Me Debe Kewa Hausa Novel Complete
ME ‘DEBE KEWA
(‘yar me gwanjo)
Writing By Amnah El Yaqoub
Dedicated to Bilkisu’s name
https://chat.whatsapp.com/GnQsZx4Pn7QHpdshIPWwtu
1&2
Da sunan Allah mai Rahma mai jin qai,ina sake yiwa Ubangiji godia daya nuna min ranar dazan fara posting wannan labarin lafiya,littafin ME ‘DEBE KEWA na dad’e da fara rubutunsa,tun kafin na rubuta littafin MAWAHIB nake faman rubutu akan littafin ME ‘DEBE KEWA,idan har akwai wani sharri wanda zai amfani al’umar Annabi asandin wannan labari,ina roqon Allah karya bani damar dazan kaishi qarshe,ina roqon Allah yasa na rubuta abinda zai amfani al’uma baki d’aya,Alkhairin dake cikin wannan labarin ina roqon Allah ya sadamu dashi,ina roqon ku kada kuyi amfani da qyale-qyalen dakukaci karo dashi acikin wannan labari,kuyi amfani da darasin da littafin yazo muku dashi,ina Addu’ah ga duk wasu mata iyayenmu da qannanmu,da yayunmu masu juna biyu ubangiji Allah ya saukesu lafiya,wanda suka rigamu gidan gaskiya da wanda sukai rashin iyayensu Allah yaji qansu yayi musu Rahma,Allah yasa Aljannah ce makomar mu baki d’aya,Allah yayi mana tsari da talauci,Allah ya sauqaqa mana wannan yanayi na matsin rayuwa damuke ciki.
ME ‘DEBE KEWA littafin kud’i ne,naso in kawo muku shi tun 2023 kamar yanda na saba kawo muku littafi sau biyu a shekara,amma Allah bai nufa ba sakamakon wasu uzurirrika dakuma salon bincike da labarin yazo min dashi.
Kudirar Allah Hausa Novel Complete
Akwai wanda suke siya littafi na,saisu koma gefe su dinga siyar dashi,ban yarda ba,ban amince ba,ko kad’an daga cikin labari na ban yarda ajuyamin ba bare asiyar dashi,babu kyau shiga haqqin mutum bare kuma d’an uwanka musulmi.
Wannan labari gaba d’ayansa na sadaukar dashi ga dukannin masu Suna BILKISU,yanda sunan littafin yazo ME ‘DEBE KEWA, ina Addu’ah Allah yasa ya ‘DEBE muku KEWA.
Lokacin dana rubuta littafin MAWAHIB,dayawa daga cikin masoyana suna min complain littafin yayi tsada,dan Allah na rage suna so su siya,harma da wanda suke cewa dan Allah inci gaba da rubuta labari akan farashin 300 Naira,nikuma ina ganin ai dad’in labari shi kesa mutum ya siyeshi ko naira nawa aka sa,to kunfi qarfina 😣, dama saboda ku Amnah take rubuta littafi,idan babu Readers babu rubutu,kamar yanda kuka roqa gashinan littafi daidai da aljihunku,dan Allah idan kinsan zaki siya ne domin ki dinga fitar min dashi zuwa group to wallahi na haqura da 300 dinki😭
Ku riqemin amana dan Allah,duk wacce taga tayimin magana ta private ban saurareta akan lokaci ba,tayi haquri,tayi haquri,tayimin uzuri dole zan saurare ta saboda Amina ta kowa ce,ta dukkanin fan’s dinta ce🥰
ME ‘DEBE KEWA naira 300 ne kacal,duk wanda yakeson wannan labari zai iya yin payment ta wannan account number
0164549488
Amina muhammad
GTbank
Tareda turo shedar biya ta wannan number 08033300034
masu tura kati transfer kokuma photon Kati,zaku iya turowa ta wannan number 08033300034
_____
Garin Malam…Hadejia Area,Jigawa State.
{ 1986.}
Shekaru Talatin da Bakwai baya.
