Bazawara Ce Ita Hausa Novel Complete
Bazawara Ce Ita Hausa Novel Complete
By
Rasheeda S Director
INAYIWA UBANGIJI GODIYA DAYA KUMA ARAMIN LOKACI NAKUMA DAWOWA DAWANI SABON LITTAFINA MAISUNA BAZAURACE’ ITA
INAROKON ALLAH YABANI DAMAR FADAR ALKHAIRI ACIKINTA YASARKAKEMIN ZUCIYATA CIKINTA DAWAJENTA
ALLA KAJIKAN BABY KHAIRAT KASA MAICETON
free page
🅿️1
Ahankali take sauka daga matattakalar bene,kacokam hankalinta yakoma kan wayarda ke rike ahannunta,yarinyace da baza tawuce ‘yar shekara 19 ba farace soll irin fari maikyanna,kyakyawace nakarshe,tanada tsawonta daidai kwarkwado baza’akirata doguwaba sannakuma bagajeruwa bace” tsawonta daidai,tanada manyan nonuwa ga uwa uba hips,duk d’aga kafarta dazatayi sai ilahirin jikinta yamotsa”irin motsinda duk lafiyayyen namiji idan yayi tozali dashi saiyawun bakinsa yatsinke.
Soyayya Da Karamar Yarinya
asannu ta idda sauka, ta’isacikin katafaren parlour wanda yaji kayan’alatu dana more rayuwa,parlour ne babba yakayatu iya kayatuwa”
Asannu ta’isa cikin parlourn tazauna bisakan d’ayadagacikin, lafiyayyun kujerun da kejere acikin parlourn, har’alokacin idanunta nakan wayan,
lokaci zuwa lokaci saita saki murmushi mai matukar karawa fuskarta kyau,
“takai tsawon 20min a zaune tana aikin latsa wayar,sanna tamike tsaye,tajuya takalli gefenta tasauke manyan idanunta saman dinning, saita yamusa fuska tareda jan d’an karamin tsaki,asannu tafara d’aga kafarta ahankali tanufi wata kofar dake gefe dacikin parlour tanafadin “Aunty Rukayya! Aunty Rukayya!.
dai-dai lokacin tatura kofar, takusa kanta ciki,
masha Allah ranb’a she-shen kitchen ne mai matukar kyau danko yatsaru yaji kayan duniya,
wata ‘yar matashiyar matace wacce akalla shekarunta zasukai 27 tsaye acikin kitchen d’in tana d’auraye kwanukan datayi amfani dasu, tajuyo tanafad’in “yaya lfy da irin wanna kiran haka?.
baki taturo gaba
tace “Aunty Rukayya kinsan bazaki iya yin aiki ked’aiba kikace bakya bukatar ‘yar aiki,
duba kigani 2:00pm amma ace haryanzu ba’a kammala abinciba nifa kinsan bana jurar yunwa,tund’azu nashirya zanfita kuma yanzu haka Aysha jirata take zamutafi shopping saikirata take nafito mutafi yunwa tahanani fita,
wlh zan fad’awa Ya Al’ameen kawai ad’auko ‘yar aiki dan mutun yarikacin abinci dawuri,dansaboda kishinki kikoramana ‘yar aiki gashi yanzu komai mutum wai saidai yayi dakansa.
murmushi Aunty Rukayya tayi, tace “toh aini kena taimaka danki juri yin aiki dakanki koda ace kinje gidan mijinkine aiki bazai baki wuyaba dan kinrigada kinsaba,kinga tunda kinason cin abinci dawuri saikirika zuwa munayin aikin tare,kinga kekanki zaki karu dawani abun,
Tace, “lallaima cemiki akayi ban’iya aikinba?.
Aunty Rukayya tace “nasan kin’iya amma kikara akan iyawarki.
tace “Allah ni bazan wani iyayin aiki ba nidai bari Ya Al’ameen yadawo me aiki za a d’auko,
Aunty Rukayya tace “to ay laifin Yayan nakine tunda shi yasani yin girki har kala hud’u wai zaiyi bako,da ace girki d’aya zuwa biyune danajima dagamawa.
baki tatab’e tagota tagefen Aunty Rukayya tad’au plt tabubbud’e kulolin datashirya girkin aciki,manyan idanunta tawaro tareda bud’e baki cikeda mamakin ganin yanda tatsara girke-girke na musamman har kala hud’u,tajuyo takalli Aunty Rukayya “tace duk wanna girkin nabakonne? saikace wani Minister ne zaizo.
“to wayasani ko Minister ne”cewar Aunty Rukayya,yamusa fuska tayi tareda kawar dakanta gefe tana fad’in “cankuma tamatse muku kuda bakon naku, akanshi azauna ab’atawa mutane lokaci,Aunty Rukayya dai dariya kawai tayi dan tasan halin ta da tsiwar tsiya bata kyale kowaba,tad’ibi abincin tafito parlour
takoma kan kujerar data tashi tazauna,
Turo kopar parlour akayi tareda sallama,ta’ammsa sallamar tareda turo baki gaba takuma ture plt d’in abincin tareda kwabe fuska, tayi rau-rau da ido,asannu Wanda yayi sallamar ya’iso inda take,yanafad’in “subhanallahi! Wayatabaki shalele?. Tamatse idanu da karfi saiga hawaye shar-shar harda jan hanci,cikin muryar kuka
tace “ba Aunty Rukayya bace,
Yace “Rukayya to me Rukayyan tayimiki!?.baijira amsartaba yashiga kwallawa Rukayya Kira,dasauri tafito daga cikin kiching,
Cikin d’aga murya yace “mekikayi mata!?,yafad’a tareda nunata da yatsa,
binsu da ido dukansu tayi,kana tace”toni mekuma zanyi mata?.cikin Kuma d’aga murya yace “ba’abun da natan bayeki bakenan amsa nakeso kibani.
Sunkuyar dakanta tayi tana alhenin yanda, Ya Al’ameen yake goyawa kanwar tasa baya kodakuwa itace batada gaskiya, bama shikad’aiba duk family su,katse mata tunani yayi dafadin,dake nakefa,
D’ago kanta tayi
tace “wlh ni ba abinda nayi mata kawaidai akan girkine tamayar masa yanda sukayi,
Yajuyo yakalleta,
Yace”wai hakane?.
Kai ta gyad’a tanaci gaba da masar kwalla, numfashi yasauke tareda susa bayan keyarsa,shi kwata-kwata ma yakan mance da halin kanwar tasa sonta yakan mantar dashi,
Gyaran murya yayi yaceda Aunty Rukayya
“jeki cigaba da ay kinki,yasunkuyo yadau plt d’in yamaida mata gabanta,yace”ci maza abinki shalele laifinane da bance afara yimiki girkinki kafin na bakon ba,kiyiwa yayanki afwa, kai tagyad’a tareda goge y’ar guntun hawayen fuskarta,
ahankali tafara cin abincin kamar bazataciba,shiko mikewa yayi yabi bayan Aunty Rukayya,
korabin abincin bataciba tature plt d’in gefe.
tamike tsaye
tana lallasa waya takarashi akunne,
hello fito mutafi. tafad’a taredad’au kar
gyalenta da da ‘yar karamar Jakarta
dake hannu kujera,
tanufi kofar fita daga parlour tafito farfajiyar gidan.
