Littafan Hausa Novels

Da Aurenah Hausa Novel Complete

Hotunan Yadda Ake Kwanciya Da Mace
Written by Hausa_Novels

Da Aurenah Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

DA AURE NAH

*NA

 

 

*HAUWA’U SALISU*

 

 

 

 

KAINUWA WRITER ASSOCIATION

“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`

 

 

 

 

 

Bissimillahirrahmanirrahim

 

 

Dukkan godiya ta tabbata ga Allah ubangijin Talikai

 

 

 

 

Page 1

 

 

 

Tsaye suke kan kwanar layin ya zuba mata ido yana binta da wani maya taccen kallo ita kuma ta sadda kanta kasa

 

Dan haka nace yakamata najiyo meke faruwa acan

 

 

 

Inason kidago kanki ki kalleni kisa idanunki a idanuwana Huwailat don natabbatar da gaskiyan abunda bakinki yafada nidai nasan Allah shiya doramin sonki da kaunarki a xuciyata Dan haka bana jin akai wani Abu da xai kauda kaunarki a xuciyata Huwailat kinsan yanda xafin kauna take a xuciya kuwa tabbas nasan baki saniba da kin sani ba abunda xaisa kidinga wasa da numfashina

Ta dago ta kallesa so daya ta sadda qanta qasa tana murmushi tana jin dadin kalaman da Yusuf kefada mata duk sanda suka hadu jitake tamkar tafi kowa sa ar masoyi a duniya

Magana nake dakefa Huwailat amma kinqi magana kinsan da cewa maganarki na bani qwarin gwiwa sosai wajen ganin mun cika mura dinmu ta dago ta sake kallonsa tai murmushi

Bansan abunda xancemaba amma nasan dai Kaine farin cikin raina sannan Kaine cikar muradina INA farin ciki naga randa burinmu xai cika tana daga ido ta hango wani dake tafowa naga tai maxa tabar gun shima Yusuf yai nasa hanyar

Abun tambaya waye Wanda ya katsema masoyannan hanxari

Diyam Hausa Novel Complete

Kubiyo Haupha don jin cikakken lbr mai cike da ban tausayi ban takaici cin amanah da yaudara

 

 

 

*NA*

 

 

*HAUWA’U SALISU*

 

 

 

 

 

 

 

07081095452

 

Page 2

 

 

 

 

Godiya ga My M K

 

 

 

 

Cikin sauri tafada wani gida ta maido kofa ta rufe ta cire hijab dinta ta fada dakinta ta kwanta saman kujera

Tabbas ina matuqar Qaunarka Yusuf amma yaxan da wannan jarabawa data sameni

Anya inada hankali kuwa da nafara sonka tabbas akwai tashin hankali sosai agabana Wanda bansan iyakar inda xai tsayaba

Tib tib taji alamar shigowan mutum a falon tai masa kallo daya ta maida kanta ta kwantas saboda idan tana cikin tunanin Yusuf bata Qaunar ko kadan taga gilmawai Amadu a idonta

Mintuna kadan ya fito yasake gittawa ta gabanta ya fice ta girgixa kai ta koma tunanin hanyar da xata sake ganin Yusuf

Sallamarsa taji cikin matuqar murna ta rufe eyes dinta alamar barci take tanajinsa ya daga labulen dakin ya xubamata ido yana murmushi yasake wata sallamai amma taqi motsawa cikin tafiyansa ta isa da taqama yashigo falon ya duqo fuskansa dai dai nata yana jin yanda take fidda numfashin ta ya lumshe ido yasa hannu ya shafa fuskarta yai mata kiss a kumatunta ina matuqar qaunarki wadda bansan sanda na afka cikintaba yasake shafa mata fuska yana qarema fuskanta kallo ita kuma taqi bude idonta wai barci take da Gaske

Murmushi yayi nasan kina jina sai dai nima baxanso kifarkaba Dan kada nadaina ganin wannan kyakykyawan fuska nakiba Dan sainaga kinfi kyau ahakan yana magana yana shafa fuskanta ahankali yana xagaye bakinta da yatsansa

