Littafan Hausa Novels

A Gidanmu Take Complete Hausa Novel

Soyayya Da Karamar Yarinya
Written by Hausa_Novels

A Gidanmu Take Complete Hausa Novel

 

 

 

 

 

 

 

 

*A GIDANMU TAKE!!!*

_story/written by_
_jiddah S mapi_

_Follow me on wattpad_ jiddahpretty

Hi guys this is my first story hope I will have your maximum co-op ration

*NOTE:* Banyi wannan littafin sabida wani ko wata ba, labarin kirkirrarre ne sabida haka akula sosai.

_dedicated to fateemahsardauna_

Page 1&2

“Haba Ahmad meyasa bazaka dauki kaddara ba, kasani fa kowani dan Adam da irin tasa kaddarar, na wani yafi na wani amma Sam kai baka dauki kaddaraba.

Nan naga Wanda aka kirada suna Ahmad ya dago kanshi, yana hawaye fuskarshi tayi ja, buɗe baki yayi yanason yin magana amma ya kas, sai kuka yake kamar wata mace, hadda shesheka dakyar ya iya cewa “Haba Habeeb ya bazanyi kuka ba, bacin kai kasan abinda yake damuna, idan Banyi kukaba me zanyi?” Yaƙare maganar cikin sanyin murya.

Gyara zama Habeeb yayi haɗe da cewa.
“Addu’a ya kamata kayi Ahmad, domin itace abinda yakamata kowani musulmi yayi, a lokacin daya samu kanshi cikin yanayi na kunci.”

“Ya isa haka Habeeb, ka ƙyaleni naji da abinda yake damuna, bawai ka cikani da surutunka ba, sanin kanka ne nayi babban rashi a rayuwata, rashin daba zan taɓa mantawa ba, tunda narasa FATEEMAH narasa komai,
na wulaƙantata, na ƙuntata mata, nayi mata abinda bazata taɓa mantawa daniba, Ina zanga Fateemah? Ina zanji labarinta? tana raye ko Tana mace?” Ɗan jinkirtawa da maganan yayi, kana ya cigaba da cewa.
“Idan Tana raye Ya Allah Ka bayyana min ita, idan kuma tamutu Allah Ka kai haske kabarinta!!” Ya ƙarashe maganan yana wani irin gunjin kuka.

Awannan lokacin har Habeeb ba’a barshi abaya ba, duk dauriyanshi shima seda yayi hawaye, yana me tausayawa abokinnashi.
*** ***

“Wai Ina kike ne BINTU? kiyi sauri dan Allah kinsanfa mommy Tana jiranmu a mota.”

“Ina zuwa Sis HABEEBA, gyalena nake dubawa ban gani ba.” Naji wata siririyar murya Tana fada.

“Kiɗauki nawa a wardrobe mana bintu.” Habeeba tafaɗi haka cikin yanayi na ƙosawa.

“Okay nama dauka ae ganinan.” Beentu tafaɗi haka tana mai ƙoƙarin yafa gyalen ajikinta.

“Okay dama koban ce kidauka ba zaki dauka kenan?” Habeeba tafaɗa tana ɗan kallon gefen da Beentun take.

Nan naga Beentu na sauƙowa daga kan step, cikin takunta mai ɗauke da nutsuwa. Farace sol doguwa siririya, tana da manya manyan idanu, bakinta dan karami, ƙoƙarin gyara gyallen take, tayadda zai zauna akanta.

Cewa tayi “Haba My Hussaina, Kinsan fa bama haka dake, kuma naga kema ay kinasa abuna ko my sis?”

“Da ma ay haka zakice, kullum se kinwa mutum laifi kizo kina mishi sanyin murya, to yanzu de muje kinga Mom nata kirana, kusan 6 missed calls tayi min” Habeeba tafaɗi haka tana mai duban wayarta dake riƙe a hanunta.

“Okay to muje” Cewar Beentu.

A tare suka fito daga falon suna sauri.

