Littafan Hausa Novels

Alkibla Hausa Novel by Huguma

Assadiya Hausa Novel
Written by Hausa_Novels

Alkibla Hausa Novel by Huguma

 

 

 

 

 

 

 

 

ALKIBLA*

_(THE BATTLE OF LOVE)_

 

*_HUGUMA_*

 

01

 

 

*_Da sunan Allah mai rahama mai jin ƙai_*

 

 

*dukkan godiya sun tabbata ga Allah madaukakin sarki daya bamu aron rai da lafiya,tsira da aminci su qara tabbata ga shugabanmu annabi muhammad S A W*

 

 

*_littafin ALƘIBLA,labari ne dana qirqeshi mafi rinjaye kan soyayya,saidai kuma hausawa sukance ba’a rasa nono a ruga,akwai wani sashe na matsalolin da mafi yawan ‘yammata ke fuskanta a wannan zamanin game da samarinsu,wanda kusan basu san daga inda matsalar take ba_*

Sanadin Caca Hausa Novel Complete

_a wannan karon ina neman afuwan masu karatu,littafin alqibla bazai kai yawan littafin siradin rayuwa ko alqawarin Allah,saidai ina fatan zai nishadantar ya kuma qayatar daku in sha Allah,ASHA KARATU LAFIYA_

 

*ALLAH YAYI RUQO DA HANNAYENMU

 

*KIJI TSORON ALLAH,KARKI TABA KAYAN DABA NAKI BA*

 

____________________________

 

 

 

*GOVERNMENT GIRLS UNITY COLLAGE KACHAKO*

 

 

 

Makekiyar harabar makarantar ‘yammatan ta kwana dake garin kachako wato government girls unity collage cike take da dandazon al’umma,wanda mafi akasarinsu dalibanta ne,da kuma wasu daga cikin iyayen yaran dake ta faman qoqari dakai kawon kwashe yaransu zuwa gidajensu don gabatar da hutun zangon karatu na uku wato third semester.

 

 

Daga can gefe daya na harabar makarantar kana iya hangen yadda matashiyar ke tsaye goye da hannayenta sanye cikin wankakku kuma gogaggun unifoarm da suka amsheta sosai,ta zubawa harabar makarantar tasu idanu,kamar wadda aka baiwa aikin qididdige yawan al’ummar dake karakaina a wajen,kyakkyawar fuskarta babu alamun fara’a ko kadan.

 

 

Duk da cewa duka duka shekarunta ba zasu haura goma sha biyar ba,amma kana iya tantance kyan zubi diri gami da siffa da Allah ya bata.

 

 

Mai matsakaicin tsaho ce,ma’abociyar doguwar fuska da fata wadda bata cika haske ko duhu ba,ta yadda ba zaka iya kiranta da baqa ba,hakanan ba zaka kirata fara kai tsaye ba,tana da manyan idanu wanda ba’a fiya gane girmansu ba idan ba budesu tayi sosai ba duk sadda taso hakan,daga cikar girarta kawai zai gaya maka tana da yalwar gashin kai,Allah ya yi mata ado da dimple guda biyu a kumatunta hagu da dama,wadanda sukan bayyana duk sanda ta bude baki da niyyar magana,walau tayin ko bata yi ba.

 

 

Sake gyara tsaiwarta tayi idanunta na tara ruwan hawaye,duk da basu kai ga xuba ba amma duba daya zakayi mata ka gane hakan,iya damuwa ta damu ta kuma matsu,burinta kawai ta ganta a gida,Tana da burin son ganin mutane a rayuwarta da suke da gurbi na musamman a zuciyarta,duk da cewa ta rasa babban bango kuma jigo a rayuwarta,amma duk da haka bata rasa wasu daka iya xama makwafinsa ba bawai madadi ba.

 

 

Abinda ya qara mata zaquwa da son ficewa daga makarantar tunda wurwuri kamar sauran dalibai shine,komawar ‘yar uwa kuma qawa a wajenta gida tun lokacin yin hutu da fitar dalibai baiyi ba,sakamakon lalura data sameta,wadda ta tilasta aka maidata gida,banda haka,bata da wata damuwa mai yawa kan jimawar tata.

 

 

“Fatima sa’id dabo,fatima sa’id dabo” daga bayanta taji ana kwarara kiran sunanta,a nutse ta waiwaya tana duban mai kiran nata,daya daga cikin ‘yan ajinsu ce ladifa hamza,ci gaba tayi da dubanta har ta iso dab da ita

“Anzo daukarki,tun dazu ‘yan gidanku ke nemanki” da mamaki ta maida dubanta farfajiyar da take tsayen sannan ta dawo da dubanta kan ladifa,tayi tsammanin inda ta tsaya din zata iya ganin shigowar motar da tazo daukar nata,bata tanka ba saita fara takawa kawai don barin wajen,ladifa ta rufa mata baya tana tsokanarta kan rashin kuzarinta,da yadda ta zama wani sukuku kamar ba ita ba tun tafiyar munira gida ta barta.

 

 

Tunga taja ta tsaya lokacin data kusa isa dab da motar da akace tazo daukarta din,mamaki bayyane qarara a fuskarta,wannan ba daya daga cikin motocin gidansu bane,duk wani ahali na gidansu yasan wannan motar waye,ya kuma san da zaman motar,yaushe yazo?,ya akayi ya yarda ya bada motar a daukota?,shine da kanshi?,saita girgiza kanta da sauri,bashi bane,don ko a mafarki tasan bazai taba zuwa daukar wani daga cikinsu ba.

 

 

Murfin motar da aka bude yasa ta maida hankalinta sosai ga motar,wani matashin saurayi ne ya fito,wanda dukka a qalla shekarun haihuwarsa ba zasu rufa ashirin da biyar zuwa da shida ba

“Ko baki shirya komawa gidan bane?” Ya dan daga murya yana fadi idanunsa a kanta,hakanan fuskarsa babu yabo ba fallasa,kai ta kada tana son tambayarsa da yaren kurame kan shi da waye sukazo?,saidai bata kai ga tambayar ba murfin sit din baya ya bude shima,wata matashiyar ta sake fitowa,wadda a qiyasce suna iya yin shekaru daya da ita,fuskarta washe da fara’a tana duban zahra dake tsaye.

 

 

“Suprise ko?” Matashiyar ta fada cikin sautin qyalqyala dariya,ba tare data shirya ba itama qaramar dariya mai qaramin sauti ya kubce mata,wadda hakan ya baiwa dimple din dake kumatunta damar bayyana,sa’annan kamar wadda aka qarawa qaimi ta doshi motar,tunda taga hafsat cikin motar ta tabbatar ba abinda take zargi bane

“Wallahi kun shammaceni,na farko na zaci daga gidan abban gwammaja za’azo daukana shi yasa na zauna jiran motar gidan,na biyu kuma saina ganku anan,ya akayi haka…?” Cikin dariya hafsat tace

“Shigo daga ciki kisha labari….dama naci alwashin koda gold akayi motar nan saina shigeta ai”

“Mayya….saida kika shiga din kuwa” zahra ta fada tana dariya

“Sarakan surutu…zaki kama mata sauran kayan ku shige mu tafi ko kuwa har sai lokacin da ya diba mana ya cika bamu koma ba?” Cewar daya matashin saurayin dake a mazaunin driver,cikin shadda dinkin zamani.

 

 

Leqensa zahra tayi ta window,saita fashe da dariya tana cewa

“Wai,congratumatur ya musty…..yaudai an dana,kaga ko yadda motar tama kyau kamar taka?,anya ba zakayi ratse ba kaje kadanyi shawagi ka dawo ba?” Murmushi mai kama da dariya shima ya saki yana cewa

“Bari kawai…..don dai kawai nasan yana sane da lokacin daya bamu ne,wallahi yau da sai na tsatse motar nan son raina…ke kinga yadda ‘yammatan makarantar nan ke wani kallona…..”

