Littafan Hausa Novels

Abadan Hausa Novel Complete

Written by Hausa_Novels

Abadan Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

Abadan Hausa Novel Complete

DA ‘IMAN*

 

 

⏯1⃣

 

 

 

A hankali ta tsallako tatitin kai tsaye kuma ta shige dogon layin dake gabanta,ta dubi tsahon layin duk da yawan al’ummar da yake da shi a dade yake babu kowa tankar anyi shara,hakan baya rasa nasaba da irin ranar da ake kodawa kamar mutum yaa dora hannu akansa yace wayyo Allah

 

Doctor Yusuf Hausa Novel Complete

sannu a hankali take ci gaba da tafiya tamkar mai tausayin qasa,a zahirance idan ka ganta sai kayi tsammanin ranar bata dameta ba saboda yanayin yadda take tafiya,saidai sam tana daga cikin wadanda rabar ma tafi gallaba,don har Allah Allah take taga ta isa gidansu,saboda leshin dake jikinta dinkin riga da skert da kuma dogon hijabinta mai hannu dake qara mata zafi wanda ya zamo too match ne da kaya jaka da ‘yar jakar swagger dake maqale a kafadarta

 

 

babu wata doguwar tafiya ta iso qofar gidan nasu wanda ke rukunin gidajen marasa wadata,duk da ginin bulo da bulo ne saidai bai samu arziqin fulasta ba bare a kai ga fenti,ta cire jakar kafadarta tana shirin shiga soron gidan idanunta ya sauka kan hauwa wadda ta cakare cikin kwalliyar atamfa,wani matashin saurayi ke fiskantarta wadda yanayin tsaiwar tasu kawai zai fahimtar da kai zance suke,dauke kanta tayi tamkar bata gansu ba don wannan dabi’a ta hauwan bama ita ba duka yaran gidan na bata haushi

 

 

ta tsakiyarsu ta raba zata wuce kasancewar babu wata hanya sai ita taji saurayin na fadin‘’barka da dawowa antyn mu‘’

‘’yauwa sannunku‘’ta amsa masa ba yabo ba fallasa tare da shigewa cikin gidan

hauwa dake binta da harara kamar qwayar idonta zai fado ta ja wani matsiyacin tsaki

”gaskiya haruna kana bada ni wallahi,wai ksi me yasa kullum baka da,burin da ya wuce ka yarfani a gun wannan matar ne,me ma kake nufi ne ni fa ban gane ba”

”yanzu laifi ne kulu don na gaisheda yayarki,kuma fa kin sani tana da kirki wlh,uwa uba ilimi da nutsuwa”

cike da masifa hauwa ta qwalalo ido

”iyeee,to ko zaka koma gurinta ne haruna,a gabana zaka dinga yaba wata uwar mata da ta shekare gaban iyaye aka rasa mai dauka?”

 

 

 

ganin hauwan ta hau da yawa yasa ya sassauto”haba kulu na,wata kai yake a gurina ai kema kin sani,ni mai zanyi da wata mace a duniya indai ba ke ba?”

duk da koda tan da yayi ta dade a kumbure kafin ta sauko ta yarda suci gaba da tadinsu

 

 

sallama tayi tsakar gidan kamar yadda ta saba duk da ta san babu mai amsa mata matuqar ba mamanta bace a tsakar gidan ko hindatu,ile kuwa bata samu kallon arziqi ba bare na tsiya duk da inna hadiza dake zaune gabas da tsakar gidan nasu tana kasa wake da shinkafar siyarwarta cikin samirun da duka suka sha lamba,zaune kusa da ita kuma huwaila ce ke nata zarafin na qulla kunun tsamiya cikin farar leda tana lodawa a botiki

 

 

bata fasa ce musu sannunku ba kamar yadda basu fasa ja mata tsaki ba tare da binta da harara har ta cire toms dinta ta kwashesu a hannunta don gudun samun sabani ta shige rumfar mahaifiyarsu ba da sallama,tana iya jiyosu sun fara sana’ar tasu wato yada habaici da baqaqen maganganu

