Littafan Hausa Novels

Anya Baiwa Ce Hausa Novel Complete

Written by Hausa_Novels

Anya Baiwa Ce Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

ANYA BAIWA CE?*

 

Na

 

*AMEERA ADAM*

 

 

_LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, GAME BUƘATAR VIP POSTING SAU BIYU A RANA ZAI BIYA 400, GABAƊAYA ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM ZA’A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR 0706 206 2624,DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._

 

 

FREE PAGE 1

 

 

 

Tafe take tana ɗan waige dan gudun kar wani ya ganta ko taci karo da wani a hanya, saboda abin da ta gano take san zuwa ta isar da shi ko ta samu ɗan alheri, aikuwa batayi aune ba tana shiga soron tsakiya suka yi gware da mutum a zabure ta ja da baya tana sauke ajiyar zuciya kamar wacce tayi tseren gudu, kallan tsaf yayi mata yana karantar yanayinta yasan tabbas akwai abinda ke ƙunshe cikin bakin ta, aɗan diriri ce ta kalle shi ta ce.

 

“Yautai mugun tsuntsu masha miyarka sai yayi dare”

 

Kallanta yayi sai da yayi murmushin gefen baki yana ƙara karantar yanayin ta sannan ya ce, ” Tauraruwa mai wutsiya…, Kura kike ga tsoro ga ban tsoro. Ina zaki kike sauri kina ta juye-juye haka? ” Sai da ta juya hagu da dama ta kuma leƙa soron ƙarshe tana mai miƙa wuya cikin ƙasa da murya ta ce, ” Gobara daga teku maganin ta sai Allah, wata ƙura ce take ƙoƙarin kunno kai a cikin gidan nan amma karka ce kaji daga baki na ” ta ƙarasa magana tana kuma duba gabanta da bayanta.

 

“Jakadiya Kubura kenan, ay harbi ga ɗan jaki gado ne, kuma iya ruwa fidda kai gayamun ina sauraron ki kowa ya biya allon sa ya wanke ” ya faɗa cikin son jin labarin.

 

Sunkuyowa tayi dabda shi sannan ta ce, ” Kasan koda girgiza kurna tafi magarya, mai tsoron a mutu shi yake maho ” Ƙara gyara tsayuwarta tayi sannan ta ce, ” Ƙaramar kyauta tafi babbar rowa ” ta ƙarasa faɗa tana miƙa masa hannu alamar ya bata wani abu.

 

Ya gano abinda Jakadiya ta ke nufi, dan haka ya sa hannu cikin aljihu ya ɗebo mata silallah ya zuba mata akan hannun ta yana faɗin, ” Ke dai ciki kike mai manta kyautar jiya, kuma Kura kike mai manta alherin baya”

Mu da Yaran Mu Hausa Novel Complete

Juya su tayi cikin jindaɗi ta kunto bakin zaninta ta ɗauresu tana faɗin, ” Domin rana ɗaya ba’a ƙin zuguri, kuturu da kuɗinsa alkaki sai na ƙasan langa, buɗe kunnen ka yanzu zaka sha labari, ashe Fulani Zaliha ciki gareta har ya girma, kasanta da shegen nunkufurci ba ta cika bada fuska a shiga sashenta ba ” zaro idanu yayi waje shima yana waigen bayansa sannan ya ce, ” Lallai tsugunne bata ƙare ba ansai da kare an sayi Mage, naji daɗin wannan albishir naki jeki anjima zan neme ki ” ya faɗa yana yin gaba abinsa.

 

Jakadiya Kubura ta fahimci sarai inda maganar Galadima ta dosa har yaje bakin ƙofa ta ce masa, ” Injunan ka sammako wani tafe ya kwana, kuma hargagin ɗan damisa bashi tsorata Namijin zaki, ka taka a sannu kasan Fulani Maryama ba kanwar lasa ba ce ” kamar bazai bata amsa ba sai kuma ya juyo ya ce mata, ” Tabbas inkaji mutum na tsoron dare ba’a ɗaure shi ya ƙwance bane, Ki bar ganin allura ƙarama itama ƙarfe ce, dan haka bazan ce miki komai ba mu zuba mu gani kowa tasa ta fishsheshi ” yana gama faɗa ya sanya kai ya fice daga cikin soron.

 

Bin bayansa tayi da mugun kallo sannan ta ce, ” Mai ƙafa huɗu ma ya faɗi bare mai biyu, ajuri zuwa rafi wata ran tulin zai fashe ” tana faɗa ta juya ta cigaba da tafiya, kai tsaye sashen Fulani Maryama ta nufa.

 

Tana shiga ta zube ƙasa cikin salon kirari ta fara magana, ” Barka da hutawa Uwargida na bango madafar bayi, uwar marayu uwar mara gata mai iyayenma kin gamai musu komai, Ƴar sarki jikar sarki Matar Sarki kuma gaki Uwar Sarki, Allah ya ƙara girma ya raya mana Yarima mai jiran gado, Mulki da Sarautar Masarautar Kano gaba ɗaya ta ku ce, Mai Uwa agindin murhu bazai ci miyarsa lami ba… ” murmushi Fulani Maryama tayi saboda jin daɗin kirarin da Jakadiya tayi shiyasa ma ta katse ta da faɗin, ” Jakadiya anjima zan turo da saƙon maɗi mai ke tafe da ke?? ” russunar da kai Jakadiya tayi tana mai sauya yanayin fuskarta cikin damuwa ta ce, ” Tuba nake Uwar gijiyata banzo dan isar da mugun labarin nan dan wata manufa ba sai dan ki tashi tsaye ki ɗau mataki kuma asan abin yi, Kaicona da tuntuni ban ankare ba har lamarin ya girmama, amma dukda haka ba za’a rasa abinyi ba dan ba’a rasa nono a riga, ina mai neman gafarar ki saboda labarin bamai daɗi bane ranki shi daɗe ”

 

Tunda Jakadiya ta fara magana Fulani Maryama gabanta ya yanke ya faɗi saboda tasan labarin bazai mata daɗi ba, shiyasa a hargitse ta wurgo mata tambaya, ” Jakadiya banasan Kewaye-kewaye tafi kanki tsaye, Me yake faruwa ne?”

 

Jakadiya kara sauya muryarta tayi ta ce, ” Ina neman gafararki da jin kalamai na dama Fulani Zaliha ce ke da juna biyu, kuma ayanayin dana lura har yayi ƙwari…” cikin tsananin tashin hankali Fulani Maryama ta ƙunduma wani ashar sannan ta ce, ” Aikin me kike tun tuni baki sanar dani ba tunda wuri? ”

 

Jakadiya ta bata amsa da, ” A gafarce ni Uwargijiya ta kinsan Yarinyar da nunk…”

 

Katseta Fulani tayi cikin tsawa ta na faɗin, ” Ya isa haka, Lallai Fulani Zaliha ta ɗebo ruwan dafa kanta, Samun sararin kuturu gaɗa a cikin rama, wato haka ta miƙe ƙafa da yawa? Lallai abinda ya faru a shekarun baya dole ya ƙara faruwa yanzu, tabbatas dole labari ya ƙara maimaita kansa, Aikuwa kowa yaci tuwo dani miya yasha, tashi kije Jakadiya anjima zan neme ki bayan Sallar Isha’i ”

 

Jakadiya najin haka ta kuma rissinawa ta ce, ” ALLAH ya huci zuciyar Fulani, Ramin kura da wuyar shiga a gayawa kare yayi hankali, tabbas bakin rijiya ba wajen wasan makaho bane wace ce Fulani Zaliha da zata iya haɗa sahu da Uwar ɗakina, ni mai bin Umarnin ki ce akowanne lokaci ” Jakadiya na gama faɗa ta tashi ta fice zuciyarta fess saboda tasan ba ƙaramin alheri zata samu ba.

 

Tunda Jakadiya ta fito daga ɗakin, Fulani Maryama ta kasa zaune ta kasa tsaye sai kaiwa da komawa take, abun duniya gabaɗaya ya isheta, ita kaɗai sai saƙa da warwara ta ke tana san nemarwa kanta mafita, Jaririnta ɗan kimanin wata biyar da ke kwance ta je tasa hannu ta ɗauke shi tana juya shi cikin zuciyarta da shawarar da ta yankewa kanta.

 

A fili ta fara surutai kamar wata zautacciya, ” Yarima yanzu kai ake shirin yiwa kishiya a gidan nan, tabbas bazata yuwu ba tunda ban bari wata ta haifi namiji ba dole na dakatar da cikin Zaliha ”

 

Jakadiya tunda ta fito daga sashen Fulani Maryama kai tsaye sashen su ta wuce tana zumuɗin sauraron kiran da Fulani Maryama ta ce zata yi mata, kamar wacce a ka mintsina tashi tayi ta fito daga sashen bayi wani gida ta faɗa bakin ta ɗauke da sallama, ” Balaraba matar Ciroma dake tankaɗe ta amsa mata sallamar tana faɗin.

 

” Yau kuma Jakadiya ce da doshin magariba haka?? ” Kujera Jakadiya ta janyo ta zauna sannan ta ce, ” Eh ko bakya maraba da zuwan nawa ne?? ” cigaba da tankaɗenta tayi ta bawa Jakadiya amsa, ” Ni na isa nace banten Sarki yayi ɓurtu, ai hanyar lafiya abita da shekara, meye labari?? Dan nasan bakin ki baya rasa motsi?? ”

 

Murmushi Jakadiya tayi ta ce, ” Ai dama ni kujera ce dole a zauna dani, kuma abokin cin mushe ba’a ɓoye masa wuƙa, wai kuwa kinsan Fulani Zaliha na ɗauke da juna biyu?? Wa ya sani ma itama ko Namijin zata haifo ni zanso ma ta haifo Namijin naga yanda Fulani Maryama zatayi ” ta faɗa tana ƙasa-ƙasa da murya.

 

Da sauri Balaraba ta saki rariyar Hannunta waigawa bakin ƙofa tayi sannan ta cewa Jakadiya, ” Da gaske kike wannan maganar?? aikuwa muddin zancen nan yaje gun Fulani Maryama kinsan bazai mata daɗi ba, kuma kinsan dole wani abu ya biyo baya”

 

Jakadiya ƙara matse bakin zanin ta tayi ta ce, ” Ai a bakin wawa akanji magana, wai da kunne yaji muguwar magana wuya ya tsere, kinsan dai ai ciki badan tuwo akayi shi ba, bayan ke babu wanda yasan da wannan maganar ”

 

Tsuke fuska Balaraba tayi da alama bataji daɗin maganar Jakadiya ba dan haka ta maida mata da martani, ” Tafasar tukunya bata gefe ɗaya bace, haka nan abinda baki ya ƙulla hannu bashi iya kunce shi, idan kinji makaho ya ce ayi wasan dutse to tabbaci haƙiƙa ya taka dutse, Jakadiya koma dai mene ne daga bakinki wannan maganar ta fito kuma ni nan da kika gani na iya taku na”

 

Miƙewa tsaye Jakadiya tayi tana gyara ɗaurin zaninta ta fara takawa har sai da taje wajen bakin ƙofa sannan ta juyo ta ce, ” Mutum fari ne shi ke rina kansa ya zama baƙi, bakinki dai ƙanin ƙafarki kuma harshenki linzaminki ” bata saurari mai Balaraba zata ce ba ta fice daga gidan.

 

 

_UMMOU ASLAM BINT ADAM

[26/09/2021, 01:58] Ameera Adam *FIRST CLASS WRITERS ASSO*

 

 

*ANYA BAIWA CE?*

 

Na

 

*AMEERA ADAM*

 

 

_LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, GAME BUƘATAR VIP POSTING SAU BIYU A RANA ZAI BIYA 400, GABAƊAYA ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA’A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR 0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._

 

 

FREE PAGE 2

 

 

 

Da daddare Bayan sallar Isha’i Jakadiya ce tafe tana lalube har ta ƙarasa sashen Fulani Maryama, da sallama ta shiga ta russuna tana cewa, ” Barka da hutawa Uwar ɗakina ance kina san ganina yanzun nan ”

 

Fulani Maryama dake tsaye hannunta ɗauke da Salman miƙawa Jakadiya shi tayi ta ce, ” Jakadiya inasan muyi tafiyar sirri kamar yanda muka saba da ke a shekarun baya, ayau basai gobe ba zamu kai ziyara ga Boka Marduska, saboda bazan iya kwana da maganar da kika sanar da ni ba, batare na nemi mafita ba ”

Riƙe Salman Jakadiya tayi tsam kamar wani zai ƙwace shi sannan ta ce, ” Duk abinda kika ce haka za’ayi, bani da ikon bijirewa umarninki, da kai da kaya duk mallakar wuya ne ”

 

Fulani Maryama na gama jin haka ta juya ta shiga cikin ɗakinta, cen ƙasan adakarta ta buɗe ta ɗauko wani kurtu tasa hannu ta ɗebo waɗansu irin wuri guda biyu da wani ɗan ƙaramin zobe, maida kurtun tayi sannan ta dawo gurin da tabar Jakadiya ke tsaye.

 

Miƙawa Jakadiya Wuri ɗaya tayi sannan ta fara karanta waɗansu irin ɗalasiman tsafi, ba’a ɗauki lokaci ba sai wani haske ya mamaye gurun atake suka ɓace daga cikin ɗakin.

 

Tsaye suke abakin wani kogon dutsen dake cikin wani surƙuƙin daji mai matuƙar duhun gaske, Fulani Maryama runtse idanunta tayi ta fara ƙwalawa bokan kira har sau uku, ” Marduska! Marduska!! Marduska!!! ” tana gama faɗa ta buɗe idanunta.

 

Ji sukayi ankece da wata mahaukaciyar dariya sai da aka ɗan ɗauki lokaci anayi sannan aka tsagaita, sannu a hankali haske ya mamaye gurin, cikin wata irin murya aka fara basu umarni, ” Ku sanya ƙafafunku cikin waccen ƴar ƙoramar sannan ku tako ku shigo ciki.

 

Kamar yanda aka gaya musu haka suka bi umarnin mai magana sannan suka shiga cikin kogon dutsen, daga cen nesa suka hango shi zaune akan buzun damisa, gaba ɗaya jikinsa lulluɓe yake da gashi tamkar ba bil Adam ba, Fulani Maryama na gaba Jakadiya na biye da ita a baya.

