Littafan Hausa Novels

Abotace Ko Kuma Soyayya Hausa Novel Fitattu Uku

Assadiya Hausa Novel
Written by Hausa_Novels

Abotace Ko Kuma Soyayya Hausa Novel Fitattu Uku

 

 

 

 

 

 

 

 

ABOTACE KO KUMA SOYAYYA?

_(SAFANA ALIYU JAWABI)_

08136746004

 

 

 

*IDAN KINA SO TO KINEMA NUMBERS D’IN DAKIKA GANI*

 

 

 

*KOWANNE AKAN FARASHI 200 GUDA BIYU 300 DUKA 500 SAI MUNJIKU

 

 

 

 

*HASASHE*

 

( suspect )

 

 

_writting and story_

 

“`by“`

 

 

*AUTAR MANYA*

 

 

 

 

*FREE PAGE*

 

 

 

 

*BISIMILLAHIR RAHAMANIRRAHIM*

 

 

 

 

sau kowa take daga step ɗin benen..cikin sautin ƙarar takalmin ta mai tsini gakuma ƙarar taunar cimgam ɗinta ƙas_ƙas wanda ya zame mata al,adar rayuwarta…ahaka har taƙarasa sauka daga kan benen zuwa parlourn ƙasan gidansu..neman waje tayi ta zauna akan ɗaya daga cikin manyan kujerun dasuke parloun tare da zage zip ɗin ƴar ƙaramar jakarta wayarta” taciro _ƙirar iphone 11new mordan_ tafara operating ɗinta cikin alamun gwanan cewa.

 

 

Ahaka ta zauna har wajan _30 mint_ batare da ta dena danne danne akan wayar tata ba..secan taja wani ɗan guntun tsaki.mtsww kafin daga bisani..ta kalli agogon dake ɗaure a tsintsiyar hannunta..miƙewa tai cikin azama..tare da ɗaukar ƴar jakarta.takama hanyar fita daga parloun…wata mata na hango tana saukowa daga kan benen parloun cikin shiga ta alfamar ma wadda ta amsa sunanta shiga se ƙamshin turare take zubawa… cikin sauri naga ta ƙarasa saukowa daga kan benen hartana ƙwarewa wajan kiran wannan budurwar.

 

Ke *mimi* wait daka ta tare da saurin zuwa inda take sannan tafara mata magana cikin faɗa!! yanzu *mimi* ke dan bakida hankali kina nufin ahaka zaki fita ? nace ahaka zaki fita ? jibi shigar jikinki waye ze dubeki yace ɗiyar musulmi ce…shin wai ina ma zakije da sanyin safiyar nan kika salallaɓo inda ban ga saukowar ki na biyoki ba da haka zaki fice baki gaya mini ba shin inama zakije yau saturday babu lectures’ ko ban isa kiga yamin ba? .zum ɓuro baki budurwar tayi cikin nuna alamun jin haushin faɗan da wannan babbar macen ke mata wadda da alamun maman tace” sanna tace’ haba *momy* ni maye acikin shigar nan tawa fisabilillahi kowa ya takura min a gidan nan babu mai sona tafaɗa cikin shagwaɓa irinta sangar tattun ƴaƴa..hmm lallai haka ma zakice zaki wuce sama ki canza kayan jikinki ko sena saka waya na zaneki!! cikin sauri da gudu ta juya aguje tana kuka ta kama ƙafar benen ta hau..

 

 