Ya Al’ameen nashiga kiching d’in yatadda Aunty Rukayya tsaye ya’isa inda take yarungume ta tabaya numfashi tasauke tad’ago hannu tashafo gefen fuskarsa,ahankali tafurta “kagaji ko?.saida yalumshe idanunsa yakuma bud’ewa sannan
yace
“sorry My Ruky kinsan yarinyarna karamar yarinyace kinsan shikuma yaro d’an lallamine ki..saurin juyowa tayi batareda tabari yakarasa zancen nasaba, Dan tasan kullum kalmar nasa baiwuce kiyi hakuri yarintace ke damunta ba, ita yanzu harta saba da halin kanwar tasa danshi baya tab’a ganin laifinta,kullum ayarinta take.
Tace”taho muje kad’an watsaruwa saikafi jindad’i.
Tajanyo hannunsa suka fito.
Tamfasetsen gidane maid’aukeda part uku,asannu tanufi d’aya daga cikin part biyu dasuke jere,ahankali take d’aga kafarta tana haurawa bisa steps d’in dazai sadata dakofar shiga cikin part d’in,
dasallama tashiga cikin parlour,wata dattijuwar mata ce wacce akalla shekarunta zasukai 50 years tanazaune acikin parlour dawasu yara biyu ‘yan kanana shekarunsu baiwuce 3 years ba,
dagudu yaran suka mike ajikin matar suka taho suka rungumeta,
“oyoyo Mamy
yaran sukafad’a sunad’ada rungumeta,
murmushi tayi tadad’a janyosu jikinta tareda shafa kansu,
tasunkuyo dai-dai tsawonsu ta sunbaci goshinsu da
kumatunsu,
tace ” Hi
Guy’s kuna lfy?
cikin maganarsu dabata gama nuna abakinsuba,
sukace
“Eh, “Mamy zakije damu?
ido tad’an waro saita d’aura hannunta a kumatunta tadafa tad’an juya idonunta sama kamar maiyin nazarin wani abu,suko yaran yanda tayin haka suma sukayi,
d’ayanda ke gefen damanta yasauke hannunsa a kumatunsa, yaja hannuta dak’ekan fuskarta
yace, “Mamy tachi mutafi,saiyariko hannun d’ayan yanafad’in
” Hussain jomupita.
mikewa tayi tana murmushi, tace “Hassan Hussaini,kuzauna yau badaku zantafiba kujirani yanzu zan dawo bajimawa zanyiba zankawo muku tsarabarku kunji?,
kai suka gyad’a mata,
tace ” yauwa good boy’s,
tariko hannunsu takarasa cikin parlour inda matar nan take,tazauna kusa da ita,
yaran suka zame ahannunta suka koma kafar dattijuwar,kunnuwarsu tarike tana fad’in
“nikutashimin anan sarakunan yawo,kukenan duk inda za’aje saikunce zaku,kodashike laifin uwar takuce data maidaku kamar jaka duk inda zata saitaje daku,
baki taturo gaba tace “Ammee sud’inne jakkar? dankawai sunce zasubini,
Ammee tace
” Ai su wad’annama sunfi jakka ni kid’ibesuma kutafi sun’isheni dama dashegen surutun nan nasu.
tace “Ammee keda kanki zakije nimansu anjima,dan dai yau bada mota zanfitaba napep zamushiga da Aysha kuma banaso sud’ibi kurar hanya datare zamu tafi,Ammee kikula dasu sosai.
Ammee tace” to masu ‘ya’ya,dadai kin d’ebesu kuntafi da wanna dokokin da ake gindayamin akansu,
Murmushi tayi tamike tsaye
Tace “Ammee kidai kulamin dasu Allah idan bahakaba kuka zanyi tayimiki kuma bazan tab’a yin shiruba harsai Abba yadawo yararrasheni dakansa, dan yau ko Ya Al’ameen da Ya mujaheet da Ya jabeer ne suka rarrasheni bazan tab’a yin shiruba,
Dakuwa Ammee tayi mata,
Tace “kinci gidanku ja’irar yarinya kawai,yoni kansuzo ay na nakad’a miki dukan tsiya kinga sazo suyimiki lallashin da tushi,
Bubbuga kafa tashiga yi tareda matse idanu,
Dasauri Ammee tace
“Ya’isa shikenan jeki zan kular mikidasu.
Saida takuma sunbatar yaran agoshi kafin tafi,
Tanafita direct bakin get tanufa, dasauri wani dake goge d’aya dagacikin motocin dake jere a parking lot yayi saurin isa inda take,kamar zai durkusa kasa tsabar girmamawa,
Yace
“Ranki shidad’e wata motar za’afito da ita?
Yayi maganar kansa asunkuye,
Hannu tad’aga masa batareda tace dashi komaiba,
Ganin hakan kuwa yasashi saurin jadabaya dan yafahimci abinda take nufin,dan har idan kuwa yana bukatar cigaba da ay kinsa tokuwa kada yakuma tanbaya nabiyu, ay bashiri yayi saurin barin gurin,
Tunkan ta’isa jikin get d’in mai gadi yayi hanzarin bud’e mata karamin kofa,takusa kai tafice acikin gidan.
Shiru unguwar babu motsin kowa,lafiyayyun gine-gine ne tareda shinfe d’ed’d’iyar titi wacce aka kawatata da koyayen wuta da furanni masu matukar kyau da kyalli da d’aukar ido.
Bakajin motsin komai sai iska mai fidda sassanyan kamshi mai matukar dad’i ke ketashi,Wuse Kenan.
Asannu talumshe idanunta tareda shakar daddad’ar kamshinda ke yawo asassanyan iskar dake kad’awa.
Gadukkan alamu tana matukar jin dad’in yanayin,sai murmushi take tana dad’a jefa kafarta akan shin fid’ed’iyar titin,
Abin mamaki duk dakuwa girman titinna Amma ba’alamar ababen hawa ko guda, hasalima shiru gurin yad’auka.
Kofar wani get tatsurawa ido wacce kedaga can sallaken titin,saita ja tsaki afili tafurta,
“Amma kincika ‘yarrainin wayo sokike ni najiraki kenan?
Tayi maganar tareda d’ago wayarta talallasa takara akunnenta anad’agawa
Tace
“Kinfasan banajira,
Aysha dake biye dakiran
tace
“Sorry tawan gani dafda bakin get zanfito,
Yamusa fuska tayi cikin salonta nako oho tasauke wayar, dai-dai nan ta’iso tsakiyar titin.
Damugun gudu wata mota tasharo kwana,
cikin razana dafirgicin ganinta atsakiyar hanya, gakuma mota gadan-gadan yanufota da mugun gudu,idan tace zatakoma dabaya tofa motar zata iya karasowa gareta hakama idan tayi gaba,
Kara takwalla tareda kankame idanunta,arazane yataka wanin wawan burki,
“inanlillahi’wa’inna’ilaihirraji’un’ yafurta amatukar tsorace,
Dasauri yab’alle marfin motar yafito, yataho inda take durkushe sai kakkarwa take har alokacin idanunta narufe,
Hannusa narawa yamika yariko hannuta yad’agota tsaye,
“Waiyo Allah, Kai Allah nagode maka daka tsayar iya haka ay ni nayi zatonma nabigeki gaba d’aya, kaigaskiya na auna arziki.
