Littafan Hausa Novels

Dafin Namiji Hausa Novel Complete

Written by Hausa_Novels

Dafin Namiji Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

*DAFIN NAMIJI

_True life story._

 

 

_NA:_

*_K_SHITU🦋_*

09133307121

 

 

 

*_[2023]_*

 

_Ban yarda wani ko wata ta sauya min littafi na ta kowace hanya ba batare da izini na ba_.

Kuskuren Kaddarata Hausa Novel Complete

*_BISMILLAHIR RAHMANUR RAHIM_*

 

*_D’AND’ANO_*

 

_SHAFI NA D’AYA DA NA BIYU_

*1-2*

 

 

Tafiya take yi cikin natsuwa, har ta k’araso bakin k’atan gate d’in gidan su, k’wan-k’wasawa tayi mai gadi ya bud’e Mata, yana yi mata sannu da dawowa, cikin sauri driver yazo yace “hajiya ina wuni, an dawo lafiya?.”

Cikin muryar ta mai dad’i ta amsa da ”lafiya qlw ya Aiki?.”

“Aiki Alhamdulillah.”

“to ma sha Allah.” tace ta shige cikin gidan, “Mammy Mammy! Kina ina?.”

“haba ZAINAB! Wannan kira haka, bayan kinsan ina kitchen, ai saiki ja Girki ya zube mun ajiki.”

Dariya tayi tace…”haba mammy Dan na d’an Kira ki inji kina ina ,Wallahi yunwa nake ji, sosai mi zan d’an samu in ci?.”

“Kije gurin baba sa’a akwai fura data damawa sadeek kice ta baki ragowar da aka aje, a fridge saiki sha.”

“Thank you mammy na.”

Da sauri ta nufi hanyar kitchen tana zuwa ta gaya wa baba sa’a ta bata, furar ta wuce d’akin ta ta sha ta cire, uniform d’in islamiyar ta tayi wanka Kafin ta gama shiryawa an kira sallah, tayi magrib ta sauko k’asa gun su, dad sukayi fira bayan isha’i suka ci Abinci around 10:00PM kowa ya tafi ya kwanta…..

*ALHAJI ISMA’IL LAWAL*

Shahararren d’an kasuwa ne mai ji da kyau uwa uba kud’i kamar mai, Allah ya yishi d’an Adam mai zurfin ciki, bazaka tab’a iya gane kanshi ba koda ka shekara biyu dashi, Dan Allah ya yishi da sanin ya kamata ga ilimi da tausayin jama’a Katsinawa kowa na ji dashi saboda kyawawan, halayan sa da Kyauta, matar shi d’aya Halima mace ce mai kirki da kyawawan d’abi’u ga tsafta da kyau, Yaran su Biyu Abubakar sadeek sai Zainab. Allah yasa yaran su ba watsa-tstsu bane ga natsuwa da tarbiya, babu ruwan au da girman kai sadeek nada shekara 26 ,zainab bada 19 shi ya gama secondary school ya fara *ALQALAM* level 300 ita kuma tana *CHAIRISH* school of nursing duk cikin yaran shi Yafi San zainab Dan Akwai natsuwa da biyayya babu ruwan ta da rashin kunya……

 

Yau Monday tunda wuri Zainab ta shirya kayan ta Dan hutun su ya k’are zasu koma school, Fuskar ta cike take da fara’a, bayan ta gama shirya komai nata ta dawo parlor gun mammy, duban ta mammy tayi tace ”Daughter har kin shirya kenan?”

Murmushi tayi, kana tace…. “E mammy! ina ya sadeek? kwata-kwata ban ganshi ba ko da za’a yi breakfast.”

“kinga Wallahi yana School.”

”Mammy jiya ba kince mun ya dawo anma, dama mishi fura ba?.”

“Eh ai yana sha yatafi.”

“Oh to nagane.”