bin bayanta da kallo nayi domin in ƙarewa shigar jikinta kallo dannima inga meye dalilin momy na cewa ƴarta batai shigar da za,a kirata da ɗiyar musulmai ba? baki nasaki ina kallon ƙudirar ALLAH yarinyar mace har mace ga baiwar kyau ga diri sedai sam babu shigar arziƙi a jikinta domin kuwa komai na jikinta a bayyane yake hatta ga shatin inner wears ɗinta ana kallo muraran ta cikin shigar material ɗin jikinta wanda ya bayya tsantsar surar jikinta dama kaff ilahirin baiwar halittar ƴa mace da allah ya bata..uwa uba gakuma uban gashinta wanda akai mata kalba mai haɗe da jan gashi ta zubo da ita har gadon bayanta..mayafin data yafa kuwa bashida maraba da babu..nishi kaɗan kuwa zatai kayan jikin nata su yage tabbas koni dana ganta ban zata tanaji hausa ba “bare har na dan gantata da musulunci..saman benen ta ƙarasa inda ta shiga wani babban parlour wanda yafi na ƙasa girma da tarin kayan more rayuwa wani ɗaki naga tashige a guje sannan ta faɗa kan gado tana kuka haɗe da barbaje pillows ɗin dake kan gadon…. tana cigaba da yin kukan ta se can”naji wayarta ta fara ringing…se kuma naji ta tsagaita da yin kukan nata tare da ɗaukar wayar cikin kuka ta fara..magana wadda na kasa kunne na dannaji dawa zatai wayar sannan kuma lallai wannan wayar mai muhimmanci ce tunda har ta katse kukanta ta ɗauketa sannan kuma uwa uba ina zataje da wannan shigar?….wadda har sanadin dakatar da ita da momy tayi yasaka ta jin haushi harma da yin kuka? ɗaga wayar tai sannan tafara magana hellow sw…………

[4/7, 3:05 PM] Baby Bintu: *FITATTU UKU*

 

*_Na kud’ine *

 

*ZAMU CIMMA BURIN MU*

_(BABY BINTU)_

0810 470 9652

 

*HASASHE*

_(AUTAR MANYA)_

0814 210 5218

 

*ABOTACE KO KUMA SOYAYYA?*

_(SAFANA ALIYU JAWABI)_

08136746004

 

 

*IDAN KINA SO TO KINEMA NUMBERS D’IN DAKIKA GANI*

 

 

*KOWANNE AKAN FARASHI 200 GUDA BIYU 300 DUKA 500 SAI MUNJIKU

 

*ABOTACE KO KUMA SOYAYYA?*

 

 

 

( *Love and romantic story* )

 

*Writing*

 

*By*

 

*Safnah aliyu jawabi*

 

( *Mrs Abdullah*;)

 

*Wattpad*

 

*Safnah aliyu jawabi*

 

*Free page*

 

*BISSMILLAHI RAHAMANIR RAHIM*

 

,,,,,Zaune take gabaki ɗaya hankalinta baya jikin ta da alamu akwai abinda ke damunta,domin kuwa kallo ɗaya zaka mata ka tabbatar da haka ,gabaki ɗaya idanuwan ta sunyi ja sun kumbura. Rungume ta akayi ta bata cikin sauri ta juyo don ganin wanene, murmushi tayi tace,”lil sis are you back?

 

Marairaice fuska wacce ake kira da lil sis tayi kamar zatayi kuka tace,” har yanzu kuka kike?

 

Cikin sauri ta shiga share  hawayan ta tana girgiza kai ,tana sharewa wasu ke bin bayan wasu.

 

Kallon ta wacce ake kira lil sis tayi tace,”ki daina wahalar da kanki,i know it bazaki taba daina waba, Nasani hamma Yazid yafini agunki,kinfi sonsa sama dani,tunda gashi kina niman hallaka kanki saboda shi,bayan kinsan duk duniya bana da kowa sai ke.

 

Duk kansu kuka suke candai batol tace,” ki daina kuka lil sis kanki zaiyi ciwo kinji dearn adda batol?

 

Yau kam babu Baton wani daɗin baki, domin kuwa lil sis kuka take harda shesheƙa ,kallon ta batol tayi gabaki ɗaya yarinyar ta kara jagula mata lisafi tace,”yanzu kina son adda batol tayi ciwo kota mutu?

 

Cikin sauri lil sis tashiga girgiza Kai tana cewa,”a a.

 

,”Yauwa to daina kuka idan ba haka ba ,mutuwa zanyi,rike hannunta tayi ta saita daidai kirjinta tace,”kina jin yanda kirjina ki bugawa?

 

Nod da kai kawai tayi mata tana share hawayan ta.

 

Kallon ta batol tayi tace,”yauwa haka nake ji duk Lokacin da wani yace,” na rabu da hamma yazid ko kuma na daina tunanin sa.