“Basusan duk bige bane baba” zahra ta fada tana qyalqyalewa da dariya gamida shigewa gidan baya,ya soma qoqarin tada motar bayan duk sun rufe murafun yana cewa

“Aina miki dare xakimin rana,tunda na kankaroki nazo daukarki a wannan dalleliyar motar ba”langabar dakai tayi ta koma kalar tausayi

“Haba ya musti,ni dakai fa bata baci,kada kasa ‘yan uba suyi mana dariya”

“Dariya kuma ta nawa?” Wancan saurayin dake daya site din ya fada yana sake kwanciya sosai jikin kujerar motar

“Kaji ko?” Zahra ta fada tana bata fuska

“Rabu dashi,duka adawa ce,ba wanda zai ganmu a rana” mustapha ya fada yana harar shamsu dake gefansa zaune,wanda bai sake tankawa ba ya yamutsa fuska kawai gami da cewa

“Oho dai,maji ma gani”.

 

 

Kusan wannan ‘yar tsamar ba wani sabon abu bane a wajensu,sun riga da sun saba da hakan,wanda ba komai bane ya kawo haka ba face fahimtar juna da sabo dake tsakaninsu,duk da cewa akwai banbancin iyaye,duka sun fito daga mahaifa daban daban.

 

 

Saida suka hau titi sosai sannan ta gyara xama tana duban hafsat

“Wai ya akayi ne haka?” Dariya hafsat tayi kafin tace

“Wallahi ya hajja ce tace ya bada a daukoki,da yaqi ma tace to bari ta kira mas’udu ya bada tashi tunda shi ta isa dashi,to sai da yaji haka sannan ya bayar……zahra ma tana kusa sai data saka baki” tabe baki zahra tayi tana juyar da kanta xuwa window,tadan dubi titi kadan sannan ta dawo da dubanta ga hafsat

“Sai kace xai mani gafara motarma sai an roqeshi,ni wallahi ya hajja data sani bata roqa ba…..bama wannan ba,na dawo hutu da farinciki da burin samun sake,musha soyayyarmu nida hafiz,zuwansa nasan komai saiya rushe wallahi,babu wani sauran sake,bayan shi har gida ake biyoshi,ya kuma baje kolin soyayyarshi babu jin kunyar kowa,amma mu ya hanamu katabus babu gaira babu dalili,bayan yafi kowa sanin tsarin gidan,yanzu daka yi candy za’a zuba maka idanu ka kawo wanda zaka aura,idan babu ya zama jarraba,yanzun kuma kana tsaiwa dasu shiya hana ruwa gudu,haba” ta qarashe masifar dajan tsaki,dariya hafsat keyi abinta tana qarawa,kafin tace komai shamsu ya waiwayo yana dubanta

“Ke yarinyar nan da gaskene fa zaki qone tun kafin ki tafasa” hararar wasa ta jefa masa

“Saimu zauna ai ku jiqamu kusha,kunfi kowa daga murya idan bamu tsaida miji ba….”

“Meye a ciki,sadaka kawai zamu bada ku a masallacin malam ayuba” ya fada cikin shaqiyanci yana qyalqyalewa da dariya,wanda ya saka mustapha ya dara shima,baki ta tsuke ita kuwa kana tace

“Allah ya kiyaye ya sawwaqe,wuce nan wallahi”.

 

 

Da ire iren wadan nan hirarrakin suka ci gaba da tafiya cikin motar,tana tambayar hafsat wasu abubuwa da bata nan akayi,da kuma wadanda ta tafi ta bari,shamsu dai bai gaji da tsokanarta ba ya sake cewa

“Sai tambaya kamar makahon daya warke daga makanta,kamar wadda aka sallamo daga gidan yari” fuska ta narke wanda da alamu lokaci zuwa lokaci tana da dabi’ar shagwaba wanda batasan ita kanta tana dashi ba,kusan a jininta abun yake

“To ya shamsu don Allah meye maraba,kowa an barshi yana jeka ka dawo amma ni an turani boarding saboda shawarar da wannan mutumin ya bada,kuma wai aka amince masa”

“To ya za’ayi sai haquri,kinsan shi,idan ya kafe akan abu,amma kuma da wuya idan ya kafe din a kasa ganin alfanun hakan” baki ta zumburo tana mita

“Kaidai kawai kana goyuwa da bayanshi ne a fakaice”

“Ko kadan,ke dince kin fiya qorafi a kan lamuransa,bayan dukka mun riga mun saba da halayyarsa”

“Ai shikenan” kawai ta fadi,don batason zancan yayi nisa,saita kamowa hafsat wani zancan suka shiga.

 

 

Tafiyar a qalla awa daya harda wasu mintuna masu dan dama a kai suka isa unguwar gadon qadon qaya dake qwaryar birnin kano,bakin wani gida mai manyan kagantu tsaho da kuma fadi suka tsaya,wanda kallo daya zaka masa tun daga waje kasan cewa ba mace ko mutum daya zuwa biyu bane kawai ke zaune cikin gidan.

 

 

Zaka sake gasgata hakan lokacin da gate din gidan ya bude motarsu ta kunnu xuwa ciki,sassane daban daban qunshe cikin gidan,a qalla akwai sashe hudu zuwa biyar,kowanne na mazaunin gida mai xaman kanshi.

 

 

Kamar mai jira,tun kafin ya kammala daidaita tsaiwar motar ta balle murfin motar ta kwasa da gudu tamkar qaramar yarinya ta nufi daya daga cikin gine ginen dake tsakiyar gidan,madaidaicin gini guda daya dake hannun dama.

 

 

Baki dukka suka sake suna dubanta,duk da cewa sun sani ba tun yau ba halin xahra din na daban ne,quruciya da rawar kai kamar bata qara komai cikin shekarunta.

 

 

Da sauri saurinta take kutsa kai zuwa sassan ‘yar tsohuwar,burinta kawai ta cimmata,don ba qaramar kewarta tayi ba,sabo da shaquwa ne mai yawa tsakaninsu,wanda babu makamancin irin wannan tsakaninta da kowanne jika nata koma bayan zahrar.

 

 

‘Yar kyakkyawar dattijuwa tsaye gaban freezer tana yunqurin ciro wani abu tana magana da wata matashiyar budurwa dake xaune kan daya daga cikin kujerun falon sanye da hijabi mai hannu kalar blueblack,kallo daya zaka mata kasan shekaru sun fara tura mata,saidai yanayin tsafta da son gayu irin nata ya qawata tsufan nata sosai,don kana iya hangen ragowar jan lalle dake qafarta wanda bai gama fita ba,da tajajjiyar sumarta dake cikin dankwali,wadda ke cike da furfura,saidai kuma awanke take fes cikin tsafta da tsari,sam bata lura da shigowar xahra cikin falon ba sai sautin muryarta daya karade ilahirin falon.

 

 

“Hajja!” ta fada cikin nuna zallar farinciki tana nufarta,kafin takai ga juyowa tuni zahran ta isa gareta,ta kuma cukuikuyeta gami da rungumeta tsam ta baya tana dan tsalle

“Yan makaranta….barka,barka” ta fada fuskarta na fadada da fara’a,wanda ke bayyana farincikin dake cikin zuciyarta,yake kuma alamta tarin qaunar dake tsakaninsu

“I miss you my hajja” zahran ya fada tana dariyar farinciki

“A’ah,sauya harshe dai,ni ba gane wannan surkullen naku nake ba,yanzu yayanku ya gama nashi ya fita” dariya zahran ta saki tana sakin tsohuwar,saidai sautin ‘yar dariyar da taji daga gefanta yana hankalinta ya kuma hanata furta abinda tayi niyyar fada din,ta waiwaya tana duban sashen.

