Bestyn Mijina Hausa Novel Complete
BESTYN MIJINA
DAGA ALƘALAMIN:FARIDAT HUSAIN
MSHELIA(UMMU-JIDDAH).
*ZAFAFA WRITERS ASSOCIATION*
*Sis Zainab ta BESTYN MIJINA comments section, wannan shafin dungurungun naki ne Turai ta ce a baki tare da tirelan cash Allah ya bar ƙauna da soyayya*
SHAFI NA ISHIRIN DA SHIDA.
FALMATA POV.
Haɗa hannayena biyu na yi suka yi wani irin ƙara alamun shirin faɗa amma ganin wani irin kallon banza da Nu’aym ya watso min yasa suna ƙarasowa na maza da sauri dan haka suka Gara kai da bangon wajen tare da komawa da baya suka faɗi magashiyan,
Ji kike ƙass!ƙass saboda yanda ƙasusuwan jikinsu ya garu da ƙasan tiles ɗin da ya yi ma falon ƙawanya,
Mata ta ce Hausa Novel Complete
Salati sauran yayunna su suka rafko ganin abin da ke faruwa Nu’aym kuwa kauda kan shi ya yi tamkar bai shi a wajen ganin sun gagara miƙewa yasa suka yi kan su cikin masifar da ke cin su a rai,
Wani daɗi ne naji ya ziyarci ne ganin yanda duk suka shiga tashin hankali jiyo ihun Minal kuwa sai tsala ihu take tana ƙiran Hajiyarsu saboda yanda ƙugunta ya bugu abinka da siririya wacce ƙashi ya yi ma jikinta yawa,
A fusace Babbar yar su ta ce”Kana kallo matarka na shirin karya ma Hajiya ƴanmata amma ba matakin da ka ɗauka an ya kana cikin hayyacinka kuwa Nu’aym?”
“Ina fa yake cikin hayyacin shi bayan an riga da an wanke an ba shi ya sha an wannan kiti murmuran yarinyar Allah ya isa tsakanina da ita”ce war Hajiyarsu wacce ta shigo falon gidan namu yanzu,
Miƙewa ya yi tsaye cikin haɗa fuska ya ce”Ni ba macen da ta isa ta wanke ta bani in sha sai dai Inna gadaman sha da kaina so ku daina ganin Falmata asiri ta min yasa na aureta,inaaa sam ku daina tunanin hakan soyayya ce yasa na aureta tare da ni’imar dana hango kwance a ƙwayar idonta,daga yatsun ƙafarta dana kalla kawai na san wace mace ce ita dan haka zaɓina ce ita kuma ina samun gamsuwa dubu bisa dubu tattare da ita”
Sakatoto haka suka saki baki suna kallon Nu’aym wanda ke shararo zance ko kunyar idon mahaifiyar shi da yayun shi bayaji balle kuma ƙannen shi da ko daga cikin ma basu shiga ba,
Hajiya wacce ta sandare a tsaye tana kallon fatar bakin shi cike da mamaki tare da ta’ajjubin tilon ɗan nata wanda ta mallaka ma soyayyarta tare da nuna mi shi gata mara misaltuwa miyau ta kalato ta jiƙa maƙoshinta da shi ganin irin kallon da suke bin shi da shi yasa ya ce”Duk ku ka jawo fa Allah saboda da kun kyaleni da zan hukunta Falmata gwargwadon laifin data aikata a gareku duk da su Balaraba(babbar ƴar su)sun ce ta zageki amma Ni banji ba a video kuma in da gaske ta aikata ai zata ƙara kuma wa kuma Ni ba kyaleta zanyi ba amma haka kurum kun yi zuga kun zo kun tsaya min akai a dole sai na saki matata to wallahi ba ku isa ba dan daidai iyawarta tana nata hakurin dani”,
“Mu kake faɗa ma haka Nu’aym lallai wuyarka ya isa yanka ka riƙa ka ƙosa ban taɓa sanin rashin kunyar ka ya kai haka ba sai yau”,
Murmushi ya yi cikin son tura musu haushi ya ce”ku fice min a gida kawai shine zai fi malamai haka kawai kuna zige min Hajiyata dan kun ga tafi sona”,
Har tsuma jikinsu yake yi Falmata kuwa wacce ke cike da mamakin yanda Nu’aym ya yi musu ta yi mutuwar tsaye tsabar mamaki “ashe yana sona da man?”ta tambayi kanta ai bata samu damar kai ƙarashen zancen nata ba taji ya daka masu autar su tsawa”Out!”