Ganinba xai dainaba ta bude idonta dontasan baqaramin aikinsabane yai abunda yafi hakanba

Dariya yai mai qarama fuskansa kyau dama nasan ba barci kikeba Dan naga fitarsa yanxu ai baki isayin barciba kawai kinamun rowan ganin wannan idanuwan masu saukar da nishadi garenine kawai

Dariya tayi sosai Wanda yasaki baki da hanci yana kallonta ji yake tamkar ya rumgumeta yanda dariyanta kesaukar masa da kasala a jiki amma yasan baxata bariba koda yake xai jure akwai lokaci

Ahankali ta daina dariyan ta dauke hannunsa dake bisa cinyarta tamike tsaye taje wajen wani lungu ta dauko wata kula ta miqa masa batare datai maganaba kin ansa yayi kinsan baxan ansaba saikin bude naga miye ko

Murmushi tayi ta bude kulan saiga faran shinkafa da mai da yaji da maggi mai Star guda bisa kagani saika ansa ko malam dariya yayi baxan ansaba kije kidauko cokali kixo muci Dan yunwa nakeji daman sosai

Kallon kafiye rigima taimasa kasanfa naci nawa wannan nakane daxun naso nafadama muka rabu ba bankwana

Yatsine fuska yayi kekika jiyo nidai anji abunda nafada Dan haka in anaso naci aimun yanda nace idan kuma bakiso to wlh xan kwana da yunwa nasan xakiyi farin ciki ko ya kalleta sosai yanason yaji abun da xatace

Kallon dai taimasa na kafiye rigima ta aje kulan ta nufi wani qaramin daki ta dauko cokali biyu ta dawo

Dariya yasa mata kina nufin kowa da nasa wai baki isaba da guda xamui amfani nidake sannan kexakiban Nima na baki Indai kinason da gaske naci abincin ga yunwa inaji kinsan inada ulcer shiru tayi kanta a qasa tanajin rigimar da yakemata yau kuma tasan baxata iya barinsa da yunwa ba gara ace ta kwana bata cibada ya kwana da yunwa saboda shine kawai kesata farin ciki yaxama dole itama tasakasa koda bata son abunda yasata yaxama tilas ta jure taimasa

Kallonta kawai yake yana qara yaba kyan jikinta Dan ba qarya Huwailat kyakykyawace ajin farko a cikin mata Allah yabasa dama r cika burinsa kanta koda yake bakowane namiji xai samu kamar Huwailat yarabu da itaba sai marai rabo amma kuma ai ba a maraya sai raggo Dan haka xai jure xai dake harya sameta cikin nuna jin haushi yatashi ya nufi qofa bata San sanda ta jawo rigansaba yadawo baya pls Karka tafixan baka murmushi yai yadawo yaxauna yabude bakinsa dariya tayi ta girgixa kai baka gudun wani yashigone kallon ko a jikina yaimata ahankali taxuba masa abincin a bakinsa cikin taqama yake cin abincin yanata basarwa ya ciko cokali yanufi bakinta batada yanda xatai tabude bakinta yasaka mata ahaka dai sukaita cin abincin harya qare tabashi ruwa yasha

Yakalleta xanje wani waje nida Abbas saina dawo cikin shagwaba tace firako

Haba wane fira xani inada kamarki ba firabane sainadawo xan fadamaki har bakin kofar gidan ta rakasa tana daga masa hannu shima yana dago mata har suka daina ganin juna takoma ta hada kayan ta wanke

 

 

Wacece Huwailat waye Yusuf waye Amadu

 

 

 

 

Kubiyoni Haupha danjin wannan amsar

 

Nagode

 

Da Aurenah

 

Written by Hauwau Salisu

 

 

Page 3

 

Baxan gaji da miqa godiya ta da jinjina ga my m k ba Allah yabar tare Ameen

 

 

 

 

 

 

