Littafan Hausa Novels

Al-amarin Zuci Hausa Novel Complete

yadda ake tsara budurwa a waya
Written by Hausa_Novels

Al-amarin Zuci Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

AL- AMARIN ZUCI 1

.

Na Bilky Giro 1

.

Alhj hassan,Alhj Hussain,Alhj isma’il ‘yaya ne ga Alhj usman mai nera, matar sa daya tak Hajiya Zeenatu ita ce uwar ‘ya’yansa. Sun kasance suna zama ne a cikin garin zamfara. Wannan family Kansu a hade yake, hakan ne ma yasa suke zama a gida daya sai dai kowa da nashi part Saboda gidan babban gida ne sosai , iya haduwa gidan yahadu, kasancewar Alhj usman mai nera hamshakin mai kudi ne sosai gashi ya kasance shi mutum ne mai son jama’a da taimakon talakawa. Haka ma duk ‘ya’yansa ba bare a ciki, domin ko wannesu Allah ya hore masa dukiya,dukiya kuwa abinda ake kira dukiya domin duk wanda yaga family din yasan dala ta zauna ba sai an gaya masa ba. Alhj Hassan shi ne babba matarsa Hjy Fatima ‘ya’yansa biyu maza faruk da Hafiz.

 

Dangantakar Zuci Hausa Novel Complete

Alhj husain shi ma matar sa daya Hjy zainab, sai dai har yanzu Allah bai basu Haifuwa ba. Alhj isma’l matansa biyu Hjy saratu da Hjy khadija ‘ya’yansa hudu duk maza,Hashim,yusuf,’ya’ya ga HjySaratu. Salim,Ali ‘ya’yan Hjy Khadija. Zaman da suke zama ne mai hade da hadin kai da kwanciyar hankali ba’a cika jin kansu ba.

.

faruk shi ne mai dan girma a cikin ‘yayan,akalla yanzu yana shekara 9, yana primary 5 ne a yanxu. Amma idan yana fitar da lafuzzan turanci,kamar a secondry yake,gashi kyakkyawa fari tas dashi ga natsuwa da hankali,shiga rai shi yasa a familyn duk anfi ji da shi. Faruk ne zaune yana jiran fitowar momy (zainab )ummanshi ce ta aiko shi da dan wake yakawo mata. Yauwa dana, kace mata na gode,ya mika mata kulan ya fita,tayi zaune domin taci, sai dai yajin yau ba yawa, kiranta a waya tayi maman faruk ya akayi yau yajin ba yawa…..naga alamar so kike ki cutar muna da baby shiya sa na fara rage yajin,ko dan kinga mijin baya nan ne…ai bai ko san da cikin nan ba….ke haba meyasa,kinsan indiya yaje,idan nagaya masa bazai ma bari yayi abinda yaje yi ba sabida tsananin murna,kinsan mun shekara goma da aure ba haifuwa,haka ne fah Allah ya bada masu albarka,amin,amin nagode.

.

Yau ne Alhj Hussain (Daddy)zai dawo daga indiya,Momy sai shirshiryen tarbonsa ta ke,ta kammala abinci ta shirya tsaf tayi kyau sosai tana sanye da wani blue din material mai ratsin fulawa pink jiran isowar sa kawai take,da yake yace mata karfe 1:00pm zasu sauko gashi yanxu daya saura, tadan kishingida Kafin ya iso. A cikin barcinta da bai riga yayi nisa ba taji sallamar sa,da saurin ta tashi ta rungume shi,tamai sannu da zuwa,sai kallon ta yake yanda ta kara mishi kyau….yadai kallon fa, kinga yadda kika kara kyau,haske,cika, ko ni dana je indiya albarka…um um fah,Allah kuwa,kunnensa ya tara a bakin ta, gaya min meye sirrin,ni dai ba wani sirrin muje kaci abinci akwai lbr mai dadin ji,da gaske ?eh. Ya gama cin abinci yayi wanka suna kwance suna firar ya bayan rabuwa…yauwa baki fada min lbrn ba,to rufe idonka na gayama, tooo….,wannan wane irin lbr ne haka da sai na rufe idona, kai dai nace ma ka rufe,to na rufe, Allah ya karbi addu’ar mu da muka dade munayi domin yanxu ina dauke da juna biyu …..da gaske!! Allah kuwa,tana magana ne a cikin jin kunya,rugumar ta yayi yana mata kiss ta ko ina,yayi sujjada yana mai cewa “Allah na gode ma da kasa zan ga kwai na a dunya,Allah ka bamu masu yawa masu albarka, kuma kasa muna da yawancin rai.

.

Amin mjina…..bari naje na gayama family wannàn abin farinciki….ai kowa ya sani,ya akayi su ka sani, domin na san ki da kunya baza ki iya fada ba ,zazzabi ne mai tsanani nayi kamar bazan yi rai ba,sai da muka je asibiti,bayan an dubani suka ce ina dauke da juna biyu,baka ga yanda family ke murna ba hardai Hajiya da Alhaji….to ni meyasa ba’a gayamin ba sai yanxu? Saboda ina so ne na baka surprise,zaka fi farin ciki, kuma nasan idan na gayama baza ka bari ka, karasa abinda kaje yi….Allah kuwa da ranar zan dawo ba shiri. Haka rawu taci gaba domin yanzu momy haifuwa yau ko gobe. Faruk ne da sallamar sa tare dan rissinawa ya gai da momy,ta amsa sallamar tare da amsa gausuwar.

.

Halan dai anzo ayi magana ne da kanwar?eh mommy. Da yake tun lokacin da cikin mommy ya fara girma kusan kullum sai ya zo ,wai magana su ke yi da kanwarshi ta cikin cikin,ni Billy giro abin har mamaki ya ke bani. ya naga kamar ranka a bace faruk,wasu ne suka bata min rai a school wai baza ki haifa min kanwa ba sai dai Kane,ni kuma ai nasan Allah shi ne maiyi ……kuma a kullum nayi sallah sai na roki Allah ya bani kanwa…to kasan da haka kake bata ranka a banza faruk, ni ma kawai na tsinci kai na ne da ance kane zaki haifa min sai inji raina ya baci tunda kannaina duka maza ne ina so na sami kanwa…….haka ma wasu na can na neman da namji,basu samu ba….to Allah dai ya ba ka kanwa amin mommy. Hanun sa ya dora a cikin momy,yana mai cewa. “Kanwa ta wai sai yaushe xaki fito a daina mun gori,mu rika yawo tare’yan ajinmu su dai na minkurin kanwa,nima na rama…hmm kai dai kullum baka gajiya kana magana da abinda bai ko xo duniya ba…. lah kinga umma tana motsi …duk abin nan da akeyi a idon daddy ne sai dai ba wanda ya ganshi,murmushi kawai ya keyi,ya jingina a bakin kofar. Umma ce ta fara hango shi tsaye yana kallon su cike da sha’awa….a’a Alhj kai ne a tsaye sai faman kallon mu kake nida dana….danki mai kanwa ..ai inaganin idan baki haifi ‘ya mace ba,bansan ya faruk zai yi ba. Allah dai ya taimaka ki haifo macen,amin ya Allah.