Haka ta shirya ta driver ya Kaita ya dawo tunda ta shiga taga wata bak’ar mota nata bin bayan ta amma saita dake ta basar ta chigaba da tafiya, ganin bata da niyyar tsayawa yasa mai motar danna mata horn, amma kamar kurma tayi banza ta kyaleshi ,shi kuma ya saki murmushi mai k’ayatarwa tare da saurin parking d’in motar, ya fito cikin k’asaita, da taku na isa da ji da kai irin na wad’anda kud’i ke gayama karya, shan gabanta yayi yace “haba y’anmata? Ya kinji ina ta yi miki horn amma ko ki tsaya.” Ko kallan shi ba tayi ba ballan tana ya sanya ran zata bashi amsa ,duban ta yayi ya k’ara cewa “beauty miye sunan ki?” ra tsawa tayi ta gefen shi ta wuce har cikin ranshi ya yaba da irin kyawun ta, saidai Ashe ita ba ma wayayya bace d’an k’aramin tsaki yaja, koma mota cikin jin haushin ta, Jan motar sa yayi a fusace ya nufi

GORUBA ROAD

Wani tank’ame-men gida yayi horn, mai gadi ya bud’e masa, ya shige da motar sa, direct d’akin sa ya nufa yaje jikin mirror ya tsaya yana k’arewa kansa kallo Dan yasan Allah ya yishi kyakykyawa toh miyasa tak’i koda kallan sa…..

 

A b’angaren zainab bayan kwana biyu ta manta dashi karatun ta takeyi kawai,hankalin ta kwance Dan bata da damuwa ta komi, Yau ta kama WEDNESDAY Yau Khaleed ya kuma shiryawa, ya nufi CHAIRYSH Dai-dai lokacin ta fito tana Neman k’awar ta Rahma Cikin sa’a idanuwan sa suka hasko masa kyakykyawar fuskar ta, da sauri ya fito daga cikin motar ya nufe ta Cikin d’an sauri sannan yace….”ji mana Y’an mata.”

Waigowa tayi ta kalle shi sai Kuma ta jiya tare da matsawa kad’an, duban ta yayi sama da k’asa babu laifi doguwa ce sosai kalar kyawawan mata masu Kyakykyawar suffa, Saida ya danne wani Abu sannan yace…”Sunana Sulaiman Umar! Wanda akafi kira da KHALEEL Ke fa?”

Kamar ba zata bashi amsa ba sai taja numfashi tace “ZAINAB ISMA’IL”.! Murmushi yayi yace “Owkayh ko zamu iya shiga cikin mota, muyi wata magana?” Girgiza masa kai tayi Alamar A’ah sosai yaji haushi Amma Ya daure yace “Toh please ki taimaka min da number ki.” da kamar zata ce wani Abu sai Kuma ta fasa tasaka mishi, dai-dai lokacin rahma ta iso, hararar ta Zainab tayi tare da Jan d’an tsoki tace….”Dallah malama ki wuce muje, duk kin wani b’atawa mutane lokaci A banza.” mtswww dariya Rahma tayi Dan hasala zainab d’in tace “haba zee-zeee wallahi JB ne yazo shiyasa, kika jini shuru, amma I’m sorry dear. ” Jan hannun ta tayi suka barshi tsaye ba tare da yace uffan ba

*DAFIN NAMIJI…

_True life story._

 

 

Written by:

K_shitu

09133307121

 

 

*[2023]*

 

_D’AND’ANO_

 

_SHAFI NA UKKU DA NA HUD’U_

*3-4*

 

*BISMILLAHIR RAHMANUR RAHIM*

 

Suna komawa department d’in su, Rahma ta fara jera mata tambayoyi, Shigowar Maryam d’ayar k’awar tasu, yasa Rahma nufar ta tana fad’in “banza Labari ya barki, Yanzu wani had’ad’d’an, guy yabar gun Zainab.” wata harara Zee ta banka mata, cikin sauri tace “Sorry K’awata, ba ni na kar zoman ba, rataya Aka ban.” Pillow ta wurgo mata yayin da Maryam ta tuntsire, da dariya tace “Rahma kice Yanzu ,mun samu zeen love.” cikin matsa-nanciya dariya tace “gaskiya baki da dama maryam” kawai saita fice waje ta bar musu d’akin Dan ta sansu sarai, Sun iya tsokana, Ganin wata Bak’ar mota K’irar *KIA* ta shigo makarantar yasa ta, Kallon motar sosai kamar taso tasan wani nata da irin motar, A mamakin ta sai ganin Kawu Mustafa tayi ya, fito daga ciki shiyasa ta zaro manyan idanuwan ta sosai taji gaban ta ya fad’i, amma saboda jarumta sai ta dake ta k’irk’iro murmushi tace….”Ina yini Kawu na, na kaina”

“Lafiya lau d’iya ta ya makaranta?”