 

Zama sukayi sannan Fulani ta kalli bokan zata fara magana ya ɗaga mata hannu sannan ya kuma kecewa da dariya, sai da yayi mai isarsa sannan ya fara magana,

 

” Ai duk wanda ya bamu iska dole kwaɓarsa tai ruwa, Maryama kin ɗauke mana ƙafa na wasu shekaru sai da buƙatarki ta tashi zaki waiwayo mu ”

 

Fulani Maryama ta russunar da kai ta ce, ” A gafarceni sarkin bokayen duniya, nayi kuskure awancen lokacin amma yanxu baza’a sake ba ”

 

” Na amshi tubanki kuma nasan abinda yake tafe dake, kalli nan ” ya janyo wata ƙwarya mai cike da jini yana nunawa fulani.

 

Tana leƙawa Fulani Zaliha ta gani kwance akan gadon ta tana baccinta hankali kwance, jinjina kanta tayi ta cewa Murduska, ” Ya babban boka sarkin bokayen duniya so nake a salwantar da cikin da ke jikinta inda hali ma akashe su gaba ɗaya, domin bayan Salman bana san kowacce matar sarki ta sake haihuwa acikin su saboda bansan gaba mai zasu haifo ba kuma bansan mai hakan zata haifar ba ”

 

Ƙwala-ƙwalan idanunsa ya kafe ta dasu yana ce, ” Daga ganin Sarkin fawa sai miya tayi zaƙi, badan kinzo ayanxu ba da tuni sauran damar data rage miki ta ƙare gaba ɗaya ” A zabure Fulani Maryama ta ce, ” Ban fahimce ka ba Marduska ”

 

 

Wani mudubin tsafinsa ya ɗauko yasa wata jelar ɓauna dake hannun sa na hagu cikin ƙwaryar ya yarfawa mudubin, inuwar wani ɗan ƙanƙanin Yaro ce ta bayyana na ɗan wani lokaci sannan ta ɓace, maida mudubin yayi gefe sannan ya maida kallonsa ga Fulani Maryama ya ce, ” Alƙalami ya riga da ya bushe, duk duniya babu wani ko wata da zai iya dakatar da cikin jikinta har sai ta haifeshi, Zata haifo Ɗa namiji Mai kama sak da Mahaifinsa kuma koda baki ci wannan Alwashin ba haihuwa ta dakatawa Sarki Aminullah, duk wacce kika ga ta kuma haihuwa sai dai in wani ne mahaifinsa ba Aminullah ba ”

 

Cikin damuwa Fulani Maryama ta ce, ” Yanxu babu wata mafita da zaka bani ya Shugaba na?? ”

 

Wani Allon jar ƙasa ya ɗauko ya jingine ya na faɗan waɗansu irin kalmomi, yana watsa wani tafasashen jini dake cikin wani ƙoƙon kan Ƙwarangwal, yana cikin haka baiyi aune ba sai gani sukayi Allon jar ƙasa ya ruguje wani irin hayaƙi mai wari na fita daga jikinsa.

 

A tsorace gaba ɗaya suka ja baya Marduska ba ƙaramin tsorata yayi da ganin faruwar haka, cikin yanayin firgici ya fara magana, ” Tabbas Ruhin wasu ababen hallita na katange da shi, idan na matsanta halaka shi ba mu ba hatta Aljanun da suke taya ni aiki sai sun halaka, maganin kar ayi kar afara inba haka ba wanda baiji bari ba yaji woho ”

 

Fulani Maryama jikinta ne ya gama sanyi amma duk da haka zuciyarta bata karaya ba ta ce, ” Marduska abar batun Halaka shi tunda ni kaina ganau ce ba jiyau ba, amma bayan haihuwar sa ba damar a aiwatar da wani aiki akansa ko a nakasa shi? ”

 

Matsawa yayi bakin wutar dake ci ya ɗebo wani garin magani mai haɗe da garin naman mage da haƙoran jemage ya zuba aciki, take wutar ta kuma tashi sama sannan wata ƴar ƙaramar ƙorama ta bayyana aciki, daga cikin ƙoramar wasu litafan tsafinsa ya ɗebo guda biyu ja da baƙi, baƙin ya fara jefawa cikin wannan jinin dake cikin ƙwarya sannan ya zura kansa yana karewa Ƙwaryar kallo dake ta zaɓalɓala.

 

Sai da ya gama kallo tsaf sannan ya ɗago da kansa da yayi gumi sharkaf ya fara mata bayani, ” Tabbas cikin biyun za’a iya gudanar da ɗaya amma biyun bazasu iya wanzuwa akanshi ba, zamu iya nakashi ta kowacce siga haka nan zaki iya sawa a fitar dashi daga cikin masaurautar, amma shi ne kuskuren da zaki fara tafkawa a rayuwar ki, domin kuwa ta wannan silar dukkan asiran da kika binne za’a binciko domin kuwa allura ce zata tono garma”

 

Fulani Maryama harta fara jin daɗi ƙarshen maganarsa ya sa ta shiga damuwa, kallansa tayi cikin rashin fahimta ta ce, ” Bangane mai kake nufi ba? ” mayar da ƙwaryar yayi cen gefe ya ce, ” Abinda na gani kenan zaɓi ya ragewa mai shiga rijiya…, kowanne zaɓi kika ɗauka yana da nashi ƙalubalen da zaki fuskanta ki nutsu da kyau ki saurare ni inba haka ba zakiyi gudun gara ki faɗa gidan zago ”

 

Jakadiya dake gefe tayi tsuru sai raba idanu ta ke cikin zuciyar ta ta ke faɗin, ” Lallai Fulani Maryama kema ba ƙaramar makira ba ce, amma ajuri zuwa rafi…, Ay bahaushe ya ce inzaka gina ramin mugunta gina shi gajere, amma lallai wannan Ɗa na Zaliha ya zama kainuwa dashen Allah, wata ƙila shi ne zai zama magajin mulki muga ta tsiya, dama ance kayun Ɗan ƙwarai ya gaji Ubansa ”

 

” Ina sauraren kowacce kalma da zata fito daga bakinka kuma kowacce zan saka ta amazaunin da ta da ce ” Fulani Maryama ta faɗa.

 

Miƙe ƙafafunsa yayi da gaba ɗaya gashi ya rufe su sannan ya fara mata bayani, ” Zabi na farko zamu iya baki garin maganin da za’a zuba masa a ruwan wanka ina nufin wankansa na farko a duniya kuma ko yaya ne asamu a bashi wannaa maganin ya sha, sai kuma na turare wanda ita Zaliha tana fara Naƙuda zaki turara mata, karki bari yaro ya faɗo ba tare da kin turara shi ba, to idan kika yi haka bazai iya gani da idanunsa ba, har tafiya da magana ke komai da kika sani sai dai ayi masa, saboda zai kasance a kwance sai dai duk abinda za’a furta zai ji shi babu abinda zai iya wanzarwa ”

 

Murmushin jin daɗi Fulani Maryama tayi ganin haka yasa boka ya ce mata, ” Sai dai akwai sharaɗin da zaki kiyaye, akwai ruhin wata da na gani tana jingine da shi, zata shigo cikin gidan masarautar ku tana ƙasƙantacciya muddin kika bari ta shigo cikin gidan sarautar, abubuwa marasa daɗi zasu fara faruwa gareki kuma duk ranar da tayi tozali da shi suka haɗa ido, a ranar aljanun dake riƙe da ƙafafunsa zasu tarwatse alƙadarinsu zai karye, idan kika yi sake ta ɗau wani abun ci ko abin sha ta bashi da hannunta to a ranar suma aljanun da ke riƙe da bakinsa zasu gushe zai fara magana, sai dai aranar zai fara wani irin ciwo kamar zai mutu zai yi ta amai ba ƙyaƙyƙyautawa kamar zai amayar da ƴan hanjinsa, hakan zai ɗaga hankalin Mai martaba har yasa anemo wanda ya bashi wani abu tunda shi zaiyi tunanin guba ce aka bashi, amma ba haka bane amayar da gubar da take jikinsa yake ta tsawon shekaru ”

 

 

 

_UMMOU ASLAM BINT ADAM_

[26/09/2021, 02:13] Ameera Adam: *FIRST CLASS WRITERS ASSO*

 

 

*ANYA BAIWA CE?*

 

Na

 

*AMEERA ADAM*

 

 

_LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, GAME BUƘATAR VIP POSTING SAU BIYU A RANA ZAI BIYA 400, GABAƊAYA ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA’A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR 0706 206 2624,DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._

 

 

FREE PAGE 3

 

 

Ajiyar zuciya Fulani Maryama ta sauke sannan ta ce masa, ” Wace ce yarinyar? Kuma daga wane gurin zata xo? Babu damar dakatar da zuwan nata? Ya za’ay na gane ita ce dan na ɗauki matakin daya dace akanta?? ”

 

Boka ya ce, ” Daga ni har sauran matsafan duniya babu wanda ya isa ya ja da yarinyar domin ita ɗin FILSIFI ce, abinda muke kira da FILSIFI kuwa aharkar bokan ci, tarraya ko haɗakar shuɗaɗɗun ruhika mabanbanta daga jinsi Mabanbanta, zo ki duba nan ” ya ƙarasa faɗa yana buɗe mata wannan jan littafin da ke gefensa.

 

Zanen wasu matasan mata ta gani guda uku sai dai duk cikinsu babu wacce zanen fuskarta ya fito sosai daga ƙasan kowacce anrubuta wani irin gwamammen rubutu, ta farko ya fara nuna mata yace, ” Wannan da kike gani ita ce Muhaibish ita ta rayu ne tsawon dubbannin shekarun da suka gabata, Ƴar Sarkin jinsin Fararen Aljanun ƙarƙashin ƙasa ce, tunda take bata taɓa taka doron ƙasa ba ”

 

Zaro idanu Fulani Maryama tayi tana mamakin abinda ya faɗa, ta biyu ya nuna mata ya cigaba da cewa, ” Wannan kuma sunan ta Kalimsiyat Ƴar sarkin fararen Aljanu ce amma ta nan doron ƙasa itama ta rayu atsawon dubbanin shekaru, acikin wani littafin bincike na karanta cewar ta yi rayuwa ne tun bayan zuwan Annabi Yusuf (A.S) ita kuma tunda ta ke bata taɓa nutsawa ƙarƙashin ƙasa ba a matsayinta na jinsin aljanu, kuma ita Kalimsiyat mace ce mara haƙuri mai faɗan gaske, kuma abinciken da nayi dukkan su biyun kashe su akayi bisa doron zalinci, kuma abinda zai baki mamaki kusan duka ruhinsu guda ne, sai dai banbancin nahiya da zamani.

Sai ta Ukun su ita ce aka ce zata xo aƙarshen zamanin nan, sunanta Rayzuta ita ta haɗa dukkan abubuwan da waɗancen suke dashi harma da wanda suka rasa, ƴar baiwa ce me ɗauke da ɓoyayyun al’amura, ita kanta batasan da wannan baiwa tata ba.”

 

Yana rufe baki cikin azarɓaɓi Fulani Maryama ta ce, ” To itama ta ukun nasu Aljanar ce? kuma meye alaƙar su da junan su? Kuma meye alaƙarta da gidan masarautarmu? ”

 

” Maryama kenan azarɓaɓin me kike yi? Ai duk gaggauwar asara ta jira samu, kuma duk gaggawar unguwar zoma ta jira a haihu, mai kike ci ne na baka na zuba inkinyi haƙuri sannu-sannu bata hana zuwa sai dai adaɗe ba’a je ba ”

 

Murmushin tayi sannan ta bashi amsa da, ” Hmmm Marduska ai Ranar biyan buƙata rai ba’a bakin komai yake ba, na ƙagu na ji matsayin Yarinyar da ka ce da kuma ya alaƙarsu ta ke? ”

 

Marduska ya cigaba da cewa, ” Har zuwa wannan zancen da nake miki ruhin su na nan ya wanzu a dora ƙasa, sai dai babu inda zasu ya da zango sai akan cikon ta ukunsu, kuma ba kowa bace cikon ta ukunsu sai Yarinyar da nace miki karki sakankance har ta shigo Masarautar ku, har yanxu mudubin tsafi na ya gagara gano mun mutum ce ko kuma itama tana cikin jinsin Aljan, sai dai bincike ya nuna akwai wani ɓoyayyen al’amar dake bibiyar jinin zuri’ar sarki Aminullahi ”

 

Damuwa ce ƙarara a fuskar Fulani Maryama ta kuma jefo masa tambaya, ” Ita yarinyar ba dama ka nuna mun hoton fuskarta yanda zan gane kamaninta? ”

 

Mudubinsa ya janyo ya fara wasu surutai yana watsa masa wani ruwa mai yauƙi, wata irin ƙara suka ji ta tsagewar mudubin har sai da suka tsorata, cikin damuwa Bokan ya ce, ” Gaskiya gaba ɗaya aikin da kika zo dashi akwai damuwa da tashin hankali, haka kawai banci nanin ba nanin zata ci ni, na dakata akan binciken Yarinyar nan saboda ceton rayuwa ta ”

 

Abin duniya gaba ɗaya ya dami Fulani Maryama amma duk da haka ba ta gushe ba tana faɗin, ” Ka taimaka mun kayimun wani abu, ni da kai kaɗai na dogara ”

 

Wani mugun kallo ya bi ta dashi sannan ya ce, ” Baki da hankali ne a gabanki munanan abubuwa suka faru amma zaki ce na taimaka miki kinga idan kinganni a lahira kaini akai, babu uwar da zan iya taimaka miki, bincike na biyu da zan gaya miki shi ne, idan kika sa aka fitar da shi tun yana jariri to ba makawa acikin ƙasa da makwanni goma zai faɗa gurin da zai gamu da ita wannan yarinya kuma dawowarsu shi da ita bazai miki daɗi ba, dabara ta ragewa mai shiga rijiya…”

 

Zufar dake goshinta ta goge sannan ta ce masa, ” Marduska wai dole sai akaina wannan masifun yarinyar zasu sauka? Kaina ya kulle fa, dan Allah ka bani mafita…” katse ta yayi da ƙarfin gaske yana cewa, ” Da alama kin manta dokar kogon dutsen, azaba ta gaggawa zata iya wanzuwa agareki ” sunkuyar da kai ƙasa tayi ta ce, ” Tsafi ya dafa tuba nake bokana Sarkin bokayen duniya, ina gwanin wani ga nawa Aljani Garbunsa ya ƙara ja da zamanin ka ”

 

Motsa bakinsa yayi alamar jindaɗi sannan ya ɗauko wani ruwa dake cikin tukunyar ƙasa ya ɗaga shi sama da hannunsa ya fara surutunsa na tsafi, ya jima ahaka sannan ya sauko da shi ya leƙa wani tiriri ne yake fitowa, sai da ya gama kallon ƙwaryar ya ce, ” Akwai wasu ɓoyayun al’amura mai tafe da sarƙaƙiya, da alama shuɗaɗɗun abubuwan baya ne zasu iya dawowa wata ƙila Tarihi ne zai kuma maimaita kansa, amma bani da tabbas harsashe ne nayi, ƙarɓi wannan ” Ya miƙa mata wata manyan layu sannan ya cigaba da bayani.

