Littafan Hausa Novels

Anjane Hausa Novel Documents

Toilet infection
Written by Hausa_Novels

Anjane Hausa Novel Documents

 

 

 

 

 

 

 

 

 

ANJANE

(Rashin sani)

★★★★★★★★★

 

 

_*PAID BOOK*_

 

 

Story/written by Ouummey.

 

Wattpad @ouummey.

 

 

 

From The author of:

Anjane

*HAƘORIN DARIYA*

*ƘASAR MU A YAU*

*BA NI DA LAIFI*

*SARAKI (the accused prince)*

*ABOTA CE KO SOYAYYA*

*And now…….ANJANE (Rashin sani) PAID BOOK*

 

 

 

 

 

*FREE PAGE 001*

 

 

 

Ina the name of Allah the most beneficient, the most glorious and the most merciful.

 

Dubun salati ga fiyayyen halitta Manzon tsira Annabin mu Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallam.

 

Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah maɗaukakin sarki mai kowa me komai da ya Wada ta ni da rai da lafiyar da na sake dawowa gare ku cikin wani salon rubutu na daban, Allah yadda ka bani ikon fara rubutun nan lafiya kasa in gama lafiya, Allah ka bani ikon rubuta abinda ze amfane ni ya amfani al’umma gaba ɗaya, ya Rabb ka hane ni rubuta abinda ze cutar dani ya cutar da ƴan uwa musulmai.

 

At long last nake cewa hellooooooo to You my fans.

 

Gani dai na sake dawowa, Ouummey ce dai taku tafe cikin wani sabuwar tafiyar da nake fatan ku so kuma ku ƙauna ce shi fiyeda littattafai na na baya, soyayyar da kuka nuna min a littafin

*SARAKI da ABOTA CE KO SOYAYYA*

is really amazing and unpredictable, am using this opportunity to say thank you once again, Ouummey loves you so dearly.

 

Sedai fa ba kamar baya ba this novel isn’t FREE kamar na baya, it’s a *PAID BOOK at ₦300 ONLY!!!.*

 

Na sani you guys won’t make me feel unloved or ashamed, nasan zaku nuna min ƙaunar da kuke min ta hanyar siyan littafina dan rubutu na ba abin yar wa bane, isn’t so??!.

 

Kar dai na cika ku da surutu, ga duk me buƙata zai/zata biya kuɗin ta ta wannan account ɗin, RABIATU ABDULLAHI

2391368231 ZENITH BANK tare da turo shaidar biya ta 09013101854

Ko a turo katin MTN ta wannan number

09013101854.

 

Son so fisabilillah .

 

 

WANNAN LITTAFIN SADAUKAR WA NE GARE KU MY FAMILY, HEART U ALL AND ALLAH YA QARA MANA ZUMUNCI DA QAUNAR JUNA, AMEEN.

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

________________________📖 Gudu take cikin fitar hayyaci cikin dokar dajin dake da shegen duhu duk kuwa da cewa ba wai dare ne ba dan lokacin bai wuce ƙarfe huɗu da rabi zuwa biyar ba, takun mutanen da take jiyo wa a bayan ta yasa ta tabbatar basu daina bin ta ba haka suna daf da ita, wani irin kuka ne ya kubce mata ta shiga yin shi tana sakin numfarfashi, bata san me yasa azzalumai suka yi yawa ba a duniya, bata san me ita ko ƴaƴan ta suka tare wa maƙiyan ta ba da suke san se sun shafe labarin su ta kowace hanya, a rayuwar ta bata da abokin gaba tun daga yarinta har zuwa girman ta, kai har zuwa yanzu da take wannan gudun na ceton ranta da na ƴaƴan ta bata san dalilin neman kashe su ba.

 

Kukan da yarinyar bayan ta fara ne yasa na gane jaririya ce sedai ba wai ɗanyar haihuwa ba dan zata kai watanni, bata rufe bakin ta ba wani kukan ya shiga tashi, se a lokacin na lura goyon gaba da baya ne matar tayi kuma da alama ƴan biyu ne dan itama ta gaban macece, wannan kukan shi ya kuma ruɗar da uwar ta saki nata kukan me sauti tana cigaba da gudun da take yi.

 

“Yauwa gata can, ku ƙara gudu mu cin mata tun kafin ta kai ga ficewa dajin nan dan na gaban sa ya fishi duhu ba lallai mu iya ganin ta ba”.

 

Cikin azama ta ƙara gudun ta dan jin abinda wani da take zaton shine babban su yace, burin ta a lokacin be wuce ta fita daga nan ta faɗa dajin gaban ba dan tsira da numfashin su sedai bata kai ga hakan ba taji saukar katako ta bayan ƙeyar ta, su ne suka jefo mata ko kuwa daga ina yake ba ta sani ba.

