A Jini Take Hausa Novel Complete

A Jini Take Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

A JINI TAKE

*(IZZATA)*

 

By

_*Zarah Maitama (Mhiz Innocent)*_

 

 

 

_Bismillahir rahmanir raheem_

 

 

_*CHAPTER ONE*_

Page _01

 

 

 

__La’asar ce sakaliya dan kuwa rana ma ta kusa faɗuwa. Babu laifi akwai iska, irin iskar nan me daɗi, duk da ba lokacin sanyi bane, se dai yanayin garin sosai yayi kyau da kuma daɗi. ‘Yan mata ne guda biyu ke tafiya sanye cikin hijab dogo har ƙasa kala ɗaya. Ɗayar da niƙab a fuskarta ta saƙala jaka a kafaɗarta, yayin da ɗayar ke sanye da hijab kawai. Hannun wadda ke sanye da niƙab riƙe yake da wani ƙaramin kyakkyawan yaro, fari ƙall da shi, wanda ba ze wuce 5years ba sanye cikin uniform, wanda hakan ya alamta min cewar daga Islamiyya suka dawo. A hankali na kai dubana zuwa fuskar wadda babu niƙab a fuskarta, kwata_kwata kyakkyawar fuskarta ta babu annuri, da alama wani abun ne ya ɓata mata rai ko kuma akayi mata. Se dai duk da yadda fuskarta ta ke a haɗe hakan be hanani ganin tsagwaron kyawun fuskarta ba, wadda idan ba dan shigar da ke jikinta ba da kai tsaye zan iya kiranta da balarabiya, dan kuwa komai na ta yayi kama da nasu, dara_daran idanu masu ɗauke da baƙar ƙwayar ido me matuƙar ɗaukar hankali da wani irin ƙyalli, dogon siririn hancinta da ke zaune ɗass akan fuskarta kamar an zama, se kuma ɗan ƙaramin red lips ɗinta me matuƙar kyau wanda shi ne yafi komai ƙawata fuskarta. Har suka ƙarasa gida babu wadda tace da er uwarta komai.

 

Babban gida ne me kyau sosai, duk da ba wani ƙyale ƙyale ne a gidan ba amma kasancewarsa me girma da kuma yanayin ginin gidan na zamani ne yasa ya ƙawatu matuƙa. Tun a parlour AFAAF ta jefar da jakar hannunta da tun da suka fito daga makaranta ta kasa maƙalata a kafaɗa se riƙeta tayi a hannu, wucewa ɗaki tayi kamar wadda aka kora. Ammi ta bi ta da kallo kafin ta dawo da kallan nata kan AFRAH dake kwance niƙab ɗinta tace

 

“Ke lafiya kuwa? Yau kuma me aka yiwa Afaaf?” Dariya wadda aka kira da Afrah tayi daidai lokacin da ta ida kwance niƙab ɗin fuskarta, wanda hakan ya bani damar ganin kyakkyawar farar fuskarta wadda kallo ɗaya na mata na gane ita ɗin er biyun Afaaf ce, dan kuwa kamarsu ɗaya sak, kamar yadda Afaaf ke da manyan idanu haka Afrah ke dasu, dogon hanci da ƙaramin baki me kyawun gaske haka Afrah ke da shi, ba dan tsayawa nayi ina kwatanta muku kamanninta ba da bazan iya gano wani banbanci a tsakaninsu ba, saboda kamarta su ta ɓaci, banbancin da zan ce na gano guda ɗaya ne shi ne, saɓanin Afaaf da ke ɗauke da baƙar ƙwayar ido ita Afrah brown ne da ita me maiƙo.

 

“Tubarkallah Masha Allah!” Shi ne abin da na faɗa sanda na sake tabbatar da lallae waɗannan en biyun irin waɗannan da ake kira da identical twins ne, se dai su waɗannan nin sun fita daban ta hanyoyi da dama, a ƙiyasce ba zasu wuce 17 years ba, kowaccensu na da kyawun jiki me kyau, hatta kuma da jikinsu ba zaka iya banbance wani banbanci ba dan kuwa dukansu basu da ƙiba.

 

“Ammi ita da Gwani ne..” Afrah ta faɗa da siririyar muryarta me daɗi wadda ke ɗan rawa a duk sa’ilin da take magana, zaka ɗauka tsoro ko wani abun makamancinsa ke sanya muryarta ta rawa, se dai ba haka bane, haka muryarta ta take a halitta, hakan kuma shi ke ƙara ƙawata muryarta ta ta sake zama ta daban.