 

” Ita wannan layar ki saƙaleta aɗakinki zata taimaka miki na bunnuwar wasu sirrika na ki, wannan kuma ki binneta akan ƙofar shiga gidan masarautarku, bance zata Hana faruwar komai ba sai dai wannan layar zata hana tonuwar muhimmin sirinki musamman akan wance yaran, kinfi kowa sanin dai ba jinin Aminullahi ba ne hasalima ba jinin masarautar Kano bane, to ki saƙale ta gun da kikasan bazata faɗo ba, ita wannan ta ƙofar gidan wasu aljanune zasu miki gadin bakin ƙofar don hana ta shigowa, amma banda tabbaci yaƙini nake watakila shigowar Rayzuta gidan ya sa ta faɗowa wata ƙila kuma bazata faɗo ba, kuma na lura da faɗuwar gaba a duk lokacin da zaku haɗu da ita wannan yarinyar, sai ki riƙe wannan duk lokacin da kikaji faɗuwar gaba ki dinga lura da waɗanda suke tare da ke, ni nayi iya yi na ku tashi ku bani guri ”

 

Jakadiya dake gefe tsumu tayi najin kalaman boka cikin zuciyarta ta ke faɗin, ” Au dama Salman ba jinin Takawa bane? Lallai duk inda makirci ya je Fulani Maryama ta kai cen, babu ko tantama ɗan wajen Fulani Zulaiha shi zai zama magajin Izza, muje zuwa mahaukaci ya hau kura na tabbata akwai ranar da Ya zata ɗakin Ƙanwa, Fulani Maryama kinyi shuka a idon makwarya, lokaci na nan zuwa da kwaɓarki zatai ruwa, tafiya sannu-sannu kwana nesa. ”

 

Kamar Fulani Maryama tasan abinda yake ran Jakadiya aikuwa ta juyo cikin tsuke fuska ta fara mata magana, ” Jakadiya duk abinda kika ji agurin nan ki tabbata da ya zama sirri banasan kowacce magana ta fito daga bakinki, bakinki ƙanin ƙafarki, kinsanni sarai kinsan wacce Fulani Maryama bani da kyau banida daɗi, idan na sake naji wata magana ta ɓilla waje to daga gareki ne, kuma insa a hallakaki ba abu ne mai wuya agurina ba ”

 

Jakadiya sarai ta san Fulani Maryama zatayi abinda yafi haka ma ta rissinar da kai ƙasa ta ce, ” Wane ni da wannan ɗanyen aikin ya Shugabata indai wanda ya mutu zai dawo to maganar nan zata tashi, ai duk wanda ya ƙona rumbunsa yasan inda toka take tsada, ina ni ina bayyana sirrin Uwar gijiya ta idan nai haka ai kamar na daɓawa kaina wuƙa ne ”

 

Fulani Maryama ɗauke kanta gefe tayi tana faɗin, ” Ki tabbatar da kin kiyaye abinda kika faɗa domin ni ginshiƙin dutse ce kowa yayi karo dani shi ka faɗi, idan kunne yaji gangar jiki ta tsira ” Jakadiya haɗiye yawu tayi mai ɗaci saboda jin haushin maganar Fulani, cikin zuciyarta ƙwafa tayi ta ce, ” Tunkafin ahaifi uwar mai sabulu balbela ta ke da farinta, Fulani Maryama dani kike zance wallahi duk wannan wulaƙancin da kike mun akwai lokacin da zan farke miki laya. ”

 

” Muna godiya Ubangidana maganin kuka na dukda yau ce rana ta farko da zan fita daga kogon dutsen bada biyan dukkan buƙata ba, amma ni mai bin umarnin ka ce akan duk abubuwan daka gindaya mun, tsafi ya dafa hatsabibancin ka ya cigaba da wanzuwar har ƙarshen zamani ” Fulani Maryama ta faɗa tana karɓar layun da ya bata.

 

Cikin jindaɗin kirarinta ya ce, ” Taɓewa ta tabbata ga mai yin shirka kije tukwicin aikinmu na ga cikin bayin Masarautar ku kamar yanda muka saba duk lokacin da kuka ziyarce mu, zan ƙara miki tuni idan kun wayi gari da mutuwar wani bawan babu ku babu cin kayan sadakar inba haka ba zaku bishi, ku fice daga kogon dutse kuna masu ambatan sunan mu ” yana gama faɗa ya ɓace daga gurin, Jakadiya da Fulani tashi suka yi suka fita, suna zuwa bakin kogon dutsen Fulani ta kuma runtse idonta tana karanta ɗalasiman tsafin, atake haske ya kuma mamaye su suka ɓace daga gurin.

 

Lokacin da suka koma cikin Masarautar tuni dare ya tsala babu motsin komai sai kukan tsuntsaye da ƙananan dabobbi, Fulani karɓar Salman tayi dake hannun Jakadiya sannan ta ce mata, ” Ƙuda wajen kwaɗayi akan mutum ina fatan baki manta maganar boka ba ” rissunawa Jakadiya tayi ta ce, ” Ina ankare ya shugaba ta ”

 

 

_UMMOU ASLAM BINT ADAM

Ameera Adam: *FIRST CLASS WRITERS ASSO

 

 

*ANYA BAIWA CE?*

 

Na

 

*AMEERA ADAM*

 

 

_LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, GAME BUƘATAR VIP POSTING SAU BIYU A RANA ZAI BIYA 400, GABAƊAYA ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA’A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._

 

 

FREE PAGE 4

 

 

 

Fulani taɓe baki tayi ta ce, ” Yayi miki kyau ai kowa rai ya yiwa daɗi baya mai shi ba, magana ta ƙarshe da zan gaya miki, kiji ki ƙi ji ki gani ki ƙi gani, zaki iya tafiya ” tana gama faɗar haka ta juya ta shige ciki ta bar Jakadiya a tsaye.

 

Jakadiya bin bayanta tayi da harara sannan ta juyo ta fi ce daga sashen Fulani Maryama ta wuce cen sashen su.

 

Washe gari tun Asubar fari Lantana ta ƙaraso ɗakin Jakadiya hankali tashe tana kwala mata kira tana bubbuga ƙofar, kasancewar bacci bai ishi Jakadiya ba taji haushin tashin da Lantana ta yi mata, cikin masifa ta fara magana, ” Ke Lantan wannan kiran mafarautan da kike mun da farar asubahi na lafiya ne? Sai kace naci na wani ban biya ba, Mtsswwww jaraba kai ko yaushe baka da hutu ” ta ƙarasa faɗa tana zare sakatar ƙofar.

 

Lantana haushi ne ya fara kamata cikin tsiwa ta ce, ” Ke Jakadiya kullin cikin yiwa mutane jaraba kike to kizo kiga abunda Sahura take yi muma farkawa mukayi muka ga tana wani irin abu ” gaban Jakadiya ne ya yanke ya faɗi da sauri tayi gaba Lantana na biye da ita.

 

Suna shiga suka samu idanun Sahura sun kakkafe jikinta sai wani irin karkarwa yake bakinta na fitar da dafara, Kuka Jakadiya ta fashe dashi tana rungumo Sahura dake cikin wani hali, lokaci ɗaya taji Sahura na shaƙuwa jikinta ya sandare daga nan numfashin ta ya ɗauke.

 

Jakadiya rungume Sahura tayi tana fashewa da wani irin kuka mai tsuma zuciya, sai da tayi mai isarta cikin jimamin rashin jikarta ta fara magana, ” Shikenan ni Kubura bani da kowa Sahura ke kaɗai kika rage mun yanxu kema babu ke kin mutu kin barni kaico mutuwa baki mun adalci ba, babu Ƴaƴa babu Jika, Allah ya jiƙanki Sahura ” haka Jakadiya ta dinga surutai da ƙyar aka raba ta da gawar jikarta, ba ƙaramin tausayi Jakadiya ta bawa mutane ba musamman yanda kowa yasan irin ƙaunar da ke tsakaninta da jikar ta ta ɗaya tilo, kafin wani lokaci tuni mutuwar Sahura ta ƙaraɗe cikin gidan, bayan ansallaci Sahura mutane suka shiga sintirin zuwa yiwa Jakadiya gaisuwa.

 

Jakadiya ce durƙushe a ɗakin Fulani Maryama har zuwa lokacin hawaye ne kwance a fuskarta, Fulani ce ta fara mata magana, ” Jakadiya ya ƙarin haƙuri? ” Jakadiya goge kwallar idonta tayi sannan ta ce, ” Da godiya Ranki shi daɗe ”

 

” To Allah jiƙan musulmi, ga wannan ayi sadaka da shi ” wata jaka ce ta miƙowa Jakadiya, Jakadiya da tsanar Fulani ta ɗarsu a zuciyarta ji tai kamar bazata karɓa ba, amma gudun kar Fulani Maryama ta ganota yasa ta miƙa hannu biyu ta karɓa tana zabga godiya, zuciyarta a dagule ta fito daga sashen Fulani Maryama.

 

Jakadiya haka ta shafe kwanaki bakwai cir bata cin abincin sadakar da akeyi, da yake ma tana cikin jimamin mutuwar ko yunwar bata cika damunta ba inma taji yunwa sai dai ta nemi gasara ta dama kunu ko tayi farau-farau, a duk duniya yanxu babu wacce Jakadiya ta tsana take jin haushin ta sama da Fulani Maryama dan gani take ta sanadin ta ne ta rasa Ƴar jikallenta guda.

 

Bayan kwana biyu Fulani Maryama sai saƙa da warwara take a cikin zuciyarta, tana tuna maganganun da Boka ya sanar mata fargabar abin da zai biyo baya.Ta kaɗu sosai da yadda karon farko Boka ya bankaɗo wani muhimmin ɓoyayyen sirrinta, amma data tuna irin tuggun da zata shirya sai ta mayar da komai ba komai ba, ta zubawa sarautar Allah ido tayi da jiran tsammanin lokacin haihuwar Fulani Zaliha. Domin a nan ne zata aiwatar da dukkan ƙudurinta.

 

Bayan kwana biyu Mai Martaba na zaune a turakarsa Fulani Maryama na gefe a zaune, ta kalleshi sai dai gabaɗaya baya cikin walwala cikin kissa ta ce. “Mai Martaba wannan yanayin sam bai kamace ka ba, Allah ƙara lafiya da nisan kwana shugaba kamar kai wannan yanayin bai dace da kai ba, Bango madafar bayi idan har zaka dinga shiga cikin damuwa, to mu da sauran talakawanka ya zamu kasance.” Mai martaba cikin damuwa yace. “Wallahi ina yawan yin mummunan mafarki akan ƙanwarki Zaliha ina yawan mafarki mara kyau akan cikinta” gaban Fulani Maryama ya faɗi ɓaci rai ya sauka a zuciyarta amma da yake ta iya duniyanci sai ta aro damuwa ta yafa a fuskarta ta ce. “Haba taƙamar bayi adalin Sarki mai adalci, ai zakaran da Allah ya nufa da cara ko ana muzuru ana shaho sai yayi, ka kwantar da hankalinka Fulani Zaliha zata sauka lafiya tunda alamar ƙarfi tana ga mai ƙiba, nidai a iya sanina Fulani Zaliha tana cikin ƙoshin lafiya kuma zata haife mana ƙanin Yarima lafiya” farinciki ne ƙarara ya bayyana a fuskar Me martaba, janyo hannunta yayi ya sumbaceta yace.

 

“Allah ya yi miki albarka Maryama ke ɗin ta daban ce saboda haka kike ƙara birgeni, naji daɗin yadda kika riƙi ƴan uwanki da zuciya ɗaya kuma kika riƙe girman da Allah ya ɗora miki, hakan ne yake sa nake tunanin ko bayan raina zuri’ata zata haɗa kanta.” Murmushi Fulani Maryama tayi ta ce. “Dole ƙanwar naƙi wa ya isa ya ja da abin da Mai Martaba yake so, ai duk abin da ka nuna kana so har bada ina ƙaunarsa”Mai Martaba daɗi yaji sosai yadda take bashi kulawa akan sauran matansa. Cikin zuciyarta Fulani Maryam ta ce. “Da ikon Allah bazai zo duniya lafiya ba mu zuba mu gani”

 

*BAYAN WATA UKU*

 

Fulani Zaliha ce durƙushe tana naƙuda, gefenta Marka ce sai Jakadiya dake riƙe da ita, daga bakin zaure Shamaki ne yake sallama, da sauri Jakadiya ta fita gurinsa, ƙwarya ce da rubutu aciki ya miƙa mata yana faɗin, ” Gashi Takawa ya ce a bata ta sha ashafe cikin da shi ” karɓa Jakadiya tayi ta koma ciki ta ɗago kan Fulani Zaliha da ta haɗa uban gumi, a wahalce ta sha bayan ta gama sha aka Shafe cikin da sauran.

 

Bankaɗa labulen ɗakin akayi ko sallama babu, Jakadiya na ɗago kai tana shirin masifa suka haɗa ido da Fulani Maryama fuskar nan tata babu annuri, wani tunani Fulani Maryama tayi lokaci ɗaya ta sauya yanayin ta cikin ruɗewa ta ce, ” Jakadiya ashe Fulani na kan gwiwa amma ba’a turo ansanar mun ba sai yanxu labari ya je mun ” Jakadiya cikin rawar murya ta ce, ” Ai wato…Nima zuwa na kenan, na fito zanje wajenki Takawa ya ayko da rubutu ”

 

Marmushin Markirci Fulani Maryama tayi ta ce, ” Bari nazo na riƙeta kije ki kawon garwashi yanxun nan ga ragowar turaren da akamun lokacin naƙudar Yarima ” Suna haɗa ido Fulani ta watsawa Jakadiya mugun kallo ba shiri Jakadiya ta fice.

 

Fulani na shiga ta riƙe Fulani Zaliha tana mata sannu.