 

Faɗuwa tayi sedai da sauri tasa hannu ta dafe ƙasa dan gudun kar ƴar ta taji ciwo, jin takun su daf da ita yasa ta hanzar ta miƙewa duk kuwa da yadda taji jini na bin wuyan ta ban da kuma jirin da take gani, neman wajen fakewa take yi sedai kamar babu wani loko a dajin, a lokacin ba ta rayuwar ta take yi ba ta rayuwar ƴaƴan ta ne, ta sani ba lallai su tsira daga hannun wadan nan azzaluman ba sedai tana fata ƴaƴan ta su tsira ko da kuwa ita zata hallaka, yara ne da basu san komai ba basu kuma fara komai a rayuwar su ba dan yanzu ne suke watanni na uku da haihuwa, ba zata so rayuwar su ta tsaya iya nan ba haka kuma ba zata so maƙiya suyi galaba akan ta ba, ta sani saboda yaran ake neman kashe ta saboda kada uban su ya sami wani haske ko ƙanƙani a rayuwar sa.

 

Bata san me yasa marasa imani suka cika faɗin duniya ba sedai tana tausayin mijin ta kuma uban ƴaƴan ta, yaran ne dukkan wani farin ciki, jin daɗi da walwalar sa shiyasa mahassada ke neman ganin sun raba shi dasu har itama ta samu nata rabon ƙaddarar, rayuwar su cike take da baƙin duhun da bata taɓa tunani ba se a yau da take wani siraɗi na mutuwa ko rayuwa, se a yanzu ne abubuwa da dama suka dinga dawowa kanta da yaci ace ta ankare da su tuntuni sedai tsabar pious heart ɗin ta yasa bata taɓa zargi ko kawo wani mummunan lissafi ba, se a yanzu ta tabbatar da tabbas tayi kuskure, kuskure kuma mafi girma na ɗaukar cewa kowane ɗan Adam kyakkyawar zuciya gare shi.

 

Wani ɗan haske da take hangowa yasa ta nufi wajen cikin matsanancin gudu cikin fatan Allah ya kawo mata matserata ko da ta rayuwar ƴaƴan ta ne kaɗai, ta yarda ita ta mutu in har zasu rayu, tana fatan suyi kyakkyawar rayuwa ba dan saboda komai ba se dan kwaɗayin samun addu’ar su, Manzon Allah yace addu’ar ƴaƴa salihai ga iyayen su karɓaɓɓiya ce haka kuma sune kawai arziƙin da mutum ze mutu ya bari a duniya ya tadda shi a ƙiyama bayan sadaƙatul jariya wanda tasan bata da rabo a wannan ɓangaren dan ko tunanin hakan bata taɓa yi ba.

 

**********

 

Kamar ko wane hutun makaranta in an yi, yau ma tafe take da ƙafa kamar yadda ya zame mata jiki ba kamar ragowar ƴaƴa masu gata ba da za’a je ɗaukar su a mota, mashin ko keken amalanke ko kuwa motar ƙurƙura, ita da ƙafa take takawa har zuwa ƙauyen su wanda tsakanin shi da makarantar tafiyar awa huɗu da mintuna ne a ƙafa, bata taɓa jin ba zata iya ba dan tana matuƙar son karatun kuma ta san in ma ba tayi ba kanta kaɗai ta cuta dan shine kaɗai gatan da take tunanin zata iya samu da ze zama sanadin canjuwar rayuwar ta da ma duniyar ta gaba ki ɗaya.

 

A hankali ta shiga takawa lokacin dan ta gaji, tsakanin ta da ƙauyen su be wuce tafiyar mintuna Talatin ba dan ta kawo kusa sosai sedai a yadda ta gaji se take ganin in tayi yanke ta cikin daji zata fi saurin zuwa gida maimakon ta bi ta hanya sosai, ba ɓata lokaci ta danna kai cikin dajin cikin dajin ba tare da tsoro ba dan shiga daji a jinin su yake dan sun saba, in basu shiga yin itace ba sa shiga tsinkar magunguna ko kuma kayan marmari ko kuma yawon su.

 

Ƙarar gudun da taji yasa ta ɗan dakata tana tunanin anya lafiya, jin kamar gudun ba na mutum ɗaya ba yasa ta ɗare wata doguwar bishiya da sauri ta yadda zata samu damar ganin abinda ke faruwa, mace take hangowa da goyo har biyu wato gaba da baya tana gudu yayinda wasu mutane masu riƙe da makamai suke binta, hankalin ta taji ya tashi duk da bata san me tayi musu suke bin ta ba sedai a ƙananan shekarun ta tasan ba abu me kyau yasa suke bin ta ba tun da har ga makamai banda haka kuma mutane da yawa na shiga wannan dajin dan aiwatar da munanan ayyukan su saboda duhuwar dajin na basu kariya daga idanun jama’a, bata san me yasa ba sedai kawai taji a ranta ya zama dole ta taimaki wannan matar, ba zata bar wannan azzaluman su yi galaba a kanta ba.

