Littafan Hausa Novels

Arman Maleek Hausa Novel Complete

Written by Hausa_Novels

Arman Maleek Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

ARMAN MALEEK

*DAGA ALƘALAMIN*

SALMAJI ƳAR LELEN ROYAL STAR CE

Sadaukarwa ga Aminiyata Sadiya Abbakar Maru (Ƴar gatan royal star)

ROYAL STAR WRITER’S ASSOCIATION
{R.S.W.A}

*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_

*Alk’alaminmu ‘yancinmu*

 

PAGE 1.

 

Cikin Natsuwa jerin gwanon Motoci kusan guda biyar kirar Mercedes Benz , farare ne sol gwanin sha’awa, suke tafiya, duk in da motocin suka wuce ɗaga musu hannu da jinjina ake, wanda hakan ma ya isa ya shaida maka, ba ƙaramin mai daraja da ake ganin mutuncin shi bane a motar, sai da suka zo gurin wani Babban hospital kafin su fara rage gudu, a hankali suka fara sulalawa cikin Asibitin, sai da suka shiga cikin tafkeken parking space din cikin Asibitin kafin su tsaya.

duk fitowa mutanan da suke cikin motocin suka yi, sai wata mota daya da go budeta ba’ayi ba, a hankali aka bude murfin motar, kamshin turaren Huge Boss da ya daki hancina ne ya tilasta min ɗago da idanuna, hankan kuma yy dai-dai da zuro fararen ƙafafunshi fararw tass, wanda suke cikin takalmi half cover fari mai kyau, yana yin zubin takalmin kawai zaka kalla kasan cewar na Sarakai ne.

 

tun daga ƙafafunshi na fara ƙarewa kallo, har izuwa kwaurinshi wanda farar Alƙyabba mai torch din Golding da ta mammaye gaba daya jikinshi, wanda har fuskarshu ba’a iya gani, sai dai hannayenshi da ya zuro, wanda ya ke gyara igiyar Alƙyabbar jikinshi.

A hankali ya sanya kyawawan fararen hannayenshi, ya dan jaaa hular Alƙyabban da yake jikinshi, Masha Allah, kyakyawa ne sosai, duk kuwa da ban ga fuskarshi da take nannaɗe da rawanin da yake a kanshu ba, idanubshi kawai da gefen fuskarshi na samu nasarar gani, idanunshi manya ne dan kai tsaye za’a kiransu da Lu-lu Eyes ko ace Oil Eyes, dan har wani mai-mai ko in ce ruwa-ruwa ne a cikin idanun nashi, farare ne tas, sai dai maimakon back eyes ball , sai nashi y kasance royal blue.

Sune Suka Janyo Min Hausa Novel Complete

lumshe idanun nashi yy, wanda hakan yy nasarar bayyanar da zara-zaran Eyes lashes dinshi, da suke baƙaƙe sidiƙ, idanunshi y bude tare da dan juyasu a hankalin, kafin ya fara tafiya, cikin yalwatacciyar natsuwa da kamalarshi.

Sauran Fadawan da suke bayanshi ne suka fara take mishi baya, cikin natsuwa duk suka nufi cikin Hospital din.
shigarsu kuma tayi dai-dai da shigowar motar Ambulance da take ta ihu, cikin gaggawa gaba daya nurses din da suke cikin Asibitin da Drs duk suka nufi waje in da Ambulance din ta tsaya.

cikim gaggawa aka fara fitowa da Majiyatan da suke cikin Ambulance din wanda kallo daya zaka musu kasan cewar Haɗarine Hadarin ma mugun haɗari wanda baya kalluwa, daga gaba dayan su bb wanda bai rasa wani sashe na jikinshi ba, duk jini jikinsu bb kyan gani, masu rauni zuciya ma daga cikin nurses din sai kuka suke, Drs din kuwa dama su sun saba gani, hakan yasa abun bai wani ɗaɗarasu da ƙasa ba, sun damu amma bawai kamar nurses din ba.fiffito dasu aka yi, amma sai suka yi cirko², ba’a shiga da su ciki ba.

Mutanan da suka shiga ciki ne suka fito , gurin da mutanan suke tsaya suka nufa,
abin ya mugun ɗaga musu hankali, wanda yasa da damarsu suka fara zubar da hawaye,daya daga cikin Drs din ne ya ce “wannan sai dai ku shiga dasu Amma bb alamar rai a jikinsu”, ya fada yana niyyar juyawa, hannunshi mutumin ya kama, idanunshi da dago tare da tsurasu akan mutumin da sauri cikin ƙanƙan da kai yace “Allah ya taimaki Sheikh Arman wannan Haɗarin ya munana, bashi da kyan gani, bana tunanin za’a iya fitar da mai a ciki”, ya fada cikim zallar jimami.

sakin hannunshi yy ya ƙarasa gurin motar, yana zuwa idannshi ya sauka akan wata Yarinya da take sharɓe gaba daya jikinta jini ne, wanda yasa bama a iya ganin fuskarta sa boda jinin da ya wanke gaba daya illahirin jikinta, ga wani farɗeɗan ciwo da ya zagayo tun daga kanta har tsagin fuskarta ɓangaren haggu, gaba daya Yarinyar ba zata wuce 7years ba, royal blue eyes din shi, ya juya a kam Yarinyar da kallo daya yy mata ya gane tana numfashi, a hankali ya furta “Yah Subhanallah”, ya fada yana kutsa kanshi cikin tarin Jama’ar gurin.

yana zuwa bai ɓata lokaci ba ya dauketa chaak tare da nufar cikin Asibitin da ita, cikin wata Golden Voice mai dadin gaske, wadda kamar ana busa sarewa ya fara kiran “Doctor! Doctor!! Doctor!!!”, ya ƙarasa faɗa cikin gajiyawa da rashin son magana, Dr din da ya mishi mgn Ɗazun ne y fito da sauri jikinshi na rawa, miƙa mishi Yarinyar yy , da ido ya mishi alama da a duba ta, da sauri ya karɓi Yarinyar da bb alamar rai a jikinta, Accident and Emergency room ya nufa da ita da sauri.