“Ku gaggauta fice min daga gida shashashun banza kawai da wofi a gaban idona dan bakuda kunya kun zo zaku daki matata to wallahi ko a bayan idona na ji wannan labarin sai na karya yarinya biyu.”ai ko kafin ya rufe baki har suna rigegeniya wajen ficewa daga Falon gurin ya rage daga Ni sai Hajiyarsu sai shi wacce ta yi mutuwar tsaye,
Daka min tsawa nima ya yi rai a ɓace tare da rufeni da faɗa ta inda yake shiga ba tanan yake fita ba dan ya ɗaura alhakin faruwar komai duka a kaina dan da ban tanka musu ba da duka hakan bata faru ba,
Jin yanda yake zagina da bina da munanan kalamai yasa na juya a fusace zan shige ɗaki kamar zai kifa haka ya biyoni zai danƙoni na yi saurin danna ma ƙofa key dan sai in sha duka a banza a wofi,
Bubbuga ƙofar ya shiga yi yana umurtana da in buɗe ƙofar naƙi sulalewa ya yi a gurin ya dafe kan shi dake matuƙar Sara mi shi,
Hajiyar shi kuwa cije leɓe ta yi dan ta tabbatar da ya danƙeni a wannan lokacin tabbas da ya haɗa min jini da majina sai dai kash na arce amma ba damuwa gobe ma rana ce dan in kere na yawo zabi na yawo watarana za su haɗu,
Kwafa ta yi ta juya cikin hanzari tana niyyar barin falon a tsiya ce Nu’aym ya miƙe ya riƙota tare da rumgumeta duk yanda taso ɓanbare shi daga jikinta ta kasa saboda yanda ya mata riƙon tsauri,
“Sakeni tunda ka zaɓi matarka akaina,bani baka daga yau…….”ya yi saurin rufe mata baki da tafin hannunshi gudun kar ta mi shi baki,
First love ki yi hakuri
First ubanka ce ba First love shegen yaro kawai!
Jin bai ce komai ba yasa ta cigaba da ce wa “ba dai har ka san daɗin mace da zaka tsiyatani da yan’uwanka a gabanta ba to ka je mun yafe mata kai aje a ci gaba da soyáyyá Majnunun laila.”
Kuka ya fashe mata da shi wanda ya san shine lagonta na ƙarshe da zai yaƙeta amma sai yaga ta raba shi da jikinta tana neman shigewa ta fice ta bar shi da sauri ya danƙi ƙafarta dan tabbas ya san yau ya Kaita bango cikin ɓacin rai ta ce”Tsine maka kake so in yi ko me Nu’aym?”,
Girgiza kai ya yi cikin kuka ya ce”Kasheni na ke so kiyi in huta da irin ƙiyayyar da yayuna mata su ke gwada min kawai dan na kasance namiji tilo a cikinsu Kuma kin fifita soyayyata a kan su”shiru ta yi tana nazarin shi an ya yaronta bai zauce ba?to ko dai ya fara shaye-shaye ne?”
Ina cikin hankalina Hajiyata sam zauce ba kuma ban sha komai”ya faɗi hakan tamkar ya san tambayar da zuciyarta ke mata,
Kawai dai na gaji ne da wariyar launin Fatar da suke gwada min kamar ba ciki ɗaya muka fito ba,kuma na gaji da tuhumar ki akan Meyasa ba ki samo min ɗan’uwa namiji ba tunda na san ba kece ke bada haihuwa ba kin ga Inna mutu shikenan sun huta tunda basa son farincikina”nan da nan ta ji zuciyarta ya sanyaya ta riƙo shi tare da yin tattaki ta isa tsakiyar falon ta zaunar da shi a ƙasan carpet ina kuma ta zauna a kan kujera mai zaman mutum ɗaya”,
Gunjin kuka yake yi ta yi saurin janyo shi tare da hana shi furta abinda ya ke son amayowa a hankali ta ce”Duk dai a kan soyayyar matarka ka ke wannan boloƙonko?”
Sam wallahi Hajiya saboda ita kanta matar ba jindaɗin zama da Ni take ba kin fi kowa sanin halina nan ya kwashe kaf zaman da muke yi ya zayyano mata jinjina kai ta yi alamun gamsuwa dan ta san halin Nu’aym sam bai iya ƙarya ba ko kashe shi zata yi gaskiyar nan ce dai zai faɗa madadin ta tausaya min sai ta samu point ta yanda zata ɓatani a idon shi da idon duniya cikin ruwan sanyi ba tare da kowa ya zargeta ba dan ita har ga Allah bata sona kuma bata jin zata taɓa sona har gaban abada,
Tofah!ke kuwa me kika mata ta yi miki irin wanna tsanar?
an ya ba wata a ƙasa kuwa?
“Soyayya gamon jini ce ai Sahiba sannan so da ƙi halitta ce wanda Allah ya halitta guda biyu ɗaya na korar ɗaya ne idan an zauna an fahimci halin juna to ita bata ban daman haka ba balle ma har ta san kyawawan halina ƴaƴanta mata sun hana mu shaƙu sam”
Ikon Allah to Allah ya shiga tsakaninmu da mugayen dangin miji
“Amin ya rabbi Tawajena”kwanciya ta yi tare da runtse idonta wani kasala ta ji ya mamaye gaɓɓanta nan da nan ta fara sakin hamma ganin tana lumlumshe ido yasa uwargidan Sani ficewa ta ja mata ƙofar dan zuwa ta ɗaura sanwa dan ita keda girki.
A tashi lafiya ƴar mutan Machina gari mai dutsen amarya da kogo,garin da macizai ke Mulka😂.
TURAI POV.
Godiya na ke masoyana, tabbas na ga tarba mai kyau daga Fans ɗin BESTYN MIJINA kun ƙarfafa min gwiywa dan haka ga shi ku yi breakfast dinner is coming in the night in sha Allah 💃
Ummu-jidda.
[…] Bestyn Mijina Hausa Novel Complete […]