Littafan Hausa Novels

Amfanin Tafarnuwa 7 Ga Lafiyar Dan Adam

Written by Hausa_Novels

AMFANIN TAFARNUWA 7 GA LAFIYAR DAN ADAM

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Amfanin Tafarnuwa 7 Ga Lafiyar Dan Adam

by Ishaq Ismail Binciken manazartan kayan ci da sha wato Nutritionist ya tabbatar da cewa ta’ammali da tafarnuwa na da matukar amfani wajen inganta kiwon lafiyar dan Adam.

 

Cikin alfanun cin tafarnuwa akwai kara karfin kuzari ga ma’aurata.

 

Akasari ana amfani da tafarnuwa ne wajen a matsayin kayan kamshi da kara dandanon abinci, sai dai bincike ya tabbatar da cewa ana amfani da ita wajen rigakafin cututtaka bila adadin. wasu daga cikin amfanin tafarnuwa kamar haka:

 

1. Cutar asma Tafarnuwa na da tasiri wajen rigakafi da rage radadin cutar asma, inda ake bukatar mai cutar a duk dare kafin ya kwanta barci, ya dafa tafarnuwa ya sha da madara. Haka ma, wanda cutar ta taso masa, za’a iya bashi nikakkiyar tafarnuwa.

 

2. Tari da sanyi Ana amfani da tafarnuwa wajen rigakafin sanyi da tari inda ake bukatar mai fama da tari, ya tauna tafarnuwa ko kuma ya hadiye ta kai tsaye ba tare da hada ta da komai ba.

 

3. Atini da gudawa Tafarnuwa na kashe kwayoyin cuta da ke cikin ciki wadanda akasari su ke janyo atini da gudawa.

Maganain Karfin Maza

4. Matsalar ido Tafarnuwa ta kunshi sunadarai irinsu, quercetin, selenium da vitamin C wadanda duk suna taimakawa wajen rigakafin cututtukan da suka jibinci idanu musamman kumburi ko kuma kaikayi.

 

5. Hawan jini An ribatar tasirin tafarnuwa wajen rigakafin cutar hawan jini inda aka lakanci amfani da ita akai akai. Sakamakon wani bincike ya nuna cewa man da aka tatse daga tafarnuwa na taimakawa mai cutar hawan jini daga kamuwa daga cututtukan da hawan jinin kan haifar.

 

Rage kiba Tafarnuwa ta kunshi sunadarin allicin wanda ke kona kitsen da ke haddasa illa a jiki.

 

7. Narkewar abinci Yawan amfani da tafarnuwa cikin abinci yana taimaka wa wajen saurin narkewar abinci a cikin ciki ta yadda sunadaran gina jiki za su yadu cikin jini a kan lokaci.

 

8. Kara karfin mazakuta ga namiji Sakamakon wani bincike ya nuna tafarnuwa ya kunshi sinadarin Aphrodite wanda ke taimakawa ma’aurata wajen kuzari yayin saduwa da iyali.

About the author

Hausa_Novels

Leave a Comment