Yana shiga ya shimfiɗeta kan gadon da aka tana da domin masu rashin lpy mai tsanani ko haɗari, gaba daya gadon yana kewaye da na’u’o’i , na ceton ran Dan Adam, da sauri Dr din ya dauki
stethoscope da yake ajiye a saman wani dan table in da anan ne ake ajiye duk wani abu mai muhimmanci da Drs suke buƙat amfani da su domin ceto ran marar lpy.

cikin Sauri ya juyawa Yarinyar baya tare sa zage zip din yar rigar jikinta, ya ajiye a gefe, kwantar da ita yy tare da daura stethoscope din a kirjinta ɓarin dama, domin jiyo sauti bugun numfashinta, a hankali ya jiyo bugun numfashinta da yake chan ƙasa sosai wanda in baka saurara ba ba zaka iya jiyowa ba, da sauri ya dauki ya matsa gurin Ventilator, (Na’urar hura iska ita ce injin da ke shaka wa mutum yayin da huhu ke samun waraka. Yana aika iskar oxygen ko iska zuwa cikin huhu ta cikin bututu mai bakin ciki kuma yana ba da damar carbon dioxide ya tsere. Ana sanya bututun a cikin bututun iska ta hanci ko baki), cikin Jaddada wannan lamari ya ci gaba da gyara mata jikinta, sai dai irin manya-manyan rauni kan da suke jikin Yarinyar ya bashi tsoro, domin raunika ne wanda ba lallai in mutum ya jisu a jikinshi ya iya rayuwa ba.

jinin da yake ta zuba a tsakiyar kanta ya fara tsayar mata, ganin wani kwasheshen ciwo yasa, ya dauki scissor ya fara iske mata gurin da taji ciwon, tsorata yy lokacin da yy arba da ciwon da yake kanta, wanda yasa har ya matsa ba, yanka ce sosai wadda ta shiga cikin kanta, wanda har naman kanta ana iya hangowa.

bai san lokacin da kwalla ta zubo mishi ba, sa boda zallan tausayin Yarinyar, a hankali ya shiga mata ɗinki a kan, har ya gama yana hawaye, duk in da ta ji ciwo ya wanke mata, ya gyara mata karayar da tayi, kafin ya fara gofe mata jinin fuskarta, bayan ya gama da ya kalli fuskarta, sai da zuciyarshi tayi wani kyakywan bugawa, sa boda ganin yarda fuskar Yarinyar take, wadda jini duk ya dan bubushe mata, Fara ce sosai, yana yin zubin halittar fuskarta da farin fatar jikinta kaɗai ya isa shaida maka cewar ba cikakkiyar yar Ƙasar Nigeria bace, dan tafi kama da Larabawa ko Turawa.

bayan ya gama ya shiga duddubata, domin ganin in ta samu wani Internal Injury, abun da ya gani yy bala’in girgiza mishi tunaninshi, wanda yasa sai da ya dago ya kalleta,na wasu minutes kafin ya ci gaba da aikinshi, bayan ya gama, ya fidda sakamakon Gwaje-gwajen da aka mata, tare da fitowa yana goge idanunshi da fuskarshi da suka yi jaaazir tsabar tashin hankali.

ko da ya fito wayam yaga ƙofar, ko ha’a faɗa ba yasan Sheikh Arman-Maleek Abdul-azeez Sarki ya tafi , domin lokacin Sallar Juma’a yy wanda kuma yana da tabbacin duk lokacin da ya shigo Ƙasar shine yake Limancin Central Mosque din da yake cikin Abuja .

da sauri ya shiga cikin Office dinshi domin shirin tafiya shima, sai da ya gama kafin ya fito, kiciɓis yy da wata nurse cikin harshen turanci ya fada mata ta kula da Patient din da take ER(Emergency room), jinjina mishi kanta tayi, kafin ya wuce
, yana hawa kan titin da sai kai shi Asokoro Central mosque da yake cikim Abuja, ya fara jin daddar muryar Sheikh Arman-Maleek tana tashi ta cikin abun ƙara karfin saurin maganar da yake cikin Masallacin wanda ya ƙaraɗe gaba daya Unguwar ta Asokoro, cikin dadda kuma sanyayya tattausar muryarshi yake huɗuba , tare da nusar da jama’ah da baiwar da Allah ya bashi ta iya magana.

har ya ƙaraso harabar tankamemen Masallacin da yake cike da Al-umman Annabi yana jin Muryar Sheikh din na ratsa cikin kunnuwanshi, a hankali cikin natsuwarshi shima ya nufi cikin Masallacin in da ya fara tara jama’a, sosai wanda da ka kalli yawansu ma zaka san ba mutane ne kawai ba, dole ma akwai ƙarin wasu jama’ar.

Cikin Masallacin da ya kusa cika ya shiga, kusan gaba daya Masallacin ta kusa cika da mutane, hakan yasa sai kusan sahun karshe ya samu , yana shiga bai fi sa 2 minutes ba aka kabbara Sallah,cikin tsari da tausasa harshe yake karatun Al-qur’ani mai girma a cikin Suratul Khafi, cikin zaƙi da dadin muryarshi yake karatun har aka idar da Sallah, mutane ne suka fara fita, bayan idar da Sallah Juma’an, kusan kowa da yake cikin Masalacin sai da ya fita, kafin Sheikh Arman ya fara takowa domin fita, ta wata ƙaramar kofa da take gefen kusa da gurin da Liman yake, bakishn dauke da Tasbhi yake tafita, yana yi yana lumshe idanunshi, har ya fito daga cikin masallacin.

Escort dinshi da suke a waje suna jiranshi je da Fadawa suka take mishi baya, har gurin motarshi,, bude mishi akayi, sai da ya tattare Alƙyabbar jikinshi kafin ya shiga, rufewa aka yi,bayan duk tarin mutanan da suka rakoshi sun shiga mota , kafin aka fara tafiya , a jere cikin tsari.

