Littafan Hausa Novels

Aisha Humaira Hausa Novel Complete

Yadda Ake Rikita Maigida Yayin Kwanciya
Written by Hausa_Novels

Aisha Humaira Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

AISHA HUMAIRA*

 

 

*1*

 

*Aisha humaira*

*Aisha humaira*

!!wai kina ina ne yar nan inakiran ki kina jina amma kika min shiru ko se na shigo dakin?

Zaki fito ko sena shigo!

Bakin ta kamar ya hade da bango tsabar tsiri dan masifa

Ke da’ada wai kin fiya takurawa mutum wallahi Allah

Ta jefe ta da cokalin hannun ta

Kaucewa ta yi hade da kyal- kyalar dariya ta dau bokiti tayi hanyar bangaren baffa idi tana yan wake-wake.

Baffa na alwala a tsakar gida ya daka mata tsawa ke wai aisha humaira yaushe zaki nutsu ne ki shigo gida ba sallama se wake.

Yi hakuri baffa na tuba

Kullum a haka kike ai dama kin tuba.

Sum sum ta shige cikin gidan

Inono na kan sallaya tana lazimi haba ta rike cike da mamaki a ranta tace wannan yarinyar da shakinyanci take

Inono ina wuni

Kai ta gyada mata saboda lazimi ne a bakin ta.

 

Fatima Bintu Hausa Novel Complete

Inono ina fatima bintu?

Daki ta nuna mata bokitin ta ajiye a tsakar falo ta yi cikin dakin da gudu fatima bintu na bacci taji an fado mata a ka

Ihu ta zunduma tsabar tsoro tana mikewa kuwa aisha humaira tasa mata dariya harda tsugunawa kasa

Fad’ima bintu ta tsuguna ta gartsa masa cizo a kunnen ta tsalle ta daka tana ihu

Inono ta shigo da sauri da carbi a hannun ta wallahi se kun fita daga gidan nan wallahi yanzun nan na rantse da girman Allah.

 

Suka yi waje da gudu.

Aiko suka ci karo da hamma yusuf ya tsaya tsabar takaici yana kallon su kullum ku rayuwar ku a gudu kuke da tsalle kamar wasu yan biri ko to maza maza ku yi ciki kusa hannun ku a sama.

 

Narai narai da ido fadimatu tayi ta kasa motsi a gun ita ko aisha humaira tsaki tayi ta zumburo baki ta juya keya, mamaki ya kama shi ya rasa ma mezai ce musu tsawa ya daka musu kun tsaya kuna kallona ko sena make ku mara sa kirki marasa mutumci.

 

Ni ruwa zan debo ma da’ada,fa!

Mariya ya kwalawa kira ta fito da sauri tana gani hamma

Dauko bokitin da’ada a dakin inono ki debo mata ruwa ki kai mata kice aisha humaira na sata aiki.

Tom hamma yusuf.

Tusa keyar su yayi dakin inono yasa suka sa hannun su a sama.

Shi kuma ya zauna kan kujera yana kallon su duk wadda ta sauke ya rakwashe ta a kanta

Se la’asar inono ta lallaba shi ya kyale su.

 

Suna fita suka shiga bangaren adda mardiya (matar yayansu ce) tana tuka tuwon alkama dan hamma idirisa yana son tuwon alkama.

Suka zazzauna aa yan gidana se yanzu

Kede bari adda ai yau mun shiga wani hali

Da me fa?

Hamma yusuf mana

Au ai kun saba se kuyi tayi ai kun ki girma ai zan sa shi ya sa a saku a lalle.

 

Suka yi kwal da ido a waje

 

*2017*

*AISHA HUMAIRA*

 

 

*2*

 

Lalle kuma suka kyalkyale da dariya gaba dayan su harda tafawa suka yi shewa ahayee yerhh!!.

Mardiya ta kama baki yan banza kun rika ai dama hamma din naku yana nan a daka.

Da gudu suka kuma yin waje .

Dakin da’ada suka shiga kuma zaman su keda wuya da’ada ta kama aisha humaira tana duka daldaldal

Ai tuni fadimatu tayi waje tana dariya da kyar aisha humaira ta kwace ta fyalle a guje

Tayi dakin adda rabi tana kuka adda na daka ta juyo da sauri yaya?