 

Da sauri ta ɗirko daga bishiyar tareda nufar wajen matar da saurin ta dan gasu da suka saba da dajin bawa wani ganin duhuwar sa, da sauri ta fizgi hannun matar daidai lokacin da wani yayi nasarar sakar mata harbi a ƙafa ganin yadda take wahalar dasu, wani kogo ne na bishiya ta shigar da matar haka kuma da sauri tasa hannu ta since goyon bayan ta ganin wuyar yarinyar na reto alamun ta suma ko ta mutu, a galabaice matar ta kwanto ta gaban ma ita kuma tayi saurin tare ta.

 

Numfarfashi kawai matar ke yi dan ta galabaita to the extent da bata iya ko da buɗe idanun ta sosai balle tayi magana, hannun yarinyar da bata san wacece ba ta ruƙo da sauri tana fizgar numfashi kamar me asthma, da ƙyar ta buɗe baki da idanun ta tayi magana mara tsayi

 

“A…am..maa..naa, su..su..tsira..dan.. Allah”.

 

Wani irin duka ƙirjin yarinyar ya shiga yi jin abinda matar ke faɗa, da sauri ta shiga jijjiga ta,

 

“Ki tashi Aunty mu gudu, kar ki rufe idanun ki ni ban san inda zan kai yaran nan ba wallahi”.

 

Bata iya tace mata komai ba se yatsun ta duka goma ta ɗaga mata kafin ta shiga nata nuni da zobunan dake jiki wanda guda biyar ne, uku a hannun dama biyu a hannun hagu, da sauri ta sa hannu ta cire mata dan a tunanin ta sun dame ta ne, wuyan ta ta sake nuna mata nan ma ta cire mata sarƙar jikin ta da ɗan kunne, ajiyar numfashi matar ta saki tana buɗe ido sosai cikin ƙure ƴaƴan ta da kallo kafin wannan karan cikin cikakkiyar magana tayi magana

 

“Ki kula min dasu dan Allah, ban bar komai ba a wannan duniyar se su, sune fitilar zuciyar mahaifin su, kije dasu na baki halak malak amma dan Allah su tashi cikin kyakkyawar tarbiyya kamar kowane cikakken bahaushe musulmi, kije dasu ki kula dasu da wannan kayan sarƙar na hannun ki dan Allah kar su cimma na su kashe mu gaba ɗaya, kar ki tsaya wata magana dan ni tawa ta ƙare ko basu kashe ni ba mutuwa zan yi dan bana jin akwai ragowar jini a jikina, fatana ƴaƴana su tsira kuma alhamdulillah Allah ya turo min ke dan cetar su, ki tafi, ki tafi gasu nan, dan Allah ki tafi”.

 

Jin takun nasu da gaske kusa daf da bishiyar yasa yarinyar damƙe set ɗin sarƙar hannun ta ta zuba cikin jakar makarantar ta ta buhu dake hannun ta tare da saɓa yarinya ɗaya a ƙafaɗar ta ta goye ɗaukar tare da ɗaukar jakar buhun ta shige cikin dogayen ciyayin wajen cikin rarrafe dan kar su gan ta, seda ta ɗan yi nisa sannan ta tsaya jikin wata bishiya tana kallon yadda suka cimma matar a inda ta bar ta, haske haske sauka dinga yi da wayoyin hannun su cikin neman inda ta ɓoye yaran sedai basu ga komai ba, tsawon lokaci kafin suka koma wajen da suka bar uwar da mutum ɗaya na gadin ta,

 

“Yanzu ya zamu yi, me zamu cewa matar nan game da ɓatan yaran?”.

 

Ɗaya daga cikin su ya faɗa kafin ɗaya ya kai ƙafar sa yana shurin matar da ke jingine har lokacin yana tambayar ta inda ta kai yaran sedai tuni ta faɗi rigija alamar rai yayi halin sa, tsabar jinin dake kwance a inda ta jingina zaka yi zaton wata ƙaramar dabba aka yanka, wani mugun tsaki mutumin ya saki kafin ya umarci ragowar su ɗau gawar tata sukai mota shi kuma ya cigaba da bincika wajen sedai dake ba sanin kan dajin yayi ba ko kaɗan be ko kai wajen da yarinyar take ba rungume da baby ɗaya a ƙirjin ta idanun ta na zubar da hawayen tausayin matar da kuma ƴaƴan dake hannun ta da yanzu suka zama marayu, bata san wane irin marasa imanin mutane ne yanzu ke rayuwa a wannan duniyar ba, ko ina cike da azzalumai, kowa ba ya tausayin kowa, kowa ba ya san kowa, kowa kan sa kawai ya sani, ya ilahi duniya ina zaki damu.

