Littafan Hausa Novels

Anyi Walkiya Hausa Novel Complete

Written by Hausa_Novels

Anyi Walkiya Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

ANYI WALKIYA

 

NA M. JABO & MAMAN

TWINS COMPLETE.

 

 

AN YI WALK’IYA 1-3

©Mrs Saif & Hauwa M. Jabo

®NHW

Da gudu take hawa kan matattakalar benen,

kamar zata fad’i, tana k’wala kiran “Mummy!

Mummy!!” da sauri Mumyn ta fito daga wani

d’aki, tana cewa”lafiya?? Arfat irin wannan kira

haka! sai ka ce wadda ta yi gamo?.”

A jiyar zuciya ta sauke, tare da k’ank’ame

Mummy, sannan cikin shagwaba tace ” Mummy

ba yaya Abeed ba ne ya biyo ni, wai sai ya

dakeni,” “Duka! Ai ko ruwan sama bazai dakar

min ke ba bare shi, wai ma to me kika masa da

zai dake kin?”

Arfat na shirin magana ya k’araso gurin yana

fadin”Yauwa Mum mik’o min ita, Allah yarinyar

nan yau sai na 6a66allata a gidannan, don

akanki zan huce haushi “. Ya k’arashe maganar

yana k’ok’arin janyota daga jikin Mum.

Mummy tace”Nak’i na mik’o ta, kaji yaro, amma

bakada ma kunya, ai ko mutuwa na kunyar idon

mahaifi, yarinya har bayan mamanta ta b’uya

kana a mik’ota, sai kace wata y’arka, wai kai

me yake damunka ne Abeed?

Mai ya faru kake neman 6a66alamin yarinya

haka,?” Abeed yace “Mum yarinyar nan tana

zubar min da class Wallahi,ke kuma kina wani

kakkare mata,” ya fad’a yana wani yarfee

hannuwa, yana juya jikinsa irin dai yanda

hadaddun guyz sukeyi d’innan “Mum wata

nataciyyar yarinya ce ta lik’a min, ita kuma ta

wani mak’alemun, kamar mayya haka take, Allah

Mum tafi gum mannewa, kuma duk adalilin

Arfat” ya fada yana nunata da yatsa yana

hararanta, “don k’awarta ce, ita ta ba ta

numberta, kuma ko Mum? Ba irin wulak’ancin da

ban mata ba, amma ta k’i daina kirana dan naci

irin nata”

Mummy tace” haba Abeed ina laifin wanda yace

yana sonka ? Yanzu dan Allah akan haka za ka

dakar min yarinya, tanason ta had’a sunnar

Annabi kai kuma kana shirme, to in gaya maka

ban yarda ba.”

Arfat da ta la6e bayan Mum tace ” Mum kuma

ba ki ganta ba, Allah ta hadu na k’arshe bakiga

yanda take yarfa gayuba”

Danllah rufee ma mutane baki, ya ja dogon

tsaki, “had’uwarta ta banza, ke wai yaushe zaki

gane cewa yanzu komai saida Coins ake yinsa,?

Yanzu gaya mun waye babanta a k’asar nan.?

‘yar gidan malam Shehu da ita ta zo tana

damuna kawai”.

Mummy murmushi kawai ta yi, dan tasan

k’arshen zancen kenan yace talakace, ” Talaka

bawan Allah nidai M. jabo da M. Twins munsan

cewa talauci daga Allah ne, haka dukiya ma

daga Allah, mafi d’aukaka da soyuwa a gurin

Allah shine maki tak’wa a cikin bayin Allah ”

Mum kam idan da sabo ta riga ta saba da halin

Abeed, tun bai kai haka ba, halinsa ke nan tun

yana yaro, tun tana ganin kamar k’uruciya ne,

har yazo ya girma bai daina ba, yanzu kam har

ta daina tunanin yarinta ne, don shekarunsa ya

wuce a kira shi da k’aramin yaro.!