Ba da’ada bace ba ta dake ni

Kai aisha humaira kin fiya rashin ji wallahi kin fiya kiriniya har se kin kure an miki duka kike jindadi.

Ta kyabe fuska ta juyo a hasale.

Cikin fada da bacin rai kamar zata make addan

Addan tace kai ni kike ma wannan kallon.

Wallahi na kara miki dukan.

Ba saiki dake ni ba din in gani.

Tabdi jan tayi kan ta da sauri ta gudu wallahi sena hadaki da isuhu ya min maganin ki ya zane min jikinki tukuna zan ji dadi.

 

Gidan su amira ta je ta sameta cikin kayan makarantar islamiya zata wuce makaranta tama makara mama na mata fada

Taga aisha humaira kamar an jefo ta.

 

Mama ta kama kai shi kenan Allah ya kawo min ke se kuyi tayi ai amma wallahi se kunje makaranta yanzu in ba haka ba zan sa a kira min yusuf ya zane mun ku wallahi kun fitini kowa gwara ma wannan yaran ya yi ya dawo ko na samu sa’ida a gidan nan

Amira ta ce nifa mama na shirya to maza jeki dauko kayan ki ku wuce makaranta

Sum sum suka shirya suka wuce

A hanya tace ke amira yaushe hamma zai dawo?

Ke har so kike ya dawo?

Eh man kinsan ina matukar san sa

Tab wannan mugun?

Ke kul kar ki soma ki kuma ce masa mugu

Hmm kya ji dashi ke kika sani

Amma ai mugu ne hamma.

Mintsinin ta tayi tayi kara suka sa dariya.

Suna gama daukar karatu suka yi hanyar gida suna hira.

A kofar gida suka ga hamma yusuf amira tayi sunkui da kai ta gaid shi

Ya amsa da yar fara’a

Aisha humaira ta sa dariya harda kyakyatawa yusuf ya harareta tayi cikin gida ita kuma

Amira ta tsaya suka dan gaisa da shi sannan ta tafi gida.

 

*2017*

 

*AISHA HUMAIRA*

 

 

*3*

Zaunawa tayi a tsakar dakin da’ada tana kallon ta tana tsinta,to mutniyar ayi hakuri a yi wa da’ada ahuwa kin ji?

Ta zumburo mata bakin ta.

Haba yar lele tawan ki yi hakuri kar a ji kan mu a sa mana dariya.

Sannan ta juyo sai suka kuma sa dariya suna hira ta bata abinci taci.

 

Ke yar nan dazi gidan su mutumin ki aka kawo mun waya muka gaisa da wannan yaron

Wa kuma?

Masdook mana

Ta zabura ta mike da sauri haba hamma ne ya bugo amma ba a ban wayar ba.

To ba kina makaranta ba ?

Kash banji dadi ba mama bata kyautan ba to ya tambaye ni ko ?

Ina fa ya dai bugo mu gaisa ne kan me zai tambaye ki?

Ta zumbura mata bakin ta kai da’ada yana sane ai

Ta kyabe baki sha kurumin ki ina ji dazu ana maganar za a kai kudin auran sa

Ta mike da sauri wa?

Masdook mana

Na shiga uku

Da’ada da gaske ko da wasa

Ta mata dakuwa kaniyar ki kina ji ko se ki shiga uku saboda auran shi

Da’ada ya za ayi haka ni bazan yarda ba kam wallahi tallahi se an warware

Ke ni na ga ta kaina yau ni bintu dan ubanki zaki hana ne

Ta zauna dabas tana kuka da’ada ke ma fa kin san tun ba yau ba ina san hamma kuma shi ne zaki bari a masa aure?

Da’ada ta kama bakinta na ga ta kaina kar ki sake a ji ki ma a gidan nan zaki hana aure ne ke yaushe kuka yi da shi yana sonki zai aure ki?

 

Kafin ya koma man da muka hadu dashi a gidan su hajojo da daurin auren hamma isyaku.

 

Yaushe kuke magana dashi har da zaku yi soyayya ba a sani ba ?