 

Kallon ta lil sis tayi tace,”adda batol ki faɗawa hamma Yazida kina sonsa kinga sai afasa aura masa adda  nadiya.

 

Rufe mata baki tayi cikin sauri ta shiga dube duben ko wani yana kusa yaji abinda lil sis tace,sauke ajiyar zuciya tayi tace,”karna kara jin kinyi irin wannan maganar kinji lil sis ?

 

,”Hamma Yazid aminina ne a idon duniya,saidai aguna shine duniya ta he is my world my heart and soul belongs to him and him alone,Amma ki sani lil sis hamma yazid yayi min nisa, nisan da bazan taba cimmasa ba.

 

Kuka take sosai, lil sis kuwa gabaki ɗaya ma kasa kuka tayi jinta take kamar ba ita ba.

 

Saida ta gama kukan ta sannan taja hannun lil sis suka shiga cikin gidan nasu.

 

Afalo suka tarar da mumma tana kallon wani shiri da ake a arewa 24 ,kallon su tayi tace,”yauwa batol dama yanzu nake shirin zuwa na kira ki, Yazid yana hanya yakira ki yafaɗa miki kuma kin bar wayar aguna.

 

Baki na rawa tace,”to..to..to mumma Allah yakawo shi lafiya.

 

Kallon ta mumma tayi tace,”yanaji bakin ki yana rawa ,Kuma idanuwan ki duk sun kumbura kodai har yanzu ciwon idon ne??

 

“Eh amma yanzo da sauki.

 

“To ALLAH yakara sauki.

 

“Ameen.

 

Ɗakinta ta shiga tayi waka ta fito  sanye da duguwa riga baƙa mai kyau da kyalli, batayi kwalliya ba amma tayi kyau mattuka.

 

Zaune yake ya hakimce saman 3siter yana danna waya,ƙamshin ta daya jine yasa ya juya cikin sauri, Kallon kallo sukewa juna , kowa da abinda yake sakawa aransa,batol ce tayi saurin sauke idanuwan ta ganin hawaye na neman zuba.

 

Ganin haka yasa yazid fashewa da dariya yace,”na ɗauka batol jaruma ce zata iya jure kallon idon jarume kama ta.

 

Troying pelo ta dauka ta jifa masa ,baiyi wata wata ba shima ya jefa mata,namfa suka fara ke waya falon suna dariya,fitowa mumma tayi tana tafi tace,”dama Nasani suwaye idan baku ba?

 

,”Kunyi girma amma har yanzu baku daina halin naƙu ba, kallon Yazid tayi tace,”harda kaima wai kana biye mata,hmmm naga yanda zakiyi batol lokacin da matar sa ta ɗauke shi kika nime abokin wasa kika rasa,abinda zaifi miki sauƙi kawai kima ki fitar da mijin ayi muku aure rana ɗaya duk mu huta.

 

Lokaci ɗaya zuciyoyi biƴu suka buga da karfi ,tuni numfashi ya shiga barazanar ban kwana da gangan jikin su jin maganar mumma, ruwan da mumma da lil sis suka sha suka rage duk kansu suka kafa abaki lokaci ɗaya,saida suka shanye kowa ya ije gorar ruwan ,nanfa suka shiga kallon juna kallo mai cike da ma’anune da dama…..

 

*Tofa makaranta ko yaya zata kaya tsakanin  batol da Yazid ?*

[4/7, 3:05 PM] Baby Bintu: *FITATTU UKU*

 

*_Na kud’ine_*

 

 

*ZAMU CIMMA BURIN MU*

_(BABY BINTU)_

0810 470 9652

 

*HASASHE*

_(AUTAR MANYA)_

0814 210 5218

 

*ABOTACE KO SOYAYYA*

_(SAFANA ALIYU JAWABI)_

08136746004

 

 

*IDAN KINA SO KINNEMA NUMBERS D’IN DAKIKA GANI*

 

 

*KOWANNE AKAN FARASHI 200 BIYU 300 DUKA 500 SAI MUN JI

 

 

 

