Littafan Hausa Novels

A Dalilin Da Namiji Hausa Novel Complete

Written by Hausa_Novels

A Dalilin Da Namiji Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

A DALILIN DA NAMIJI (1)

 

..“A yau ne Alqalin babban kotun shari’ar musulunci da

yake cikin garin Kaduna ya yanke wa wata mata mai suna

Fatima Ibrahim hukuncin daurin rai da rai a gidan yari,

abisa laifin da ake tuhumarta da shi na halaka babban dan

mijinta mai suna Nasir, ta hanyar watsa mishi ruwan zafi

duk jikin sa, wanda hakan ya yi sanadiyyar salbewar duk

wata fata da take jikin shi, bai dauki tsawon awa daya ba a

asibitin “BIBA HOSPITAL” ya ce ga garin ku nan.

Mijin matar mai suna Alhaji Muhammad shi ya damqa

matar ta shi a hannun hukumar ‘yan sanda, kuma ya tsaya

tsayin daka akan lallai sai da ya qwatarwa danshi mai

rasuwa haqqin shi akan azzalumar matar ta shi wacce ba

ta da tsoron Allah ko kadan azuciyarta inji mijin na ta. Ga

dai yanda tattaunawar tamu ta kasance da shi.”

Gaba daya ‘yan matan da suke zaune a tafkeken falon suka

qara shiga nutsuwar su don jin yanda tattaunawar za ta

kasan ce.

Fitowarta kenan daga ban daki daure da “Towel” a jikinta,

ta rufa wani qaramin tawul din akanta, fuska ba walwala ta

zauna a kan kushin mai zaman mutum uku, sannan ta dauki

“Remote” a gefenta ta qure Radio sosai tamkar zai fasa

masu dodon kunne.

“Ya sunan Malamin?”

Dan jaridar ya jefa wa mutumin da suka kira mijin matar da

ake tuhuma tambayar

“Sunana Alhaji Muhammad Yusuf.”

Mutumin ya amsa da cikakkiyar muryar da ba ta nuna

jimami ko kadan.

Aziza da Azima Macizai Ne Hausa Novel Complete

“A yau ne aka kawo qarshen shari’ar nan da aka dauki

tsawon watanni uku anayi tsakanin mai dakinka Malama

Fatima da Marigayi danka Nasir , mai zaka iya cewa akan

hakan?”

“Alhamdulillah! Godiya ta tabbata ga Allah (S.W.T) da ya

kawo qarshen wannan shari’ar, tabbas ina cikin farin ciki

da godiya ga Allah domin an fitar wa da mai haqqi

haqqinsa, mata irinsu Fatima wadanda basa tsoron Allah

ko kadan azukatansu wannan ya ishe su darasi, amma idan

har sunada tunani.

Tun lokacin da marigayi Nasir Allah ya jiqan shi ya

tabbatar min da Fatima ce ta aika ta mishi hakan kawai don

ya ziyar ci gidan ta a matsayin shi na dan mijinta karo na

uku tun bayan dawowar shi daga qasar Malesia karatu,

lokacin da ya fada min hakan bai fi saura minti ashirin

Allah ya dauki rayuwarsa ba, kuma na daukar mishi

alqawarin ko da zanyi yawo tsirara sai na daukar mishi

fansa, don haka ayau ina mai farin ciki matuqa.

Su kuma ma su irin halinta ina ma su fatan Allah ya shirye

su idan kuma ba ma su shiryuwa ba ne Allah ka tarwatsa

su aduk inda su ke a fadin duniya.

“To yanzu ya matsayin igiyar auran da yake tsakanin ku?”

Dan jarida ya sa ke jefa mishi wannan tambayar.

“Tun ranar da abin ya faru na yanke igiyar aurena duka

ukun da yake tsakanin mu, kuma na danqa mata takardar

ta tun kafin a kawo qarshen wannan shari’ar.”

“Akwai zuri’a a tsakanin ku?”

“Babu yaro ko daya a tsakanin mu shekarar mu biyu da

aure amma ko batan wata bata taba yi ba.”

“Ba ka tunanin wani irin kallo da iyayanta zasuyi maka?”