Da’ada a tambayi amira tasan komai ai

Shi ne ze ci amanata ya ce wata zai aura

Da’ada ta ce tabas bazai yi haka ba tunda ya miki alkawari se ya cika alkawarin nsn bs wadda zai aura sai ke

Dadi ya kama aisha humaira ta yi bacci mai dadi ranar za a bata hamma masdook

Tunda da’ada tasa baki mayafi ta ja tayi gidan su amira tana kallo kuwa ta ce ke zo kiji.

Me zaki zo ki dameni a daran nan?

Ke nayi kwaba fa kuma bana tsoro amma ina fargabar hamma masdook sede ki zame min sheda kawai nake so.

Me kika aikata?

Fada mata tayi tsalle amira tayi ta dire tace keda wa?ni amira wallahi baki isa ba kar ki soma sa ni a cikin haukan ki hamma masdook din zaki sa ya min tijara ba ban san anyi ba

Shi kenan ai kar ki taimake ni nima sena ki taimakon ki hamma yusuf ysce yana sonki da zan miki hanya amma na fasa

Riko ta tayi tsaya kawata zan miki

Ko kefa tayi wani murnushi me kayatarwa na mugunta ta gyara tsayuwarta suka tafa

 

*2017*

 

*AISHA HUMAIRA

4

*na khairat up*

Amma kin san akwai matsala ko idan hamma masdook ji wannan labarin

Ke kin fiya tsoro ni wallahi akan shi ba abunda bazan yi ba kome ze mun sena aure shi wallahi sena aure shi.

Kallo ta bita dashi kawai tana jinjina karfin hali irin na aisha humaira .

Komawarta gida keda wuya ta shiga dakin su amma bata samu da’ada ba sai ta zauna a kasan carpet tana jiran dawowar ta

Bata wani jima ba ta dawo ta zauna kasan ita ma sannan cikin fara’a tace ke kwantar da hankalin ki a kan masdook baza kiyi kuka ba insha Allah kin same shi kin gama daga gun baffan ki nake yanzu nasa aka kira min shi baffan naki da abban masdook din na masu bayanin kudurina kuma ba wanda ya musa min a cikin su kamar yadda nayi tsammani tabbas muhammad ya cika dan halas me tarbiya ya maidani tamkar mahaifiyar sa ko dangin su na asali ban taba ce masa yi ba yaki yi ba tankar ni ce na kawo shi duniya.

Komai aisha bata ce ba illa ranta fes take jin sa da wannan daddan labarin hamma masdook zai zamto nawa.

Da’ada waccan fa dazai aura?

Kwantar da hankalin ki ke kadai ce bai isa kawo wata ba .

Dariya tayi na jindadin abunda ta fada ranar baccin dadi tayi.

 

 

Zaune yake kan kujera yana duba wasu takardu a kan tebur din sa tun kafin ya fara duba patients amma ran shi a bace yake ya rasa dalili kawai Allah Allah yake yi ya samu hutu ya koma gida.

 

Wayar shi ya dauka ganin tana ringing kuma sunan abban shi ya gani a kai an rubuta

*abbu* dauka yayi da sauri ya ce salamu alaikum,

Wa’alaikum salam

Ina kwana *abbu* ina gajiya an tashi lafiya

Lafiya lou ina son ganin ka masdook

Abbu yaushe zan zo

Ko gobe ma kazo

To abbu insha Allah zan ajiye komai nazo

To ina sauraron ka.

Ajiye wayar yayi amma fa gaban shi na faduwa abbu be taba masa irin wannan kiran gaggawar ba in ba yau ba wayar ya dauka ya kira yusuf

Hello masdook

Yusuf fada min akwai abunda yake faruwa a nan gida ne?

Aa me ka gani?

Kawai naji a jikina akwai abunda yake faruwa nan gida

Aa feel free har yanzu banji wani abu ba kila sai ka zo din se muga

To ina fata hakan ne

Amin

Amma wai har yanzu bska dawo ba.

Wallahi kuwa kila mu koma tare da wayanan yaran nake son maidawa boarding baffa nake lallabawa ina gamawa zan kaisu munjibir a huta kila su ma su nutsu.

Haka ne amma wayan na yara ?