”hmmm idan da ranka kasha kallo,kaje ka gama yawon dandinka ka dawo dakin uwa kayi zamanka”

”kema huwaila idan banda abinki a banza suka qi aurar da ita?ba ana fasa musu kai da cewar kyakkya wa,bace ‘yarsu?,ai dole su maisheta jari”

”hmmm,Allah wadaran naka ya lalace kuwa,wataran kuwa za’a dire abun kunya cikin gidan nan,a juri,zuwa rafi da tulu debo ruwa”

 

 

duk sunajin abunda suke fada daga ita har maman tata,wanda idan da sabo tuni sun saba,saidai babu mai tanka musu,kan dadduma ta taradda maman tata,da alamu sallar azahar take abatarwa,saboda haka ta sabule jakarta ta ajjiyeta saman kujera hade da hijabinta ta sake yowa tsakar gida don,dauro alwala,har ta gama,alwalar tata basu fasa muna nan maganganganunsu ba,babu wadda ta daga kai ta kalla a cikinsu duk da irin suyar da zuciyrta ke mata da radadi,ta ajjiye,silifas,din da ta daura alwalar tana niyyar shigewa rumfar tasu

 

 

isyaku dan wajen inna,hadiza ya tawo a guje hannunsa dauke,da kwanonsha cike da kunu,bata ankara ba taji shi yana bin skert dinta ziwa qafafunta,da,sauri ta kalli yaron dake tsaye qerere ya zuba mata ido tace”haba isyaku me yasa baku iya tafiya ne a hankali?”

baki ya murguda ya galla mata harara

”eh din,ba sai a koya min ba,ban iya ba,aikin banza taqi aure ta damu mutane cikin gida”

ranta ne yayi masifar baci,yaron da a qalla ta bashi shekaru kusan goma sha biyar shi zai tsaya a gabanta yana gaya mata haka,hannunshi ta,finciko ya qaraso gabanta,kafin ta aiwatar da komai ta jiyo muryar inna hadiza cikin kaushi da haya gaga tana fadin

”ke,kada ki kuskura ki taba min yaro wallahi,idan kuwa kika sake hannunki ya kai kanshi to zamu kwashi ‘yan kallo dake wallahi”

 

 

bata saurari kurarinta ba ta yarfawa isyaku mari domin dama ko da,safe kafin ta fita sai da ya mata wata tijarar kuma tana kallo bata ce uffan ba sai dariya ma data sheqe da ita ,ai kuwa kanta tayo yana fadin

”kutumar uba,wallahi yau sai kin gane shayi ruwa ne”

gadan gadan ta nufota wand hakan yayi daidai da shigowar malam mamuda cikin gidan

”kai kai lafiya?”

”yauwa malam gwara da Allah ya kawoka,wallahi mun gaji da zaman wannan balagaggiyar tsakaninmu,ita ba aure ba ita ba karuwanci ba,ta ishemu ta ishi yarranmu?”ya katseta da fadin

”to yanzu me kuma ya faru?”

”wai wannan dan talilin yaro ta daddage ta zabgawa mari don kawai ya zuba mata kunu bai sanig bau,to wallahi ba zan yarda ba,ko ya rama ko ni na rama masa da kaina”

 

 

”kai isyaku me yasa haka”

”baba ban sani bane ba fa,kuma ni wallahi sai na rama”

”ke *maryam* bashi haquri”

babu yadda ta iya haka tace kayi haquri

shi kuma ya tubure ramawa zaiyi,da qyar uwar tasa ta lallabashi ya haqura

hawaye na bin kuncinta ta shige dakin nasu,maman na zaune bisa daddumar yadda ta barta ko motsawa bata yi ba bare tasa baki a cecekucen da akeyi,bata ce da maryam din uffan ba kamar yadda itama batace din ba,ta dauki dadduma guda daya daga inda suke ajjiyewa ta tayar da sallah

 

 

ta dade akai tana miqawa Allah kukanta kafin ta sallame,tana ninke sallayar ne taji maman tace

”na sha gaya miki maryam dole kici gaba da haquri matuqar dai kina zaune ne cikin gidan nan”wasu sabbabbin hawayen ne suka zubo mata,ta koma gefan daya daga cikin kujerun falon ta zauna tana fadin

”mama,ke kanki shaida ce akaina,amma duk yadda kakai ga haqiri wataran mutanen gidan nan sai sun saka kayi misbehaving,yanzu mama kamar isyaku fa qanin bayana mama?”