 

 

Kusan a tare suka sakarwa junansu murmushi

“Kicemin keda kishiyarki ne hajja……anty takwara ina yini” ta fada tana qarasawa inda matashiyar ke zaune,wadda fuskarta ke fadade da fara’a tana duban zahran gami da gyara mata wajen xama ta hanyar tattare hijabinta zuwa jikinta ta duban zahran itama

“Lafiya lau takwara…..ya makaranta?”

“Alhamdulillahi….gamu yau mun samu ‘yanci”

“Aikuwa dai kam,gida akwai dadi” daga haka ta maida dubanta ga ya hajja wacce ta samu waje ta zauna

“Hajjata….me dame aka tanadarmin?” Tayi maganar a shagwabe kamar yadda ta saba

“Duk abinda takwarata keso” hajjan ta fada tana dariya,qaramin tsalle najin dadi ta doka ta fada saman kujera tana cewa

“Allah yabarmin hajjata”

“Eh qwarai,kafin ki shukamin wata tsiyar taki ba” da sauri zahra tadan bata rai tana wulqita idanu,kana ta maida dubanta ga hajjan

“Haba hajja….Allah yasa ba gaban ‘yan adawa kika fada ba,da kin saka sunmin dariya,musamman su o’o” ta fada tana dan satar kallon zahra.

 

 

Sarai zahran ta fahimci wa take nufi,saita murmusa tana qunshe dariyarta gami da girgiza kai,kasancewarta mai sauqi da sanyin hali,marason yawan magana da rashin daukar al’amura da zafi

“Inna wuro….inna wuro rigima” ta ambaceta da sunan da yawanci akafi kiranta dashi cikin gidan,saita waiwaya tana duban zahran

“Eh ai nasan kin fahimta…..don nasan bakison laifinsa” ta fada tana sake bata fuska kamar wadda aka zaga,hakan ya sanya zahra yin dariya dole tana kada kai cikin jin nauyin ya hajja dake zaune a wajen.

 

 

“Sarkin neman magana,idan ya jiki kuma ya hukuntaki kice wani abu daban,shin kin shiga ma cikin gidan ma kin gaisa da mutane ko kuwa kkka zauna neman magana….” Kafin xahran ta baiwa hajja amsa hayaniyar ‘yammatan gidan ta soma dosowa falon

“Tofa,Allahumma salli ala,aikin dawo,yanzu zaku taru ku dinga hanani sakat,sauqin abunma dodonku yana gari shima”

“Ni wallahi hajja ki dinga hanashi zuwa duk sanda zanzo hutu,tsakani da Allah fa hanani sakewa yake,hutun wata daya kacal din da nake samu saina qareshi cikin rashin jin dadi” baki hajjan ta kama tana dubanta,ta rasa wanne irin abune haka irin na zahran,qara kusantowar hayaniyar tasu alamun suna bakin falon yasa ta dauke kai ba tare da tace komai ba har suka qaraso cikin falon riqe da hannuwan jakankunan zahra guda biyu,wanda ta barsu a farfajiyar gidan bata samu daukosu ba saboda tsabar zumudi.

 

 

Kyawawan matasan ‘yammata su biyar rigis sanye da unifoarm,wanda yafi kama da unifoarm din islamiyya,hudu daga cikinsu farare ne ba kamar kalar fatar zahran ba,yayin da daya ce kawai ta dauki kalar fatar zahra,dukkaninsu shekarunsu ba zasu wuce suma sha shida sha biyar din ba,saidai duk wadda ka kalla a cikinsu a ganin farko xaka tabbatar basu kama qafar zahra wajen kyau da zubi ba,duk da cewa babu mummuna duk cikinsu,kowacce da irin nata kyan,amma saiya zamana zahran ta zama zahara sosai a cikinsu.

 

 

Wani ihun murnar ganin juna suka saki kowacce na neman wajen zama

“Kai amma naji dadin dawowarkin nan wallahi,kinxo akan gaba” salma daya daga cikin ‘yammatan ta fada,harara yusra ta jefa mata daya daga cikin fararen ‘yammatan

“Eheen,kedai kin shiga uku wallahi”

“Ke kuma fa,tara kika shiga?” Salma ta fada itama tana maidawa yusra hararta duk da cewa mai kama da dariya dariya ce

“Kinga manta da ita,bani nasha ya akayi?”

“Bari mu saka labule tukunna saboda ‘yan saka eyes…..”

“Kunga ku tashi ku bani waje tun ban kira yayanku ba” hajja ta fada saboda sanin hali,ta sani sarai labarin nasu baya wuce na samarinsu shi yasa tayi musu haka,sosai suke wasan jika da kaka da ita,tun tana fada da fushi harta haqura ta qyalesu ta zubawa sarautar Allah idanu,harya zamana ma yanzu bata damuwa ya zame mata jiki,mutum daya ne tak da idan yana nan take samun salama,saboda dukkaninsu shakkarsa suke,kuma tsoron hukuncinsa suke.

 

 

“Idan wajen mama zaki don Allah ya zahra kice mata yanzu zan shigo na mata bayanin aiken” yusra ta fada tana duban zahra wadda ta miqe da wayarta a hannu tana murmushi

“Bafa can zata ba” hafsat wadda ta shigo daga qarshe ta fada

“Kema ai tunda kika ga ta miqe tana doka murmushi ai kinsan kwanan zancan” hafsat ta sake fada tana yin fuska,cikin dan jin kunya da nauyi zahra tace

“Kamar a kunnenshi kika fada” saita soma yin gaba cikin sauri sauri yayin da hafsat ta bita da magiyar ta tuba tayi haquri ta fice abinta tana dariya.

 

 

“Ni ina mamakin yadda soyayya ke gudana tsakanin yaya da yaa zahra”

“Ahto ai haka Allah ke lamarinsa,ku kuke masa wani kallo da bahagon hukunci,saboda ALƘIBLARKU ta bambanta ta wajen ra’ayi,kowanne bawa komai irin halinsa akwai yadda Allah ya sallada wanda zai iya zama dashi ya kuma rayu dashi”.

 

 

Tsam zahra ta miqe tana maida hijabin unifoarm din jikinta,wanda har yanzu bata kai ga cirewa ba tana cewa

“Bari na shiga ciki kan ku gama lacture din” don sam bata son irin wannan dogon sharhin na hajja,gani take koda yaushe aikinta shine bashi kariya dason wankeshi a idanunsu,bagan sun riga dasun gama sanin halayyarsa ciki da waje,kuma kowacce cikinsu ta kwana da sanin wannan,so tana ganin babu buqatar dagiya wajen bashi kariya da yima halayyarsa kwaskwarima a tsakaninsu.

 

 

Kamar hajjan zatayi magana sai kuma tayi shuru kawai ta bi zahran da kallo sanda take ficewa daga falon abinta ko a jikinta,har takai bakin qofa saita dakata

“Don Allah hajja wayata,tunda na dawo nake jina ba dai dai ba,na tabbata nuruddeen nacan yana nemana wallahi,tunda yasan yau zamu dawo” daquwa wannan karon ta watsa mata

“Qaniyarki,yanzu nake muku nasiha kika tashi kika barni zaune wajen,shine yanzu kikeso naje na dauko miki waya,idan kin damu ai kinsan mazaunarta kije ki dauko da kanki” dariya tayi cike da nishadi,ita da hajjan sun saba hakan,suyi tsiya suyi dadi,duk yadda suka kai ga shaquwa da juna amma indai akan irin wannan batunne sun saba haurawa,ita sam dole saita sanyata sun jitu da juna,ita kuma tana jin wannan shine abu na qarshe a rayuwarta da bazai taba yiwuwa ba,komai nasu yasha banbam,tun kan ta mallaki hankalin kanta yadda ya kamata ta fahimci alqiblarsu tasha banbam,hakan ya haifar da duk wani abu dake gudana a yanzu.