Huwailat Abdullahi Samaru shine cikekken sunana mahaifina Alh Abdullahi yakasance Dan Asalin garin Adamawane Wanda yawon Neman nakai yakawosa jahar Kaduna Har Allah yasa ya xauna a cikin samarun zariya inda yasamu wani Bawan Allah yabashi Shago ya dinga jire masa Dan yaga yana da Amana cikin ikon Allah kuwa akaita samun alkhairi nan da nan ko anbasa Sallamarsa bai ansa Dan Yana masa duk abun buqata da Alhajin yaga haka bayan wasu yan shekaru sai yabude wani shagon ya danqasa ga Abdullahi yace gashinan kaima katsaya da kafafuwanka kamar kowa kaje gidana Ku daidaita da Zuhra nabaka ita xaman haka nan ba Aure ya isa cikin matuqar farin ciki yai Godiya matuqa har yanajin kamar almara wai shine xai Auri Zuhra yarinya mai kyau da kamala koda yaushe cikin shigar mutunci gata da daraja manya gaskiya yayi dace Allah yasa tasosa dayafi kowa murna dajin dadin rayuwa

Abdullahi ko kana da wadda kake sone naima shigar sauri inji Alhaji Mamuda cikin washe Baki Abdullahi yace ko kadan wlh ina matuqar godiya Allah yasaka da alkhairi ya qara girma amma inba damuwa xan shirya naje can wajenmu Dan nafada masu suxo Neman Auren yaqara sunne kansa Qasa Alhaji yace ba damuwa indan wannan inka shirya kaimun magana yai godiya sosai yatashi ya tafi yana tunanin yanda xai fuskanci Zuhra da wannan almari ko xata Amince koko baxata Amince ba fargaba ta samu xuciyarsa karfa taqi yarda hakan baqaramin tada masa hankali xaiba amma dai xai jaraba xuwa anjima da dare gunta yaji ta bakinta fatansa yaji khairan daga gareta

 

Dare nayi Abdullahi ya shirya tsab yacaba kwalliyarsa ya fesa turarensa yaje gun Zuhra Dan yagabatar mata da kansa da abunda yakawosa abun farin ciki Zuhra tafada masa ita mahaifinta yafara fadamawa kafinshi kuma ta yarda ta Amince fatanta yariqeta da mutunci

Sundan taba hira yafada mata xaije garinsu Adamawa yataho da iyayensa su naima masa Aurenta taimasa fatan alkhairi suka rabu

 

Bayan sati Abdullahi yakama hanyar Adamawa ya fadama yayyensa da Mahaifiyarsa don Mahaifinsu Ya rasu sun jinjina lamarin inda suka dinga nuna masa yahakura yai Auren gida yafi yaje wata uwa duniya yai Aure ga kuma yan uwansa mata cike da gari amma saiya tsallaka wata Jaha can shidai yadinga kwatanta masu qima da darajan Alhaji Mamuda harmada son da yakema Zuhra

Akan dole suka yarda suka shiryo suka biyoshi da duk abunda yafada masu anayi na al adar samarun

Sai dai suna xuwa labarin yasha banban Dan Alhaji Mamuda yace baxai amshi komiba sai sadaki naira dubu goma wannan karamci ya birgesu sun kuma yarda da maganar Qaninsu daya fada kan Alhaji Mamuda Dan haka cikin mutunci akai komi da komi suka tsaida biki nan da sati guda kacal

 

Da daddare Alhaji Mamuda ya kira Abdullahi yatambayesa kana da inda xaka aje matarkane

Yace mun magana da Abokina Isiyaku xai nema mun gidan haya kafin nayi nawa in Allah ya hore

Alhaji Mamuda yai murmushi yace to tawa gudummuwar itace gidana dake qasan layin shagonka yasa hannu ya dauko takardun gidan yamiqa masa Allah ya Baku xaman lafiya

Kasa magana yayi Dan Alhaji ya gama masa komi ga mata ga jari ga matsugunni lallai Alhaji mutum ne harda rabinsa ma