Gidane d’an qarami wanda yake d’aukeda d’aki qwaya d’aya jal ginin qasa,be samu arziqin samun Katanga irinta d’akin ba,wato katangar qasa,saide yasamu arziqin samun katangar zana,ita kanta zanar da’akai katangar da’ita batakai har qarshe ba saida kara aka qarasa ta.
Gidan abushe yake qaraf bashida komai face wata madedeciyar bishiyar maina me mutuqar sanyi,kana ganin gidan kasan gidan wani mashahurin talaka ne futuk wanda bashida cin yau bare na gobe.
Kyakykywar mace me shekaru aqalla talatin da biyar tagama share gidan daqyar saboda tsohon cikin datake dauke dashi me mutuqar girma haihuwa yau ko gobe,gumin fuskarta ta share,ta nufi qasan bishiyar gidan ta zauna tana maida numfashi tareda lumshe idonta tanajin dad’in is’kar datake kad’awa,jingina tayi da jikin bishiyar hakan yasa d’an kwalin dake d’aure akanta yazame yafad’i,wani uban gashi me sheqi da bala’in tsawo ya bayyana,gashin nata baqi ne sid’ik,ita kanta idan ka kalleta karon farko zaka tabbatar matar manya ce,asalin kalar farar fatarta zaisa kagane cewa ba ‘yar Nigeria bace.
Ahankali tajuya ta kalli d’akinsu da tsakar gidan wanda babu komai yaqare,babu abinda zata samu tasa acikinta,amma duk da haka cikin dauriya ta shafa qaton cikinta tace”kayi haquri kaji,Babanka zaizo yakawo mana abinci”
Kafin ta d’auke hannunta daga kan cikin,mijinta yashigo gidan bakinsa d’auke da sallama,tun kafin ya qaraso inda take yagama qare mata kallo yana sake yiwa Allah godia daya azurtashi da Samun mace kamarta, yasan cewa banda qaddara da qudurar ubangiji itadin ba sa’ar aurensa bace,amma sai gashi ubangiji bai dubi hakanba, ya mallaka masa ita amatsayin mata d’aya tilo.
Zama yayi kusa da’ita har jikinsa yana gogar nata,ya kalleta cikeda kulawa da tsantsar so sannan yace”Mai Gadon zinare yakike zaune haka kai babu dankwali?”
Murmushi tayi dimples dinta suka bayyana,wanda suka sake qawata kyawun fuskarsa na asalin buzuwar qasar Nijar,cikin shauqin qauna tasaka hannunta tafara tattare dogon gashinta,cikin sauri yasaka hannunsa yana tayata tattare gashin,cikin jin dad’i tace”Malam zafi naji,bansan lokacin da dankwalin yafad’i ba,da alama de yau kasamo mana abinci,na ganka da farinciki”
Murmushi yayi,sannan yasake gyara zamansa yana fuskantarta “wato Bilkisu duk lokacin dana tuna inada mace kamar ke acikin gidana,hankali na yana kwanciya,duk rashin kud’i na da talaucina,inde na kasance tare dake kina ‘DEBE MIN KEWA,ina farinciki ne saboda nasamo mana kud’i masu yawa har kimanin naira dubu d’aya” ya qarasa maganar yana futo da kud’in daga aljihunsa ya ajiyesu agabanta.
Takardun naira ashirin-ashirin ne dayawa sai kuma qwandaloli da ficika.
Kyawawan fararen idonta ta zaro,cikin tsananin mamaki dakuma ganin yawan kud’in yasa ta kalli mijin nata tace”Malam Ina kasamo wannan kud’ad’en masu yawa haka?”
“kekena nasiyar Bilkisu,lissafa kigani cefanan kwana nawa zai mana?”
Manyan idonta ta lumshe sannan ta bud’e,taja hannunsa guda d’aya tad’ora akan qaton cikinta,cikin damuwa ta kalli mijin nata tace”dani da d’ana zamu jure duk wata yunwa amma ba zamu jure ganinka babu abinda kake sana’ah dashi ba,yanzu daka siyar da kekenka dame zaka dinga dako kana samo mana abinci?,meyasa kasiyar?”