”Alhamdulillahi yasu Aunty Fauziyya?.”

“Duk suna nan lafiya.”

Daga haka tace mishi suje d’akin su, Dan ko wata rana bai ganta A nan ba, Haka suka tafi zuciyar ta fam da mamakin sa ,saidai ko da wasa bata nuna masa hakan ba saima fira da suka yi kamar mintuna 30 sannan yace ya wuce ya bat 10k da k’yar ta amsa sannan ta masa godiya ta dawo, saidai Kawai zuciyar ta bata yarda dashi ba duk da K’anin mahaifin ta ne……

Lokacin da ra koma d’akin su dan ta dawo daga rakiyar sa sai kawai ta b’oye Kud’in a akwatin ta ta dawo suka hau fira dasu maryam, haka har lokacin ya shud’e sosai Zainab tana da Mugun suruta da tsiwa amma tana da natsuwa, wannan kenan, Bari muji waye Kawu *MUSTAFAH*

Tunda mahaifan Alhaji ISMA’IL suja haife shi basu sake haihuwa ba sai bayan Shikara Bakwai dan haka A lokacin isma‘il saida yayi wayau sosai sannan aka mishi k’ani tun tasowar mustafa ya d’aurawa kansa bakin ciki da hassada Dan bayan rayuwar mahaifan sa ruk’on su ya dawo hannun y’an uwan mahaifin sa da yawancin su suna da wadata sosai Shi ISMA’IL Baba Kamal ya d’auke shi, shi kuma Mustafa Kawu Jabir ya d’auke sa haka rayuwa ta chigaba da tafiya har ISMA’IL Ya fara business Sosai ubangiji, ya fara d’auka ka sa yayin da shikuma Mustafa yake Secondary school A lokacin da Allah ya k’ara bud’awa ISMA’IL lokacin Allah ya yiwa kawu Kamal rasuwa Mutuwar tasa ta ratsa sa sosai Saidai Har Allah ya karb’i Baba Kamal bai tab’a haihuwa ba, Haka aka hak’ura da rashin Kawu Kamal saidai Abun mamaki Bayan rasuwar Kawu Allah ya kawo wa Isna’il wasu mahaukatan kud’ad’e tare da chigaba, saidai Ya tsare zakka da sadaka Shiyasa Allah ke kare sa Ana haka Aka ta kura sa akan wai yayi Aure, shidai har ga Allah zai bi umurni ne kawai yayi badan yana da wacce yake so ba sanshi kwata-kwata mata basa gaban shi Haka wata rana ya had’u halima suka yi Aure yayin da Shi kuwa Mustafa ya karanci fannin computer science, saidai ko kama k’afar Isma’il bai yi ba A gurin kud’i! Sosai dangi suka taso ISMA’IL gaba shi ya rasa mi yayi musu dan haka ya barwa Allah lamurran sa daga haka shima Mustafa ya auri matar sa Fauziyya Dan itama Allah ya yita mace, mai mugun kwad’ayi da San abun duniya duk hassadar da yake wa, Isma’il ita ke tura sa…. K’iri-k’iri ya saina zuwa gidan ISMA’IL ya daina, shiga harkar sa kullum idan ya tashi Neman kud’i ba kunya zau tambaye sa shi kuwa, ruwan sa sai kawai ya basu, Ko da matar sa ta haifi yaro namiji zuciyar sa ta k’ara bushewa, Dan a halin yanzu ya tsaani d’an uwan sa Amma daga baya ya Fara sakewa dashi yana shiga jikin sa Amma a koda yaushe yakan,Gaza danne bak’in cikin sa duk sanda yaga Sadeek da zainab, Dan shi Fauziyya ko b’atan wata bata tab’a yi ba.. Hakan yasa ko harkar yaran baya shiga baya, sakar masu fuska shiyasa babu ruwan su dashi sai gashi yau wai yazo ma Zainab visiting anya masu Karatu kun yarda d zuwan sa?……

 

Khaleel ne ke waya yana ta b’ab’b’ata fuska cike dsa gajiyawa yace “Please abar yarinyar nan mana Dan ta cika kilbibi, ni nama fara gajiya ita ace yarinya kamar, ba wayayya ba.”

