Asararun Almajirai Sirrukan da Yakamata Ka Sani
RUQYA A SAUQAQE DOMIN SAMIN WARAKA DAGA ALJAN KO SIHIRI
Akwai hanyoyi guda uku mara lafiya zai iya ɗaukar hanya ɗaya yayi amfani da ita daga cikin ukun nan.
HANYA TA FARKO •1
A nemo ganyen magarya guda bakwai ɗanye ko busasshe,
Sannan a sami wani abu kamar bokiti ko wata roba babba wacce za’a ajiye ruwa mai kyau sosai acikinta, ruwan da zai iya kaiwa tsahon sati ɗaya, kwana bakwai kenan ana amfani dashi, sai a zuba ganyen magaryar acikinsa a murje shi, ta yadda zau gauraye d ruwan.
Bayan haka sai a karanta wannan acikin ruwan:👇
1• Suratul Baƙarah gaba ɗayanta.
2• Qulhuwallahu Ahad 3.
3• Falaq 3.
4• Nass 3.
A sami wanda ya iya karatu sosai koshi mara lafiyar idan zai iya karantawa da kansa, to yayi da kansa, saiya zauna a kusa da ruwan a yayin da yake karatun numfashinsa yana shiga cikin wannan ruwan.
Bayan angama karatun sai mara lafiya ya rinƙa ɗibar ruwan kofi ɗaya yana sha kullum, kofi ɗaya tak.
Sannan kuma sai a sami wani tsumma ko tawul sai a ɗebi ruwan a wani abu daban sai a rinƙa tsomashi aciki ana goggowa ajikinsa har sai dukkan jikinsa ya sami wannan ruwa, ya zama dai kamar wanka yayi dashi, shima kwana 7 mutum zaiyi hakan.
A Gidanmu Take Complete Hausa Novel
In sha ALLAH TA’ALAH ko sihiri ko aljani ko kambun baka ko maye ne ya kama mutum, indai yabi wannan hanyar da muka kawo yayi komai cikin nutsuwa, to zai sami lafiya da iznin ALLAH.
HANYA TA BIYU •2
Mara lafiya ya sami waɗannan abubuwan:
• Man zaitun.
• Man Habbbatu sauda.
• Man tafarnuwa.
• Zuma ya sami kamar cikin robar yoghut ƙarama.
Idan zai yiwu a sami na kamfanin HEMANI, kuma kowanensu 60ml sai a haɗesu wuri ɗaya a rinƙa shan cokali biyu da safe, cokali biyu da Rana cokali biyu da yamma.
Insha ALLAHU TA’ALAH duk abinda ke damun mutum zai rabu dashi, idan kuma wannan hanyar tayi wahala, to sai mutum yabi hanya ta uku.
HANYA TA UKU •3
Ita wannan hanyar ɓangaren man shafawa ne sai a nemi:
• Vaciline na habbbatu sauda.
• Vaciline na zaitun.
• Jibda.
• Jan miski.
Sai a sami ruwan zafi a saka kwalbar aciki mayukan zasu narke, zasu tashi sai a haɗesu wuri ɗaya acikin wata kwalbar babba, sai a rinƙa shafawa sau uku a rana, amma kafin a shafa ayi karatun ruƙya acikinsu:
• Ayatul kursiyu 1.
• Qulhuwallahu 3.
• Falaq 3.
• Nass 3.
Idan an karanta sau ɗaya ya wadatar basai ansake karantawa ba idan za’a shafa.
Sai a rinƙa shafawa idan za’a kwanta bacci kaɗan amma ake shafawa kamar dai yadda ake shafa turare ajiki, da kuma bayan anyi wanka bayan mutum ya shafa man daya saba shafawa, sai a dangwalo maganin a shafa sama-sama.
Sannan kuma sai da safema a shafa, ko kuma idan mutum zai shiga sha’anisa ya shafa a ƙalla sau uku dai a rana.