Kansa ya sunkuyar qasa cikeda damuwa da rashin sanin makomarsa,cikin nata ya shafa sannan yace”Bilkisu bake kad’ai bace,idan ban sai dashi ba mezan baku kuci?”
Hannunta tad’ora akan nasa hannun wanda yake kan cikinta sannan tayi murmushi dimples dinta suka futo ta kalli cikin idonsa tace”shima yaron cikina zaiyi haquri,yasan cewa yau Babansa bai samo mana abinci ba”
Cikin jin d’adi ya kalli fuskarta yace”Bilkisu waye yace miki namiji zaki haifa ne?”
Cikinta ta shafa cikin kulawa dajin dad’i tace”Babu Wanda ya fad’amin,amma Ina fata,Ina Addu’ah Allah ya azurtani da d’a namiji,zan saka masa sunan mahaifina sannan kuma sunan fiyaiyen halittafi Annabi Muhammad (s.a.w)”
Murmushi yayi,ya kalli cikinta sannan yace”Bilkisu ko mace kika haifa,ko namiji, zanyi farinciki da duk abinda kika haifamin,kuma ko abinda na mallaka zai qare gaba d’aya,insha Allah abinda zamu haifa sai yayi karatun Boko,kwanaki dana shiga qasar Hadejia,Naga wani yaro matashi yasa wannan baqaqen kayan(Suit) irinta manyan ma’aikata,yana magana yana zaro turanci sai abun ya birgeni,naji duk duniya babu abinda nakeso irin boko,amma tunda ni Allah yasa banida rabon yin boko har iyayena suka rasu, insha Allahu zan tsaya tsayin daka,Inga jinina yayi karatun boko,sannan….”
Kafin yaci gaba da magana suka jiyo ana kwad’a sallama a qofar gida.
Tashi yayi yafita,yana zuwa qofar gidan nasa yaci karo da mutane kusan su bakwai,d’aya daga cikinsu mai kimanin shekaru ashirin da takwas yace”Malam MANU kud’in bashin mu mukazo kar6a,duk wanda kagani anan yaji labarin kasaida keken kane shine ya biyo bayanka kabashi haqqinsa,amma inaso kafara sallamata saboda bashina yakusa shekara biyu a kanka kullum kalmar haquri kake fad’amin”
Malam Manu yayi shiru kamar an doka masa sanda,yasauke wata nannauyar ajiyar zuciya yad’ago kansa ya kallesu yace”jama’ah,dan Allah kuyi haquri,ku rufamin asiri kamar yanda Allah yarufa muku,wallahi zan biyaku bashin ku,bamuda abinda zamu ci nida iyalina….”
‘Daya daga cikinsu wanda yadan manyanta yace”kaga dakata malam Manu,yaushe mukai dakai zaka biyani kud’ina?”
Cikin sanyin jiki yace”Tun wata uku dasuka wuce yadace nabiyaka”
Cikin rashin tausayi mutumin yameqa masa hannu sannan yace”to Alhamdulillah,qirgosu naji d’uminsu…”
Malam Manu baisake cedasu komai ba yajuya yashigo gida,baqin ciki da taqaici yasa baisan lokacin dayaji wani irin hawaye mezafi yazubo daga idonsa ba.
Tana ganin haka tasan cewa ba qalau ba,tashi tayi daqyar ta qarasa wajansa,cikin damuwa tace”Malam meyake faruwa? Yanaga jikinka a sanyaye mutuwa akayi?”
Hawayen idonsa yashare daqyar sannan yace”Bilkisu masu kar6ar bashi ne,nabasu haquri sunqi tafiya,Ina murna na saida kekena zamu samu abinci ashe duk da haka ban tsira ba,bamuda komai a gidannan wanda zan d’aga in siyar,babu abinda yarage min saide wannan kayan na jikina zan saida musamu muci abinci”
Ya qarasa maganar yana mata nuni da kod’ad’d’an yadin dayake jikinsa.