Direct Hanyar Garin Gombe suka nufa, idanunshi na lumshe bakinshi bai gushe da Ambaton Allah ba har suka yi nisa sosai suka raba dai-dai tsakanin Abuja da Gombe, A hankali ya fara bude Royal Eyes dinshi, tare da kallon wayar da take gefenshi wadda take ta vibrating , ga kuma haske da take kawowa.

a hankali ya kai zara-zaran fararen yatsun hannunshi, ya dauki wayar tare da yin Receiving call din, a hankali ya kara wayar a kunnenshi ba tare da sanin mai kira ba, Wata Muryar ce mai sanyi da dadi ta daki dodon kunnenshi wadda tasa ya dan lumshe ido, yarda ya dan saki jikinshu ne kawai zai fahimtar da kai wanda yake kiran nashi yana da matuƙar muhimmanci a gareshi,a hankali cikin halin rashin son magana yace “l’ll call you late “,yana fadar haka ya kashe wayar .

ko Ajiyeta a in da take bai yi ba, wani call din ya ƙara shigowa cikin wayar tashi, “`Jaddi“` sunan Mai kiran nashi ya bayyana a kan screen din wayar, sai da ya lumshe idanunshi kafin ya dauki kiran, A hankali yace “Assalamu alaika”, daga cikin wayar muryar wani tsoho ta fara magana cikin harshen turanci , sai da na ƙarewa fuskar wayar kallo kafin na gane ashe number bata Nigeria bace, number ƙasar waje ce.

shi din ma da ya dauka ba wata maganar kirki ce ta haɗashi da shi ba, daga uhmm sai uhumm, shi kenan abun da yake ce mishi, har suka yi Sallama.

4hours ne ya kai su Gombe daga Abuja, direct titin Abdul-azeez Arman-Maleeek Sarki roaud suka nufa, basu tsaya ko ina ba, sai gaban wani tankameman get din gidan Sarauta wanda gaba daya gidan fenti ne irin na daɗɗiyar masarauta, fentin da ba’a samunshi a ko wace Masarauta sai masarautar da ta Haura shekara ɗari biyu da wani abu, tsarin gini da shigar mutan gidan ma ya isa kara tabbatar maka da dadewar Masarautar, a hankali ya bude idanunshi da suka dan zurma sa boda wahalar tafiya, dan tunda ya shigo ƙasar bai samu ya huta ba.

Get din gidan aka bude, in da motacin suka fara shiga a hankali, suna shiga ƙaramin get wanda zai sadaka da cikin gidan in da mutane suke, aka saki wani Algaita da busa wanda ba ko wace Masarauta ake yinshi ba, sai Masarautar da suke da Kambun Sarauta, sanan Algaitar nan da Busar ba wani ne yake yinsu ba, suna busa kansu ne a duk lokacin da wani wanda yake da Haƙƙin Mulkar Sarauta idan ya biyo ta ƙofar wanda bama kowa ne ake budewa ita ba.

matse idanunshi yy sosai, dan baya son busar nan da Algaitar dan a duk lokacin da za’ayisu to gaba daya tsikar jikinshi na zubuwa ne, sai ya rasa Natsuwarshi har sai yata Addu’o’i, yanzun ma hakan ce ta kasance, har suka ƙarasa parking space aka bude mishi mota bai bude idanunshu ba, kuma bai yi wani abu da zai nuna cewar zai fito daga motar ba.

 

kusan 10 minutes da bude mishi ƙofar motar kafin ya fito, A hankali, cikin kamala da cikar Zati yake tafiya, yana babbazar Alƙyabbar da take jikinshi, hannun na rike da wani dan sada irin na sarakai ko kuma wani gawurtacce a cikin gidan Sarauta.

Ƙofar Fada da ta fi ko ina tsaruwa da shan Ado a cikin gidan Sarautar ya nufa a hankali, kafin ma ya iso, har an shiga An mishi iso da Sarki, yana zuwa ya shige, duk sauran mutanan da yake tare da su , suka tsaya a waje.

Laɓɓansa dauke da Tasbhi da Addu’o’i ya shiga, yana mai yin Sallama ciki-ciki, wata sanyayyiyar murya ce ta Amsa mishi Sallamar daga ciki , a hankali ta ci gaba da tafiya zuwa ciki, Kishingiɗe ya samu Sarki akan kujerarshi, yana shiga ya tashi ya zauna, har ya ƙaraso cikin Fadar idanunshi na cikin kanshi, shi kuwa idanunshi na ƙasa dan baya kallon mutane, kullum idanunshi a ƙasa……..
[2/22, 5:33 PM] ƳAR LELEN ROYAL STAR CE🧚‍♀️🧚‍♀️: 🌼🌼ARMAN MALEEK🌼🌼

*DAGA ALƘALAMIN*

SALMAJI ƳAR LELEN ROYAL STAR CE🧚‍♀️🧚‍♀️🧚‍♀️.

SADAUKARWA GA AMINIYATA MASOYIYATA SADIYYA ABBAKAR MARU (ƳAR GATAN ROYAL STAR )

“`WANDA YAKE SON A TALLATA MISHI HAJARSHI. ZAI IYA TUNTUƁATA TA NUMBER NA KAMAR HAKA.

07033371851

ZAMU TALLATA MAKA HAJAR KA CIKIN SAUƘI DA RANGWAME“`

 

*🌟ROYAL STAR WRITER’S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_

*Alk’alaminmu ‘yancinmu*

 

PAGE 2.

A hankali ya ƙarasa gurin kujerar da yake zama a kullum da ko Yaushe in ya shigo cikin Masarautar, zama yy tare da dan Zamowa with full respect yace “Sannu da hutawa Lamurɗe”, ya fada a hankali cikin natsuwar da ta zame mishi jiki, dan murmushin da ya tsaya mishi iya kan fuskarshi yy tare da cewa “Sannu da sauka Arɗo”, jinjinw kanshi yy bai ƙara cewa komai ba,sai da suka nisa kusan 5 minutes kafin Ahmad Arman Maleeq(Ƙanin Mahaifin Arman Maleeq), yace “Ya Barkindo da jiki ?”, ya fada maganar na tsaya mishi iya laɓɓanshi.

a hankali cikin natsuwa da kamala ya bude laɓɓansa tare da cewa “Alhamdulillah”, ya fada tare da mayar da idanunshi ya lumshe, tsureshi yy da ido na dan wani lokaci kafin ya juya idanunshi, ya dade sosai a gurin Ahmad Sarki kafin ya miƙe, A hankali yace “zan shige”, bai ji Amsar da Allaraini ya bashi ba ya fice a binshi.

