofi mai kyau da tsafta ta ajiye ta ce” Babangida, ai ba zai baka amsa ba , Docter baya son ganin likita, sau biyu yana zuwa yana kin bashi dama, dama so nake ka zo na sanar maka.”
Baki Docter Ahmad ya kama yana kallonta, sai kuma ya yi murmushi ya ce” Gaba kad’an zan ringa lab’ewa ne tunda an fara saka min ido a gidan nan, in ba abin Umman *FATIMA ZAHRA* ba me ya yi saura da ya wuce shiga kabari? Wai ku Docter zai cewa na daina cin nama, sai dai Allah ya bashi hakuri domin babu abinda zan daina d’and’annawa a cikin launin dandanon dake dadad’a min zuciya dan gudun abinda yake rubutace ba kuma zai kauce ba.”
A hankali *SULAIMANE AHMAD SULAIMANE* ya d’an zubawa fuskar Aunty amarya ido dan gannin reaction d’inta, sanadiyar sunnan da ABAH ya ambata , sai ya ga kanta a kasa na yan dak’ik’u sannan ta mike ta nufi Kicin ba tare da ta kuma furta koda A ba.
Kansa ya maido wajen ABAH , a lokacin da ya girgiza kai bayan ta bar wajen ya ce”…
*Alhamdulillah.*
🕐🕐🕐🕐🕐🕐🕐🕐🕐🕐
*DAƘIƘA BIYAR*
🕐🕐🕐🕐🕐🕐🕐🕐🕐🕐
_MALLAKAR_
*SAJIDA NIGER*
*Da sunan Allah mai rahama mai jin ƙai*
_2_
*Garabasa , garabasa, 😁🥰, dole na gwongwajemu ai, in sha Allah daga yanzu har zuwa na rufe free page daga bakin page 10 du mai so ya garzayo ya biya dari ukunsa, ta hanyar transfer ko katin MTN, account number 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank sai ki bani shedar biyan ta wannan number +22793811618, idan kuwa katin ne shima ka turon hoton ta number +22793811618, MUTANENA na NIJAR ga naku, katin Sahelcom ko ta airtel ta dala daro, watau 500 francs, sai ku karkare ku turon hoton ta wannan number da take tawa +22793811618, sai kun zo🥰🥰🥰🥰🥰*
Kansa ya maido wajen ABAH, a lokacin da ya girgiza kai bayan ta bar wajen ya ce” Ban san ranar da zata fuskanci rayuwa a kan y’ar da ta haifa da cikinta ba, Allah shi kyauta.”
Bai ce komai ba, sai ci gaba da ya yi da dan mamatsa ƙafafuwan Aban nasa, a haka Aban ke ta yi masa bayani a kan abubuwan da suke da buk’ata, ba wai kayan abinci, sutura ko harkar wutar lantarki ba, a’a, abubuwa na rayuwa dake iya b’illowa yau ko gobe, wasu taimako ne da sauransu, sannan ya kawo masa karar kanninsu mai sunna JAMILU cewar an kawo karar baya karatu a makaranta, ya yi abokan banza yana yawace yawace a makarantar, har ya yi sa’in’sa da malaminsu, a nan nema ya dan yi dan tsam ya ce” Shi JAMEEL din?”
Aba ya sheda masa kwarai kuwa,
Bai ce komai ba ya ci gaba da sauraron Aban har ya dawo kan maganar yan mata biyu da za’a aurar da kuma k’anninsa AMIR Ahmad SULAIMANE, shi ake jira ya saka rana da dai sauransu, watau bayanin kud’ad’en gadajensu da dukkan abinda ake yi.
Murmushi ya yi ya sake d’agowa ya dubi mahaifinsa ya ce” In sha Allah, za’a yi komai, Abah, sai kana hutawa fa, ka ringa rage magana sosai da yaren nan, idan sun yi ba daidai ba ka saka a kawo su cen in sha Allah zamu zauna mu tattauna.”
Baki da Hanci ABAH ya bud’e yana kallonsa, sai kuma ya yi daria ya ce” Kai Babangida, kai Babangida, so kake ka yiwa Y’a’yana mugunta ko? Gaka nan fuska fara, hannaye farare ama ban san me kake yi masu a cikin duhu ba da suke jin tsoronka, shikenan dan sun min laifi sai na tura maka su cen inda bana nan ba zan tare masu ba? Aa gwara ka daka a gabana ta yadda idan zaka karya zan tare. ”
Shima murmushi ya yi yana sake sada kansa tamkar wani wanda ke gaban sirikansa , yanzun ma bai ce komai ba.
