Buri Uku Hausa Novel Complete
Buri Uku Hausa Novel Complete
*Rasheedat Usman*
_(Ummu Nasmah)_
*بسم الله الر حمن الر حيم*
“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`
*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻
**
*Paid Book*
Godiya ga Allah madaukakin sarki da ya bani ikon samun damar rubuta wannan labarin, tsira da aminci su tabbata ga cika makin Annabawa Muhammad (SAW) har izuwa iyalan gidansa da Sahabbansa, Allah ya bani ikon rubuta dai-dai abinda zamu amfani gaba ɗaya.
Mahaukaci ne ko aljani Hausa Novel Complete
SADAUKARWA
*Ga Ahalina GIDAN SHANU DUTSE ina matuƙar alfahari gareku.*
GODIYA TA MUSAMMAN
*Ga Kakana farin cikina Alhaji Babba, gidan shanu Allah ya jiƙansa da rahama ya yafe masa kurakuransa yasa mutuwa ta kasance hutu a garesa.*
_*MARUBUCIYAR*_
-Nasmah Ko Nasirah.
-Sauyin Rayuwa.
-Sara Da Sassaqa.
-Akan Ƴar Uwata.
-Indo A Birni.
-So Bai San Jini Ba.
-Hatsabibiya Saude.
-Ruɗanin Zuciya Biyu.
-Doctor Hassan.
-Ƙauyen Mu
-Gelle Bingel.
-Aminaina Ko Ita?
-Ƙullalliya.
-Jalala.
*Tsokaci*
Ƙagaggen Labari ne banyi sa dan cin mutuncin kowa ba, idan kinga/kaga yazo dai-dai da yanayin rayuwarka ko halinki labari ne yazo da haka.
*Gargaɗi*
A guji juya min littafi ta ko wacce siga ba tare da izini na ba ƴan You Tube a kiyaye, yin hakan kuskure ne kuma zan iya ɗaukar mummunan mataki.
Gareku ɓarayin fasaha wadanda bakwa ramin kanku sai wani yasha wahalar haƙar nasa ku afka, to ku fita daga idona na rufe duk shegiyar yarinyar da ta kuma shiga gonata, tabbas sai na yi fatale da ita, a kiyaye kowa ya iya allonsa ya wanke IDAN KUNNE YAJI……..
*Page 1*
“Lubna ita fa Nakasa ba Kasawa bane! Meye aibun Ahmad dan yace yana sonki ko na kasarsa itace Aibun nasa, ko shi ya halicci kansa? Saboda yace yana sonki shine zaki wulaƙanta sa? Kifa ji tsoron Allah Lubna banga laifin sa ba dan yace yana………….”
Wani irin matsiyacin kallo Lubna ta jefawa Samra bakinta ta taɓe tare da zubar da miyau cikin ƙyama da jin ƙunar maganar Samra Lubna tace.
“Ya isa haka Samra kunnena ya fara gajiya da jin waɗannan baƙaƙen kalaman naki marassa daɗin sauraro!! Allah ya tsari gatari Noma!! Dubeni da kyau sama da ƙasa Samra kinsan ko da girgije kurna tafi magarya zaƙi, ni kalar matar manya ne, ba wani can matsiyaci nakasashe mai dattin riga da hula ba irin Ahmad, Yes Ahmad yana da aibu masu tarin yawa, mai ake da talaka matsiyaci nakasashe, Allah ya tsareni Auren tsiya Auren Wahala, Allah wadaran Auren talauci kinfi kowa sanin ni macece da nake da BURI UKU a Rayuwata kuma sai na kai gaci, komai rintsi komai wahala!! Ko da tsiya kai ko ana Ruwa ana iska komai rintsi sai na cika BURI UKU na.”
Numfashi Samra ta saki tare da girgiza kanta tana kallon Yadda Lubna ke magana cikin izza da taƙama tamkar ƴar shugaban ƙasa, murmushi ta saki zaman ta, ta gyara kafin tace.
