Littafan Hausa Novels

Alkama Bisa Dutse Hausa Novel Complete

Written by Hausa_Novels

Alkama Bisa Dutse Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

*ALKAMA* *BISA* *DUTSE*

 

*ANFA*

 

*14*

 

 

Kwance take ad’aki tana kuka ,saka makon mararta dake ciwo,gashin kanta dukya barbaje yasauka gefen fuskarta saura sun sauka abayanta ,kana ganinta zakasan kukan harda shagwab’a take yinshi , sanye take da T_shirt bak’a da red d’in skirt,Wacce tafito da haskenta da zallar kyan datake dashi Wanda Allah yamata, kana fan nta zakasa y’an matanci yabayyana ajikinta kasan cewarta Mai d’an girman jiki.

Da k’yar ta lallab’o tafito daga d’akin tafito falo dafe da mararta ,ganin ba kowa afalon tafita tayi hanyar b’angaren hajiya.

Rayuwan Kaddara Hausa Novel Complete

Tana shiga b’an garen hajiya a falo ta tadda hajiyan ,hajiya najin motsin mutum da sheshek’ar kuka abanya tajiyo akid’ime, jiyo tayi tana kallonta had’eda k’ank’ance idanuwa tace.

“Amma wallahi yarinyarnan anyi bak’ar almugira ,yanzu saboda mugunta dazama da bilki shine zakizo ki tsoratani saboda kowa yamatsu inkau yayi yadda yakeso agidan d’ana da jikana,to wallahi ta Allah Bata mutumba.

Cikin shagwab’a da buga k’afa Maya tace”Toni ba Banda lafiya ba,marana tunjiya yake ciwo ko bacci banyiba cikin dare.

“Toshine Dan Ni kin rainani bazaki tsaya gurin munafukar uwar taki kice Mata bakida lafiyaba Saida kikazo Nan kid’agamun hankali saikace ninace mujahidu yakawoki gidannan,Kinga kikiyayeni kitafi chan gurin ubannanki kicemai bakida lafiya ,tunda shiyaji yagani zai iya ciyadda k’attai agida, ai yananan saikiyi chan gurinshi tunda Bai fitaba…”

Tana cikin wannan fad’an nata dabataji Bata gani ,sai gani tayi anbud’e k’ofar falonta ,k’amshin turaren Tom ford da agurin mutum d’aya kawai tasanshi tajuya tana kallon k’ofar falonta.

sanye yake da red d’in polo da farin wando ,bayanshi SAFINA ce cikin doguwar riga y’ar Dubai had’e da mayafinta.

Sake da Baki hajiya tak’uramai ido tanaganin kamar amafarki ne bashibane.

“Kaine AL’MUSTAPHA Koko mafarki nakeyi?

murmushi yad’anyi kad’an dayatsaya saman labbanshi yak’araso kusa da ita yarungumeta, cikeda farin ciki tak’an k’ameshi itama kamar za’a k’wacemata shi.

“Maraba maraba da jikalle na ,shina baka kirani kafad’a mun zaka dawoba?

D’aya daga cikin kujerun yasamu yazauna ya lumshe idonshi Alamun agajiye yake batare da yaba hajiya amsaba,kusa dashi SAFINA tazauna tana gaida hajiya,harararta hajiya tayi ta amsa dakyar.

Kuka Maya tasa tana kallon k’afarta da jini yakebi Yana b’ata gurin datake tsaye.

Azabure hajiya tamik’e tana kallonta itama tasa kuka tana cewa.

“Wallahi yarinyarnan muguwace kirasa inda Zaki tsaya kib’ata da k’azantarki sai falona?”wannan wane irin jinine ,ke kenan daga yawo ba d’ankwali da rashin sa rigar nono ,gaki nono bakad’an ba kitamuna yawo cikin gida ga maza da wad’annan shegun kayannaki kamar Zaki tsallake wuta,nidai bantab’a ganin hakaba ,to wallahi ki tsaya karki matsa kib’atamun wani gurin barni inji da tiles d’ina dakika b’ata,Ina binta fito kikiramun bilki tazo ta gyaramun guri tunda ita akaba rik’onta baniba.