Cikin son kwantar masa da hankali tace”ya’isa,kayi haquri kadena kuka Ina zuwa”
Dan kwalin kanta tacire,dogon gashinta na asalin buzuwa ya bayyana,ta warware dankwalin tayafashi akanta sannan ta qarasa qofar gidan da sallama, d’aya daga cikinsu ne yazaburo tun kafin tayi magana yace”kudin ne?”
Yayinda sauran suka qura mata ido suna kallonta saboda tsananin kyawunta dasuka gani,cikin zuciyarsu kuwa mamaki suke dama acikin wannan qauyen nasu na Garin Malam ashe akwai matan India aciki?🤔
Murmushin qarfin hali tayi tace”A a, kuyi haquri,dan Allah ku qara masa lokaci insha Allahu zai biyaku kud’in”
Wanda yafara tambayarta kud’in da farko yanzu ma shine yasake yimata magana yace”kinga…idan kud’in ki kazo kawowa to kawo kiwuce, idan ba kud’in kika kawo mana ba,juya kituro mana Sulaimanu”
Murmushi tayi idonta na kawo ruwa,sannan ta meqa musu dubu d’ayan hannunta wanda malam Manu yabata,cikin rawar murya tace dasu “gashi”
Babu musu suka kar6a, lokaci d’aya hawaye yazubo daga cikin idonta zuwa kan farar fatar fuskarsa,hawayen ta goge tace”dan Allah kubamu ko naira ashirin ne mu sayo wani abun muci…”
ko sauraren ta ba suyi ba suka fara fad’a akan kud’in kowa yanaso a bashi kasonsa aciki,saboda kud’in sunyi kad’an akan yanda sukebin Malam Manu bashi, ahankali ta girgiza kanta tajuya tadawo gida tana jiyo hayaniyar su suna fad’a akan yanda za’a raba kud’in.
Zama tayi akusa dashi baisan ma ta’iso ta zauna ba yayi nisa acikin tunanin halin dasuke ciki,shiba kowa ba duk danginsa sun rasu, ita ba kowa ba dan’uwan ta qwaya d’ayane shima yana qasar nijar,ya kalli katangar gidansa ta Kara da zana gaba d’aya duk ta mutu gara ta cinyeta kad’an yarage afara ganinsu daga waje,kana ta6ata zata Iya fad’uwa.
Maganar data masa ne yasa yadawo hayyacinsa,yasaka hannu yagoge hawayen idonsa bayan yagama jin kalaman ban haquri daga matar tasa.
Wani yaro ne yayi sallama da wata roba a kansa,yana zuwa yabata robar yace”Balki ME GWANJO waiga niqa inji innata”
Cikin sauri ta kar6i niqan tareda ladan niqan nata naira goma,ta dubi yaron tace”to Ashiru kadawo anjima kad’an ka d’auka mata”
Yaron Yajuya yafice da gudu,batayi qasa a gwiwa ba tatashi takoma wajan datake niqa da dutsin niqa irinna da can,tsumma tasa tagoge jikin dutsin, sannan tafara zuba geron akan dutsin, tadora wani dutsin d’an qarami Wanda ake riqe shi da hannu, sannan tafara niqa musu geron,yunwa tasa cikinta ya murd’a,lokaci d’aya wani irin hawaye yazubo mata,tasaka bayan hannunta ta share taci gaba da niqan.
Tsaf tagama yin niqan burabusko ta ajiye musu agefe, sannan ta dawo wajan Malam Manu dayayi tagumi hannu bibbiyu yayi zurfi cikin tunani tazauna sannan tabashi naira goman da Ashiru yakawo mata ladan niqan datayi, ta meqa masa kudin tace”Malam kayi haquri kadena tunani dan Allah,duk wani tsanani yana tareda sauqi,kaje ka siyo mana gari da siga ashago sai musha”
Cikin sauri ya kar6i kud’in sannan yatashi tsaye yace”to Bilkisu,ubangiji Allah yayi miki Albarka”
Cikin kulawa ta amsa masa,sannan ta kwanta tana maida numfashi tareda shafa qaton cikinta tanajin tsananin qaunar cikin tana sake ratsata.