Godiya yafara xubawa Alhaji ya dakatar dashi ya shige gida yabarsa cike da farin ciki yaje ya gwadama yan uwansa suka sake Aminta da Dan uwansu yasamu ubangida nagari mai alkhairi dabaya da qyashi

Anan suka dinga masa nasiha da kwatanci kan yariqe matarsa da qima yaqara daraja Alhaji Dan ya gama masa komi ya guji son xuciya duk da ba halinsa bane amma xuciya batada kashi

 

Ranar juma a yakamata daurin Aure bayan an sauko sallan juma a aka daura Auren

 

 

Zuhra Adamu Samaru da Angonta Abdullahi Garba Adamawa

 

 

Amarya ta tare gidanta cikin kwanciyar hankali da lumana

Ahankali Arxiqinsu keta habaka a gefe guda kuma Yakoma karatunsa inda yasamu damar shiga jami ar Xariya cikin nasara da taimakon Allah ya kammala karatunsa Sirikinsa ya nema masa aiki a cikin Zaria

Asannan Zuhra tana da yaranta Hudu Abba ne Babba Mamuda shiyaci sunan Alhaji sai Mustapha nabi masa Garba da suke cema Malam saini Autah Huwailat

Tunda nafara wayau na girma nake da burin karatu mai xurfi Dan akwai wani makwabcinmu Alhaji Sanusi Dr naji ana kiransa amma bantaba ganinsa da kayan malaman Asibitiba Dan haka nake tambayar yah Abba waishi Dr dama basaiya saka fararen kaya bane kuma ba sai yayi alluraba

Sabodame kika tambayen saboda naga Alhaji Sanusi baya sasu amma ana kiransa Dr

Dariya yayi kincika Tambaya Autar Mama Aiba dole saika karanci Likita ake kiranka Dr ba shi akan karatunsa ne yazama Dr dariya nayi to Yah Abba kenan nima xan iya xama Dr Ashe nan gaba ammafa ni nafison naxama Dr din Dalibai manya

Sanin halina da tambayoyi yasa yace to kidage xan saki makarantai kuwa

Ina gama primary naci ta kwana nan kuma Mama tace bata yardaba natafi wani uwa duniya saboda karatun boko naita kwana kodai asakemun ko kuma nabar makarantai

Da Qal akasamo min Jeka ka dawo dake nan cikin garinmu nafara xuwa

Ina Class 3 nafara samari abunda yajamun fada sosai a gidanmu Wanda har kuka yinakeyi in anamun fada

Amma duk da hakan acikin samarina ina matuqar son wani Habeeb a bayan Anguwarmu yake so tari inxani islamiyya ina kamasa yana kallona da mun hada ido xai murmushi baitaba min magana ba amma fuskansa baya raboda murmushi duk sanda muka hadu

 

Da Aurenah

 

Written By Hauwau Salisu

 

 

 

Page 4

 

 

Kullum na wuce sai nadan dakata naga ko Habeeb xai tsaidani yafadamun abunda yake boyewa amma ina baitaba hakanba wasa wasa naji kaunarsa sosai a raina

Ran wata talata danaje islamiyya nida kawayena ana maganar samari nikam murmushi kawai Nike Dan banda tacewa

Hafsat ta kalleni Huwai anya kuwa babu magana bakinki naga kinata murmushi

Bakomi kawai dai tare suka dau ihu inkunji Huwai tace kawai dai to akwai maganganu bama dayaba

Zainab tace kawai kifada mana muji abunda ke faruwa

Sanin bama boyema juna damuwa nafada masu komi akan nida Habeeb yan iskan tare suka saka ihu wlh kundace inji Hafsat

Akwai yanda xa ai Habeeb ya furta maki kalmai so kobaiso Huwai cikin murna da jin Haushin sunan da suke kirana nace tayaya kenan Zainab

Tayanda dole ya furta inkuma ba sonki yakeba xamu gane saimu sake shawara dass gabana yafadi inbai sonafa