“Hmmm! Lubna ki lura da kyau so da yawa abubuwan da muke so, mukafi kwallafa rai dasu sunfi wahalar damu a rayuwa.. sunfi mana wahalar samu.. Kuma sunfi nisa damu, A da ne ake cewa duk abinda mutum ke yi kar ya gaji har sai ya cimma gaci!! A yanzu kuwa ba’a a ɓata lokaci wurin tsayawa tsintar duk abinda ya suɓuce da gangan, dai-dai ruwa dai-dai tsaki, the more ka na kara nisa the more kana ƙara haɗuwa da abun da ka baro a baya. Hmmm!! Ita fa wannan rayuwar tamkar haƙar rijiya ce, ba dole sai an samu ruwa a haƙa ɗaya ba, idan ka tona kaga babu ruwa, ka sauƙaƙawa kanka ta hanyar rufewa sai ka sake Sabuwar haƙa duk dai burin shine a samu ruwa, ba’a taɓa samun nasara a cikin tozarci, ka bawa kowa darajar da Allah ya basa da nakasashe da lafiyayye duka abu guda ne a wajen Ubangiji, ya duka ya halicce mu ne domin mu bautata masa, wanda ya halicce mu ma bai banbanta mu ba akan me mu zamu banbanta kanmu, ki daina kai kanki inda Allah bai kaiki ba, dole ne ƘWARYA TABI ƘWARYA Lubna.”
Dariya sosai Lubna tasa kafin ta tsagaita da dariyar tace.
“Wannan ai Ahmad ɗin zaki faɗawa ba ni ba, shike ƙoƙarin haƙawa kansa rijiyar da bazata taɓa kawo masa ruwa ba, ki sanar dashi ya sauya haƙa wataƙila ya samu ruwan ga sabuwar haƙar sa, Samra bana ƙaunar Ahmad na tsanesa!! Bazan taɓa son shi ba har abada wallahi na fi ƙarfin Matsiyaci nakasashe irin Ahmad , TAHIR ALBURAWI shine muradin rayuwata, shahararren jarumin da ya yi ƙaurin suna a duniya bama ƙasarsa ba, attajirin da za’a kirasa lamba na biyu a cikin Nigeria, shi nake da BURIN mallaka, ba matsiyaci irin Ahmad ba wanda bai kashe yunwar cikinsa ba, bare ya fara tunanin kashe na wani.”
“Hmm! Lallai iska yana wahalar da mai kayan kara, TAHIR ALBURAWI shine kike Burin Aura ta yaya zaki fara ganinsa bare ki fara tunanin soyayya tsakanin ku har kuma ta kaiku ga Aure, inuwar Tahir kin isa ki tsaya wajen bare kuma har ki fara tunanin soyayya tsakanin ku hmmm!! Lallai kin ɗauki Dala ba gammo a kanki Lubna.”
Samra tayi Maganar tana jan doguwar tsuka, Goggo da ke gefensu zaune ne tace.
“Allah ya miki albarka Samira ke da kike da hankali kenan, amma da shike ita Lubabatu sheɗan ya mata huɗuba a kanta, kinji ai dogon burin da bazai taɓa cika ba ta ɗauka, Allah ya shiryeki Lubabatu ki gane Annabi ya faku, ki dai yiwa kanki faɗa ki fitar da miji ki rufawa kanki asiri Astagafurullah!! Tsayayyen saurayin ma ai bakin halinki ya hanaka samu, tunda kinki talakawa Yan uwanki, shi Ahmad ɗin ma da kika raina ai shine yazo ya shinshinaki kowa kika fitsare guduwa yake, shine kawai ya tsaya kai da fata zai aureki, amma ki mutstsike idanunki kice ke kinfi karfinsa, butulu kawai.”
Goggo tayi Maganar cikin faɗa, tura bakinta Lubna tayi tace.
“Haba Goggo ina ruwanki a cikin Maganar mu, haka kawai ki sanya mana baki tsofai tsofai da ke, gaskiya wannan ba dai-dai bane, Samra tashi mu tafi, ba duk kune kuka sani cikin wannan ƙaskantacciyar rayuwar ba ta takaici, ni wallahi da ba’a haifeni ta tsaginku ba, ina ma laifin ace ko ɗan gidan masu rufin asiri a jefani amma a sai na fado a wannan gidan baƙin talaucin tirr mummunan kaddara.”
Tayi Maganar tana jawo hannun Samra miƙewa Samra tayi cikin rashin jin daɗin maganar Lubna suka fice daga ƙaramin ɗakin nata, bakinta Goggo ta taɓe cikin zuciyarta tana yiwa Lubna fatan shiriya, a zauren gidan sukayi sallama da Lubna, Samra ta tafi nasu gidan, cike da rashin jin daɗin maganganun ƙawarta duk taso mata magana akan wannan maganar da ta faɗawa goggo, sai kuma tayi shiru kawai, Lubna kuma ta koma ciki tana kunƙuni.
