Littafan Hausa Novels

Burin Rai Hausa Novel Complete

Written by Hausa_Novels

Burin Rai Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

BURIN RAI

 

 

Alƙalamin

 

_*Zainab Muhammad (Indian Girl)*_

 

 

Littafin kuɗi ne

 

 

*NOTE*

_Wannan littafi mai suna *BURIN RAI* littafi ne da zai ƙayatar kuma ya nishaɗantar ya faɗakar, littafi ne mai cike da tausayi,makirci,soyayya da dai sauran su ku dai ka wai ku biyo ni muje cikin labarin_

 

 

*GARGAƊI*

 

_Ban yadda wani ko wata su yi amfani da wani sassa na labari na ba ba tare da izinin na, idan ba haka ba kuwa wallahi! Wallahi!! Wallahi!!! Ubangiji yana kallon ku kuma shi zai ɗaukar min fansa_

 

 

 

P1⃣-2⃣

 

“Ya Ashraf mene yasa ba zaka so ni ba? Ban isa ka so ni bane? Ko kuwa ban da abinda zaka so ni? Ya Ashraf mene aibu na ka faɗa min domin na sani”

 

Magana take cikin kuka mai taɓa rai da zuciya.

 

Cikin tsana ya dube ta kafin, Ya ce”Bana ƙaunarki Ashna na tsane ki bana ko ƙaunar ganinki, tsanar da nai miki mai muni ce wadda kwakwalwa ba zata iya ganewa ba Ashna …”

Rayuwata Hausa Novels Complete

Da sauri Ashna ta katse Ashraf daga cigaba da faɗar waɗannan munanan kalaman a gare ta, me yasa baya sonta ko dai ita mummuna ce? Taiwa kanta tambayar tana kuka ya yin da ta toshe duka kunnuwanta da tafukan hannayenta.

 

Cikin kuka mai shashsheƙa Ashna, Ta ce”Ya Ashraf naji ka tsane ni amma to meyasa ba zaka iya aure na ba duk da ka tsane ni? Ya Ashraf wallahi idan har ka aure ni zan iya jure duk wani wulaƙanci da cin kashi. Ya Ashraf kai ne *BURIN RAI* na”

 

Marin da Ashraf ya wanke ta da shi sai da taga wasu taurari masu wuta, tsayawa kukanta ya yi ta zuba masa ido tana kallonsa fuskarta kuwa inda ya mareta har ya yi ja abinka da farar fata.

 

“Daƙiƙiya wawiya shashasha kawai mtssss”

 

Ya ƙarasa maganar da jan tsaki tare da shigewa ya bar wajan.

 

A guje itama ta wuce zuwa sashin su tana rusa kuka, mahaifiyarta dake kitchen ta ganta da ido ta bita tana mai tambayar kanta me kuma akaiwa Ashna.

 

Ɗakinta ta nufa tana shiga ta faɗa gatonta tana mai cigaba da kukan.

 

Mahaifiyar ta ajiye aikin da take ta nufi ɗakin nata dan jin meya sameta.

 

Tun da ta tunkari ɗakin ta fara jiyo kukanta domin iya ƙarfinta take kukan, tura ƙofar ta yi bakinta ɗauke da sallama ta shiga ɗakin.

 

Zama ta yi bakin gadon tare da taɓa bayan Ashna kafin, Ta ce”Ashna lafiya meya same ki kika shigo kina kuka haka? Ko wani ne ya rasu?”

 

Shuru Ashna ta yi ba tai magana ba sai kukanta da ta cigaba da yi.

 

“Wai Ashna ba magana nake miki ba iyye ki kai min shuru?’

 

Mahaifiyar Ashna ta faɗa tana kallonta.

 

A hankali Ashna ta miƙe zaune kafin ta ɗaga jajayan idanunta da suka rune lokaci ɗaya, Ta ce”Mammy mene aibuna? Bani da kyau ne? Ko bana da hali me kyau? Ni ba…”

 

 

“Kinga dalla rufe min baki, wannan wane irin abu ne na tambayeki kina tambayata? To ma wai me ya kawo duk waɗannan tambayoyin?”

 

Mammy ta katse Ashna daga waɗannan magan ganun nata marasa kan gado.

 

Cikin kuka Ashna Ta ce”Mammy Ya Ashraf ne yace ya tsaneni baya ƙaunata da duk wani mai ƙaunata, Mammy mena rasa da yai min wannan tsanar?”

 

Wani irin takaici ya kama Mammy tai tsaki sannan, Ta ce”To sai me dan Ashraf yace baya sonki dama ana soyayya dole iyye, kinga! Kinga!! Kinga!!! Ashna ki fita idona na rufe”

 

Ashna ta kalli Mammy a shagwaɓe da, Ce wa”Mammy Allah ni ina son sa kuma ba zan iya son kowa bayan sa ba Mammy dan Allah ki faɗawa Daddy ku aura min shi”

 

Baki Mammy ta saki tana kallon Ashna, wai yau Ashna ɗinta ce take wannan maganar cabɗi abin babba ne *BURIN RAI* akwai shi da girma.