Muryar shi a fusace ya amsa da cewa,

“Ita din marainiya ce a hannun qanin Babanta na aureta,

kuma tunda ya ji abin da ta aika ta ya zare hannunshi daga

kanta bayan ya yi mata Allah ya isa rainon da ya yi mata,

kuma ko iyayanta su na da rai bazan da mu da duk wani

abu da ya za su ce ba, don kuwa da bai fi da ba.”

“To amma…..”

“Dakata Malam tambayo yin na ka sun ishe ni haka, ina da

abinyi”

Ya katse dan jaridar ya na gwama numfashi cike da fusata.

“Qarshen tattaunawar da ta gudana tsakanin wakilin mu

kenan da mijin mai laifin, wakilin namu ya nemi tattaunawa

da uwar marigayin amma hakan bai samu ba, kuma ya

nemi tattaunawa da mai laifin itama ta qi ba mu hadin kai,

kalma daya kawai ta iya furtawa ga wakilin namu, fuskarta

cikeda hawaye ta ke nanata kalmar

“ADALILIN DA NAMIJI” Daga nan ta barke da matsanancin

kuka yayin da ‘yan sanda sukai awon gaba da ita cikin

motar shiga ba biya fi ta da Allah ya isa, nan muka kawo

qarshen shirin na JAKAR MAGORI….”

Dif ta sanya hannu ta kashe Redion, hankalinta atashe,

kyawawan idanunta sun rine zuwa jajaye saboda tsananin

tashin hankali. Safa da Marwa take a tsakiyar falon tana

doka hannunta na dama cikin na hagu, tsawon minti goma

ta dauka tana hakan, daga bisani ta zube akan kujerar data

fara zama tun bayan fitowarta daga wanka. Hankalin ‘yan

matan da su ke zaune a falon yana kanta, da alamun jira su

ke ta furta wani abu sannan su ma su samu bakin magana.

Idan kunaso zan cigaba

[23/02, 6:30 am] +234 813 298 6866: A DALILIN DA NAMIJI (2)

 

“Me maza su ke so su mai da mu a duniyar nan?” Ta furta hakan muryarta a kausashe tana kallon ‘yan matan cikin falon daya bayan daya. Karar shigowar sakonni ba qaqqautawa aduk wayoyinta guda uku da su ke cikin daki shiya katse mata maganganun data fara yi. “Safiyya kwasomin wayoyina a daki” Ta fadi haka tana kallon daya daga cikin ‘yan matan da suke zaune a falon. Daqiqa goma tsakani ta fito riqe da wayoyin a hannunta, sai da ta dan rusuna sannan ta miqa mata wayoyin. Duk saqonnin sun fito da ga guri daya ne. number ce kuma babu suna, 7777 shi ne number da ya turo mata saqon. Gyara zama tayi don kuwa saqon mai muhimmanci ne a garesu, saqon wayar Black Berry dinta ita ta fara karantawa a fili don sauran ‘yan matan su ji meya qunsa. “TARIHIN FATIMA IBRAHIM WACCE TA KASHE DAN MIJINTA NASIR” Hakan aka rubuta da manyan baqi a farkon saqon. Ta dan tsagaita tana kallon fuskokin cikin nazari daya bayan daya, kowacce a zaqe take da son jin cigaban saqon, don haka ta dora da ga inda ta tsaya “Marainiya ce gaba da baya, iyayanta Allah ya dauki rayuwar su tun tana ‘yar shekaru uku a duniya, hatsarin mota sukayi a hanyar su ta dawowa da ga Abuja zuwa Kaduna. Marigayi Alhaji Ibrahim mahaifin Fatima shahararren mai arziqi ne, Fatima ita kadai ce diyar shi a duniya, mahaifiyar Fatima ‘yar Zindar ce a jamhuriyar Nijar. Yawon kasuwanci ya kai mahaifinta can qasar har Allah ya hada fuskokinsu, sannan ya sanya soyayya mai tsanani a tsakaninsu har sukayi aure, bayan kai ruwa ranar da akai da mahaifan Aisha (Kakannin Fatima na wajen Uwa) kan cewa ‘yar su baza ta yi aure a wata qasa ba. Lokacin da kakannin Fatima na wajen Uwa su ka samu labarin rasuwar ‘Yarsu da mijinta sunyi kuka sosai, kuma sunzo har akayi kwanaki bakwai da rasuwar, sun buqaci tafiya da Fatima amma Alhaji Musa qanin mahaifinta ya ce sam! Hakan bazai taba yuwuwa ba, sunyi rabuwar dutse da hannun riga, wanda hakan ya yi matuqar tunzura su har suka sha alwashin yanda su ka rasa ‘yarsu Aisha mahaifiyar Fatima su ka haqura itama Fatima sun haqura da ita har abada, indai ita jinin su ce zata neme su amma su kam baza su taba nemanta ba har gaban abada idan akwai.