Tunda Samra ta shiga cikin ɗakin su babu abinda take sai nazari da lissafin maganganun Lubna TAHIR ALBURAWI _anya kuwa Lubna tana da hankali tasan abinda take faɗi kuwa, idan har TAHIR ALBURAWI shi ne mijin da ta ke son aure tabbas zata mutu batayi Aure ba, ina zata fara haduwa dashi har ta samu dama, Hmm! Ko inuwarsa zaiyi wahala Ace Lubna ta gani bare kuma shi da kansa Allah buwayi gagara misali Allah ka dawo min da Aminiyata cikin hayyacinta domin da alamu ta dauko hanyar da zata wahalar da ita_ Tayi Maganar zucin tana taɓe bakinta tare da jingina jikinta da bango muryar Inna Rahaina taji tana doko mata kira, wani irin bugawa ƙirjinta yayi, hankalinta ya tashi runtse idanunta tayi tana jin yadda sautin kiran da Inna Rahaina ke mata, yake dukan ma’aunin da ke tantance jin kunnenta, tabbas wannan kiran bana lafiya ba ne babu shakka yau tasan kashinta ya bushe a hannun Inna Rahaina, cikin gajiyayyiyar muryarta mai ɗauke da Amon tsoro ta amsa jiki na ɓari, daƙyar sawunta suka samu damar miƙewa ta fito waje cikin nauyin jiki da bugun zuciya, daga nesa da Inna Rahaina ta tsaya cikin sanyin murya tace.
“Inna gani.”
“Inna gani! Ni ce zan matso kusa da ke dan kutumar ubanki, shegiya matsiyaciya mai tujajajjen ido, ki matso nan gabana ko na ƙariso na karya miki ƙafa shasha wawiya.”
Hawaye ne masu ɗumi suka gangaro idanun Samra, jiki na ɓari ta ƙariso gaban Inna Rahaina ta sunkuya kafin tayi magana taji saukar rankwashi a kanta, runtse idanunta tayi tana jin azabar ranƙwashin na shiga har cikin kwakwalwarta cikin faɗa Inna Rahaina ta hau cewa.
“Dan bura’ubanki gidan uban waye kikaje kika barni da aiki a cikin gidan nan, kin tafi yawon gantalin naki na bin maza da kika saba ko, shegiya jarababbiya wace ta biyo uwarta, wacce irin jaraba ce uwarki bata gwadawa malam ba, kullum ta zugen wandonsa na sunce tsabar jarabar uwarki, shine ke kikaje kikayi gadon tsiya, to ahir ɗinki da barina da aiki dan uwarki, kuma wallahi yau ke da wancan daujajjen ɗan uwan naki baku da abinci a cikin gidan nan, naga shegen da ya shiga min madafi ya ɗauki abinci yaga yadda zanyi dashi.”
Wani irin tsinkewa zuciyar ta yayi cikin rawar baki da tausayin Nuruddeen tace.
“Dan girman Allah Inna Rahaina kiyi haƙuri, karki hana Nuruddeen Abinci, wallahi babu inda naje gidan su Lubna kawai naje, kafin na fita na dubaki ban ganki ba, banga kuma anyi cefene ba shi yasa nayi zaton yau ba girki, ki yafe min dan Allah ki bawa Nuruddeen abinci ko ni baki bani ba.”
“Babu wanda zan bawa a cikin ku kuma banga uban da zaisa na baku ba koda kuwa uban naku, ki tashi ki bani waje.”
“Inna Rahaina please dan Allah kiyi haƙuri.”
Bangajeta Inna Rahaina tayi tana jan tsuka ta shige ta barta a wajen, idanunta Samra ta runtse tare da mikewa cike da baƙin ciki da kuncin rayuwa, ko kaɗan bata jin daɗin zama da matar mahaifin nata tunda mahaifiyarta ta rasu farin cikin ta ya gushe idan har tayi dariya to ba’a cikin gidan ba ne, zauren gidan ta fito tana leken inda zata ga Nuruddeen, can ta hangosa kusa da musa mai sai da rake a ƙofar gidan nasu, kiransa tayi ya taho da gudu duk da Nuruddeen yaro ne da bazai wuce 11yrs ba yana da wayo sosai tsayawa yayi a gabanta yace.