Malam Manu bai jimaba yadawo hannunsa daukeda garin kwaki da siga,shine yajiqa musu,yadawo yazauna akusa da’ita yace”Bilkisu tashi musha gaarin”
Saida ta runtse idonta sannan tatashi daqyar,tazauna tafara sha.
Canjin hannunsa daya rage na qwandala biyu ya’ajiye agabanta yace”ki adana wannan canjin a wajanki ko zaki sai wani abu,garin nera biyar nasiyo mana,da siga na naira uku,yau nayi muku horon yunwa keda abinda ke cikinki Bilkisu kiyi haquri”
Cikin kulawa tace”Babu komai malam”
Basu sake magana ba har suka kammala cin garin, sannan yayi mata sallama yafita nema,sai alokacin tasamu nutsuwa,qarfin jikinta yadawo harta samu damar gyangyad’i anan qasan bishiyar.
Baidawo gidan ba sai yamma lis,hannunsa d’aukeda baqar leda,alokacin tana zaune tana tunanin yanda zatayi tasamu kudi taje tasaro kayan gwanjo kamar yanda tasaba siyarwa kafin jarinta ya karye.
Zama yayi kusa da’ita yace”Bilkisu ga gaarin kwaki nasake samo mana”
Wani irin farinciki ne ya wanzu a fuskarta,ta kalleshi da kulawa “Ina kasamu kudi Malam?”
Cikin farinciki yace”bakin titi naje na zauna, sai Allah yakawo wani baqo,na kar6i kayansa nayi masa dako,yad’auki naira hamsin yabani,shine naje shago nasiyo mana garin kwaki dashi,kinga ai zamu dade muna ci”
Gaarin taduba tagani sannan tamaida dubanta gareshi tace”ai kuma babu abun had’i malam,ko zaka daure kamaida masa saiya rage gaarin yasako mana siga na canjin?”
Saida malam Manu yayi jimmm…sannan yace”eh kema kuma kince wani abu,to bari naje nakai masa,duk abinda kikace ai haka za’a yi Mai gadon zinare…”
Murmushi tayi batare datace masa komai ba,har yaje yadawo tana tunanin mafita akan yanda za’a yi tasake Samun jarin kayan gwanjo amma tarasa mafita.
Bayan sunyi shirin bacci da daddare tanajin yanda yake shafe mata jikinta da Addu’ah,ta kalli kyakykywan Black Beauty d’in mijin nata tana yaba irin kulawar dayake bata duk da bashi dashi,cikin qasan zuciyarta tanajin qaunar sa tana sake ninkuwa aranta,cikin kulawa dawata irin soyaiya tace”SULAIMAN….”
Cikin sauri ya kalleta,saboda zai Iya cewa yadad’e rabon dayaji Bilkisu takira sunansa kai tsaye,saide Malam,amma yasan cewa duk yanda akayi maganar dazata fad’a masa tabbas mai muhinmanci ce,cikin kulawa yace”na’am mai gadon zinare”
“inason ganin qanina FAROUQ,inaso bayan na haihu kayimin qoqari nasamu naje naganshi,idan ba’a samu kud’in ba,to kasamu ko saqon wasiqa ne atura masa,baisan inada ciki ba,tabbas da yasan halin danake ciki,zaizo yaganni”
“Bilkisu wannan ne abun dakike buqata?”
Ahankali ta d’aga masa kanta alamun amsawa.
Ajiyar zuciya yasauke yace”nayi miki alqawari insha Allah zanyi abinda kikace Bilkisu,kina haihuwa dazaran kin zubar da wanka zamu shirya ni dake muje can nijar d’in kiga danginki,kinga nima nasake ganin FAROUQ d’in,rabona dashi tun bayan aure na dake”
Daganan yad’aga hannayesa yayi karatu yatofa acikin hannun nasa, sannan yasake bin jikinta yana shafa mata addu’ar har hannunsa yasauka akan manya-manyan nashanunta,wani irin numfashi ta sauke najin dad’i,tanajin yanda yake murza mata nashanunta ko kad’an batayi kuskuren hanashi ba,daga baya ya lalla6a ya kwanta,yanaci gaba da abinda yake har yayi nasarar futo dasu waje yad’ora bakinsa akai,wani irin numfashi taja med’an qara wanda yake nuni da cewa taji dad’in abinda yafara d’in,wannan dalilin yana d’aya daga cikin abinda yasa take qaunar Manu,kuma tayi haqurin zama dashi saboda shid’in ba baya bane ta wannan Fannin,ya’iya sarrafa mace sosai.