Cewar mutumin dake Jan motar,yacigaba
“Kiyi hakurifa wlh ban lura da mutun na tahowaba,Allah dai yasa bakiji ciwo ko kad’anba dan naga kinata matse hannuki,
Yafad’a yana kokarin riko hannun nata, sai asanna tabud’e idanunta jin bugun zuciyarta ya dai-daita, tayi saurin sake hannuta batareda ta bari yasami damar rikeshiba,
tazabga masa wani uban harara tareda jan dogon tsaki,
Tace
“wlh Allah yayimaka babban taimako daka bigeni da wlh yau kayi bankwana da farin ciki, kana tuki kamar baka gani duba kagani yanda kashafamin datti ajiki ni wlh Allah bayarda zanyiba,yaza’ayi karika tuki sonranka saikace anyimaka titin kaikad’aine.
Yace “Kiyi hakuri wlh bada gan-gan
nayiba nayi kokarin kauce miki amma saidad’a kusawa kikayi, babu yanda zanyine kingama ay Allah yatakaita kiyi hakuri.
Sosai tadage tarika surfeshi dayimasa tsiwa ita adole kawai shine bashida gaskiya,shiko hakuri yarika bata darokonta akan tayi hakuri tatafi.
Ahankali yakoma yajinginu dajikin sit in motar, yalumshe idanunsa alokaci guda yabude,saiyaja guntun tsaki, yakalli kayataccen agogon da ke d’aure ahannunsa,akalla yakai tsawon 20min azaune acikin motar,shibawai rikicin dasuke bane yadameshi ba,barinshi da’akayi zaune acikin mota kuma ana batamasa lokacinsa akan wani shirmen banza, yakai dubansa kan titin har alokacin tananan tana zuba tsiwa, nanma wani tsakin yakumaja, idan ransa yayi dubu to yabaci,
Cikin zafin nama yab’alle marfin motar yafita ,
Wow Masha Allah
“Allah yayi halitta anan,
Inda suke yanufa yana fad’in “wanna wace irin rashin mutuncine Sadeeq? yazaka barni zaune acikin mota kazo katsaya yin wani shirmen banza.
Yajuyo gareta yanunata da d’an yatsa
Yace
“Kewaye daza azauna baki hakuri kina fad’in bazaki hakuraba!?
Wlh inda ni nake driving inna da bigeki zanyi inbige banza inga mai zai faru,kifito kan titi kina tafiya kamar titin na ubankine,harza’a tsaya ana baki hakuri kitsaya kinayiwa mutane rashin kunya,
Yamaida dubansa ga Sadeeq
Yace
“Kaikuma banza mara aikinyi katsaya batamin lokaci akan wani banzan Abu kazauna saibata hakuri kake kamar wata uwarka,
Sadeeq dai murmushi yy
Yace
“Komadai me yanzudai tahakura muje.
Ido taware cikeda masifa
Tace
“Waya fad’amaka nahakura ay wlh tunda yazageni yajawa kansa musifa, dakuma kakecewa wai titin na ubanane inda Kai kake tukin daka bigeni,aiko dakayi bankwana dafarin ciki,rayuwarka kuwa zatakare a firizin kaid’in titin na tsohonka ne dazaku rika gudu son ranku.
Takarashe maganar cikeda tsiwa tanayi tana ware manya idanunta tareda kad’asu cikin wani irin salo namusamman.
Azafafe yad’aga hannu zai kaimata mari Sadeeq yayi saurin rike hannunsa,
Yace
“Haba Man mezaka buga anan kadubetafa du-du nawa take wanna ay batafi sa’arsu Zahara ba,baikamata mu mubiye mataba,
Kallon Sadeeq yy
Yace
“Zaginanafa tayi,
Wlh saina koyawa yarinyarna hankali wawuya kawai.
Sadeey yace
“To ay kai babbane saikayi hakuri,
Sadeeq yarika bashi hakuri da tausasaki yajanyo hannusa yamaidashi cikin mota,
Aysha dake tsaye duk abinda yafaru akan idonta yafaru,tajinjina kai tana mai mamakin hali irin nakawar tata ita babu wanda takyale daga nagidan har nawajen tagirgiza takaraso inda take.
Sadeeq sanda yatabbatar daya zauna kafin yarufe marfe motar,yazago gefen sa yashiga yaja motar sukayi gaba.
Aysha tace “taho mutafi,kamar jira take tajuyo cikin masifa,
Tace
“Ay wlh saiyasan waya zaga idan yasaba wulakanta mata yashare tokuwa yau zaisan yataba gamonsa.
Saikuma tasaki kuka tana bubbuga kafa akasa cikin muryar kuka had’eda shagwab’a
Tace
“Allah bazan kyaleka kaci banzaba saina nuna maka ni ‘yargatace gaba da baya.
Aysha tace “kidaiyi hakuri kingama suntafi abinsu bakuma saninsu kikayiba bare kinuna masan.
Dakyardai Aysha tasamu ta lallab’ata sukatafi,
Tuki Sadeeq yake Amma hankalinsa naga abokin nasa ganin yadda yahad’e rai sai’aikin jan tsaki yake tareda taunar lips d’insa nakasa,
Numfashi Sadeeq yasauke saikuma yasaki ‘yar karamar dariya,
yace
“Kai wlh Allah yataimakemu dayarabamu da wanna rikicacciyar yarinyar, kai kaji yarinya da rikici ko,
Ammadai gaskiya taburgeni,ni tana maganarma gabad’aya jikina b’ari yake dan gaskiya yarinyarfa tahad’u idan tajuya idanunta kamar naruga aguje haka nakeji,saiyakuma sakin dariya,
Yace
“waikai Man baka lura dahakan bane? Wlh yarinyan tahad’a komai gaskiya taji kayan had’ifa sosai,
harara yagurga masa yace “banza namamajo kace dama duk wulakancin datayimin kaika shirya,shiyasa kad’aukoni wai nayimaka rakiya zuwa gidan abokinka, daka barni agida abina da banzo nahad’u da bacin ran waccan banzanba, to saime inta had’un zaka iya maidani gida saikaje gurinta.
Sadeeq yace “yihakuri mutumina aini nad’aukokane dankaga gari kai kenan duk sanda kazo hutu kasarna saidai kakarici zamanka agida bazaka fita kad’an yawataba,kuma ay ni duk son matana bazance inason waccan yarinyarba dan tafi karfina, dankuwa da matan manya tafi kama,kamar irinsu governor minister dadai sauransu,
Saikuma irinku manyan kusoshin Nigeria.
Azafafe yajuyo yace wad’in ni Allah yasawake ai ko mata sun kare aduniya bazan tab’a auren waccan wawuyar yarinyarba,
“Kanaji ko Sadeeq?
Sadeeq yace “inajinka
Yace”idan zakarika yin kwatancenka kadaina misaltawa dani.
Dariyar shakiyyanci Sadeeq yayi yace “to ranka shidad’e.
Daidai nan suka iso bakin get yadanna hon maigadi yawangale musu get suka kusa cikin gidan, Sadeeq yadaidaita parking yafito shiko nahakimce acikin motar,saida Sadeeq yazago gefensa
Yace
“Fito mushiga mana,
Kamar bazai fitaba saikuma yazuro kafarsa waje yamike tsaye, kallo d’aya yayiwa gidan yad’auke ido,
tsayuwarsu yayi daidai dashigowar wata mota,direban yagyara parking ajerin motocin dasuke cikin parking lot,dasauri yafito yazaga yabod’e marfen baya cikin girmamawa yad’an jadabaya dan nacikin yasamu damar fita, wani farin dattijo ne yafito daga cikin motar akalla shekarunsa zasukai 60 cikin shigarsa na kamala da dattako.
Dasauri Sadeeq yamaso inda yake cikeda girmawa yace
“barka da dadawowa Abba.