har ya shige ta gaban wani side mai kyau da tsari, sai kuma ya dawo baya, a hankali ya doshi cikin palon sashen, tura ƙofa yy a hankali yy Sallama, cikin palon yana tura kanshi ciki.

cikin Kaɗuwa da razani Hamshaƙiyar tsohuwar matar da take zaune nannaɗe cikin wata ƙasaitacciyar shiga, mai kyau irin ta Masu fada a ji, ƙarasowa yy cikin palon, ya zauna fuskarshi bb walwala ko kaɗan, fuskarta ta haɗe fiye da Yarda take baya, kyakyawa ce fara tasss da ita, tana da manya idanu, da hanci har baka, sai dan ƙaramin bakinta, yana yin kallon da take bin Sheikh Arman maleeq kawai zai gamsar da cewa akawai wani abu mai kama sa ƙiyayyaeshi a cikin ranta.

Cikin Yar isa da taƙama tare da jin kanta a Sama tace “sannun Isasshe Saukar yaushe ?, yau kuma daga wata duniyar ?, Ya Ubanka yaji da jiki?”, ta fada cikin gatsali , idanunshi ya bude ya watsasu akan fuskarta a ƙaro na farko tun da ya shigo cikin palon.

Harshen shi ya taune kafin cikin ƙarfafa harshenshi da kumbura bakinshi, ya ce “Uhmmmm”, abun da ya furta kenan bai ƙara kallon in da take ba, ita ma din bata damu da maganar tashi ba, bata kuma damu da lafiyar Mahaifin nashi ba.

a Hankali ta miƙe tayi cikin bedroom dinta ba tare da ta ko kalleshi ba, Sheikh kuwa haka ya gaji da zama ya miƙe tare da barin palon, zuwa sashenshi da bayan na Sarki da Sayya(Mahaifiyar Ahmad Sarki , tsohuwar da ya fita daga sashenta) bb sashen da ya kai shi kyau a cikin Masarautar.

Fadawan da suke a ƙofar shiga cikin sashen ne suka bude mishi, ya shiga cikin palon bakinshi dauke da Kamilalliya kuma cikakkar Sallama kamar yarda Addini ya tanadar, bb kowa cikin palon, sai dai hakan bai hana komai da yake cikin palon yin aiki ba kama daga kan Fankokin da suke kunne da AC har kan hasken da ya mamaye gaba daya palon , wadda ya haska ko ina tanwar kamar rana.

 

kuma ko ina ƙal-ƙal bb alamar ƙazanta ko wani najasa, a hankali ya fara taka ƙafarshi tsakiyar palon, idanunshi a dan janye, har ya ƙarasa kan kujera 2 siter ya zauna , a hankali ya ƙarasa jaanye idanunshi gaba daya ya lumshesu, yana sauke numfashi a hankali cikin natsuwar da ta zame mishi jiki, a hankali ya dan sanya hannunshi ya fara zare half cover din da suke ƙafarsa, yana sauke numfashi a hankali,har ya gama zarewa a hankali yajaa numfashi tare da furta “Subhnallah wal-hamdulillah waa laaa’illaha’illalahu wallahu Akbar, Suhbanallah”, ya furta yana ƙara rumtse idanunshi.

nauyin da ya ji kanshi ya fara mishi sakamakon ciwon kan da ya riskeshi, yasa ya sa hannunshi tare da fara zare farin rawanin da yake kanshi ,bakinshi na kiran sunan Allah har ya gama zareshi.

kyakyawar sumar kanshi da take a barzaze mai kala biyu, ƙasa baƙiƙƙirin irin sumar Asalin Fulani, sai kuma Sama Brown kalar sumar turawa, wadda ta kasance kamar an rinata, sai dai ba rinatan akayi ba, zallar sumar kanshi ce a haka , a hankali ya dago kanshi, tsura mishi idanu nayi , sai dai na kasa ganin fuskar tashi, wadda sumar kanshi ta sauko ta rufe mishi gaba daya fuskarshi, sai dai kyakyawan cute lips dinshi da suka ƙasance pink irin na mata ake iya gani, da kyakywan sajenshi wanda ya haɗe da gumenshi, mai mugun yawa, san har kusan kirjinshi , baƙi sosai irin gemun larabawa.

a hankali yasa hannunshi ya fara zame gashin kanshi da ya zubo mishi akan fuskarshi, da sauri na matsa dan na mugun firgita da yana yin zubin tsarin fuskarshi, dan kallo daya in ka mishi baza ka gamsu cewae mutum bane, abu na farko da Zuciyarka zata fara raya maka shine ba mutum Bane Aljani ne, dan sam baya kama da mutane, sa boda tsananin kyanshi.

yana da kyan da ba kowa ne ya taɓa ganin irin kyan ba, kyanshi Ainahin kyau ne marar Algus , fari ne sosai wanda farin nashi ya sirka da jaa – jaa wanda ba’a cika ganin irin wannan farin a mutanan Nigeria din mu ba,sai dai mutanan waje, yana da yar faffaɗar fuska da bata cika fadi ba, sannan bata cika tsayi ba dai-dai misali.

yana da siririn hanci da ya dace da kyakyawar fuskarshi, uwa uba bakinshi da Idanunshi, wanda su zaka kalla ka tabbatar da cewar ba Asalin dan ƙasar bane, sa boda yarda suke, idanunshi ba za’a kirashi da blue ba ba za’a kirasu da light blue ba sai da ace musu royal , wanda suka ƙarawa fuskarshi kyau, bakinshu kuwa dan mitsitsi mai dauke da pink lips , a hankali ya bude bakinshi, jerarrun fararen haƙoranshi farare tas masu kyau da daukar ido wanda har fuskarka kana hange ta cikinsu ne ta bude , kafin a hankali yace “Alhamdulillah”, wanda na lura da cewar hakan ya riga ya zame mishi jiki, dan duk motsawar da zai yi sai ya kira sunan Allah.