.

Amma akwai ki da abin dariya mimi,kinga yadda kika Fuske…ya baxan fuske ba kina min zance marar dadin ji, wanda ko a mafarki bana so haka ta faru…..da wasa nake miki fah,ya zanyi wanann tunanin nace yayan ki bazai aure ki ba, wannan soyayya haka…ni dai zancen ya isa haka,ko abin motsa baki ban kawo miki ba,duk kin bi kin birkita min lissafi,afwan cewar Zainab. Momy ce zaune a falo Mimi kwance a saman kafafunta tana game a waya,nikuwa Mimi yaushe zaku fara waec da neco?a wannan watan mommy…amma baki da abinyi sai danne,dannen waya,ai Mommy duk dare kafin nayi barci sai nayi karatu,haba mommy na, ai kinsan bana wasa da karatu,haka kam amma ki kara dagewa kinji,inshaAllah mommy. Abba!wai wa zai kaini school yau,kasan fa jarabawa ce damu bana so nayi latti,yayanki zai kaiki,wanne daga cikinsu?Hafiz kuma a kullum shi xai rika kaiki..Abba why?shi ya zabi haka,hmm lai ma yaya Hafiz yayi hakanne don yana tunanin zan soshi,to meye abin yi tadan yi shiru kadan kafin ta samo amsa…yes hakan zanyi yayi dai dai. …Tana magana ne a cikin zuciya. Kome zata yi oho,muje zuwa….

.

Tafe suke ba mai magana a cikinsu. Hafiz ya katse shirun,yadai Mimi shirun fah,ina dan revising ne shi ne kaji shirun yayi yawa…ok yayi Allah ya taimaka,ameen yaya shima murmushi yayi yaci gaba da driving dinsu. Haka suke kullum basu cika wani surutu ba soboda revising dinda take yi,kuma tayi hakanne domin kar ya takura ta,amma shi abun yana dan damunsa sai dai yabar abun ne a zuciyar batare da ta fahimci hakan ba. Kamar kullum yau ma zai kai ta school yake tambayar ta. Mimi meyasa kullum bita kike kamar wacce bata karantu ba ,bayan nasan ba haka kike ba, da kinyi karatu zaki fahimta, basai kin sake ba,amma yanxu kullum sai kinyi bita…uhm ..eh.. am ina so ne in kara fahimta. Yanayin maganar ta ya gane cewa da gangan take bita kullum,kaddai ace yarinyar nan bata sona shiyasa take min haka..a’a dama haka take bata cika son damuwa ba idan za’a je school, dayan bangaren zuciyarsa ne ke bashi amsa. Zee!!..ya akayi,mimi mutumen ki ya fara gano ni…kamar ya ya Mimi? kinsan nace miki kullum revising nake a mota har mu iso,to ya fahimci yi ne kawai nake don kar ya ta kurani,gaya miki yayi?

.

A’a yanayin fuskar sa ne ya bani amsa…nikuwa Mimi me zai hana ki fito fili ki fada mashi cewa faruk ke sonki,na tabbata idan yaji zai hakura. Kinsan bai riga da yace yana sona ba….amma ai duk wanda yaga yanda yake baki kulawa yasan akwai so mai tsanani,gsky ni kaina tausayi yake bani ranar da zai furta min ince a’a,ina jin nauyi sosai a matsayin sa na yayana. Kinga kawata ga shawara,yaushe ne yaya faruk zai dawo?kesan daga shekara sai shekara yake kawo muna ziyara saboda yanayin aikinsa,inaga yayi wata 7 da kawo muna last ziyara,kenan saura wata biyar kafin yazo….tab amma da saura dai kika ce,kuma kinsan kafin wannan lokaci zai iya furta miki, abinda nayi tunani ki matsa ma yayanki akan yadawo kina son ganinsa,na tabbata a yanda yake sonki zai dawo..zee kinsan ban cika son matsa mishi ba…kinkuwa san dalilin haka,sai kin fada. Ba makawa yanayin yadda kuke gudanar da soyayyar ku da yaya faruk, idan Hafiz ya gani zai fahimci Ku masoya ne, na gaske,kwarai kuwa zee shawarar tayi,kinga abu yazo cikin sauki.

.

Allah ya biyaki zainab,shiyasa nake sonki…Ameen Mimi. Kwance take a daki ta na tunanin yadda zata bullowa yayanta faruk ba tare da ta, takura mishi ba….karar wayar ta ya katse mata tunani koda ta duba faruk ne wani sassayyan ajiyar zuciya tayi tare da murmushi kamar yana ganin ta. Hello yayana,hy my mimi,ya exam, Alhamdulillah,ki na dai karatu sosai ko? eh yaya sosai. Sai da suka dan taba fira take cewa “yaya ni gsky nayi missing dinka da yawa idan kai bakayi missing dina ba…haba! Mimi Allah nima nayi missing dinki, ai nakusa na dawo…to amma yaya har wata 5 fa,haka ne Mimi yau da gobe cikin ikon Allah sai kiga har lokaci yayi. Amma kiyi hkr kinji Minima to yayi yaya Allah ya kaimu lokacin ameen my Mimi shiyasa nake sonki kina saurin fahimta. Haka suka cigaba da firar su ta masoya kamar ba zasu aje waya ba. Mimice da Zainab a karkashin wata bishiya suna jiran azo a dauke su daga makaranta.

.