”ya isa kada ki saka abun cikin ranki,Allah yana tare dake ba wai ya manta da ke bane”

cikin sanyi wanda ya zamto halittarta ta goge fuskar tata cike da tawakkali da miqa lamuranta ga Allah

”to mama”shine abunda ta fada a sanyaye

 

 

 

*ABADAN*

 

 

 

 

*assalamu alaikum masoya,xaku ga nun canzs sunan littafin mu zuwa ABADAN,haka ya faru ne sakamakon yin wani littafi a baya mai wannan sunan,ina muku fatan alkhairi*

 

 

 

▶2⃣

 

 

Hundatu ce tayi sallama ta shigo rumfar sanye da unifoam ruwan tsamigaye riga da zani sai farin hijabinta kafadarta rataye da jakar makaranta fara,tana cire takalminta hade da socks tace

”anty maryam ya na ganki yau a gida da wuri?”

dan dafe kanta tayi kadan tace”yau da wuri na kammala aikin ne shi yasa,kuma dama bana jin dadi sosai”

cikin nuna damuwa ta zauna saman kujera

”sannu antin mu,ko na karbo miki magani?”

murmushi tayi har fararen jerarrun haqoranta suka bayyana

”idan banda abun hindu wanne me chamist za’a samu da uwar ranar nan?”

ta dage gira”haka ne fa anty”

”ki duba locker kusa da gadona akwai paracetamol ki dauko ki sha,tuntuni da kika shigo baki gayamin ba har kika tsaya fada da mutane ko?”

 

 

ta karyar da kai ”ayyah maman mu ba haka bane,sallah kinga muka gama yanzun ai”

”dawa antin tayi fada mama?,wannan maras kunyan ne isyaku ko?”

”shine mana”

a fusace ta miqe zata fita maman ta yi kiranta

”ina kuma zaki?”

”mama don Allah ki barni naje naci uwar yaron nan don Allah,yayi matuqar raina yaya maryam,dan iska mara kunya kawai”

”ko da wasa naji kinje gurinsu sai na sabarmiki”

ba haka taso ba amma babu yadda ta iya haka ta wuce daki tana kumbure kumbure ta sauyo unifoam dinta ta dawo dan kitchen dinsu wsnda daki ne gudun tashin hankali suka maida shi kitchen ta zubo musu shinkafa da miya da salad da maman tayi a faranti daya,duka suka sa hannu

 

 

hindatu tace”dama zamu samu ruwan sanyi yadda ake zabga ranar nan wlh”

”ai insha Allahu da na dauki albashina,zan siya mana qaramin firji”

cike da doki hindatu tace

”eh wlh yaya”

mama ta dubi maryam din”yanzun maryam ba zaki yiwa kanki fada ba?,bama zancan aure kike ba zancan siyan firji kike ki saka mana,duk yadda mutane ke maganganu tamkar ma ke din baki damu ba maryam?”

 

 

duk sai taji abincin ya fice mata a ka,ta sunkuyar da kanta,Allah ne kadai yasan abinda take ji a zuciyarta,itakam tasan ba domin mamanta bata sonta take mata wannan fadan ba,tana yine sabida qauna,ita din ma da za’a tona zuciyarta tabbas babu dadi

 

 

 

 

Zaune take cikin rumfar tasu wadda ke da madaidaiciyar yalwa,kujeru ne one sitter two sitter da kuma three sitter masu dan sauqin farashi,falon malale yake da tyles ruwan madara da labulaye suma ruwan madara masu sauqin kudi,sai kayan kallo da suka hada da t.v ta xaune da d.v.d,komai na falon madaidai cine dai dai talaka wanda albashin maryaman ne da qoqarinta ya kai falon ga zama haka

 