Tsawon lokaci yana abu d’aya kamar jariri,ahankali tasaka hannayenta tariqe fuskarsa dashi,cikin sanyin murya me cikeda kasala dajin dad’i tace”meyasa Manu na baya gajiya da shan wannan abun ne?”
Murmushi yayi yace”ajinina abun yake Bilkisu,bazan Iya daina soba,koda abunda yake cikinki yazo wannan duniyar,bazan Iya barmasa yadinga sha shi kad’ai ba”(🙈)
Murmushi tayi me sauti,bata qara cemasa komai ba,hakanne yabashi qwarin gwiwar jiyar dasu wani irin dad’i wanda yasa suka manta da hali dakuma quncin rayuwar dasuke ciki.
Washegari da safe garin kwakin daya siyo musu jiya shi suka jiqa sukasha,sannan yayi mata sallama yafita,bai dad’e da fita ba aka kawo mata wankau,babu musu ta kar6a tazauna tafara wanke musu kayan tana daga zaune,tana cikin shanya kayan wankin aka sake kawo mata surfen dawa,shima ta kar6a ta surfa ta bushe musu,tanemi waje ta zauna ta qirga kud’ad’en data samu yakama naira dari biyu da hamsin,kudin ta ajiye agefenta, sannan ta zubawa tafin hannunta ido tana kallon yanda hannunta yayi wani iri,uwa uba gefen hannunta duk yayi kanta gashi hannun yayi wani irin tauri kamar ba hannun mace ba,amma data tuna yawan kudin data samu har d’ari biyu da hamsin sai hankalinta ya kwanta ta manta da batun halin da hannun nata yake ciki,taji komai yawuce.
Hijabin ta ta d’auka tazura, sannan ta nemi niqab dinta ta d’aura,tafuto tanufi gidan Tabawa me kayan gwanjo,gaba d’aya kudin hannunta tabata,tasiyo wasu daga cikin kayan gwanjo na yara,bata koma gida ba saida tabiya wajan wata tela tarage mata fad’in kayan,sannan ta nufo gida tashiga maqotanta tana shaida musu cewa ankawo kayan gwanjo.
Bayan Malam Manu yadawo ta nuna masa,yayi farinciki sosai yayi mata Addu’ah akan Allah yasa albarka, Washegari da safe bayan malam Manu yafita itama shiryawa tayi kamar kullum tasaka niqab dinta tashiga cikin gari,tana tafiya ahankali tana shiga gida-gida tana tallar gwanjon kayanta,kasancewar yanayin damuna ake ciki hakan yasa bata dawo gida da kaya ko d’ayaba,dukansu ta saida su tas.
Cikin farinciki tadawo gida ta zauna ta qirga kud’in da ribar data samu dakuma uwar kud’in gaba d’aya kud’i suka koma naira d’ari bakwai,cikin farinciki ta d’aga hannunta tafara godewa Allah bisa ni’imar dayayi mata,dakuma nasibin datake dashi akan kayan gwanjo.
Malam Manu kuwa bai nufo gida ba sai yamma lis, yana cikin tafiya yaga mutane sunsha gabansa,cikin tashin hankali yaja yatsaya saboda ganin gaba d’ayansu babu wanda baici bashi awajansa ba,ciki harda Aminu me shago wanda yaje ya kar6i bashin alabo a wajansa tun Bilkisu tana laulayin ciki,cikin qarfin hali malam Manu yace”Aminu ya akayi kukasha gabana kuka tareni haka babu magana,aiko hannu kwabani mu gaisa ko?”
