Littafan Hausa Novels

Amanar So Hausa Novel Page 16

Written by Hausa_Novels

Amanar So Hausa Novel Page 16

 

 

 

 

 

 

 

AMANAR SO

(Sai wanda yasan hakk’in so)

 

Story writing by✍🏻

Maryam Anas Brando

(Momeeyn Irfan)

 

 

*🌟ROYAL STAR WRITER’S ASSOCIATION🌟*

{R.S.W.A}

 

 

*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*

_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_

 

*Alk’alaminmu ‘yancinmu*

 

 

🅿️

15&16

 

**************Farouq ne ya kalli Mufeeda fuskarshi babu yabo babu fallasa ya ce “haba baby Mufeeda ya ki keso nayi?kina so in rufeki da fad’a saboda kince min wani yana sanki hmmmm innai haka ai sam bancika Namijiba wallahi sam,ni nan cikakken Namijine,ba a haifi Namijine da zai tsoratani a’kan soyayyaba ,soyayyarma kuma danasan bashi da power a’kan wadda yake so,cike da alfahari da izza Farouq ya cigaba da magana”duk duniya banga Namijin da yakai naji tsoronsa ba akan mace sannan bazan ce Miki kar ki so shiba duk da ma dai bansan wanene shi ba ban San matsayin shiba,sannan bana buk’atar na sani ,nasan dai ni cikakken Namijine zan iya karawa da ko wani irin Namiji a faggen soyayya ,dan haka shege ka fasa ni dashi .

 

Laifi Tudu Page 20 Hausa Novel

Kallanshi kawai Mufeeda keyi ko k’iftawa bata yi gaba d’aya ta kasa tan-tan cewa farinciki zatai akan kalaman Farouq d’in ko a’kasin haka,Mufeeda ce ta ce “ni fa bance ka rufeni da fad’a ba my Farouq daman abinda yasa na fad’a maka saboda kada daga baya kazo ka sami labari kuma ni kaga laifina.

 

 

Murmushi Farouq ya yi cike da izza ya ce

 

“Haba sweet Mufeeda wallahi ba zanga laifinki ba ai na dad’e da yarda da irin soyayyar da ki ke min ,nasan bazaki tab’a bawa wani zuciyarki ba bayan ni nasan zaki rik’emin amanar soyayyata ko da bana duniyar ma baki d’aya, kin ga kuwa mai zai sa in d’aga hankalina saboda wani ya nuna yana sanki .

 

 

 

Murmushi Mufeeda tayi cike da jin dad’in kalaman Farouq d’in ta ce “k’warai kuwa kai kad’ainazab’a a cikin zuciyata sannan kai kad’aine,kada kaji komai my Farouq Mufeedan ka tana tare da kai a kowani hali,murmushi Farouq d’in ya yi wanda shi kad’ai yasan ma’anarsa sannan ya ce “ngd sosai cweet Mufeeda yanzu dai sai ki huce gida kada Momy taga kin jima tayi miki fad’a ,Mufeeda ce tace “okay bara nazo na tafi naga lokaci ya d’an ja yanzu sai yaushe?kallanta Farouq ya yi sanan ya ce “sai munyi waya kawai zuwa dare ,nagode sosai ,sannan ki kulamin da kan ki,da to Mufeeda ta amsa sannan sukai sallama cike da kewar junansu suka rabu.

 

 

 

 

Bayan Mufeeda ta koma gida Momy take tambayarta ina atamfar da suka shiyo,kai tsaye Mufeeda ta ce mata ai tabawa mai d’inkin su Zahra ya yad’inka mata daganan taja bakinta tayi shuru ,Momy ta ce to “ya yi kyau ni yanzu zan fita zuwa bayan la’asar zan dawo sai ki d’aura girki kafin na dawo kin san bana san girkin dare.

 

“To Momy in sha Allahu bari naje na yi sallah naga biyu ma ta gota,da to Momy ta amsa mata sannan Mufeeda ta shige d’akinta.

 

 

 

Bayan ta idar da sallar ne da d’auki wayarta dake cikin jakarta,tana bud’e wayar taga 3missedcall Ahmad ya yi mata duk da bata yi save d’in number ba tasan tabbas shi ne tsaf ta gane k’arshen number d’in nasa,tsaki Mufeeda taja sannan ta a’jiye wayar gefenta ,aikuwa tana a’jiye wayar kiran Ahmad d’in yak’ara shigowa wayar a’karo na hud’u ✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻

 

 

 

Yawan comment yawan typing

 

 

 

Read

Share

Comment 👍

 

 

Momeeyn Irfan ce

Y’ar Amanar Royal ⭐

About the author

Hausa_Novels

1 Comment

Leave a Comment