 

kusan kaf gidan babu muhallin da yakai tsaftar nan,ko yaushe zaka sameshi a goge qal yana qamshin turaren garwashi ko na tsinke,hakan ke qara haddasa qiyayya da kishi mai zafi tsakanin mama *amina* da sauran abokan zamanta

 

 

sanye take da pakistan riga da wando wanda rigar tasa ta kai mata har gwiwa,dan kwalin pakistan dinne daure a kanta,duka hankalinta ta tattarashi kacokam kan wayarta da tayi googling din wasu sabbin girke girke,shirun da dakin da ma gidan baki daya da yayi shi ya qara mata nishadi da fahimtar abunda take karantawa,

 

 

sallamar da ta jiyo anayi cikin tsakar gidan ita ta ja hankalinta,ta sauke wayar tana amsawa tare da cewa ”a shigo”

mai sallama ta sake maimaitawa lokacin da take shigowa rumfar tasu,da sauri maryam ta sauke wayar a gefanta fuskarta dauke da murmushin farinciki wandayayi sanadiyyar bayyanar dimple dinta ta miqe

”radiya..saukar yaushe kenan mutanen south africa?”

harara wadda aka kira da radiyan ta cilla mata

”hmmm,babu wani nan,wlh baki da abinda zaki kare kanki da shi,yanzu ma ni ba gunki nazo ba,mama na kawowa jikanta ta ganshi”

”oh ni maryama,laifi baya qaremin,me kuma nayi”ta fada cikin murmushi da dafe kai

harararta dai ta sakeyi”kinfi kowa sanin laifinki maryam,sati na guda da dawowa qasar nan amma ko mai kama da ke ban gani ba,ina dira nigeria kece ta farko da na fara yiwa tex amma ko matsayin reply ban samu ba”

 

 

”yanzu dai yo haquri don sonki da annabi ki zauna tukun,don mama bata nan ta tafi kitso”ta fada tana karbe kyakkyawan baby boy din dake sabe a kafadarta,tare suka zauna idon maryam na kan yaron”masha Allah laquwwata illa billah fadil”yana kan kadarta ta shiga kitchen din su ta dauko mata ruwa da lemon sobo cikin fridge din da daqyar ta shawo kan mama da dadin bakin hindatu aka siyoshi suke lemon siyarwa a kuma fita kunyar baqi idan anyi

 

 

”bismillah”tace da ita bayan ta tsiyaya mata lemon

”bani dana kawai na wuce”

”haba sister,kada fa ayi mana dariya a ganmu a rana”

”ke kika jawo hakan ai”

”kinsan Allah banga saqonki,ki yarda dani bani da lokaci wallahi yanzu isashshe idan ba weekends ba saboda aiki”

da qyar ta samu ta shawo kan radiya bayan ta mata alqawarin zuwa mata a wannan weekend din wanda daga nan suka fada hirar duniya

 

 

radiya ta ajiye glass cup din bayan ta kalli maryam

”maryam har yanzu dai batun aure shiru?”sakin ajiyar zuciya tayi sannan ta tabe baki

”hmmm,barni kawai radiya,samun miji na gari yanzun ya zamo wuya,mazan yanzu duka ‘yan garari ne,yawancinsu ba aure ke kawosu gurinki ba”

”anya maryam,bana manta fa yawan samarin da kike da su tun muna school”

”radiya kenan……manta da wannan,na fada miki yawa yawansu ba don Allah suke sonki ba,sun lallabo ne kawai su kwashi abunda suka kwasa na rasa wannan masifa kamar hadin baki?kamar ni kadai sukewa haka,ke dai ki sani kawai a addu’a radiya”ta qarashe maganar muryarta na dan rawa alamun kuka keson zuwa mata

”shikenan maryam,insha Allahu na miki alqawari ba zan fasa sakaki cikin addu’o’ina ba,komai yayi farko yana da qarshe”

 

 

a hankali suka fada wasu hirarrakin nasu a haka maman ta cimma su,tunda ta dauke fadil bata dawo da shi ba sai da zasu tafi,sabulai ta bawa radiyar sinqi biyu da turare,hannu biyu amsa tayi mata godiya sannan maryam ta amsheshi ta biyo radiyan qofar gida don raka ta