 

Ganin kuka me sauti na neman kufce mata yasa ta miƙe wa ta shiga tafiya a hankali cikin takatsantsan dan ba zata so abinda ze jawo hankalin mutanen cen ba balle har su kashe Innocent babies ɗin hannun ta, tafiya me ɗan nisa tayi kafin ta fita daga dajin ta yanka ta cikin gonaki ta shiga ƙauyen su, garin yayi luf luf babu rana se iska me daɗi kasancewar magrib ta doso kai dan yanayin na nuna alamun be fi karfe biyar da rabi zuwa shida na yamma ba.

 

Ba tare da  tunanin komai ba ta nufi gidan su da yake babban gida kuma ginin ƙasa ba, sallama ta shiga kwaɗa wa a ƙofar babban zauren su sedai ba wanda ya amsa mata kamar ko da yaushe, sa kai tayi ta nufi sashen da take rayuwa yayinda tsirarun mata da yaran dake babban tsakar gidan bin ta da kallo suna maganganu ƙasa ƙasa ganin ta goyon jaririya ga kuma wata a hannun ta.

 

Wata sallamar ta kuma yi a ƙofar sashen su sedai nan ɗin ma ba’a amsa mata ba se dogon tsakin da aka ja, kai a ƙasa ta shiga ƙofar tana tafiya a hankali kamar wata ɓarauniya ko wadda ƙwai ya fashewa a ciki, inna mariya dake tsugunne bakin malalallabta tana rege shinkafa ta tsugunna har ƙasa tana gaisar wa sedai maimakon amsa se zagi da yarfe ne ya biyo baya kamar yadda ta saba

 

“An dawo daga yawon ta zubar ɗin da sunan Makarantar boko, atoh mun dai sani ba wata wata boko se tambaɗewa da karuwa ci da ake yi ake fake wa da boko, wa ya sani ma ko an yi guzurin ɗan boko a ciki”.

 

Bata wani damu da abinda Inna mariyar ta faɗa ba dan ba yau ta saba ba, ba ita ba kusan duk ƴan gidan ma haka suke cewa, bata damuwa ne dan tasan ita karatu take yi ba yawon kafuwan ci ba kamar yadda suke faɗa, gaban ta ne yayi kwanci kwanci ya faɗi lokacin da yarinyar da ta Saɓa a kafaɗa ta calla wani irin kuka me sauti cikin Muryar ta ta jarirai, ashe ta daɗe da farkawa tun lokacin da sanyin la’asar ya buge ta amma bata dawo hayyacin ta ba se yanzu.

 

Zabura Inna mariya tayi tana dafe ƙirji cikin zare ido

 

“Me nake ji haka kamar kukan jarirai?”.

 

Ta faɗa tana juyowa ga yarinyar da tayi saƙare cikin tashin hankali, bata yi tunanin me ze je kazo ba lokacin da ta karɓi yaran, bata yi tunanin abinda ze iya faruwa ba dan a lokacin ba abinda ke ranta face ganin ta tseratar da rayuwar su, sam a lokacin ta manta da wane kalan mutane take rayuwa se yanzu da yarinyar ta shiga kuka kamar yadda aka san jarirai ƴan watannin ta da haihuwa.

Yan Dandi Hausa Novel Complete

“Innalillahi, a’uzubillahi ni mariya jikar me shanu, me nake gani a hannun ki haka SALAME kamar jaririya?”.

 

Yarinyar da aka kira da salame bata iya tace komai ba yarinyar bayan ta itama ta shiga kuka alamun itama ta farfaɗo, gaba ɗaya se hankalin ta ya rabu kashi kashi, ga kukan yaran ga kuma kururuwar da Inna mariya ke yi mata, bata san me yasa taji zuciyar ta na zafi ba jin kukan yaran dan har tsakiyar ranta da kanta take jin kukan dan haka d sauri ta zauna tana ɗora ta hannun ta kan laps ɗin ta ta shiga kiciniyar kunto ta bayan ta, jijjga babyn ta shiga yi tana tapping ta kan cinyar ta dan tayi shiru shiyasa sam bata lura da mutanen da suka taru saman kan ta ba se da Muryar kawu Habibu ta ratsa kunnen ta lokacin da ya daka mata razananniyar tsawar da ta sa har ta kusa yar da ƴar hannun ta kafin tayi saurin tare ta………………..✍🏻

 

 

Ya Rabb ka tsare mu daga sharrin zuciyoyin mu ka hana mu hassada, baƙin ciki da ƙyashi ga nasara da ɗaukakar wani, Ameen.