*ZAMU CIMMA BURIN MU*

_(BABY BINTU)_

 

 

 

_Praise be to Allah, Lord of the world_

 

_praise be to Allah who created men and empower him with knowledge_

 

_peace and blessing of Allah be upon beloved our prophet his family and his friend, the prophet Muhammad s.a.w Said wisdom is a lost property to the believer where ever it he pound it_

 

 

_*NOTE*_

_It is fiction to be like a true life story, I don’t do it to curse or abuse somebody, I guess if it comes across your life story am apologizing, I don’t do it because of you_

 

 

_*IN THE NAME OF ALLAH THE MOST GRACIOUS THE MOST MERCIFUL*_

 

 

*TA’BA KALASHE DAGA .

 

 

 

*General hospital kawo kaduna*

7:00 am

 

 

 

Haka agogon dake cikin hospital d’in yanuna sansanyar iskar safiya sai kad’awa take yayinda kowa yaketa hada hada acikin asbitin majinyata da masu kula dasu likitoci sai Kai kawo suke aworld world

 

Zafin So Hausa Novel Complete

 

Kwance a emergency world numfashin shi Yana futa sama sama ga oxygen clinder ama’kale afuskan shi da alamu yanajin jiki gefe guda wata dattijiya ce wacce bazata haura shekaru hamsin ba aduniya kuka take tana shar’ban majina idanun ta sun kad’a sunyi jawur idonta akan wanda yake kwance ta’kura mai ido ko kiftawa batayi Addu’ah kawai take Allah yatashi kafad’un shi ita tunda take Bata taba ganin kalan wannan soyayya ba….. sallama akayi daga kofa aka shigo hakan yakatse Mata tunani dasauri tawaiga sai Kuma tazabura tana nunata da yatsa Amma muryanta baya futa sosai kuka tafashe dashi tadu’ka ‘kasa cikin makyarkyata tace

 

 

“Baiwar Allah kiwa Allah kiwa Annabi kirabun min dajika shikad’ai yarage min aduniya kitaimaka kinisancemu indai son dakike ikirarin yimasa nagaskiyane ki…….

 

 

 

Cikin kuka itama tadu’ka kasa tace “kaka wallahi bazan TA’BA iya rayuwa babu Yazidullah ba shine fitilar dake haskaka rayuwata sanadiyyan shi NASAN waye d’an Adam asanadiyyan shi nasan me akekira da daraja dan Adam shine yakoyar dani darussan rayuwa shine yakoyar dani yanda zan bautama Allah wallahi Kaka inkikace narabu dashi mutuwa nima zanyi kitaimaka min yau mubar garin Nan namuku alkhawari zamuyi nisanda mommy bazata TA’BA gano inda mukeba Kaka karkice min intafi karki Kara korata kaka please….. kukane Mai karfin gaske yaci karfin ta”

 

 

Hayaniyar su tasa yafara ‘ko’karin bud’e idanu sakamakon jin muryan abunda yake muradi dare darana yasake gani Koda daga nesane, ahankali yakai hannunshi yacire oxgen d’in yanayin ido biyu da ita yayi wani irin zabura yasauka agadon saigashi agabanta

 

 

Cikin tashin hankali kaka ta’kara fashewa dakuka tana kallon yanda suka kura ma juna idanu kowanne bakin shi sai makyarkyata yake haka jikin suma alamu suba son suyi magana

 

 

Cikin karfin hali yace “darling”

 

 

“My Yazidullah I miss you so much sai Kuma tayi hugging d’in shi kamar wata zata kwace Mata shi, shima rungume ta yayi back suka fashe dakuka mai cin rai, kaka ma kuka take tarasa meke Mata dad’i idanunta sun jeme saboda kuka kanta sarawa yake sosai daurewa kawai take

 

 

Cikin kuka Yazidullah yace “darling why zaki za’ba barin iyayen ki da gatan ki kizo gareni alhalin ni talaka NE Wanda baida cin yau balle na gobe kikalli yanda mommyn ki yasa akamin tasa an wula’kanta mu tasa an tozartamu duk akan muna son juna shin meye laifin zuciyata dan takamu da soyayyar ki shin meye laifina kifad’a min pleaseeee tell me what’s my fault tell meeee yafad’a cikin tsawa gamida da tureta tayi baya kamar zata fad’i saikuma tadafa bango haki kawai take dakyar tatsaida kukanta tace