_see me next page_

✍️🏻 *Jidderh S Mapi*
[6/23, 12:43 PM] Ummi Tandama: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*A GIDANMU TAKE!!!*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

_story written by_
Jiddah S mapi

_dedicated to fateemahsardauna_

_wattpad jiddahpretty_

Page 3&4

Suna fita daga falon habeeba ta kwalawa driver Kira yace gani hajiya

tace Ina mommy yace ay hajiya ta dade da tafiya tace bazata iya jiranku ba idan kun gama ku sameta agidan abinci
ok to kaimu driver yace to nan suka shiga motar suka tafi
bayan driver yayi parking naga sun shiga wani waje me kyau Wanda naga ma’aikata da uniform suna rabawa mutane abinci wasu kuma suna dafawa

Wasu na wanke plates daga gani de wannan gidan abinci ne Wanda yayi suna agarin

ADAMAWA Ina daga kaina naga an rubuta HASSY and HUSSY’S KITCHEN

suna fita a motar idanun mutane suka dawo kansu Ana tacewa kaga ‘yan biyun hajiya bada kunku asare

Kuje gida kuce yafadi habeeba ce kadai me cewa sannunku

Samarai barka da war haka ita kuma bintu sai murmushi take nan naga sun nufo wata kykkyawar mata wacce zatakai shekara 40 habeeba tafada kan cinyar matar

Tace mommy shine kikayi tafiyarki kika barmu

matar da aka Kira da mommy naga tayi murmushi nan naga tsananin kamanta da habeeba tace ba dole natafi ba

Kun tsaya kunata shirme kuma kunsan yau ranar biyan ma’aikata ne

Mommy ai bintu ce ta tsayar damu kinsan yanayinta dayin Abu kamar karkashi

Aa karki sake kizagammin ya zo maya my bintu kizauna anan

Bintu tayi murmushi tace mom inason yau zanyi stew da kaima
Mom tace Haba bintu yazaki gajiyar da kanki kizauna kihuta kinji my bintu

Aa mom kibari zanyi
Toshikenan bazan hanakiba jekiyi

Ahmad dama nayi niyan tafiya yau amma bazan iya tafiya nabarka awannan yanayin ba

Nagode habeeb Allah yabarmin kai dan Allah habeeb ko bayan na mutu idan kasamu my teemah dan Allah ka aureta sabida kai Kadai nayadda dakai Kai Kadai nasan zaka riketa da amana tinda kasan bakar wuyar datasha kasan na zalinceta naci amana dan Allah kayimin wannan alkawarin�

Matar Lameer Hausa Novel Complete

_see me next page_
[6/23, 12:44 PM] Ummi Tandama: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*A GIDANMU TAKE*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

_story/written by

Jiddah s mapi

_dedicated To fateemahsardauna_

_wattpad_
Jiddahpretty

Page 5&6

Ahmad kadaina irin wadannan maganganun

Banajin dadinsu Sam meyasa kake maganar mutuwa bayan bakaga fateemahn kaba

Ahmad insha Allah Bazaka mutu ba seka ga fateema

Ka nemi yafiyanta Sannan ku Gina rayuwa me kyau

Kuma inada tabbacin fateemah zata yafe maka

Habeeb bana tinanin my teemah Zata yafemin koda bayan raina ne

Habeeb babu abinda yake damina kamar yanda mommy tadau

Zancennan da zafi ka duba kagani

Yau kusan shekara daya ban sa mommy a idona ba

Yazanyi da rayuwa ta ya karashe maganan yana me hawaye

Abin tausayi

Habeeb kam ba bakin magana

Shi mamaki ma abun yake bashi wai ace yau

Ahmad ne yake kuka yana fada mishi damuwanshi

Shida magana ma be dameshi ba

Gsky dayana da yanda ze taimaka mishi daya yayi

Amma shi besan ma ta ina ze fara ba

Allah ka gaggauta kawo mana karshen

Matsalarnan Ameen

*BINTU*

Mommy wai meyasa bintu take zubar mana da class ne

Kiduba fa yanzu wajen masu aiki zataje suyi tare

Gsky mom abinda takeyi bata kyautawa wannan aji down ne😏

Habeeba kibi rayuwa a hankali

Ita duniya a hankali ake binta

Wanda batazo bama Tana jiranshi bale muda muke cikinta

Ni gsky mom kina daurewa bintu gindi dama nasan

Niba sona kike ba

Bawai bana sonki bane beebah babu Wanda ze haifi da

Yakishi sede idan kaddara ne

mom tafada idonta yana cika da hawaye

A hankali tajuya kanta yanda bintu bazata ganta ba ta goge idonta

Bintu kuwa iyayen son aiki tanata girki suna dan hira da ma aikatan

Dan ita ba ma’abociyar son magana bace

Cikin hiranne wata Wanda suka dan saba da bintu

Take tambayan bintu

Friend dama inason inyi miki wata tambaya

Ok nabeela inajinki

Amma Allah yasa ranki baze baci ba

Aa ba komai yi maganarki ok

Dama inason tambayanki tum bayau ba

Hajiyace ta haifeki!!!?