Ahankali AL’MUSTAPHA yabud’e idonshi ya saukeshi kan Maya dake kuka tana yarfe hannunta cike da shagwab’a,idonshi yad’auke dagakan fuskarta data duk’ar yad’aura akan k’inrjinta dake rawa saboda yarfe hannun datakeyi,dasauri yad’auke idonshi ya lumshe ya k’ara relaxing akan kujerar.

Kallonta SAFINA tayi cike da tsana saboda taga sanda AL’MUSTAPHA yajuya yad’an ma mayar kallon sakonni yakauda kanshi had’e da basarwa.

Hajiya data buga tagumi tana ganin binta tafito tace”yauwa binta fita kikiramun bilki yanzunnan tazo Ina kiranta.

Tunda binta ta fita SAFINA ke hararar Maya kamar zata daketa saboda jitake kamar takasheta ita daga ganin yarinyar batai mataba ,kallonta hajiya tayi ta tab’e Baki had’e dacewa.

“Kinsan Allah sai kinbiyani d’akina dakika b’ata ,duk kikatashi aure saina fad’ama mijinki zubar jini kikeyi gashi bakisa rigar nono ,nononki yazube abanza yak’aro Miki watamai d’agaggen nono.

 

Kallonta Maya tayi ashagwab’e tana turo Baki still tana yarfe hannu.

Hajiya zatayi magana bilki tashigo tai mamakin ganin AL’MUSTAPHA da matarshi Kuma da Alamun isowarshi kenan ,dama sunsan indai yadawo saiyafara shiga wurin tsohuwarnan kafin yaje b’an garen kowa harna iyayanshi ,tana ganin yadda jini Kebin k’afar Maya tahau salati”shikenan Allah nagode maka, tunkafin muje asibiti acire cikinnan gashi zai fita dakanshi ,kallonta hajiya tayi “bangane ciki ba ?a Ina tasamo ciki wazaimata ciki?cewar hajiya data mik’e tsaye tana kallon mayar dake kuka tana yarfe hannu da girgiza Kai.

“Ai hajiya idan suka tafi makaranta insun tashi Bata dawowa da wuri ,sunce tafiyarta take gun wani saurayinta sai chan yamma sai tadawo,wallahi hajiya yarinyarnan har dukanta nayi Amma batajin magana ,abunda yasa bantab’a fad’ama kowaba cewa za’ai sharri kakema d’a tunda bakai ka haifeshiba.

Kallon bilki kawai binta keyi idonta nakawo ruwa Dan tasan sharri kawai bilki kema Maya.

“Aiko wallahi yau sainasa anzaneki ,bilki kiramun Tahir na lallasamun ita,agidannan za’ai ciki daga taimako Zaki b’ata Mana y’ay’a.

Ai bilki najin haka takira Tahir awaya dan tabbas tasan Yana nan Bai fita aikiba .

Sunanan tsai tsaye sai AL’MUSTAPHA da SAFINA ne kawai azaune Tahir yashigo .

Yana shigowa hajiya Bata bashi damar gaisuwaba tace “yarinyarnan attahiru zaka zanemun seta suma ,sai tafad’amana agidan ubanwa tayo ciki ,karwanda yakira SHEIK saita daku tafad’i gaskiya.

Tahir najin ance ciki tayi gakuma jini dake zuba Nan yagasgata maganar su hajiyan ,bulalar Cable yajawo yayo kanta ,dagudu tayi kan AL’MUSTAPHA da mik’ewarshi kenan zai shiga d’akin hajiyar yahuta.

rungumar data mishi abazata yasa itadashi suka zube akan kujerar daya mik’e ,k’irjinta daba bra Yana sauka kan k’irjinshi ,k’an k’ameshi tayi dak’arfi tana k’arasa wani kuka Mai bantausayi ,sai falon yad’auki shiru kamar anyi mutuwa sai kukanta kawai dake tashi.

Bulala Tahir yad’aga zai rik’ota ya zabga Mata , AL’MUSTAPHA yamishi wani mugun kallon dayasashi komawa baya.