“Dallah b’ace mun da gani, kamin na k’araso na

makeka kamin ka maketa a gun,” yayi gwafa, ya

gangaro yana guna guni, “ke kuma idan na

kamaki I will show u.”

************

Yarima Fadeel Hausa Romantic Novel Complete

Alhaji Bashir Nasari, shine cikakken sunan

mahaifinsu, haifaffen garin kano, kuma

hamshak’in d’an kasuwa ne, yana da arzik’i

sosai don yana d’aya daga cikin manyan ‘yan

kasuwa a jahar kano.

Matarshi d’aya Hajiya Maryam, wadda suke kira

Mummy.

Allah ya azzurtashi da yaransa uku Muhammad

da ake kira da Abeed, sai Arfat sai kuma Afrat.

Gida ne wanda mamallakan sa suka gina cikin

so da k’aunar juna, ga ilimi dai_dai gwargwado

suna da tarbiyya.

Sai dai Abeed ya fita daban, akwai girman kai

da Jin shi wata tsiya ne, uwa uba rashin ganin

talaka da gashi, don shi duk abinda zai had’ashi

da talaka baya son shi kwata_kwata a

rayuwarsa

Don haka ya k’udiri niyyar shi ba zai yi aure ba

sai ‘yar wani babban mai kud’i a k’asar nan ko a

duniya baki d’aya.

Duk da iyayenshi suna nuna masa illar hakan

amma ba abunda ya chanza daga halinsa…..

Www.jabohauwa.WordPress. com

Www.hauwajabo.blogspot.com

M Twins 😍 Auntie M. jabo

 

 

 

AN YI WALK’IYA 4&5

 

©Mrs Saif & Hauwa M. Jabo

®NWA

Misalin 8:30AM, ya fito cikin shirinsa na zuwa

office, saboda shine MD. na babban companyn

Daddy dinsu, dake sharad’a phase 2.

Direct dinning area ya nufa, da nufin yin

breakfast, karaf idonsa akan ladi, ya hango ta

(d’aya daga cikin masu aikinsu) ta gifta ta

wurin dinning table d’in, hakan shi ya tilasta

masa tsayawa tare da k’wala mata kira, jiki na

rawa ta k’arasa inda yake tace”ga ni yalla6ai ” ”

ke wai wani irin kunnen k’ashi ne da ke ? Eh?

Sau nawa zan ce dake idan an kawo mun abinci

kada ki kuma zuwa ko hanyar da aka bi aka

wuce da abincin, bare kuma kusa da shi”? cikin

rawar murya tace “don Allah ka yi hak’uri, akasi

aka samu yallab’ai, naga har takwas da rabi na

d’auka ka tafi ohis, shiyasa amma ba da niyyar

zu……. ” ya katseta tare da fad’in “shut up!

tashi ki ba ni wuri ‘yar sa’ido kawai, har an san

lokacin da nake fita da kuma lokacin da nake

dawowa, munafukai ‘yan sa ido”jiki a sa6ule ta

mik’e ta fice daga parlourn.

Wani wawan tsaki yaja, sannan ya juya a

yangace ya hau kiran Afrat , da d’an hanzarinta

ta fito daga d’akinsu tace”ga ni yaya”

Abeed yace “waye ya yi girkin can ?” tare da

nuna mata da hannu, tace” haba sai ka tambayi

wanda ya maka girki, ni na yi mana” ya harareta

“ke banason rashin kunya kinaji, are you sure ke

kikayi,?” Kamar ba zata amsaba chan ta ta

gyad’a kai tare da cewa “Im pretty sure”.