Haba nabeela wannan wace irin magana ce yazakimin wannan tambayar?

Bacin kinsan mu ‘yan biyune nice babba

Gsky bintu ba kowane ze yadda ba

Duba da irin yanayinki Kiga beebah mana

Tana Kama da hajiya

Amma ke Sam babu abinda yahadaki da hajiya ta kamanni ko hali gsky akwai abun dubawa anan

What are you saying nabeela!!!?

Cewar mom Wanda tin farkon maganarsu takejinsu

Ta taso tambayar bintu kota gama hadin?

See me next page

_Wattpad_
Jiddahpretty
[6/23, 12:44 PM] Ummi Tandama: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*A GIDANMU TAKE!!!*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

_story/written_by
Jiddah S mapi

_dedicated to fateemahsardauna_

Page 7&8

A take suka juyo ganin yadda mommy tayi maganan da karfi

Nan take jikin nabeelah yayi sanyi ganin yadda yananayin mommy yacanza a lokaci kankani

Haba nabeelah wannan wace irin magana ce meyasa kike son sa shakku a zuciyar

‘Yar da Nina haifeta a cikina? shin bakida labarin Akwai ‘yan biyun da Sam basa Kama da juna?”

“meyasa ku mutane
Bakwa gane abune yanzu da ace bani na haifi bintu ba dazaki hada abinda Baza’a taba cewa ke kika hada ba” saikuma tsaya

“Gsky bana son irin wannan tambayar”

Kai daga yau ma kada nakara ganinki da bintu Dan nan gaba bansan mezaki ce mata ba

“Kiyi hakuri hajiya in Allah ya yadda hakan bazata Kara faruwa ba….” inji Nabeela

“Banason dogon magana nabeela nariga nagama magana” hajiya ta mayar mata

“Bintu wuce mutafi”
Tafada cikin bacin rai

“To mommy” cewar bintu wacce tinda mommy tafara fada ta Sunkuyar da kai saida zasu tafi ne takuma ɗaga kai tadubi Nabila wacce duk kunyar momy ya isheta

*AHMAD*

Dakyar habeeb yasamu ya lallabashi yai shiru

“Ahmad gobe idan Allah yakaimu kafin in tafi dan Allah inason muje asibiti Aduba lfyrka dubi yadda karame” inji Habeeb

“Aa base naje asibiti ba maganin cutana bana asibi bane Maganin cutana my teemah ne idan nasameta zan warke insha Allah” inji Ahmad

“Toshikenan yanzu de ka kwanta kahuta sannan karage damuwa saboda zata haddasa maka cuta” inji Habeeb

“Nima Bari nakira agida nafada musu na shaida bazan samu dawowa ba sai gobe”

Mommy na isowa wajen Beebah tasamu sit nata ta zauna rai ɓace

Beebah bataga fuskar tambaya ba

Sai takarasa wajen Bintu tace “Bintu yanaga ran mommy a bace”

“babu komai sis” inji Bintu saboda tasan idan Beebah taji maganarnan bazata ɗauka da sauki

“Yazakice min ba komi bayan gashi ranta a matukar ɓace”

 

“Nace miki ba komai ke meyasa kin fiye naci ne? Inji Bintu

“Ko zaki dake nine to?” cewar Beebah

“Nibance zan dake kiba dan haka kimatsa min anan” Bintu ta mayar mata

“Zaki fara ko beebah meyasa bakya girmama tane tagirmeki fa” inji mommy

Beebah ta zumburo baki tana kunkuni wai datayi magana sai ace ta girmeta abinda baifi ƴan mintuna ba

“Yanzu de kutashi mutafi gida sabida yau yayanku ze dawo” cewar mommy

“Yee mommy dagaske kik?”cewar beebah

“Dama nataba miki karyane?”

