Littafan Hausa Novels

Ba Zan Barshi Ba Hausa Novel Complete

Soyayya Da Karamar Yarinya
Written by Hausa_Novels

Ba Zan Barshi Ba Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

BA ZAN BARSHI BA

 

Rubuta labari da tsarawa(Mrs Ibrahim

 

 

Ba zanyi free Page da yawa ba dan haka kuyi k’ok’arin siya domin ci gaba da karanta wannan book, domin k’arin bayani (09138585050)

 

 

*🌟ROYAL STAR WRITER’S ASSOCIATION🌟*

{R.S.W.A}

 

 

*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*

_(R.S.W.A)Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_

 

*Alk’alaminmu ‘yancinmu*

 

 

Paid Book#300

 

Free Page 1&2

 

Bismillahir rahamanurrahim

 

 

Wannan Littafin ƙirƙirarran labari ne idan hali ko wani abu yayi dai-dai da rayuwarki/Ka dan Allah kuyi haƙuri, domin ni ban yishi dan cin zarafin kowa ba se dan faɗakarwa Ilimantarwa tare da nishaɗantarwa, wannan book salansa na musamman ne kada ki bari abaki labari 300 ne babu tsada.

 

Mai Ciki Hausa Novel Complete

 

 

…………Laila maike damunki? maike faruwa ne? dan Allah ki faɗamin, ki duba kiga yanda kika dawo kin zama abun tausayi, wallahi lokacin da kina gida kinfi haka kyau da ƙiba amma yanzu daga yin aure kin sanja sai kace ba auran soyayya kuka yiba, to idan hakane ai banga amfamin auran ba maimakon mutum yayi ƙiba sai kuma ya dinga ramewa”.

 

 

Wanda aka ƙira da Laila ne tace”Nadiya maiyasa bakwa yarda da abinda nake faɗa muku?wannan maganar da nake yawan faɗa yauma ita zan faɗa miki ni Laila babu abunda ke damuna dan haka kibar wannan maganar please”.

 

 

“Uhmmm shikenan amma ki sani barin kashi aciki baya maganin yunwa ni dai zan ci gaba da miki addu’a duk abinda ke damunki Ubangiji Allah Ya miki maganinsa”.

 

 

“Ameenn kam, Yanzu dai bari na tashi na ɗaura girki nasan Habibi yana gab da dawowa” “Uhmm su Habibi manya to ni dai zan wuce gida sai kuma wani lokacin” “Haba Nadiya kada dan na miki wannan maganar yasa kiji haushi dan Allah ki tsaya kici abinci”.

 

 

“Wallahi Babu komai Laila kawai dai zan tafi ne, amma kada kisa wani Abu aranki” “To shikenan Nagode ki gaida gida” da haka tayi mata rakiya har bakin ƙofa kana ta dawo.

 

 

Bayan ta dawo ta ɗaura girki kana ta fara gyaran Palo bata wani jima ba ta gama kana taje tayi wanka shirinta tayi cikin Lace ɗinta ɗinkin riga da sket, masha Allah kayan sunyi mata kyau ajikinta, bayan ta gama shiryawa abincin ta jere a danni kana ta zauna, bai fi 10minutes ba taji Hon ɗin mota cikin murna ta tashi domin taro Habibinta tana zuwa ta amshi jakar hannunsa tana mishi sannu da zuwa sai dai kash ko kulata bai yiba Murmushi Laila tayi domin bayau ta saba ganin haka daga gare shiba, bin bayasan tayi ta same shi zaune akan kujera”Habibi sannu da zuwa” bakinta uku amma sam ko kallonta baiyi ba”Habibi dame zaka fara wanka ko abinci?domin Yau abinda Ka fi so shi na girka maka” ta faɗa tana Murmushi tsuka yaja kana yace”wai dan Allah Laila maiyasa kike mugun damuna? yanzu dan Allah daga zuwana kin fara isata da shegen surutu, to bara kiji babu abinda zan ci agidan nan domin ni naci abinci haka shima wankan bana jin zan iya, wai ma intambaye ki dan Allah maiyasa baki da zuciya ne?” Murmushi tayi duk da kalanmansa sun sosa mata rai can kuma tace”Haba Habibi taya zanyi zuciya da abinda nake so, kome zaka min bazan taɓa yin zuciya ba amma dan Allah kayi haƙuri akan takura maka da nayi in sha Allah bazan sake ba” ta faɗa tana tashi daga wajan.

 

 

 

“Haba Yarinyar kamar mayya kullum kana faɗa mata magana amma Sam bata ji” ya faɗa yana danna wayarsa.

 

 

Laila kuwa tana shiga ɗaki ta aje masa jakar kana ta zauna abakin gado wasu zafafan hawaye ne suka fara ziyarar fuskanta”Allah kana ganin Halin da nake ciki, Tunda nazo gidan nan ban samu farin ciki koda na kwana ɗaya ba, gashi ina son mijina bazan iya rayuwa idan babu shiba, Allah ka bani ikon jure duk wani wulaƙanci da zemin ina son mijina *BA ZAN BARSHI BA*” ta faɗa tana kuka.

 

 

Ta jima tana kukan kana da tawo Palo amma ta samu baya nan zama tayi domin taga ta ina zai fito, kafin ta ankara taji dariyarsa tana juyawa ta ganshi shida wata budurwa suna ƙoƙarin shiga ɗakinta, da sauri Laila ta miƙe tace” Habibi me zan gani haka?haba Habibi maiyasa kake cutar dani?maiyasa bakamin adalci yanzu dan Allah dame wannan tafi ni dahar zaka kawota cikin gidana kuma kana ƙoƙarin shigamin da ita har ɗakin aure na?”.

 

 

“Ikon Allah Yanzu Laila ni kike jerawa wannan tambayar kamar kin samu sa’anki?okey ba laifinki bane amma zanyi maganinki, ita wannan da kike gani ta fiki komai awajena, Baby wuce mushiga naga Uban da zai hanaki shiga” Ya faɗa suna barin wajan.

 

 

 

Zama laila tayi awajan tana kuka kamar ranta zai fita can kuma ta tashi ta goge hawayenta zama tayi akan kujera tace………✍🏻

 

 

 

Taɓɓɓɓɓ My Fan’s Yanzu aka fara wasan😍domin wannan somin taɓi ne, ku dai biya 300 kusha karatu.

 

 

Masu buƙatar group domin samun karanta wannan Book kuyi haƙuri kumin magana ta wannan number 09138585050 domin yanzu na daina fitar da Link

 

Mrs Ibrahim ce

About the author

Hausa_Novels

Leave a Comment