“Adda gani.”
“Nuruddeen me kakeyi acan ɗin.?”
“Adda rake muke fere masa sai ya bamu ishirin ishirin.”
“Meyasa yau baka tafi Islam ba.”?
“Adda to Baba bai ba ni kuɗin satin ba yace sai yau idan ya dawo na haƙura da zuwa yau sai gobe idan ya bani sai naje.”
“Shikenan yau ba abinci maza kaje wajen Lubna kace ta baka abinci taci nasan zuwa yanzu sun gama girki.”
“Ba abinci kuma Adda bayan naga Inna Rahaina tayi shinkafa da miya ɗazu Aliyu ya fito dashi yana ci.”
“Hmmm!!! Nuruddeen kaje kawai ka amsa a can ɗin bana son yawan magana.”
“To Adda zanje.”
Yayi Maganar yana Kada kansa tare da juyawa da kallon tausayi take bin ɗan uwan nata yaro karami zai tashi cikin wahalar rayuwa _Allah ka mana sauyin wannan rayuwar ko albarkacin wannan yaron da baisan komai ba_ tayi addu’ar cikin zuciyarta tana komawa cikin gidan.
********
“Ahmad wai ina zamuje ne ba dai gidan su wannan yarinyar marar mutuncin zamu koma ba ko.”?
Golding eyes ɗinsa ya ɗago masu kalar ruwan zaiba ya kalli Mujahid gurgu ɗan uwansa wanda Allah ya jarrabesu da Rashin ƙafar da zasu tsaya a kanta su taka ƙasa, kyakkyawan Mutum matsalar sa ɗaya itace gurgunta fari ne sol mai kyakkyawar fuska wanda saje ya yiwa fuskar kawanya, duk da rashin gyara da rashin samun kulawa da bayayi amma hakan bai hana kyawun fuskarsa bayyana ba.
“Hmmm!! Can ɗin dai zamu je Mujahid.”
Ɗan zaro idanunsa Mujahid yayi alamun firgita, murmushi Ahmad yayi ganin yadda abokinsa Mujahid ya zaro idanunsa yace.
“Ya naga kamar ka tsorata daga cewa can zamuje.”?
“To ai dole na firgita Ahmad, wai kai baka da zuciya ne Ahmad meyasa bazaka gujewa inda ba’a ƙaunarka ba, yarinyar nan ta nuna cewa ta fi karfinka, zaginka fa take duk sanda ka tsaya a ƙofar gidan su, amma duk har yanzu kana sonta a hakan bazaka haƙura da ita ba.?”
“Na sani Mujahid ni ba kowa bane face mabaraci nakasashen da na rasa wani sashi na jikina, talakan da bani da komai sai abinda nayi bara na samu, Tabbas da gaske ta ke tafi karfina domin kuwa babu mace mai daraja kamarta da zata yarda ta aureni domin gujewa kanta shiga cikin wahalar rayuwa, bata da laifi.”
Mujahid dubansa yayi da kyau tare da cewa.
“To amma duk kasan wannan shine bazaka hakura ba, tunda da kanka ka yiwa kanka hisabin tafi karfinka.”?
“Zuciya itace ta ke hanani gujewa Lubna ina matuƙar sonta shiyasa zuciyata ke nuna cemin nakasata ba kasawa ba ne zan iya abinda lafiyayye zaiyi, ina tsananin ƙaunar ta bazan iya rabuwa da ita ba, duk da nasan tafi ƙarfi na.”
Bakinsa Mujahid ya taɓe tare da cewa.
“Shikenan Allah ya maka zabin abinda yafi alkairi, amma dai nikam bazani ba kaje kawai kai ɗaya.”
“No Mujahid karka min haka mun saba tafiya tare dan Allah muje.”
“Ni fa Bazanje na tsaya ina ji tana zaginka raina yana ɓaci ba, kawai kayi tafiyarka.”
“Hmmm!!! Kaga nifa naje ta zageni ma daɗi nake ji muddun zanji muryarta to ni daɗi nake ji, ka daina damuwa dan ta zageni.”