 

 

©️ Ouummey 📚✍️.

 

 

☑️Ote, Comment, share and patronize fisabilillah.

[03/12, 11:30 am] +234 901 310 1854: Ouummey 02 [ 10/11/2022 12:16 PM ]

 

★★★ *ANJANE* ★★★

(Rashin sani)

★★★★★★★★★

 

 

_*PAID BOOK*_

 

 

Story/written by Ouummey.

 

Wattpad @ouummey.

 

 

 

From The author of:

 

*HAƘORIN DARIYA*

*ƘASAR MU A YAU*

*BA NI DA LAIFI*

*SARAKI (the accused prince)*

*ABOTA CE KO SOYAYYA*

*And now…….ANJANE (Rashin sani) PAID BOOK*

 

 

 

 

 

 

 

FREE PAGE 002

 

 

 

 

 

 

 

 

 

________________________📖 “Dama na daɗe da sanin lalacewar ki kawai kika saka gaba shiyasa kika dage ke se kin yi wani karatun boko saboda ki samu mafaka dan kin san a nan bazan lamunci wannan iskancin ba shi kuma megari har da wani ɗaure miki katara, zaki faɗa min wanda yayi miki cikin da kika haifi waɗannan shegun ƴaƴan ko se naci uban ki, shegiya ƴar iska kawai”.

 

Kakkarwa jikin ta ya shiga yi haka ma bakin ta rawa yake tsabar tashin hankali, da ƙyar ta iya buɗe bakin ta tana sharar hawaye

 

“Kwarankwatsa ni ba ƴar iska bace kawu, wallahi bani na haifi ƴaƴan nan ba ni ban taɓa iskanci ba ku yarda dani”.

 

Wani tokari kawu Adamu ya sake mata a bakin da take magana take kuwa bakin ya fashe ya shiga fitar da jini, dafe bakin tayi da sauri hawayen ta na ƙaruwa saboda azaba

 

“In ba ke kika haife su ba to tsinto su kika yi?, Kaji min sheɗaniyar yarinya, wato har kin san ki buɗe wa wani gardi cinyoyi ko, Abu bani icen can me wuta, yau in baki faɗi gaskiya ba ba abinda ze hana ni kwaye fatar bayan ki da wuta”.

 

Kukan ta ne ya ƙaru ta shiga rantsuwa da magiyar su yadda ita ba ƴar iska bace sedai ina no one is willing to listen to her, ɗebe yaran Inna mariya tayi ta dangwarar da su a dandaryar jar ƙasar wajen shi kuwa kawu habibu ya shiga dukan ta da wannan icen,ihu ta shiga yin tun ƙarfin ta har Muryar ta ta dishe amma ba wanda yaji ko ɗigon imani ko tausayin ta balle ya bawa kawun haƙuri.

 

Seda ya dake ta iya yadda yaso kafin ya jefar da icen dake fitar da hayaƙi alamun akwai wuta a jikin sa har lokacin ya dubi kawu Adamu

 

“Kaje yanzun nan ka sanar da maigari kafin su iro su dawo mu tafi mu kai shegun yaran can, mukam Kamisu ya mutu ya bar mana annoba wallahi, haka kawai muna zaman zaman mu ya haifo shegiyar ɗiyar sa ya mutu ya bar ta gashi nan ta jawo mana abin kunya da Allah wadai zata lalata wa ƴaƴan mu suna”.

 

Da kallo kawu Adamu yabi bayan kawu habibu da ya fice yana ƙananun magana saboda masifar da ke cin sa a rai kafin ya maida hankali inda Salame ke tsugunne a takure kayan jikin ta duk sun yayyage saboda dukan da tasha, tsaki yaja ya sa ƙafa ya fice yana shura siɗaɗɗun takalman sa da suka ci duniya dan ƙullin leda a jikin su ya fi biyar.

 

Feƙeƙƙen zanin ta Inna Abu ta tattare tana kaiwa zaune kan jar ƙasar da ta kwanta saboda ruwan da aka yayyafa mata

 

“Ni yanzu damuwa ta saurayin A’ilo kar yace ya fasa auren ta saboda kayan kunyar da wannan annobar ta jawo mana”. Ta ƙarashe tana jefa wa Salame dutsen da yayi nasarar sauka a kan ta take kuma kanta ya fashe sedai ba’a iya banbance yadda yake zubar da jini dan ciwukan jikin ta ma duk jinin suke fitar wa so se ya haɗe.