Yace “kin dai san halina duk ranar da ku ka

sake ku ka bawa ‘yan aiki girkina sai kun

gayawa aya zak’inta, tace” haba yaya ai ba ma

ba su, ni ko Arfat muke yi, “gud kya iya tafiya”,

ta wuce aranta tace “sau nawa kana lamushe

girkin yan aiki, har kana santi, wane mara aikin

ne zai zaman tashi tunda asuba yana maka girki,

sai kace wasu matanka,” ta wuce d’akinsu, ya

zauna ya yakuci wannan ya tsikari wanchan, duk

jarabarshi baya iya chin abinci sosai, ya k’are ya

wucee office…

 

 

******

Misalin k’arfe12 na rana Mubarak babban abokin

Abeed ya kai masa ziyara a office d’in sa, bayan

sun gaisa yake sanar da shi zancen dinner da za

a yi na auren abokinsu Jabir.

Sannan ya k’ara da cewa “please Abeed ka yi

k’ok’arin attending, don nasan halinka yanzu za

ka fara kawo mun k’abli cikin ba’adi”

Sai da ya d’aga hannayensa ya watsar alamar

ko oho,!, Sannan ya ce ” alright yanzu gaya

mun venue da time na ji idan zan iya zuwa

gurin”,murmushi Mubarak ya yi yace “za ma ka

iya zuwa wurin, don ba 6oyayyen guri ba ne”.

Abeed yace”No my man, ba abin da nake nufi ba

kenan , I mean gurin ya yi had’uwar da kamar

irina zai je wurin ko kuwa”?

Mubarak hannunsa ya d’auka ya d’ora kan

goshinsa yace “oh! Abeed ka na ba ni mamaki

wallahi, wai mai…….” hannu Abeed ya d’aga

masa alamar ya saurara haka.

Sannan yace”just answer my question ”

Mubarak yace” ok, a golden Dragon ne”. Almost

5 minutes bai ce komai ba, har Mubarak ya gaji

da shirun yace”ya dai?

ba ka ce komai ba “. Sannan Abeed ya yamutsa

fuska, wanda ya k’ara bayyanar da kyansa, a fili,

“gaskiya ba zan je ba ne cox wurin bai mun ba!”.

Mubarak ye zaro ido cike da mamaki, “yanzu

Abeed golden Dragon ne bai maka ba?” Kai ya

gyad’a alamar Eh..

Mubarak yayi murmushi, dan yasan Abeed saida

rarrashi, ya cigaba da cewa “gaskiya my man

idan ka yiwa Jabir haka ba zai ji dad’i ba”

Abeed yace”ban yi don na 6ata ransa ba, zan

masa waya ma na bashi hak’uri, bana son zuwa

guri ne na tarar da tarkacen mutane marasa aji

a gurin, wannan ne kawai badan wannan ba

zanje mana” “amma ai ka san waye Jabir! kuma

ka San waye mahaifinsa a garin nan, so bana

tunanin za’ayi k’aranta a gurin, ka sa ni ma ko

ka had’u da wata ‘yar minister acan ya fad’a

yana murmushi.

Ya tsine fuska Abeed ya yi, yace” ‘ ya’yan

ministers ai suna suka tana, kamar ‘yar k’

aramin minister mai zan yi da ita” shi dai

Mubarak ido kawai ya zuba yana kallonsa domin

al’amarin Abeed ya girmi tunaninsa, da k’yar ya

samu ya lalla6ashi ya amince akan zai je.

Muje zuwa muji mizai faru a gun…….

Www.hauwajabo.blogspot.com

Www.jabohauwa.WordPress.com

M Twins & Auntie M. Jabo

 

 

Wacce Zamuyi Book:

AN YI WALK’IYA 4&5

 

 

©Mrs Saif & Hauwa M. Jabo

®NWA

Misalin 8:30AM, ya fito cikin shirinsa na zuwa

office, saboda shine MD. na babban companyn

Daddy dinsu, dake sharad’a phase 2.