Abba yafad’ad’a fuskarsa da murmushi
yace “yauwa Sadiku kuna lfy daiko?
Sadeeq yaritsina yashiga gaidashi
Daga inda yake tsaye yad’an ritsina yace “barka da rana,
Abba yakuma fad’ad’a murmushinsa yace “yauwa wanake gani kamar
*MAHFUS* Tukur Shali kodai kamace?.
Sadeeq yace “shinedai Abba bakamaba.
Abba yace “toh lallai marabanku, Kai Sadiku abokin naka baisan dazuwan na kubane?
Sadeeq yace “yasani Abba.
Abba yace “toshikenan ni bari nashiga ciki.
Abba nashigewa
Sadeeq yaciro wayarsa ya daddan yakara akunnensa “hello mun iso.
Ya Al’ameen dake zaune a parlour yamike tsaye yanafad’in naji kace kun iso, au bakai d’aya bane?
Sadeeq yace “Eh nida mutumina ne,
Ya Al’ameen yace “wani mutumin naka?
Sadeeq yace “kafito mana zakaganshi ay.
Dawayar rike akunnensa yafito, da mamaki yake kallon wanda Sadeeq yazo dashi,dankuwa bai tab’a sammanin hakanba, yayi mamakin ganin wanna fuskar anan, dukda kuwa yasan cewa abokinsa Sadeeq yana abokantaka dashi sosai, Amma kasan cewarsa babban mutum wacce duniya tasanshi take Kuma burin cigaba darayuwarsa acikinta baiyi zaton ganinsa haka dasaukiba,dukda kuwa hakan bazai iyabashi wuya wajen ganin nasaba kasancewar suma duniyar tasansu Amma sanin da akayiwa MAHFUS Tukur Shali yagirmi sanin nasu.
Ya Al’ameen cikin sakin fuska yamikawa MAHFUS hannu,shimadai bayabo bafallasa yamiko nasa hannu sukayi musabaha,sanna yayi musu jagora zuwa cikin part d’inshi,
Cikin katafaren parlour sa yayi musu masauki,
Hira suka bude, Sadeeq sai zuba surutu yake shiko MAHFUS wayarsa yaciro yashiga latsawa batareda yasanya musu baki acikin hirar tasuba,
Aunty Rukayya tafito suka gaisa itama tayi mamakin ganin MAHFUS d’in, taje takawo musu kayan ci dana sha wandatashirya
tacikasu dashi,
Sadeeq yawashe baki yace”Kai amarya Kuma uwargida duk wanna namune?
Tayi murmushi tace “duk nakune idan bai isabama sai akaro,
Ato lallai mungode kinga dama yunwa nakeji rabondanaci abincin kirki tun daren jiya shimad’in sanda nashiga gurin hajiyata naci.
Ya Al’ameen yace “ay tunda rawar ido kasa gaba kakasa tsayar da mace guda ka aura ay kuwa kaida samun nutsuwa kaci abinci yadda kakeso cikin kwanciyar hankali babushi,dubekafa harkafara zama tuzuro”
dariya Sadeeq yatuntsire dashi yakalli gefenda MAHFUS yake saiyakuma fashewa da dariya,cikin muryar dariya
yace
“Todai badani kakeba yanzukam kanayi Dana gefen daman kane Dan naga alama soyake yamutu tuzuru,yakarashe maganar tareda kuma shekewa da dariyan shakiyyanci kad’an yarage yashake da loman abincin dayakai bakinsa.
Ya Al’ameen yace”ay garashi kaifa ba yarinyar dazaka gani bakace kanasoba Amma haryau kakasa fidda guda cikinsu,
Yace”saurin me kake kunkusa kusha biki dankuwa yanzu nafidda matar aure Abida zan aura,
Ya Al’ameen yace “Allah dai yasa dagaskene bayaudararta itama zakayiba,
Duk hirar dasuke d’inna MAHFUS baice dasu kalaba abincin da Aunty Rukayya tazubamasa ko kallonsa baiyiba,
Ya Al’ameen yalura dahakan sai yace dashi “Bismillah tareda nunamasa plt d’in abincin gabansa,
Kallo d’aya yayiwa abincin yad’auke ido batareda yace kalaba, har Sadeeq yagama cikin abincinsa shiko drink bai kurb’aba,
Sadeeq ko yasan hali shiyasama baice dashi komaiba,
Adaidaita ne ya’ajesu abakin get, koda suka fito kosallama batayiwa Aysha ba tayi wucewarta ciki, Aysha ko baki tabud’e tana binta da kallo daga bisani taketare titi tashiga gidansu,
Direct part 3 tanufa dasallama tatura kofar parlour, takusa kanta ciki tana isa tsakiyar parlour, tawurgarda jakar hannunta da bag d’inda talodo shopping inta aciki, tacire mayafin kanta da d’ankwalinta da takallimin kafarta duk tayi wurgi dasu atsakiyar parlour,
Jin karar wurga abu yasanyasu kallon inda karar ke tashi,sananin mamaki yacika shi
” itacefa shin wanna mutunce ko aljana to mekuma yakawota nan?yy tanbayar aransa saiyaji ransa gabad’aya yab’aci,
Murmushi Ya Al’ameen yy yace “shalele har andawo kenan?
baki taturo gaba tayarfe hannu cike da shagob’a
tace “Allah Ya nagaji tafad’a tareda zama hannun kujerar dayake,
Yace”badole kigajiba bayan ba’a mota kika tafiba duk kind’ibi kurar titi,
Sadeeq kam baki da hanci yabud’e yana kallon ikon Allah
Ya Al’ameen yakallita tareda yin murmushi yace “shalele bakiga ba’i ba kigaidasu.
tad’ago takalli inda yake nuna matan ita kwata-kwata batama sanda mutani agunba, kallon mamaki tashiga yimusu tabud’i baki dazummar yin magana,karaf suka had’a ido aiko tamurgud’a masa baki tareda wasa masa harara,tamike tsaye
Aunty Rukayya dake tsaye agefe tace “him waikingaji watakilanma fad’a kikanimo kikecewani wai kingaji,
buga kafa akasa tashiga yi tareda yarfe hannayenta tanafad’an Ya Al’ameen kagantako saikuma tasaki kuka.
Yace”ke Rukayya inarunki aina kikaganta tayi fad’an?
Yishiru abinki jekihuta kinji’
Kai tagyad’a sanna tajuya tahaura step anan tabar kayanda tawatsar dasu.
Haushi da bakin cikine yaturnike zuciyar MAHFUS aransa yace ashedai tsiyar asali tasamo yaja guntun tsaki afili,
Saiyanzu Sadeeq yadawo daga tafiyar wucin gadin dayayi azaune agun, yadawo dakallonsa kan MAHFUS wanda yahade rai kamar an aikomasa da bakin labari, saiya maida dubansa ga Ya Al’ameen
Yace” Al’ameen wannafa ya akayi naganta anan?
Ya Al’ameen yace “wa waikananufin shalele?
Yace “Eh..Eh hakadai naji kakira sunanta bantab’a ganinta anan bane,
Dariya Ya Al’ameen yy yace”Kai Sadeeq JUHAIFAH ce bakasaniba,
Zama Sadeeq yagyara yace wata JUHAIFAH kana nufin JUHAIFAH dana sani…………..