 

“Sauƙin abin ma shima ƙanwar sa wasila ta taɓa yin cikin nan kin ga ba zasu ɗaga mana kai ba”.

 

Cikin rashin jin daɗin maganar ta Inna Abu ta haɗe rai dan duk abinda ze sa a Faɗi aibu ko a soki saurayin A’ilo bata so dan ba ƙaramin morar shi suke yi ba, wannan maganar da Inna mariya ta fara yasa ta miƙe tana ficewa da ƙafar ta da duk take cike da faso manya manyan saboda rashin sa takalmi.

 

Hararar ƙofar da ta fita Inna mariya tayi dan ba ƙaramin haushin Inna Abun take ji ba saboda yadda take musu ɗaukar kai kan saurayin A’ilo dan gaskiya duk gidan ba wanda ya taɓa saurayi me maiƙo kamar ta dan ɗan gidan maigari ne, kukan da yaran suka kuma sanya wa a tare yasa taji takaicin ta ya ƙaru.

 

Ji take kamar taje ta shaƙe su har se sun mutu sedai rashin imanin ta be kai haka ba so se ta dubi Salame da bata ko numfashin arziƙi saboda wahala ga kuma azabar da ciwukan jikin ta ke mata

 

“Kin tashi kin kwashe wannan tsiyar dake neman hanani nutsuwa ko se na kwashe su na watsa a rijiya?”.

 

Duk yadda jikin ta ya kai ga nauyi saboda dukan da tasha ban da azabar da take ji amma haka ta miƙe ta shiga takawa cikin ƙarfin hali har ta kai inda suke kwance se ciccilla hannaye da ƙafafu suke yi, a kafaɗa ta ɗora ɗaya tana runtse ido saboda zafin da taji dan akwai ƙuna a wajen ɗayar kuma ta rungume ta wuce akurkin ɗakin ta da ke daf da zubewa saboda yadda ya takwarkwashe, duk da gidan dukan sa na ƙasa ne amma babu ɗaki mafi muni kamar nata dan madafar su ma tafi shi nesa ba kusa ba.

 

Kan yagalgalallen buhun da take kwanciya ta shimfiɗar da yaran kafin ta kuma fice wa ɗauko jakar buhun ta, cikin ɗan hanzari ta ƙara sa ta ɗauke jakar ganin Inna mariya bata wajen da alamu ta shiga bayan gida ne.

 

Cikin cije baki ta kai zaune gefen yaran ta shiga bin su da kallo tana yaba kyan su a ranta kafin kuma ta ji wani sabon so da tausayin su na ratsa ta tuno yadda aka kashe mahaifiyar su,

 

‘duk abinda ze faru bazan yarda in rabu da ku ba, mutuwa kawai zata  raba tsakanin mu insha Allah”.

 

Ta faɗa a ranta tana jingina da bangon ɗakin sedai da sauri ta janye jin raɗaɗin da ya ratsa kwanyar ta hakan na shaida mata akwai ciwo a nan ɗin ma.

 

Ƙofar ɗakin taje ta saya kafin ta tuɓe kayan makarantar jikin ta da suka yagalgale saboda ƙunan wuta da kuma dukan ice, wani koɗaɗɗen zani ta ɗauko wanda dama uku ne kawai da ita kuma da su take rayuwar yau da gobe ta ɗaura, wanka take son yi sedai ta san yau ko mutuwa zata yi ba zata samu ruwan zafi ba se kawai ta ƙudure yi da na sanyin ta fita zuwa ƙatuwar rijiyar su dake tsakiyar gidan.

 

Babbar rijiya ce dan dukkan su na iya ɗiban ruwa a lokaci ɗaya dan tana ɗaukar guga sama da biyar, ƴan mata biyu ne suke ɗiban ruwa suna hirar su, tun da ta nufo wajen suke dariya suna nuna ta, duk da bata jin me suke cewa dan da ɗan tazara tsakanin su amma tasan ba abu me kyau suke faɗa ba, hakan ba sabon abu bane a wajen ta dan duk faɗin gidan ba zata iya ɗaga mutum ɗaya tace gashi me son ta da ƙaunar ta bane, daga masu ƙi da tsanar ta se kuma ƴan ba ruwa na sune wanda ba zasu dake ta ba ba zasu zage ta ba sedai ba zasu taimaka mata ba irin su kawu Adamu kenan.

 

Ƙaramin guga ta ɗauka ta zura cikin rijiyar ignoring all the curses da suke rending mata ta shiga ɗiban ruwan ta dan tun da da basu samu dalili ba ma ƴar iska suke ce mata balle yanzu da ta zo da ƴaƴa har biyu gida,

 

“Iyayen karuwa dai sun yi asarar haihuwa, ke in kika bibiya ma sule me shago ne yayi mata cikin da ta haifi yaran nan dan kin ga shine kaɗai yake kulata a garin nan”.