[06/03, 7:40 am] +234 803 496 8241: *ALKAMA* *BISA* *BUTSE*

 

*ANFA*

 

*15*

 

 

Kallon fuskarta yayi datayi facha facha da hawaye ,Yana mamaki yaza’ai y’ar yarinyarnan tayi ciki metasani ,jin shiru yasa Maya ta d’ago Kai had’e da bud’e lumsassun ida nuwanta dasuka d’an kumbura saboda kuka.

Tana bud’ewa direct suka sauka cikin nashi idon,d’an lumshe idonshi yayi yazameta ahankali zai mik’e ,Maya jin zai ajiyeta yatashi ta tab’e fuska zatasa mishi kuka, ganin zatai kuka ,ya girgiza Mata Kai had’e da d’aure fuska ya maidata kan kujera ya mik’e,kallonshi hajiya tayi datayi mutuwar tsaye tana mamakin wannan makirar y’a ,tarasa Wanda zata b’atama Kaya sai d’an jikallenta ,wani k’ololo ne ya tsayama hajiya.

Kallonsu itama hajiya bilki takeyi zuciyar ta na tafasa narashin dukan daba’ayima mayaba ,itako SAFINA kawai yadda zatayi da rayuwar Maya tafara tunani ,yaza’ai saboda bak’in karuwanci tarasa Wanda zata runguma sai AL’MUSTAPHA ,har jininta na b’ata mishi wando,ita tunda take ko kallar jinin period d’inta be tab’a ganiba , wallahi Dole tatashi tsaye tasan yadda zatai da yarinyar Nan.

AL’MUSTAPHA Yana mik’e wa Saida yafara hawa stairs d’in batare da yajuyo ba cikin sanyayyar muryarshi dake cike da natsuwa yace”kar asake atab’ata hajiya ,akaita asibiti kuma,Yana kaiwanan yashiga d’akinshi dake kusa Dana hajiyar.

 

Kallon Tahir hajiya tayi dake rik’e da bulalar Cable a hannunshi tace.

“Wallah attahiru bansan Kai mugu bane sai yau,Kai yanzu dan kacika me bak’in zalinci yarinyarnan zaka duka da wannan zabgegiyar bulalar sai kace tayi kisan Kai ,insu nabila ne zaka barine atab’asu?almugirin banza Wanda yasha nonon y’an kindimashin.

Fuska yad’aure Yana harararta yace bake kikace azaneta ba ,inda su nabilarne zasuyi abunda tayine ,bakiji cewa akayi yawonta take tafiyaba….?

“Ka harari bilki da k’yamushasshan kakanka uban bilki,wallahi inda AL’MUSTAPHA yafiku kenan bama had’i narantse,shifa ko k’annan ubanshi basukaishi hankaliba da hangen nesa ,dabadan wani abubama danace har mujahidu,Amma dai Bari inyi shiru tunda shiya haifeshi, shima baxaiso inzagi ubanshiba ,shiyasa Sam bana zagin halimatu agaban AL’MUSTAPHA saboda nasan bazaiji dad’iba ,Dan duk abunda zai b’ata ran AL’MUSTAPHA banasan shi ahto.

Cike da b’acinrai hajiya bilki tafita fuuuuu idonta yayi ja saboda haushin hajiya da takaicin AL’MUSTAPHA.

Tana fita hajiya ta harari inda tabi had’e dacewa ,mummunar banza kawai Mai bak’in Hali.

“Wuce kakai y’ar mutane asibiti yanzu kafin ranka yab’aci ,inko kamusamun wallahi uwarkace zatabar gidannan.

“Binta kamata ki taimaka Mata ta gyara jikinta yakaita asibitin.

Daga haka hajiya tafita tayi b’angaren hajiya babba.

Tana shiga taga hajiya halima zata fita,hajiya tace Ina Zaki halima dawannan ranar ,rana Mana tunda shad’aya tayi ,aikyabari sukusa gama na rana tunda dai yanzu ancinye na safe,Kinga bama wannanba ,zuwanai infad’a Miki AL’MUSTAPHA yadawo Yana b’angarena yakwanta yad’an huta,nafita hak’k’inkine nafad’a Miki amatsayinki na wacce ta haifeshi .

Murmushi tayi tace”haba hajiya aibakomai ,basai kinfad’amunba AL’MUSTAPHA ai nakine.