Hafiz ne tafe a cikin mota ya iso inda suke yayi fakin,mimice ta tashi tana cewa “yaya sannu da zuwa,yauwa…barka da wuni yauwa sannu zainab. Yaya faroooook!!!! da gudu ta tafi ta fada jikinsa shima haka rungumeta yayi,yana cewa my Mimi!!! Sai faman sauke numfashi take tare da janye jikinta. Yaya da wani yace min ga ka can da sai nayi gardama kafin na juyo,sai Allah yasa nice na fara hango ka, Mimi kenan wannan gudu haka baki ji ciwo ba dai ko?a’a yayana…ai ko naji ciwo bazai dame ni ba tunda gaka a gabana…..su Hafiz ne da Zainab suka karaso,Hafiz ya mika ma faruk hannu suka gaisa. Ita ko Zainab sai cewa takeyi ai ke har kin bamu tsoro wlh…..yaya faruk sannu da zuwa yauwa Zainab ya exam mun gode Allah,to Allah ya bada sa’a, ameen. Hafiz ashe har yanxu mimi bata san ta girma ba…Allah na sani yaya .. to meyasa kikayi gudu haka idan kika jiwa kanki ciwo fa …ai kaine yaya kamin bazata,tana magana ne a cikin shagwaba, shi ko faruk sai kallonta yake yanayin yanda take shagwabar ta,yana birge shi.

.

Yaya Hafiz dama kasan yaya ya dawo?a’a nima yanzu na ganshi…Mimi kenan kamar yadda kika ganni bazata shima haka ya ganni. Amma yaya shine kaki karasowa kayi fakin nesa damu, to ai kin hango ni duk da nesa nake daku….yaya…

.Mimi yakoyi yanayin yanda tayi magana ne, a shagwabe ,su dukansu sai da abin yabasu dariya, Mimi sai faman kallon sa take yayi kyau,ya kara haske dagani yana cikin koshin lapiya. Meye tambayar ki mimina?yaya meya sa kadawo tun lokacin dawo war ka bai yiba?kece Mimi…..ni kuma…daga kansa yayi alamar eh,to ai kace min nayi hakuri,haka ne. Mimi nakasa jurewa ne, ace kin nemi alfarma ban miki ba,Mimi a duk duniya bani da wani buri sama da inga na faranta miki,Mimi fata na a kullum ki kasansce cikin farin ciki da walwala babu wata damuwa a tattare da ke. na gode yaya na gode kwarai da kulawar ka a gare ni Allah kuma yasaka ma da Aljannat fiddausi,ameen Mimi Allah yasa mu dukan mu mukasance a cikinta. su dukansu suka amsa da Ameen.

.

Bayan sun dawo ne,Mimi tayi wanka tayi kyau sosai kamar ba indiya,sanye take da riga da siket English wear ta yafa wani karamin gyale Kalar kayan,tana saukowa ne zuwa falo,anan ta sami mommy zaune. Mommy nah,ashe yaya faruk ya fita,to zai zauna ne yayi ta jiranki har sai kinfito,yadai ce ki same shi a dakin sa,to mommy bari naje. Kwance yake yana sauke gajiyar tafiya daga shi sai singlet da shortniker,bacci yanason ya dan dauke shi. Sallamar Mimi yaji,Mimi ina zuwa, sai da yasaka jallabiyar sa,sannan ya bude daki, tsaye yayi yana kallonta ba tare da ya bata hanya ta wuce ba. Kwata,kwata ta canza masa domin wani irin kyau yaga ta kara, sai murmushi take dimple dinta na lutsawa…my Mimi tsokanan ya isa haka,wannan murmushin ai sai in manta hanyar gidanmu…aah yaya,to ai a cikin gidan naku kake,kaga baza ka manta ba. Yaya, aka ce kace insameka,dama abinci naso kikawo min amma har naci,sai dai barci da nake sonyi,ok yayi bari naje wurin kaka musha fira kenan,ayi barci lafiya,ok bye my Mimi. Ta tafi shiko yashiga dakinsa. Written by Bilkeesu giro [4:54PM, 10/3/2015] Billygiro: AL-AMARIN ZUCINa Bilky giro 18kakaaaa!!!….gani a bayan ki yau baza ki tsorata ni ba,ai ba tsorata ki zanyiba,nayi ta sallama ne baki amsa ba shine nakira da karfi ko zaki ji. Kaka ina Alhaji yayi wai, bacci yake,watakilma kin tashe shi da wannan kuwar taki,kaka ai gara ma ya tashi ya ga amaryashi sabon jini,takarasa maganar ne tare da shiga daki. Alhajina ashe ka tashi da barcin…an wuni lafiya,lafiya Kalau mimi,ina abokin ki,barci yake,koda yake bai jima da shigowa ba.cewar Alhaji. Shi ne ni kika zo kika tayarnmin da miji amma shi kin barshi yana bacci?eh kaka, shi dan hutu ne….ai kuwa shima yanzu zanje in tashe shi tana magana ne tare da dauko maya finta. Koda Mimi taga dagaske take ta rirrike kaka tana cewa kaka don Allah yi hakuri Allah ya gaji dayawa,cikin marai rai cewa take magana. to zaki sake tada min maigida? a’a amma ai kinsan nima matar sa ce,…kamar yadda shima din faruk mijina ne ba,kaka kenan nikadai ce matarsa bana zama da kishiya……

.

Domin tuni na sa yayana ya miki saki ukku….ayya ai ni bana sakuwa….Sallamar Hafiz da Ali ce ta katse musu fira,kuma da alama Hafiz ya ji abinda suke cewa sbd yanayin fuskarsa yanuna. Kaka ce ta amsa sallamar,bayan sun gaisa ne Mimi ke tambayar Ali, “yaya Ali ina takwarata,ina fatan lafiya kalau take,lafiya lau, tace ma a gaida ke,ina amsawa,shi yaya Hafiz yaki gaya muna wacece antinmu…hmm Mimi kenan kena ke so amma a cikin rashin sani na fada sonki domin dana san faruk ke sonki da bazan fara ba,sai dai saukin abin ban furta miki ba….yaya yadai naga ka zurfafa, tunanin me kake,ba komai Mimi. Kaka ni zan tafi,to a gaida mutan gida,za suji inshaAllah. Daddy inaso inje shan ice cream na dade ban je ba,Mimi ni bana iya yawon nan yau ki je faruk ya kaiki…shan zakin ne yata shi ko…mommy pls ki banni inje,ai baxan hana kiba jeki tunda daddyn ki, yace kije…thank u my mom tayi mata kiss a kumatu ta fita a guje. Da isar ta,ta banki kofar dakin bako sallaam fito daga wanka kenan yaji an banki kofar dakinsa bako sallama,dagowar da zai yi yaga waye, sukayi ido hudu da Mimi.

