Littafan Hausa Novels

Ban Dace Dashi Ba Hausa Novel Complete

Written by Hausa_Novels

Ban Dace Dashi Ba Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

BAN DACE DASHI BA

By Hafsat Hisham

 

 

Page. 1

 

 

_Bismillahir Rahmanir Rahim_

_Da sunan Aallah mai Rahama mai jinkai_

_In the name of Aallah the Beneficent the Merciful_

 

 

_After the successful of (sune suka janyo min) now we are back with (ban dace dashi ba)_

 

Abroad,

Sanye take da dogon wando da rigar sanyi mai hood, ta rufe kanta da hular rigar wanda ya rufe rabin fuskarta tareda kitso da aka yi mata kirar kalaba wanda ya bazu, kanta a kasa take tafiya tana sauri, kafin ta ankara taci karo da mutum, under her breath tace,

Nufin Allah Hausa Novel Complete

“Sorry….”.

Maheer ya bita da kallo cike da mamaki, Kasim ya tab’oshi saying,

“Let go…”.

Maheer yace, “Wait… Wannan yarinyar da nayi karo da ita muryarta da kammanin fuskarta sak irin na abokina ne wanda nike nema tsayin shakaru…”.

Kasim yace, “Kana nufin Mujahid, yaron nan da ya kasa fita daga tunaninka…”.

Maheer yace, “Yeah… Duk da sau daya na tab’a haduwa da yaron nan amma ya kasa fita daga tunanina, kallo daya zakayi mashi ka fahimci yana cikin damuwa, har zuwa yanzu ina jimamin halin da zai kasance a ciki…”.

Kasim yace, “Wannan kuma kai da bakinka kace min macece…”.

Maheer yace, “Ehhhh macece saidai muryarta da kammanin fuskarta sak irin nashi ne, but ita wannan tafi kama da black Americans, bata yanayi da en Nigeria… Saidai zuciyata tana ayyana min cewa zata iya kasancewa tsanin da zai sadani dashi…”.

Kasim yace, “Ta ina zaka iya samota a kasar nan?”.

Maheer yace, “Wait and See…”.

Kafin Kasim ya ankara Maheer ya b’ace babu shi babu alamarsa, under his breath yace,

“What’s so special about that boy da har Maheer ya kasa mantawa dashi…”.

Direct ta wuce inda locker take ta bude ta dauki abun da yake a ciki sannan ta juyo, Maheer yayi nemanta har ya gaji yayi tsaye yana bin wajen da kallo wanda yake dauke da floors da yawa, samunta abu ne mai matuk’ar wahala a gareshi, idan ya sameta miye zaice mata, ji yayi an taboshi yana juyawa yaci karo da ita, da turanci wanda yake zaune akan harshenta tace,

“Ka tare min hanya…”.

Da sauri ya matsa ta wuce tana tafiya da sauri-sauri, ya bita da kallo fuskarsa dauke da mamaki the more yake hango fuskarta the more yake ganin Kammanin da takeyi da Mujahid, abokinsa….

Kafin ya ankara har ta b’acewa ganinsa, ya dafe kai saying,

“Shit…”.

Kasim ya k’araso saying,

“Ka ganta ne…”.

Maheer yace, “Na ganta saidai na kasa mata magana…”.

Kasim yace, “Dama meyyy zaka ce mata? Ka manta da wannan abun…”.

Maheer yace, “I can’t… Momcy kullum cikin maganarsa take kamar yadda na damu hakanan itama ta damu…”.

Kasim yace, “Let go…”.

Direct suka wuce Villa dinsa da suke a zaune, tun daga wannan lokacin tunaninta ya addabi zuciyarsa, yana rufe idanu zai hango fuskarta a lokacin da tayi crossing dinsa ta wuce, sai tunaninsa ya koma kacokan a kanta, wayarsa ce tayi ringing ya duba yace,

“Momcy ce…”.

Kasim yace, “Allah sarki Momcy, idan kun gama ka bani mu gaisa…”.

Maheer yayi picking call din saying,

“Momcy… Mujaheed…”.

Momcy tace, “Did you see him?”.

Maheer yace, “No, na hadu ne da wata black American, fuskarta da muryarta sak irin nashi ne kuma zuciyata tana ayyana min cewa zata kasance hanyar da zan hadu dashi…”.

“Da kuwa nayi murna, yaron nan a kullum dashi nike kwana dashi nike tashi, idan na tuna yadda yake bleeding, Allah ya kareshi a duk inda yake… Kayi magana da ita…”.

Maheer yace, “No amma zanyi k’ok’arin ganin na sameta… Kasim yana ta hararena domin ban bashi ba kamar ba ya da wayar kiranki…”.

“Ba yarona mu gaisa…”.

Maheer ya lumshe idanu tareda mik’a wayar wa Kasim, yayi zurfi a tunani yana k’ok’arin nemo hanyar da kai k’ara haduwa da ita a wannan kasar mai girma….

Tun daga wannan ranar tunaninsa ya koma a kanta, kwata-kwata ya daina tunawa da abokinsa Mujaheed, abun har tsoro yake bashi….

************

Maheer yana rangadi a daya daga cikin wurarensa dake a kasar, yayinda bodyguard dinsa suke mara masa baya, still yayi a sanadin hangota da yayi zaune tana sirfing coffee, tana sanye ne da dogon wando da riga wacce ta tsaya mata a daidai kugunta, kitson dake a saman kanta yayi baya ya bazu a gadon bayanta, kitson yafi mashi kama da zane amma yana ganinsa akan en boxing, smile ne yayi escaping akan lips dinsa yayi taking steps tareda jan kujerar dake opposite da ita ya zauna yana mata murmurshi saying,

“Hi…”.

A hankali ta d’ago tana kallonshi da dara-dara idanunta, tace,

“What? Did you want to sleep with me… You speak hausa, Right?… Ba haka nike ba, kaje inda suke, har wawasonka zasuyi sai ka zab’a ka darje sannan…”.

Maheer kallonta yake cike da mamaki idanunsa a ware, jin hausar Nigeria tar a bakinta, saida ta watsa mashi wani mugun kallo sannan ta zaro kudi daga pocket din wandonta ta ajiye akan table ta mike tareda taking step daya zata wuce, Maheer ya mike da sauri tareda kama hannunta saying,

“Please…”.

Kamar walkiya ta juyowa tareda sakar mashi masu nausi (punch) a fuska saida wutar kansa ta dauke na wasu seconds, ya tafi hutun rabin lokaci, yayi still yana kallonta cike da mamaki jin nausinta ya zarce na wasu mazan, cikin ransa yace,

“Karfi ne da ita…”.

 

WhatsApp 09169472057

 

 

Hafsat Hisham

About the author

Hausa_Novels

Leave a Comment