*Slm* *masoyana* *inamaisanardakucewa* *wanna* *littafin* *nasayarwane* *gamaibukatarsaya* *saiya* *tuntubi* *wanna* *number* *08034690723* *naira* 300 *kacal* *aturakatin* *mtn* *tawanna* *number* *08034690723* *kokumata* *asusun* *banki* *tawanna* *number*
*Sunusi* *yufuf* *Aliyu*
*0421042738*
*GT* *Bank*
SAI KA/KI TURA SHAIDAR BIYA TAWANNAN NUMBER 08034690723
Mommyn twins ceFollow this link to join my WhatsApp group: 🌺 BAZAURACE’ ITA!🌺
بسم الله الرحمن الرحيم
___________________________________
🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION🤝🏻
{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}
____________________________________🌺 BAZAURACE’ ITA!🌺
By✍🏻
Rasheeda S Director
~Free~ ~page~
*Wanna* *littafin* *nasayarwane* *gamai* *bukatar* *saya* *naira* *300* *kacal* *saika* *tura* *katin* *mtn* *tawanna* *number* *08034690723* *kokumata* *ta asusun*
*banki*
*Sunusi* *yusuf* *Aliyu*
*0421042738*
*GT* *Bank*
SAI KI/KA TURA SHAIDAR BIYA TAWANNA NUMBER
08034690723
🅿️2
Ya Al’ameen yace “itacedai,
Sadeeq yakuma washe baki yanafad’in “Kai lallai girma bawuya yaushene JUHAIFAH tagirma haka,kasanfa ni rabona da ita tun wani hutun dana taho daga india,Kuma lokacin tana yar piciciya,
MAHFUS dayacika harwuya, ganin yanda Sadeeq yaketa wani zakewa, yamike tsaye tareda zura hannayensa cikin aljuhun wandonsa, ganin haka yasanya Sadeeq mikewa shima
Sadeeq Yace “to bari mutafi saiwani lokaci kuma,
Ya Al’ameen yace “to mungode fa sosai.
Sadeeq yayiwa Aunty Rukayya sallama Ya Al’ameen yayimu SU rakiya hargurin mota harsanda sukafita agidan kafin yakoma ciki.
Amota kuwa Sadeeq saizuba masa surutu yake,yanafad’in gaskiya girman yarinyarna yabani mamaki,yaran na yaushe aka haifesu amma wai harsufimu baki, saiyakuma tunsuriwa da dariyar shakiyyanci yace “wlh harnatuna diramarku nad’azu Kai abin yabada kala.
Duk surutun da Sadeeq yake,azahiri jinsa yake abad’ili kuwa hankalinsa bayagun,dankuwa yayi zurfi acikin duniyar tunanin daya tafi,wacce tazame masa jiki,
Akoda yaushe idan yatuna sai hankalinsa yayi mummunar tashi saidai tashin hankalinsa nayau yafi nakullum ,dafe kansa yayi wacce keyimasa masifaffen tsarawa,
Cikin hatsala yace “ya isheka haka Sadeeq!.
Kunshe bakinsa Sadeeq yayi baikuma cewa komaiba
Saida sukayi nisa sosai sanna Sadeeq yajuyo yasaci kallonsa har alokacin fuskarsa ad’aure take,kiris yake jira yafashe, aransa yace him wanna mutumin idan yahad’e rai nikaina shakkar yimasa magana nake dan suffarsa gabad’aya canzawa take,
Ganin sunata tafiya baikuma San inda zai saukeshiba yasashi fad’in
“Man, gidanka zan kaika ko gidan Mommy?.
Shiru yy masa saida yad’au tsawon 10min kafin yace
“gidan Mommy .
Sadeeq yajuya akalar tafiyar tasu izuwa gidan Mommy dake Maitama
Wata tamfatsetsiyar gida Sadeeq yadanna hancin motarsa ciki,Kai Fan’s tsayuwar fad’amuku irin girma da tsaruwan gidanma bata lokacine,Dan saina cika page d’aya bangama kwararo muku bayaniba,akarshedai zancemuku kuhasasho dakanku.
Ko parking baijira yakarasaba yabud’e marfin motar yafita,
Cikin salon zolaya Sadeeq yace “mutumin babu ko ‘yar sallamar nanma, baikulashiba yayi shigewarsa.
Shiko yaja mutarsa yayigaba.
Asannu ya’isa jikin wata glass yad’aura hannusa ajiki saiga glass d’in taware gidabiyu,yashige ciki, katafaren parlour ne wacce tsaruwansa yawuci misali,bakajin komai sai tashin sanyi maihad’eda daddad’an kamshi ketashi,har ya’isa sakiyar parlour yanakokarin ketare cikinta saiyaji ance, “Kai MAHFUS.
Dasauri yajuyo danjin muryar mahaifinsa,yayi mamakin ganin mahaifan nasa zaune acikin parlour Amma haryawuce baigansuba,
Yajuyo ahankali ya isa inda suke tareda zama saman kafet kusa dakafan Daddynsa,
Yace”sorry Daddy banlura daku bane,
Daddy yatsura masa ido danson nazartar yanayin dayake ciki,daga bisani yy gyaran murya, yace”MAHFUS meke damunka?.
Saurin d’agowa yayi yace “wani abun kagani ne daddy?.
Daddy yace “sosaima kuwa tunda harka iya wucewa batareda kasan munacin parlourn nan ba. Mommy tace “gaskiya kam.
Murmushi yy yace “Daddy kawaidai bacci ne yacikamin ido ga gajiya, Sadeeq ne yad’ibeni yarikayawo Dani duk yagajiyar dani.
Daddy yace “ato tashi maza kajeka wasa ruwa saikaji dad’in yin baccin,
Toyace tareda mikewa yahaura sama inda zai sadashi da part insa dake cikin gidan.
Yanashiga bedroom yafad’asaman lafiyeyyen gadonsa wacce Tasha gyara saikamshi ketashi, yad’au tsawon mintuna kwance sanna daga bisani yamike zaune,asannu yashiga kwab’e kayan jikinsa,yarage dagashi sai boxer yafad’a bathroom yasakarwa kansa ruwa maisanyi batareda yacire boxer jikinsaba,rumsa idanunsa yayi dakarfi lokacinda ruwan kesauka azakiyar kansa, yacusa hannayensa cikin gashin kansa tareda yamusashi,cikin wata irin yanayi yataune lips d’insa nakasa,dogon tsaki yaja yacire hannaYensa akansa, yadunkule hannunsa tareda naushin d’aya hnnunsa,aransa yace “meyasa zuciya zaki d’auramin damuwa akan abunda baishafeniba?.afili yakuma furta, meyasa?meyasa?meyasa!?.yafad’a cikin karaji,Wanda saida ilahirin bathroom d’in yad’auka amon muryarsa.
Yajima sosai kafin yafito daure da towel akugunsa wardrobe yabud’e yaciro farar jallabiya yasaka sanna yahaye saman bed bajimawa bacci yad’aukeshi.
Numfashi Mommy tasauke tace “Alhj ni lamarin yaronnafa yafara isata kai bakaga saiwani sussunkuyar dakai yakeba, waidan karmu had’a ido dansabo nayimasa magana akan aure,harsai yaushene zaisan yagirma,
Sa’o’insafa daga mai yara ukune saibiyu, hatta kannensa Wanda yagirme musu duk sunyi aure harda yaransu,mu harsai yaushene zamuga jikokinmu?.
Zama Daddy yagyara yace “him ai bake kad’ai abun kedamunkiba, musamman idan nadubi kaina yanzu shekaru sunfara ja,yakama ta kam ace zuwa wanna lokacin ya’ajiye iyali,
Kwanaki danayi masa zancen, sainazamo surukinsa dazarar yaganni saiya nimi boyewa haka yarika wasan buya dani,
Mommy tace”to ai nima kwanaki danayi masa zancen guduwa yayi yabar kasar baki d’aya,baikuma dawowaba saiwanna karon.