.

Da sauri ta dauke idanunnta akansa domin bata saba ganin sa,a haka ba. Dagashi sai towel ga gashin kirjin sa duk ya kwanta luf ,luf dashi,gabanta sai dukan uku,uku yake domin tasan yau fada ne rabonta. Wai ke Mimi! yaushe ne zaki yi hankali ki daina gudu!da har zaki shigo min daki ba sallama! bayan kinsan ba abinda na tsana irin a shigo min daki ba sallama,sai kace dakin arna,get out of my room!stupid girl kawai. Gabaki daya ta rasa natsuwar ta,da kyar ta samu ta iya cewa “yaya am so sorry pleasedajin maganar ta yasan kuka take,nan take yaji bai kyauta ba. Mimi kuka kikeyi?yi hakuri raina ne ya baci da yawa,gaya min me ke tafe dake, tayi shiru ba amsa, yaxo dab da ita Mimi magana fa nake miki,am sorry fadamin mekike so, dama…. ta sakeyin shiru hawaye na zuba a idanunta domin ta tsani fada a rayuwar ta har gara ma a daketa da ayima ta fada.

.

YA MU CI GABA?

January 26 at 8:11am · Public

 

AL-AMARIN ZUCI 2

.

Jawota yayi, ya rungumeta yana dan bubbuga bayanta,alamar rarrashi,har saida ya tabbatar ta sauko sannan ya sake tambayar ta,nan take cemishi daddy yace inzo ka kaini wurin shan ice cream. Har yanzu shan ice cream na nan baki daina ba ko? ya dan lakuci hancinta yana murmushi ita ma haka, sannan yace “jeki shiryo ki zo mu tafi. Suna hanyar su ta dawowa ne take tambayar sa”yaya ni meyasa ba’a bari ina driving da kaina? kibari idan kika gama secondry school sai ki fara driving da kanki kinji,to yayana ai nakusa, domin cikin wannan watan zamu kammala. To Allah ya kaimu,Amin, yaya yaushe zaka koma ne? sai bayan wata daya’ amma kamar yayi yawa,a yadda kasa ba zuwa, eh haka ne ina son in huta da yawa ne…right! ni kuma sai in ganka da yawa kenan shiyasa nake kara jin sonki a cikin zuciyata mimi har nake tunanin bazan iya rayuwa bake ba…nima haka yayana i love you so much more .

Mimi!!tashi baccin ya isa haka kinsan yau ranar family meeting ne,ina so mu karasa aikin mu cikin lokaci,to mommy. Dayake duk za’ayi family meeting kowa da kalar abincin da zai kai, bayan angama meeting kowa shi zai dibi abincin son ransa, suna masu ci cikin zumunci da yarda da kuma aminci. Kowa ya hallara a babban falo, Alhaji Hassan shi ne ya bude taro da addu’a,Alhaji ne, ya tashi yana cewa “dama yau rana ce wacce muke tattaunawa akan abubuwa da dama ciki harda warware matsalolin mu da suka shafi wannan family, sai dai yau Alhamdlillahi babu matsala ko daya inshaAllah fa ce alheri da na zo muku dashi. Alherin shi ne za’a sa ranar daurin auren Mimi da faruk,wadan da dama kowa yasan suna son juna sosai da sosai. Duk da haka nasan zaku yi mamaki sosai saboda ba wanda ya kawo auren su kusa,nima a daren jiya nayi wannan tunani ya kamata a yi auren nan kafin faruk ya tafi tunda Mimi ce yake jira kuma ta kare karatun ta, na secondry, in yaso idan mijin ta ya amince ta ci gaba da karatu, sai taci gaba. Gaba ki daya falon yayi tsit kowa na saka abu a cikin zuciyar sa kuma da alama abin yayi matukar yi musu dadi,akasin faruk wanda tun lokacin da aka fara zancen zufa ke karyo masa har yanzu. Ko meye dalili oho,muje zuwa…..

.

Ina fatan wannan hukunci da na yanke yayi? gaba dai falon ya dauka sai cewa suke”yayi gsky hakan yayi daidai Allah ya tabbatar da alheri.Amin Ko akwai mai magana a cikin masoyan?cewar Alhj hassan.Eh Abba, faruk ne ya furta hakan tare da mikewa tsaye,fadi maganar ka muna jinka. Don Allah famly kuyi hakuri da abinda zai fito bakina musamman ma Alhj da Mimi nasan zaku fi kowa jin haushi da kuma mamaki akan abin da zan fada. Alhj inaso ayi hkr a janye aure na da Mimi….saboda me! alhaj hassan ne cikin kakkausar murya yake magana, faruk kana da hankali kuwa?meye dalilinka…..Abba wlh bana son Mimi…..INNaLILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI’UN falon ne ya dauka da hakan sai da kowa ya mike saboda tsananin mamaki akasin mimi wacce ko mikewa ta kasayi tana nan zaune kamar gunki,idanunta na kan faruk ko kiftawa basayi saboda tsananin mamaki.

.

Tas!!Tas!!Tas!!kake ji Abba ya wanke faruk da mari uku masu kyau cikin tsananin bacin rai…ka ga kyale shi haka, faruk fada muna dalilinka na cewa baka son Mimi,alhj nima haka na sami kaina da bana son Mimi a cikin ‘yan kwanakinan nayi duk yadda zanyi in maida son yaki amma wlh ina son Mimi abaya shiyasa banaso ayi auren nan nasan wahala kawai zatayi…..Hauka! to bari kaji in gaya maka aure ba makawa sai anyi in yaso ka kasheta, dan rainin hankili..a’a alhj hassan cewar abban Mimi, baza ayi haka ba tunda baya so shikenan….wlh ba makawa auren nan sai anyishi kuma cikin satin nan inshaAllah. Kuma ka bace ka bamu wuri,koda abba ya juyo ya ga Mimi zaune shar hawaye na zuba a idonta,kuma har yanzu idanun ta na kan faruk …Mimi !mimi! Abba ne ke jijjiga ta,ko motsi taki, fa ce hannuta da ta nuna faruk dashi, amma sai ta kasa furta komai ganin sukayi ta zube kasa sumammiya innalillahi wa inna ilaihi raji’un kowa yayi kanta sai yayyafa mata ruwa ake, da kyar suka samu ta farfado aka wuce da ita cikin gida. Faruk sai kuka yake sosai akan rashin fahimtar sa da ba’ayi ba.Hafiz yaja shi zuwa dakinsa. Hafiz wlh na kasa gane wannan al’amari da zuciya ta tazo min dashi…… sai kuma wani irin kuka ya kwace masa. .

