Littafan Hausa Novels

Badi ba rai Hausa Novel Complete

Written by Hausa_Novels

Badi ba rai Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

Badi ba rai Hausa Novel Complete

 

 

MRS SADAUKI

 

 

FCWA

 

 

 

1 to END

 

***LA GRANDE HÔPITAL DE MARADI***

 

 

“Wayyo Allah Ummana mutuwa zan yi,zai kashe ni don Allah ka bari wayyo na banu na lalace! “wani ɗan matashin saurayi da ba zai wuce 26years ba yake wani irin zabura yana kuka,wasu likitoci huɗu sun ɗanne shi yayinda wani Dr ke tura yatsun shi a duburar saurayin wasu ruwa suka fara fitowa, ƙuraje duk sun caɓe wurin babu kyawun gani .

 

Dakika Biyar Hausa Novel Complete

Ƙara tura yatsun na shi Dr ya yi a karo na ba adadi sai ƙoƙarin maida duburar yake amma abu ya cutura ganin saurayin na wahala yace “ku sake shi ina zuwa” likitocin da suka dannesa suka ja ba,shi kuma Dr yana fitowa da sauri wata mata ta tare shi ta na cewa “ya mutu ko?don Allah ka faɗa mini mine ne ke damun shi?”kallon matar yayi tana sanye cikin wata dakakiyar gizna blue kana ganinta kasan nera ta kwanta babu wata alamar wahala a tattare da ita.Da hannu ya yi mata alama da yana zuwa wani room ya shiga ya fito ya sake koma ɗakin da ya fito da farko.

 

 

Reza ce sabuwa dal ya fiddo cikin gidan ta sai allura da zare,wani marayen kuka matashin ya saki jin Dr yace aƙara kwantar dashi ga kuma reza a hannun shi,ihu ya soma yana neman agaji lokacin da Dr yake ɗaiɗaye matatar fatar wurin jini sai zuba yake kafin yasa magani ya wanke wurin ya tusa masa auduga.

 

 

Turo shi akayi bisa gado na maras lafiya aka nufi bloc dashi,”Mama ku saka hannu a nan domin sai an yi mashi tiyata”Dr ya faɗa yana jin tausayin matar ,hannunta na karkarwa ta amshi biro tayi signé.

 

 

 

A ɗakin tiyata kuwa Dr ne kusan uku suka duƙufa kan saurayin nan,a ƙarshe dai détruire ɗin duburar tashi akayi aka mashi wata sabuwa a ciki.

 

Fito dashi aka yi aka kaishi ɗakin hutu,sai da ya kwashi awani ne sannan ya farfaɗo da hajiya mahaifiyar shi ya fara cin karo wadda ta rakuɓe wuri guda idonta sunyi jajur alamun ta ci kuka sosai.

 

 

Dr ne ya shigo ya sake duba shi da tambayar inda ke mashi ciwo,kujera Dr ya samu ya zauna yace “tun ɗazu mahaifiyar ka ke kuka ta na son sanin miye mafarin ciwon ka, to na fi so ka sanar da ita da kanka,sannan kar ka yi mani ƙarya don ni likita ne na san komi”tunda Dr ya fara magana Sageer ke ɗaga kai alamun zai faɗi gaskiyar.

 

 

Rumtse ido yayi ya fara bada labari kamar haka:

 

Shekaru biyu da suka wuce nayi aikin gini,ina lebarenci ne ni da sauran abokaina uwanda ba suda aikin yi.

 

Kwatsam sai wani mai kuɗi ya bada kwangilar gina masa gida,har mun kusa kamallawa yace ginin bai masa ba a rogaza shi a sake mishi wani kala. Wannan lamari kowa sai da ya jinjina asarar da aka yi amma ba mu da halin cewa a’a tunda kuɗin shi ne,haka muka sake ɗora wani bayan ɗan danƙaro ya murje wancan.