Sosai ABAH ke hirantarsa, shima yana bashi amsa a matsayinsa na wanda ya fi sakewa a gabansa fiye da kowa, sai da ya d’auki lokaci a gabansa sannan ya mik’e yana yi masa sallama da niyyar bi d’aki d’aki ya gaisar da iyayensa har zuwa na mahaifiyarsa sannan ya wuce gida.
A hankali Abah dake kallonsa ya ce” Nace ba, wannan agogo kuwa tai min kyau, nawa ka siyeta ne?”
Ja ya yi ya tsaya, ya juyo yana kallon Mahaifinsa, dama tunda ya ga yana bin agogon nan da kallo ya san da wata a k’asa, watan kuwa ba komai bace face son sanin kud’inta, dan ya tabbata so yake yi ya san shin ya sayeta da mak’uddan kud’i ko da sauk’i? In da mugun tsada ne yanzu a bud’e babin wa’azi kala kala harda su maganar zakka, bayan Alhamdulilah yana kamanta abinda adini ya zo da shi.
Murmushi ya yi ya dawo ya duka yana balewa ya ajiye a daf da hannun Mahaifinsa a tausashe ya ce” Abah, bata da tsada kuwa, gatanan ina so ka saka , Allah ya karra maka lafiya…..Docter zai zo gobe da sasafe in sha Allah, ka taimaka ya dubaka, kafafuwanka sun tasa….bana so na ga sun tasa ka ji?”
Irin yadda ya tsatsareshi da ido sai da ya ji kwallah na taruwa a tasa,
Murmushi ya yi ya dauki agogon ya mayar masa a hannunsa ya ce” Kai kuwa, abinku na yara me ya hadani da shi, ina dai jin tausayinka ne, kuma ina dan son yin nasiha, lokaci zuwa lokaci a ringa rage siyan tsada sosia, dan nauyin kar ya yi yawa a zo a shiga hurumin gwamnati da kuma harkar talakawa…., Abahna ka san ko me bawa zai yi, idan bai rike bakinsa daa hannunsa da cin haram ba da sauki, ka kiyaye cin zali ko yayane, ka ji tsoron Allah shi shi kadai, bayan wannan ko waye ka barshi ya gwada ikonsa cikin damar da Allah ya bashi ka ji?”
Murmushi ya yi a hankali ya gyada kansa, ya dauki agogon ya mayar a hannunsa,, dan ba zai yi musu da mahaifinsa ba, ba kuma zai ja ya ja ba, haka kuma ba zai tsaya yace masa kar ya masa nasiha ba , dan nasiharsa shine kwarin gwuiwarsa, mahaifinsa shine na biyu a cikin layin abinda ke saka shi kiyaye dokokin Allah, daga Alkur’ani sai shi, ba zai iya duban idannuwan mahaifinsa yace da shi wannan agogo ya siyeta ne dan halin haka ya bashi dama, ba zai kwatanta masa a yanzu yana samun kudin da bai san yaya zai kamanta su ba, kamar wanda ake bashi rabonsa ,……bashi da abin fadi sai hamdallah, kuma in sha Allah zai rage siyan tsadar, dan a gaskiya yana siyan tsada, da wannan ya fice, Mahaifinsa ya bi shi da kallon tausayi da kuma addu’a, cikin ikon Allah sai da ya ringa haihuwar ya’ya har bakwai da matansa biyu sunna komawa ga ubangijinsa , shine na farko da ya zauna, daga shi kuma har yanzu babu wanda ya rasu, bai wani dauki shekaru ba, dan bai fi talatin da biyar ba, ama a haka Allah ya saka masa albarka, bayan dogon karatu ya fito ya damki aiki mai daraja har ya zamo kafada mahutar dangi da jama’ar gari
A muntuce ya ringa bi daki daki, tun daga kan aunty Amarya, har zuwa dakin mahaifiyarsa wato uwar gidan Docter Hajia ZUWAIRIYA ,
Kowance idan ya shiga bangarenta ya gaisheta, yakan saurara ya saurari bukatunta, da kawo kararta da sauransu dai, abinda ba za’a rasa ba , ba zai bar wajen ba har sai ya biya mata dukkaan bukatunta da yake iyawa, wa’inda baya iyawa kuwa yakan yi addu’a ne ya tashi
A dakin Aunty amarya kawai ya shiga ya fito bata ce tana bukatar kudi ba, ko ta kawo karar yar uwarta ba, har ya gama dan zama ya mike ya bar bangarenta ta bishi da addu’a kanta a sade dan fushin mijin bai saketa ba, watau da ya fadi sunnan da bata so, bata kauna ba kuma zata tana so ba!