.

Hafiz nasan yanzu Mimi zata yi tunanin na cuceta….to kai meyasa baka bar abin a ranka ba watakil ko son zai dawo bayan anyi aure, hafiz bana tunanin haka,kuma bana so kyautawa ta da Mimi ya dawo rashin kyautatawa, domin idan na aureta a cikin rashin sonnan bansan mai zai faru ba,ban taba tunani cewa soyayya ta da Mimi zata dawo hakaba,faruk addu’a ya kamata kayi domin wannan al’amari na zuciyar ka yana da ban tsoro da al’ajabi. Mommy, yaya ya cuceni, yayi min ilar da har in mutu bazan mantaba,me nayi maka da zaka min haka.. ashe da gaske ne cewar zainab namiji ba dan goyo bane,mommy yaya yasa na tsani maza a duniya, Allah ya…kul!! kar ki kuskura ki kara tunanin furta wanna mummunar Kalmar….wayyo Allah mommy na yazan da raina…. wani irin kuka ya kwace mata mai tsanani. Kiyi hakuri Mimi dama haka rayuwa take soyayya na zama ki,haka kuma ki kan koma so kiyi hkr kinji, ki rungumi kaddara,tajawota jikinta ta rungume, tana mai kara rarrashin ta. Faruk baka kyauta wa family din nan ba,faruk me ya hada ka da mimi da har zakayi wannan furucin da ba Mimi kadai taji zafinsa ba. Umma wlh mimi bata min komai ba kawai haka naji a zuciyata bana sonta…..da kin kyale dan iskan yaron nan marar mutunci, wanda hankalinsa kadai ake gani amma baya dashi…a’a Alhj kada zafin zuciya ya debeka kayi wa yaron nan baki.

.

Abbah don Allah kayi hakuri nasan nayi kuskure,ko kallon inda faruk yake baiyiba ya tafi abinshi. Faruk kodai wata ce kagani kanaso?ko daya umma ,abin sai kace tabin jinni, ko wani abu ya hadaka da wani ne ko sabani akan mimi ko yace yana sonta kaci mai mutunci,umma gsky babu,hmm faruk kenan mai hankali bazai ji wannan zance ya yadda dashi ba,dole akwai wani a bu kasa,umma…faruk, tashi kawai kabani guri. Zainab kizo akwai magana,ok sai nazo kenan,ta aje wayar tare da share hayen da suka zubo mata. Barka da wuni mommy yauwa Zainab yau kece a gidan namu?eh mommy, to ya mutan gida lafiya lau,jeki Mimi na daga ciki. Mimi ya ake ciki ne? naga duk kin ya kuce…Zainab aure za’ayi min da Wanda baya so na,aure Mimi?kuma da wanda baya sonki?kwarai kuwa zainab,waye wannan, yaya faruk,dama kuna da wani dan uwa ne faruk bancin faruk dinki,shi dai da kika sani zainab,shine guda ba kari,kuma shi da kansa yace baya sona….. What!!Mimi meyake nufi da haka….cin amana, mana har sai kin tambaya bayan ke da kanki kin taba nunamin halin da namiji naki yarda …..innalillahi wa innailaihi raju’un amma yaya faruk yaci amanar soyayya….ganin nake kamar wata ya samu,tunanin da nake kenan mimi.

.

Wato Mimi kin nuna masa so, ba ko dan ajin nan na mata,matsalar kenan, zainab,ai ya fahimtar dani yanzu,amma nasan abinyi. Koda Zainab ta fito suka yi kicibis da Hafiz zai shiga dakin mimi,tsaya wa yayi yana kallonta batare da ya bata hanya ta wuce ba. Sai yaga tayi mai kyau sosai fiye da kullum….yaya Hafiz ina so zan wuce,oh sorry Zainab,sannan ya bata hanya ta wuce. Yaune ranar daurin auren Mimi da faruk,anyi matukar yin taro kamar ba’a mutuwa,bayan an daura aure ne za’ayi walima,baxa su samu damar yin wasu buku kuwa ba,domin basu da isasshen lakaci, saboda zasuyi sammako zuwa London. Zainab ce ke shirya Mimi sai tsokanar ta take,amarsu ta ango kinga yadda kikayi kyau kuwa na tabbata ko makiyin ki yaganki sai ya sake kallo ,meye amfanin haduwar, miji baya so…hmm ni bana son kina zancen nan fa…Allah, to na daina. Kina birge ni mimi ta yadda kika cire damuwa a cikin ranki,kamar ba abinda ya faru.

.

Zainab na fahimci idan nasa damuwa a raina bani da wata riba face rashinta,na fiso in maida lamarina a wurin ubangiji, da yaddar Allah inhar da gaske yaya keyi na yadaina sona inshaAllh idan na dage da addu’a zai soni. Zainab ko London muka je zanyi harkar gabana ne,zan nuna kamar dama can bamu shakuba, amma zan masa duk wata biyayya da mata take ma mijinta. Mimi kenan meyasa zakiyi haka…. so kike in shishshige masa in yaso ya kara jin haushi na ne…hmm zainab muma daina maganar nan pls, saboda raina kara baci yake. Bayan angama walima, Mimi da Zainab ne a daki, suna kallon fotunan da suka dauka a waya,Mimi wannan foton duk yafi kyau,bari a turama yaya faruk yagani tunda bai ganki ba….a’a Zainab karki tura…da sauri zainab ta tashi domin ta gudu.

.