Dariya Daddy yayi yace” Son Kenan d’anrigima, ammadai kidaina masa masa da maganar dayawa, adai bishi ahankali harya fidda matar dayakeso.
“Haba Alhj goyamasa baya kake?, to idan mukaci gaba da sakamasa ido ay saiyaji dad’in cigaba dazamansa ba matar,
Daddy yace “bawai inanufin azuba masa ido kwata-kwata bane,kinsan shi ba mai yawanson damuwa bane, so kada yawan yi masa maganar yasakashi shiga da uwa, so kisan yadda zakirika yimasa maganar bawai koda yausheba, ay yamallaki hankalinsa yasan dai-dai da rashinsa,lokacine kawai baiyiba idan lokaci yayi saikiga komai yawuce.
Hmm kawai Mommy tace dantasan dama bagoya mata baya zaiyi amaganarba, saidai yabi bayan d’an nasa.
Daddy irin iyayennan ne masu matukar son ‘ya’ya amma son nasu baya hanasa yimusu tarbiya dai-dai gwargwadon yadda addini ya shar’anta..
Barcinta take cikin kwanciyar hankali, firget tamike kamar an zabureta,sanye take da doguwar rigar bacci pink, takalli agogon dake d’aure akan dorowa 2:00pm,
mika tayi tareda yin salati,
tamike tsaye tashiga bathroom, brush tafara yi kafin tagudanar da wanka, sanna
tad’auro alaula tafito,tashinfid’a sallaya tagabatar da sallah,koda ta’idar gaban miro tazauna,mayuka tashiga shafawa ilahirin jikinta masu sanyin kamshi,sanna tayi simple makeup, Masha Allah kyawun ta saiyadad’a baiyana,ta isa gaban wardrobe taciro riga da sket na atamfa d’inkin opin shoulda tasaka, bakaramar daukar fatarta yayiba, tafito parlour babu kowa saitawuce saman dinning,tashiga bubbud’e tarin kulolin dake jere asaman dinning d’in, yamusa fuska tayi saitakuma janyo wata kula tabud’e. had’ad’d’iyar chips ne wacce taji kayan masarufi kala-kala, tazubashi cikin plt sanna tahad’a tea a cup,tanaci tana kurb’ar tea d’in bawani mai yawa taciba,tamike tasauka asaman dinning d’in,fita tayi acikin part d’in gabad’aya, tanufi part 1.
Tundaga kofar shiga part d’in tafarajin hayaniya,sauri takara Dan jin sautin muryoyin dake tashi acikin parlour,da sassarfa tashige cikin parlour, tana fad’in “oyo yo my brother’s.
Saikuma taja tatsaya tareda hard’e hannayenta akirji tawani turo baki gaba, gabad’aya hankalin ‘yan cikin parlour yadawo kanta,dasauri wasu maza guda biyu suka taso suka rungumeta
Tareda fad’in
Oyo yo my shalele saiyanzu aka tashi abaccin?.
Cikin muryar shagwab’a tace “ay ni baruwana daku tunda yanzu kundaina sona,Ya Al’ameen ne kad’ai da Abbana sai Ammee na da Baby twins d’ina kad’ai kesona yanzu.
Ido suka ware dukansu biyu suka had’a baki wajen cewa “waya fad’amiki mun daina sonki!? Suka karasa maganar tareda lankwasa Kai cikin santsar so dakaunar kanwar tasu. Hassan da Husain dasuke cinyar Ammee suka mike aguje sukazo inda su JUHAIFAH suke tsaye,Husain yace “uncle muma kundaina sonmune?
Hassan yace “Eh basu kawomana chocolate ba sundaina son mu.
Gabad’aya parlour yad’auki dariya Ya Mujaheet yace “lalala wane mu chocolate d’inku yana nan a ajiye namancene ban ciro muku ajakaba, dagudu suka koma jikin Ammee suna fad’i yee uncles suna son mu.
Hannayensu tarike, tad’ago Kai takalli d’ayan dake gifen damanta tace ” Ya Mujaheet,sanna tajuya d’aya gefen tace “Ya Jabeer, tomeyasa dakukazo baku nemeniba?.
Takarasa maganar tareda bubbuga kafa akasa tana mitar shagwab’a
Ya Mujaheet yace “mun isa muzo bamu nimi shalele JUHAIFAH ba,ai muna sauka d’akinki muka fara shiga mun taddaki kina bacci ne shine muka zonan Dan mubarki kiyi barcinki mai dad’i.
Ya Jabeer yace “kwarai kuwa Dan bamaso mukatse miki baccinki shiyasa,
Tace “au to shikenan zan hakura Amma da sharad’i,
sukace “to muna jinki.
Tace “to sai Ya Jabeer yamin faretinsu na sojoji tukun,
Ya Mujaheet yace “to Jabeer yimaza kafara,
Ya Jabeer ko yadaddage yarika zabga fareti asakiyan parlour,itako sai dariya take da salle kamar Baby, su Hassan da Husain suka rika tayata,idan ya ce ya isa?.saitace bai isaba yakara.
Abba dayaga abin bana kare bane, sai yace “taho nan Mamana kibar yayan naki yahuta haka.tace “to. tajuya zata gun Abba saita washe baki dafad’in laa Aunty Nuwaira dama dake akazo ay bangankiba?.
Nuwaira takalli mijinta wato Ya Mujaheet, sanna tamaida kallonta ga JUHAIFAH
Tace “inakuwa za kiganni bayan yayun naki sun lullub’eki,aranta kuwa cewa take lallai JUHAIFAH tanaganin kauna da soyayya agun wanna family.
taje kusa da Abba tazauna,nan shima tashiga zuba masa shagwab’a,yayinda dukansu suka biyemata,
Hira sosai suka bud’e har saida lokacin sallar la’asar yayi kafin, Abba da Ya Al’ameen Ya Mujaheet Ya Jabeer,sukanufi masallaci, Ammee tashige ciki itama dan gudanar dasallan, Aunty Rukayya takoma part 3 part inta kenan,Aunty Nuwaira itama tatafi part 2 wanda yake part intane idan sunzo hotu da mijinta.JUHAIFAH ko, kin tafiya tayi, anan toilet in parlour tayi alaula takuma yi sallan acikin parlour, nan suka dawo suka sameta,sanna suka d’aura daga inda suka tsaya, lokacin sallace kad’ai ketadasu, har karfe 11 dare suna gun,saida Abba yace dasu kowa yaje yakwanta saida safe Kuma. kafin taron ta watse..
Shirin barin kasar yake tayi Dan hutunsa yakare,kuma ayaune jirginsu zai d’aga dakarfe 12 nadare izuwa kasar Canada zaune yake abakin gado yana shirya kaya acikin a kwati,Mommy taturo kofa dasalla,ya Amsa tareda rufe akwatin yaturashi gefe, ta’isa tazauna kusa dashi,
Yace “barka da dare Mommyna.
murmushi tayi tace “yauwa Son, anakan Shirin kenan?