 

 

Kanta tsaye ta nufi dakin gadon ya hajjan,harta kusa sai kuma ta sauya akalarta zuwa kitchen dinta,inda take jin qamshin abinci na fitowa.

 

 

A nutse ta tura qofar tana wara idanu don ganin wace a kitchen,kamar kullum gaji ce,’yar aikin hajjan qwaya daya tilo data jima da ita,takun shigowarta ya sanyata waiwaya tana duban qofa,cikin fara’a da washe baki ta qarasa waiwayowa gaba daya

“A’ah,ashe kina hanya inna wuro…..marhaba da uwar dakina” murmushi zahra ta saki,saboda gaje ta wajenta ce sosai,yadda ya hajja ke ji da ita haka itama gaje ke ji da ita

“Yauwa inna gaje,na sameku lafiya”

“Lafiya qalau alhmdlh inna wuro,ya makaranta?”

“Mun gode Allah” zahra ta fada tana neman wajen zama saman kanta,kusa da wasu kwanuka data gani a rufe,hannu ta miqe tana shirin budewa gami da cewa

“Me aka tanadar mana haka yaketa zabga qamshi”

“Gasunan bude ki gani,duka naki ne hajja tace a yi miki” a nutse ta dinga budewa tana dubawa,sosai taji dadi har ranta,hakan kuma ya bayyana zuwa saman fuskarta,batun yau ba ta shaida da soyayyar da kakar tata ke mata,bata san me yasa ta fita daban cikin jikokinta ba,ko don sunanta taci?,ko kuma don ita din ita daya ce ta zama marainiya a cikin tarin jikokin hajjan?,saita ture wannan tunanin ta sanya hannu ta soma daukan abinda ke cikin kwanon tana sawa a bakinta.

 

 

Duk sai data gama dandanawa sannan ta fara lashe yatsunta tana cewa

“Ashe dai ‘yar tsohuwar nan na sona haka,bari naje cikin gida na gaida mutane inna gaje na dawo” ta fada tana ficewa da dan sauri saurinta ba tare data saurari abinda inna gajen ke cewa ba.

 

 

Sai data fara biyawa ta dakin ya hajjan ta dauko wayartata hade da charger,ta shiga dakinta dake sassan ya hajjan ta jona chargy sannan ta fito.

 

 

 

*MAMUHGHEE* _UBAIDMALEEK_

 

*BILLYN ABDUL*

_MAKAUNIYAR QADDARA_

 

*HAFSAT RANO*_MABUDIN ZUCIYA_

 

*MISS XOXO*_DALAAL_

 

*HUGUMA*_ALƘIBLA_

 

 

*ZAKU IYA BIYAN NAKU KUDIN TA WANNAN HANYAR*

 

 

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

 

 

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

 

*_08085405215_*

 

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

 

0903 234 5899

23/10/2021, 08:35 – 👍🏻👍🏻: *KIJI TSORON ALLAH,KARKI TABA KAYAN DABA NAKI BANE,BA MALLAKARKI BANE*

 

02

 

 

 

 

Falon yanzu babu kowa duka sun yoye sai ya hajjan kawai,tana zaune tana gyara falle fallen littafin dala’ilu,da alama ta karantasu ne suka kuma hargitse mata take gyarawa,don ita din har tsufanta bai hanata bibiyar litattafan addini ba.

 

 

Ta baya ta rungumeta tana cewa

“Ashe dai har yanzu ana yi dani ‘yar tsohuwa mai ran qarfe,bari naje na dawo na kwashi gara,Allah dai ya jiqan tsohon mijinki” daga haka ta juya cikin sassarfa tana barin falon.

 

 

Wannan karonma da kallo ya hajjan ta bita,cikin ranta ta amsa addu’ar data yiwa mijinta kuma masoyinta,tana jin yarinyar cikin ranta sosai fiyr da sauran jikokinta,su biyu kacal suka samu irin wannan babban matsayin,duk da qoqarin boyewa da take da kuma nuna duka dai dai suke.

 

 

Tana yawan godiya ga Allah daya sanya qauna da zumunci mai qarfi tsakanin ahalinta,tun daga kan yaranta zuwa jikokinta,tsabar son su zamaTsintsiya madaurinki daya ya sanya tun mijinta na raye suka yanke zaman dukka yaransu maza tattare a waje daya,matanne basu da wannan ikon ko qarfin a kansu,hakan kuma yayi tasiri wajen sake maida zuri’ar tata tsintsiya madaurinki daya,duk da ance zaman tare zo mu zauna zo mu saba,hakanan baka rasa banbancin halaye da ra’ayi wanda kan kawo sabani lokaci zuwa lokaci,saidai a nata ahalin akwai qarancin hakan sosai,don bazai yiwu ace babu ba,kusan halayya ce tadan adam,kuma sunna ce ta zaman tare.

 

 

Duk da wannan babban abinda ke bata mamaki da daure mata kai shine rashin jituwar dake tsakanin zahran da yayanta,kusan abune daya dauko dogon tarihi ya kuma samo asali da tushe tun da dadewa,tun abun bai zama wani abun damuwa kallo ko dubayya ba har takai a yanzun yana damunta lokaci zuwa lokaci,saidai tana saka ran watarana komai zai zama tarihi,kamar akwai sauran quruciya ne jikin xahran.

 

 

Sashen yayan mahaifinta da suke kira da abba babba ta fara shiga,sashe ne mai kyau kamar yadda ainihin ginin gidan ya nuna,babban falo wanda ya cinye set din kujeru har guda biyu,dakuna a qasa kitchen da bandaki,sai dakunan matan gidan dake sama,duk da kowacce tana da guda daya a qasa.

 

 

Mommy ta tadda a falon ,wanda ke mazaunin amaryar abba babba tana cirewa yara da dawowarsu gidan kenan unifoarm,wanda dukkansu yaran gidan suna makaranta guda ne,akan daukosu tare a kuma kaisu tare,bisa jagorancin drivern gidan a wadatacciyar motar da aka ware musu don wannan hidimar.

 

 

Kanta ta daga tana amsa sallamarta sanda take cirewa yaronta safarshi,fuskarta fadade da fara’a tace

“Maraba da ‘yan boarding” qarasowa tayi tana murmushi,ta zauna hannun kujerar tana amsawa gami da yiwa mus’ab da ake cirewa safa tsiya

“Wai kai bakasan ka girma bane,saura kadan kayi shekara goma fa,amma har yanzu safa ake cire ma”

“Murmushi mommy ta saki

“Kema kya fada inna wuro,kullum sai an cire masa kamar yaron goye…” Dariya ta sakeyi tana kuma dan tsokanarsa kafin daga bisani ta juya tana gaida mommyn,fuska a sake take amsata,ta tambayi abba babba

“Abbanku ai kinsan ba zama,tun sassafe ya fita kasuwa”

“Mama fa?” (Uwar gidan mommy)

“Yau suna hidima ne,ita dinma tun dazu ta fice” jin haka yasa ta miqe tana zura hannu a aljihun rigarta,ta soma zaro alawa masu dan girma tana rabawa wadanda ta taras a falon,duk data girmesu amma ba wani girma ne me yawa can ba,shekarun data basun bazai gaza biyu zuwa uku ba,idan yayi yawa hudu

“Baki gajiya,keda kika dawo daga makaranta harda wata tsaraba” murmushi kawai ta yiwa mummyn tana ficewa.

 

 

Sashe na biyu ta shiga,sassan abba yusuf,wanda keda matan aure biyu shima da yara tara,amarya nada uku,uwargidan nada shida,shima dai kamar shigen ginin waccan sashen,komai cikin tsari,da alama kusan dabi’ar jama’ar gidan ce wato tsafta,su dinma faran faran suka gaisa ta wuce sashen abba abu wanda cikakken sunanshi shine abubakar,matarshi daya da yara bakwai,sai abban tsakiya shima matarshi daya,daga nan sai sashen mahaifinta.

 

 

Sashe ne dake da girma da qima a idanunta,yake kuma da dimbin tarihi cikin rayuwarta,sashen da a shekarun naya suka rayu kamar sauran sassa dake gidan,cikin walwala farinciki da qaunar juna,qarqashin inuwar adalin uba kuma mahaifi a wajenta,saidai ta farat daya mai rabawa ta raba mai raba soyayyar iyaye da ‘ya yansu wato mutuwa,a lokacin da suke tsaka da gudanar da rayuwarsu.

 

 

Mahaifinta uba ne da ya zama daya tamkar da dubu,wanda bashi yiwuwa ta manta soyayyarshi garesu,musamman ita din da take ‘yar fari a wajensa,ta kuma ci sunan mahaifiyarsa,saiya zamana soyayya da kulawar da yake bata ta dabance,har kullum mutuwarshi sabuwa ce a ranta,rana da lokacin basu taba bace mata ba daga idanunta.

 

 

A hankali tayi sallama cikin falon,qannenta dake xaune suna cin abincin rana suka amsa,cikin farinciki qauna irin ta ‘yan uwantaka suka miqe suna mata oyoyo,fuskarta washe da fara’a take amsa musu,wanda hayaniyarsu ta fito da mahaifiyarta dake kitchen.

 

 

Kyakkyawar mace mai kyan zubi da haiba,ma’abociyar tsafta nutsuwa da kyakkyawar dabi’a,wanda kyawun dabi’arta ya sanya koda bayan rasuwar mai gidanta dangin mijinta suka kasa rabuwa da ita,suka roqi alfarma taci gaba da xama dasu har zuwa sanda xata buqaci aure,su kuma zasu tsaya mata tamkar nata dangin.

 

 

Duk da cewa bata rasa wani gata ko kulawa daga nata dangin ba,amma hakan bai hanata amsar tayinsu ba,saboda tsantsar dattako irin na uwar mijinta,da yadda ta nuna mata qauna da kulawa tun haduwarsu har xuwa yau din,bugu da qari kuma,bata jin xata iya sake aure a sauran rayuwarta data rage,tunda ta rasa miji daya tamkar da dubu irin sa’id uban ‘ya’yanta.

 

 

A nutse ta qarasa daura da inda mahaifiyar tata ke zaune

“Ina wuni ummi”

“Lafiya qalau,ya makaranta ya kuka barosu”

“Lafiya lau ummi,wannan karon duka babu dadi,ni kadai aka bari a makaranta,yasira ta rigani dawowa” tana zare carbin hannunta ta amsa

“Eh ai jikin nata alhmdlh da sauqi,jiya na shiga na dubata” ajiyar zuciya tadan saki

“Tana raina ummi,gobe in sha Allahu nima zanje na dubata”

“Ya kamata kuwa,don dazu yaayan ma ya kirani yace an daukoki ko?”

“Eh su ya musty ne ma suka je a motar wancan mutumin” sosai ummin nata ta tsareta da idanu tana kallonta,sai a sannan ga gane tabargazar data tafka,saita dauke nata idanun tana son wayancewa

“Inna wuro?,waye wancan mutumin?,yayan naku?,ashe qara lalacewa kike?,duk fadan da nake miki bakiji kenan?” Marairaice mata tayi,don idan da sabo ta saba da fada daga wajen ummin indai a kanshi ne,abu na qarshe kuma data fi tsana kenan a rayuwarta

“Kiyi haquri ummi,mantawa nayi,bazan sake ba” kanta ta dauke kawai daga gareta,tasan ta fada ne kawai,amma wannan halayyar ta jima dason rabata da ita amma ta kasa,ta zame mata jiki,rabuwa da ita sai a hankali,bata tashi daga wajen ba sai data ji tace

“Allah ya kyauta,Allah ya rabaki da wannan halin”.

 

 

Dakinta dake sashen wanda ba kasafai ta fiya kwana a ciki ba ta wuce,tsaf yake kamar ko yaushe,duk da bata kwana ciki amma kullum saita gyarashi,’yar madaidaiciyat cupboard dinta ta bude,ta zabi kayan sawa adadin wanda takeso,ta debi kayan kwalliya mayafanta da sauran muhimman abubuwa don maidasu sassan hajja,saboda muddin ta dawo hutu tafi xama a can,bama ita kadai ba duka ‘yammatan gidan dakin dake sashen hajjan suke tarewa har sai ta koma.

 

 

Ita dinma tafison zaman can din,saboda tafi sakewa sosai fiye da sassansu,hajjan na barinta tayi yadda takeso koma bayan ummin nata dake da tsauri da kuma dokoki iri iri.

 

 

Kai tsaye ta koma sassan hajjan,duka sun fice da alama kowacce akwai abinda zatayi,hakan ya mata itama saboda wanka takesonyi ta kuma rama bashin baccin da batayi ba daren jiya a makaranta,don su kwana waqe waqe na murnar tafiya gida hutu,gabanin asuba koma kowa ya shiga sabgarsa taci gaba da hada kayansa da kuma bin layin wanka.

 

 

Sai data fara zuwa gun wayarta dake chargy,hopefully ta taba screen din ya kawo haske cikin zumudi,don ta tabbatar zata iske texs ko miscal na nuraddeen kamar yadda ya saba mata a kullum idan ta dawo hutu.

 

 

Saidai kuma ga tarin mamakinta babu kiran hakanan babu saqon nashi,sosai abun ya daure mata kai,amma saita bashi uzuri,ta shiga ta duba balance dinta.

 

 

Naira hamsin ce tayi ragowa a layin nata,ta tuna zahra takwararta ce ta mata transfer kyauta ana ya gobe xasu koma hutu,tunda tace ga wanda ya tura mata kudin ta raba musu 50/50 a ciki sai taji credit din bai burgeta ba,amma yanzun zai mata amfani,don haka kai tsaye ta shiga rubuto lambobin nuraddeen daka wanda ta jima da haddacesu ta danna kira,take sunan my happiness ya bayyana saman screen dinta,ta kalli sunan ta saki murmushi tana kuma sauraron yadda wayar ke ringing.

 

 

Dab da zata katse aka daga,sallama ya fara yi mata,saita sauke a jiyat zuciya cikin shagwaba tace

“Nayi fushi”

“Afuwa,kaina bisa wuyana,kina raina inata son na karki,damac ce ban samu ba”. Duk da uzuri ya nema amma sai taji banbarakwai,don wannan shine karon farko daya soma neman uzuri irin haka a wajenta,amma saita saki murmushi

“Nayi maka,amma fa lasam nayi kewarka da yawa”

“Nima haka princess,an dawo lafiya?”

“Lafiya qalau alhmdlh”

“Ya makarantar,ya mutan gidan?”

“Kowa lafiya lau” zai soma magana taji ana mata warning cewa kudinta sun kusa qarewa,daga bisani ta tambayeshi me yace

“Nace ne ina hajja da ummi”

“Duk lafiya na samesu…..” Ta kasa kunne taji yace xai shigo a yau din,saidai tuni kamfanin waya suka katse kiran saboda qarewar kudin wayar tata,saita aje wayar gefanta tana dan dubanta,tasan cewa babu jimawa xai biyo sawun kiran nata,don haka ta zauna daura da wayar tana dan gyaran kayanta tana dakon kiran.