“Ahmad ina mungun mamakin rashin zuciyarka wallahi, Soyayya kam hauka ne, yau tsawon wata huɗu kenan haduwata da kai Ahmad, a cikin wata hudun nan ko wacce rana da sabin al’amura kake zuwa, musamman akan wannan yarinyar, na tabbata da kana da iyaye da sai sun dakatar da kai akan wannan wahalar da kake sha akan Soyayyar banza son maso wani, mtsss, ko ni nan da ace nasan ɗaya daga cikin danginka da sai na sa sun dakatar da kai.”
Murmushi Ahmad ya saki, yana kada kansa tare da cewa.
“Karka damu Mujahid dama shi abu mai tsada ba’a cika samunsa cikin sauƙi ba, kai dai kayi haƙuri ka rakani kamar yadda ka saba.”
Bakinsa ya taɓe yace.
“Shikenan ai sai ka jirani nayi wanka mu shige.”
Murmushi kawai Ahmad ya saki.
Sai da Mujahid yayi wanka sannan suka garo keken guragunsu har ƙofar gidan su Lubna, sun ɗan juma tsaye kafin suka samu yaron aike.
Lubna tana zaune Umma da Goggo suma suna gefe guda yaro yayi sallama.
“Wai ana sallama da Lubna inji wani a waje.”
Ɗago idanunta tayi ta dubi yaron kafin tayi magana Umma tace.
“Je kace gata nan zuwa.”
Juyawa yaron yayi da gudu ya fita.
“Umma yaya zakice ina zuwa bayan bansan waye mai kiran ba, wama ya sani ko wannan matsiyacin nakasashen ne.?”
Daga cikin daki taji muryar Baffa na cewa.
“Kinci uwaki Lubabatu, har sai kinsan mai kiranki zaki fita, wato idan Ahmad ne bazaki fita ba kenan ko, ki jira kanki fa Lubabatu rayuwa fa Sauyi ne da ita baki san yadda zata sauya miki ba, ki tashi kije kiga waye ne dan gidan ku.”
Bakinta Lubna ta tura tana ƙunƙuni ta miƙe.
Kanta Umma ta girgiza tana kallonta ta zari hijabi a fusace ta fice, shi ɗin ne kuwa da bata kaunar gani.
“Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un!! Ni dai Allah ya hadani da masifa sai kace wanda na zagi sama, kai wai baka da zuciya ne, haba dan Allah ka rabu dani mana.”?
Mujahid runtse idanunsa yayi Maganar na masa kuna a cikin ransa dalilin kenan da baya ƙaunar rako Ahmad, numfashi Ahmad ya saki tare da sakin murmushi yace.
“Tabbas akanki bani da zuciya, ina sonki ina matuƙar Ƙaunar ki ta yaya zan iya rabuwa da ke, dan Allah ki rufa min asiri ki soni ki Aure ni, bazan iya rayuwa idan ba tare da ke ba.”
Yamutsa fuska Lubna tayi tare da shekewa da dariya tana masa kallon off and down kafin tace masa.
“Bazaka iya rayuwa ba tare dani ba Hmm!!! Lallai kuwa zaka mutu kwananka bai ƙare ba, domin kuwa ni bana sonka na tsaneka, kai amma dai Allah ya isa tsakanina da kai ka dubeni sama da ƙasa na maka kalar ƙasƙantattu walaƙantattun mutane irinka!!! Ina ga bayan nakasar taka kana da tabin ƙwaƙwalwa saboda Kaga Baffa yana tilasta min na saurareka shine bari ka wuce gona da iri!!! To ahir dinka wallahi ko shi baffan ma lokaci na basa, mtsss banza kawai, sai kata tsayuwa a wajen wahalalle.”
Tayi maganar tana zabga masa harara tare da shigewa gida.
Bakinsa Mujahid ya taɓe yace.
“Hmmm!!! Ka samu abinda kake so, zamu tafi ne ko mu tsaya cin mutuncin bai isheka ba kana bukatar kari.”
“Bazaka fahimta bane Mujahid ni nasan yadda nakeji a zuciyata akanta, mu tafi.”
Yayi Maganar yana gara keken nasa, shima Mujahid yabi bayansa.
************
*Senator Nura Alburawi Hause*
Nasreen idanu ta zubawa Momy da ke zaune ta haɗa ranta tamau sai famar huci take, tamkar wacce aka aikowa da mummunan labari, kanta Nasreen ta girgiza tare da mikewa ta shiga kitchen ruwa ta dauko ta ijiye gaban table na alfarma da ke gaban Momy ta koma wajen zamanta dai-dai Daddy na shigowa.