 

 

 

 

 

******

“Na kira wayarka a kashe ina kaje”

 

Sautin maganar ya fito ta cikin wayar zuwa cikin kunna sa.

 

Cikin sanyin murya, Ya ce”Neema wallahi na ɗan fita ne na bar wayar kuma a ɗaki”

 

Wani dogon tsaki Neema taja kafin, Ta ce”Dama ai dan ka wulaƙanta ni yasa ka bar wayar a ɗaki nai ta kira ba a ɗaga ba”

 

“Sorry Baby kin san ba zan taɓa wulaƙanta ki ba”

 

Ashraf ya faɗa a marairaice.

 

 

Tsaki Neema taja kafin ta kashe wayar.

 

Hankalin Ashraf ya tashi ganin ta kashe wayar, da sauri ya aje wayar ya faɗa toilet a guruje yai wanka ya fito ya shirya cikin wani black boyel mai kyau.

 

Wayarsa ya ɗauka ya fice daga ɗakin yana sauri.

 

 

“Kai Ashraf ina zuwa haka kake wannan saurin?”

 

Ammy da take saukowa daga bene ta faɗa.

 

Cak Ashraf yaja ya tsaya kafin ya juyo ya kalleta, Ya ce”Ammy wallahi zani gidan su Neema ne muna wayata kashe min”

 

Ammy da ta ƙarasa saukowa daga steps ɗin benan ta faɗa.

 

Ta ce”Tofa akan wannan dalilin zaka?”

 

“Ammy fushi fa tai”

 

Ashraf yai maganar kamar zai kuka.

 

Jirgiza kai kawai Ammy tayi kafin, Ta ce”Allah ya kyauta, sai ka dawo”

 

Yana jin Ammy ya fice daga falon kai tsaye wajan aje motoci ya nufa ya shiga tare da mata key ya nufi get mai gadi ya buɗe masa ya fice.

 

Tuƙi yake yana da ɗa dialing numer ta amma taƙi ɗagawa ƙarshe ma kashe wayar tai gaba ɗaya.

 

Paking ya yi lokacin daya iso ƙofar gidan su Neema, fitowa ya jingina da motarsa yana neman yaron da zai aika gidan dan a kira masa ita.

 

Wani yaro ne ya fito daga gidan da sauri Ashraf ya tare shi tare da aika shi ya kira masa Neema kafin ya koma ya jin gina da motar yana jiran fitowar yaron.

 

Da sallama yaron ya shiga gidan, mahaifiyar Neema dake tsakar gida tana hura gawayi ta amsa sallamar da.

 

Ta ce”A’a Sadik ya kuma ka dawo ina aiken?”

 

Sadik Ya ce”Umma wai ana sallama da Anty Neema inji wannan me motar”

 

Umma da sauri Ta ce”Allah da gaske kake Sadik?”

 

“Allah kuwa Umma shine”

 

Sadik ya faɗa.

 

Kira Umma ta shiga kwallawa Neema dake ɗaki wadda duk abinda ake tana jiyowa.

 

Miƙewa tai tana dariya mugunta kafin, Ta ce”Ashraf kenan in dai Neema ce ka shigo hannu”

 

Gama faɗar hakan ke da wuya ta fito tsakar gida.

 

Ta ce”Umma gani”

 

Cikin zumuɗi Umma Ta ce”Ke maza kije waje wannan yaron mai mota ya zo, yau Allah ya yi da rabon za muci abinci da nama kai Sadik je kace gata nan”

 

Haɗe rai kafin Ta ce”Umma nifa babu inda zani dan haka yai tafiyarsa ma”

 

Umma ta banka mata harara da, Ce wa”Wallahi sai kin fita dan baƙin ciki”

 

Neema ta shiga zumɓure zumɓure.

 

“Zaki wuce ki fita ko sai na jofo miki wannan maficin?’

 

Umma ta sake faɗa da tsawa.

 

Da sauri Neema tai soro tana dire dire duk da babu mayafi a jikinta ga ɗinkin irin mai banka ɗar nan ne.

 

“Au haka zaki fita babu mayafi? Koda yake jeki ni dai ki samo mana na cin nama”

 

Umma ta faɗa tana yashe baki.

 

Da sauri ya nufo ƙofar gidan yana ganin Neema ta fito, ja tai ta tsaya tare da riƙe ƙofar tana jifansa da wani wulaƙantaccan kallo.

 

Cikin harara tace da shi, “Lafiya malam meya kawo ka ƙofar gidan mu?”

 

“Neema meyasa zaki min haka ki kashe waya alhalin banji kin ce kin haƙura ba?”

 

Ashraf ya faɗa cikin rauni.

 

Hannu Neema ta ɗaga ta wanke shi da wani lafiyayyan mari kafin ta fara magana…

 

 

 

 

_Indian Girl Ce_

About the author

Hausa_Novels

Leave a Comment