[23/02, 6:30 am] +234 813 298 6866: A DALILIN DA NAMIJI (3)

 

Bayan komai ya lafa riqon ta ya koma hannun qanin mahaifinta, Babu wata rayuwa ta jin dadi da Fatima zata qarar wanda tayi a gidan qanin mahaifin nata Alhaji Musa. Makarantar gwamnati ya sanya ta sabanin ‘ya’yan shi da su ke makarantar kudi, duk wadanda ya kamata su tsawatar mishi ya gama siyesu da kyaututtuka, fantamawarshi kawai yakeyi da dukiyar data gada a gurin mahaifanta. Da dadi ba dadi har ta kammala Secondary School, inda ta fito da sakamako mai matuqar kyau, babban burinta taci gaba da karatu amma sam Alhaji Musa yaqi ba ta damar hakan, amma ‘ya’yan shi da mazan da matan duk babu wanda yake cigaba da karatu a qasar nan, tanaji tana gani dole ta hakura da burinta na cigaba da karatu. Alhaji Muhammad aminin kawunta ne name kud da kud, duk wani qulle qulle na kawun nata Alhaji Muhammad ya sani, tun tana aji uku a Secondary School yake damunta da maganar soyayya, nauyin shi ta ke ji sosai, domin ta daukeshi tamkar qanin mahaifinta. Ba tareda tambayar amincewa ko ra’ayinta ba Alhaji Musa ya daura mata aure da Alhaji Muhammad. Hannu bibiyu ta sa ta rungumi aurenta, duk da ba ta son mijin nata ko kadan, gidanta daban da gidan Uwargidanshi, yana nuna mata kulawa daidai gwargwado, saboda yana sonta kuma tana daga cikin jerin matan Allah ya kyautata surar jikinsu, dana fuskarsu, qarin armashin kuma shine yarinya ce karama. Ita da Hajiya Ramatu uwargidanshi suna zaman lafiya, domin ba ko da yaushe suke ganin juna ba, Idan bada wani qwaqwqwaran dalili ba suna daukar tsawon lokaci ba su hadu ba. Ba su fara samun matsala ba saida babban dan Alhajin mai suna Nasir ya dawo gida daga inda ya ke karatu acan qasar Malesia, tunda suka je airport da niyyar dauko shi ita da Alhaji da Hajiya ta lura da irin mayen kallon da yake bin ta da shi. Nasir bunsuru ne gurin bin mata tun kafin ya tafi karatu qasar Malesia, da yaje can kuma sai idanumshi suka qara budewa, duk yarinyar da ya qyalla ido a kanta kuma yayi sha’awarta sai yabi duk hanyar da zaibi domin ya samu biyan buqatar shi. Tun ya na can ya ji labarin Dadyn shi ya yi aure amma bai taba tunanin daqwalwa irin wannan ya aura ba, ganin farko da ya yi mata gabanshi ya yanke ya fadi, daqyar yayi qarfin halin daidaita nutsuwarshi don kada ya bada kanshi a gaban iyayan shi. Suna tafe a mota zuciyar shi tana saqa mishi hanyar da zai bi dan cimma mummunar manufarshi a kanta. Ita kuwa a zuciyarta take ta addu’ar Allah ya dai dai ta zaman su da shi dan sam bata fahimci wane irin kallo yakeyi mata ba, a zaton ta kallon tsana ne da tunanin yana taya mahaifiyar shi kishi ne, a minti biyar ya mantar da ita wannan tunani ta hanyar fara janta da hira yana kiran ta “Aunty Fati” Duk iyayan ransu cike yake da farin cikin dawowar dan na su dan haka sam hankalin su ba shi a kan Fatima, idan ya tsomata a hirar shi a darare ta ke amsawa