Nan wayan mommy yafara ringing

“Yawwa ga shima yana Kira”

amsawa tayi takara a kunnenta

“Hello my son yakake? ok se gobe? Amma meyasa yau bazaka dawo ba? Ok to Allah yakaimu goben” saikuma ta kashe wayar

“Kunga yayan nakuma yace se gobe ze dawo” mommy tafaɗa musu

“Kai amma naji haushi mommy” cewar beebah

Mommy tace “Yau da gobe duk dayane beebah kawai muyi addu’a Allah yakawo shi lafiya”

“Ameen” cewar bintu

_See me next page_

_wattpad_
Jiddahpretty
[6/23, 12:44 PM] Ummi Tandama: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*A GIDANMU TAKE!!!*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

_story by_
jiddah S mapi

_dedicated to fateemah sardauna_

Page 9&10

Washe gari bayan sun gama breakfast ne,

Habeeb yake cewa Ahmad

“To kaga ni yau zan tafi kuma bazan dawo nan dawuri ba”

Saboda wannan zuwanma dakyar mommy tabarni.

Acewarta bataso nayi nesa da ita

Dan Allah Ahmad kada kasa tinani a ranka

Sannan kuma karka gaji da Zuwa gidanku neman tuba a wajen

Mommynka

“Aa Habeeb bazan iya zuwa inda mom take ba gsky”

Sabida mom idan taganni bacin ranta karuwa yake

Har Tana barazanar Zata tsinemin idan harna sake zuwa inda take

Ba tareda Fateemah ba

Kai innalillahi wa’inna ilaihiraji’un abun haryana kai da hakane Ahmad

Wlh Habeeb shiyasa kaga damuwan sunyi min yawa narasa yanda zanyi

Yanzu ma tafiyar da zakayi banso ba

Koba komai kana debemin kewa.

Amma yana iya, idan kaje ka gaida mommy

Da kannan ka duka
Nagode Allah yabar zumunci

Habeeb yace Ameen

Ahmad yace “Kashirya nakaika airport karkayi missing flight”

Ok

 

Bintu kinga yau broh ze dawo

“Kizo mushiga kitchen dakanmu muhada mishi delicious”

Bintu tace “Ok sis karki sami damuwa muje”

Suka tashi suka shiga kitchen suna ta hira

Mommy Tana kallonsu Tana Mejin farin ciki a zuciyarta

tace “Allah yasake hada kanku my twins”

*AHMAD*

Tafiya suke a mota suna hira shida Habeeb.

Nan Habeeb yake kara jaddada masa akan yakula da kanshi yadaina yawan tinani.

Ahmad yace “kaga karka dameni tin jiya kana ta maimaitamin kalma daya kamar karatu”

Ohh “dama nasan bazaka taba canza haliba Ahmad”

Eh naji bazan canza ba

Dahaka har suka isa airport

*BINTU*

Bintu kuwa anata aiki a kitchen bebba se surutu take zubawa.

Banda eh, aa, to,
Ba abinda Bintu take cewa har suka gama hada frid rice da kaji

Bintu tahada sobo me cucumber

Mommy tace “yanzu natura driver yaje dauko shi a airport
Wai ya karaso”

Yeeeee mommy “Aida kin fadamin da tare zamu tafi dashi”

Kai Beebah kin fiye gaggawa

Haba mommy “yabazanyi gaggawa ba yaufa kusan 2weeks ban ganshi ba sede waya”

Bintu kuma murmushi kawai tayi

Horn sukaji abakin gate

Nan Beebah tafita da gudu Tana oyoyo yaya oyoyo

Kafin driver yagama parking harta fara

Bubbuga motan

Seda yafito da sauri yana oyoyo my sis

Nan ta rungumeshi kamkam Tana murna

Yace ina dayarki? Tana falo itada mommy

Ok mushiga daga ciki

Suna tafiya Tana rike da waist nashi har suka shiga falon.

Tana cewa “yaya kadauko tsaraban toh”

Mushiga de tukun kinsan tsarabarki ta daban ce.

Mommy tace “oyoyo my son sannu da zuwa nan itama ta rungumeshi tana murna”

Bintu ta tsaya Tana tayi mishi murmushi

Yace “kekam meyasa bazaki Waye ba Bintu”

kullum kina cikin rashin sabo da mutum.

Cheww Allah yakyauta halinnan naki.