Cikin tsantsar rashin kunya Aminu yace”Malam Manu munji labarin ka saida kekenka harka samu sukunin biyan bashi amma mu dayake munyi shiru mun zubama ido shine kahanamu namu kud’in,to munga alama kud’ad’en mu kariga kaci ham,ba futowa zasuyi daga hannunka ba,danhaka gara muyi maka dukan kud’inmu ko zamu huce taqaici…”(🙆🏻♀️)
Cikin sauri Malam Manu yace”ku tsaya kuji,kuyi haquri nayi muku bayani wallahi suma wanda suka kar6i kudin…”
Basu bari Malam Manu yagama magana ba suka rufeshi da duka saida suka kaishi qasa,daqyar wani tsoho daya dawo daga gona ya qwaci malam Manu a hannun su,gaba d’aya sun nuna masa jiki,gefen bakinsa ya fashe saida wannan tsoho yabashi sauran ruwa irin wanda ake tafiya dashi gona ya wanke bakinsa, sannan yabashi haquri suka rabu.
Koda ya koma gida bai fad’awa Bilkisu abinda yafaru ba saboda kada hankalin ta yatashi,cikin sanyin jiki Yanemi waje yazauna jikinsa ko’ina yana masa ciwo,umarni yabata tadafa masa ruwan wanka,cikin farinciki kuwa tatashi tadora masa ruwan, yaga sai fara’ah takeyi kamar gonar auduga da alama zata bashi wani daddad’an labari ne,ido yazuba mata yana aikin kallonta,yana tuna irin baiwar da Allah yayi mata na kyau dakuma shi Karan kansa baiwar da ubangiji yamasa na Samun ta amatsayin mata, ya tabbatar da’acikin birni suke babu yanda za’a yi manyan masu kudi su barshi ya auri Bilkisu,duk wani kai kawo datake yana kallonta kamar yasamu tv.
Koda yafuto daga wanka shiru yayi yana kallonta yayi jirim…kamar wanda aka masa albishir da mutuwar sa.
Baiwar Allah Bilkisu batasan yana mata wannan kallon ba,saida ta juyo ta fuskanceshi sannan tace”Malam meyafaru?naga yanayin ka ya sauya meyake damunka?”
“Bilkisu duk lokacin danake tare dake inajina wani mutum na daban,kina ‘DEBE MIN KEWA aduk lokacin dana kasance cikin qunci ko tunani,babu abinda yake damuna Ina tunanin hanyar dazanbi ne domin insamo kud’in dazan siya miki raagon suna tunda kin shiga watan haihuwar ki”
Murmushi tayi ta kalleshi tana sakin ajiyar zuciya tace”saboda wannan kake tunani? to Abishirinka,ga kud’in kayan gwanjon dana siyar d’azu naira d’ari bakwai ne,ka ajiyesu awajanka kafara tarawa insha Allahu zamu tara kud’in abun suna”
Cikin farinciki ya kar6i kud’in yana kallonta yace”Bilkisu bai kamata ki tara kud’in abinda zamu siya ayi miki yanka dashi ba,wannan haqqinane amatsayina na uba”
Cikin rashin damuwa tace”karka damu Malam,zan iya sadaukar maka da komai nawa inde zamu taru mu rufawa kanmu asiri,kasaki ranka muyi farinciki malam,ubangiji yana sane damu”
Cikin farinciki Malam Manu yace”hakane Bilkisu,Allah yayi miki Albarka,Allah yabaki abinda kikeso duniya da lahira Bilkisu”
Cikin farinciki tace”Amin Malam”
Kallon kud’in hannunsa yayi,yad’ago kansa ya kalleta lokaci d’aya jikinsa yayi sanyi,kallonta yake kamar ba gobe,saide kwata-kwata batasan yanayi ba,zuciyarta tana cikeda farinciki ta kyautatawa mijinta, tasa shi walwala,akoda yaushe fatan ta tayi sana’ah ko zasu samu su rufawa kansu asiri shiyasa kowa yasanta a unguwar inde aikin hannu ne,babu abinda batayi,itace niqan dutsi,wanki, surfe,dakuma saida kayan gwanjo idan tasamu ribar kud’i me yawa.