muryarta a sanyaye. Hakan ba qaramin burgeshi ya ke ba, shauqin sha’awarta ya yi ta dibar shi har suka isa gida. Ba ta bar gidan ba zuwa gidanta sai bayan sallar magariba gab da isha’I, da yake Alhajin a gidan ya ke da kwana sai ya hada ta da Driver ya kaita gida. Da sauri Nasir ya miqe ya na kallon iyayan shi fuska a sake ya ce, “Bari in raka aunty Fati gida sai mu dawo tare da Drivern” Jikinta sanyi qalau ta ke kallon shi don rashin ga ne manufar wannan cusa kai da ya ke mata, Izinin tafiyar da ya samu da ga gurinsu ya hanata tankwabar da shisshigin shi , sai ta qara yi musu sallama ta nufi harabar gidan. Dukkansu suna zaune a bayan motar ba mai cewa wani uffan, amma idon shi ya na kanta tamkar zai cinyeta danye, ba qaramin takurata ya yi da idanun shi ba don haka ta takure acan jikin motar a zuciyarta ta ke addu’ar Allah yasa su isa gidanta lafiya ko zata samu sa’ida da ga mayataccen kallon da yake bin ta da shi. Suna isa ta dakatar da Drivan a qofar gida, ta balle murfin motar ta fita sannan ta leqa kanta ta saqon glashi ta ce, “Nasir Allah ya huta gajiyar tafiya mu kwana lafiya” Tana fadin haka ta karasa da sauri ta ciro key a jaka ta na buxe get din gidan ba, bataga fitowar shi daga mota ba balle lokacin da ya nufota kawai muryarshi ta ji a kusa da ita ya na fadin “Haba aunty na rowar ruwan gidan ki za ki yimin?” A dan firgice ta sa ki key din ya fadi qasa muryar ta na rawa ta ce, “Ba… ba… ba haka ba ne, na… naga su Alhaji suna can suna jiranka ne.” Bai ce komai ba ya tsuguna ya dauki makullin ya bude get din ya shige ciki ya bar ta nan a tsaye. Ganin da ta yi ba sarki sai Allah ga idanun Driver tun xazu ya na kanta ya sa ta yi shahadar bin bayan shi, har ya samu nasarar bude qofar falonta ya shige ciki don ha ka ta hada da sassarfa zuwa cikin falon. Yana kwance akan kujera mazaunin mutum uku idanun shi alumshe, jakarta ta aje akan kushin ta nufi kichin, lemu da ruwa masu matuqar sanyi ta jero a cikin faranti ta dora Cofi guda biyuta kawo mishi. A zaune ta tarar da shi hannun shi riqe da remot din T.V ya na canza tashoshi, a gefe daya ta aje farantin, sannan ta dauko dan qaramin table ta dora akai, a gabanshi ta ajiye, sannan ta saki fuskarta tace “Bisimillah.” Maqe kafadar shi ya yi tamkar wani qaramin yaro sannan ya fara kashe mata idanu irinna gogaggun ‘yan duniya. Muryar ta da mamaki ta ce “Me ya sa? Bayan ruwa ka buqaci sha?” “Ni ba irin wannan ruwan nake so ba” Ya fada ya na tura baki, ya fara kwarkwan ce tunaninta, domin kuwa ya girme mata nesa ba ku sa ba, a qalla zai girmeta da shekaru goma sha hudu, wanda ya riga ka kwana dole ya riga ka tashi. Sam bata fahimci inda ya dosa ba don haka ta ce, “Dare ya na qara yi fa kar su Hajiya su ji shirun yayi yawa” “Bikin Magaji ya na hana na Magajiya ne?” ya jefa mata tambayar ya na qara qura mata ido.

About the author

Hausa_Novels

1 Comment

Leave a Comment