Littafan Hausa Novels

Baitul Jinn Hausa Novel Complete

Written by Hausa_Novels

Baitul Jinn Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

BAITUL-JINN

 

 

LABARI DA RUBUTAWA

 

ZAINAB SALIHU YARIMA ( SARAUNIYAR KANAWA)

 

 

 

GODIYA

 

Dukkan yabo da godiya ta tabbata ga Allah Subhanahu wata’ala da ya bani ikon zuwa muku da sabon Littafina mai suna Baitul-jinn, Allah ya bani ikon rubuta abun da yake dai dai ka haneni da rubuta wanda ba dai dai ba Ameeen.

 

Rashin Haihuwa Hausa Novel Complete

 

 

BAYANI

Wannan littafin ƙirkirarren labari ne mai cike da abun tsoro, wa’azantarwa da ilmantarwa da sauran darussa da dama wanda zaku gani, sannan akwai ban dariya sosai ku dai kawai ku biyo alƙalamin ƴar mutan zazzau, Ban yarda wani kuma ya juya min labarina ba ko a ɗoramin a wata manhaja ba tare da izinina ba saboda haka a kiyaye don Allah.

 

 

SHAFI NA UKU

 

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEEM.

 

 

BIRNIN DAMASHKASH

 

 

Kande ce take zaune a tsakiyar ɗakinta cikin tsakiyar salasainin dare tana wasu surkulle tana zagaye wani madubi can wani haske ya mamaye ɗakin da jikin madubin fuskar wata tamikakkiyar tsohuwa ce ya bayyana a jikin madubin duk da ba’a ganin fuskar da kyau saboda gashi da ya sauko ya rufe mata fuska, kwayar jan idon ta kawai ake hange, tana riƙe da wani sanda mai tsananin walwali tamkar na zinare, tsohuwa ce sosai saboda har rankwafawa bayan ta yayi, ɗago da gwala gwalan jajayen idonta tayi ta buɗe baki cikin amon sauti ta fara magana, ganin abun da suke bin bakinta shi ya tsoratani na kusa sakin alƙalamin rubutu na amma da yake kun san ni ɗin jaruma ce, tuni na dake domin cigaba da kawo muku mai zai faru, ban farga ba naji sautin wannan tsohuwa tamkar saukan aradu tana faɗin cewa, “dole ki ƙara haƙuri kande ina sane da duk wani uƙuba da Hajiya Nazla take gana miki a gidan nan, amma ki sani ta haka ne kaɗai zai kaimu ga cikan burin mu zamanki a gidan nan, sannan kuma tabbass alamun nasara ya fara tunkaro mu domin yanzu haka na fara samun wasu bayanai daga Ruhin da ke tare da ke, domin duhun da muke gani da in muna bincike yanzu ya fara washewa, saboda haka kar muyi gaggawa, domin alkaluman zafi sun nuna mun cewa tabbas a cikin gidan nan za’a haifi yarinyar nan, kuma ke nake so ki karɓi haihuwar, sai dai matsalar har yanzu na kasa gano wacece zata haifi ƴar.!

Ƴar tsohuwar nan ta ƙarisa magana tana taune kunamun da suke bin gefen bakinta, ajiyar zuciya Kande ta sauke ta fara magana, “amma uwargijiyata kina ganin zamuyi nasara burin mu zai cika, nifa duk jikina yayi sanyi yau kimanin shekaru Ashirin da takwas ina aiki a gidan nan amma kullum ce mun kike lokaci ya kusa zuwa amma har yanzu shiru.”

“Hhhhhh ke Kande kin san ba’a Musu da ni kuma duk abun da na faɗi zai faru to dole sai ya faru.!

Tana gama faɗin haka ta ɓace bat hasken ɗakin ma ya ɗauke baki ɗaya duhu ya mamaye ɗakin.

 

 

 

******************

ƘAUYEN JEKA NAYIKA

 

 

“Ya za’ayi ma a ce wai an girka abinci daga ajiyewa a nan an cinye alhalin mu kaɗai ne a gidan, kawai rainin wayau ne na Zeey zeey yau ya motsa don taga bamu iya girkawa ba, to kowa kawai yaje ya sha cornflesk ko tea duka kichin suka nufa don samun abun da zasu ƙarya ga mamakin su suna shiga kichin suka ga abinci a jere a kan kantar kichin ɗin, basu tsaya wani dogon tunani ba suka baje a nan kichin ba bissmillah ba komai suka hau cin Abinci.

 

Wani kyakkyawar saurayine santalele tsayawa misalta muku kyawun shi ma ɓata lokacine, yana kishingide a kan wani lafiyayyen kujera na sarauta, gefen shi wasu zuƙa-zuƙan ƴan mata ne suke ta rausayawa gefe guda kuma wata ce take mai tausa wata kuma tana bashi fruit a baki, wani basamuden Aljani ne ya zo ya zube gaban Yareeem bakin shi na rawa yake faɗin, “Allah ya taimaki Yareeman Aljanu da Mutane, sarauta a jininku yake kun mulki Aljanu kun mulki Mutane, gaba salamun baya salamu, ina wani shugaba wanda ba kai bane babu shi, albishiri nake maka an samo wannan yarinyar da zata haifo maka muradinka kuma cikar burinka….✍️✍️✍️

 

Yau kuyi hakuri da ni ba yawa typin, amma in har naga ruwan comment sannan kuje Youtube chanel ɗin don girman Allah ku danna mun subscribe ga link can a sama, don Allah ku taimaka.

 

More subscribe more posting

 

Zeeey ƴar mutan zazzau ce

About the author

Hausa_Novels

Leave a Comment