 

“Gwani kuma? Me ya faru? Wani abun ta sake yi?” Ammi tayi tambayar a jere. Girgiza kai Afrah tayi kafin tace

 

“A’ah Ammi, kawai dai an chanja mana malami ne, yanzu Gwani AFFAN ne malamin ajinmu.”

 

“Auu shi ne take fushi saboda makarantarta ce ko kuwa me?” Ammi ta faɗa a ɗan zafafe. Se da Afrah ta ɗan yi kalar tausayi da fuskarta gudun kada Ammin ta fusata sosai sannan tace

 

“A’ah fa Ammi, ita abin da ya ɓata mata rai yadda ya aiko wai a faɗa gobe ze fara da karɓar hadda.” Tsaki Ammi ta ja tana girgiza kai, wannan hali na Afaaf na ƙona mata rai wani lokacin, kamar ba za tace komai ba se kuma tace

 

“Idan ta so kada tayi, zata haɗu da ni ko da Abbanku.” Daga haka ta miƙe ta bar parlourn. Bin ta da kallo Afrah tayi ba tace komai ba se dauke ajiyar zuciya da tayi sannan ta dawo da dubanta cikin ɗakin kana ta miƙe ta wuce ɗakinsu.

 

 

.. Se da Afrah ta gama komai sannan ta koma kan gado, ta ɗauko Qur’an ɗinta dake cikin jaka ta buɗe ta soma karantawa. Tana cikin yin karatun Afaaf ta fito daga toilet da alama wanka tayi, ta ƙarasa ta shirya cikin kayan bacci sannan ta dawo kan gadon tana ƙoƙarin kwanciya. Rufe Qur’an ɗin Afrah tayi sannan tace

 

“Me za ki yi?” Se da ta harari gefe sannan tace

 

“Bacci zan yi.” Karo na farko kenan da na fara jin muryar Afaaf wadda itama cikin ikon Allah muryarta su iri ɗaya ce, dan idan wata a cikinsu ma tayi magana ko da ka sansu ba zaka banbance ba se dai idan ka ga fuskarsu.

 

“Malama ki ɗauki Qur’an ki yi karatu, kin san dai halin Gwani.” Se da ta tura baki sannan tace

 

“Ai yau so nake na ƙure shi wallahi, mutum se faɗin rai da nuna shi wani ne bayan ba kowa bane. Ban da tsabar iyayi meye na wani cewa ze karɓi hadda a ranarsa ta farko a ajinmu? Ni babu haddar da zan yi.” Ta faɗa tana neman waje zata kwanta. Da sauri Afrah ta riƙota tace bayan ta haɗe rai

 

“Lulu ki fita a idona wallahi. Gwanin kike faɗa wa haka? Ki tashi malama ki yi karatu kin san dai ba ɗaukar iskancinki ze yi ba.”

 

“Don Allah Didi ki ƙyaleni.” Afaaf (Lulu) ta faɗa a ranta tana sake tuna wannan ƙarfa_ƙarfar da Gwanin ke ƙoƙarin yi. Cika hannunta Didi tayi kana ta haɗe fuskarta waje ɗaya ta cigaba da haddarta a zuciya. Ita kuwa Lulu kwanciyarta tayi, se dai yanayin yadda ta ga fuskar Didin ya hanata yin baccin. Tsaki ta ja a hankali ta miƙe zaune tana tura baki. Ita kuwa Didi ko kallanta ba tayi ba, duk da dama ta san Lulun ba zata iya kwanciya tana fushi da ita ba. Sauka Lulu tayi ta ɗauko Qur’an ɗinta ta koma kan gadon itama, bata kalli Didi ba ta soma karatunta a zuci, se dai ba haddar take yi ba, dan kuwa ta riga ta ƙudurcewa kanta ba za tayi haddar ba, se dai kawai ta shiga muraja’a hankalinta kwance. Ta riga Didin idarwa, da ta ga har lokacin bata kalleta ba se ta ɗora kanta akan kafaɗar Didin da itama take kan aya ta ƙarshe a maimaita haddar da take yi. Se da ta idar sannan ta saka hannunta ta buge kan Lulun. Tura baki Lulu tayi kafin tace

 

“Kai Didi, nayi karatun fa. Kiyi haƙuri.” Murmushi Didi tayi dan itama ba wai tana fushi da Lulun bane kawai dai ta ɓata ranta ne dan tayi karatun, dan haka tace

 

“Toh na ji, amma dai ki dena abin da kike yi musamman akan Gwani Affan, ni ban san me ya tare miki ba!” Taɓe baki Lulu tayi dan ita sam bata da buƙatar jin magana akan Gwanin, ko a makaranta ne kuwa ballantana a gida.