 

“Kai anya kuwa sule ne, kin ga fa Inna tace yaran sun yi kusan watanni biyu da haihuwa shi kuwa ai rabon shi da ita tun da tayi ƙaryar jarabawa ta zauna wata goma a makaranta”.

 

“Eh ba mamaki ma a can wani malamin ya ɗirka mata cikin, kin san dama buba ya faɗa mana kafirai ne”.

 

Haka suka cigaba da maganganun su na aibata ta amma bata kula ba ta ɗibi ruwan da take buƙata ta koma sashen su, da saɗab saɗab ta zagaya wani ɗan fili dake bayan ɗakunan su ta yaye zanin ta kwara wa jikin ta ruwan, sauƙin ta ruwan rijiya akwai ɗumi ban da haka kuma yau ɗin an yi rana sosai shiyasa ya sake yin ɗumi kamar an gauraya dana zafi.

 

Zanin ta mayar tana barin cinyayyen bokitin a nan wajen ta koma ɗaki bayan ta leƙa ta tabbatar Inna mariya bata wajen, yarinyar da ta fi yin kuka ta ɗauka ta shiga jijjigawa har ta yi baccin wahala dan yunwa suke ji sedai bata san me zata basu ba, haka tayi wa ɗayar ma ta samu itama tayi bacci.

 

Tuno da wata hamsin a jakar ta yasa ta maza ta jawo jakar ta shiga zazzage ta, kayan sarƙar babar ƴan biyu da suke zube a ƙasa ta ɗaga ta shiga kalla tana yaba kyan su kafin ta shiga hawaye sanin me su ta daɗe da zama gawa, hawayen ta share ta shiga tattara su tana mayar wa haka dan ta san a yadda suke da kyau muddun Inna mariya tayi ido biyu dasu shikenan sun zama nata.

 

Hamsin ɗin ta shiga juya wa a hannun ta tana tunanin ta yadda zata fita daga gidan ba abin ta haura ta katanga ba jikin ta na mata ciwo.

 

Dan son samun sauƙin fita ta siyo musu kunu ta basu ta ƙara sa inda take ajiye gishiri dan tasan hakan kawai zata yi taji sauƙin raɗaɗin ciwon har ta iya haura katanga zuwa anjima.

 

Gishirin ta ɗauka tare da kwance ƙullin da tayi wa ledar ta ɗebo a hannun ta tana runtse ido saboda azabar da ta dan zata ji ta kai kan guraren da ƙunar take, duk yadda zugi da raɗaɗi ke ratsa ƙwaƙwalwar ta bata dena ba har se da ta gama kafin ta kwanta tana fidda numfashi ɗaiɗai kamar me cutar asthma.

 

Wannan horon kawu habibu ne lokacin da tana hannun matar sa Inna Abu kafin ta dawo hannun kawu iro, tun tana yarinyar indai tayi laifin da aka dake ta haka kawu habibun ze ɗebo gishiri ya dinga danna mata a wajen ciwon, karon farko da ya fara yi mata da hankalin ta suma tayi amma ko da ta farfaɗo haka ya sake yi mata.

 

A lokacin seda ta suma so uku amma ba hakan yasa ya fasa abinda yayi niyya ba, tun daga lokacin kuma yake mata wannan azabar, tun tana damuwa tana shiga tashin hankali har tazo ta daina ba kuma wai dan bata jin zafi ba se dan ta riga ta saba danne zafi da raɗaɗin a ranta.

 

Tsawon lokaci kafin taji kamar an yi ruwa an ɗauke duk ta daina jin azaba shigar gishirin jikin ta haka kuma tuni waccan azabar ta disashe ta zafin ciwon shiyasa se ta ke jin yanzu kamar babu ciwo a jikin ta, koɗaɗɗen zanin ta ta maida tare da zura rigar sa ta salallaɓa ta fita jin an shiga sallar magrib, ta katanga ta haura kamar yadda ta ƙudira.

 

Gudu ta sha sosai kafin ta kai ga isa wajen Sare me kunu, hamsin ɗin ta miƙa mata tana numfarfashi tare da faɗa mata ta bata na Naira goma ƙullin biyar biyar, a farar leda aka ƙulla mata ko wanne kafin a saka a baƙar leda ta miƙa mata,da hanzari ta karɓa sannan ta wuce wajen sule me shago, bata tsaya amsa tambayoyin da yake mata ba na ance ta dawo da ɗanyen goyon shegun yaran da ta haifa har biyu ba tace ya bata siga na goma se madara ta Ashirin.