Direct dinning area ya nufa, da nufin yin

breakfast, karaf idonsa akan ladi, ya hango ta

(d’aya daga cikin masu aikinsu) ta gifta ta

wurin dinning table d’in, hakan shi ya tilasta

masa tsayawa tare da k’wala mata kira, jiki na

rawa ta k’arasa inda yake tace”ga ni yalla6ai ” ”

ke wai wani irin kunnen k’ashi ne da ke ? Eh?

Sau nawa zan ce dake idan an kawo mun abinci

kada ki kuma zuwa ko hanyar da aka bi aka

wuce da abincin, bare kuma kusa da shi”? cikin

rawar murya tace “don Allah ka yi hak’uri, akasi

aka samu yallab’ai, naga har takwas da rabi na

d’auka ka tafi ohis, shiyasa amma ba da niyyar

zu……. ” ya katseta tare da fad’in “shut up!

tashi ki ba ni wuri ‘yar sa’ido kawai, har an san

lokacin da nake fita da kuma lokacin da nake

dawowa, munafukai ‘yan sa ido”jiki a sa6ule ta

mik’e ta fice daga parlourn.

Wani wawan tsaki yaja, sannan ya juya a

yangace ya hau kiran Afrat , da d’an hanzarinta

ta fito daga d’akinsu tace”ga ni yaya”

Abeed yace “waye ya yi girkin can ?” tare da

nuna mata da hannu, tace” haba sai ka tambayi

wanda ya maka girki, ni na yi mana” ya harareta

“ke banason rashin kunya kinaji, are you sure ke

kikayi,?” Kamar ba zata amsaba chan ta ta

gyad’a kai tare da cewa “Im pretty sure”.

Yace “kin dai san halina duk ranar da ku ka

sake ku ka bawa ‘yan aiki girkina sai kun

gayawa aya zak’inta, tace” haba yaya ai ba ma

ba su, ni ko Arfat muke yi, “gud kya iya tafiya”,

ta wuce aranta tace “sau nawa kana lamushe

girkin yan aiki, har kana santi, wane mara aikin

ne zai zaman tashi tunda asuba yana maka girki,

sai kace wasu matanka,” ta wuce d’akinsu, ya

zauna ya yakuci wannan ya tsikari wanchan, duk

jarabarshi baya iya chin abinci sosai, ya k’are ya

wucee office…

******

Misalin k’arfe12 na rana Mubarak babban abokin

Abeed ya kai masa ziyara a office d’in sa, bayan

sun gaisa yake sanar da shi zancen dinner da za

a yi na auren abokinsu Jabir.

Sannan ya k’ara da cewa “please Abeed ka yi

k’ok’arin attending, don nasan halinka yanzu za

ka fara kawo mun k’abli cikin ba’adi”

Sai da ya d’aga hannayensa ya watsar alamar

ko oho,!, Sannan ya ce ” alright yanzu gaya

mun venue da time na ji idan zan iya zuwa

gurin”,murmushi Mubarak ya yi yace “za ma ka

iya zuwa wurin, don ba 6oyayyen guri ba ne”.

Abeed yace”No my man, ba abin da nake nufi ba

kenan , I mean gurin ya yi had’uwar da kamar

irina zai je wurin ko kuwa”?

Mubarak hannunsa ya d’auka ya d’ora kan

goshinsa yace “oh! Abeed ka na ba ni mamaki

wallahi, wai mai…….” hannu Abeed ya d’aga

masa alamar ya saurara haka.

Sannan yace”just answer my question ”

Mubarak yace” ok, a golden Dragon ne”. Almost

5 minutes bai ce komai ba, har Mubarak ya gaji

da shirun yace”ya dai?

ba ka ce komai ba “. Sannan Abeed ya yamutsa

fuska, wanda ya k’ara bayyanar da kyansa, a fili,

“gaskiya ba zan je ba ne cox wurin bai mun ba!”.

Mubarak ye zaro ido cike da mamaki, “yanzu

Abeed golden Dragon ne bai maka ba?” Kai ya

gyad’a alamar Eh..

Mubarak yayi murmushi, dan yasan Abeed saida

rarrashi, ya cigaba da cewa “gaskiya my man

idan ka yiwa Jabir haka ba zai ji dad’i ba”

Abeed yace”ban yi don na 6ata ransa ba, zan

masa waya ma na bashi hak’uri, bana son zuwa

guri ne na tarar da tarkacen mutane marasa aji

a gurin, wannan ne kawai badan wannan ba

zanje mana” “amma ai ka san waye Jabir! kuma

ka San waye mahaifinsa a garin nan, so bana

tunanin za’ayi k’aranta a gurin, ka sa ni ma ko

ka had’u da wata ‘yar minister acan ya fad’a

yana murmushi.

Ya tsine fuska Abeed ya yi, yace” ‘ ya’yan

ministers ai suna suka tana, kamar ‘yar k’

aramin minister mai zan yi da ita” shi dai

Mubarak ido kawai ya zuba yana kallonsa domin

al’amarin Abeed ya girmi tunaninsa, da k’yar ya

samu ya lalla6ashi ya amince akan zai je.

Muje zuwa muji mizai faru a gun…….

Www.hauwajabo.blogspot.com

Www.jabohauwa.WordPress.com

M Twins😍 & Auntie M. Jabo 🍃

[4/11, 2:54 PM] Wacce Zamuyi Book: 💫AN YI

WALK’IYA 9💫

©Mrs Saif & Hauwa M. Jabo

®NWA

Cikin 6acin rai Abeed ya koma gida, parking

kawai ya yi ko kulle motar bai yi ba, ya wuce

part d’in sa, ransa a dagule yake gaba d’aya,

yana tunanin wai yaushe ne burinsa zai ciki, ya

samu yarinyar da ta dace da shi, wacce ya ke

mafarkin samu, domin shi kansa yanzu ya

hak’ik’an ce da ya na buk’atar aure, amma

matsalar duk ‘yan matan da ke sonsa yanzu ya

raina arzikin iyayensu, duk da cikin su babu

wadda za a d’auka ace babanta matsiyaci ne,

don dai shi ya d’auki k’atoton buri ya sakawa

zuciyarsa, dole sai ‘yar mai hannu da shuni,

lokaci d’aya ya tuna da wacce akace tanasonsa,

wai babanta yayi rik’on logal government, dai

rainin wayo, wani dogon tsaki yaja, yadan juya

kwanciyar sa, ya kalli a gogon d’akin yana

lumshe ido.