 

 

“Kasani duk abunda mommy tamuku Banda masaniya sai yanzu nasamu nafito naje gida akacemin ai ankoreku Kuma kana hospital three days Ago bakasan wake kankava kaduba mu’ujiza irin ta Allah inazuwa saigaka kasamu lapia Yazidullah kasani nice mahadin rayuwar ka kaima haka nice komai naka kataimake ni kuzo mubar garin nan kodan *MUCIMMA BURINMU* domin daga yanzu zuwa kowane lokaci iyayena zasu binciko inda nake Kuma zasu kamaka kataimake ni kuzo mutafi dan Allah”

 

 

Cikin karfin hali yace “bazan TA’BA tafiya dake ba inaso kikoma kima mahaifiyar ki biyayya but please do me a favor, promise you will be mine yafad’a Yana kallon ta ido cikin ido

 

 

Kuka tafashe dashi tace “ha’ki’ka nitakace har abada dukkan namijin daya aure ni ya aure gangar jikina ne Amma zuciya da ruhina suna tare dakai kamin alkhairi d’aya”

 

 

“Tell me and I will do it Insha Allah”

 

 

“Kadawo gareni konan dayaushe NE zanjiraka karka rabu da soyayya ta duk runtsi duk wuya tunda munce tunanin mu d’aya ruhin mu d’aya wajen zaman mu d’aya anan cikin duniya har a lahira muna tare shine alkhawarin dazakamin kawai”

 

 

Kallon ta yayi idanun shi sunyi jawur yace “loving makes me whole this our love will never died darling promise you will be mine I come back for you darling you hold my life you are my praise u be always on my mind promise you wait for me I’ve think of you every day my love I will pray for you everyday my lov…….. Maganan shi yama’kale ne sakamakon ganin police d’in dasuke shigowa dagudu kusan su Ashirin kowanne d’auke da bindiga ga karnuka kamar za’a je Kama ‘barawo

 

 

 

Dasauri kaka taje takama Yazidullah ganin shi suka haro suna saitashi da bindiga shima RIK’E ta yayi suka fashe da kuka Mai cin rai

 

 

Mommy NE tashigo tana taunan chewing gum ga black space datasaka cikin Isa ta’karaso gaban ta tamata wani kallon baki da hankali sannan tafallama mata Mari ajere har sau biyu tace “khairat Ashe Baki da hankali ban saniba Ashe dama bonono kikamin kikazo wajen wannan matsiyacin Wanda baisan darajar manyaba to wallahi kinja Masa zai Kare rayuwarsa agidan kaso Kuma awulakance office kutafi dashi idan wannan tsohuwar najadun tahana kuhad’a harda ita”

 

 

Wani uban ihu da kururuwa khairat tasaki cikin d’aga murya tace “mommy wallahi idan kikasaka aka kulleshi saina kashe kaina k……..”

 

 

Cikin zare Ido da daka Mata tsawa tace “kin Dad’e Baki kashe kannaki ba mara mutunci Wanda batasan darajar kantaba Kuma aure dake da Alhaji mansur babu fashi ko gawarkine sai ankai Masa gidansa tafad’a tana janta sukai waje suka bar police na kiciniyar karban Yazidullah ahannun kaka domin tari’ke shi tamau shima haka kaka sai kuka take tana Basu ha’kuri Amma Basu san tanayiba

 

 

 

Cikin rashin imani suka hau dukan Yazidullah dasauri kaka tatare aiko Babu tausayi suka ci gaba da dukan su Saida suka musu lilis numfashin Kaka sai fisga yake sannan suka d’ebe su sai station

 

 

Hankalin Yazidullah yatashi ganin idon Kaka Yana kakkafewa kumfa nafuta abakinta hannun shi tari’ke cikin tsananin azaba tace yazid kasaurara kaji mezance maka, dasauri yamatsa da kunnen shi kusa da bakinta wasu maganganu tafad’a mashi gaba d’aya jijiyoyin kanshi duk sun mi’ke idanun shi sun kara yib jawur adaidai nan suka kawo station.