 

Jakadiya na kawo wuta Fulani Maryama ta kunce turaren wajen boka ta barbaɗa, ba’a jima Jariri ya faɗo yana tsanyara kuka, Fulani Zuwaira da Fulani Bilkisu na kawo kai suka ji kukan jariri, da sauri Fulani Bilkisu ta ce, ” Lallai mun shigo a sa’a Barka da arziki ” suna shigowa kowa yayi turus saboda ganin Abunda Fulani Zulaiha ta haifo, sai dai kowannen su haɗiye abinda ke ransa yayi gudun kar afuskanci halin da Suke ciki.

 

Bayan an yanke mabiyar angyara gun ruwa aka kawo na wankan jariri. Kasancewar Fulani Maryama ita yaro ya faɗo a hannunta ita aka bawa ruwan, fakar idanun su tayi ta damƙi garin gurin boka haɗe da ƙafar jaririn ta sa acikin ruwan wankan.

 

Lokacin da garin maganin ya garwaye jikin sa wani irin kuka ya fashe da shi, amma babu wanda ya kawo komai sai ma tsokarsa da Marka ta ke cikin waƙa tana faɗin, ” Ka zama Jarumin maza karka zama rago mana matsoraci bashi zama gwani, jinin Aminullahi yafi ƙarfin wasa kyawun ɗan ƙwarai ya gaji ubansa”

 

 

_UMMOU ASLAM BINT ADAM

[12/10/2021, 19:42] Ameera Adam *FIRST CLASS WRITERS ASSO

 

 

*ANYA BAIWA CE?*

 

Na

 

*AMEERA ADAM*

 

 

_LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, GAME BUƘATAR VIP POSTING SAU BIYU A RANA ZAI BIYA 400, GABAƊAYA ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA’A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._

 

 

FREE PAGE 5

 

 

 

Fulani Maryama zuciyarta fes wani shu’umin murmushi tayi har ya bayyana a fili ta ce. “Marka ai ɗana jarumi ne kamar yadda ɗan uwansa salman yake” Jakadiya ce ta fita ta yiwa Sarki albishiri Marka ta fara ƙoƙarin gyara Fulani Zaliha. Har aka gama yiwa Jaririn Fulani Zaliha wanka bai daina tsanyara kuka ba, tana gamawa ta gyarashi sannan ta ce. “Fulani barka da arziki bari na ƙarasa ciki na bar yarima yana bacci kar ya tashi ki samu ki ci abinci ki kwanta ki huta.” Fulani Zaliha ta ce. “To na gode Yaya Allah ya huta gajiya” Fulani Maryama ta wuce sashenta.

 

Kafin wani lokaci tuni haihuwar Fulani Zaliha ta zaga cikin gidan masarautar, sanƙira bi yake ko ina yana shelar sanar da ƙaruwar da Mai martaba ya samu , cikin lokacin ƙanƙani cikin garin Kano ta samu sakon haihuwar da aka yiwa Sarkin Kano Aminullahi.

 

Jaririn Fulani Zaliha tun ranar da aka haifeshi yayi wannan kukan bai ƙara wani kuka da ƙarfi yadda wani zai iya ji ba, Fulani Zaliha bata kawo komai ba saboda wannan ce haihuwarta ta farko kuma bata taɓa kawowa ranta komai ba, tafi alaƙanta haka da yaro ne shi mara rigima saboda wasu jariran basu cika rigima ba. Matan cikin masarauta da sauran bayi tsegungumi sukeyi akan Fulani Maryama na rashin nuna matsanancin kishinta akan ɗan Fulani Zaliha duk da yadda kowa yasan Fulani Maryama da matsanancin kishi. Fulani Zaliha ba ta shan wahalar rainon Jaririnta dukda akwai masu kula dashi amma sam bashi da rigima. Tun daga ranar kuma Fulani bata ƙara takawa ta leƙa saahen Fulani Zaliha ba har sai da yayi kwana uku, da wata yammacin ranar ta shirya cikin shiga ta alfarma irin ta jiƙaƙƙun matan sarakuna, tafe take cikin takun ƙasaita da taƙama kamar ba zata taka ƙasa ba. Ga duk wanda yayi arba da Fulani Maryama kallo ɗaya zai mata ya tabbatar da ita ɗin tabbas jinin masarauta ce gaba da baya, duk yadda ka kai ga kallan ƙurulla zai yi wuya ku haɗa ido da ita batare da janye idanuwanka ba kuma duk sanka da ka fahimci a wane yanayi take zaiyi wuya ka fahimci halin da take ciki. Tana tafe kunyangarta na biye da ita da Salman a hannu har suka ƙarasa sashen Fulani Zaliha, lokacin da ta shiga sashen Fulani Zaliha na zaune tayi kwalliyar ta fito shar da ita ga wani kyau da ta ƙarayi irin na masu jego, Fulani Maryama zama tayi kan lallausar shimfiɗar Fulani Zaliha baiwar ta tsaya daga rumfa.Da fara’arta Fulani Zaliha ta ce, “Barka da shigowa Yaya da fatan kin wuni lafiya ya kwanan Yarima” Fulani Maryama wani murmushi tayi mai wuyar fasaltuwa ta ce. “Lafiya kalau masu jego ya kwanan ɗannawa” Fulani Zaliha kunya taji bata amsa ba ta ƙwalawa baiwarta kira tana bata umarnin kawo Jaririn, a fakaice Fulani Maryama take ƙarewa Fulani Zaliha kallo tana ƙara jin wata irin tsanarta a zuciyarta.

 

Lokacin da aka kawo mata Jaririn karɓar sa tayi tana murmushi sai dai ƙasan zuciyarta har wani zafi take ji saboda yadda taga kamaninsa dana Mai martaba na ƙara fitowa, a fili ta shafa fuskarsa ta ce. “A jinjira baƙwan duniya yana rigima kuwa?” Fulani Zaliha ta ce, “Tun kukan farko da yayi bai ƙarayi ba bashi da rigima” Fulani Maryama na shirin yin magana taga hawaye na gangarowa daga idanuwansa, buɗe baki yakeyi yana ɗan juya kansa wanda yake nuna yunwa yake ji, Fulani Maryama murmushi tayi me sauti ta ce. “Ai dama bazai yi ba indai ya biyo gida kinsan Yarima ma haka nayi goyonsa, ungoshi naga kamar yunwa yake ji” a kunyace Fulani Zaliha ta karɓeshi miƙewa Fulani Maryama tayi tayi mata sallama zata wuce har ta je bakin ƙofa ta juyo ta ce. “Sai fa kinsa ido akansa saboda ɓoyayyun maƙiya duk yadda kika kai ga ganosu sai kin gaza a masarautar nan dan haka ki bi sannu” murmushi Fulani Zaliha tayi ta ce, “In sha Allah Yaya kinsan zakaran da Allah ya nufa da cara ko ana muzuru ana shaho sai yayi” Fulani Zaliha zuciyarta ɗaya ta faɗi haka ita kuwa Fulani Maryama juyowa tayi amma sai ta wayence da murmushi ɗauke a fuskarta ta ce. “Kinyi gaskiya kuma nasan da haka amma duk da haka tsugunne bata ƙare miki ba amma fa shawara ce na baki.” tana kaiwa nan ta fice daga ɗakin.

 

Tun daga ranar Fulani Maryama bata ƙara shiga sashen Fulani Zaliha ba, kuma zuciyarta fes ta fita daga ɗakin saboda yadda da dukkan alama haƙanta ya cimma ruwa. Shirye-shirye ake ta gudanarwa na shagalin suna daga sassan ɓangarori na cikin masarautar. Ranar suna Mai martaba ya raɗawa Jariri sunan Saifullah suna kiransa da Saif, anyi shagali sosai ɓaki daga garuruwa suka kawo ziyara wajen taya Mai Martaba murnar samu Ɗa namiji a karo na biyu.

 

Anyi taron suna angama lafiya kuma daga ɓangaren Mejego da jaririnta suna cikin ƙoshin lafiya. Bayan wata uku Mai Martaba ne zaune a fada shi da Waziri, ga duk wanda ya dubi yanayim Mai Martaba zai fahimci tsantsar damuwar da yake ciki, amma da yake namiji ne jajirtacce farat ɗaya bazaka fahimci ainihin yanayin da yake cikin ba. Waziri ya ɗuƙar da kai cikin sigar girmamawa yace. “Allah ya taimaki takawa ya ƙarawa Sarki lafiya, Muna zaune aka aika da saƙon kiranmu” Sarki Aminullah ya jinjina kai sannan ya ce.

 

“Waziri wani abu yana damunmu kuma babu wanda muka aminta da mu tattauna dashi sai kai” Waziri ya ɗago yace. “Wannan haka haka yake” Sarki yace. “Mun lura da yaron wajen Zaliha kamar bashi da wadatacciyar lafiya, kuma na lura da yanayin Mahaifiyarsa ita kanta ta fahimci haka sai da tana shakkun sanar dani. Waziri ina san maganar nan ta zama sirrin saboda kunnuwa da idanun Fada suna bibiyar halin da ake ciki, banasan a fuskanci halin da yaron nan yake ciki inasan ka nemo min mai magani a sirrance ta yadda babu wanda zai fahimci halin da ake ciki.”

 

Waziri ya numfasa yace. “Allah ƙadiran alamanyasha’u gaskiya akwai matsala babba dukda kasancewar ba shine Yarima ba, amma sirrantawar yana da matuƙar fa’ida. A cen garin Zaria akwai wani mai magani dana sani yana bada magunguna sosai, dan haka insha Allah zan shirya naje na karɓo maganin sai a jarraba da ikon Allah za’a dace.” Mai Martaba yace. “Waziri me zai hana ya gayyato mana mai magnin ina ganin kamar hakan zaifi” Waziri yace, “Duk yadda kace haka za’a aiwatar da kai da kaya duk mallakar wuya ne” Mai Martaba yace. “A shirya tafiya gobe aje a gayyato mana shi” Waziri ya amsa daga nan ya fice daga fadar.”

 

Da daddare Fulani Zaliha ce zaune a turakar Sarki ta zuba uban tagumi, Sarki Aminullahi ya kalleta yace.”Me yake damunki Zaliha” idanunta ne suka ciko da ƙwalla muryarta na rawa ta ce. “Mai martaba Saif ne nake lura da yanayinsa bashi da ƙosasshiyar lafiya, na lura fa ko gani kamar ba ya yi, gashi har yanzu kansa baya tsaiwa hatta irin gwarancin yarannan banji yana yi ba, abu ɗaya kawai nasan yanayi idan na kira sunansa zan ga yana ɗan motsawa.” Fulani Zaliha na kawo nan a zancenta ta rushe da kuka. Rungumeta yayi ajikinsa tsam kamar wani zai ƙwaceta ya fara rarrashinta, yana buga bayanta harta lafa da kukan sannan yace. “Ina lura da halin da kike ciki kuma na fahimci duk abinda kika gayamun, dan haka na aika a kira mai magani a sirrance inasan ki zama jaruma karki bari magauta su ga kukanki, Insha Allah Saif zai samu lafiya ki kwantar da hankalinki.” Haka dai Sarki yayi da lallashin Fulani Zaliha har ta sauko ta daina kuka.

 

Bayan kwana biyu Mai magani suka ƙarasa ta ƙofar baya suka ƙaraso ɗakin sirri wacce take bayan gari, Saif na hannun Mai martaba mai maganin ya shigo hannunsa ɗauke da wata jakar fata ta magunguna, yana zuwa ya ƙurawa Saif kallo nan take ya fara tsanyara wani irin kuka, jinjina kai yayi ya ce. “Tabbas ancutar da shi da guba mai tsanani sai dai zan iya taimaka muku da yardar Allah koda kuwa bazai warke gabaɗaya ba.” Mai maganin kwance jakarsa ya farayi nan take ya dafe ƙirjinsa ya fara wani irin kakari kafin wani lokaci ya yanke jiki ya faɗi ƙasa matacce.

 

 

_UMMOU ASLAM BINT ADAM

[13/10/2021, 18:53] Ameera Adam: *FIRST CLASS WRITERS ASSO

 

 

*ANYA BAIWA CE?*

 

Na

 

*AMEERA ADAM*

 

 

_LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, GAME BUƘATAR VIP POSTING SAU BIYU A RANA ZAI BIYA 400, GABAƊAYA ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA’A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._

 

 

FREE PAGE 6

 

 

Hankali a tashe Waziri da Mai martaba suka kalli juna ganin abinda ya faru da mai magani, ƙanin Mai maganin da ke gefe da sauri ya faɗa kan ɗan uwansa yana kuka, Mai Martaba cikin al’ajabi haɗe da tashin hankali ya kalli Waziri yace. “Waziri a ji da bawan Allahn nan bamasan a tara mana jama’a, ashirya tafiya ƙasar Zazzau a sirrance batare da wasu sun sani ba, zan aiko da takarda akaiwa da iyalansa tare da kyautuka masu yawa.” Yana gama faɗa ya juya ya fita ta ƙofar baya cikin jimami” Lokacin da Mai martaba ya ƙarasa cikin turakarsa dare yayi sosai babu komai sai kukan tsuntsaye da ƙananan dabbobi, Fulani Zaliha na tsaye sai safa da marwa take yi da ka ga yanayinta zaka fahimci tana cikin damuwa, tana jin motsin Mai Martaba da sauri ta ƙarasa ta tarbeshi gabanta sai faɗuwa yake tunaninta ɗaya wacce amsa Mai martaba zai bata.

 

Ganin Mai martaba tayi ya shigo cikin shigar da yayi ta ɓadda kama, sanye yake da kayan bayi fuskarsa naɗe da rawani sai Saif dake rungume a ƙirjinsa, har kusan gware sukayi da Fulani Zaliha ta ɗan ja da baya tana kallan yanayinsa, a hankali ya taka kan lallausar shinfiɗarsa ya zauna yana sauke ajiyar zuciya a hankali. Fulani Zaliha zama tayi a gefensa ta ƙarɓi Saif dake hannun Sarki Aminullah yana shan ɗan yatsansa, kallan ɗan nata take zuciya a karye ta ce. “Allah ya taimakeka har dace ba ko?” Sarki Aminullah yace. “Mai maganin Allah yayi masa rasuwa” a hargitse ta ɗago tana kallansa bakinta na rawa ta ce.