Ita ma Mimi biyo ta tayi aguje,Zainab na kai wa bakin kofa taci karo da mutum, gata rungume a jikinsa, sannu,sannu take tada kanta, saboda tana fargabar waye, koda ta dago idonta taga Hafiz, da sauri ta janye jikin ta, cikin jin kunya, har bata son hada ido da shi shiko gogan wani farin ciki ya ziyar ceshi sai tunani yake ina ma ace mallakin sa ce…… yaya hafiz yi hakuri bada sani na bane…no zainab,ba komai ai ya wuce Mimi, faruk yace “tunda safe ne tafiyar ku,daga kai tayi alamar taji,domin dariya ne sosai ta keji,saida yafita sannan, ta fara dariya sosai tana nunin zainab,shi ne dai dai dake…kinga banaso to ni inaso,kanki ake ji,kin tura foton? ai dama wasa nake miki….a’a ai tunda kin tura a kirjin yaya Hafiz zai je wa yaya faruk ko? Mimi!!…Zainab…yayi zan rama ne, cewar zainab. Mimi ce agaban mommy da daddy su nayi mata nasifa akan tabi mijinta sau da kafa,nasifar ta ratsa ta, hakan ya sata kuka sosai,kenan dai zantafi in barku mommy zanta fi gurin wanda baya sona ni kadai ke sonsa mommy…..yi hakuri kinji mimi ya isa,tashi muje cikin gida ki musu bankwana.

.

A filin jirgi,Mimi sai kuka take mai cin rai ta rirrike abba,tana cewa,”Abba na fasa auren tunda shi baya sona…..kaka ki gaya ma su da gaske nake na hakura….Alhaji don Allah ka taimakamin kajenye auren nan nafiso na zauna daku, haka take binsu tana kuka amma bawanda yace mata kala saboda ta basu tausayi har basu san me zasu ce mata ba,baba Bashir kadai ne yayi karfi halin yaimata magana, yi hakuri Mimi nasan cewa, yayanki bazai cutar da ke ba, amatsayinki na kanwa a gare shi, ki yi hakuri kinji, daga kanta tayi alamar taji tana, mai share hawayenta. Zainab ce ta rungume ta suna jin kamar kar su rabu, faruk ne yaxo, ya ja hannuta su ka shiga jirgi,suna masu yi musu bye bye. A cikin jirgi ne faruk ke kallon Mimi yana magana a cikin zuciyar sa”yau wai Mimi ce ke kukan bazata bini ba, bayan ada kuka take zata bini,lailai nayi kuskure. Bayan sun isa ne,Mimi sai kallon gidan take yayi matukar birgeta gashi da fadi,mutun zai sakata ya wala,haka ta fada a cikin zuciyarta.

January

 

AL-AMARIN ZUCI 3.

.

ya nuna mata dakinta, shiko ya tafi nasa dakin,wanka tafarayi, ta kwanta domin ta samu ta sauke gajiyar tafiya, bacci barawo ya dauke ta. Koda ta tashi,ta samu ya aje mata takeaway gashi dama tana jin yunwa sosai,ta zauna taci saida ta koshi, bata da abinyi kuma tana fashin sallah,tashi tayi tana yawata wa,a cikin gidan anan taga wurin wasan basket ball gashi ko a gida wasanda sukeyi kenan hakan yayi matukar yimata dadi, ai ko saida tayi ball sannan ta koma ciki,ganin marece tayi. Wuraren karfe goma na dare tayi shirin bacci kenan,taji motsin shigowar sa,”wai yanzu naji dama, ni kadai a gida tun dazu sai kace maiya,kwantawarta keda wuya ya shigo dakin da sallamarsa ,ta amsa sallamar tare da gaishe shi, ya mika mata ledar hannusa tare da amsa gaisuwar,ba yabo ba fallasa. Gasashiyar kaza ce da hollandiya milk a ciki,taci sai, dai ba sosai ba, domin taci ragowar na dazu,tasa saura a firij,tayi kwanciyar ta,sai safe.

.

Ba ta farka ba sai wuraren karfe goma na safe, tayi wanka,ta shirya cikin wasu kana nan kaya,riga da siket, rigar iya cibi, sai siket dinma ma iya cinya tayi kyau sosai,saida ta gyara ko ina fes,sanna taje kici neman abinda zata ci, ba komai a kicin din,illa kayan tea,sauran kazar jiya ta dumama ta hada da tea ta ci. Kwance take falo tana game da wayarta,da tagaji ne da game ta kunna tv, tana kallo. Yau sati daya kenan amma ba abinda ya canza kullum abinci saye take ci,ga kadaici na damunta,tun zuwanta bata yi waya da kowa ba,sabida bai saya mata layin canba,shi ne ta yanke shawarar idan ya shigo xata masa magana. Bashi ya shigo ba sai karfe tara da rabi,tana kan sallaya tana karatun Qur’ani taji shigowarsa,saida da takara minti talatin sannan,ta je dakinsa da sallamarta,sai da yabata izini sannan tashiga. Zaune ta same shi bisa gado yana dan wani aiki da laptop,daga shi sai singlet da wando. Yaya sannu da aiki,yauwa sannu yabata amsa ne batare da ya ko kalli inda take ba.

.

yaya dama cewa nayi me zai hana a siyo kayan abinci,akan wane dalili? ganin nayi zaifi sauki,gashi kuma nagaji da cin abincin sayarwa,ni da nake siya bance miki naga gaji ba sai ke,da ci ne kawai naki,dan kin raina ni ko? yaya meye raini anan kuma,ganin nayi siyen kayan abinci yafi sauki,saboda kinfini fini sanin abinda yakamata ko?mamaki ya bata sosai ganin a hasale yake magana, Allah ya huci zuciyarka,ta furta hakanne tare da fita daga dakin a tsorace domin ganin take ko dukanta zai iya yi. Ta koma dakinta cike da mamaki,tana cewa”rashin so bala’i ne, idan ba haka ba wannan maganar ce zata hasala shi,ina ma ace yanzu ne kake so na ba a lokacinda nake gidanmu ba,amma sai lokacin da zan yi rayuwa a gidanka zaka ji baka sona,yaya meyasa zuciyarka ta zo maka da wannan al’amari? Wanda ni bazan iya jureshiba,why?yaya. Kuka take sosai,tana rokon Allah ya sauya mata wannan al’amari,cikin sauki, tana cikin kuka ne bacci barawo ya saceta. Ba ita ta farka ba sai asuba,tayi sallah taji baza ta iya komawa bacci ba saboda yunwar da take ji,kici ta nufa domin ta hada tea,ga mamakin ta sai taga kayan abinci makil ,wato dama jiya yaya ya siyo kayan abinci,shi ne yayi tamin fada,kamar ma ba zai siyo ba. Nan take, tahada musu breakfast mai rai da lafiya, gida duk ya kamsashe,a dining table ta jera komai,sannan taje tayi wanka,ta shirya ne cikin super Holland riga da siket sun dan kamata kadan, tayi daurin dankwalinta, mai kyau ta jashi baya, gaban gashin ya kwanta sosai,ta sake sauran gashin a bayanta. Ta fito das,das,da ita sai kamshi take,dakinsa ta kwankwasa sai gashi ya fito da shirin fita,saida yaji wani abu da ya ganta,tayi kyau sosai,cike da murmushi ta gaishe shi, ya amsa ba yabo ba fallasa.