Wayarshi da take ring yasa hannu ya dauja ba tare da ya duba wanda yake kiran ba, a hankali ya ƙara wayar a kunnenshi, daga chan ɓangaren aka ce “Assalamu alaika Yah Sheikh”, a hankali ya Amsa Sallamar har lokacin bai shaida wanda ya kirashi ba, sai dai yana ji a jikinshi kamar ya san muryar ko kuma ya taɓa jinta a wani guri.

Cikin sauke Ajiyar zuciya Dr din yace “Ranka ya dade Yah Sheikh “, ya fada a ƙasalance yana gyara amanshu kan kujerar da yake zaune,a hankali ya furta “Uhmmm!”, wanda shi din ma na lura ya zamar mishi jiki, ya fi ganewa yy hakan da yy magana.

A hankali yace ” ni ne Dr din da ka bawa Marar lpy Ɗazun”, a hankali yace “hope everything is fine”, ya haɗa yana lumshe idanunshi da sauke numfashi, jinjina kai Dr din yy tare da cewa “to lpy ba lau ba, dan gaskiya ta samu babbar matsala ga kuma dama matsalar da take fama da ita, sai abun ya haɗu ya ƙara dagula lissafin jikinta”, gyara zama yy tare da sauke numfashi, kafin yace, “ina bukatar duk wani information a kan ta, send me”ya fada yana kashe wayar.

A hankali ya mike ya shige ciki , wata ƙofa ya nufa, yana budewa wani kyakyawan bedroom mai dauke da bed da wadrobe sai carpet , bedside drower , sai wata doguwa kujera 3siter wadda za’a iya kwanciya kai, gefe kuma wani dan lugun ne mai dan faɗi, wanda yake dauke da table wanda litattafan Addini ne kawai a kai, sai wata Yar kujerar zama, wadda da alama ita ce wadda ake zama ayi karatu, Sallayarshi da Chasbharshi Agefe a ajiye .

A hankali ya ƙarasa gefen babban bed din da ya mamaye kusan rabin bedroom din, bai zauna ba, sai ta nufi wani ƙofa in da anan wani kyakyawan bathroom mai tsaro irin na wayyayu ya bayyana, wani katon mirror da yake ajiye a gefen bathroom din ya dan tura, wanda take wata ƙofa ta bayyana , da mamakina naga ya murɗa hannun ƙofar ya shiga ciki, wani rantsatsen bedroom da ya fi na baya haɗuwa ne ya bayyana.

gaba daya kayan bedroom din green ne da white, wanda kalar tayi mugun fito da bedroom din, gefen bed din da ya sha shimfiɗa da green and white bed sheet ya nufa, bai zauna ba daga tsaye Shehi ya fara warware igiyoyin Alƙyabbar jiknshi, sai da ya kunce kafin ya zameta daga jikinshu a hankali, cikn natsuwa ya ajiyeta a gefen bed din, lokacin kuma na ƙare mishi kallo, babban mutum ne sosai dan a kalla in bai yi 33 years ba zai iya yy 29 to 30 years, yana d dan faɗi ba sosai ba yana da tsawo da faffadan kirji, ba za’a kirashi mai jiki ba ba kuma za’a kirashi marar jiki ba,bashi da ƙiba yana tsaka tsakiyar jiki, irin na Jarumai ko in ce sadaukai.

bayan ya zame Alkyabbar ya ajiye, wani farin boyel ne mai kyau da taushi ya bayyana , ya ji dinkin surfani da ya kasance Golding , sosai dinkin yy kyau kuma ya dace da jikinshi, wata ƙofa naga ya ƙara nufa, nan kuma wani Bathroom din ya ƙara bayyana wanda shima komanshi ya kasance green da white gwanin kyau.

bottom din gaban rigarshi ya shiga ballewa, bayan ta cire rigar wata rigarce ta ƙara bayyana, haka bayan ya cire dogon wandon Boyel din wani wandon mai dan tsayi da ya kusa rufe ƙafarshi ya bayyana, ajiye kayan da ya cire yy a jikin hanger, matsawa yy jikin shower ya sakar wa kanshi ruwa, a hankali ya furta “Subhanallahi”, ya fada yana lumshe lu-lu eyes dinshi, wanda hakan yy sanadiyar kwanciyae eyes lashes dinshi, wanda suka kwanta a ƙasan idanunshi suka yi zaro-zaro sakamakon ruwan da take sauka a kanshi wanda yake gangara har cikin jikinshi gaba daya .

gashin kanshi kuwa gaba daya ya rufe mishi fuskarshi ya zamana ba’a iya ganin fuskarshi, sa boda gashin kanshi da ruwa ya jiƙa ya zubo, ya dade sosai ruwan na dukan jikinshi, kafin ya dauki wani soso mai taushi da Sabulun Dove mai gyara fata da sanyata taushi ya fara gogawa jikinshi ba tare da ya cire kayan jikinshi ba, while ruwan da ya kunna yana dukan kanshi.

duk kuwa da ga komin wanka nan amma bai damu da yin wankan ciki ba, domin yana koyawa kanshi rashin jin dadi, domin yana duba wanda basa da dukiya ya suke, shin lokacin da Allah ya yanke maka wani jin dadi ya zaka yi?, hakan yasa wani lokaci yake dan nuna wa jikinshi ba fa kullum ake kwana gado ba dolle wata ranar a kwanta a ƙasa.

har ya gama wankan mai matsa daga ƙasan shower din da take dukan jikinshi ba, sai da a ko wane lokaci yana ƙara rumtse idanunshi da kiran sunan Allah har ya gama wanka.

yana gamawa ya nufi wata Yar kofa ya bude, ya shiga tsarin jararrun kaya ne musu kyau da tsari tare da tsada suka bayyana a cikin gurih, wanda hakan ya tabbatar min da cewar gurin Adana kaya ne.

dan sakaya ƙofar yy..kusan 10 minutes kafin ya turo ƙofar ya fito kamshin turaremshi na Huge boss din da na shaƙa ne ya tabbatar min da fitowarshi, cikin wani shigar ta Ash din Jallabiya har wa yau kanshi na nannaɗe da rawani , a haka ya fito yana ta baza kamshi, kafarshi sanye da wani slippers mai taushi a hankali yale takawa har ya fita dayan bedroom din , zama yy kan bed, tars da daukar wayarshi da take haske alamar shigowar saƙo, a Gmail dinshi ne aka turo mishi saƙon.