”ke da nasir fa muka zo”

cikin mamaki take kallin radiyar”amma baki da mutunci,ki bar bawan Allah a mota duka lokacin nan yana zaman jiranki”

fuska ta yatsina”rabu da shi,fada mukayi da shi sulhu yake nema shi yasa”

”Allah ya shiryeki radiya ”abunda ta samu ta iya fada kenan don sun qaraso gaban motar”

 

 

gidan gaba ta shige ta dora mata fadil saman cinyarta suna gaisawa da nasir din

”munfa yi fushi maryam gaskiya”

sassanyan murmushinta tayi”to ayi haquri tunda na wanke kaina next week ina tafe insha Allahu ranan sunday”

”to Allah ya nuna mana”

sallama sukayi ta koma cikin gidan radiyan na jaddada mata ta cika alqawari fa

 

 

 

 

tana cusa kai gidan suka ci karo da *BINTA*

dauke da botikin awara zata fita inda aka fi kaurin,maryam dince ta fara ja da baya don tasan bata qi ta bangajeta ta wuce ba,duk da hakan ma dai bata tsira ba daga tsaki da harar da qanwar bayanta ta saba jifanta da su ba koda zasu hada hanya ne sau miliyan

 

 

ta rasa me ra tsarewa yaran da iyayensu,gaba daya anbi an cika zukatansu da qinsu,qannenta ne duka amma babu daya dake ganinta da gashi,saidai duk da haka rashin mutunci wani yafi na wani

ga tsantsar rashin tarbiyya da qin karatu da aka dasawa zucoyoyinsu,ta rasa wannan wacce iriyar rayuwa suka zabawa kansu,da wannan tunanin ta qarasa falonsu ta zube saman kujera tana rowon Allah daukinsa kan halin da take ciki

 

 

 

*mrs muhammad ce*

 

 

*ABADAN

 

*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*

 

 

 

 

 

 

▶3⃣

 

 

 

 

 

sanye take da material silk dark pink wanda aka yima ado zane na qaqen flowers manya,yayin da ta yane kanta da mayafi baqi tayi rolling dashi wanda ya maisheta tamkar jinsin larabawa,qaramar jaka ta sagale a gwiwar hannunta sai baqin toms mai kyau,sosai shigar tayi mata kyau tamkar bata da wata matsala a rayuwarta

 

 

a rumfa ta tadda mama tayi mata sallama tace mata a dawo lafiya ta gaida fadil da mamarshi,suna zaune a tsakar gidan kamar ko yaushe ko wacce ta maida hankalinta kan kayan sana’arta,wanda da zaki tambayesu suk cikinsu babu wadda zata iya gaya miki taqamaimen inda yaranta suke,sana’arsu ta fiye musu komai

 

 

da sauri ta fara qoqarin ficewa daga gidan don bata fatan daya daga cikinsu ta,ganta balle ta jefeta da kalmar da zata bata ranta,saidai duk iya saurinta bata ci nasara ba sai da huwaila ta ganota

”uhmmm,mutanen burtali,an fita kenan”

bata fasa sauri don ta fice a gidan ba kamar yadda bata ko waiwayo ta dubesu ba

 

 

cikin soron sukayi kacibus da *AZARA*,qanwar ta ce ta hudu wadda tayi aure da yaranta uku,ba laifi mijinta na iya bakin qoqarinsa duk da wasu abubuwan bai iya dauke nauyinsu,sai kuma Allah ya hadashi da mace mai izgili izza da rainuwa,azara akwai rainuwa da izgili saidai ba laifi rashin kunyanta da sauqi akan ta sauran yaran,tunda ko babu komai idan sun hada zata tsaya su gaisa koda zata jefeta da habaici a fakaice

 

 

yanzun ma hakance ta kasance,fuskar maryam din fadade da murmushi ”maraba da mutanen fanshekara(unguwar da take aure)”ta fadi tana miqa hannu zata amshi yaron axaran yaqi zuwa saboda dan banzar qiwar da yakeyi,azaran tace

”hmmmm,sannunku kuma”

”azara yaron nan qiwa yake haka?”