Kina gani fa ‘yar uwarki tazo tayi min oyoyo

Amma ke kina tsaye

Daga nanne Bintu taje ta rungumeshi

Yahada su duka uku ya rungume sunata murna

 

“Ahmad yana komawa gida ya kwanta agado yana tinanin mommynshi
da kanwarshi”

Wai yau shine Kanwarshi wanda yafi so aduniya take gudunshi?

“Yau shine mommynshi take ikirarin tsine mishi”

“Idan yatuna rayuwarshi na da se yayi kuka”

*WANENE AHMAD*?

AHMAD KABEER yarone awajen alhaji kabeer.

Alh kabeer shahararren dan kasuwane

“Wanda yayi suna a duniya”

Alhaji kabeer de dan asalin garin adamawa ne

Shi asalin fulani ne

Wanda yafara harkar kasuwanci tin yana saurayi

Allah kuma ya buda “mishi sabida yanda yake da kyauta da taimakon talakawa”

Alh kabeer yabude gidan marayu tin yana saurayi,

sabida yadda Allah yasa mishi tausayin marayu a zuciyarshi.

Dan hakane har yaki yin aure

” dan yana gudun kar ya auri matar dazata hanashi taimakon marayu”

Iyayenshi ne suka nema mishi aure Agidan marayu Wanda shiya bude da kanshi

Acewarsu zatafi jin tausayin marayu ‘yan uwanta

“Inda suka nema mishi wata kyakkyawar yarinya me Suna mariya”

“Ba matsala a auren mariya da alhaji kabeer sabida mariya Yarinyar kirkice”

Bayan shekara hudu Allah be kawo musu haihuwa ba

Har abun yafara damin mariya

Inda alhaji kabeer yake cemata

“karki damu mariya haihuwa na Allah ne”

“Idan ma Allah be bamu b! Baga gidan marayu ba, semu dau daya murike kaman mu muka haifa

Mariya tace “haba Alhaji kasan fa akwai banbanci tsakanin ɗa da kuma ɗan riko”

Aa mariya ɗa na kowa Ne!

Ganin yahau matsifane mariya tayi shiru

“To dahakane har Allah yakawo ranar haihuwanta inda aka sha shagali akayi murna”

Akasawa yaro sunan baban alhaji kabeer wato AHMAD.

Ahmad de yasamu gata dan kota ina anaji dashi

“Ahmad kyakkyawa ne”

Fari Ne shi, dogo, da dogon hanci, ga karamin baki, Atakaicede shi yayi kama da larabawa.

Sede kuma matsalar shi nada yawa

Yanada girman kai sosai

Ga kallon banza

“Ga zama da abokan banza”

Wasu abubuwan dayake yi abokai ne suke zigashi

“Sai yayi ta tsula rashin kunya son ranshi”

Dafarko yasamu daurin gindi awajen iyayenshi

Se daga baya abun yafara damunsu

*bayan wasu shekaru*

“Dahakane har allah yasake basu haihuwa”

“Yarinya taci sunan wacce take kula da gidan marayu na mahaifinsu wato FAREEDAH”

Fareeda de kykkyawa ce tana Kama da Ahmad sosai.

“Sannan kuma tinda aka haifi fareeda Ahmad yakara bude sabon rashin kunya”

Shi adole yana da kanwa

Bayan haihuwar fareeda fareeda ne Alhaji kabeer yafara diban yaranshi suna zuwa gidan marayu kai tallafi.

Acewarshi idan sun girma suma zasu taimaki marayu.

“Ranar farko dasukaje gidan marayun”

Ahmad yasa fararen kaya masu kyau yanata Hada rai danshi beso zuwa ba.

“Bayan an tara yara ana raba musu kudi ne”

Alhaji kabeer yahango wata kyakkyawar yarinya.

“Tana zaune a gefe tana kallonsu tana murmushi”

Alhaji Kabeer yaɗan tsaya da rabiyar yana kallonta.

Se ya yafito ta da hannu yace zo!

Yarinyan ta tashi a hankali tana tafiya

Harta iso su, seta durkusa tace gani.

“Alhaji Kabeer yayi mamakin wannan yarinya batafi shekara goma ba”

Amma take da natsuwa haka gata dakyau.

Shi kuma Ahmad se harara yake tayi wai ana bata mishi lokaci

Alhaji yace “ya sunanki?”

Ahankali tace “sunana Fateemah”

 

About the author

Hausa_Novels

2 Comments

Leave a Comment