“Wallahi shiyasa halimatu duk kinfisu hankali gaki y’ar masu ku’di , shiyasa fa zakiga masu kud’i akwai hankali mutuncinsuma dabanne wallahi,murmushi hajiya babba tayi tana kallon hajiyar.

“Yanzu dai matar AL’MUSTAPHA tare suka dawo bance ki sakar Mata fuskaba ,duk had’u zamuyi muja jikinmu daga gurin y’ar banzar harse tayi ciki ta haihu,bantab’a ganin d’an me kud’in dabaida hankaliba se safino,bazai yiwu taita wani binshi kamar jilaba kullum tana nahik’e dashi tak’i yin ciki.

“Hajiya to kikasani ko laifinshine Bai tashi haihuwar ba.

“Kedallah rufemun Baki ta Ina , AL’MUSTAPHA dakeda tsinannan hankali ta’ina zeyi wannan wautar ,Baki ganin idansu maryama yaransu sukazo yayita nannan dasu ,suma gashegen mak’alemai dasuke kamar shiya haifeshi yayita asarar kud’inshi,baridai ya haifi nashi wallahi kowa rik’e nashi zaiyi baruwana dawani zumunci, zumunci me bamai ba d’an bawan Allah ko biyar to bazai yiwuba ,inzaki wuce kifara biyawa b’angaren mujahidu kikiramun shi idan AL’MUSTAPHA ya huta za ayita ta k’are.

[06/03, 7:40 am] +234 803 496 8241: *ALKAMA* *BISA* *DUTSE*

 

*ANFA*

 

*16*

 

FOR ADVERTISEMENT CONTACT ANFA VIA THIS NUMBER 09036676645

 

Hajiya bilki tana fita direct sashen anty amarya tanufa ,azaune ta taddata da tana kallon tashar Bollywood.

Dasauri anty amarya tajuyo taga hajiya bilki agabanta tana huci.

“Meya faru hajiya?

“Kina jina da wannan tsohuwar ,attahiru tana zaman zamanshi tace akirashi yazo yazane kafirar yarinyar chan ,Amma saboda ganin shegen miskilin yaronnan shikenan tafara xagin attahiru ,dame AL’MUSTAPHA yafi sauran yaran gidannan ,Amma taita nuna banbanci atsakaninsu Dan kawai yafisu arzik’i shima waye baisan kud’in sata bane,Dan bazai yiwu ace nemanshi bane yabashi ,ai harda kud’in ubansu yake had’awa Kuma duk sunada hak’k’i aciki ,to wallahi nagaji zansami SHEIK infad’a mishi inzai d’au mataki ya d’auka inko ba hakaba wallahi sai mu d’auka da kanmu.

 

“AL’MUSTAPHAN yadawone?yaushe yadawo har akai wannnan bdirin bansaniba,cewar anty amarya tana mik’ewa daga zaunen datake ceke da tashin hankalin dayawanzu afuskarta.

“Ina fatandai bashi kad’ai yazoba?Allah yasa da y’ar arzik’in Nan yataho kinsan Saida ita komai zai tafi yadda mukeso,tunda kinsan hajiya ba santa takeba dama damama uwar AL’MUSTAPHAN.

“Da ita yazo kinsan itama tasan hannunta bazata zauna yataho shikad’ai ba Dan batasan wace tsiyar tsohuwarnan zata k’ullah mataba.

wayar hajiya bilkice ta d’auki kukan neman agaji sai tace.

Amarya Bari zamu k’arasa magana domin neman mafita.

“To badamuwa akwai dama maganar danikeso muyi koda zuwa anjimane ko gebe zan shigo b’an garenki mutattauna akai.

“To sai kinshigo d’in, daga haka tajuya tafita tai sashenta.

 

Tunda suka d’auki hanyar asibiti,Tahir baicewa Maya komaiba sai lokaci lokaci da yake juyowa yakalleta sakamakon kukan shagwab’ar da takeyi,kawai yadda yarinyar keda kyau da shagwab’a shike matuk’ar birgeshi, yarinyar so take away ,gata d’anya shakaf shidai tunda yake neman

Mata Bai tab’a ganin wacce tamaiba haryadawo Nigeria yaganta a wurin mom d’inshi, everything about her is very attractive.