”ko ba ya qiwa aike yayi miki tunda ba ganinki yake ba,mu ko nsmu gidan ba’a zuwa saboda bamu da komai”

murmushi maryam tayi,don ta fahimci inda tasa gaba

”ko daya ba haka bane azara,kinsan bani da lokaci sai weekends,to su din ma sai wani zarafin ya shigo ya cinye wunin naka duka”ta kawar da maganar don kada tayi nisa ta hanyar cewa

”ina sauran yaran?”

”kunun aya ne bai qare ba na,barsu su qarasa saidawa don kada ya lalace shi yasa ma ban taho da su ba”

 

 

wani abu ya tokare maryam,wato irin rainon da aka mata shi zata yiwa nata ‘ya’yan,a maimakon ta bata amsa da sun tafi islamiyya don a yanzu lokacinta ne sai tage gaya mata ta barsu gun talla?,du du du yaran nawa suke?,kamar tayi mata magana kuma sai taja bakinta ta tsuke don kada cibi ya zama qari

”sai ina kuma?”azaran ta tambayeta bayan ta gama qare mata kallo

”wallahi zani gidan raliya ne”

”hmmm,babban goro sai magogin qarfe,su ai sun isa ayi da su din,bari na qarasa ciki ko,sai kin dawo”

danne zuciuarta tayi ta murmusa

”to shikenan,idan na dawo na tadda ke to”

”o’o,anya zaki tadda ni kuwa,wannan fitar taku ta manya wa yasan ranan dawowarku”

”to ki gaida gida”

”gida zaiji”

 

 

tana tafe a layin zuciyarta cunkushe da tunane tunane,hasbunallahu wa ni’imal wakeel ta dinga karantawa har ta iso titi,akwai qarqncin motocin haya kan titin nasu ko kuma ace kusan duk wadda tazo cike take da ‘yan makarantar boko da suke dawowa gida,kusan motoci uku ne suka tsaya don bata lift saidai ko kallo basu isheta ba,hakan,na yawan faruwa da ita kasancewar unguwar nasu na maqotaka da unguwar nasarawa G R A,duk sanda hakan ta faru takan yawaita neman tsarin Allah,sannan takaici mamaki gami da tsoron maza kan sake yawaita cikin zuciyarta,basu da burin da ya wuce suga sun samu damar da zasu shiga rigar mutuncinki su wuce su barki babu batun aure

 

 

da qyar ta samu wata da yara yan makaranta biyu a ciki,ta masa kwatance inda zai ajjiyeta

 

 

cikin murna raliya ta tarbeta,cikin falonta suka zube bayan ta cikata da kayan ciye ciye suka hau hirarsu da bata qarewa fadil na bisa cinyarta,

”kinga kawo fadil din na riqe miki shi tunda yayi bacci ki samu kici wani abun,idan ba haka ba bazai barki kici komai ba”

”a’ah qyalemin shi”

cikin haka wayar raliyan ta soma tsuwwa,ta cirota ta duba screen din tana fadin ”abban fadil ne”

magan sukayi ta tsawon minti biyar sannan ta kashe tana duban maryam bayan ta miqe

”yace yana miki sannu da zuwa,bari,na saka miki wani film ya dan debe miki kewa ni shiga kitchen ya kamani,abban fadil ne zaiyi baqi”

”haba kema raliya naji zancan shiga kitchen kuma na zauna,ai kinsan sai anyi da ni”

”sannu uwar madafa”ta fada cikin zolaya

”na karba,ko kin manta kan abinda na samu degree kenan”

”wannan gaskiya ne,bani fadil din to na kwantar da shi sai mu wuce kitchen din ko?”

