Littafan Hausa Novels

Biba Bala’i Hausa Novel Complete

Written by Hausa_Novels

Biba Bala’i Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

BIBA BALA’I

 

_MALLAKIN_

*Faɗimatu Musa Usman*

 

(“`Mmn Khairat & Muslim“`)

 

 

 

“`Wannan littafin ba free bane littafin kuɗi ne idan kina buƙata zaki biya naira d’ari 200 ne kacal, akwai complete document ɗin sa .“`

 

 

لبسم الله الر حمن الر حيم

 

“`Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga ubangiji mad’aukakin sarki, mai kowa mai komai ubangijin talikai.“`

 

“`Ya ubangiji ka k’ara tsiran ka ga masoyin mu Annabi Muhammad (S.A.W) da zuri’ar sa da sabban sa baki daya“`.

 

 

1&2

K’ofar gidan damk’am yake da jama’a babu masaka tsinke ta ko ina jama’a ne a zazzaune hatta k’ofar da zata sada ka da cikin gidan cike take da mutane babu hanyar wucewa, sannan babu abunda yake tashi daga cikin masallacin k’ofar gidan sai zallar karatun alk’ur’ani mai girma, na muryoyin hazik’an fasihan mutane daban daban, cikin muryoyin k’warewa suke karanto k’ur’anin ciki karatun warsu irin karatun ma na allo,

Baqar Aqeeda Hausa Novel Complete

daka shigo cikin unguwar zaka ji sautin karatun ya karad’e duk wani sashi na unguwar, da mutum ya tsaya ya saurara dole karatun ya matuk’ar burge shi sabida kowanne harafi suna fitar da shi yadda ya dace, kai ko kafiri ne yaji karatun dole sai zuciyar shi tayi sanyi sabida yadda suke fitar da hak’k’in kowanne harafi kuma suke bawa ko wanne harafi matsayin shi, hakan ne yasa dan dazon jama’ar Annabi wad’anda aka gayyata da ma wanda ba’a gayyace su ba suka halaccin gurin domin samun ladan sauraron karatun alk’ur’ani mai girma.

 

 

Wasu mata ne wajen su goma da ganin su babu Allah a ran su suka tunkaro k’ofar gidan gadan gadan, suna k’arasowa suka tadda jama’a damk’am masu sauraron karatun alk’ur’anin, burki suka ja daga gefe ganin taron mutanen yayi yawa wata ‘yar lukuta wacce duk ta fisu sauran matan nagari ta dubi wata ‘yar figigiya wacce duk cikin sauran matan ba mai rashin nagarin ta saidai amma daka mata duban tsaf zaka gane akwai tarin shekaru masu yawa a tare da ita, duban ta lukutar tayi tare da karayar zuciya tace “Anty yanzu ta yaya zamu shiga gidan nan?, dubi tarin jama’ar da suke gurin babu hanyar wucewa fa”.

 

 

Wacce aka kira da Antyn ya mutsa fuska tayi tace”wad’an nan tarin garadan da aka zube a k’ofar gidan nan ba su isa su hana mu ai watar da k’udirin mu ba, indai ni BIBA na amsa suna na to babu wani shege daya isa ya hana ni aiwatar da abinda nayi niyya,kuma wannan karatun da ake nasan ba dan Allah ake yin shi ba sabida haka karatun su bazai hanani inyi abinda nayi niyya ba, ni yin karatun ma yamin dad’i sabida zan shiga gidan nayi abinda naga dama ba tare da sanin mutanen waje ba balle akawo d’auki, sabida sautin karatun bazai bari aji abinda ke faruwa a cikin gidan ba, don haka ni kinga yin karatun ma yayi dai-dai da ra’ayi na, sabida haka ku biyo ni mu zagaya ta k’ofar baya nasan a bud’e take tunda nan an mata babakere”.

 

 

Juyawa tayi suka bi bayan ta yooooooo, suna zagayawa kuwa cikin sa’a kuwa k’ofar a bud’e take mata nata shige da fice ta k’ofar, suna isa kuwa batare da b’ata lokaci ba suka kunna kai cikin gidan.

 

 

Suna shiga batare da sallama ba suka nufi sashin matar gidan, mata sai binsu ake da kallo amma ba wacce ta iya yi musu magana, suna b’angaren matar gidan naga sun nufi wani d’aki wanda da ganin shi kasan na yaran gidan ne akwai suka banka kai cikin d’akin ba tare da neman izini ba, suna shiga kuwa cikin nasara suka hango wacce suka zo domin ta a can k’arshen d’akin k’awaye na zagaye da ita da alama ma kamar rarrashin ta suke yi, batare da wani b’ata lokaci ba BIBA ta k’arasa inda take ta damk’o wuyan ta ta hau duka tamkar ta samu jaka, su kuma sauran matan da suka yo mata rakiya suka rufarwa sauran ‘yan matan dake cikin d’akin.

 

 

 

Babu abunda kake ji sai k’arar duka da koke koke, koken koken ne ya fargar da matan dake cikin b’angaren, cikin tashin hankali suka yo cikin d’akin da gudu domin suga abinda ke faruwa, suna k’ara sowa kuwa suka ga mata na ta jibgar yara kutsa kai sukayi domin kawo musu a gaji amma me? suma suna shiga matan nan suka rufe su suma da duka ko ta ina.

 

 

Matar gidan kuwa koda taji sautin duka da koke koke ta garzayo d’akin da gudu tana zuwa ta hango su Biba ne, tabayi gigin shiga d’akin ba baya taja tana ambatar sunan ubangiji, d’akin ta ta nufa da sauri ta daddannan number ta kara a kunne bata dad’e da kara ta kunne ba ta fara magana cikin rud’ad’d’iyar murya”KAMIS ka maza ka shigo gida Matar ka tazo zasuyi kisan kai maza ka shigo ka kawo d’auki……..”.

 

 

Kafin ma ta k’arasa magana tuni Kamis ya katse wayar yayo cikin gidan a sukwane cikin matuk’ar tashin hankali.

 

 

 

 

“`ASTAGFIRULLAH WA’ATUBU ILAIH“`.

 

About the author

Hausa_Novels

Leave a Comment