Banji mai na cikin Wayar yace ba sai kawai naga Khaleel ya saki murmushi Cikin kuma jin dad’i yace “Na gane sai mun, had’u ina gdy.” Aje Wayar yai yana sakin wani makirin murmushi tu’ki ya chigaba dayi fuskar sa A sake Wani had’ad’d’an gida ya nufa chan bayan gari, yana shiga ya d’auko Wani Abu ya rufe Rabin fuskar sa Wasu mutane na gani kamar bodyguards, dukkan su fuskokin su a rufe ga wani bak’in glasses da suka sanya, Darewa su suka hud’un suka bashi hanya ya shige cikin wani d’aki wasu mutane na gani su biyar zazzajne bisa wata kujera.

Gaida su yayi, Saidai babu Wanda na iya ganin fuskar sa tattaunawa sukayi har wajen 4:00PM sannan ya baro, gidan tare da mak’udan kud’ad’e, daga nan Ya koma gida ya shirya ya baje bisa makeken gadon sa Wayar sa ya d’auko yayi dialing number Zainab saida ta tsinke ya sake kira sannan ta d’aga ba tare da tace komai ba….Sallama yayi ta amsa sannan yace “Kin ko gane mai magana?.”

Daga chan b’angaren tace ”A’a gaskiya.” dariya yayi sannan yace “Khaleel ne.” Haka suka chigaba da for sosai yake janta da barkwanci, haka yai ta kiranta suna gaisawa yana ta fad’a mata kalaman soyayya.

Yau Friday so shirye-shirye take yi Dan yau Khaleel zai zo ta kasa zaune ta kasa tsaye, lura d hakan da su Rahma sukayi ne yasa suka dinga tsokanar ta rahma har da cewa, wai karya k’ara ganin laifin ta idan tana JB hidima….

 

Ita dai banza ta musu haka yazo bayan sallar juma’a yazo sukai ta wannan karon itama ta tabbatar mishi da tana son sa yayi murna sosai kamar ya had’iye ta Dan farin ciki, da zai tafi ya Kawo kedoji guda ukku chikeda kayayyaki da kayan kwalliya da k’yar ta karb’a tayi godiya suka yi, sallama ya tafi Sosai soyayya mai k’arfi ta wucin gaban misali ta shiga tsakanin su, cikin sati ukku……

 

Yau Weekend ina gida zaune nake bisa kujera 2seater yayi Sadeek ya shigo shida Abokin sa Farhan ina ganin sa na sha mur, Dan nama shiru kwata-kwata, sallama suka yi, na amsa ciki-ciki kallo na Farhan yayi ya tab’e baki yace………

 

*🤝 SDEENDTM DATA SERVICES🤝*

*MTN* . *Airtel*

1GB = ₦300. 1GB = ₦300

2GB = ₦600. 2GB = ₦600

3GB = ₦900. 3GB = ₦900

4GB = ₦1200. 4GB = ₦1200

5GB = ₦1500. 5GB = ₦1500

 

*GLO* . *9MOBILE*

1.5GB = ₦500. 500Mb ₦500

2.9GB = ₦1200. 1.5GB ₦8000

4.1GB = ₦1600. 2GB ₦1600

5.8GB = ₦2100. 3GB ₦2000

7.7GB = ₦2700. 4GB ₦2500

 

*VALIDITY: 30DAYS/1MONTH*

_For cable subscription or sell recharge card_

_Call this number or WhatsApp._

 

 

 

*08066268951*

 

 

K_sshitu

About the author

Hausa_Novels

1 Comment

Leave a Comment