 

 

qarfe hudu da mintina ashirin suka kammala,lafiyayyen girki ne wanda maryam ta gwada basirarta akai,ita kanta raliya komawa tayi gefe tana kallonta don bata zaci qawar tata takai haka ba,biyar saura ta suna falo,ta soma hada kayanta don tafiya gida ”amma diyana(haka suke kiranta wani lokaci a makaranta)ki sake wanka mana wannan aiki da kika sha”

”ai dole ne,amma fa idan na isa gida”

”ai ko wlh anan zakiyi”

murmushi tayi wanda har dashashinta sai da ya bayyana

”kinsan dai bana wanka na maida kayan da na cire,ni kuma ban taho da spare ba”

”tsarabarki ta south africa tana nan,saiki zabi daya a ciki kisa”

duk wayon,maryam sai da raliya ta sata yin wankan ta kawo mata ledar tsarabar ta zabi doguwar riga guda daya da tasha adon jajayen dutsina masu yawa da sheqi

 

 

a falo ta taddata”kinga kuwa maryam yadda rigar nan ta miki,Allah ya kawo miji na gari,gaskiya ba qaramar hidima zamu sha ba”

”har yanzu babu abinda ya ragu a surutun raliya”

”haka miskilanci kyau da ajin maryam diyana har yau yana nan”duka sai suka sa dariya,yana daya daga abinda ya sa qawancensu ke ma maryam dadi,raliya akwai vbarkwanc,inda kuma halinsu yazo daya ta bangaren haquri da dauke kai

 

 

qarar bude get din gidan ne yasa suka ankara da isowar abban fadil

”kinga har sun iso ina nan a zaune,biyar harda kwata”maryama ta fada tana miqewa

”kinga malama koma ki zauna tunda sun riga sun iskemu tare ai bakya tafi ba,ki bari mu tari baqinmu qarasa ladarmu tare”babu yadda ta iya haka ta koma ta zauna,ta fiddo wayarta tqna yiwa hndatu texs ta sanar da mama tana nan tahowa raliya ce ta tsaidata

 

 

tana cikin sending sallamar baqin ta ratsa dodon kunnenta,a sanyaye ta dago tana amsawa,su uku ne abban fadil na hudu,duka sai taji ta a takure gashi raliya ta shiga ciki sako mayafi,sai ta miqe tana daukar jakarta tace

”sannunku da zuwa,abban fadil yanzu raliyan ta shiga ciki bari na mata magana”

dakatar da ita yayi

”a’ah yi zamanki,nasan a gajiye kike kunsha aiki bari na fito da ita,jabir bari na fito da madam”

 

 

falon yayi shiru su duka harda baqin,wayarta na hannunta tana danne danne amma sai take jinta a takure,gashi daga raliyan har nasir din shiru kamar an shuka dusa

”madam haka ake kula da baqi?”

tajiyo maganar lokaci guda,ta daga kanta don ganin me maganar,shije zaune opposite dinta,sanye yake da shadda hartin da hula,murmushi ta danyi a taqaice

”ai bani bace matar gidan,ku jirayi fitowarta”

”ke da ita din ai daya ne,don na tabbata yarda ce tasa suka barki da baqinsu”

sai ta maida idonta kan wayarta don bata da abun ce masa,Allah ya taimaketa masu gidan suka qaraso

 

 

gaishe gaishe ne suka biyo baya da ‘yan hirarrki,saidai duk lokacin da bisa kuskure idonta ya kai sashen da wanda ake ka kira da jabir sai ta tsinci idanunsa na bisa kanta,wanda hakan har ya fara damunta,nasir ya musu jagora zuwa dining domin cin abinci hakan yasa ta cema raliya

”to ai na gama ko,bari na wuce gida”

”tunda ba da mota kika zo ba ki bari mu kammala sai mu wuce tare ko?”

ta jiyo muryar jabir din na fadi

”kasan kuwa kusa da unguwar take ba”inji nasir

”haka,ne fa,shikenan kin huta hawa keke napep”inji raliya

”amma kinsan baxaiyiwu su kaini gida ba,idan mama ta ganni kuma nace mata su waye?”

”indai mama kike ji zan kira tq na gaya mata”inji raliyar

 

 

cikin zuciyarta ta ja tsaki,

”wannan jabir dan shiga hanci ne wlh”babu damar musu tunda duka ido na kanta haka ta koma ta zauna tana jira su kammala,yana bisa dining din amma idanunsa na kanta har raliya ta ankara,cike da gulma ta tabota

”ke,inafa tsammanin kinyi tsuntuwa yau a gidannan”

cikin rashin fahimta tace

”ta me fa?”

hararta tayi ”kiji min ‘yar rainin sense,kina nufin baki lura da irin kallon da jabir ke miki ba?”

