Safreen Hausa Novel Complete
*SAFREEN*
By
Habibty Muhammad
(ⓂⓊⒽⒶⒷ)✍️
Duk kan yabo da godiya ya tabbata ga Allah subaha nahu wata’ala.
*بسم الله الرحمن الرحيم*
E.1_
Tana zaune a cikin ɗakinta mai katafaren girma wanda ke ɗauke da kayan zamani iri iri, sanye a cikin sa, kaida kaganta kasan bata da matsala domin kuwa kuɗin sun zauna masu.
Chatting take yi ita da Yayan ta Suhail sai taji muryan Ummynsu tana kiran ta daga parlour.
Gawurtattu Uku 2024 Hausa Novels
“Ke! Safreen! Safreen!! Safreen!!! Kina ina ne?.”
“Na’am Ummi gani nan zuwa yanzu fa.”
Ummi ta ce ma ta bayan ta ƙari so palon “Dama Safuwan ne yabar system ɗin sa anan, yace shi zai fita ana nemansa da gaggawa a Hospital baze samu damar ya mayar dashi ba, yace in kira ki kimayar masa dashi Bedroom nasa ga key din nan sai kikai masa.”
“Okay Ummi tohm babu damuwa.”
Da takai ta ajiye masa saita dawo wajen Ummin tana faɗin.
“Ummi bari naje na ɗauko waya ta na nadawo musha fira.”
Ummi ta amsa ma ta cikin Murmushi tana faɗin.
“Toh Auta sai kin fito, Murmushi ita ma Safreen tayi kana ta juya izuwa Bedroom nata.
Bata wani dade ba saiga ta nan ta fito hannunta ɗauke da wayarta mai tsada, Ƙarisawa tayi ta kwanta akan cinyan Ummi tana dariya tare da faɗin. “Ummi kin san menene?.”
Ummi ta ce da ita “A’a saikin faɗa Auta na.”
Safreen tayi saurin cewa dama magana nake nida Yaya Suhail yanzun sai kuma kika kirani fa.”
Ummi sai ta ce ma ta “Toh me kika ce masa?.”
“Nifa bawani abu nace masa ba, kawai dai so nake na tabbatar da maganan da Yaya Safuwan ya faɗa minne nacewa jibi wai zai dawo, shi ne nake tambayan sa kan cewa da gaske ne?.”
Ummi murmushi kawai tayi tana faɗin “Allah ya shirya min ke Auta, watoh da baki yarda da maganan da Safuwan ya faɗa miki ba ke nan ko?.”
Sosai Safreenn ta saka dariy tana kare kanta da cewa
“A’a Ummi kinga ni ina zaman lafiya na karki hadani da Yaya Safuwan dan wallahi za’a sha kallo ni da shi, saita kara fashewa da wata sabuwar dariyar cike da nishaɗi.
Ummi tayi gefe kanta tana faɗin “Allah yanuna min ranar da za’a ce kin dai na neman tsoka nar nan, Yarinya sai tsokanar tsiya amma ga tsoro kaman farar kura.”
Ummi bata bar Safreen tayi magana ba dan tasan Wacece Safreen yanzun sai ta ishe tada surutu, shiyasa ta ci gaba da faɗin.
“Allah yamiku Albarka sannan ya raya min ku bisa tafarkin na gaskiya.”
“Allahumma Ameen….” Kawai Safreen ta fada sai tayi shiru kamar mai tunani.
*TOHM MAFARI KE NAN KAƊAN DAGA CIKIN SABON NOVEL DA (MUHAB) ZATA FARA KAWO MUKU, SABUWAR MARUBUCIYA MAI TAFE DA SALO NA MUSAMMAN*
*FATAN ZAKU KASANCE TARE NI DANI WURIN BIBIYAR WANNAN LABARI DOMIN JIN IRIN SALO DA DARASIN DA YAKE TAFE CIKI*
HABIBTY MUHAMMAD (MUHAB) CE
*FATAN ALKHAIRI GA KOWA*
*Make sure you drop your comment , vote and like with share for everyone thank you*… Much Love
Add Comment