.

yayana breakfast na jiranka,batare da ta tsaya jin me zai ce ba,ta juya hade da jawo jelar gashinta zuwa gaba, wato ta maida shi saman kafadar ta,hakanne yabashi damar ganin show me your back,tafiya take kamar wacce ba qashi a jikinta,tana wani irin laudi,ga hips da Allah yabata duk da haka bata kiba ba rama,ya salam,Allah yayi halitta anan, tun randa nake da mimi ban taba ganin tayi kyau irin wannan ba,cewar faruk. Abinci suke ci amma sai mamakinta yake kamar wacce bata da damuwa a tattare da ita.Da zai tafi har bakin mota tarakashi. Haka sukaci gaba da rayuwa har tsawon wata ba wani sauyi,kwalliya nan tanayinta yadda ya kamata,abincin ta lafiya ko makiyinta yaci bazai ce baiyiba,tana masa biyayya dai dai iyawarta, gata da tsafta,uwa uba tana ibada ba dare ba rana. To ni Mimi mena rageshi da shi,amma nakasa miado sona,ko dai zan hakura da kaine yaya….a’a Mimi gajen hakuri bana ki bane,ki tuna fa a kwai Allah,kici gaba da hakuri da kuma addu’a, cikin ikon Allah sai ki ga komai yadawo daidai. Tana magana ne da zuciyar ta, haka ne fa,tayi maganar ne a fili. Faruk ne zaune a falo yana kallo,kamshin turaren ta ne ya dawo da hankalinshi wurinta sanye take da doguwar riga ta kanti baka mai dogon hannu, anyi mata kwalliya da fararen duwatsu,ba dankwali a kanta,tayi matukar yin kyau.

.

Sai dai yanayin fuskarta ya nuna akwai damuwa a tare da Ita. Zama tayi akusa dashi, yana saman kujera ita tana kasa,tafara da cewa. “Yaya kaje a bainar jama’a ka tozartani baka dubi zumuncin da ke tsakanin mu ba,ballantana har kaji kunyar mahaifina, agabansa ka furta cewa baka sona, hawaye ne shar ke fita a idonta amma hakan bai hana ta cigaba da maganar da takeyi ba,yaya idan har wani laifi naima meyasa baka kira ni a gefe ka gaya min ba har saida kaje a cin jama’a, kasa iyayenmu a cikin bacin rai da bakin ciki,nayi hakurin wannan, amma bazan iya jure wannan ba ….. Ya isa mimi!….ya isa haka!… wai me kikeson cewane da har sai kin bata min rai kafin ki fada?yaya tun lokacinda muka zo banta taba fita ba, bantaba waya da kowa a gida ba, ko da yaushe ina cikin kadai ci, yaya, ya kake so nayi da rayuwata ne…kuka take sosai shiko faruk duk gabadaya tausayinta ya lullube shi, jikinsa yayi sanyi sosai. Mimi pls kiyi hakuri tun zuwammu da kwana biyu na saya miki layi, koda naje kai miki nasamu kina bacci,shi ne na saka, a cikin drawer,Allah na manta in gaya miki amma kiyi hakuri,kinji, Yaya kana nufin Abba bai taba tambaya ta ba,Mimi ko nakira Abba baya daga wayana yayi fushi dani kuma inajin kunyar kiransu daddy,sai su Alhji da kaka kawai, amma sukan tambaye ki,sai dai, akanyi rashin sa’a bana gida.

.

Yaja hannunta suka je dakinta,drawer din ya bude ya dauko layin. Miko wayarki a saka layin,ta dauko wayar ta bashi,yauwa yanzu kinga sai a kira daddy ko?eh yaya,ringing daya tayi aka daga wayar,tare da amsa sallama,daddy Mimi ce, mamana aikinsan muryanki bata bace ,ya can din?lafiya lau,ya yayanki yana lafiya?lafiya lau. Daddy nayi mising dinku dayawa ina momyna,ga momynki,Mimi injin dai kunan lafiya dai ko?Allah mommy, lafiya kalau muke to in jin dai kina masa biyayya, yadda yakamata, Allah momy ina masa,to kici gaba da yimasa biyayya kinji,inshaAllah komai zai bi daidai,sun dade sosai suna waya,sannan takira su kaka suma ta gaisa dasu,yaya gaskiya akira abbah tayi maganar a cikin shagwaba. Kirashi mana,amma nasan ni bazaiyi magana dani ba,yaya zai yi magana dakai….hmm Mimi kenan bakisan Abbah ba ne idan yayi fushi….Ya daga wayan fa,Abba barka da wuni,a’a ‘yata Mimi kece?eh Abbah nice,ina fata dai yayanki baya cutar dake?bayan min komai…..amma don Allah kayi hakuri da abinda yayi,Mimi bawai banyi hakuri bane,inaso in kwatar miki ‘yancinki ne…ko bakya so?inaso abba …to ki barni dashi kawai so nake sai yagane kuskurensa,ga ummanki, tanaso ku gaisa,bayan sun gaisa ne,umma tayi,tayi mata nasifa akan taci gaba da hakuri,sannan ta aje wayar,tana mai kallonsa,idanuwansa sunyi jawur,kingani ko nagaya miki….kayi hakuri yaya,jawoshi tayi jikinta ta rungumeshi,tana kara kwantar mai da hankali.

.