 

“Mai Martaba ɗazu kace Mai maganin yana ɗakin sirri yana jiranka” Sarki Aminullah yace. “Zaliha lamarin Ubangiji yafi gaban komai, yana gabda haɗa magunguna Allah ya karɓi rayuwarsa.” Fulani Zaliha ta jinjina kai ta ce. “Allah ya fimu sanin dalilin faruwar haka. Amma gani nake larurar Saif anya babu sihiri a ciki?” Kallan da Sarki Aminullah ya yi mata ne yasa ta haɗiye wani yawu tana sunkuyar da kai ƙasa ta ce.

 

“Allah ya huci zuciyar Takawa a gafarceni ban faɗi haka saboda ɓacin ranka ba” Sarki Aminullah yace. “Zaliha karna ƙara jin makamanciyar irin wannan maganar daga bakinki, kina nufin yafi ƙarfin Ubangiji ya jarrabceshi da wani ciwo ne? Karki bari shaiɗan yayi tasiri a zuciyarki har ya kaiga kin fara zargin abinda ba haka bane” Fulani Zaliha kukan da take ɓoyewa ne ya ƙwace mata, wani irin kuka take me tsuma zuciya Mai martaba jin kukanta yake har cikin zuciyarsa, takowa yayi a hankali ya karɓi Saif ya kwantar da shi sannan ya rungumeta yana lallashinta, sai da ya ga ta tsagaita da kukan sannan yace.

 

“Zaliha dole na gaya miki gaskiya koda bazata miki daɗi ba saboda gujewa faɗawa ga halaka, zato a musulunci haramin koda ya kasance gaskiya abinda nake so da ke ki cigaba da kai kukanki gurun Ubangiji, shi zai magance mana duk abinda yake damunki, karki nufi kowa da sharri sai kiga Allah ya kare ki duk wanda ma ya nufe ki da shi koda yana nasara wata rana mugun abinsa zai koma kansa saboda ramin ƙarya ƙurarre ne. Allah ya fimu sanin dai-dai amma ni bana zargin akwai wanda zai iya cutar da abinda kika haifa a cikin masarautar nan, ki riƙi ibada kamar yadda nasanki da ita Allah zai kawo mana waraka cikin ƙudurarsa.” Fulani Zaliha goge hawaye tayi tana gyaɗa kai Sarki Aminullah ya cigaba da kwantar mata da hankali.

 

Fulani Maryama banda zarya babu abinda take yi a soron baya cikin shigarta ta baɗɗa kama, motsin tafiya taji da sauri ta matsa cen kusurwar bango ta maƙale kamar ba kowa a gurin. Shigowa yayi yana ɗan dube-dube murya ƙasa-ƙasa yace. “Allah ya taimakeki” da sauri Fulani Maryama ta fito ta ce, “Ya ake ciki Ɓoyayyiyar Fuska?” Mutumin yayi murmushi mai sauti yace. “Allah ya taimakeki tabbas kin tabbata murucin kan dutse baki fito ba sai da kika shirya, tuni ya riga da ya mutu har lahira” Murmushi Fulani Maryama tayi ta ce. “Lallai ka tabbata lumbu-lumbu wutar ƙaiƙayi” Mutumin da take kira da ɓoyayyiyar fuska yace. “Ya gara ta kanyi da dutse…” Fulani Maryama tayi dariya mai tsauti ta ce. “Sai kallo, kallonma daga nesa” suka bushe da dariya lokaci ɗaya, Fulani Maryama ta sunkuyo ta ce. “Kasan idanun Masarauta na lura da shige da fice sai wani lokaci idan mun ƙara haɗuwa” tana faɗar haka ta juya fice ta ƙofar baya.

 

Tun daga ranar Mai martaba ya cigaba da neman masu magani amma wani abun damuwa duk wanda aka ɗauko sai dai ya faɗi take ya mutu, wani kuma a ranar da aka shirya za’a gurinsa za’a je a samu labarin ya mutu ko kuma ya kwanta matsananciyar jinya. Tun Mai martaba bai fara damuwa ba har abun ya fara damunsa, daga ɓangaren Fulani Zaliha duk ta rame saboda damuwa. Sarki Aminullahi tun yana neman masu magunguna a ɓoye har ya fara nema a fili, masu magunguna daga sassan garuruwa suke zuwa domin kawo nasu maganin amma babu nasara, nasara ɗaya aka samu masu Maganin sun daina mutuwa sai dai idan sunzo babu wani canji da ake samu daga jikin Saif. Haka aka dinga tsegungumi a cikin masarautar musamman yadda mutane suka lura da yadda Sarki Aminullahi ya ɗora soyayya akan Saif. Hakan ba ƙaramin ɓatawa Fulani Maryama rai yayi ba da sauran Matan Sarki Aminullah, sai dai su basu wani damu sosai ba dan sun san har abada babu shi babu karagar mulki.

 

Haka aka cigaba da tafiya har Saif ya shekara guda a duniya amma ko zama bayayi, hatta kwanciya sai Mahaifiyarsa ta juyashi, Fulani Zaliha ta riga da ta tabbatar da Saif baya gani sai dai ji da kunne tana yi masa magana take fara jujjuyawa, har zuwa wannan lokacin Sarki Aminullah bai ƙosa da nemawa Saif magani ba amma babu wata nasara ko cigaba da ake samu.

 

 

Jakadiya ce ɗurƙushe gaban Fulani ta ce. “Barka da hutawa giwar mata uwar Yarima hasken talakawa, an aika kina nemana” Fulani Maryama cikin Isa da ƙasaita ta ce. “Yau zamu kaiwa Marduska ziyara” A firgice Jakadiya ta ɗago tana kallan Fulani Maryama amma ta kasa furta koda kalma ɗaya ne” Fulani Maryama ta cigaba da cewa.

 

“A yanzu nake san zuwa basai anjima ba” bata saurare ta ba ta wuce cikin ɗaki ta ɗauko Yarima Salma ta miƙa mata tace. “Zamu je domin biyan buƙatata ina ƙara jan kunnenki Jakadiya bakinki ƙanin ƙafarki ina tausaya miki azabar da zan aiwatar miki muddin sirrina ya fito daga bakinki” wuri ta miƙa mata sannan ta fara ambatar kalmomin da Boka Mardusk ya bata ta dinga ambata aduk lokacin da take san ziyartarsa.

 

Durƙushe suke gaban Boka Marduska ya kalleta sannan ya wage ƙaton bakinsa yana ɓaɓɓaka dariya bakyan gani sannan ya ce. “Maryama buƙatarki ta biya” Kin fito da ƙudurun a juyar da hankalin Sarki daga kan Zaliha da Ɗanta Saif ko?” Fulani Maryama ta gyaɗa kai Boka Marduska yace. “Wannan dai ta biya sai dai wata buƙatar kuma” Murmushi Fulani Maryama tayi ta ce. “Tsafi ya dafa ka daɗe kayi ƙarko irin na dabino, hatsabibancinka ya dauwama har ƙarshen duniya” tana rufe baki ta ɗire masa jakar kuɗin da ta taho dasu sannan suka miƙe zasu tafi har sunje bakin Ƙofa yace. “Sai dai kiyi haƙuri Maryama wannan karan makusancinki zamu ɗauka a tukwicinmu lamarin bazai miki daɗi ba.” Yana rufe baki ya ɓace daga gurin gabaɗaya.

 

_UMMOU ASLAM BINT ADAM

[15/10/2021, 12:18] Ameera Adam *FIRST CLASS WRITERS ASSO

 

 

*ANYA BAIWA CE?*

 

Na

 

*AMEERA ADAM*

 

 

_LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA’A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._

 

 

FREE PAGE 7

 

 

Wani abu ne ya tsargawa Fulani Maryama tun daga tafin ƙafarta har tsakiyar kanta nan take jikinta yayi sanyi, a sanyaye ta kalli Jakadiya murya a raunace ta ce. “Jakadiya ina jin tsoron wanda Boka Marduska zai ɗauka, tsoro nake kar wani mummunan abu ya faru da Yarima Salman” Jakadiya cikin zuciyarta ta ce. “Ya rabbi samawati kasa jinin Salman ne tukuwicin da Boka zai ɗauka, yooo dama duk wanda ya sayi rariya ai yasan zata zubda ruwa” jin Jakadiya tayi shiru yasa Fulani Maryama ta ce.

 

“Jakadiya magana nake fa kina ji na” Jakadiya ta sauya fasalin fuskarta zuwa yanayin damuwa ta ce. “Allah ya taimakeki ba dan kar kalamaina za suyi kaushi ba da nace ki gaggauta yin istigifari saboda Salman Kainuwa ne dashen Allah, domin Jelar raƙumi tayi nesa da ƙasa babu wanda ya isa ya cutar da Salman da yardar Allah shine Sarki me jiran gado.” Fulani Maryama ajiyar zuciya ta ce. “Jakadiya shiyasa duk cikin masarauta babu wacce nake ƙauna kamar ke saboda ke kike kwantar mun da hankali a duk lokacin dana tsinci kaina a wani hali” tana gama faɗar haka ta fara karanta kalaman data saba sannan suka koma masarautarsu.

 

Washegari da asubar fari saƙo ya iso musu daga Masarautar Gombe na rasuwar Mahaifin Fulani Maryama wanda shi kaɗai ya rage mata a duniya, Dattijon arziƙi ne shekarunsa Tamanin da bakwai. Jam’ar ƙasar Gombe ba ƙaramin jimami sukayi ba na rashin adalin Sarkinsu marigayi Sarki Abdullahi bn Abdurrahman, lokacin da Mai martaba Sarki Aminullah ya samu wannan saƙon ba ƙaramin jimami yayi ba, tunaninsa ɗaya yadda zai sanarwa da Fulani Maryama rashin mahaifinta musamman da ya tuna yadda take matuƙar ƙaunarsa.

Fulani Maryama tun da gari ya waye ta ga Salma cikin ƙoshin lafiya damuwarta ta lafa amma a daren ranar ko baccin kirki batayi ba, saboda fargabar abinda zai faru batasan waye Boka zai ɗauka daga cikin ahalinta ba. Tana zaune Yarima Salman na ta ƴan wasanninsa Jakadiya ta shigo da sallama, ga wanda zai ƙarewa Jakadiya kallon tsaf zai fahimci tana cikin farinciki tana shiga ta sauya fasalin fuskarta cikin damuwa ta durƙusa ta ce. “Barka da kyakkyawar safiya uwar gijiyata Mai martaba ya umarceni da sanar dake yana jiranki a turakarsa.” Buɗe ido Fulani Maryama tayi da mamakin kiran da Sarki yake mata ta ce. “Jakadiya kinji sabon labari ne?” Jakadiya a zuciyarta ta ce. “Mugun labari ma kuwa amma idan kinje kyaji da kanki” a fili Jakadiya ta ce. “Ranki shi daɗe babu wani sabon labari da ya iso fada a wayewar garin nan”

 

Fulani Maryama miƙewa tayi gabanta na faɗuwa ta wuce har taje bakin ƙofa ta juyo ta ce. “Ki kira Binto ta kula mun da Yarima ina dawowa” Fulani Maryama bata jira cewar Jakadiya ba ta fice. Jakadiya ta bi bayanta da wulaƙantaccen kallo a hankali ta ce. “Fulani Maryam kenan ai duk wanda ya sayi tsintsiya yasan zatayi shara da sannu zaki fara girbar abinda kika shuka” ta ƙarasa gaban Yarima Salman ta waiga hagu da dama sannan ta dungure masa kai ta ce. “Kai kuma Falalu sai zare idanu kake kana fala-fala da kunnuwa, ko waɗannan fatalin kunnuwan naka ya isa a gane basu da alaƙa da Mai martaba.” tana jin ya fara kuka ta ɗauke shi tana cewa. “Yarima babban gwarzo badai ƙyuya kake ba ke Bintoto zo maza Fulani Maryama ta tafi gurin takawa” bata rufe baki ba sai ga Baiwar ta shigo da sauri, Jakadiya cikin masifa ta ce. “Ke dalla ki dinga nutsuwa yarinya sai rawar kai kamar taci sadakar miji.” Jakadiya dangwara mata Yarima tayi ta miƙe ta ce. “To gashinan ki kula da shi dama aikinki ne ni kinga wucewa ta”

 

Fulani Maryama zaune ta samu Sarki bayan ta gaisheshi ya amsa sannan yace. “Maryama kinsan dukkan mu daga gurin Ubangiji muke kuma gurinsa zamu koma, yarda da ƙaddara me kyau da marar kyau wajibi ne ga duk musulmin ƙwarai kuma duk wanda kikaji anwayi gari da mutuwarsa to Ubangiji ya fi mu ƙaunarsa shiyasa ya ɗauke bawansa.” Fulani Maryama ta gyaɗa kai jiki a sanyaye Sarki Aminullah ya cigaba da cewa.”A ɗazu aka aiko ɗan aike daga ƙasar Gombe cewa Allah ya yiwa Mai martaba rasuwa, Allah ya jiƙansa ya gafarta masa Ubangiji ya kyauta namu zuwan” Tun Sarki Aminullah bai rufe baki ba Fulani Maryama ta rushe da matsanancin kuka, ana cikin haka sauran Matan sarki suka ƙaraso ganin yanayin da Fulani Maryama take ciki ya sanyaya jikinsu. Zama sukayi cikin ladabi suka gaida shi sannan ya ci gaba da cewa.

 

“Dukkan Mai rai mammaci a yanzu ba kuka ya kamata kiyi masa ba yafi buƙatar Addu’arki, Mai martaba mutum ne mai karamci da dattako dan haka Addu’a ya kamata muyi masa Allah ya jiƙansa ya gafarta masa dan haka ku shirya zamu kai gaisuwar rashin mahaifin Maryama Ƙasar Gombe nan ba da jimawa ba.” Jiki a sanyaye Su Fulani Zaliha suka yiwa Mai martaba da Fulani Maryama ta’aziyya sannan suka miƙe kowacce ta shige sashenta. Fulani Maryama tana kuka tana haɗa hanya ta tashi ta nufi ɓangarenta zuciyarta fal damuwa da jimamin rashin Mahaifinta.