*********

Goggo wacce nake tunanin y’ar uwar Dadyn su

Abeed ce, zaune take tareda Mumy suna hira,

Abeed ne ya shigo ya gaishesu cikin sakin fuska

sannan ya wuce d’akin sa, nan suka fara hirar

yau da kullum, har Goggo ta gangaro akan

abinda ya dad’e yana damun ta,

“hajiya yaran yanzu sai a hankali, sam basa

tunani basa naziri, yanzu za ku ga wasu yaran

masu kud’i idan za su yi aure sai su rik’a

hangen wadda mahaifin ta ya dame nasu ya

shanye da naira, don zilama, maimakon su nemi

dai_dai su, tunda Malam bahaushe ma ya ce

“dai_dai ruwa dai_dai tsaki, kuma kowace

k’warya da abokin burminta” sannan ma ina

laifin su yi k’asa_k’asa su nemi ‘yar talaka

bawan Allah suma su samu su lasa, kinga ai an

taimaki juna an rufawa juna asiri ta wannan

hanyar, amma ba a yi saboda buri ya cikawa

masu irin wannan halin zuciya, kowa sai dai-dai

shi,” Mumy tace “Wallhy zancen ki dutse

Goggon yara, nima abin yana damuna,

musamman idan naga halin yaronnan banajin

dad’i sam, amma kinsan kosu talakawan akwai

nasu sabida sai su k’wallafa dogon buri wa

yaran su, su mayar da yayan nasu kamar jari,

domin wasu sai ka ga sun zaune jiran mai d’an

maik’o_maik’o har yarinya ta tsofe a gida, ba

iyayenba ba ‘ ya’yan ba, kije gida ki rasa gane

uwa da yaran gida, akwai wani gida da mukaje

ta’aziya, a gidan naga mata ‘yar kyakyawa,

wacce nake tunanin zata haifi yara biyu ko uku,

nake tambayar matar gidan, an mata amarya ne,

dan tare na gansu, sai take cemin ai ‘yar kice

wance, wallhy saida na kai zaunedDan mamaki,

na tuna yarinyar sa’ar Muhammad ce fa! Amma

har yanzu tana gida,” Goggo ta saka dariya, ”

kin bani dariya, wai an miki amarya ne” itama

Mumy dariyar tayi suka ci gaba da hira” wannan

zamanin kowa kwad’ayi ya yi masa yawa, bayan

sun mata Allah ke yin komai, domin kowa an

riga an rubuta k’addararsa tun kafin ya zo

duniyannan, we just trace, sai ka ga budurwa ta

zauna jiran Mr right har ta tsofe tun tana samun

masu zuwa har lokacin ta ya wuce ya zamana

bata samu, ta tashi a tutar babu, k’arshe sai ta

auri wanda bataso, sabida da yawa masu

wannan burin, wallhy basa auren mazan da

zuciyar su takeso, saidai dan kud’i, su tashi ba

wan ba k’ani, ta yi haihuwar guzuma ‘ya kwance

uwa kwance, ba mai d’an maik’o_maik’o ba mijin

kwatakwata” nan ma saida suka dara, Goggo

tace, ” nifa kina magana kina saka engilishi,

kuma kinsan ba ganewa nakeyiba,” sukayi dariya

gaba dayan su, Goggo tace, ” Allah ya sa masu

wannan halin su gano su bari dan ba alkhairi

acikinsa” ameen Mumy ta amsa dashi,

Na kalli M Twins nace “nifa al’amarin Abeed

yana bani mamaki domin ya d’ebo da zafi, kace

sai ‘yar wane ko wane,” M. Twins tace ” ?kedai

bari Aunty Jabo, Allah na d’auka irin wannan

abin matane kawai keda wannan hali, ashe har

maza ma sunayi, abin kunya, amma hausawa

sun ce “kowa ya d’ebo da zafi bakinsa”………..”

Www.hauwajabo.blogspot.com

Www.jabohauwa.WordPress.com

M Twins😍& Auntie M. Jabo ✍🏾🍃

[4/11, 2:54 PM] Wacce Zamuyi Book: 💫AN YI

WALK’IYA 8💫

©Mrs Saif & Hauwa M. Jabo

®NWA

K’arasawa ta yi in da Mufeeda ke tsaye kamar

an dasata ta ce “mufy ya na ganki a tsaye,

bayan ya tafi dama nasan ba lallai ya amince da

buk’ata na ba”.

Cikin yak’e Mufeeda ta ce “kar ma ki yi wannan

tunanin Fadeela, zai so ki da yardar Allah, yanzu

ma don bai ganki ba ne na tabbatar idan ya yi

ido hud’u dake ba abinda zai hana ya so ki”.

A jiyar zuciya Fadeela ta yi, sannan ta ce “ta

yaya zan kuma had’uwa da shi bare har ya

ganni?? Kar ki manta, ko sunansa ban sa ni ba,

bare in da ya ke”.

Murmushi Mufeeda ta yi, ta ce ” idan akan

wannan ne ki kwantar da hankalinki kamar

tsumma a randa, idan kullum kike son ganin

Abeed za ki gan shi da yardar Allah.”

Cikin mamaki Fadeela ta ce “wow! nice name,

sunansa kenan”?