hakan yasa ya zauna cikin bawa Saƙon muhimmanci , a hankali ya bude saƙon, Abun da ya gani yy mugun girgiza mishi tunaninshi, tare da sanya duniyarshi cikin wani, firgitaccen yana yi, a hankali yace “Innalillahi wa’inna’ilaihi raju’un, Allahumma Ajrni fiii masibati “, ya fada yana ƙara duba saƙon Dr din .

kafin ya gama banbance halin da Yarinyar take ciki a lokacin Dr y kira, a hankali ya ƙara mishi bayani, “kamar yarda na rubuta maka, gaskiya tana buƙatar ganin Manyan Likitoci domin su dubata da kyau tare da bata duk wani treatment da ya kamata, babbar Jijiyar dai da take riƙe da jinta tare da maganarta ne ta samu matsala domin tama zaro daga in da take sakamakon mumunan haɗarin da sukayi, sannan ta ko ina jikinta raunika ne, gashi kuma tana dauke da Asthma mai karfi sosai, gashi kuma wani sashe daga zuciyarta yana da matsala, kodarta ma daya tana da matsala, wadda in ba’a gaggauta mata aiki ba zata iya rasa Rayuwarta, gaskiya Yarinyar nan tana ciikin haɗari domin ta shiga cikin Critical condition. wanda bayanin shi zai yi wuya, da mugun wahala ta rayu”,ya fada cikin wani yana yi.

wani zazzafan breath Shehi ya sauke, cikin kamilalliyar muryarshi mai tattare da gaji yace “Uhmm”, yana fadar haka, ya,kadhe wayar dan ya tabbatar da cewar Dr din ya gaɓa duk bayanan da zai mishi.

Agogon bangon da take maqale a jikin bangon bedroom din ya kalla, ganin lokacin Sallar Magrib ya gaba to, ya sashe miƙewa, dan in dai yana nan bb mai Limancin Masallacin Masarautar sai shi.

A hankali ya……

 

Littafin nan na kuɗi ne #400 ne kuɗinsa,ga mai so zai iya tuntuɓata domin sanin ta yarda zai biya kuɗinsa.

 

07033371851

DAGA TASKAR ƳAR CE🧚‍ARMAN MALEEK

*DAGA ALƘALAMIN*

SALMAJI YAR LELEN ROYAL STAR CE🧚‍♀️🧚‍♀️🧚‍♀️

SADAUKARWA GA AMINIYATA MASOYIYATA SADIYYA ABBAKAR MARU (ƳAR GATAN ROYAL STAR)

“`MASU SON A TALLATA MUSU KASUWANCIN SU ZASU IYA TUNTUƁATA AKAN NUMBER NA KAMAR HAKA.

07033371851“`

*🌟ROYAL STAR WRITER’S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_

*Alk’alaminmu ‘yancinmu*

 

Page 3.

 

A hankali ya miƙe, tare da daura baƙar Alƙyabba mai dan saukin nauyi a jikinshi, tare da ƙara gyara Rawanin kanshi, sai yy fito A Ahmad Sudeis sak.

cikin Kamala da natsuwa yake tafiya, yaba ta ƙara baza kamshin turarem Huge boss da, ya kama mishi jiki sosai dan har ko bai sa ba, to zaki ji kamshi a jikinshi.

yana Zikirin maraice ya fito daga bedroom din, zuwa palo, kasantuwar yana da Alwala yasa bai tsaya yin wata ba, ya nufi hanyar fita, a ƙafarshi yy shiga tattaki zuwa Masallacin da yake faron Masarautar in da anan kowa dan cikin Ahlin masarautar yake gabatar da Sallarshi.

yana tafe yana zikirinshi, har ya ƙarasa Masallacin, gaba daya Jama’ar da suke bakin Masallacin suka miƙe, tare da fara mimmiƙa mishi hannu, suna gaiswa, wani ɗan tsoho ne yace “Yah Shehin Malamin mu ka guji Ƙasarmu , bayan lokaci mai dan tsawo da ka bar nan sai a cikin Talabijin muke ganin ka, fatan dai komai lafiya?, Ya Mai martaba Abdul-azeez Arman Maleeq Sarki da jiki?”, ya fada yana dunƙule hannayeshin.

karo na farko da tunda ya shigo cikin Masarautar da yy amfani da tattausar murya mai dadin Sauraro yy tsohon magana a hankali cikin rashin son maganarshi, ganin lokacin Sallah na shigewa Yasa ya nufi cikin Masallaci duk mara mishi baya suka yi suna Addu’ar Samun Sauƙin wa Abdul-azeez Arman Maleeq Sarki
, gurin Liman ya tsaya tare da kabbara Sallah cikin zazzaƙar muryarshi, gaba daya garin sai yy tsitttttt ana saurarar sautin karatunshi.

Masallacin kuwa kowa ya natsu, zukatansu gaba daya sun narke da jin Muryarshi da suka dauki tsawon wattanni basu ji ba, haka har Aka ƙarasa Sallah, gyara zamanshi yy, tare da nannade ƙafafunshi ya juya gurin dubban jama’ar gurin, wanda bb wanda ya fita duk suna zaune, suna jiran karatunsa.

Manyan Littatafan Addini ya dauka, dauka tare da fara koyae da su, cikin harshen fulatanci in yy da hausa yy da fulatanci yy da turanci, dan kusan rabin mutansn basa jin hausa, wasu kuma basu ciks fahimtar fulataccin ba, kasantuwar garin ya haɗa ƙabila biyu, hausa da fulani.

har lokacin Isha yy yana zaune yana koyar da su, sai da A kayi Sallar Isha kafin ya mike zuwa cikin gida, bakinshi yana ambaton sunan Allah,haka ya ratsa dukkan parts din da suke gidan har ya isa nashi part din,yana shiga ya zauna a palo tare da lumshe idanunshi, da suke dauke da tsananin gajiya , da barci.

bai fi 10minutes da zama ba, aka turo ƙofar Pallon, bai ɗago da idanunshi ba har wanda ya shigo ya iso tsakiyar palon, bb ko Sallama haka ta tsaya mishi a ka, a hankali ya fara bude idanunshi har ya saukesu akan Jadda da take tsaye.