 

Fulani Maryama bayan ta gama shiryawa ita kaɗai a ɗaki ta fara magana. “Wannan masifa da me tayi kama saboda Allah a ce wai tsiyar Boka Masduka akan Mahaifina zata ƙare alhalin ni babu wata tsiya da naga ta sauya, aikuwa wallahi ba zanyi rashin mahaifi a banza ba kowa yaci tuwo dani miya yasha.” tana rufe baki ɗau jakarta ta rungumi Yarima ta fito, lokacin da suka fito ita da baiwarta a lokacin tuni Sauran Matan Sarki sun fito tsayuwarta babu jimawa sai ga Fulani Zaliha ta fito rungume da Saif a hannunta. Mai martaba na fito daga turakarsa ya ƙare musu kallo Fuska a ɗaure ya kalli Fulani Zaliha ya ce. “Ina zaki da yaron hannunki?” Fulani Zaliha bata kawo komai a ranta ba ta ce. “Allah ya taimake ka gurin rasuwar da ka bada umarnin zuwa”

 

Sarki Aminullah yace. “Ki mayar da shi ciki” a firgice ta ɗago da kai ta ce. “Bangane ba ranka shi daɗe” Sarki Aminullah yace. “Abinda na faɗa da farko, ya za’ayi mu tafi da nakasasshen yaro cikin jama’a” idanun Fulani Zaliha ne suka ciko da ƙwallah nan take ta fara hawaye, Mai martaba bai jira cewarta ba ya wuce ya barta a gurin. Babu wacce ta tanka mata haka suka wuce suka barta a gurin, Fulani Maryama dukda tana cikin halin jimami hakan bai hanata jin zuciyarta fes ba saboda ko ba komai tasan batayi asarar mahaifi a banza ba. Kafin ta ƙarasa tuni Mai martaba ya shiga cikin motarsa itama ta wuce motar da su Fulani ta suka shiga, suka ɗauki hanyar tafiya. Motar da suke ciki mota ce irin ta wancen lokacin me shige da fasalin Ladi ba ɗuwawu, tafiya sukayi me nisa har suka ƙarasa ƙasar Gombe.

 

Kwanan su ɗaya a masarautar Gombe suka juyo gida duk wanda yaga irin kukan da Fulani Maryama take yi sai ya matuƙar tausaya mata, Fulani Zaliha kuwa duk a ɗaɗɗare take kasancewar ta lura da Mai martaba kamar fushi yake da ita, ko gaishe shi tayi ciki-ciki yake amsawa a haka har suka dawo gida zuciyarta a dagule musamman idan ta tuna da abinda Mai martaba ya gaya mata. Tun daga ranar kuwa Sarki Aminullah ya daina shiga sabgarta da ta Saif, shi da ita sai dai kadaran kadahan babu wata kyakkyawar alaƙa a tsakaninsu, ko turakarsa ta zo da Saif zai ce mata ta mayar da shi. Haka Fulani Zaliha ta ci gaba da ƙunsar baƙin ciki idan abun ya yi mata ciwo sai dai ta shiga ɗaki tayi kuka me isarta, cikin dare kuma bata fasa kaiwa Allah kukanta ba haka ta duƙufa ba dare ba rana ta fauwalawa Allah lamuranta. A haka rayuwa ta cigaba da gangarawa har aka shefe shekara biyar sai a wannan lokacin cikin ƙudura ta ubangiji ta fahimci Saif ya fara koyon zama dukda har ya kai waɗannan shekarun bata fasa koya masa zama ba, kuma bata fasa kaiwa Allah kukanta ba. Babu wanda ta gayawa kuma a ranar da ta ga haka ba ƙaramin murna tayi ba, a cikin ƙasa da wata huɗu zaman Saif yayi ƙwari dan a yanzu tana iya zaunar da shi ta tafi aikin gabanta, har sai da zamansa yayi ƙwari sannan wata rana suna zaune da Mai martaba ta sanar masa. Ga mamakinta sai ta ga bai yi wani murna ba dama kuma batayi tsammanin zai nuna jin daɗin nasa ba, tun da yadda ta lura ba wani ji yake da shi ba ko dan shi nakasasshe ne oho, saɓanin Salman da yanzu duk inda Mai martaba yake yana gefensa. Shikuwa Saif sai ya shafe sama da sati biyu basu haɗu da Mahaifinsa ba, saboda ko kaɗan Baya ƙaunar Fulani Zaliha ta raɓo shi da shi. Sarki Aminullah shi kansa abinda yake yiwa yaron yake damunsa sam baya jin daɗi a ransa wani lokacin abun har damunsa yake yi, sai yayi kamar yace a kawo masa Saif sai kuma yaji sam baya ƙaunar ya raɓe shi, a wannan lokacin Saif na da shekara shida yayinda Salma yake da shekara bakwai a duniya, Fulani Maryama babu wani abu da yake damunta a yanzu saboda bata da wani abu da zai ɗaga mata hankali, tun da ba ita kaɗai ba hatta sauran mutanen da ke cikin masarautar sun san fifikon da Sarki Aminullah yake yi tsakanin Saif da Salman.

 

Lokacin da Saif ya kai shekara goma lokacin ya ƙara girma sosai kammaninsa dana Sarki Aminullah ba ƙaramin ƙara fitowa sukeyi ba, a wannan lokacin cikin ikon Allah ya fara jan ciki a haka yake zuwa duk inda yake san zuwa a sashen mahaifiyarsa, dan ma ta hanashi fita saboda bakin mutane da ƴan tsegumi yana fita ake dandazon zuwa kallansa, da ƙyar Fulani Zaliha ta shawo kan Mai martaba aka samo me koya masa karatu, da farko Sarki Aminullah faɗa ya rufe ta da shi lokacin da ta sameshi da magananar. Sai da ya gama sauraronta yace.

“Haba Zaliha ke meyasa kin fiye fitina yaron da yake a nakashe ta yaya zai iya koyan karatu?” Fulani Zaliha ta ce. “Allah ya taimakeka hakan ba yana nufin zamu barshi haka babu ilimi ba tunda yaron nan ba ciwon hauka yake yi ba kuma babu abinda ya samu ƙwaƙwalwarsa, Allah ne ya hallitoshi haka ba dan baya ƙaunarsa ba, yaron nan ba kurma bane duk abinda nake faɗa yana jina kuma wata baiwa da yake da ita duk inda na aikeshi a ɗakina kome nace ya ɗauko min zaije ya ɗauko min, kana ganin idan muka barshi babu ilimi Allah bazai tuhumemu ba Mai martaba? Dan Allah idan ma bazaka ja shi a jikinka ba saboda nakasarshi ka taimaka masa ya samu ilimin bautawa Ubangijinsa, Amma ina tuba gurinka bansani ba ko kalamaina sunyi ƙushi” ta ƙarasa maganar tana zubda ruwan hawaye. Mai martaba shiru yayi yana jin tausayinta cikin zuciyarsa yake ayyana tabbas yasan abinda ta faɗa gaskiya ne sai yaji gabaɗaya bai kyautawa kansa ba, janyota yayi jikinsa ya rungume ya fara lallashinta ya ce. “Ina ji a jikina sam ina aiwatar da rashin adalci amma ni kaina bansan me yake damuna ba, na rasa sanda na zama haka dan Allah ki dinga taimaka mun da addu’a kinsan mijinki da ba haka yake ba, Dan Allah idan ina cutar da ku ki yafe karki bari Ubangiji ya kamani da laifin da bansan ina aiwatar da shi ba.” Ɗagowa tayi ta kalli ƙwayar idanunsa tabbas tasan da ba haka yake musu ba ita da ɗanta, idan batasa son zuciya ba zata iya cewa duk cikin matasan yafi ƙaunarta, idanunta ne suka cigaba da kawo ƙwalla murya a sanyaye ta ce. “Ina yi maka addu’a a duk lokacin da na sanya goshina a ƙasa nayi imani da Allah addu’a ta bazata taɓa faɗuwa a banza ba, Allah zai kawo mana mafita kuma nida ɗana bamu taɓa ƙullatakar a zuciyarmu ba” Lumshe idanunsa yayi cikin jindaɗin kalamanta yace. “Insha Allah zan sa a kawo Malami ya dinga koya masa karatu shikenan” murmushi tayi tana gyaɗa masa kai sannan suka cigaba da hira.

 

Tun daga ranar aka samowa Saif Malamin da yake zuwa yana koya masa karatun addini dana boko, kuma sosai yake ganewa dan dai bashi da baki da yake mayar da karatun da aka biyasa ne, Saif Allah ya bashi basira ita kanta Mahaifiyarsa har mamaki takeyi idan yaji muryarka sau ɗaya ya gane ka, kuma yana daga kwancen nan yake taya mahaifiyarsa wasu ayyukan, ya lura Mahaifinsa bayasan ya dinga ganinsa a fada hakan ne yasa ya ganje jikinsa sai ya shafe wata guda bai halarci fada ba idan yaje ma Salman ya dinga hantararsa kenan yana ƙyararsa daga ƙarshe ma har suna ya sa masa kwantaccen. A haka rayuwa ta cigaba da gangarawa da daɗi babu daɗi har aka shafe wasu shekaru masu yawa.

 

BAYAN SHEKARA GOMA SHA BIYU

 

Wata rana Sarki Aminullah ya tafi ɗaurin aure ƙasar Adamawa a hanyarsa ta dawowa suna tafe a mota shida dogarawa uku tayar motarsau ɗaya ta fita, duk yadda direban motar yaso dakatar da motar hakan bai yuwu ba saboda kan motar ya kwace masa, da sauri motar bayansu tayi parking wacce sauran dogarawansa ne a ciki, Motar su Mai martaba cikin daji ta shiga bisa tsautsayi ta dinga bi ta kan wasu masu Fulani sai da ta kai ga wata bishiya sannan motar ta mutu, wani ikon Allah Sarki buguwa kawai yayi a kafaɗa sai gocewar ƙashi da yayi a ƙafarsa, Direban motarsa ne suka ya samu karaya sauran mutanen motar kuma duk buguwa ce. A hankali ya buɗe motar ya fito kasancewar jin koke-koken yaran da motarsu ta bige.

 

Kafin ya ƙarasa tuni Dogarawan ɗayar motar sun nufo gurin da suke da sauri suka kama Sarki Aminullah suna masa sannu, cikin galabaita yace. “Ku ƙyaleni kuje ku duba bayin Allahn cen” da sauri suka ƙarasa gurin suka samu mata Huɗu a akwance sai ƴaƴayensu uku da suke kuka Cen gefe suka hango wani bafulani da alama iyalansa ne jini na zuba ta kansa, Sarki Aminullah ne ya kira jami’an tsaro na garin Kano ya sanar dasu halin da ake ciki, ba’a ɗauki Jami’an tsaro na garin da suke suka ƙaraso tare da motar asibit suka kwashe su gabaɗaya zuwa asibiti.

 

A cikin mutanen da motar Mai Martaba ta bige mace ɗaya ce ta rayu, sai ƴaƴansu biyu suma kuma basu ji wani ciwo sosai ba, Mai martaba ya bada umarnin a wuce dasu gida a haɗasu da uwar bayi. Su kuma sauran gawarwakin tare aka yi musu suturu Mai martaba da kansa ya sallace su aka kai su makwancinsu.

 

Daga cikin Waɗanda aka wuce da su gida Akwai Inna Habi sai Maryu da Abu, tunda aka doshi shiga gidan sarautar Maryu ta fara ganin wata irin walƙiya na hasawa tana giftawa har tana neman kashe idonta, kanta ne yayi mata wani dummmm ga jiri da yake neman ɗaukanta, suna shiga cikin gidan kanta ya hau sarawa nan take zazzaɓi ya rufeta, sama-sama take jin kamar hayaniya akanta amma tana waigawa babu waɗanda suka hayaniyar babu alamarsu.

 

 

TO FA YANZU WANSAN ZAI FARA ƊAUKAN ZAFI

 

 

_UMMOU ASLAM BINT ADAM

[16/10/2021, 19:24] Ameera Adam: *FIRST CLASS WRITERS ASSO

 

 

*ANYA BAIWA CE?*

 

Na

 

*AMEERA ADAM*

 

 

_LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA’A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._

 

 

FREE PAGE 8

 

 

Abu ce ta dafata ta ce, “Maryo lafiya kuwa” Maryo lumshe idanu tayi tana jin kanta yana daɗa sara mata ta ce. “Abu wallahi kaina ne yake juya mun ji nake juwa na ɗiba na” Inna Habi ta ce. Sannu Maryo kinji? Bayan shi ko wani abun yana damunki?” Uwar bayi cikin masifa ta ce. “Kai dallah kuyi ku ɗaga ƙafa sai tafe kuke kamar masu tausayin ƙasa haba, banda ma ku baƙin takawa ne kwa tsaya kuna mun tafiyar rangwaɗa wallahi sai kun fanshe wannan rangajin da aikin wahala” Gabaɗaya babu wanda ya kula ta har suka ƙarasa sashen bayi Uwar bayi na zuwa da ƙwalawa Zainu kira da sauri ta fito cikin girmamawa ta ce. “Gani uwar bayi” a yatsine Uwar bayi ta ce. “Ga baƙin takawa ne ki kaisu ɗakinku” tana gama faɗar haka ta juya ta fice.

 

Zainu ce ta musu jagora zuwa cikin ɗakinsu, a gajiye su Inna Habi suka zauna a fakaice suke bin cikin ɗakin da kallo, sauran bayin da ke sanye da kayan bayi sai binsu suke da kallo jin ance baƙin Mai Martaba ne, suna nan zaune Jakadiya ta shigo cikin gidan kamar wacce aka jefo haka ta tsaya daga bakin ƙofar ɗakin tana binsu da kallo, Inna Habi ce ta russuna ta ce. “Ina wuni Inna” Jakadiya ya mutsa fuska tayi ta ce. “Kar dai kune baƙin takawa?” Murmushi Inna Habi tayi ta ce. “Eh mune” Jakadiya ta taɓe baki ta ce. “Ai naga alama to amma ba Inna sunana ba, ni da kika ganni Jakadiya ce babu wanda bai san matsayina ba a gidan na” Inna Habi ta gyaɗa cikin ladabi ta ce. “Zamu kiyaye” Maryo tunda ta zaune ta dafe kanta sama-sama take jin maganganunsu kuma har zuwa wannan lokacin bata daina jin maganganun farkon shigowarta masarautar ba, Jakadiya ta gyara tsayiwa tana gyara ɗaurin zaninta ta ce. “Yaya sunanku kun zuba mun na mujiya sai kallona kuke” Inna Habi ta ce. “Ni sunana Habiba wannan kuma Zainabu Abu ga Maryo duka ƴaƴana ne” Jakadiya ta ce. “Yayi kyau zan wuce sai na ƙara zagayowa” Jakadiya na wuce Inna Habi tabi Jakadiya da kallo lokaci ɗaya suka haɗa ido da Abu, ita kuwa Maryo duk budurin da akeyi kanta na ƙasa saboda sarawar da yake mata. Inna Habi ce ta ce. “Maryo lafiya kuwa ko jikin ne?” Maryo ta ce. “Inna wallahi har yanzu kaina sarawa yake ga wata irin hayaniya da nake ji” Inna Habi ta ce. “Kinsan gidan sarakai na’a rabasu da jama’a dole kiji hayaniya” Maryo taja ta jingina da bango tana runtse idonta.