Dana shiga damuwa kuwa Dan Habeeb kawai xuciyata ke Kauna

Zanyima Anas magana kan inason ya dinga tareki a hanyar gidansu Habeeb kuna gaisawa sannu a hankali kuna nuna ma Habeeb akwai wata a qasa sannan ke kuma ya xama dole kidaina masa murmushi koda yaimaki hakan xai sakasa tsaka mai wuya yaji gara yafada maki abunda ke damunsa kai tsaye

Wani sanyin dadi naji naratsa duk ilahirin jikina sai dai bansan a gd a lurafa Zainab kinsan su Yah Abba basa barina da saurayi

Haba Huwai kamar ba maceba kina ta bada mata

Nan suka gama caccakata muka rabu kan gobe xamu fara gwada Habeeb

 

Washe gari kau da wuri na shirya kamar yanda nasaba nafito ina xuwa anguwansu Habeeb na hango Anas xaune kan dandamalin wani gida yana latsa waya sadda kaina nayi amma kamar ance dago mukai ido hudu da Habeeb yasakar mun murmushi amma Dan cimma burina na matse na maida masa martani a xuciyata

Ina cikin tafiya naji sallamar Anas a gefena nadan waigo na dubesa naci gaba da tafiya shima yana bina a baya baifi taku biyar na isa gun Habeeb ba naja na tsaya na xubama Anas ido inasan jin meke tafe dashi

Anas ya gyara tsayuwa yace malama Huwailat kenan inata binki kina guduna bakisan abunda Allah ya tsaraba a tsakaninmuba

Dan satar kallon inda Habeeb yake nayi naga gaba daya hankalinsa akanmu yake Dan haka nasaki murmushi nace hakane

Malama Huwailat Tun randa nadora idanuna akanki naji sonki ya shiga xuciyata inata maki hannunka mai sanda kinki ganewa Dan haka nake gudun kada wani yaimun kafa naxo gareki da qoqon barana

Abaxata mukaji tari ya turnuke wani muduka muka waiga saiga Habeeb yanata tari damm gabana yafadi

Miyasaka Habeeb kwarewa haka banda amsar tambayana Dan haka na dubi Anas nace kai hakuri sainayi shawara nayi gaba abuna

Tun daga nesa su Hafsat ke mun dariya Dan haka ina isa na banka masu harara na shige get din islamiyyar

Sanin hali yasa suka biyoni suna guntse dariyansu wai wane iskanci ne haka xaku sakamun dariya daga xuwana

Bafa dake mukeba dafa Habeeb muke munsan saiya afka tashin hankali yaganki dawani

Hmm yan iska nan dai nabasu labarin abunda yafaru suka saka ihu dama munsan xa a rina Kawata kinci gari

To idan antashima Anas xai rakaki gida cikin dariya nace bansan iskanci sokuke Ku kashemunshi ne

Ohhh kaga farin shigan love fa to ai duk cikin kankaro maki sone kawai kedai muje xuwa

Haka kuwa akayi muka jero muka tafo nida Anas Yanaban labarin yanda yake matuqar Qaunar Zainab inata murmushi Dan sun birgeni dago idon daxan muka hada ido da Habeeb ya hade rai yayi kicin kicin abunsa kamar xai fashe na matse naikamar bangansaba muka rabasa muka wuce yabimu da kallo rai bace nace bakai taurin kaiba yanxu akafara axuciyana nayi wannan furucin

Tun daga nan Sai Habeeb ya tsiri yimun Sallama idan xan wuce nikam na ansa naqara gaba inkuwa yaganni da Anas saiyaita baqin rai yana maxurai ko Anas yai masa sallama bai ansawa

 

Ran wata juma a narakosu Hafsat sunxo duba mama bata lafiya muna tafe muna labarin Habeeb yacika xurfin ciki kawai muka tsinkayi muryansa yana sallama ya dubi Zainab yace malama nadan ganki mana inba damuwa

Bansan yanda ake samun faduwar gabar baxataba sai a lokacin karfa Habeeb yace yanason Zainab cab Dana shiga Tara ni Huwailat