mayar da idanunshi yy ya rufe, san dama yasan wani kayan sai Amale, cikin zazzaƙar muryarshi yace “ke baki iya Sallama ba ?, ko ke Arniya ce ?”, ya fada cikin rashin damuwar cewae Ita Jaddar Babbar mace ce dan A kalla zata iya yin 95 a shekaru,sai dai yarda ta zubar da girmanta, sa boda yar da take babbar da batasan girmanta ba, ta tsaneshi bata son shi, bata kaunar Mahaifinshi da Mahaifiyarshi Da Yan uwanshi kullum neman abun da zai cutar da su take nema.

wani kallo ta mishi tare da cewa “ai kasan ni dangin Maimoon ne Uwarka sune basa Sallah dan Ubanka”, ta fada cikin harzuƙa…

taɓe bakinshi yy bai ce mata komai ba, ita kuwa haushin rashin kulatan da yy yasa ta fice a faɗace tana zazzaga mishi zagi, sai da ta bar gurin kafin ya miƙe, ya nufi hanyar Upstairs dinshi, yana zuwa ya tura ƙofar ya shiga, bai zauna a na dayan ba sai ya shige chan na biyun, bathroom ya shiga yy wanka tare da dauro Alwala ya fito, Shafa’i da Wuturi yy, yy Addu’o’i da karatun Al-qur’ani, kusan 11pm yana karatub cikin muryarshi mai dadi kafin ya miƙe daga in da yake.

gefen bed ya zauna, tare da dan daura hannunshi akan cikinshi, ya lumshe idanunshu, fuskarshi ya dan yamutsa tare da dan shagwaɓeta, kaɗan irin na Shagwaɓaɓɓun da in suka samu wuri to zasu zuba shagwaɓa, a hankali ya miƙe ya nufi fridge din da ke kusa da bed din.

budewa yy , tare da fitar da peak milk mai sanyi sosai, tare da wata gorar zuma mai kyau, cup ya dauka ya daurayo, ya dawo tsakiyar carpet din da yake walale bakin bed din shi,zuba madarar yy ya sanya zuɓa, tare da sanya Spoon ya fara jujjuyawa sai da ya tabbatar ya haɗe jikinshi.

kafin ya dauka da Bissimillah..!, dauke a bakinshi ya kafa kanshi, sai da ya shanye tasss kafin ya ajiye cup din, sanyayyiyar gyatsa ya saki tare da lumshe idanunshi.

 

gefe ya mayar da cup din da gwangwanin ya, matsa ya jingina kanshi da jikin bed din yy shiru, idanunshi a lumshe kamar msi barci, a zahirin gaskiya kuwa ba barcin yake ba,tunanin rayuwa kawai yake..

A hankali guraren 1 ya miƙe daga zaunan da yake, ya nufi bathroom, alwala ya ƙara daurowa, yana fitowa ya sanya wata lafiyayyiyar Dubai Jallabiya mai masifar kyau black da tayi asalin fito jishi da tsantsae farin fatarshi.

gurin pray met dinshi ya matsa, tare da kabbara Sallah, cikin zazzaƙar muryarshi ya ringa rairo karatun Al-qur’ani, har guraren 4 sai da aka fara kiran Sallah Subhi kafin, ya tsagaita ya koma gefe yana karatu da Tasbihi 4:30am ya miƙe , Sabon Wanka da Alwala yy, tare da chanja kaya, ya nufo hanyar waje.

Shi daya ya fara takawa daga cikin Masarautar zuwa Masallaci , a hankali yake tafiya, bakinshi kuma har lokacin bai gushe da ambaton sunayen Allah ba da Addu’o’i tare da Tasbhi , haka har ya fita daga part dinshi, ya fara ratsawa ta cikin masarautar da bb kowa, bb motsin kowa, sai sanyayyiyar Iska Asuba da take kaɗawa, wadda take dauke da ni’imomi da wani yalwataccen nishaɗi, iska ce mai sanyaya zuciya, da sanya ruhi cikin natsuwa, iska ce mai dauke da iskar hadari wanda ya gangamu garin yy baƙiƙƙirin kamar za’a kece da ruwa.

haka yake tafiya cikin rashin tsoro, har ya ƙarasa Masallacin da bb kowa a ciki, A hankali ya ƙarasa cikin Masallacin, sai da ya dudduba komai kafin ya fito, tsayawa yy daga dan gaba cikin rumfar Masallacin, ya kauɗa kiran Sallah cikin sanyayyiyar muryarshi mai dadin gaske.

wadda tayi sanadiyar tashin kusan dukkan Al-ummar Masarautar tashi daga barcin da suke yi, gaba dayansu zuciyarsu tayi wani irin taushi jikimsu duk ya saki, kwaɗa kiran Sallarshi na biyu ne yy Sanadiyar tashin duk wani mai gigga-giggan masu Jinnun da suke cikin Masarautar, dan dama aje ne, duk lokacin da zai sauka masarautar, yy kiran Sallah to , duk wani mai gigga-giggan Aljannu da suke cikin Masarautar sun tashi.

cikin Azama gaba daya Ahlin Masarautar maza gaba dayansu suka yo Masallaci domin gabatar da Sallah Subhi , kafin kace Kwabo Masallacin da bb kowa ya cika damkam da Mutane, wanda cikarsu ma har tayi yawa, hakan zai shaida maka ba mutane ne kawai ba, cikin Nishaɗin da ya tsinci zuciyarshi a cikinshi, ya fara karatuh Al-qur’ani cikin Surarul Maryam, wanda gaba daya dadin Surar da Daddin Muryarsa yasa illahirin Aljannu , Mutane , Dabbobin da suke cikin gidan suka yi tsiiiittttt suna saurararshi, hatta da iskar Hadarin da take kadawa da karfi sai ta daina kaɗawa da karfin, sai sanyayyyiyae iska da take ratsa ko ina, har sai da ya idar da Sallah, gaba daya wata iriyar iska mai karfi ta fara kaɗawa.

kan kace wani abu ruwa ya fara dan sauka a hankali, duk da haka sai da yy musu karatu sosai kafin a tashi, shine last din fita daga Massalacin sai da ya rufe kafin, ya fara tafiya cikin natsuwa .