 

Bayan kwana su Inna Habi na zaune Mai martba ya aika kiransu da a wannan ranar har sun fara sakin jikinsu da waɗanda suke kwana ɗaki ɗaya, sai dai alhinin rashin da sukayi da ƴan uwansu. Gabaɗaya suka ƙara gurin Mai Martaba a fada yana zaune da shi da Galadinma sai Waziri, Cikin girmamawa suka gaishe sa Sarki Aminullah bayan ya amsa ya ƙara da cewa. “Ya baƙunta” Inna Habi ta amsa da, “Alhamdulillah ranka shi daɗe” Sarki Aminullahi yace. “Masha Allah, maƙasudin kiranku na kira ku ne domin naji tarinku da ainihin garinku da inda zamu je mu sadu da ƴan uwanku, dan mu jajanta musu da rashi ƴan uwa su da sukayi” Inna Habi hawaye ta goge murya na rawa ta ce.

 

“Allah ya taimake ka a yanzu dai maganar da nake maka bani da kowa kaine uwata kaine ubana, Mutumin da ya rasu lokacin da kukayi hatsari Mahaifina ne” Inno ta tsagaita da maganar tana share ƙwallah ta ci gaba da cewa. “Mahaifina ne shi kaɗai ya rage mun kuma shima Allah ya karɓi rayuwarsa.” Sarki Aminullah ya ce. “Baki da dangim mahaifi ko mahaifiya” Inna Habi ta ce. “Bansan dangin Mahaifi da mahaifiyata ba, sai dai wata rana Mahaifiyata kafin ta rasu ta taɓa bani labari cewar ita da Mahaifina ƴan ƙasar Agadaz ne wani daliline ya rabosu daga garin sakamakon rashin amincewa da Iyayensu sukayi da aurensu, tun da suka baro garinsu basu ƙara komawa ba wannan dalilin yasan nida ƴan uwana muka tashi bamusan kowa daga danginsu ba, na taɓa aure da ƴaƴa uku sai mijin ya rasu lokacin da ciwon baƙwan dauro yazo yarana suka kamu da ciwon ta sanadin haka na rasa ɗaya daga ciki, sai biyu ne Allah ya barmun su gasu nan har sun fara girma, dangin Mahaifinsu tun bayan rasuwarsa suka gujeni da yake fulanin tashi ne tun daga lokacin bamu ƙara sa kowanne daga cikinsu ba. Daga cikin waɗanda suka rasu akwai Mahaifina, Mahaifiya sai ƴan uwana guda biyu wannan shine tarihina.” Cikin tausaya Sarki Aminullah yace. “Allah ya jiƙansu ya gafarta musu.'” Inna Habi ta ce. “Amin ya rabbi” Sarki ya ci gaba da cewa. “Zamu ci gaba da riƙe ku a ƙarƙashinmu Allah ya albarkaci rayuwarsu” Gabaɗaya suka amsa da Amin. Maryo tun da ta zauna take ƙurawa Sarki Aminullah ido har sai da shi kansa ya lura da irin kallon da Maryo take masa, mamaki ne ya kamashi saboda yasan duk cikin talakawa da fadawansa da sauran masu sarauta da suke ƙarƙashinsa basa iya haɗa ƙwayar idonsu da nashi, sai gashi ya haɗa idanu da Maryo yafi a irga amma ta kasa ɗauke ƙwayar idonta a kansa, Waziri da Galadima ba ƙaramin mamaki sukayi da ganin haka, har sai da Sarki Aminullah ya kalli Inna Habi yace. “Ya sunan yaran naki” Inna Habi ta ce. “Wannan Zainabu ce muna kiranta da Abu ita kuma wannan Maryama ce muna kiranta da Maryo” Inna Habi ta ƙarasa faɗa tana nuna Maryo da har lokacin ƙwayar idonta na kan Mai Martaba, Muryar Sarki Aminullah ce ta katseta ta sunyar da kai ƙasa taji yace. “Allah yayi musu albarka, zaku iya tafiya” Cikin ladabi suka russuna suna godiya gai Mai Martaba sanannan suka fice.

 

Tun kafin su fice daga farfajiyar Sarki Aminullah Maryo ta tirje a gurin ta ce. “Inna wallahi nasan wannan Sarkin kuma ko jiya a tsakiyar dare sai da ya zo gurina yace inbishi mu tafi…” da sauri Inna Habi ta sa hannu ta toshewa Maryo baki tana waigawa gefe da gefe muryan cen ƙasa ta ce. “Ke Maryo ahir na ƙarajin makamanciyar wannan maganar sai ranki ya ɓaci, so kike wani yaji ya kai ƙararmu a koremu bayan Allah ya rufa mana asiri? Idan aka koremu ina muka kama ki rufa mana koda wasa karna ƙara jin haka” A dai-dai wannan lolacin Fulani Maryama ta ƙaraso cikin soron da alama wucewa zata yi, binsu tayi da kallo daga ƙasa har sama har ta wuce su taga babu wanda ya tanka mata sai ma binta suke yi da kallo. A wulaƙance Fulani Maryama ta dawo ta ce. “Ku ƴaƴan gidan uban waye, waye Ubanku a garin nan da me kuke taƙama da har zanzo wuce wa baku gaisheni ba” da sauri Baiwar dake biye da ita a baya ta ce. “Ƙarya kuke ƴaƴan talakawa Fulani Maryama tafi ƙarfin wargi” Jiki na rawa Inna Habi da Abu suka tsugunna suka fara kwasar gaisuwa, Maryo ido ta ƙurawa Fulani Maryama babu ƙiftawa, a hankali Fulani Maryama ta fara takowa har gaban Maryo tana yi mata wani irin kallo mai wuyar fasaltuwa.

 

KUYI HAƘURI DA SHORT TYPING BANYI EDITING BA KUNSAN ƳAU WEEKEND OGA NA GIDA

 

 

_UMMOU ASLAM BINT ADAM

[17/10/2021, 19:50] Ameera Adam *FIRST CLASS WRITERS ASSO

 

 

*ANYA BAIWA CE?*

 

Na

 

*AMEERA ADAM*

 

 

_LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA’A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._

 

 

FREE PAGE 9

 

 

 

Fulani Maryama ta jima a tsaya tana ƙarewa Maryo kallo itama kuma Maryo bata ɗauke idanunta daga kan Fulani Maryama ba, wani murmushin gefen baki tayi nan take ta ɗauke Maryo da wani gigitaccen mari, nan take kanta ya sara ɗagowarta yayi dai-dai da ɗigar jini daga hancinta. Da sauri Inna Habi ta sha gaban Fulani Maryama ta ce. “Ranki shi daɗe Allah ya huci zuciyarki dan Allah ki yafe ta tayi kuskure, yarinyar nan ba lafiyayyi bace tana da matsalar ƙwaƙwalwa ne haka take yi tun kafin muzo nan” Fulani Maryama da fuskarta tayi murtuk ta ce. “Nan gaba sai ta banbance gidan da kuka baro da inda kuke yanzu, ƙarshen hauka idan a turu take a cikin gidan nan za’a saita mata zama Ni Fulani Maryama nafi ƙarfin kallon ƙasƙanci, me mulki ma a gidan nan bai isa zura mun ido ba bare ku ƙasƙantattun bayi” Fulani Maryama ba gama faɗa ta wuce fuuuu baiwarta na take mata baya.

 

Inna Habi da sauri ta fisgo Maryo da har lokacin jini na fita daga hancinta ta ce. “Maryo meye haka kike yi ne meyasa kike so ki jaza mana masifa Allah ya rufa mana asiri, anya Maryo wannan taurin kan naki zai barmu mu zauna lafiya a gidan nan” Idanun Maryo da suka rine jawur ta ce. “Inna akanme zatayi mana wulaƙanci to idan so take mu gaishe ta basai ta faɗa ba?” da sauri Inna Habi ta janye hannun Maryo suka wuce cen sashensu, sai da suka ƙure a ɗaki lokacin ta wanke jini hancinta Inna Habi ta ce. “Maryo ita rayuwar duniya ƴar haƙuri ce kinga nan gidan sarauta ne kuma a ƙarƙashin wasu muke, bamu da kowa sai Allah sai waɗannan bayin Allahn komai zaku gani a gidan kuyi haƙuri ku kauda kawunanku. Mai haƙuri shi zai dafa dutse har ya sha romo” Maryo ta ce. “Inna gaskiya wannan karan bazan yi haƙuri ba a irin haƙurin da nayi a baya ne aka cutar dani, yanzu haka zan ci gaba da haƙuri na kuma ƙare rayuwata babu jindaɗi?” tana ƙarasa faɗa hawaye ya fara zuba a idanuwanta. Inna Habi ta kalleta sosai ta ce. “Waye ya cutar da ke Maryo yaushe muka zo gidan shin tunda kika zo gidan nan wani yayi miki wani abu ne ban sani ba? Idan ma ancutar dake haƙurin dai dana baki shi zaki yi mahaƙurci mawadaci” Maryo ta ce. “Maganar gaskiya Inna wannan karan bazan zura ido ba” tana gama faɗa ta kwanta tana juya bayanta.

 

Bayan kwana biyu da yamma liƙis Bayan su Maryo sun kammala sirfen gero suna zaune suna hira ita da Abu da wata baiwa Dije, Abu ta ce. “Dije wai a gidan nan babu inda kuke zuwa ne wallahi ni ƙafa gabaɗaya ƙaiƙayi take a cen rugarmu mun saba da yawace-yawace, Abu ta ce. “Muna ai muna fita amma ba ko ina ba sai guri mai muhimmanci, kuma ai cikin gidan nan ma ya isheki yawo tunda babban gida ne, Maryo tayi murmushi ta ce. “Gaskiya ku zo mu shiga mu wasa idanu dan wallahi ni kaina na gaji da zama” miƙewa suka yi Dije tayi musu jagora suka dinga zaga gurare, sun jima suna kewaye-kewaye har magriba ta fara kawo kai lokacin sun shiga cen wajen gari banda bishiyoyi da sauran tsintsaye babu abinda yake tashi a gurin.

 

Suna tafe a hanyar su ta dawowa suka ƙaraso wajen wata murgujejiyar bishiyar kuka gida biyu da suke gefe da gefe reshensu ne ya yiwa hanyar rumfa, wajen babu komai sai kukan tsuntsaye ga wata iska me sanyi da take tashi a gurin.

 

Tunda suka tunkaro gurin Maryo ta hango wata kyakykywar fada a gurim me ɗauke da ado kala-kala masu ƙayatarwa da wata ƙayatacciyar kujera a gurin babu kowa akanta, wasu mutane ta gani kewaye a gurin suna ƙarasowa suka fara russunawa wasu kuma suna kiranta suna nuna mata karagar kujerar. Banda waige babu abinda take yi har suka so gota gurin ganin haka yasa Abu ta ce. “Maryo lafiyarki me kike kallo ne haka” Juyawa tayi suka ci gaba da tafiya batare da tace komai ba, shiru ne ya biyo baya har suka wuce.

 

Suna gabda ƙarasowa cikin Mutane suka bi ta wajen bishiyar tsamiya har sun kusa gota wajen ta ja tunga ta tsaya, Dije ce ta kalleta ta ce. “Maryo kiyo sauri kinga magriba ta kawo kai kizo mu wuce ciki” nan take kanta ya sara a hankali ta fara kallan mutanen dake kan bishiyar ta gyaɗa kai sannan suka wuce.

 

Da daddare misalin ƙarfe goma dare gidan yayi tsit yawancin bayim sunyi bacci idan da waɗanda basuyi ba ma kaɗan ne, cikin mafarki ta ganshi ya ƙaraso gurinta da hawaye fal idanunsa yana zuwa gurinta ya ce. “Sun cutar da Mahaifina a wancen karon dan ALLAH karki bari wannan karanma su cutar da shi, bani da ikon aikata komai kiyi wani abu dan Allah ki ceto rayuwar mahaifina bazan iya jure rashinsa a wannan karan ba” zumbur Maryo ta miƙe tana faɗa gumi sai kuma ta tuno da abinda ta ji, kamar wacce aka zabura da sauri ta miƙe ta fice daga ɗakin lokacin ƙafa ta fara ɗaukewa.

 

Tana fita kai tsaye sashen Mai martaba ta nufa a lokacin Sarki Aminullah na zaune yana hutawa ga damammiyar fula da taji zuma a ƙwarya, kai tsaye Maryo sashen ta nufa duk yadda dogarawa suka so hanata abun ya gagara, da sun zo riƙeta tana hankaɗe su suke faɗuwa a gurin, haka tayi ta kutsawa har sai da ta shiga cikin turakarsa tana zuwa ta ɗauke ƙwaryar furar har taje bakin ƙofa sarki Aminullah ya ce. “Wacece ke” kamar bazata juyo ba ta jima a tsaye har sai da ya fara takowa cikin wata irin murya ta ce. “RAYZUTA ce” tana gama faɗa ta fice daga ɗakin, da sauri sarki ya bita amma ga mamaki tuni ta wuce ya nemeta sama ko ƙasa ya rasa, abu ɗaya ya riƙe ya ganta sanye da kayan bayi.”

 

 

KUYI HAƘURI DUK WEEK END BAZAN DINGA POSTING DA YAWA BA SABODA BANDA TYM SOSAI. KWANA BIYU ZAKU JINI SHIRU SABODA WANI UZURI BABBA IDAN KUMA NA SAMU DAMA ZAN MUKU TYPING. FATAN ALHERI

 

_UMMOU ASLAM BINT ADAM

Ameera Adam: *FIRST CLASS WRITERS ASSO

 

 

*ANYA BAIWA CE?*

 

Na

 

*AMEERA ADAM*

 

 

_LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA’A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._

 

 

LAST FREE PAGE 10

 

 

Jiki a sanyaye Sarki Aminullah ya ƙara leƙawa harabar gurin amma babu ita babu alamarta, gyara tsayuwa ya yi ya furta, “Rayzuta? Wace me tsaurin idon Baiwa ce har za ta shigo cikin fadata ta ɗauke abinda zansa a baki na, ina masu gadin bakin ƙofar?” Sai a lokacin ya tuno da dogarawan gurin yana dubawa gefe da gefe ya hangosu a kwkkwance da alama babu me motsi a cikinsu. Tsoro ne ya fara kama shi da sauri ya ƙarasa gurin ya fara tattaɓasu yana kiran sunayensu, daga cen gefe Harisu ne ya fara motsawa yana jin muryar Mai Martaba ya miƙe a zabure yana rissina masa. Sarki Aminullah ya taka a hankali ya matsa gurin Harisu yace.