 

 

Harta gama gyaran bataji shigowar kira ba,sai data miqe tana shirin shiga bandaki ta watsa ruwa taji sautin shigowar saqo,ta miqa hannu da hanzari tana dubawa,saqon daga nuradden dinne

“Zan kiraki” abinda ya qunsa kenan,saita maida wayar ta ajjiye ranta tana cewa

“Lallai yau wanne irin busy happiness ya shiga haka” ta wuce bandakin bayan ta daura towel din wanka.

 

 

Aqalla minti goma sha biyar ta shafe a bandakin sannan ta fito tana mita

“Haba,babu inda yakai gida dadi,me za’ayi da makarantar kwana,babu abinda yakai gida dadi wallahi,inda a school ne ina ka isa ka dade haka,da tuni an matsanta miki daki fito,mtseww…wallahi badan yaaya da kuma ummi da bazan koma ba” da wannan qananun mitocin mata ta qarasa gefan qatuwar kafitar dake dakin ta zauna,wanda daura da ita ‘yar drower ce dake jere da kayan shafe shafenta,zahra ba daga baya bace wajen son ado da kwalliya,hakanan idan ta fannin yawan sutura da kayan qyale qyalen rayuwa ne tana sahun gaba cikin ‘yammatan gidan,saboda ta kowanne fanni yi mata ake dalilin maraicinta,qannen mahaifiyarta mata da yayan mahaifiyar nata dake matuqar qaunarta,wanda dukkan abinda xaiwa yaransa to lallai fa saiya yiwa zahran,hakanan ‘yan uwan mahaifinta dake gidan,duk sanda wani xaima iyalinsa saiya hada da ita,ga hajja a gefe itama da ba’a barta a baya ba.

 

 

Sa’annan uwa uba wani irin farinjini da Allah ya yiwa zahran tun tana mitsitsiyarta,don mahaifanta ma sam basa yarda a karbi abun hannun kowa akan yarinyar,haka halittarta take,tun abun na baiwa mamanta mamaki harya koma bata tsoro,hakan ya sanya tun kan ta mallaki hankalinta ta tsaya kai da fata wajen mata addu’ar samun kariya da samun miji na gari,don ita kanta tasan Allah ya yiwa diyartata baiwar wani asirtaccen boyayyen kyau,tana tsoro n kada hakan ya zama wata sila da za’a shiga rayuwar diyartata a cutata mata babu dalili,ta sani cewa sautari baiwar kyau jarrabawa ce,qalilan ne kuma cikin mutane ke iya cinyeta,musamman mata.

 

A nutse ta kammala shiryawa cikin doguwar rigar atamfa cotton mai budadden dinki,ta gyara kanta da ribbom wanda da wahala kaga kitso a kanta,duk wanda ya santa yasan bata qaunar kitso tun yarinta har zuwa yanzu data girma,duk sanda xa’a mata kitso saita tarawa mai kitson jama’a saboda tsabagen kuka,daya daga cikin abinda ya sake sawa basa jituwa da yayanta kenan,yana ganin kamar an bata ta ne an sangarta ta.

 

 

Tana tsaka da fesa turarenta mai sanyin qamshi wanda ta saba ta soma jiyo sautinsa.

 

 

Sassanyar murya mai zaqi,amma cike da kaushi da kuma fada yake magana,da alama wani abun ya faru ne,baki ta tabe tana aje turaren nata,maimakon ta fito yadda tayi niyya da farko sai kawai ta fasa,ta koma gefan katifar ta zauna tana sauraren fadan nashi,duk da cewa bata iya fuskantar me yake fada.

 

 

Baki ta sake tabewa karo na biyu

“Ayi mutum sai shegen kaushin hali da fushi,Allah ya kyauta” ta fada tana jawo filo bayan tayi rub da ciki saman katifar,sannan ta janyo wayarta tana sake duba kira ko saqon nuraddeen,saidai har yanzun babu ko daya,saita maida ta aje tana ayyanawa wala’alla bai gama uzurinsa bane.

 

 

Shigowar hafsat dakin kamar wadda aka tunkudo ya sanyata miqewa ta xauna,fuskarta a hade da alamun kamar ma hawaye ta gama yi

“Yaya?” Zahra ta jefa mata tambayar tana gyara zamanta idanunta kan hafsan

“Yaa haidar mana……shikenan da zarar ya dawo mutum bashi da sauran sakewa,kome kayi baka masa dai dai ba,haba?” Koda bata tambaya ba tasan kwanan zancen,don halayyarshi ba baquwar halayya bace a wajensu,don haka baki ta tabe

“Hmmmm,ai ni shi yasa nake godewa Allah dasu abba basu dauko aqidar sai munyi karatu ba kafin aure,inda haka ne Allah kafin mubar gidan nan saiya sa mana hawan jini” dubanta hafsa tayi

“Ni kuma kinsan hakan baimun ba,nafison naci gaba da karatu kafin ayimin aure,inda xasu sauya shawara wallahi hakan yafimin,amma ya haidar kusan yafi kowa na’am da wannan tsarin tun xamanin su ya khairiyya” hararara zahra ta jefeta dashi tana cewa

“Bakinki ya sari danyan kashi,ni da kike gani na nan ba’a da candy qalilan ce inji ‘yan arabiyya,babu wani karatu da xan tsaya wahal da kaina inayi,me yafi aure dadi?,kaida masoyinka?,ka samu ‘yanci babu me takuraka?,tabdijan,ke ai saikita zama kici takarda da biron” ta fada tana komawa zuwa kwanciyarta ta daxun.

 

 

Dariya hafsa ta saki tana daka mata duka,tana sane ta sako wannan zancan,don duk cikinsu kowa ya san ra’ayin mahaifansu ya dace da ra’ayin zahran,kuma ita hakan yayi mata dai dai

“Allah ya shiryeki zahra”

“Amin….ai dan sunna bayaqi sunna ba ko”

“Wannan haka yake malamarmu”

“Kyaji dashi” ta amsa mata tana sake jawo wayarta ta fara buga game,jifa jifa suna hira,tana kuma dakon daina jin motsinsa a falon hajjan data samu ta fita taci wani abun kafin ta dawo ta kwanta tadan matse gajiya.

KIJI TSORON ALLAH,KARKI TABA KAYAN DABA NAKI BANE,BA KUMA MALLAKINKI BANE*

 

 

03

 

 

Kusan minti talatin kafin ta daina jin duriyarsa,zuwa sannan bacci ya soma fisgar hafsat,saita aje wayarta ta miqe a hankali tana gyara daurin dankwalin kanta,ta isa bakin qofar dakinta ta zura takalmanta sannan ta wuce kai tsaye zuwa falon.

 

 

Kyakkyawan matashin saurayin da a qalla bazai wuce shekara talatin bane zaune cikin falon,saman lallausan center carfet din dake shimfide tsakiyar kujerun,ya miqe dogayen qafafunsa ya kuma hardesu waje daya yana kadasu a hankali,kallon farko da zakayi masa zaka fahimci wani irin kwarjini shimfide saman fuskarsa,wanda ke cakude da rashin fara’a da kuma daurewar fuska,wanda ko a yanzun da yake zaune shi kadai cikin falon wayarshi qirar iphone 12 na tsakiyar tafukan hannayenshi dake saman cinyoyinsa yana amfani da ita fuskarshi a hade take,da alama gwanin iya tsare gida ne qwarai,gefansa kwanukan abinci ne a jere,bata sani ba ci zaiyi ko kuma baida niyyar ci ya ajesu ne kuma baxai magantu yace azo a dauke ba.

 

 

Kallo daya tayi masa ta tabe baki,duk da bata samu nasarar ganin fuskarsa ba sai sumarshi dake gyare,ita bamai yawa ba ba kuma saisaye ba,saidai tafi kama da saisayen irin sama saman nan,tayi wani spring kamar zubin indomie,baqa sidik tana sheqi,da alama ana bata kulawa yadda ya kamata,don ba qaramin qara masa kyau da kwarjini takeyi ba,ta kuma dace da kalar kwantacciyar skin dinshi da hausawa ke cewa wankan tarwada,ga duk wanda ya dubeta yasan ya samu cikakken hutu dajin dadi,duk da kalar aikinsa bawai na hutawa bane waje daya,saboda aikine na hidimtawa qasa,da bada kariya da tsaro wa dukiyar al’umma da rayukansu.

 

 

Saɗaf saɗaf take tafiya saboda bata da buqatar ya ganta,dab da zata gotashi ya daga kanshi,saida gabanta yayi mummunar faduwa,kallo daya tak ya mata ya maida kanshi ga wayarshi,kamar baisan Allah yayi wanzuwar wata halitta ba,tilas ta fasa qudurinta na wuceshi da tayi niyya,ta dawo da baya

“Ina yini yaa haidar” kamar bai jita ba,hakan ya bala’in ɓata ranta,ta tsani wannam halayyar tasa fiye da kowacce,ita idan zai shekara zaune a waje baiyi magana ba ba damuwarta bane,amma don me mutum zai gaidashi ya watsar.

 

 

Ganin bai amsa ba ya sanyata miqewa donta wuce abinta,sai a sannan ya magantu

“Lafiya…..zoki zubamin” ya fada ba tare da ɗago daga duban wayarshi ba yana mata nuni da fulasan gefansa.

 

 

Kamar tayi tsako don takaici amma tasan bata isa ba,wato saboda tsabar izza yana jiran wanda zai zuba mishi ne,akan ya zuba da kansa ya gwammaci yayita jira har sai mai zuba masan yazo,laifin bana kowa bane saina zahra,ita ta batashi,don tana fara zuba abincin ta tabbatar girkin ma nata ne,ita ta dafa mishi.

 

 

Tana wannan tunanin zucin naman data debo a serving spoon daya ya subuce ya koma cikin miyar,take ta fantsamo man dake saman miyar,ya kuma samu kyakkyawan masauki saman farar shirt din dake jikinsa.

 

 

Da sauri ya daga kai daga danna wayar da yakeyi,ya dubi jikinsa sannan ya maida idanunsa saman fuskarta,zallar bacin rai ta hanga qarara,ta soma motsa baki da niyyar yi masa bayani saidai ya rigata magantuwa

“U r very stupid….baki da hankali ne?….”

“Ashsha…..inna wuro garin ƙaƙa?” Muryar hajja ta ratso falon,duk rashin tsoronta amma sai da taji kamar anyi mata rahama,kafin ta bata amsa ta iso

“Tashi maza ki samo omo da dan toli fefa a goge mishi” tsaki ya saki kawai yana miqewa,ba tare da yace da kowa komai ba ya soma takawa yana nufar qofar fita

“Ka tsaya a goge maka mana zaki(haka takan kirashi dashi ita da wasu mutanen,sakamakon sunan mijinta da yaci,bata iya kiran sunanshi)”

“No,barshi kawai”

“Abincin fa?” Ta fada sanda yake gab da ficewa

“Ku amfaneshi”ya amsa a taqaice yana qarasa ficewa.

 

 

Bugu hajja ta kaiwa zahra wadda ke tsaye tana yiwa qeyarsa gwalo gamida murguɗe murguɗen rawa

“Ja’irah,hala kina sane ko?” Dariya ta saki tana zama gurbin daya tashi,wanda ke fidda qamshin turarensa ta soma sake bude kwanukan tana baiwa hajja amsa

“Inda ina sane ai da sai abun yafi haka…..arashi aka samu,kuma hakan yamin dai dai”

“Zahra….zahra….kinga ki fita daga idona akan yayanku,kamar ba jininku daya ba”

“To hajja ko kinfi sonsa yanzu a kaina ne?,babu inda nake sakewa fa sai nan,haka kawai sai nan dinma yazo ya zauna ya hanamu sakewa,idan na koma wajen ummi canma yana nan,da nayi wani abu itama ta hauni da fada itama,don ya girmemu kawai saiya damemu” daga haka ta jawo fulasan tahau zubin abinci Abinta tabar hajja da kallon ikon Allah”

 

 

“Allah ya shirya” hajjan tace tana sauke ajiyar zuciya kawai,bata amsa mata ba taci gaba da zurin abincinta.

 

 

Salma ce tayi sallama cikin falon tana tsaka da cin abincin,sanye da atamfa dinkin A shape,sai dan kwalinta data zarga a kanta,hannunta riqe da qaramar wayarta me keyboard itel,wanda akafi kira da rakani kashi,kusan dukka gidan zahra ce me waya torching,ita dinma sai da aka hau rimin gafiya kafin a samu lamuncewar oga kwata kwata haidar ya barta da wayar,a hakanma bisa goyon bayan hajja,saboda abban gwammaja ne ya kawo mata,ita kuma tace sam ba za’a watsa masa qasa a idanu ba,tunda wayar bawai wata babba bace can,sannan uwa uba an hanata walwala an dauketa an kaita makarantar kwana aiko ba’a hanata riqe waya ba a duk sanda tazo hutu,tunda hutun ai baya wuce wata guda kacal,uwa uba kuma ma rashin riqe wayar yafi riqeta yawa,hakan yasa dole aka barta da abarta.

 

 

“Lalalaaaa……lallai zahra…..wannan ba kwanukan da naga yaa xahra nata fadin tashin hadawa yaa haidar abinci bane?” Sai data kai lomar qarshe na hannunta sannan ta daga kai ta dubeta

“Sune mana….kema idan xakici bismillah,zoki zuba iya zubunki” kamar wadda ta danawa wuta a jiki salma ta janye gefe da sauri tana kada hannu gami da fidda ido

“Lalala,bada ni ba saa lallen karya,inason lafiyata wallahi,haka kawai ina lallaba jikina kisa amin shaidar da xanje kabari da ita,kedai da kika shirya tarar aradu daka”

“Ba zakuci bama,kema wanda kikaci shi kadaine rabonki,tunda kika hanashi ci kema baki ci,yarinya ta zauna ta bata lokacinta saboda yaro amma a qarshe kuta yiwa aikin,to baku isa ba,ko ruwan lipto yace ku dafa masa sai kunyi qorafi,kada ma ke inna wuro kiji labari” cewar hajja,tana kaiwa qarshe ta soma qwalawa gaje kira,zahra ta mele baki

“Ko iya haka ma alhmdlh” dai dai lokacin gaje ta qaraso,hajja ta sanyata ta debe kwanukan tana ci gaba da mita,xahra ta miqe tana kakkabe jikinta

“Daɗina dake hajja baki iya samun magana daya ba…..muje sister ki bani labarin daxu”

“Zakici ƙaniyarki,zaki dawo ki sameni,nasan da wanda zan hadaki” ta fuskanci sarai me take nufi,amma tasan ba iyawa zatayi ba,don idanma ta hadata dashin ƙarshe sai tafi kowa mita da jin ciwon hukuncin da za’a matan.