Haka yayita kallonta tausayinta nad’an ratsa jinin jikinshi kamar yasaceta haka yakeji, kallonta yayi yace”can u tell me about your self?”

Kallonshi tayi ta turo Baki cike da shagwab’ar datasabayi wacce ke matuk’ar birgeshi batareda ita ta luraba Sam, Baki ta turo tace.

“There’s nothing special about me”yeah just want to know anything about you , anything.

Kuka tasamishi ,dasauri yakalleta yace”oh sorry maganar danamiki ne bakiso ?Yi hakuri bazan sakeba I mean no harm.

Cikin kukan datakeyi tace “nibashi bane banida lafiya yanzu bazan iya maganaba innaji sauk’i zan fad’amaka.

“Toshikenan badamuwa ,haryabud’e Baki zai k’ara tambayarta akan abunda akacemishi na fitan datakeyi daga school sai yafasa ganin tana cikin halin ciwo ,dakuma maganar cikin da akacemai shine yafita ajikinta.

Shiru yayi yafasa yimata maganar har suka Isa asibiti likita yadubata yace musu menstrual pain ne kawai bawani abuba ,allura zai Mata tace bataso ita abata magani,haka doctor d’in yarubuta magani yaba Tahir d’in , pharmacy suka shiga yasai mata maganin sukai gida.

Suna shigowa ta nufi b’an garen hajiya da sallama ciki ciki tashigo palon ta tadda hajiya da SAFINA a palon suna zaune bamaima wani magana ,kallonta hajiya tayi cike da k’yan k’yami tace.

“Wai miye ne sai kidinga zuwa kina cutata bayan k’azantar dakika gama zubarmun apalo Dan tsabar mugunta irin naki,me akace a asibitin?”

“Cewa akayi ciwon al’ada nefa hajiya.

“Aidama nasan bilki makirace wallahi ,salan atsaneki shine tamiki sharrin kinyi ciki,toke yanzu a inama kikasan ciki Ina kikeda Wanda zaimiki inba achan tab’ararrun y’ay’annan nataba zasu k’urmusheki ad’aki,yoo inma cikin kikayi aigwamna ke kina haihuwar munsheda Dan wannan jini dakika zubar da alamu ba wani jinkiri Muna Miki aure sai y’an dugwi dugwi ,baci zakiyi kiyita cika ma mijinki tangaran Masan shi ba ,ko kiyita kafid’irin banza bakomai acikinki sai luta lutan Kashi,tafad’i had’eda bankama SAFINA harara ,wacce tunda hajiya tafara magana tayi shiru ta d’uk’ar Dan tasan ita hajiya kema wannan habaicin ,Kuma tana tankawa zata tado AL’MUSTAPHA dake bacci asama tace tazageta har marintama takusayi shiyasa tayi shiru takama bakinta.

“Zo kizauna binta ta kawo Miki abinci badan halinkibai,kidena tsayuwarmun aka ,Kar iskanuna sutashi suyi biji biji da dukkan ku y’an falonnan Dan ban ceke da iskanci.

Dariya Maya tasa harda dafe ciki tana kallon hajiya ,cikin dariya tace.

“Narantse hajiya aljanuna sunfi naki k’arfi,nakifa tsofaffine irinki ,keda d’auka d’aya za’amiki koda aljanunki suntashi awujijji gaki ,kumafa hajiya in aka d’agaki sama kankine zai kalli k’asa k’afafunki asama.

K’an k’ance ido hajiya tayi tana kallon mayada haryanzu dariya takeyi.

“Kinci uban daya kawoki gidannan ,Ina mujahidu yazo yamaidaki inda yasamoki dama y’ar daba ce ke bamu saniba toh inh..”

Maganar dazatayi ne ta mak’ale sakamakon SHEIK dasukayi sallama shida sani da husaini.

Kuka hajiya tasa tace”dama nemanka nake mujahidu tun d’azu na aika halimatu takiramun Kai Ashe Bata kirakaba dama aljanar yarinya ka samo y’ardaba bamusani ba,to tunda Allah yayi shigowarku to kowa ya zauna anan Kar Wanda yafita atsaya har AL’MUSTAPHA yatashi ayi magana.

About the author

Hausa_Novels

1 Comment

Leave a Comment