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Acikin mota khairat sai fusge fusge takeyi tana kuka amma mommy tamata ri’ko Mai tsauri suna zuwa gida tasaka wasu police Mata tace sukulleta apartment d’inta kashedi tamasu dacewar Kar Wanda yabud’e ta sai idan za’a Kai Mata abinci duk Wanda yabarta tafito abakin aikinshi tana Kaiwa Nan tashige apartment d’inta ranta ajagule datunanin mafita gwara takira Alhaji Mansur yazo ad’aura auren tasan idan akayi auren dole khairat tazauna dawannan shawaran ta’karasa bedroom d’inta rage kaya tayi taje tayi fresh up

 

 

 

Bayan tashirya ne takira Alhaji Mansur sunjima suna tattaunawa sannan sukai hanging call d’in

 

 

 

Dining tanufa hankalin ta kwance tafara yin lunch bayan me aikinta tayi serving d’inta takusa kammalawa ne saiga Kira awayanta cewar Allah yayima kaka rasuwa dan haka zasu saki Yazidullah yasamu yaje Jana izarta inyaso wasu police zasubi shi da andawo sai sud’auko shi, jikin ta yayi sanyi amma saita dake tace “commissioner !!!

 

 

“Na’am hajjaju Samrah”

 

 

“Zan turo driver na da kud’i kubashi kuce yabar garin Nan kumai kashedi sosai kutabbatar Mai da inkuka ganshi a state d’innan gaba d’aya saikun kashe shi understand”

 

 

“Yes ma’am angama saina ganshi” cutting wayan sukai, direct bedroom tanufa tahad’a kud’in awani karamin jaka naira million d’aya driver ta Kira Yana zuwa tabashi jakan tace yakai station yanzu yadawo, cikin girmamawa ya Amsa batare dayasan menene acikin jakan ba.

 

 

 

Washa gari da misalin 3:23 Alhaji Mansur yadira agidan apalourn bak’i akamai masauki inda Yan aiki suka cika mai gaba da kayan motsa baki amma shi duk bataso yakeba burin shi yaga yar shilar da Hajiya tace tatanadar Mai akasa yaketa narka kud’i akanta Allah dai yasa akwai kaya yanda yakamata.

 

 

 

Tunda akasata ad’akin datakirada kabarin duniya take ta rasgar kuka kamar me jitake kamar takashe kanta tahuta amma Yazidullah yanuna Mata illar hakan Koda aka kawo Mata abinci ko kallon shi batayiba haka ma nadare bataciba saidai suka zo suka d’auki abunsu

 

 

Arana d’aya tajeme tayamutse kamar ba khairat Mai jida class da kwalliya ba kamar ba itabace mai ta’kama danuna izzar Nan ba saigashi lokaci d’aya akan soyayya tazama abun tausayi yanda taga dare haka taga rana domin barci duk iya satan shi nan yaganta yakyale

 

 

 

Washa gari haka tawuni bataci komai ba gaba d’aya tagalabaita dan zuwa lokacin dakyar take iya yin kukanma

 

 

 

Mommy NE dakanta tashiga d’akin direct toilet tashiga tahad’a mata ruwan wanka sannan tafito tajata zuwa toilet d’in batare data damu da halin datake ciki ba tamata wanka tasake kamota zuwa palour kwalliya tafara Mata anan ne khairat tabujire aiko tasha mari dan dole mommy takyaleta tabata Kaya cikin tsawa tace tasaka tana jiranta apalourn bak’i

 

 

 

Da har ta’ki shiryawa sai kuma take ganin this is the last opportunity datake dashi passport da ATM d’inta tad’auka ta’boye sannan tayi dressing normal harda hijab zuciyar ta na jaddada Mata cewa remember that come opportunity once in life kartayi wasa da Daman ta haka tayi ta karfafa makanta gwiwa.

About the author

Hausa_Novels

1 Comment

Leave a Comment