 

 

Kullum alhajin nan kesa a kawo mana abincin mai kyau da jus duk da ya biya mu kuɗin aiki.A duk lokacin da alhaji ya zo na kan bar duk wani aiki da nake in ta kallon shi ganin irin tsadadun kayan da yake sawa da kuma motocin shi,ashe duk abinda nake alhaji na ankare da ni.

 

 

Wata rana bayan mun ci abinci muna hira ni da abokaina nake faɗa masu burina bai wuce in yi kuɗi kamar alhaji ba, su kuma dariya suka ta yi mini dan gani suke abun ba zai taɓa yiyuwa ba.Da na ji haushi sai na yi zuciya na bar masu wurin.

 

 

Ina zaune ina ɗan jifa da ƙanƙaru sai jin murya alhaji nayi yace “tabbas za ka yi kuɗi har ma ka fini amma sai ka yi min alƙawarin zaka yi duk abindm da zan saka ka”da sauri na ɗago kai ina washe baki nan na yarda da alhaji ,adress ɗin gidan shi ya bani yace in na sabka daga aiki na same shi gida.

 

Haka kuwa aka yi, bayan na same shi gida alhazzai na tarar suna shan lemu,sai da suka gama shagalin su kafin alhajin ya yi mini iso cikin ɗaki.Nemana ya yi ta baya kafin sauran abokanan shi suma su zo suyi ɗaya bayan ɗaya na sha kuka sosai amma milliyoyin kuɗin da suka haɗa min yasa naji ni ras.

 

 

Victago na shafa a dubura, duk raɗaɗin da na ji na daure sannan kuma ba laifi na ji dama-dama.Ummana ta kasance macce mai son kuɗi ganin ina facakali da kuɗi bai dameta ba, sai ma ƙara turani da take ,a ƙarshe dai na zama costoma ɗin dukan abokan Alhaji su yi amfani da ni su bani kuɗi wanda yanzu ina da wajan mota biyar da gidaje,sannan na biya ma Umma hajj har sau biyu … “maganar shi ce ta sarƙe sakamakon numfashin shi da ya fita,dama ita Hajiya tuni ta daɗe da shiɗewa a ƙarshe duka aka yi masu wanka aka kai su gidan gaskiya….

 

 

 

*Kar ka taɓa sha’awar abun wani,ba ka san ya aka yi ya same shi ba.Kai dai kawai ka nema gun Allah,shi ma ɗin in za ka roƙa to ka yi addu’a da na halal.Dayawan mutane za ka gansu cikin mota mai kyau,tufafi mai kyau,su ci mai kyau su sha mai kyau amma in aka bincika ma ta inda kuɗin suka fito zuciyar ka za ta iya tsayawa da bugawa saboda tashin hankali.Matasa nawa ne yanzu ke jefa rayuwar su a garari saboda kuɗi? Wasu luwaɗi,wasunsu lesbian duk wannan saboda kuɗi.Dauɗar duniya mai ƙare wa ce! Ko ba komi akwai mutuwa,ga kwanciyar kabari wanda in ka shiga ba maganar kwanciya bacci ba ne a’a akwai tambayoyin da za ayi ma.*

 

 

*Na dawo ɓangaren,iyaye! A yanzu wannan duniyar dayawan iyaye ba sa bincikar ƴaƴansu ta ina suke samun kuɗi halal ko haram? A’a kawai burinsu a dai kawo masu.In aka yi rashin sa’a wani daga cikin makusanta ya yi magana akan a bincika sai ka ji uwa na cewa hassada ce!*

 

Son zuciya babu abin da bai sawa,ya Allah kar ka jarabcemu da abin da zai taɓa imaninmu ko kuma zai saka mu a garari🙏🏻 ƴan uwa mu tuna cewa duk inda muke,Allah na ganinmu ko da kuwa za mu shiga cikin dutse ne ba za mu ɓoye ma ganinsa ba.

 

 

 

Allah sa mu dace Amen !!!!!

 

 

Chamsiya Laouali Rabo

About the author

Hausa_Novels

Leave a Comment