”shine me?”

”wlh sonki yake bisa dukka alamu”

wannan karon ita ta maida nata hararar”kijimin mata,kawai daga kallon sarkin fawa sai miya tayi zaqi?”

”wlh da gaske nake,jabir mutumin kirki ne diyana,kada kice zaki qishi don Allah”

”a’ah,kinji ta da wani guntun wa’azinta,ashe har yace miki ma yana sona ko?”

”ni na gaya miki zai fada miki”

 

 

Can saman dining dinma jabirne ke cewa cikin qasa qasa da murya

”kai mutumina nifa nazo gidanka a sa’a,Allah yasa bata da wani”

dariya ya saka”tuni na harbo jirginka ai,indai bilkisu ce a iya sanina ba’a tsaida mata miji ba”

”ai kuwa bazan tsaya kallon ruwa ba,a yau zan kafa kaina”

 

 

A bakin layinsu tasa ya tsaida motar,ta bude murfin tana cewa

”na gode”

”haba madam da sauri haka?”

sai ta juyo cikin mamaki tana dubansa

”eh mana,ya zaki min illa kuma ki tafi ki barni ba tare da kin bani magani ba”

ci gaba tayi da dubansa,sai ya saisaita nutsuwarsa,baiji ko,nauyi ba ya bayyana mata duka manufarshi,da farko ta ja masa yace shikam yace baisan wannan zancan ba,babu inda,zata tafi ta barshi cikin qila wa qala,idan,ko ta tafi to zai tare ne a qofar gidansu har sai ta amsa masa koda zai shekara

 

 

maganar da sukayi da raliya ce ta fado ranta

”maryam,wlh indai aure kike so kiyi kada kiqi karbar tayin jabir matuqar yayi miki maganar,jabir bazai taba tararki da maganar banza ba,nasan jabir tuntuni,abokin nasir ne da dewa,halayensu kusan daya,hakan shi ya qara danqon abotarsu”

ita kanta a zahirance bata ga wani aibu ba tattare da jabir din,yana da kyau daidai wanda duk hassada ba zaka kira shi mummuna ba,a iya abinda ta gani da bayanan da raliya ta mata ta fuskanci zata iya amsa tayin jabir,ko don ma ran mahaifiyarta yayi fari,ko don ta samu itama ta zauna a nata dakin kamar sauran qawayenta da ‘yan uwanta

 

 

ganin shirun nata yayi yawa yasa ya sake marairaice mata ga tsammaninsa zata wofantar da buqatarsa ne

”shikenan,Allah ya shige mana gaba”

”um um maryama,wannan ba amsa bace,kice ina sonka jabir shine magana”

kanta ta girgiza cikin alkunya tace”don Allah ka barni na wuce gida,na tabbata zan sha fada gun mama,don na kai magariba a waje,tunda ka kwaahe min numbers ai sun isa”

 

 

fitowa yayi ya zagayo ya bude mata murfin yana cewa”shikenan,kin bani izini na kiraki?”

kai ta gyada masa,kafin ta dauko jakarta yayi sauri ya rigata ya bude zif din ya jefa mata kudi,ta noqe alamun ba zata amsa ba shi kuma yace indai bata karba ba to tana nufin bata sonshi,tilas ta karbi kyautar tasa,sukai sallama amma sai taga ya ja ya tsaya,kallonshi tayi ya daga mata gira

”sai na hango,shigarki gida don tsaron lafiyarki da kuma gane gidan naku koda na tashi zuwa”

murmushi kawai tayi tajuya domin shigewa layin nasu

 

 

katsam idonta kan isyaku,kai ya gyada sannan ya kwasa da gudu yayi gida,la’ilaha illa nata subhanaka inni kuntu minaz zalimin,tasan tamkar a idanun iyayenshi tayi,cikin fargaba taci gaba da takawa jabir na mata rakiya da idanu har ta shige gidan

 

 

 

About the author

Hausa_Novels

Leave a Comment