lokacin 6am tayi, a hankali yake tafiya yana sauke numfashi, sai da ya kusan shiga cikin part dinshi, kafin ruwan ya fara sauka sosai kamar da bakin kwarya, har sai da yasa Shehi ya dan kara takun tafiyarshi da yake yi, duk kuma da haka cikin natsuwa yake tafiya,har ya ƙarasa.

palon ƙasa ya zauna, yana zama wata Babbar mace da zata iya kai wa 60years fara ta fito daga wata hanya fuskarta washe da murmushi, cikin dan farin cikin da ya mamaye gaba daya fuskarta da zuciyarta tace “Assalamu alaika…!”,a hankali ya bude idanunshi,jin muryar da ta daki dodon kunnenshi.

wani murmushi da ya kusa kasheni ya sakar mata, kafin ta mayar da kamilalliyae fuskarshi kamar yarda take yace “Wa’alaikissalama…!”, ya fada cikin sanyayyiyar muryarshi, idanunshi yy ƙasa da su kafin ya dan murya zoben Zinarin da yake cikin hannunshi da yake fitar da wani kyalli na musamman.

cikin bada girma da rissinawa, tace “Barka da Asuba Shehi..!”, a hankali ya furta “Uhmmm Coffee..!”, ya fada a hankali ba tare da yace komai ba , miƙewa tayi tare da cewa “bari na haɗa maka” tana fada ta bar gurin shi kuwa ya lumshe idanunshi.

bata dauki wani lokaci mai yawa ba ya dawo hannunta daure da ƙaramin tray mai dauke da wani flask ƙarami, da cups da tea spoon sai sugar, dan tasan zalla ake haɗs mishi shi yake aa sugar da kanshi.

Stool ta jawo ta ajiye gabanshi, kafin ta dan rusunar da kanta tace “Shehi an gama”, tana fada ta matsa chan ta zauna, kan kujera ta zauna, tana dan kallonshi,shi kuwa a hankali ya bude idanunshi, tare da dan rankwafawa, ya dauki cup din ya dan tsiyayi rabin cup ya zuba Sugar tea spoon huɗu, tare da fara dan gaurayaww har ta narke, kafin ya matsa gefe, da Bissimillah ya fara dan sipping dinshi har ya shanye tass, ya ajiye cup din.

A hankali ya dan kalleta da idanunshu, yace “Ngd …”‘, ya fada yana dan mayar da kanshi akan kujerar, jinjina kai tayi ba tare da tayi magana ba.

Dan Jim sai ga wanu kyakyawan matashin Sarauyi ya shigo cikin palon, cikin dan murmushi yace ”Barka da safiya Shehi . barka da safiya Umma Jakadiya”, murmushi tayi tare da cewa “barka Zayn-Maleek . fatan kun sauka lpy ?”, dan shiru yy tare da cewa “Qlau Umma”, jinjina kanta tayi.

kallon Shehi Arman_Maleeq , Zayn-Maleeq yy tare da cewa “Yaa Shehi komai fa ya gama kammala. kayan suna wajen Masarauta zuwa Anjima za’a shigo da su.” shiru Arman_Maleeq yy bai cewa Zayn_Maleeq komai ba…

daga karshe ma miƙewa yy ya haye sama, duk binshi da kallo suka yi, kafin Zayn_maleeq ya koma inda ya tashi, tare fara haɗa Coffee sai da ya gama ya kallin Umma Jakadiya yace “Umma An jima Shehi zai raba kayan Azumi, dan wannan karon ba zamu jima ba zamu koma,na ji kuma kamar Ammie tace a taho da ke “, ya fada yana surɓar Coffeen, murmushu tayi tare da cewa “Zayn_Maleeq baki abin magana, Allah ya kai mu, ” dariya yy tare da cewa “Su Umma za’a hau jirgi a tafi Madina”, dariya itama tayi cikin sabo da irin rahar Zayn_maleeq tace “Oh Zayn_maleeq baka gajiya. abin da ba zuwana na farko bane wannan, bari na tashu na shige”, ta fada tana miƙewa..

 

******

Gaba daya kusan Drs Biyar ne a kanta bayan Nurses dukkansu sun rufa a kanta, suna dubata, dan gaba daya numfashinta daukewa yy , yana sama da ƙasa, sai shasheƙa take, gaba daya jijiyoyin jikinta sun fito, jikinta ya dauki wani rawa.

Gaba daya Drs din su fara sarewa da lamarin Yarinyar, cikin lokaci dan kaɗan zata birkice , sai kuma jikin ya dai-daita, yanzu ne abun ya fi ko yaushe gaba daya, ta birkice sun kasa yarda zasuyi da ita.

Dr Aslam wanda ya fara daukarta , ya fito yana sharce zufa idanunshi sunyi jaaazir, hatta kayan jikinshi sun jiƙe da zufa, Office dinshi ya shiga, ya zauna ya dafe kanshi…

sai kuma ya ɗago kan tare, da daukar wayarshi. lallatsawa ya shiga yi kafin ya karata a kunnenshi.

sautin ring din Wayar Shehi ne ya fara tashi cikin bedroom din nashi, lokacin 9am ,a hankali ya dan mirgina da Addu’ar tashi daga barci cikin bakinshi, ya miƙa hannunshi, ya dauku wayar, sai da ya duba sunan mai kiran kafin yy picking call din ya ƙara a kunnenshi.

Zallar tashin hankalin da ya ji a cikin muryar Dr din ne yasa ya dan muskuta ya gyara zamanshi,cikin gaggawa yace “Shehi a gaggauta fitar da Yarinyar nan domin yi mata dashen nan,dan jikin gaba daya ya rikice bb sauƙi gaba daya, numfashinta ma baya fita, gaskiya tana cikin hali, in da hali ayi duk abun da za’ayi a yau din nan zuwa gobe a fitar da ita,”sauke numfashi yy .

 

kafin yace “akwai abokina da yake irin wannan …….

 

Wannan littafin na kuɗi ne , game buƙata zai iya tuntuɓata ta number na kamar haka.

About the author

Hausa_Novels

Leave a Comment