Atine mai aiki Nasreen ta duba dake goge Screen ɗin tv tace.
“Atine ki kawowa Daddy coffee.”
Cikin girmamawa Atine ta amsa tare da shigewa kitchen.
“Barka da fitowa Daddy.”
Murmushi ya saki yana kallonta ya amsa da.
“Barka my Nasreen.”
Yayi Maganar yana duban Momy da ko inda yake ba ta kalla ba.
“Hajiya Gaje lafiyar ki kuwa.”?
Wani irin kallo ta yiwa Daddy cikin haɗa fuska tana ƙara kawar da kai gefe ta amsa masa a dakile.
“Idan bani da lafiya a bedroom zaka tsince ni, tunda kaga fuskata a haka kasan tatsuniyar gizo ai bata wuce ta Koki.”
“Hmmm!! Tahir ba nasan shine sarkin baƙin jininki abun tsanarki, me kuma akace ya aikata.”
“Ko ba’a ce ba ai ansan hali da ginin da aka ɗaurasa akai, a gaskiya Senator zuwa yanzu haƙuri na ya fara zuwa ƙarshe shekara Talatin ina haƙuri da danne zuciyata amma yanzu abin yaci tura, tura ta kai bango wallahi bazai yiwu saboda Allah ya bawa yaron nan dama ba ya dinga taka mutane yadda yaso tsoho da yaro duk basu tsira a wajen sa ba, ko tsoron bakin duniya bakwa yi, kana ɗaure masa gindi kana ƙara hurawa tusa wuta, wai yaushe ne zaka gane ɗanka yana kan mummunar hanya bana jin daɗi a matsayina na uwa ina tsoron wata masifar ta faɗa masa, gini na ke kana rushe min Senator a matsayin ka na uba, hmm!!! Tahir ya bushe yanzu yafi karfin a tankwara sa, Allah sarki rayuwa wai uba shine yake nuna yaronsa hanyar banza ita ce kyakkyawar hanya.”
Murmushi Daddy ya saki domin ya saba jin waɗannan kalaman daga bakin Hajiya Gaje coffee ɗin ya ɗauka yasha wanda atine ta ijiye masa cike da girmamawa ya kurba kafin ya dubi Momy.
“Naji Hajiya Gaje ku fito street ki faɗa min meye Tahir yayi.”
“Kana tambayata tamkar baka san komai ba Senator bayan agabanka akayi komai sannan baka ce komai ba ka nuna lallai Tahir yayi dai-dai saboda kawai anzo neman arziki wajenki, shikenan ku baza’a ci alfarmar ku ba, Hmm!!! Wannan bawan Allah yana neman ragi akan Plaza da Tahir ya buɗe shikenan sai ya dinga faɗa masa magana yana zaginsa tamkar sa’ansa amma baka dakatar dashi ba saboda baisan darajar furfura ba.”?
Numfashi daddy ya saki kafin yayi magana sukaji muryar Suhaima tana cewa.
“Wai meye abun faɗa ne anan Momy banga ta inda Yaya Tahir yayi kuskure anan ba, sun san basu da kuɗin da zasu kama hayar wajen suka nemi wajen, sanda yake sayen siminti da bulo zuwa rodi waye ya masa ragi ko ya taimaka masa, sai kuma ya yiwa kattin banza wahala, sufa talakawa dole sai da wuta ni banga laifin yaya Tahir ba.”
Bakinta Nasreen da ke gefe ta taɓe tana kallon Suhaima yadda take faɗin magana cikin nuna iko da isa, Momy kuwa a hasale ta miƙe tare da nuna ta da yatsa tace.
“mu sa’oinki ne da zaki dinga saka mana baki cikin magana, idan na kuma jin bakinki ina magana da Senator sai nayi mungun saɓa miki yau naga rashin kunya.”
“Amma dai Momy kinsan akan dukiyar Mijina ake magana kuma ya zamo dole na kare masa dukiyar sa, daga gidan dukiya na fito nasan zafin dukiya da darajar su saɓanin wanda bai tashi cikin ta ba, shi bazai san darajarta ba ko da kuwa shekara dubu yayi cikin arzikin, wadannan talakawan haka suke basu san zafin kuɗi ba.”
Zaro idanunta Momy tayi ta nuna kanta da yatsa tana faɗin.