Inaji inagani Zainab ta ware da Wanda nake kauna dare da rana mukai gaba muka barsu baya suna tattaunawa

Hafsat tadubeni karda kidamu insha Allahu xamuji alkhairi kidaina damuwa yake naimata kawai amma banda bakin magana

Wasa wasa mukai nisa ba Zainab ba labarinta wani xaxxafan Hawaye naji a gurbin idanuna cikin dabara na goge kada Hafsat ta gani

Can saimukaji Zainab na kwadamana kira damm gabana ya buga tana xuwa ta rumgume Hafsat tace nayi sabon kamu qawayena tabbas wannan yafi Anas Dan haka nayi mijin baxatani

Yasalam tafaru ta qare kenan ni Huwailat narasa Wanda nakeso sai hawaye sharrr

Cikin tashin hankali suka dubeni lafiya Huwailat

Bakomi kawai dai

Kawai dai me ko kina mun jin xafin samun saurayi Dan unguwarkune Huwai

Gaba nayi kawai nabarsu agun sunata faman kwadamun kira nai kunnen uwar shegu dasu

Ko a class ban yarda na xauna waje guda dasuba Sam har aka tashi nakamo hanyar gida dai dai inda muka saba rabuwa Zainab taban takarda gashi Huwai kimaida masa tunda naga baki amince dashiba amma kifara karantawa nagode da nuna mun jin xafi Huwai

Nai tsaye da takarda a hannuna na dai lallaba natafi yau banma ga Habeeb ba nace taya daman xan gansa tunda ya isar da saqonsa ga wadda yake mawa nikuma awa yanxu

Ina shiga gida nafada dakina na rike takarda ina tunanin nabude ko karna bude

 

 

Tofa koyaya xata kaya kenan

 

Shin da gaske Habeeb Zainab take so

 

Miye a cikin takardai da Habeeb yaba Zainab

 

Anya kuwa Huwailat xata iya karanta takardai

 

Duk kubiyo Haupha danjin amsarku

Nagode

Da Aurenah

 

 

 

Written By Hauwau Salisu

 

Page 5

 

 

Juya takardai naitayi a hannuna na gaxa budeta sai nayi kamar xan bude sai naji wata matsiyar karaya saina fasa

Karshe dai na hankada katifata na jefata na kwanta nai lub

Baqaramin daurewa nayi ba danaji kiran da Mama kemunba na tattaro duk wata jarumta nasaka nafita gun mamar

Kallo daya taimun tafara jeromin tambayoyi dama baki lafiya kikai shiru Auta

Ban hanaki xama da ciwoba batare da kinsanarmunba

Yaushe xaki daina wannan sokoncinne wai to bari yayanku yashigo yakaiki chemist adubaki

Nidai da ido nabita Dan nasan ko munje bai isa yagano ciwonaba inba fada masa nayiba

Magana nake maki Auta mike damunki ne kaina kemun ciwo mama nasha magani a makaranta

To kici abinci kije ki kwanta Allah ya sawaqe dako naso in aikeki gidansu Hajiya Abida ki kaimun kudin Adashina idan ba gixo kunne na kemunba gidansu Habeeb kenan wajen mamansu kenan ai koda gaske ban lafiya ba abunda xai hanani rarrafawa kodan naga Habeeb Dan haka nai gaggawan janyo hijab dina dake kan tagar Mama nace kawo na miqa mata ai kusane mama cikin sa a kuwa ta miqomin kudin na karba na fita

Tun daga kofar gidanmu nake hangen kofar gidansu Habeeb naga koxan gansa inda yasaba xama amma babushi ba alamarsa

Sosai naji ba dadi a raina harnaji daman ban anso saqonba na kwanta jinyar xuciyata a haka har nashige gidan nai sallama Qanwarsa Fatima ta ansamun natambayeta mamarsu tace tana ciki na jira taimata magana

Haka na xauna inata raba idanu ina qarema gidan kallo na gadai dakin mamarsu da sashen Babansu sai wani bangare danake tunanin ko shine bangarensu Habeeb Dan yana da Yayansa guda Daya Suleman duk da niban sanshiba wai soja ne yana can gun aikinsa