Mufeeda ta gyad’a kai alamar eh, Fadeela ta

cigaba da fad’in “amma mufy ta yaya zan gan

shi duk lokacin da na ke so ya gaya miki sunan

unguwarsu ne, ko wurin aikinsa ?”

Dariya Mufeeda ta yi sosai sannan ta ce”

wannan kuma sai kin ba da wani abu sannan

zan gaya miki, “6ata rai Fadeela ta yi cikin sigar

wasa ta ce” dad’ina da ke kenan, yanzu za ki

fara ja mun rai tunda kin ga ina son ji “.

Tafiya Mufeeda ta fara tana cewa” shi kenan

tunda ba kya son ji, da tuni kin mik’o wani abu,

“gabanta Fadeela ta tara tare da cewa” haba

friendy ko haka ki ka bar ni ai kin ja mun rai,

don Allah ki gaya mun”, ta k’arashe maganar

kamar za ta yi kuka.

Mufeeda ta ce “don’t cry k’awata, he’s my

cousin”, waro ido Fadeela ta yi tare da daka

tsalle ta rungume Mufeeda tana cewa “don

Allah da gaske kike yi mufy”?

Mufeeda ta ce” yes da gaske ne ko gobe ki ke

so zan kaiki gidansu ya Abeed, “Fadeela ta

kuma k’ank’ameta tare da cewa amma na ji

dad’i Allah ya sa hakan ya zama silar cikar

burina.” Mufeeda ta ce “ameen, sannan ta duba

agogon wayarta ta ce” gaskiya Fadeela dare

yayi fa, gashi lunching d’in an fara a makare bari

na kira driver ya zo, sai ya fara kai ki gida,

sannan sai mu wuce “.

Fadeela ta ce” gaskiya kam don kar ayi mana

fad’a kinsan hajiya idan ta fara,” suka saka

dariya.

Www.hauwajabo.blogspot.com

Www.jabohauwa.WordPress.com

M Twins 😍 & Auntie M. Jabo ✍🏾🍃

[4/11💫AN YI WALK’IYA 6&7 💫

©Mrs Saif & Hauwa M. Jabo

®NWA

Tun da safiyar ranar mubarak yake ma Abeed

waya akan kada ya manta please, yamai SMS ba

adadi, k’arshe ya yarda zai tafi, dan har ya

shirya dojewa.

Sai wurin k’arfe tara da minti ashirin da biyar

Abeed da tawagarsa suka shiga hall d’in, cikin

takun isa da k’asaita yake tafiya, ya rufe idonsa

da wani shade bak’i kaitsaye gurin da aka

tanada domin zaman su suka nufa.

Wohoho! Ku zo ku ga ‘yan mata yanda suka

zuba masa na mujiya suna kallo, kai basu kad’ai

ba har mazan dake gurin kallonsa suke yi

tamkar sun ga wata sabuwar halitta, shi kuwa

gogan naku ko kallo ba su ishe shi ba, tafiyarsa

kawai yake cikin isa da izza har ya isa wurin

zaman su.

Tun shigowarsa wata yarinya mai amsa sunan

Fadeela, muka ga duk ta rud’e ta rikice, sai wani

dube_dube take kamar mai neman wani abu.

Sai can kuma muka ga ta nufi wani side na

musamman, domin an yi decorating gurin sosai

fiye da inda take zaune,

Da sauri ta k’arasa wurin har tana tuntu6e, tare

da rik’o hannun wata budurwa wadda ba zata

wuce sa’arta ba, sannnan ta ce “Mufy ta so don

Allah ki gan shi shine wanda na ke yawan yi

miki maganarsa” ido Mufeeda ta zuba mata na

d’an lokaci sannnan ta ce” wai ki na nufin guy

d’in da ba ki da aiki sai na maganarsa shine ya

zo nan gurin,”?

Fadeela ta ce “eh tare da langa6ar da kanta

gefe,”

Mufeeda ta yi farr da ido,sannnan ta ce “gaskiya

fady kin ban kunya, duk yanda kika h’adun nan,

kuma kike gwara kan samari son ranki amma ki

6ige da baran soyayya akan saurayin da ko

sunansa ba ki sa ni ba”.