 

“Haka kawai fa Didi, ɗaga kansa yayi yawa kuma..!”

 

“Ni kam ya isheni haka nan Afaaf, ke kodayaushe zancenki kenan!” Riƙo hannun Didi Lulu tayi kafin tace

 

“Pls Didi mu bar maganar nan, Allah kuwa raena ɓaci yake yi.”

 

“Naa ji.” Didi ta faɗa tana ƙoƙarin miƙewa. Langaɓar da kai Lulu tayi kafin tace

 

“A’ah fa Didi, ta yaya zan san kin haƙura.. Smile..” ta faɗa tana murmushin da ya sake fiddo da ainahin kyawunta. Itama Didin murmushin tayi wanda hakan ya sake ruɗani akan tsananin kamarsu da ta sake fitowa fili, dan komai na su iri ɗaya ne hatta da murmushin kuwa.

 

 

 

… Washegari wajen ƙarfe 2 da rabi Didi ta gama shirin Islamiyya, tana kallan Lulu da tun dawowarsu daga boko ta kwanta a kan gado ita a lallai bata da lafiya. Kasancewar sun makara ne ya sanyata saurin ɗaura niƙab ɗinta a jikin ƙaton mudubinsu me kyau sannan ta ɗauki jakarta ta fito. Kallanta Ammi tayi tace

 

“Har kun shirya? Ba zaki tsaya ki ci abinci ba?”

 

“A’ah Ammi sauri nake yi, kada na makara. Idan na dawo zan ci..”

 

“Toh Allah ya tsare..” ta ƙare maganar tana kallan hanyar ɗakinsu

 

“Ina Afaaf ɗin?” Kallan ɗakin tayi sannan tace

 

“Ammi wai bata da lafiya..” Kafin Ammin ta sake cewa komai Abba ya shigo cikin ɗakin da sallama. Dogon babban mutum wanda kallo ɗaya zaka masa ka san twins ɗin nan shi suka biyo, dan kuwa shi ma a kallan farko zaka gano kyawun da yake da shi. Dukkansu suka amsa masa sallamar kafin Little ya tafi ya rungume shi.

 

“Abba sannu da zuwa.” Afrah ta faɗa.

 

“Yawwah Didi an shirya ne?” Ya faɗa mata sunan da yawanci en gidan ke kiranta da shi, wanda har shi ɗin ma wani sa’in ya kan kirata da shi.

 

“Ehh Abba..”

 

“Toh Allah ya bada sa’a.. A’ah ina Afaaf?” Ya tambaya shi ma. A wannan karon ma se da ta sake kallan ƙofar ɗakin nata sannan tace

 

“Abba wai bata da lafiya.”

 

“Ji min ja’irar yarinya, sauƙin ze sameta ne tana daga kwance.. Kai Little maza je ka tasota ta sha magani sauƙin ze sameta acan.” Babu musu kuwa Little ya zura da gudu zuwa cikin ɗakin. Da ƙarfi ya soma kiran

 

“Lulu! Lulu!!” Yana saka hannu ya soma yaye ƙaton blanket ɗin da ta rufa da shi. Duka ta kai masa sanda ya sake buɗe murya ya kira sunanta. Be kuma saurara ba ya ɗora da

 

“Abba yace ki fito mu tafi makaranta.” Ya faɗa da muryarsa me daɗi duk da akwai ɗan tsami kaɗan a cikinta. Dukan da ta masa ne ya sanya shi kai hannu ya riƙe wajen yana kwaɓe fuska

 

“Allah se na faɗa wa Abba..” ya faɗa yana shirin yin gaba.Da sauri ta riƙo shi ta ɗan sassauta fuskarta kaɗan kafin tace

 

“Ka je kace bani da lafiya..” maƙe kafaɗa yayi yana faɗin

 

“A’ah..” Tsaki ta ja dan ta san in dae ta biyewa wannan yaron se dai faɗan da Abban ze nata ya ƙaru, hakan ne ya sanyata sakinsa kawai ta shiga shiryawa tana sake cika tana batsewa. Ta san halin Abba sarai, gudun kada ya gane ciwon ba na gaske bane ya sanya ta yin kalar tausayi da fuskarta hadda aro ƙwallar ