Littafan Hausa Novels

Azeemah Hausa Novel Complete

Hotunan Yadda Ake Kwanciya Da Mace
Written by Hausa_Novels

Azeemah Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

AZEEMAH

 

 

 

Alkalamin

 

Amaryar royal star

 

 

 

Da sunan Allah Mai rahma Mai jinKai

ROYAL STAR WRITER’S ASSOCIATION

{R.S.W.A}

 

 

*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*

_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_

 

*Alk’alaminmu ‘yancinmu*

 

 

 

Page 1&2

 

 

Wudil

 

‘Yam Mata ne su uku na hango suna tawowa da botikan ruwa a kansu, gaba d’ayansu baza su wuce shekara sha shida ba, biyu daga ciki ne suke ta hira hankalin su kwance sai dariya sukeyi duk da kana ganinsu kasan ba masu hali bane Iyayansu,”kinsan Allah Ma’u jiya da muka je kasuwar nan Audi ya bani dariya yadda ya rikice miki waishi bai yadda ba yaga budurwa, k’afafuwansa harrawa sukeyi wallahi”,ta k’arasa maganar tana k’ara fashewa da dariya.

 

Abadan Hausa Novel Complete

Wadda ta k’ira da Ma’u ce tace “Allah Rabi ranki zai b’aci,na fad’a miki ki daina had’ani da wannan mai zubi da mahaukatan kinki ko..tom. dariya Rabi tayi,”haba k’awata daga tuna miki da masoyin ki”,banza Ma’u tayi da ita bata k’ara mata magana ba har suka d’anyi nisa.

 

 

Ma’u ce takai duban ta ga abokiyar tafiyar tasu da tunda suka tawo bata ce komai ba,”ke sarkin tunani to ga mutuminki can ya tawo kuma da alamu wajan ki ya nufo”,bata k’arasa maganar da takeyi ba wanda take magana a kanshi ya k’araso.

 

 

 

“Azeema tun d’azu nazo inata jiran dawowarki amma shiru,na kasa hak’ura shiyasa na biyo ki”,tunda ya fara magana wadda ya k’ira da Azeema take kallonsa, kamar ta samu Tv,ko k’ifta ido batayi,shi kuma ganin hakan yasa ya zage sai zuba yake kamar kanya duk a tunanin shi tana fahimtar abinda yake fad’a mata,sai dai kuma ita sam hankalinta baya tare dashi.

 

 

 

Rabi ce ta rik’e mata hannu tana fad’in “Malam ka rabu da ita ko ana so dole ne a’a, da kai zataji ko da Babar ka”,janta tayi suka bar wajan,da kallo ya bisu yana cije baki lallai Yarinyar nan, amma zaki shigo hannuna ne,juyawa yayi ya tafi wanda kana ganin tafiyar sa kasan ta ‘yan shaye-shaye ce.

 

 

 

“Wallahi Azeema duk laifin kine danme ba zaki bud’e baki yimai rashin kunya ba ki zage dan iska tunda shi baisan lallami ba sai dai kawai ki tsaya kina kallonsa kamar wata sokuwa,aikin banza kawai ki zauna karki k’watarwa kanki ‘yanci”, duk wannan fad’an rabi ce takeyin sa,saboda dama ta fisu baki tun suna Yara.

 

 

 

Kiyi hak’uri Azeema wata rana sai labari,komai zai wuce kamar ba’ayi ba kedai ki cigaba da Addu’a,karki biye ta zance Rabi rashin kunya ba abinda zata haifar miki sai wata sabuwar matsalar mai zaman kanta,amma Addu’a ba abinda ta bari”, ta k’arasa fad’a tana share mata hawayan da suka zubo daga idon ta.

 

 

 

Botikin ruwan ta Azeema ta d’auka da suka sauke mata hanyar gidan su ta kama ba tare da tayiwa d’aya daga cikinsu magana ba,a hankula take tafiya cike da fargabar abinda zata tarar a gidan,k’ofar wani k’aramin gidan kasa ta tsaya takai wajan minti biyar kafin ta tura k’ofar shiga gidan cike da fad’uwar gaba.

 

 

 

Sallama take tayi amma bawanda ya amsa mata duk da dama an saba k’in amsawar sai dai hakan baya hanata yi.

 

 

 

Wata k’atuwar mata na hango zaune akan kujera ‘yar tsugunne tana cin d’umaman tuwo kasancewar safiya ce lokacin,duk sallamar da Azeema take yi wannan matar tana jinta amsawa ne kawai bata da niyya, wajan da aka tanada dan zuba ruwa Azeema ta nufa ajewa tayi saboda daman daga shi ta gama,fuskarta ta wanke da k’afafuwa ,kwano ta d’auka ta nufi inda suke girki da niyyar zuba tuwan itama taci dan bata karya ba.

 

 

 

“Zonan”,matar dake zaune tun shigowarta bata d’ago ba ta fad’a,a nutse Azeema ta k’araso inda take zaune ta tsugunna,kunnan ta matar ta kama “gidan uban wa kika tsaya tun d’azu”, ta fad’a had’i da murd’e mata kunne,hawaye ne ya shiga zirya a fuskar Azeema kafin tace,”wallahi Gwoggoji ba inda na tsaya kinsan ai wajan da nisa kuma ga layi,ko da ina dawowa da Yawale ya tsayar dani bantsaya ba”,ta fad’a tana sunkuyar da kanta k’asa.

 

 

 

“Au shi Yawalen duk abinda nake fad’amai a kanki ya k’iji ko zaizo ya same ni shima,maza ki wuce ki kaimin gorona bakin Kasuwa saboda tsabar bak’in halinki shi yasa kikayi rana,to wallahi kaiki kuskura ki dawo min da shi ki tabbatar kin siyar duka”,”to amma dan Allah Gwoggoji zanci abinci yunwa nake ji wallahi”,”tashi ki bani waje shegiyar Yarinya sai tsinan nan cin tsiya kamar gara,kuma kullum jiya eh yau”.

 

 

 

“Dan Allah Gwoggoji k ibari naci Allah zan siyar miki inna fita”,”kinsan Allah Azeema idan baki ‘bace min da gani ba sai ranki yayi bala’in b’aci,idan gyatuma ce ta tu’kamin tuwan sai naji da zaki dame ni, tashi ki bani waje munafuka kita sunkuyar da Kai kamar mutuniyar kirki,sai mugun hali irin na uwar ki fal ciki”.

 

 

 

Haka Azeema ta d’au farantin goran ta tafi ba tare da ta karya ba,tunda ta fita take karo da ‘Yan makarantar su,tanaji tana gani tarasa karatun ta ya gagare ta,ajiyar zuciya ta sauke “Allah kana ganin halin da nake ciki ka kawomin mafita ka dawomin da innata cikin k’oshin lafiya”,kuka ne ya kwace mata da sauri ta shige wani siririn lungu, tsayawa tayi agun tayi kukan har sai da taji zuciyarta tayi mata sauk’i sannan ta fito,amma duk wanda ya kalleta yasan tasha kuka abinka da mai haske sai fuskar tai jawur, a hankula take tafiya har ta k’arasa inda take zama dan siyar da goran kusa da me abinci ne, kallon ta matar tayi tace “Azeema yau kinyi rana dan na zata ba zaki zoba ma”, murmushi Azeema tayi ba tare da tace da matar komai ba waje ta samu ta zauna.

 

 

Kano

 

Tun daga compound d’in gidan nake jiyo hayaniyar Yara cikin falon na shiga,tun daga bakin k’ofa na fara karo da kayan wasansu kota I. na kalla sunyi kace-kace dashi duk kuwa da girma sa hatta da fulan kujerun basu tsiraba sai da aka cire su,Yara ne su uku suka fito a guje daga wani d’aki d’aya daga cikin Kujerun suka nufa, idona nakai duba zuwa inda sukayi amma abin mamaki wata mata na gani wadda ba zata wuce shekara ashirin da bakwai ba kwance akai sai danne dannan waya takeyi.

 

 

 

“Mami kinga Irfan yayi fitsari a wando Yarinyar da take fad’ar hakan batafi shekara bakwai ba,”Iftee ranki zai b’aci wallahi in kuka dame ni kije kisamai ruwa mana meye na fad’amin”.

 

 

 

Horn d’in Mota sukaji yaran hakan yasa sukayi waje da gudu,fakin d’in Motar aka gama dai-dai tawa sannan na cikin ya fito,matashi ne baifi shekara talatin da uku ba sanyi yake cikin milk din shadda riga mai k’aramin hannu jakarsa ta zuwa office ya d’akko duk Yaran na tsaye bakin k’ofa suna jiran k’arasowar shi.

 

 

 

Hannu yakai zai d’auki Irfan da sauri Iftee tace “Abeey yayi fitsari kuma Mami bata sa mai ruwa ba”,hanci wanda ta k’ira da Abeey ya lakacewa mai bimaya Junaid yana fad’in “yadai naga super man d’in Abeey yana b’ata rai?”, d’aukar Irfan yayi ba tare da ya karashi da jikinsa ba cikin gidan suka nufa Junaid na fad’in “Abeey yunwa nakeji kuma Mami batayi abinci ba”,wuce ta sukayi ba tare daya ko kalli inda take kwance ba.

 

 

 

D’akinsa suka nufa, yana “subhanallahi super man d’in Abeey najin yunwa yanzu ya za’ai kenan?”,dai-dai lokacin ya ajiye Irfaan akan durowar gado rigar jikinsa kawai ya cire ya nufi Toilet ruwan wanka ya had’a da kansa yayiwa Yaransu duka,sannan ya shafa musu mai d’akinsu yaje dan ya d:auko musu kaya nanma kaca-kaca, kanshi kawai ya girgiza ya fito,zama yayi ya shirya su tsaf sannan ya ce su je k’asa su jira shi amma duk wanda ya ‘bata kayanshi baza aje dashi ba.

 

 

 

Baifi 30mint ba ya fito cikin riga da wando na ‘yan kanti,tashi Yaran sukayi suka bishi a baya bayan ya d’au Irfaan Mota suka shige suka bar gidan.

 

 

 

Duk abinda ke faruwa tana kwance a inda take amma ko motsawa batayi ba tare ta nuna ta ganshi a matsayin sa na mijin ta.

 

 

 

 

Nasawara GRA ya nufa da kai tsaye,kafin su k’arasa tuni Irfan yayi bacci,horn yayi Mai gadin gidan ya bud’e mai dai-dai ta parking d’in yayi ya d’akko Irfan a kafad’ar shi cikin gidan suka shiga .

 

 

 

 

‘Yam mata ne biyu a zaune a falon kallo sukayi suna d’an hira jefi-jefi,sallama d’auke a bakin su shida Yaran suka shiga,d’aya daga cikin ‘yan matan ce ta taso da sauri tana fad’in “oyoyo super man” da gudu Junaid ya k’arasa wajan ta rungume shi tayi,Irfan ya mik’a mata dan haka ta saki Junaid ta karb’e shi,”ina Ummy fa?” ya tanbaya yana zama a one seta, “tana d’akinta ta bashi amsa tana gyarawa Irfan kwanciyarsa akan kujera.

 

 

 

Sannu da zuwa ta fad’a wadda tun da suka shigo ta gudu d’aki,kallo na bita dashi pawder na gani afuskar ta da alamun yanzu ta shafa sai kamshin turare takeyi kamar mai shirin zuwa unguwa,ko kallan inda take bayyi ba,”Zakiyya zuba wa Yaran nan abinci sannan ki kawo min d’akin Ummy nima”, yana gama fad’a ya tashi ya nufi wata k’ofa acikin falon.

 

 

 

Sai yanzu na k’arewa Zakiyya kallo suna matuk’ar kama da shi sosai daga gani kasan jininsa ce,kamar yadda ya sata haka ta zubawa su Iftee abincin suka fara ci sannan ta d’au nashi shima ta bishi dashi.

 

 

 

Zaune ya samu Mahaifiyar tashi akan abin sallah tana lazumi,zama yayi bayan ta idar ya gaishe ta cike da girmamawa,cikin kulawa take fad’in “Babana kullum k’ara ramewa kakeyi, kana da dama a hannun ka amma ka kasa amfani da ita”.

 

 

 

“Ummy nidai kita sani a addu’a”,Babana addu’a ai ta zama dole tunda da raina,amma zan sake fad’ama kamar kullum ya kamata ka tashi tsaye kai wani abun…”Zakiyya ce ta turo k’ofar hakan yasa Ummy yin shiru bata k’arasa fad’ar abinda tayi niyya ba, abincin ta ajiye mai ta fita,a nutse ya faraci “Alkubus ne da miyar taushe tasha kayan ciki,bai wani ci dayawa ba ta zare hannun sa alamar ya k’oshi.

 

 

 

Junaid ne da Iftee suka shigo d’akin jikin Ummy suka fad’a suna dariya,”ja’irai ashe tare kuke”, ta fad’a tana dariya cike da soyayyar jikokin nata,”mun cinye miki Alkubus”, Junaid ya fad’a yana kwanciya kan k’afarta,”haka kuka iya ku baro gidanku kuzo ku ciyemin abinci kuma sunan da mata agidan ai na kusa dai na baku”, Iftee tai saurin cewa “amma Ummy idan kika dena bamu a ina zamuci tunda Mami batayi mana?”, kallon ta Ummy tayi sannan ta mai da idon ta kan Yusuf(Abeey)”sai kusan yadda zakuyi ai nidai na fad’a muku gaskiya”.

 

 

 

Duk wannan maganar Ummy nayin tane dan ya juyo amma kamar ma bashi acikin d’akin wayarsa kawai yake danna wa,”to kunaji kucewa Abeeyn ku yayo muku Aunty sai ita ta dunga dafa muku Abinci tunda Mamin taku ta kasa”, matsawa kusa dashi Iftee tayi,”Abeey kaima ka kawo mana Aunty sai ta dunga dafa mana Abinci kaga ummy tace zata dai na bamu,kuma dama gidansu baby zee ankawo musu suma Aunty, amma su Mamansu tana yi musu Abinci”.

 

 

 

Katseta yayi da cewa “tashi maza kuje Mota ku jirani yanzu zanzo mu tafi gida dare yayi”,dan inya kyale ta haka zatai tamai surutan banza,ta shi sukayi ita da Junaid suka fita bayan sunyi wa Ummy sai da safe.

 

 

 

Juyawa yayi wajan Ummy kamar zeyi kuka sai dai bece komai ba,ta gane mai yake nufi hakan yasa tace,”ni na fada ma kaki yarda watak’ila su idan sun fad’ama kayar da”,hannu yasa ya kamo nata ya sumbace su yana fad’in sai da safe, dan bayasan waccan maganar .

 

 

 

 

Da kallo kawai Ummy ta bishi tana girgiza kai gaba d’aya an canza mata Yaro,amma ba komai akwai Allah ta fad’a tana nade abin sallar da take kai.

 

 

 

A falo ya samu Zakiyya tana bawa Irfan ruwa bayan ta gama bashi Abinci, d’aukar shi yayi yana mata sallama ya fice daga cikin falon,”my D” aka fad’a daga bayan sa yasan ko wace hakan yasa yak’i juyawa ya cigaba da tafiya,da sauri ta shiga gabansa “haba dan Allah my love sai nayi tama magana kana share ni sannan kazo ko ka nuna alamun ma ka ganni bare ka tambayi yaushe nazo ko dai bakayi farin ciki da zuwan nawa bane ka fad’amin?”,”kin gama?” ya tanbaye ta,”eh” ta bashi amsa cike da yanga.

 

 

 

 

Okay, kawai ya ce ya wuce ya bata waje, Mota ya shige ya fice a gidan ba tare da ya kalli inda take ba

 

 

 

Duk abinda ke faruwa Zakiyya na kallo ta window,dariya tayi tana fad’in “iska na wahalar da Mai kayan kara.

About the author

Hausa_Novels

Leave a Comment