Da daddare shine yayi mata Addu’ar bacci kamar yanda suka saba,sama-sama take jinsa yana tofa mata Addu’ah saboda agajiye take tilis nan da nan wani irin nannauyan bacci ya kwasheta.
Yayinda Malam Manu yakasa runtsawa yasata agaba yana kallonta kamar bai ta6a ganinta ba,jikinsa yayi mutuqar sanyi,ahankali yasaka hannunsa ya shafa cikinta,sannan ya shafa fuskarta, wani irin hawaye yazubo daga idonsa,yadad’e yana hawaye har kusan qarfe uku nadare,ahankali yatashi yaduba takarda ad’akin,akwai wata tawada ta rubutu itama yad’aukota yayi rubutu ajikin takardar da Ajami.
kasancewar a wannan lokacin be’iya Boko ba,amma yasan yanda zaiyi rubutu da Ajami,hawayen idonsa ya share ya ninke takardar ya ajiyeta agefen fuskarta,yabude dakin yafuto, ya qarewa gidan nasu kallo, yafashe dawani irin kuka sannan yafice daga gidan cikin sauri.(😭)
Kiran sallar farko ta farka taji ana sheqa musu ruwan sama,tashafa gefenta bataji malam Manu ba,sai tayi tunanin ko yana tsakar gidane yana tattara musu ‘yan tarkace,tasake juyi daqyar saboda girman cikinta, taci gaba da baccinta,bata sake farkawa ba saida gari yayi Haske,cikin fad’uwar gaba ta yunqura tatashi tana salati saboda wani irin mummunan mafarki da tayi,saita danganta hakan da rashin yin sallar asuba da batayi ba akan lokaci,tamiqe tana hamma ta tattare dogon gashin kanta daya warware saboda bacci,tafuto tsakar gida taga yanda tabar komai jiya,haka yake yana nan yanda yake,a fili tace”to malam kode shima yau ya makara ne? bai tasheni sallah ba,ga gida yana nan yanda na barshi na kwanta,kode yana band’aki ne?”
Ta d’aga murya tace”malam!!”
Taji shiru,ta d’auki buta tashiga band’aki tagama uzurinta tafuto tayi alwala tayi sallah,bayan ta idar da sallar haka nan ta tsinci kanta da rashin kwanciyar hankali,malam bai ta6a fita yaqi sanar da’ita inda yaje ba,koda tana bacci zai tasheta yafad’a mata,to ina yaje haka?
Cikin hanzari tatashi tafuto tsakar gida gabanta yana fad’uwa,mayafin da tayi sallah dashi shine ajikinta tashin hankali yasa ko takan niqab d’inta batabi ba,suba wani d’akuna ne dasu ba bare tace yashiga ciki,d’akinsu ne qwaya daya jal kuma baya nan,qofar gida tafuto tana faman kiran sunansa, sai dube-dube take tana fad’in “Malam…!!”
Amma shiru kakeji,wasu d’aid’aikun masu tafiya gona sai kallonta suke saboda sunga abun mamaki,basu ta6a tunanin akwai kyakykywar halitta kamarta acikin qaunyensu na Garin Malam ba,wani me Keke yazo wucewa shima zai tafi gona tsabar waigowar dayake yana kallonta har fad’uwa yayi sakamakon cin karo dayayi dawani tsoho.
Tana ganin abunda yafaru tasan cewa itace sila,cikin sauri taja mayafin jikinta ta6oye fuskarta,sannan tajuya takoma gida,d’akinsu tashiga tafara tattare musu kayan Shimfid’arsu,anan idonta yasaauka akan wata farar takarda,gabanta ne yafad’i da ganin takardar cikin sauri tad’auka sannan ta bud’eta,lokaci d’aya taci karo da rubutun mijinta Malam Manu inda ya rubuta mata cewa ( KIYAFEMIN ) jikinta ne yafara rawa,taji numfashinta yana sama kamar zai d’auke,hakan yana nufin kenan Manu yagudu yabarta,daqyar tasamu ta fuzgo numfashinta tareda sakin wata irin gigitacciyar qara,wanda yajawo hankalin maqotanta.
(so sad,sorry Mama Bilki)