Da aisha da amira da fadima da mariya da kulthum

Gaskiya kam da ka kyauta

Anyway sai anjima gobe zan shigo insha Allah

Allah baka iko amin.

 

*2017

[

*AISHA HUMAIRA*

 

*5*

*na*

*khairat up*

 

Baffa na zaune a falo shi da abbu suna tattaunawa da matan su kan batun da da’ada tazo musu dashi jiya da daddare

Mama tace to me kuke jira na yin shawara?ai bai kamata ta bada umarni ba ace se anyi shawara inji inono

Ba wai shawara muke nema ba kawai ina ganin kamar masdook zai bamu matsala ban yarda da zancen aisha ba sam sam.

 

Ajiyar zuciya inono tayi tace nima dai kawai naji ne amma masdook yaushe zai tsaya soyayya da aisha fitinaniya kunsan yadda basa shiri da ita

Amma ita aisha tana matukar son sa kuma kunsan aisha humaira ita ce da’ada kuma da’ada ita ce humaira tun bayan mutuwar adda aisha(babar aisha) ta dauko ta ta maidata ta tamkar ita ta haifeta

Ni bana jin masdook zai ketare maganar mu ya ki ba an riga an zama daya amma gaskiya sai aisha tayi karatu in yaso yanzu a daura auran kamar yadda ta bukata tunda sun ci jarabawar shiga ajin gaba dama yusuf ya zo da maganar boarding meze hana su tafi can ta kara girma da wayo tunda da akwai wadda yake so baza a cuce shi ba sai ya aureta

Hmm kai ma dai abbu baka ji me da’ada tace ba bata son a mata kishiya.

Zan lallabata na mata magana har ta sauko amma ai aisha humaira bazata iya daukar nauyin masdook ba.

Haka ne.

Sallamar masdook suka ji a bakin kofar dakin amsawa suka yi ya shigo ya tsuguna suka gaisa gaba daya abbu da baffa suka tambaye shi aiki yace alhamdulilahi.

Abbu yace masdook waye ni a gun ka?

Abbu meya kawo wannan tambayar kuma

Ka bsni amsa

Kai mahaifina ne.

Alhamdulilah da’ada fa?

Bayan ku sai ita

Yayi kyau

To ni a matsayina na mahaifin ka na yanke shawarar daura auren ka da aisha humaira

Da sauri ya dago kan sa gaban shi ya buga ya dinga kallon abbu da sauran mutanen gurin gumi ya tafaso masa.

Umarni nake baka ba shawarar ka nake nema ba ko amincewar ka ba.

Abbu ban isa na ki bin umarnin ka ba kuma zan bi ko da banda komai amma abbu nayi wa zainab alkawarin aure kuma yanzu ys za ayi aisha yarinya ce bata da wayan daxata iya dani

Baffa yace mun sani kuma mun yanke shawarar za a hada da auran ka da wadda kake so kuma aisha zata koma makaranta daga baya ta kuma wayo se ku tare amma za a baka wadda kake so.

Mama tace wannan hukuncij da’ada ne ba namu ba kuma dole a bi maganarta

Insha Allah mama bazan ki ba amma aisha humairan ta yarda?

Kaje kuyi magana da da’ada zuwa jibi zamu san yarda zamu yi

Amsawa yayi ya fita jikin shi ba laka lakwas ba dadi

Dakin da’ada ya shiga jikin sa a sanyaye ya tarar da aisha da fadima da amira suna yar carafke a tsakar gidan wani irin abu ya tokare masa makogwaro tsabar takaici ya wuce cikun dakin suna gaida shi ba wadda ya amsa aisha murna ya cikata ta mike ta yi waje debo ruwa tayi wanka da kwalliya hamma masdook yazo.

A zaune ya samu da’ada tana jan carbi tana ganin shi ta washe baki tsabar dadin ganin shi zaunawa yayi ya kskalo murmushin jindadi ya gaida ta cikin filanci dan yawance haka suke magana shi da ita.

 

 

 

*2017*

 

*Aisha humaira*

*6*

*na*

*khairat up*

 

Masdook na waje na ka gama min komai tunda kake son abar da nake matukar so kaf duniyar nan ina godewa Allah da ya nuna min wannsn ranar masdook dame zan saka maka ?