Irin zaman da ya yi a saman kujera yana dan cakalar dankalin turawan da Hajia ta zuba masa da kanta irin zama ne da akan yi idan an zo gaban mahaifiya, wato ba d’ar ba dari d’ari.
Abincin yake ci, bata yi masa magana har sai da ya gama ta yi kiran daya daga cikin yarenta ta umarceta kan ta kwashe , ta kwashe ta mayar kicin ta kimtsa wajen sannan ta dawo sumui sumui ta haye sama numfashinta a makogwaro har ta shige sannan ta ja numfashi tana shigewa dakinta hadi da adu’ar Allah ya sa kar Hajia ta sanar masa cewar yau bata yi wanke wanke ba, wancen bara gurbin ta saka ta yi mata ya ci kakanin babaninta!
Hajia ta sake zubawa fuskarsa ido, sai kuma ta tabe baki tana cire kanta kasa kasa ta ce” wannan ja na lebenka kamar dai ba na lafiya ba……”
Kasancewar yana kallon fuskarta ne, kuma yana jin dukkan abunda take fada, sai ya yi murmushi bai ce komai ba, bai san me yasa kalar lebensa yake saka mahaifiyarsa koda yaushe mita a kai ba, shi dai ko goro baya taunawa bale a kai ga sigari ko giya, hasalima kamaninsa da na mahaifinsa tamkar kaki ya yi ya tofar, itace baka sannan a kaf ya’yan mahaifinsa su uku ne suka yi farinsa, ama Hajia sai tace shi nashi jan ya yi yawa anya na lafiya ne?
“Baban gida, na san abanka ya maka maganar kayan lefen yaren nan ko?” Hajia ta fada tana dubansa
A nutse ya amsata yana sake dubanta
Hajia ta hade fuska sosai ta ce” To bari ka ji abinda zan fada maka, ban lamunce maka kwasar kudi ka je ka kwashi kaya na makudan kudade ka zubawa ya’yan da kwanan duniya iyayensu ke koya masu tsanarka da kiyayarka ba, ka sani ni na haifeka babu wanda zai fi ni sonka ko sannin zafinka a duniya, ka kula Baban gida, idan nace bana so kar ka saki ka yi!”
A hankali ya dago kansa dake sade, shin yaya zai yi da iyayensa ne? Idan wannan ya ce ga abinda yake so a yi, sai wancen ya ce kar a saki a yi, ya kuma yi aiki da karfinsa da ikonsa a kansa
Bai san me yasa Hajia take yin wasu abubuwan ba wani lokacin, bayan shi ya sani mahaifiyarsa mutun ce mai matukar kyauta da son mutane
“Yaya zaka tsareni da ido kana min wani kallo kamsr sa’ arka Baban gida?, So nake ka fada min abinda abanka yace kaf ina saurare” ta sake fada harda harde ƙafafuwanta, irin jira take ta ji abinda bai yi mata ba a yi wada za’a yi
Ajiyar zuciya ya sauke a tausashe ya ce” ABAH bai ce min komai ba, nine nake so mu yi maganar da ke, sai na ga abinda ya dace a yi, MAMAH kar ki manta nine baba a gidan nan, ko me za’a yi ya zama wajibi na shanye na kuma nuna masu halin girma, da haka ne zasu yi koyi da ni idan kowa ya malaki hankalin kansa ya rike zumunci duk rintsi, Mamah, dukkan abinda suke yi ko giya suka sha babu wanda zai tunkarenk, tun daga kan AMIR har zuwa kan ummi Auta…, Ko a haka aka tsaya da sauki a irin tab’arb’arewar zamani da zumunci…”
Zama ta gyara da kyau tana kallonsa ta katse maganarsa a harzuke ta ce” Ba zai yiwu ba fa, ba zai yiwu ba, su rike zumunci ko kar su rike wannan damuwarsu ne, ba zai yiwu a taru a kashe min ɗa ba, na tabata abanku ba wani tausayinka yake ji ba, bari ka ji, idan ya ce sai ka yiwa ya’ya mata kayan daki da komai ba laifi ka yi, bayansu idan ka yarda ka yiwa matansa ko maza kayan aure ban yafe ba! Nace ban yafe ba baban gida, bama irin matar nan da yake sakawa a gaba tsofai tsofai da shi yana ikirarin soyaya, wace soyaya kuma Allah na tuba gayar yawun tsufa, na yanke magana Baban gida ba zai yiwu ba!”
