Littafan Hausa Novels

A Sanadin Maraici Hausa Novel Complete

Soyayya Da Karamar Yarinya
Written by Hausa_Novels

A Sanadin Maraici Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

A SANADIN MARAICI

*BISMILLAHIR* *RAHAMANIN* *RAHIM*

 

PAGE1️⃣↪️⃣

 

Wata yar budurwa nagani,zaune a cikin wani kayataccen parlour tayi tagumi nakira mata ido sosai naga hawaye nabin kuncinta kyakyawace ajin farko gata fara tas ga daradaran idanu,ga hanci har baka badan karamin pink lip dinta gaskiya budurwar nan yar kimanin shekaru, sha 17 ta hadu masha Allah tana cikin kukan datakene naga wata mata dawata budurwa tana biye da ita abaya suna zuwa gurin budurwar nan naji matar da wannan dayar tabayan nata suna cewa toh shegiya wato bakiyi aikin da yar leletasa kiba koh? toh wlh yau bazakici abinci ba nan tafara kwalawa ma aikatan gidan kira!.

 

 

 

Nandanan kuwa segasu sun shigo suna fadin Hajiya gamu tace yawwa dama kiran kunai infada muku kar Wanda yabawa yar iskar yarinyar nan abinci a cikin gidannan duk Wanda yabata abakin aikin sa wallahi kunji nafada muku Dan haka kukiyaye sukace toh Hajiya.

 

 

Uncle Justice Hausa Novel Complete

 

Sannan Hajiya tace daga yau kezaki dinga komai nacikin gidannan sannan kumasu ai’ki karwanda yatayata kunjini ko? sukace eh tace zaku iya tafiya haka suka fice suna Allah wadai da halin Hajiya.

 

 

 

Suna fita Hajiya tace ke KHAMEENI ki tashi kije ki gyara wa yar lele dakin ta sannan ki gyara nawa kiwanke toilet wallahi idan beyi kyau ba se jikinki yagaya miki haka wacce naji ankira da KHAMEENI ta tashi tahau sama tanufi wani daki Dan tayi ai’kin da akasata.

 

 

 

〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️

Wani kyakyawan saurayi nagani dawasu samari su 2 suma ba laifi suma sunada kyau Amman dayan duk yafisu kyau suna zauna ne acikin wani club kowanne da yanmatansu, ga kayan shaye shaye a gaban su dakagansu kasan abuge suke daya dagacikinsu naji yana cewa KHALIFA kutashi mu wuce wannan kyakyawan saurayin naji yace ok HILAL.

 

 

Nan naga kowannansu yaja budurwa 1 sun fice daga club din sunnufi motocinsu sun bar gurin naga sundau hanya nima nabisu naga sun tsaya a wani katafaran gida sukai horn kasancewar dare ne yasa megadin yafito yazo yaduba yana ganin su yakoma da gudu yabude musu get suka shige sukayi parking suka fito megadin yarugo da gudu yazo gaban wannan saurayin da aka kira dazu wato KHALIFA yana cewa yallabai kayi hakuri dazu bansan kaineba shiyasa KHALIFA bekulashiba suka shige.

 

 

 

Suka shiga wani haddan parlour, gaskiya parlour ya had`u naga kowannansu yaja budurwar sa sun shige bedroom…

 

 

 

Toh fans anan zan tsaya senaga ruwan comments zancigaba

 

 

 

*BY* *Rufaida*

 

 

Comments and share please

 

*A* *SANADIN* *MARAICI*

 

 

 

*BISMILLAHIR* *RAHAMANIN* *RAHIM*

 

PAGE 5️⃣↪️1️⃣0️⃣

 

Bangaran Khameeni kuwa duk ai’kin da Hajiya tasata se da tayi haka tagama ta fito tana fitowa Hajiya tace kingama kenan? Khameeni tace eh Ummi na gama tace ok suna tsaye Sega yar lele tashigo parlour ta zauna.

 

 

 

Tana cewa Ummi tagama ai’kin kenan Ummi tace eh geki duba kigani haka y`ar lele tashiga bedroom d`inta tana shiga tafito tace Ummi beyimin ba gaskiya ta kara gyarawa.

 

 

 

Ummi tace ke jeki kuma gyara mata haka Khameeni tashiga d`akin tacewa yar lele haba “Kausar yanzu wannan d`akinne be gyaru ba”.? tace bansani ba idan zaki kara gyara wa ki gyara idan kuma bazaki gyara ba bari na kira Ummi.