 

Madarar kusan Naira ɗari ya zuba mata haka sugan ma ya fi na hamsin ya bata yana faɗin tabar kuɗin kawai dan ba ƙaramin so yake wa Salame ba, godiya ta masa ta juya zuwa hanyar gidan su cikin gudu sosai har ta kai, ta katanga ta koma kamar yadda ta fita dan ba wata katangar arziƙi bace kun dai san fences ɗin ƙauye.

 

Hango Inna mariya a Zaune kan tabarmar da take zama daga bakin ƙofar ɗakin ta yasa ta rasa yadda zata yi ta wuce, ta daɗe tsaye kafin taga shigowar kawu iro sashen nasu, kayan hannun sa Inna mariya ta karɓa ta shige ɗaki tana masa sannu da zuwa shima ya mara mata baya, da wannan damar ta samu ta saci kofi ɗaya cikin kofunan sashen ta shige ɗaki da sauri.

 

Seda ta saya ƙofar duk da ba mai shigo nata dan ko neman ta Inna ke yi sedai tai ta ƙwala mata kira, kunun ɗaya ta juye cikin kofi ta sa sigar kaɗan ta juya da wani kara kana ta ɗau yarinya ɗaya ta fara tashin ta har se da ta buɗe ido, buɗe baki tayi da nufin komai Salame ta maza ta sa mata kofin a baki, cikin yunwar da ta galabaitar da ita ta shiga sha ba wani musu, sosai tasha kunun kafin ta saki tana sa harshen ta tana lashe saman cute small lips ɗin ta, murmushi Salame tayi ganin yarinya ma ta san zaƙi dan ta tabbatar da bata sa sugar ba baza ta sha da yawa haka ba.

 

Ajiye ta tayi inda yarinyar ta shiga cilla ƙafafu tana wasa da hannayen ta, ƴar uwar ta ta ɗauka itama ta tashe ta tare da bata kunun, itama ta sha da ɗan yawa duk da be kai yawan na ɗayar ba, ajiye ta ta ƙara ɗaya na biyar ɗin kan wanda suka rage ta ƙara sugar ta shiga sha itama dan ta san yau kam ko itace tafi kowa maita ba zata samu abinci ba a gidan nan, da ɗan dama ta rage saboda kar yaran su ji yunwa su nema kuma babu, jakar ta ta ɗora ta rufe cup ɗin dashi sannan ta juya ga yaran ta ƙure su da kallo.

 

Kyawawan yara ne Masha Allah kamar ƴaƴan turawa, ba ramammu bane dan da ƙibar su daidai sanye da kayan masu kyau suma kansu an kakkama da soso da ya daɗa ƙara musu kyau, addu’a ta shiga yi musu tana tofa masu na Mayu da baki dan akwai Mayu sosai a ƙauyen.

 

Seda ta gama yi musu addu’a sannan tayi wa kanta ta nemi waje kan buhun ta ta kwanta dan zannuwan ta biyu ta haɗa ta shimfiɗa wa yaran da har yau bata san sunan su ba dan maman su bata faɗa mata ba ita kuma bata san da sunan da zata kira su ba.

 

Washegari kuwa tun kiran sallar biyu da ta tashi bata koma ba, tana idar da sallah ta fita tsakar gidan su ta hau aikace aikace kamar yadda ya zame mata wajibi muddin tana garin, tana gama wa ta ɗau bokitan su ta fita rijiya ta shiga jido ruwa, se da ta cika ko ina kafin ta hau kunna ruwan komo, tana juye kokon ta kai duban ta kan ƙofar su Inna mariya dake kulle har lokacin, da sauri da sauri ta dafa ruwan zafi ta kai ɗakin ta ta ɓoye cikin wata madaidaiciyar roba sannan ta dawo wajen ta kashe wutar.

 

Ɗakin ta ta koma ta surka ruwan a bokitin ta ta shiga yiwa yaran wanka, wankan jariri ba sabon abu bane dan tun tana shekara bakwai aka fara bata rainon yara haka kuma tana shekara sha biyu suka fara sa ta wankan jariran su, tana gamawa Hassana kamar yadda ta raɗa wa wadda taga tafi girma a idon ta ta ɗau Ussaina ta mata ita ma sannan ta ɗau ruwan nasu ta shiga banɗakin su ta kwarawa jikin ta ta maza ta fita tare da maida bokitin ta bayan ɗaki.

 

Ko da ta koma tuni yaran sun koma bacci da alama sun ji daɗin wankan, murmushi tayi tana jan kumatun Ussaina daidai lokacin da taji Muryar kawu habibu cikin ihun kiran sunan ta.

About the author

Hausa_Novels

Leave a Comment