Idannuwansa kawai ya mayar ya rintse, lokuta da dama yakan rasa ina mahaifiyarsa ta dosa,
A lokacin da Aba ya auri matar nan baki dayansu sun nuna mata kiyaya, uwa uba y’ar da Abah ya kawo matsayin tata ya kuma nuna ta zama tasa, yarinyar na fuskantar tsangwama da kyara a wajen dangi dan ta zamto wace aka haifa ba da aure ba, wulakanci kala kala na rayuwa tale gani, mahaifiyarta da ta haifeta da cikinta ta fi kowa tsanarta dan ko kofi ta taba ba zata taba ba, rana tsaka MAMAH ta ba kowa mamaki ta dauko yarinyar nan ta hada da ƴaƴanta ta kuma jajirce a kan yarinyar ta sakata makaranta take kuma tsaye a kan tarbiyarta, har yau an kasa gane me hakan yake nufi, domin a bangarenta yarinyar ke rayuwa, a wajen mama ba zata taba fuskantar kyara ko tsangwama ba, hasalima tana rike da ita da zuciya daya kamar yadda zata taro ƴaƴanta ko ta gyara haka zata yi mata, takan ce yarinya tata ce, ama bata son uwarta, hakan na ba kowa mamaki, sai dai a duniya ita Mama bata iya rayuwa ta munafurci ba, idan tana yinka tana yinka ne, idan bata yinka bata iya boye boye ko yi da gangan ba, FATIMA ZAHRAH tana samun hutu ne da kwonciyyar hankali idan tana gaban Mamah, du fada irin na Mamah tana jin du duniya bata da wajen mafaka sai a saman kafadunta, zaka ga Mamah ta wanke ƴaƴan kaf da fada kowa ya gudu ama ita sai ta karaso ta duka ta dora kanta a saman cinyiyinta ta yi ta sauke ajiyar zuciya……….wannan tsakani nasu na ba kowa mamaki ciki harda Docter Ahmad SULAIMANE
Wannan babin Mamah ta rufe ta sake dauko na iyalinsa,
Hirar da sam bata wani so, ba kuma ya farin cikin sauraro, sai dai wace ke yi din nan itace Allah ba zai saka shi aljannah ba idan har bata daga kafarta ba, du duniya itace take kallon idannuwansa tace zan fa ci ubanka babana, kuma a saurara a yi murmushi dan ta isa, bayanta ko mahaifinsa a yanzu sun zo bigiri din da yake lalaba shi, yake kuma yi masa komai a hankali du zafi irin na AHMAD SULAIMANE.
*A bayan Layi*
A tsaye take tana bin motar mai kirar Corolla da ido sannan tana jin muryarsa yana sake kiran sunnanta a karro na uku
A hankali ta dauko idannuwanta masu kama da na mashayiya, uwa uba tsarin halitarsu tanaa da girma daidai misali, sannan fattar saman mai bugun ido ce,, irin kana kallon su zaka so fara kawar da dubanka, dan ba irin idannuwan da ake tsatsarewa da kallo bane, ga wani ruwa ruwa mai nuni da daf ake da iya fara kuka, koma sama da haka, bayan babu maganar kuka a kusa kusa a cikin tsarinta, ba dan ta kasance mai tsaurin ido ko mai taurin kai bane, ko daya, hasalima ana iya kiranta da farar kura dan tsabar tsoronta, dan tana da saurin jin tsoro, ama kuma halitarta mai bayar da tsoro ce
Farar fuskarta dake dauke da kwontacen gashi a gaban goshinta, wanda lafcecen hijabinta bai hanna su bayana ba ne ke daukan jajaja, kumatunta na neman kumbura lokaci d’aya.
Leave a Comment