Kwantar da kansa yy akafad’arta sanna yace “Eh Mommy,Allah ni nama rasa meda me zansa acikin jakarna, Mommy kinfasan ban iya shirya kayaba, gashiyau kinki shiryamin,
Goshinsa tadungure tareda fad’in “ay ko bazan sake shirya makaba Dan yanzu kagirma,saika koya dakanka,
Yace “to Mommy yazanyi na iya bayan bansaba yiba,
“To basaika aje wacce zata rikayimakaba, dan nikam narigada na sallameka saidai naji dana autana Zahara”
“To nikuma yaushe zan d’auki ‘yar ay ki dannasan bazama ta iya yanda Mommyna takeyimin ba,ko acanma idan JC yagyaramin d’aki sainasashi yakuma harsau uku,Amma baya tab’a yin kyau kamar naki,
Mommy tace “ay ko bazai tab’a yin kyauba danku gyaran gida sai mace,macenma na musamman,
Shiru yayi danjin zancen Mommy yafara canza salo, aransa yace ” to Mommy zata kawo wata zancen kuma, bai idda zancen zucin dayakeba yaji tace
“MAHFUS har idan kuwa kanaso arika yimaka gyaran dakakeso tokuwa saika aje matar aurenka agida,daganan zaka rika samun duk abinda kakeso,
cikin ko inkula yace “to Mommy menanima narasa dahar saina aje wata kafin nasamu? inada iyaye gata gakuma dukiya tome yaragemin Kuma,
tace “banason shiririta Dan bashi yakawoniba, nazone akan zancen wanna yarinyar fareeda dan banaso katafi batareda naji wata kwakkwara bayaniba,kadaisan tana sonka, inason hutun dazaka Kuma dawowa yazamana shine lokacin aurenka da ita,Dan wanna karon banaso kakuma wasamin kasa a ido, Dan munrigada mun gama magana da mom inta.
Shiru yy batareda yace komaiba,itama shirun tayi,tareda tunani iri da kala acikin zuciyarta,
zuwa can yace
“Mommy abar maganar fareedar nan Dan Allah nifa basonta nakeba,
Cikin hasala Mommy tace “gayamin wakakeso fad’amin nace!?wlh MAHFUS kaji tsoron duniya kada rud’inta tad’ebeka takaika tabaroka,kaduba tulin shekarunka Amma ace bakada mata,yanzu kahaura shekara 30 fa,kada kasa duniya tafara zarginka, MAHFUS! mekeyimaka dad’ine a irin wanna rayuwar?,yau kimanin shekaru biyar kenan kullum akan abu d’aya ake, mata biyar aka nima maka harsai ansa ranar aurenku kace Kai kafasa.saikuma tasassauta muryarta,kanaso har saimun mutune kafin kayi auren?
Tunda tafara maganar shiru yayi batareda yace komaiba sai tsura mata ido dayayi aransa yace “wato Mommy tana zargin ina mu’amala da mata awajene shiyasa take wanna zancen,murmushi yy tareda riko hannunta yace” Allah yahuci zuciyarki Mommyna in Allah ya yarda idan nadawo zan kawo miki matar dazan aura,
Tace “idan baka kawo bama wanna karon babu gudu baja dabaya aure kuwa ba fashi dakoma waye,
tamike tafita ad’akin ,
Ciccusa kayan yayi acikin akwatin yarufe, sanna yashiga bathroom yayi wanka tareda yin alaula yafito,shafa’i da wutiri yy sanna yashirya saf cikin kananan kaya, yayi shar dashi kamar wani tauraru,yakalli agogon dake d’aure ahannunsa lokacin saura minti 30 jirginsu yad’aga,
yajanyo jakarsa yafito parlour,
anan yatadda Daddy zaune yana kallon labarai a TV,Mommy nazaune agefensa tana had’a masa coffee,
Daddy yace “yauwa yanzu kuwa nake kan zancenka kagafa saura mintunane jirgin yatashi, kayi hanzari kada kab’ata lokaci,
yace “to Daddy,
Sukayi masa fatan alkhairi yafita, yanafita farfajiyar gidan cikin hanzari ya’u driver yataho ya amshi jakarsa yasashi amota sanna yabud’e masa gidan baya, yashiga,sanna yazaga yashiga mazaunin driver yaja motar sukabar gidan, suna isa airport batareda b’ata lokaciba jirginsu tad’aga, ya’u driver kuma yakomo gida,
Tunda MAHFUS yatafi baikara waiwayo Nigeria ba haryashafe kimanin wata 5,duk sanda sukayi waya da Mommy saiyace mata zaizo acikin satinna, Mommy data gaji dasa mata rana dayake saita madaina kiransa, waiko dun zaiji wani abu akan hakan yadawo,shiko dad’ima yaji data daina kiransan,
Mommy kam babu irin tunanin dabatayi akansa,waya tad’aga takira abokinsa Sadeeq, tace yazo tana nomanshe,bareda b’ata lokaciba Sadeeq yazo gidan kasancewar masu gadin gidan sun sanshi haka bai bashi wahalar shiga gidanba,a parlour ya iske Mommy cikin girmamawa yarisina yagaisheta,ta ammasa cikin sakin fuska tareda tanbayarsa ya mutan gidansu?yace “lfy lau.tace”to madalla,
“Sadeeq.takira sunansa,
yace “na’am Mommy,
Tace “Sadeeq inaso nayimaka wata tanbayace,Amma kadubi girman Allah kafad’amin sakanin ka da Allah, kada karage koka boyemin wani abu, kasani idan kaboyemin bafa zaka boyewa Allah ba!.
Yace “insha Allahu bazan boyemiki ko narage miki daga abinda nasaniba,
“To madalla,
“Sadeeq inaso kasanar Dani abunda bansaniba nagame da abokinka,
Sadeeq yace “Mommy banfahim cekiba,
Tace “inaso nasan da wasu irin mata MAHFUS yake huld’a dasu awaje, wanda har yakejin baya sha’awar yin aure,
Sadeeq yace “subhanallahi Mommy wayafad’a miki wanna kazamin zancen,
Mommy tace “bafad’amin akayiba ,ninake zargin hakan,to inba hakaba maizaisashi kinyin aure awanna shekarun nasa,
Murmushi Sadeeq yy tareda fad’in oh Mommy shekarun nasa sunkai hamsin ne da har akafara kwatance dasu, akwai wad’anda suka fishi shekaru sunanan kuma haryanzu basuyi aureba,
Tace “au kaima shiriritar zakayimin irin nashi,shiyasa kaima kakenan kunsaya garin shiririta kun kasa fidda mata ku aura,tanbayarka nayi kabani amsa,
Zamansa yagyara tareda tankwashe kafarsa,yace wlh tunda nakeda MAHFUS bantab’a ganinsa tsaye dawata dasunan soyayya ba, bare har wani alaka tashiga sakaninsu ba,wlh Mommy ina fad’amiki zancenna ne harcikin raina,
Numfashi tasauke tace “toko bashida lfy ne?
Yace “todai gaskiya wanna amsar saishi dakansa,
Tace “katabbata abinda kafad’amin gaskiyace?.
Yace “wlh Mommy duk abinda nafad’amiki babu karya cikinta, harcikin raina iya gaskiyar kenan.
“To shikenan zaka iya tafiya,
Yayi mata sallama yatafi.komawa tayi tajingana dajikin kujera,”tabbas idan kuwa MAHFUS baya niman mata awaje,to yatabba bashida lfy kena,taja numfashi tasauke tad’aura dafad’in to Amma kuwa yayi wauta dahar yabar irin wanna cutar ajikinsa batareda yasanar mana mu iyayensa mutai maka masaba. tajima sosai zaune da tunane-tunane acikin ranta har Daddy yadawo daga gun ay ki, sannu da dawowa tayimishi tareda karb’ar jakar ahannusa tashigar ciki,tawuce bathroom tahad’a masa ruwan wanka sanna tafito tace dashi yaje yawasa ruwa,kafin fitowarsa tad’auko abincinsa daga saman dinning tasauko dasu sakiyar parlour,
bayan yayi wanka yashirya yafito parlour nan yatadda Mommy zaune,zama yy tazuba masa abinci,yanaci suna d’an tab’a hira,harya kammala.