Dafa kafad’arta Fadeela ta yi tare da cewa

“friendy ba ki ga guy d’in ba ne that’s why kike

wannan maganar, kin san first class guy, full

options to shi ne, ni tsoro ma nake kar ki gan

shi ki kasa controlling kan ki ki je ki shigar da

kan ki ba ni ba” ta k’arashe maganar tare da

sakin dariya!

Duka Mufeeda ta kai mata, ta goce sannnan ta

ce “an gaya miki akwai wanda ya isa ya ture

gwamnatin k’albina ne,” Mufeeda ta cigaba da

fad’in “ni dai zo ki nuna mun in da ya ke, ga

ganshi, na cigaba da abinda na ke yi”.

Fadeela ta ce “na ga dai sun nufi wurin da aka

tanada don manya_manya abokan ango” ta

fad’a tana d’an kalle-kalle

OK, “to ta yaya zan yi na gane shi??” Cewar

Mufeeda, nari mu je na nuna miki shi ko daga

nesa ne, d’an nesa da su Fadeela ta tsaya take

nunawa Mufeeda shi, ba tare da ko na kusa da

su sun gane abinda suke yi ba.

Tun da Mufeeda ta hangoshi take wasiwasin

wani abu a zuciyarta, sai da ta zo daf da shi

sannan ta tabbatar da abinda take zato. Sallama

ta yi sannan ta ce “sannu yaya Abeed” Jin an

kira shi da yaya, ya tilasta masa d’agowa da kan

sa domin ganin mai magana.

Fuskarsa ya d’an saki sannan ya ce ” yawwa

sannunki”, ta cigaba da fad’in ashe kai ma ka zo

bikin k’awarmu”?? Jin bai ce komai, ta ce

“angon ne abokinka ke nan”??

kai ya gyad’a mata kawai, ta ce” ai ni amaryar

ce close friend d’ina”.

Jin ya kuma shiru ta ce “yaya ba ka son zuwa

gidanmu su Arfat ne kawai ke zuwa”.

Hmm! kawai ya ce, nan ma shiru ne ya kuma

ratsawa, sai da ta ga shirun yayi yawa ta ce

“dama akwai maganar da ta kawoni wurinka

idan ba za ka damu ba ka ba ni 5 minute’s

please”, kamar ba zai yi magana ba, sai can ya

mik’e ya yi mata nuni da su fita daga gurin.

Gefe suka koma, sannan ta fara masa bayanin

abinda ya kawota, ta k’arashe maganarta da

cewa don Allah yaya ka taimakawa k’awata ba

ka ga yadda ta ke sonka ba.”

Bud’ar bakinsa sai ya ce “waye mahaifinta”?

Cikin rashin fahimtar maganarsa Mufeeda da ta

ce” Babanta dai d’an siyasa ne”, ya ce

“muk’amin meye da shi”?

eh, to ni dai abinda na sa ni ya ta6a rik’on

k’warya a local government”.

“What!” ya fad’a da k’arfi, yana had’e fuska,

daga haka bai k’ara cewa da ita komai ba, sai

ga ni ta yi yana niyyar fita daga hall d’in ba ki

d’aya. Da sauri ita ma ta bi bayansa,bayan ya

isa in da ya ajiye motarsa yana k’ok’arin shiga,

ta sha gabansa tana fad’in “haba yaya Abeed ba

ka ce komai ba, ba ka ga yanda yarinyar take

mutuwar sonka ba”.

Ai kuwa sai dai ta mutu in dai ni ne, I hate her,

ya fad’a tare da shigewa mota ya ja da k’arfi da

niyyar ficewa daga wurin, dai_dai lokacin

Fadeela ta fito……………….

About the author

Hausa_Novels

Leave a Comment