 

 

Saman carfet din dakin suka zauna,salma tadan dubi hafsat dake baccinta haiqan

“Shegiya kasa,bata da aiki sai bacci” ta fada tana zungurarta,idanu tadan bude kadan,ta gane salma

“Ki saurara min ‘yar baqincikin baccin mutum” daga haka ta cusa kanta qasan filo tana gyara kwanciyarta su kuma suka shiga hirarsu

“Wai kinsan meke faruwa kuwa?”

“A’ah saikin fada” inji zahra

“Sabon kamu fa nayi” sosai zahra ta maida kallonta ga salma

“Kamar yaya?,sabon kamu bayan sulaiman din?” Farr tayi da idanunta

“Wallahi,kuma a yadda nake jinsa a raina zan iya hada matsayinsa dana sulaiman” idanu dukka zahra ta fiddo waje

“Keee salma…..kiji tsoron Allah,sulaiman din?” Kai ta gyada kai tsaye itama tana dubanta

“Shi dinfa,meye abun naji tsoron Allah a ciki?,igiyar aurensa ce a kaina koko yaya?,don kawai na zabawa raina shi a matsayin wanda raina ya amince na nuna duk lokacin da aka buqaci na nuna wanda na tsayar?” Kai zahra ke kadawa kawai dama da hagu cikin nuna zallar jimami

“Gaskiya nidai bazan iya ba,haba amana ai bata ce haka ba”.

 

 

Dariya sosai salma ta saki har tana toshe baki kana daga bisani ta tsagaita tana duban zahra

“Amma inna wuro na yadda lallai boarding ta dakusar da duk wani wayo da basirar da muka sanki dashi,wai ce miki akayi su samarin yanzun tsoron Allahn sukeyi?,ko ce miki akayi idan don saurayin yanzu yana gaya miki da nuna miki daga ke babu wata…..idan bake ba sai rijiya,kece rayuwarsa da sauransu yana nufin hakanne da gaske har a badininsa?,bance miki fau fau ba’a samun wanda hakan bane…..amma sunyi qaranci qwarai,da yansu maqaryata ne,maha’inta ne,basu da *ALƘIBLA* qila kece ta bakwai kota goma a wajensu,hakan yasanya nima bazanyi saki na dafe ba,na laru dashi shi daya ina masa son gaskiya da dukkan zuciyata da gangar jikina ba…..na shafa rana guda naji wayam” ta qarasa maganar tana bugun cinyarta.

 

 

Shuru zahra tayi nadan wasu sakanni tana nazari a zuciyarta,sam maganar salma bata samu mazauni a zuciyarta ba,hasashene kawai irin nata da kuma son baiwa kai mafaka,banda haka ita shekararta nawa da nuraddeen bata taba ganin wani abu tattareshi dashi koda sau daya bane makamancin wanda salma ke hasashe?,a kullum soyayyarsu qara gaba take,kishinta yake kiyaye bacin ranta yake,don me zata yarda da zancan salma ‘yar tamore

“Nikam bazan iya wannan kwamacalar ba” zahran ta amsa mata bayan takai qarshen nazarinta tana tanqwashe qafafunta waje daya,qaramar dariya salma tayi

“Eh….kekam taki zuciyar na daɗe da sanin cewa daban take,kinayin soyayya ne dakkan yaqini da amannarki,wanda a yanzun samun hakan yayi qaranci daga wajen mazan har matan” kusan hirar da suka dinga yi kenan a tsakaninsu,wanda har ya kusa kaisu ga musu.

 

 

Saidai basu ja da yawa ba dakin ya soma cika da ‘yammata,hakan ya sauya akalar hira suka shiga hirar sabgogin da suka shafesu,kamar qawayensu na unguwar dana islamiyya wadanda aka kawowa kudi da wadanda aka sawa rana,jarrabawar qualifying da suke fuskantarta,candy da zasuyi nan gaba da kuma aurensu da sauran hirarraki da ba’a raba ‘yammata dasu.

 

 

Duk da wannan hirar da ake amma hankalinta nakan wayarta lokaci lokaci,tana tsumayin nuraddeen kowanne lokaci,amma saidai har suka tasamma watsewa saboda lokacin ɗora girkin dare yayi a kowanne sashe,kasancewar kowaccensu duk da akwai masu aiki ɗai ɗai a kowanne sashe amma ba’a barsu sun zauna sun ta’allaqa komai a kansu ba,babu nuradden ba duriyarsa,don haka ta jawo wayarta ta miqe da ita tana tunanin zuwa wajen yaa zahra ta tura mata updated watsapp,don nata yayi expair.

 

 

Ci gaba da hayaniyarsu ta hira suke har suka zo zasu gifta ta ma’ajiyar motocin gidan.

 

 

Dukkaninsu sun hangeshi,duk da cewa bayanshi kawai suka hango amma babu wanda bai ganeshi ba cikinsu,saboda haka kowacce taja bakinta ta saisatashi gami da rage sautin muryarta.

 

 

Sanye yake da wata farar riga ƙal me gajeran hannu,wanda hakan ya baiwa murɗaɗɗen dantsensa damar bayyana,sai dogon wando shima fari gamida wani farin booth dake qafarsa,daga inda kake wucewa kana iya jiyo qamshin lallausan turarensa da iska ke kwasowa tana bazashi ko ina,ba kayan dazun bane a jikinsa,da alamu ma wanka yaje ya sake ya sauyasu saboda miyar data batashi,waya yake amsawa,kallo daya zaka masa kasan cewa yes!,aikin da yake yayi matuqar dacewa dashi,ko shafawa kayi kasan cewa shi din SOJA NE.

 

 

ƙasa ƙasa zahra taja tsaki cikin ranta

“Da wannan kayan yafi kamata ma ace jikinsa ya ɓaci dazu naga ta qaryar gayu da ƙyanƙyami” ta qarashe maganar tana fitar da tsakinta a sarari dai dai sanda ta hangi ya musty na qarasawa inda yake tsayen bayan ya baro wajen me gadi wanda da alama wani saqo ya bashi.

 

 

Suna gab da rabuwa kowa ta shige sashensu ba tare da sun ankara ba sukaji muryar ya musty na nufosu yana fadin

“Yaa haidar na magana fa ‘yammata” dukkansu babu wadda cikinta bai murɗa mata ba,yusra da tafi kowa tsoro cikinsu cikin rawar murya tace

“Wa yake kira a cikinmu?”

“Dukanku” ya bata amsa yana qunshe dariyarsa,don basu ba,hatta su da suke maza ba kasafai kiran haidar ke musu daɗi ba.

 

 

Junansu suka kalla,yusra ta sake cewa cikin qas qas da murya don kada ya jisu

“Amma me kuma muka yi masa ya musty don Allah?”

“Idan kunzo kwaji” daga haka shima ya juya abinsa don kada yayi laifi.

 

 

“Kome zai mana ai bazai rabamu da numfashinmu ba ko?,kuzo muje” inji hafsat qanwarsa wadda suke uwa daya uba daya,zahra ko tabe baki tayi,duk da cewa ita dinma a tsorace take,haka suka nufeshi sum sum kamar waɗanda suka ɗauko gawa.

 

 

Gaba daya su bakwai din suka zube gabanshi,yayin dashi kuma ke tsaye abinsa yana latsa waya kamar baisan An haliccesu wajen ba.

 

 

Saida suka tsammaci ya manta dasu a wajen,sannan ya buda baki kamar wani saraki ya jefo musu tambaya yana ci gaba da latsa wayarsa

“Wace inna wuro a cikinku?” Tambayar duk saita zo musu wani banbarakwai,tunda sunsan dai duk wanda ya kwana ya tashi cikin gidan ya san me sunan,hakan yasa suka kasa amsashi suka hau kallon kallo.

About the author

Hausa_Novels

1 Comment

Leave a Comment