Tahad’a kayakin takira hanne mai aiki takwashi kwanukan takaisu mawanki.
Shiru gurin yad’auka bawanda yakuma magana acikinsu, yayinda Daddy yakafe TV da ido yana kallon labaran da ake, Mommy tanisa cikin raunanniyar murya,tace”Daddy!. Juyowa yy yana fuskan tarta,kacokam yamaida hankalinsa gareta,Dan jin sunar data kirashi dashi,duk sanda takirashi da sunan da yaransa suke kiransa dashi to lallai wanna rana tana cikin damuwa ko maka mancin haka,tana kuma bukatar tai makonsa,tun shigowarsa yalura da akwai wani abunda kedamunta, cikin nuna kulawa
Yace “ya’akayine Mommyn MAHFUS da Zahara?mata agidan Alhj Tukur Shali Daddyn MAHFUS da Zahara,murmushi tayi danjin kirarin da yayimata, shiyake yimata aduk sanda yafahimci tana cikin damuwa,
Tace “akan batun yaronnane,kamardai yanda kasanida,yanzu watannisa shida datafiya,duk sanda nakirashi saiyacemin zai dawo asatinna,
Ni inaganin d’anna bayada cikakkiyar lfy ne,shiyasa baya da sha’awar yin aure, har yaushene zai aje iyali,su biyu Allah yabani,akoda yaushe ina addu’ar subiyunna suzamo sanadin ninkuwar zuri’a,takarasa maganar cikin rauni.
Kai ya jinjina cikeda tausayin matar tashi,yasan tana matukar son haihuwa da yawa,Amma Allah daya tashi bata saiyaba ‘ya’ya biyu rak, cikin tattausar lafazi maicikeda kwantar da hankali, yace”amma kuwa MAHFUS yy wauta ace cuta nadaminka baza kafad’a atareshi tunda wuriba, ki kwantar dahan kalinki indai akan wannane kada kidamu,nida kaina zansashi yadawo sanna munima masa magani,inya warke saiyayi aurensa,kinga daganan saiki samu ‘yan jikokinki.
Atake agon yad’aga waya yakirasa, bugu biyu yad’aga tareda yin sallama,Daddy yace “Son ya’aikin dai?, yace lfy lau Daddy komai natafiya normal,yace “madallah.
Son yaushene kake free inaso kazone mud’an tattauna.
Yace ” week inna ina free,sai last week zanshiga UK.
Ok to saika zo Dan muyi maganar,
Yace “toh
Harsunyi sallama yy saurin cewa “yauwa Daddy Mommy tayi tafiyar datace zatayinna kuwa?.
Daddy yakalli gefen datake saiya ga takafeshe da ido,saiyayi murmushi tareda fad’in a’a ammadai zatayi inaga ko gobe ko jibi idan Allah yakaimu,
Yace “to nizanzo gata,
Daddy yace ” Allah yakaimu,sukayi sallama yakashe wayar.
Mommy tace”him wato harma tanbaya yake kona tafi saboda bayaso yazo yasameni, dan inagayamasa gaskiya.
Daddy yace”haba kada kifassarashi dawani nufi mana,tunda yace zaixo to bashikenanba,Kuma ay balaifinsa bane ciwonne kesashi wanna guje-guje da b’oye-b’oyen na,Allah sarki Son insha Allahu zaka sami lfy.
Itadai shiru tayi bata kuma cewa komaiba.
Yau asabar, yakasance itace ranarda MAHFUS yasa nazuwa Nigeria,karfe shida na yanmacin ranar, jirginsu tasauka a airport dake cikin birnin taraiya Abuja,
Daddy yatura driver yad’au shi,koda ya iso gida,drect bedroom insa yanufa,yarage kayan jikinsa sanna yafad’a bathroom,wanka yy tareda alaula yafito,lokacin akakira sallar magrib saiya shirya yatafi masallaci, wanda yake can bakin get in gidan,saida akayi sallar isha,kafin yakomo gida,a parlour yatadda Mommy da Daddy da Zahara,
d’an dim yy Dan baiyi zaton ganin Mommy,saikuma yayi ‘yar karamar dariya yace “Mommy ashedai kinanan?yafad’a tareda karasawa inda suke.
Tace “yo kayi zaton natafi ko?to inanan, gashi kagama gudun kadawo kasameni,
Murmushi kawai yayi,
Zahara tace “Ya MAHFUS yaushe kazo? dan banga isowarkaba,
Hararanta yy tareda fad’in to sai akace dole saikinsan isowar tawa? wuce kibarnan dashegin gulma,
“Auta jeki d’akinki karya dakarmin ke kinji,cewar Mommy,tace to sanna tamike tayi shigewarta d’aki,
Zama yy tareda gaida iyayen nasa,
Daddy yace “kaci abinci kuwa Son?.
Yace”Eh naci d’azu acikin jirgi, Kai haba yanzu nake fad’a ba tun d’azuba,yace “to ay Daddyn banajin yunwane yanzo saidai ko zuwa anjima,
“Toshikenan.
“MAHFUS,Daddy yakira sunansa,damamaki ya amsa Kiran, danjin yadda yakira sunan nasa.Daddy yagyara Zama taredayin gyaran murya yace”musu waye naka?da mamaki yakalli Daddyn sanna yace “ku iyayenane.
“To madalla,mu iyayenkane da ubangiji ya d’auramana nauyin tarbiyantar dakai, tufatar dakai, ciyar dakai, shayar dakai dakuma kula da lfyrka,
tundaga kan ranar da aka haifeka harzu yau,
Daga kanyau zamuci gaba da kula da dukkan al’amuranka harzuwa karshen rayuwarmu,
MAHFUS bakada lfy zamukuma yijinyarka kamar yanda nauyin yin hakan yarataya akanmu.
Dasauri yad’ago yace “Daddy banfahimci abinda kknufiba?
“Inanufin bakada cikakkiyar lfy wacce itace tahanaka yin aure,Amma nayi Mamakin yadda amasayinmu na iyayenka ka kasa fad’amana wanna babbar masalar mumagan ce maka ita tunda wuri,Amma yanzuma guri bai kureba,akwai asubitoci da guraren bada magani irinna gida,Dan haka gobe idan Allah yakaimu zamu fara jarraba dukansu har Allah yasa mudace.
Tunda Daddy yafara maganar yalula duniyar tunani,”wato suna tunanin wai ciwone yahanani yin aure,saiya sinci kansa dayin murmushi afili,
Mommy tace “toh lailai watoma dariya aka baka,Kai koda munkama abun baiyi?
Yace “nifa lfyta kalau babu wani abunda kedamuna.
“Kajimin shashancin banza Dana hofi muzaka kawowa tsiya ga Abu afili kacewai bahakaba.
Daddy yace”a a dakata mana kibishi ahankali dai,idan akace za a takurasa to dame zaiji guda,
Kai Son kanajiko?
yace “Eh Daddy.
tashi kaje ka kwanta sai gobe zamuje afara baka taimako a asibiti…………..
[…] Bazawara Ce Ita Hausa Novel Complete […]