Shima rungumeta yayi,yana shafar gashin kanta,har ya fara wuce gona da iri,saurin dakatar dashi tayi,da cewa”yaya muje muci abinci,bahakan ya soba amma ba yadda iya dole yatashi suka je cin abincin,da suka gama ne suka koma kallo,har wuraren karfe goma. Mimi tashi muje muyi bacci dare yayi,wani iri taji zancen abinda bai taba yi mata ba,tashi tayi suka jera kowannesu ya shiga nasa daki,toilet tashiga tayi wanka,sanna ta fito tayi shirin kwanciya,tana kokarin kwantaya taji yana nocking kofanta,me kuma yaya yake bukata cewar mimi.Tashi tayi ta bude masa kofan, tsaye tayi tana jiran taji kome yake bukata,yanayin kallon da yake mata ne ya tunatar da ita tufafin da ke jikinta, da ita da babu duk daya ne,da sauri tajuya domin dauko hijabi,idan kinsa hijab din kizo muje dakina. Bayan sunje dakinsa ne ya umarce ta da tayi arwala,”yaya ina da arwala,to zo muyi nafila mugodewa Allah,hadi dayin addu’a Allah yasa ma aurenmu albarka,raka’a biyu sukayi ya juyo ya dafa kanta yana addu’a. Written by BilkeesuSai da yayi mata tambayoyi akan addini ya tabbatar bata da matsala, sannan,ya dauke ta chak ya aza bisa gado,tare da cire mata hijab,anan yafara gwada mata iyawarsa,sai rokonsa take yayi hakuri,Mimi bazan iya bane pls kibanni nayi,ciga ba yayi da shafarta ta ko’ina har yana kokarin rabata da kayan jikinta,yaya pls….bakinsa yasa a cikin nata yana tsotsa, sai da ya tabbatar ya kashe mata jiki sannan ya fara addu’a saduwa da iyali,wata irin kara naji Mimi tayi,wacce ni Bilky giro,sai da na bar dakin aguje ban shiryaba. Sai da safe na samu na dawo dakin, bacci suke abinsu rungume da juna. Faruk ne yafara tashi cike da farin ciki yake kallon Mimi,duk yaji taba shi tausayi yarinya ‘yar shekara 17 ya kasa hakurin bari har ta qara girma. Daukar ta yayi zuwa toilet domin suyi wanka,ya hada mata ruwan zafi da dettol ya sakata a cikin bahon wanka,qanqameshi tayi alamar taji zafin ruwan sosai,yaya da zafi tana magana ne a cikin shagwaba,sorry my Mimi,sai da yagama yimata gashi sanna sukayi wanka,suka fito,suka gabatar da sallah..

.

Shi da kansa ya hada musu breakfast,sukaci,Mimi kwanciya ta koma yi,akasin shi da yake shirin zuwa aiki,yagama shirin sa tsaf sannan ya dawo gun Mimi,yadai Mimi ko akwai abinda yake damunki?yaya zafi nake ji a gun,oh no Mimi sorry ba laifi na bane,nifa a sannu na biki,kece very tight,amshi wannan magani ko zaki ji sauki,bayan tasha maganin ne ya lallaba ta, har saida tayi bacci sannan ya fita. Ba ita, ta tashi ba sai wuraren karfe 12pm.wanka ta komayi,sannan ta gyara ko’ina na gidan tsaf,gida sai kamshi yake. Kici taje domin samun abu mai sauki wanda zata girka ,kuskus ta datafa da stew da naman kaza,sanna da dafaffen kwai,ta kai kan dining table ta jera,tana jiran dawowar sa. Wayart ta dauko takira zainab,ringing daya biyu ta daga wayar,hello Zainab Mimi ce,lah Mimi ashe,akan jiku,ya amarci,Alhmdlh,

kinji ni shiru ko zainab?har wata fa ba kira,nace ko dadin auren ne?hmm zee kenan har akwai abinda zai sa inmanta da ke in ba gushewar hankali ba,to har amin baiko ba kira kuma nasan bazaki rasa jiba,yaya ya manta bai gayan min ya aje min layi a daki ba,ni kuma ban tambayesa ba sai jiya,Allah zee banjiba dawa akayi,na baki gari ki canko,nadaisan ba kya son Habib dashi akayi ko kuwa?hmm an barki baya Mimi,da yaya hafiz akayi,dan girman Allah!da gaske nake miki zancen nan,bayan tafiyarku komai ya hadu,soyayya zamzam kamar wadanda sukayi shekara, amma nayi matukar murna wlh, Allah ya kara dankon soyayya,Amin mimi na gode,sannan suka aje waya,tana mamaki yanzu ace yaya faruk ko yagaya min,ko da yake bazai yi tunanin banji ba.

.

Bushi ya dawo ba sai wuraren 3pm,sai faman sauri yake,saboda yabar Mimi ba abinci, bai kuma yi tunanin zata iya dafawa ba,bai zame ko ina ba, sai dakinta,kwance ya sameta akan kafet din sallah tana bacci,da alama tana gama sallah tayi bacci domin ko hijabi bata cire ba. Durkusawa wa yayi cike da tausayinta, yana mai shafar fuskarta tare da bata kiss,kamshin turarensa ne ya tada ita, a hankali take bude idanuwanta cike da jin bacci,yaya ka dawo?sai yanzu nasamu damar dawowa, meeting ne ya tsaishe ni,kiyi hakuri na barki da yunwa,ba haka naso ba,ba komai yaya,abincin zaka fara ci,ko sai kayi wanka,kin dafa abinci ne?daga kanta tayi alamar eh,i hope kinci?banci ba kai nake jira,haba mimi tayaya zaki jirani bayan kina jin yunwa,yaya nafi jin dadin cin abinci da wani,amma dai irin haka ai sai ulcer ta kamaki,ki daina dogon jira haka kinji,naji, to tashi muje muci abincin,amma cire wannan hijab din. Ta cire hijabi suka tafi. Yau shi da kansa yake bata abinci a baki,tana lafe a saman jikinsa,sai wani kara narke masa take,sai da suka koshi sannan sukayi wanka. Kwance suke a bisa gado rungume da juna,ba kaya a jikinsu sai bargon da suka lulba dashi, da alama wanka sukayi,Mimi na shafar gashin kirjinsa,shiko yana shafar gashin kanta,koma wa yayi kan dukiyar fulaninta da suke rikitar dashi ko yaushe,anan tafara jin yana so ya wuce gun…”um um fah yaya,kin manta yau fa sati daya kenan,kuma kice zaki hana ni,gashi kinsan gobe ne tafiyata,yanzu yaya ni kadai zaka bari, a’a zan kayo miki wata kanwar abokina da take karatu anan,a hostel take zama,idan na dawo sai ta koma,hakan yayi miki?daga kanta tayi alamar eh,yanzu za’a barni nayi ko?kunya taji sosai har da rufe idanunta,nan suka faranta ran juna.

About the author

Hausa_Novels

Leave a Comment