Inacan inata tunani naji Muryan Mamarsu namun maraba banda abunki Huwailat basaiki shiga daga cikiba in itabatai hankalin cemaki kishigaba

Murmusawa nayi bakomi Hajiya dama mamane taban sako nakawo namika mata kudin ta ansa ta kirga tace kigaidamun ita sosai nace xataji sai anjima

Nafito xuciyata fal takaici banko kallon gabana naji nayi karo da mutum gaba daya naji na afka masa munyi baya munfada ma bango ina kwance kan kirjinsa yasaka duka hannayensa biyu yaxagayemun kugu dasu

Matsanan ciyar kunya tahana nadago fuskana naga waye wannan sannan miyasaka ya qisakina koya tureni nafadi dan nicena fito ban kallon gabana natafi duniyar tunanin Mutumin da keson Qawata baniba

Sharr hawaye suka xubo fuskana abunda yaxaja dagomin Fuska dayayi waxan gani

Habeeb ne Ashe yakalleni sosai ya girgixa kai yasaka hannu yasharemun hawayena kidinga kallon gabanki idan kina tafiya

Yajanyeni daga jikinsa ya shige cikin gidan

Ya salam so cutane jinai tamkar karda yadaina mun magana Ashe haka yakeda murya mai sanyi tab Zainab ta cuceni cikin damuwa na taka na fita daga gidan xuciya cunkushe da abubuwa da dama

Allah yataimakeni ba kowa tsakar gidan na shige dakina nadasa sabon kuka tamkar wadda akaima shegen duka har na tsawon lokaci kana na dangana najawo later nan nakasa budewa na maidata

Wasa wasa nashiga damuwa ko a makaranta inna hadudasu Hafsat ba kalan tambayan dabasamun amsar dayace banda lafiya

Zainab kuwa jinake tamkar na yanke duk wata alaqa da ita Dan itace taimun Katanga da Habeeb aganina dabata xan iya janyo hankalinsa guna yanxufa

Dan haka nake mata shaqe shaqe danma yar iskai ko a jikinta take nunamin bata damuba da duk abinda nake mata

 

 

Kamar yau nafito da niyyar xuwa gidansu Hafsat kawai na hango Habeeb dawata yarinya sunata dariya cikin tsananin kaduwa na qara matsawa inga wace mai sa arce haka tasamu Habeeb yaketa nishadi tare da ita abaxata naga Zainab ce Kawata tashin hankali da gaske Habeeb da Zainab soyayya suke yaxama dole nayi bankwana da sonka Habeeb nabarma Zainab kai koda hakan xaisaka narasa farin cikina

Cikin dauriya na qarasa nasakarma Zainab yake Dan ba murmushi bane nace yan mata daga ina tai dariya tace gunki xani sai nahadu da Yallabai ancemun jiya yaje gida bannan ina gidansu Aunty salma time din

Share maganai nayi Dan batada amfani guna nikam gidansu Hafsat xani ina fada ina barin wajen tare da mamakin Habeeb ko kallo ban isheshiba

Sanin batsayawa xanba yasa Zainab biyoni harda Dan gudunta ina juyawa naga Habeeb bayanta kawai yake kallo murmushi kwance a fuskansa

Cikin dakewa nace kefa banxace kuna magana xaki tafi kibarsa

Dariya tayi aiyace xaixo anjima gida yasameni ninai daman ban mata maganaba

Ahakadai muka qarasa gidansu Hafsat ita kadai keta xubarta nikam ciwon kaima labarin kesani wai Habeeb mutumin kirki ne yana da hankali ga natsuwa kai nashigesu ni Huwailat

Acanma haka sukaita labarinsu bana fahimta har muka fito kowa ya kama gabansa nikam na yi danasanin fitowata yafi dubu a ranai

Jarabawanmu ta fito ta J S C E naci boarding school dake hanyar abuja wato madallah baqamin murna nayiba