Sannan mace zata iya rinƙa saka cokali ɗaya na garin Habbatus-sauda acikin miya tana girki dashi yara suci, mai gidama yaci, haka kuma ana iya zubashi acikin ko wanne irin girki saboda kariya daga iska ko sihiri, ko maita ko kambun baka.
Sannan kuma mace zata iya rinƙa turarashi a ɗakinta kuma zata iya zubashi akan garwashi tayi tsuguno akansa.
Insha ALLAH duk wacce ko wanda yake fama da matsalar aljanu ko sihiri ko maita ko kambun baka, to ya ɗauki ɗaya daga cikin hanyoyi ukun-nan da muka kawo ya jaraba, in ALLAH ya yarda zai sami lafiya.
Ya ALLAH duk wanda yake fama da wata larura ta rashin lafiya ko waninta, ALLAH ka yaye masa, ALLAH ka bawa kowa lafiya ingantacciya.
ALLAH ka gafarta mana zunubanmu baki ɗayanmu Ameen.
Duk mai neman ƙarin bayani yayi mana magana ta private.
MABUDAN YAYEWAR DAMUWA GUDA 10
Mabudi na farko.
Karanta suratul fatiha ‘ita tana wadatar da Mara lafiya domin tana warkarwa ‘ita ruqya CE.
Mabudi na biyu.
Fadin wannan addu’a a lokacin damuwa,
الله الله ربي لا أشرك به شيئا
Manzo s.a.w yacewa ‘yarsa fadima, lokacin damuwa kice ” الله الله ربي لا أشرك به شيئا ”
Mabudi na uku.
Fadin” لا إله إلا أنت سبحانك إني كنت من الظالمين ” manzo s.a.w yace, addu’ar dan’uwana zeennun (annabi yunus) wanda yashiga damuwa bazai fadeta ba face Allah ya yaye masa.
Mabudi na hudu.
Fadin” حسبنا الله و نعم الوكيل ” qur’ani ya bamu labarin cewa lokacin da akazo don a tsorata musulmai cewa abokan gabansu sunyi musu tanadi babba don suji tsoronsu sai suka fadi wannan addu’a sai Allah ya amintar dasu sharrin abokan gabansu suka dawo cikeda ni’ima da falala babu wani abinki daya samesu.
Mabudi na biyar.
Fadin” لاحول و لا قوة إلا بالله العلي العظيم ” Allah zai yaye ma bawa damuwa dalilin fadinta, kuma ‘ita taskace daga taskokin aljanna.
Mabudi na shida.
Yawaita istigfari, manzo s.a.w yace mai yawaita istigfari Allah zai sanya masa yayewa akowace damuwa, da mafita akowane qunci yakuma azurtashi ta inda baiyi tsammani ba
Mabudi na bakwai.
Fadin wannan addu’a. Duk wanda ya lizimceta Allah zai yaye masa damuwoyi.
“لا إله إلا الله العظيم الحليم ،لا إله إلا الله رب العرش العظيم ،لا إله إلا الله رب السموات و الأرض رب العرش الكريم ”
Mabudi na takwas.
Lizimci wannan addu’a manzo s.a.w yace tana yaye damuwoyi kamar yadda ta tabbata a ingantaccen hadithi.
” اللهم إني أعوذ بك من الهم و الحزن و أعوذ بك من العجز و الكسل و أعوذ بك من البخل و الجبن و أعوذ بك من غلبة الدين و قهر الرجال ”
Mabudi na Tara.
Fadin wannan addu’a
“يا حي يا قيوم لا إله إلا أنت برحمتك أستغيث ”
Addu’a ce ta Neman taimakon Allah da yayewar damuwoyi manzo s.a.w ya kasance yana yinta.
Mabudi na goma.
Fadin sannan addu’a, manzo s.a.w ya kasance yana fadinta idan al’amura suka tsananta gareshi.
“اللهم رحمتك أرجو فلا تكلني إلى نفسي طرفة عين و أصلح لي شأني كله لا إله إلا أنت “
Leave a Comment