“Suhaima Ni kike ƙoƙarin fadawa magana ina faɗa kina faɗa sabod………”
Hannu Daddy ya ɗagawa Momy yana ɗago kai ya dubi Suhaima tare da cewa.
“Har abada bazaki taɓa hankali ba Suhaima, tana fadi kina fadi, saboda baki da hankali bansan wani irin tarbiyya Habiba ta baki ba, shige daga falon nan ki wuce part ɗinki shashancin banza kawai .”
Yayi Maganar yana Kada mata hannu alamun taje, wani irin haushi da takaici ne ya turnike Momy abin takaici ya gagara nuna mata kuskurenta ta rasa Senator wani irin mutum ne da baya bawa yara tarbiyya ƙwafa tayi tare da shigewa ta barsa a wajen a hasale da kallo Daddy ya bita tare da sakin murmushi da hannu ya yiwa Nasreen alamar tazo tashi tayi tazo ta zauna a gefensa.
“Nasreen na rasa yaushe mahaifiyarku zata fahimci akwai banbanci tsakanin aya da tsakuwa, sam bata da haƙuri akan lamura, meyasa zata dinga faɗa surkuwarta na faɗa hakan kan iya zubar mata da mutunci a idanun yarinyar nan Suhaima fa, uwarku bata da hkr Nasreen, Ki sanar da ita cewa bani da ikon da zan hana Tahir gudanar da hidimominsa na kuɗi bani na basa ba, ba kuma a jikina ya samu ba, bai jingina da dukiyata ba, da ƙafafuwan sa ya tsaya Allah ya dafa masa ko ficika ta babu a ciki har ya tsaya da ƙafafuwan sa duniya ta fara lissafinsa acikin masu kuɗin kasar nan na biyu, kinga kuwa ya ninkani dukiyar da bansan adadinsa ba, kenan ya fini sanin zafin kuɗi, dan haka kice mata ni bazan dakilesa ba, yayi abinda yaga dama da dukiyarsa yafi kowa sanin wahalar da yasha ya samu, ki tashi kije ki sanar da ita wannan saƙon.”
Numfashi Nasreen ta saki tace.
“Okay zan sanar da ita Daddy, amma Daddy zuwa yanzu ya kamata ka duba lamarin Momy, duka cikin maganganun ta gaskiya ne, kana da halin dakatar da Yaya Tahir kuma zaiji maganar ka tunda maganar taka yake ji, tun fa ina yarinyanta karama kuke wannan sa’insan da Momy bana jin daɗin hakan gashi har Suhaima tana neman zata dinga taka Momy duk akan tana jin yawan fadan da kuke kai da Momy kuma kaine ka bada wannan ƙofar Daddy.”
“Au ni ne nasa Suhaima ta raina uwarki ko, to zo ki dakeni dan ƙwal ubanki sai ki huce, ita uwar taki ba ita ta bawa Suhaima Kofar da zata rainata ba, tunda tana faɗa na faɗa da ita, shige a kaina ko na Saba miki.”
Idanunta Nasreen ta runtse zuciyarsa na mata ƙuna ta haura bedroom ɗin Momy da sauri tana zaune ta haɗa kai da gwiwa tayi shuru cikin yanayin baƙin ciki da damuwa sunkuyawa a gabanta Nasreen tayi tare da dafa gwiwwar ta tace.
_~AMINTATTU GUDA UKU DAGA AMINAN JUNA UKU~_
*AISHA A YABO FULANI*
*RASHIDAT USMAN OUM NASMAH*
*ZAHRA’U ABDUL M AHLAN*
_PAID BOOKS CIKIN FARASHI MAI SAUKI_
_GUDA ƊAYA #200 GUDA BIYU #300 GUDA UKUN #500, AMMA PAYMENT TA KATI YA SHA BAMBAN DA TA ACCT, GUDA DAYA #300 BIYU #500 UKUN #600, BIYA KUDIN KARATUN KU TA WANNAN ASUSUN BANKI 0006064512 Rashida Usman JAIZ BANK ko kuma katin waya ta daya daga cikin waɗannan lambobin_
08147537180
08162576936
08165550116
*Masu turo da evidence of payment wadanda suka yi transfer to acct ku turawa ɗaya daga cikin mu, don girman Allah banda vtu inde kika yiwa ɗayan mu vtu to kinyi sadaka Anty muna godiya gareku masoya
[…] Buri Uku Hausa Novel Complete […]