Sai dai su yah Abba sunce ba wannan maganar nasa kuka na kama kafar mama Dan Allah kinga yanxu na girma aji hudu xanifa bakamar wancan karan daxani daya ba

Baba dake gefe yace kiyi shiru indai makarantar kwanace kinje kingama Auta

Dadi naji sosai Dan kobanxa xan daina ganin Habeeb da Zainab Dan haka baki alaikum naita shirye shiryen tafiyana banfadama kowa a cikin kawayenaba

Ranai daxan tafi na je kofar gidansu Habeeb Dan masa kallon bankwana kallon karshe inafatan sanda xan dawo na manta dashi a rayuwata kwata kwata

Yana zaune yanata karanta wata later yana murmushi nasan ta zainab cema yake karantawa ina hangosa ya dauko Biro shima yafara rubuta wata

Cikin xubar hawaye nabar gun nakoma gida na iske yah Abba najirana mutafi

Saboda abunda nagani yasa nafashe da kuka sosai na rumgume Mama ina kuka na gaske Dan xuciyata ciwo take mun sosai da qal mama ta lallasheni na bi yah Abba muka tafi

 

Har makaranta yakaini yaban kudi yaimun bankwana yatafi gida

Hostel dinda aka kaini nabi da kallo kamar yanda yan hostel din suka Bini da kallo Allah sarki Zainab da Hafsat kuyi hakuri na karya alqawarinmu nabarku natafi wata makarantar Dan samun lafiya ga xuciyata dataki Zainab

Sai Hawaye Sharr baxata naji sunsa ihu new new tab harma kin daina da haka muka fara muma nan inji wata dake kusa dani kallonsu kawai nayi na lafe kan katifata

 

Ahaka dai naci gaba da rayuwa a makarantar ba laifi inaganewa sannan nayi sabbin qawaye Asmau da Aisha sai dai bantaba mantawa da tunanin Habeeb ba a kowace rana saina tuna dashi sosai

 

 

 

Samarun zariya bayan tafiyar Huwailat makaranta

 

 

 

Yau sati biyu kenan baiga ta wuceba bayan yaga ankoma makaranta yasan kuma bata wasa da karatunta ko makara batayi to mike faruwane da ita karfa ace dammm gabansa ya fadi hakan baxai faruba insha Allah

Nasan Allah xai mallakamun ita taxama uwa ga yarana mata gareni suruka ga Hajiyanmu kawai yasaki murmushi xai bincika yaji abunda yake hanata fitowa da xuwa makaranta yauba sai gobeba insha Allah

Aranai qagara yayi dare yayi yaje gidansu Zainab danjin abunda yake buqata shiyasan wadannan kwanakin Sam baida walwala sannan baida kuxari damuwa na shinfide a xuciyarsa wadda harta fara bayyana kanta ba shakka ba qaramin so yake mataba yarinyai nan

 

Dare nayi yaje gidansu Zainab akafada masa batanan taje Hutu garinsu Mamanta rai bace yadawo gida yarasa abunda ke masa dadi

Washe gari yana xaune yana Dan kullum din yaga Hafsat tafito daga gidansu Huwailat kamar hawayema take indai idansa ba gixo yake masaba cikin karfin hali yanufeta yajefa mata tambayar ina qawaiki kwana da yawa bana ganinta

Rushewa da kuka Hafsat tayi tasake riqe wata later gam dake hannunta tana girgixa kanta

Xufa ta yanko masa ta ko ina shin miya farune Hafsat ina Huwailat din bata lafiyane kinyi shiru kiban amsa

Takardai ta miqa masa tayi tafiyarta idan yakulama kamar hararansa take Hafsat din baibi takaiba burinsa yaga meke cikin takardai dayasaka Hafsat kuka

 

To masu karatu miye a cikin takar dai

 

Shin Huwailat ta manta da Habeeb kuwa

 

Zainab da gaske soyayya ce suke da Habeeb

 

Miya saka Hafsat kuka a gidansu Huwailat

 

About the author

Hausa_Novels

Leave a Comment