 

 

 

Khameeni tace toh zan gyara haka tahau gyara d`akin tana hawaye tana gamawa tasauka naga tashiga wani d`akin da alama nanne d`akinta tashiga toilet tayi alwala ta tada sallah tana idarwa tad`au alkur’ani tana karanta wa seda akayi issha ta idar sannan tai addu’a ta fito parlour Dan yunwa takeji.

 

 

 

Tana fitowa taga Ummi ita da Kausar a parlour suna cin abinci a dining area taje tace Ummi yunwa nakeji Ummi tace yinwar uwarki a’i nafad`a miki yau bazakici abinci a gidannan ba.

 

 

 

Khameeni tace Ummi dan Allah kiyi hakuri kafin takarasa Ummi ta d`auketa da mari tace tashi kibani guri mayya tayi gadan iyayen ta shegiya kawai.

 

 

 

Haka Khameeni ta tashi tashiga d`akinta tana kuka tazauna tayi tagumi tana cewa Ammi na da Abbah na da kunanan dabazanyi wannan rayuwar ba Allah kana ganin halin danake ciki Allah ka isarmin haka tadinga cen dai tashiga toilet tad`auro alwala tazo ta tada sallah.

 

 

 

 

Ummi ce da Kausar a d`aki Ummi tace a’i “wannan yarinyar mayya ce shegiya duk ai’kin danakeyi akanta baya tasiri Amman zata gane kuranta zanje gurin Hajiya Safiya A’i nasan zata bani shawara a kan abinda ya kamata muyi.

 

 

 

Washe gari

Bangaran Khalifa kuwa suna tashi da safe suka sallami y`an matan su sannan kowa yakama gaban sa Khalifa dai gida yanufa yana zuwa megadi ya bud`e masa yana shiga yayi parking.

 

 

 

Yafito yanufi cikin gidan yana shiga naga wata mata a zaune a kayataccen parlour ita da wata y`ar budurwa.

 

 

 

Yana shigowa y`ar budurwar nan ta tashi dagudu ta rungume shi tana cewa yaya sannu dadawowa yace yawwa Soomeey matarnan dake zaune a parlour tace ke dalla ki ‘kalemin yaro ya huta Khalifa yace aa Mami kibarta nida ‘kanwata haka yazo ya zauna kusa da Mami ya rungume ta tace son kaje kahuta yace toh Mami yatashi yafice daga parlour yanufi part d`inshi.

 

 

 

 

Khalifa nafita Mami tabishi da harara tana cewa shege matsiyaci senaga bayanka gashi nafara samun nasara d`abi unka sunfara chanzawa da sannu zan wargaza rayuwar ka Soomeey tace haba Mami wai me yaya Khalifa yayi miki haka agaban idan shi kinuna kina sanshi abayan idan shi kuma kita tsine mishi gaskiya Mami kidena Mami tace toh uwata bazan denaba shegiya me halin ubanta haka Soomeey ta tashi tabar mata parlour.

 

 

Khalifa kuwa yana shiga d`akinsa yashiga toilet yayi wanka yad`auro alwala yafito yashir ya yatada sallah yana idarwa yafara hawaye yana magana yana cewa ni Khalifa meke damuna nadena sallah kan lokaci nike shaye’ shaye neman mata ya Allah ka yafemin Allah kafitar dani daga wannan halin danake ciki yakuma fashe wa da kuka…..

 

 

Wacce Khameeni

Wanene Khalifa

 

Seku cigaba da bina dan jin cikakken labarin su

 

 

 

Comments and share please

 

 

 

*By* *Rufaida*

A SANADIN MARAICI

 

 

*BISMILLAHIR* *RAHAMANIN* *RAHIM*

 

PAGE1️⃣0️⃣↪️1️⃣5️⃣

 

 

WACCE KHAMEENI

Khameeni Abbas shine cikakken sunan ta.

 

 

Mahaifin ta Alhaji Abbah su 2 iyayen su suka haifa Adam shine babba se Abbas shine karami suntaso suna kaunar junansu basa bari abu yasami d`ayan su haka suke rayuwar su dayake mahaifin su yana da hali suna makarartan boko da islamiyya suna zaune a garin katsina.

 

 

 

Dayake tazarar su bata da yawa sosai hakan yasa suke aji d`a’ya komai tare sukeyi a haka harsukayi candy sukaci gaba da karatu fannin kasuwanci suka karanta masha Allah sunsami nasara sosai dan a lokaci kankani sukayi kud`i kasuwancinsu yafi karfi a garin kano hakan yasa suka dawo kano da iyayen nasu dama sunyi gida kowanne da gidansa.