 

“Harisu me ya faru daku haka? Harisu ɗan jim yayi kamar me nazari sannan yace. “Allah ya taimakeka na tuna, muna tsaye wata Baiwa me sanye da kayan bayi ta ƙaraso gurinmu kai tsaye ta tunkari ƙofar shiga turakarta, muna ƙoƙarin hanata ta hankaɗe mu gefe nidai daga haka ban ƙara sanin abinda yake faruwa ba.” Ajiyar zuciya Sarki Aminullah ya sauke ya waiga gefe da gefe sannan ya ƙarasa gurin Harisu har sai da ya kai dabda kunnensa sannan yace. “Harisu ka bamu hankalinka nan bama san shiririta ko shirme, musan ka bincika muna a cikin bayi mata wacece RAYZUTA? musa san ayi binciken cikin sirri ko ƴan uwanka dogarawa banasan su samu wannnan labarin, idan har labarin ya fita ranka zaiyi mummunan ɓaci” Harisu cikin girmamawa ya rissina yace. “In sha Allah zan ayi yadda kace Mai martaba Allah ya ƙara nisan kwana da jinkiri mai amfani” Sarki Aminullah takawa yayi ya koma cikin turakarsa. Harisu ne ya dinga bin ƴan uwansa yana yayyafa musu ruwa sannan suka miƙe kowanne yana mamakin abin da ya faru.

 

Rayzuta kai tsaye tana barin gurin bata tsaya ko ina ba sai hanyar dajin nan wajen bishiyoyin kukar nan guda biyu, tana zuwa ta nemi guri ta zauna tana ƙarewa ƙwaryar fura da nonon kallo. A hankali ta dinga sa ɗan yatsanta tana tsince gubar da ke cikin furar, tana nan zaune ta hanyo wasu ayarin mutane suna tunkaro ta a hankali ta fara ja da baya suna ƙara tunkarota, tana niyyar yunƙurin guduwa suka cimmata da sauri suka fara zagaye suna faɗin wasu irin kalmomi da bata fahimtarsu, russunawa suke alamun girmamawa suna ci gaba da zagaye ta wani namiji ta gani ya ƙaraso gurinta har lokacin bata gane fuskar ko waye ba, zuwa yayi ya tsaya a kusa da ita yana murmushi tare da shafa fuskarta bata yi aune ba taji ya haɗa bakinta na shi sai a lokacin ta ga fuskarsa, suna cikin wannan yanayin taji an fisgi hannunta da ƙarfin gaske. A tsorace suka juya ita da matashin da ke rungume da ita cikin mamaki haɗe da tsoro, cikin izza ya ƙarasa gurin ta ya fisgi hannunta ya fara ƙoƙarin rungumeta da ƙarfin tsiya tana gocewa. Matashin yana ganin haka ya ƙaraso da gudu zai janyeta da sauri wancen matashin ya zaro wuƙa ya yanke shi a hannu. Hannu ta fara miƙa masa alamar ya ceci rayuwarta shima ya fara ƙoƙarin miƙa mata hannu dukda jinin da ke zuba a hannunsa. Ɗagowa tayi cikin kukan ta ce. “Furzan karka bari yayi nasara akanka kafin sanin ko waye shi dan Allah ka ceceni daga gurinsa, idan ba haka ba zan kashe kaina gwara na mutu da rayuwa da wannan” da sauri matashin ya miƙa hannunsa da niyyar cetonta amma wancen ya ƙara saka masa wuƙa a tafin hannunsa, a hankali ya sulale ƙasa ya faɗi jini na fita daga jikinsa.

 

Ana cikin haka Suka hango wani ya ƙaraso gurin ya fisgi hannunta ta ƙarfin tsiya ya wuce da ita cen cikin surƙuƙin dajin ba tare da waɗancen samarin sun iya aiwatar da wani abu ba, sai ma ganin wani ayarin tayi sun rufe Furzan da duka, tana riƙe a hannunsa ta fara ƙwala ihu tana cewa. “Furzaaaaan! Furzaaaaan dan Allah kazo ka ceci rayuwa ta.”

 

Juye-juyen take yi tana mutsu-mutsu har sai da ta fara birgima a cikin ɗakin, idanunta a rufe suke bakinta na ambatar sunan “Furzaaan” Inna Habi ce ta farka ganin abin da Maryo take yi yasa ta fara tashinta a hankali. Firgigit ta miƙe jikinta ya jiƙe sharkaf da gumi, da sauri ta rungume Inna Habi ta fashe da kuka har lokacin jikinta na karkarwa kamar mazari. Inna Habi rungume ta tayi tsam tana karanto mata addu’o’in da ta iya na bakinta har sai da ta lura da Maryo ta fara dawowa nutsuwarta. Kallan Inna Habi tayi idanunta cike da hawaye ta ce. “Inna wallahi tsoro nake ji na rasa me yake damuna ina jin tsoro wallahi kar su cutar da shi” A hankali Inna Habi ta ce. “Waye” Maryo ta fara girgiza kai tana hawaye ta ce. “Wallahi bansan shi ba Inna, ni banma taɓa ganinsa ba kawai dai ni inajin kamar yana da muhimmanci a rayuwata, ina jin kamar ma na taɓa saninsa a rayuwata, amma Inna ina jin tsoron waɗannan abubuwan da suke faruwa da ni. Inna wannan mafarkan suna bani tsoro…” da sauri Inna Habi ta rufe mata baki ta ce. “Ki daina faɗa Maryo babu abin da zai faru da ke sai alkairi, rashin addu’a ne da bakwa yawan yinta akai-akai ki kwanta insha Allahu bazaki ƙara irin wannan mafarkin ba”

 

Maryo har zata kwanta ta kalli Inna Habi ta ce. “Inna har wani suna naji suna ambatona da shi amma na manta shi” Inna Habi ta ce. “Karki damu wannan yana daga cikin shirmen mafarki, bari na tofa miki addu’a babu abinda zai faru da ke” Maryo ta koma gurin kwanciyarta ta kwanta Inna Habi ta fara karanto mata ayoyin tsari, Maryo sai kusan asuba bacci yayi awon gaba da ita.

 

 

Washe gari Dogarin Sarki Harisu ya dinga shige da fice yana bugar cikin bayi mata tare da tambayar wata baiwa me suna Rayzuta amma bai samu nasarar amsar tambayarsa ba, sai da ya kwana bakwai cir yana bibiyar me wannan sunan a ɓoye amma babu wata baiwa me irin wannan sunan, hasalima yawanci duka ya san sunayensu dama waɗanda suke bakin fuska su Maryo ne kuma dama waɗannan kusan kowa yasan baƙin sarki ne. Da daddare bayan ƙafa ta ɗauke Harisu ya samu Sarki Aminullah ya sanar dashi duk abinda yake faruwa, bayan ya gama sauraron Mai Martaba yace. “Harisa mun saurareka dan haka wannan maganar a binne ta bana buƙatar jin ta a bakin wani ko wata a gidan nan” cikin girmamawa Harisu yace. “Da kai da kaya duk mallakar wuya ne, idan har kaji wannan maganar ta fita to ka yanke mun hukunci me tsanani Ranka shi daɗe.” Jinjina kai Sarki Aminullah yayi sannan ya sallami Harisu.

 

Sarki Aminullah ya jima yana nazarin abin da ya faru amma ya rasa wacece ta aikata haka, daga ƙarshe ya watsar da lamarin yana addu’a a ransa akan Allah ya yi masa tsari da duk wani mai nufinsa da sharri.

 

Maryo washe garin ranar haka ta tashi sukuku da ita bata da wata walwala, Inna Habi ta lura da haka kuma hakan ba ƙaramin sa ta yayi cikin damuwa ba, sai bayan Azahar Maryo ta ɗan saki jikinta har suka fita ita da su Abu suka gudanar da ayyukan da suke yi duk yammaci.

 

Fulani Maryama ce ɗurƙushe gaban Boka Marduska gabaɗaya yanayinta tana cikin damuwa, Ɗagowa yayi da jajayen idanunsa masu kama da gauta sannan ya bushe fa wata irin dariya yace. “Zina bata cikin tsarin aikina ba da ɗana dake Maryama tunda na lura kin zama haja kowa baje kolinsa yake akanki, idan angirma ya kamata ace angirma amma da alama kin zama holoko haɗarin kaka.” Fulani Maryama ta ɓata fuska ta ce. “Haba sarkin bokayen duniya ya nazo ka share mun hawaye na amma kuma kana gaya mini maganganu marada daɗi” Boka Marduska ya kuma bushewa da dariya sannan ya murtuke fuska yace. “Bani na kar zomon ba ko ratayar ma ba’a bani ba, karfa wani narkeken ƙaton banzan ya shirga miki ciki ki zo ki sauke ɓacin ranki a kaina” Fulani Maryama fuska cikin damuwa ta ce. “Marduska ka taimaka mini bansan ya zanyi ba wallahi idan cikin jikina ya fito bansan ya zamu kwasheta da Mai martaba ba, tunda na gaya maka wancen karon Mai Martaba ya samu lalura yanzu babu wata mu’amalar aure da muke gudanarwa mu da shi.” Boka Marduska ya zura hannunsa a cikin waka ƴar siriyar rijiya ya zaro wani garin magani ya miƙa mata yace. “Ungo wannan ki kaɗa shi a ruwa ki sha cikin zai ɓare sai kuma ki kiyaye gaba” Fulani Maryama tayi masa godiya ta ce.

 

“Marduska amma bazan iya jure rashin haka ba kuma antabbatar mana da Mai martaba bazai samu lafiya ba” Boka Marduska ya zurawa Fulani Maryama Idanu sannan ya ce. “Maryama karki fake da guzuma ki harbi karsana dama cen halinki ne, ko kin manta Salman ba jinin Sarki Aminullah bane? Gwara kiya taka tsantsan dan daga wannan bazan ƙara baki maganin zubda ciki ba mata ƴar firit da ke sai jarabar tsiya, ki tashi ki bani guri sakamakon mu zai biyo baya da daddare zamu ɗauki ɗaya daga cikin bayin ku”Boka Marduska yana faɗa ya ɓace daga gurin, Fulani Maryama da yake ita kaɗai ta kai wannan ziyarar ta miƙe ya fice daga cikin kogon dutsen.

 

Washe gari tun safe Fulani Maryama ta aiwatar da abinda ta karɓo daga hannun Boka kuma ba’a ɗauki lokaci ba ta fara zubar da jini, bayan wani lokaci cikin ya zube gabaɗaya.

Tun safiyar ranar ta fara kasa kunne taji anyi shelar mutuwa, amma taji shiru sai kusan Azahar labari ya isar mata na rashin lafiyar Baiwarta Bintu, wai tunda gari ya waye take ta aman jini labarin na zuwa gurin Sarki Aminulllah ya sa aka ɗauke ta aka wuce da ita asibiti.

 

Fulani Maryama taji ba daɗi sosai saboda sunyi sabo da Bintu a ƙalla sun kusa sheka goma tare kuma ba ƙaramin biyayya take mata ba. Sakamakon haka yasa Fulani Maryama ta sa aka tara mata bayi dan ta zaɓi wacce zata maye gurin Bintu, dan ta tabbatar Bintu dai bazata tashi ba da alama Aljanun Boka Marduska sun jinkirta kashe ta. Tara mata su akayi gabaɗaya ta fara zagaya su ɗaya bayan ɗaya tana zuwa kan Maryo ta zaɓe ta. Haka sauran suka tarkata suka wuce suna jin inama ace sune suka samu aka zaɓe su. Inna Habi Addu’a ta dinga yi a zuciyarta kar Maryo ta nuna irin halin da ta nunawa Fulani Maryama rannan, cikin sa’a kuwa Maryo ta russuna da girmamawa ta yi wa Fulani Maryama godiya sannan ta fara takewa Fulani Maryama baya har suka shige sashen matan Sarki.

 

Kamar almara suna shiga a mararrabar sashen matan Sarki ta Hango Saif ya tako da ƙafafuwansa yana tafe yana laluben bango, yana wani irin baƙin amai mai warin gaske, A zabure Fulani Maryama ta ce. “Saif kaine kake tafiya da ƙafafuwanka?” juyawa tayi ta kalli Maryo ta ce. “Maza jeki zan neme ki anjima.” Maryo ta juya ta tafi tana waigen Saif da ya haɗa uban gumi har lokacin bai daina aman ba, kafin ta fita Fulani Zaliha ta shigo tana salati ganin halin da Saif yake ciki.” Fulani Maryama har harɗewa take saboda sauri tana shiga ɗakinta ta ɗebo wuri ta fara karanta kalmomin da Boka ya bata, nan take ta bayyana a bakin kogonsa hankali a tashe ta shiga ta fara ƙwalla masa kira.

 

Dukda a lokacin rana ta buɗe amma kogon nasa da ɗan duhu saboda idanuta sun rufe bata hangoshi ba, har sai da ta kusa taka shi tana ganinsa ta ce. “Marduska kamun rai yaron nan Saif ya fara takawa wallahi da matsala” Boka ya yi mata wani irin kallo yace. “Maryama ke me yasa kanki kamar na tinkiya haka yake? Kin shafe sama da shekara ashirin kina zuwa gurin nan kuma duk zuwan da zakiyi sai kun wayi gari da mutuwar Bawa ko Baiwa a masarautarku, amma wannan zuwan da kikayi kinji shelar mutuwa ne?” Fulani Maryama da ta kasa zama saboda tashin hankali ta ce. “A’a Marduska sai dai baiwata Bintu ba lafiya tana asibiti” Boka Marduska yace. “To idan ke me hankali ce yaci ace ki fahimci akwai babbar matsala, idan kin tuna shekarun baya na gaya miki Rayzuta zata shigo gidanku kuma yanzu haka ta shigo dan haka dabara ta ragewa me shiga rijiya.”

 

 

 

About the author

Hausa_Novels

Leave a Comment