Bafan ma ita aishan ta fada min gaskiys cewa kuna soyayya ba ai da ka manta da ita ka auri wata can bare

Ya dago da kan sa yana kallon ta cikin msmaki ya nanata *soyayya*ni da aisha humaira yaushe?

Da’ada waya fada miki muna soyayya da ita?

Ita man ta fada min kayi mata alkawarin aure tun bikin isyaka ko ka msnta saboda wadda kake so?

Shiru yayi tsabar takaici koda yaji tayaya da’ada zata hada shi da yar yarinyar da ya bsma shekaru wadda bayan gaisuwa ba abunda yake hada shi da ita ace zasu yi aure.

Tabbas badan ysna ganin girma da darajar da’ada ba da tuni ya karya wannan shirin

Amma humaira zata gane kurenta badai shi zsta aura ba harta yi girman dazata hada masa tugu tabdi jam.

Da’ada Allah kara girma ya sanya alheri ni zan je gun su yusuf

To Allah maka albarka amin.

 

 

Ai ko wata atanpa ta saka yello da ratsin pink a jiki ta daura zanin ta da riga yar firit ta caba uwar hoda da janbaki a fuska ta tsaya jirsn sa ya fito ai yana ganin ta wani malolo ya tsaya masa a makogwaro ya dalla mata harara a fuska sannan ya shiga dakin su ta bishi duk da a tsorace take dashi

Wani kallo daya buga mata seda hantsr cikin ta ya kada ta soma kyarma

Ni kika je kika ma sharri ko nida ke muke soyayya ko?

Dan uban ki ina wasa dake ni zaki ma karya ai ni kike son aura ko zaki aure ni amma zaki yi dana sanin aurena zaki san cewa ni ba saanki bane ba zaki dandanani zan baki mamaki zaki yi danasanin sanin *Masdook Muhammad dikko*

Shiru tayi ya nunata da yatsa

Ta zumburo bski oho dai nidai ina sonka kuma sena aureka sede ka kashe ni na yarda in na matu a ce matsr masdook ce da ace aisha humaira kawai kums ksima dole ka soni yadda nake son ka

Mamaki ya ksma shi haka kika ce ko?

To mu zuba nida ke ya fice waje abunsa yana mamakin karfin hali irin na aisha humaira.

Ta soma hararar hanyar da ya bi ya fita.

 

A waje yaga su nas da yusuf ran shi duk a bace yake ya zauna kawai dirshan ya rasa meke masa dadi

Aa likitan birni daga ina kuma waya taba ka?

Nas kaidai bari kaina ya dau caji

Aa likita da kan sa ai se a sha panadol

Mtsw dadina da kai kennan ka fiya shiririta.

Ni’imatullahi ya katse su danuwa meke faruwa?

Wai ni yarinyar nan zata ma planning?

Wacca yarinya?

Aisha humaira mana

Meta yi inji yusif ya fada cikin xakuwa shi sa nace zan kaisu boarding

Mtsw ai in wannsn ne da sauki

Wai zuwa tayi ta fadawa da’ada cewa ni da ita muna soyayya na mata alkawsrin aure

Ita aisha humaira din

Ita man

Kiran da abbu ya min kenan sun yanke shawarar aura min ita saboda maganar da’ada dole a bita

Tabdi lallai humaira ta hsda ma zafi zainab din fa?

Sai sun duba sun yi shawara.

Lallai an kassara ka an gama da kai me wata aishs humaira zata ms bands tsiwa da rashin kunya da kinji da jawo magana inji yusuf

Ai wai makaranta zaka kaisu ksn nsn ta kuma wayo da hankali

To Allah sa haksn shi yafi alkairi

Amin suka fada banda uban gayyar.

 

Wallahi sai hamma masdook ya aureni ko kallon shi xan dings yi kullum yana dukana ko namsn jikina zai dinga yanka yana ci sai ya aureni

Harda hawayen ta

(Son maso wani)

Ta share kukan ta ita knta ta rasa yadda take mugun son sa bayan tasan ita dashi akwai banbamci

About the author

Hausa_Novels

Leave a Comment