 

 

 

Alhaji Adam ne yafara samun mata yayi aure ya auri wata yar kusa da gidansu mesuna Zainab watansu biyar da aure Alhaji Abbas shima yasami mata mesuna Khadeeja me hankali da nutsuwa tanasan iyayen sa sabanin Zainab da bata da mutunci bata ganin kowa da gashi Zainab ta tsani Abbas da matarshi batasan ganin su kokad`an.

 

 

 

Bayan wata tara Zainab ta haifi y’ar ta mace ransuna akasamata KAUSAR Zainab take cemata yar lele shekara yar lele 1 Khadeeja mata haifi y`ar ta mace ransuna akasamata KHAMEENI.

 

 

 

Kausar da Khameeni sunyi wayo sosai Kausar duk inda taga Khameeni setaci zalinta Zainab ma indai taga Khameeni seta daketa.

 

 

 

Mahaifin su Alhaji Abbas Allah yaimasa rasuwa sakamokon rashin lafiya dayayi mutuwar tataba mahaifiyar su itama bata jimaba tabi mijinta.

 

 

 

 

Khameeni tana tsoran Hajiya Zainab da y`ar ta Kausar shekara Khameeni 2 akasata a makaranta boko da islamiyya tare akasa su da Kausar kullun se Kausar taci zalin Khameeni gashi Khameeni tana da hakuri sosai.

 

 

Shekaru nata tafiya

Haka rayuwa taci gaba da tafiya Hajiya Zainab tafara bin boka duk asirin datake baya kama Alhaji Abbas da matar shi da Khameeni sabida a tsaye suke da addu’a shiyasa bata samin galaba akansu.

 

 

 

 

Alhaji Abbas ya wayi gari da matsananciyar rashin lafiya baya iya komai sedai komai A’i masa sun shiga tashin hankali anje asibiti Amman ba sauki gaba d`aya yana kasa a lokacin shekarun Khameeni sha 12 Allah yaiwa Alhaji Abbas rasuwa hakika sunji mutuwar sa itakuwa Zainab tayi farin ciki sosai dama tana neman hanyar da zata shekasa lahira sabida tasan aikin boka yayi shiyasa Alhaji Abbas yana kasa sekuma Allah yatakaitamasa wahala yad`auki rayuwar sa gaba

d`a’ya.

 

 

Alhaji Abbas yabar ma Khameeni dukiya me yawa yanzu Alhaji Adam ne ze cigaba da juya mata.

 

Haka aka share makoki bayan shekara 1 Khameeni tayi saukar alkur’ani a lokacin tana da shekaru 13 haka Ammi n ta tacigaba da kula da ita.

 

 

 

Khameeni ta haddace alkur’ani me girma Ammi ta had`a mata walima anci ansha walimar ta ‘kayatar sosai haka akagama walimar.

 

 

 

 

Hajiya Zainab tasami wata ‘kawa hatsabibi ya itakekaita gurin boka wato Hajiya Safiya.

 

 

 

Kausar kuwa dama batasan karatu barima na islamiyya tama dena zuwa gaba d`aya Alhaji Adam kuwa Zainab ta rufe masa baki baya iya magana kometayi.

 

 

 

Bayan shekara 4 lokacin Khameeni tagirma shekarunta 17 kuma tayi candy yanzu tana jiran saka mako.

 

 

 

Washe gari Ammi tatashi da ciwan ciki me tsanani ko asibiti ba ajeba itama tace ga garinkunan Khameeni taji mutuwar sosai tayi kuka haka akakaita makwancinta na gaskiya.

 

 

Zainab tayi farin ciki Dan kuwa gurin wani hatsabibin boka taje shine yasawa Khadeeja ciwan ciki.

 

Haka Khameeni ta hakura Alhaji Adam ne yatasota a gaba tadawo gidansa tunda ta dawo Zainab da ‘yar ta Kausar suke tsangomarta kullun Khameeni tana cikin kuka sedai tai taiwa iyayen ta addu’a.

 

 

 

 

Alhaji Adam kuwa duk abinda Zainab takewa Khameeni yasani yanaso yayi magana Amman ya kasa sabida anrufe masa baki.

 

 

 

Khameeni kuwa a tsaye take da addu’a Zainab kullun burinta taga bayan Khameeni Amman Allah baya bata dama.

 

 

 

Khameeni yanaso taci gaba da karatu Amman Zainab ta hana hakan yasa ta hakura.

 

 

 

Hakika Khameeni tana shan wuya a gidan Ummi wato Zainab da yar lele Kausar suna gallaza mata matuka.

 

 

Toh masu karatu kunji wacce Khameeni

 

 

Comments and share please

About the author

Hausa_Novels

Leave a Comment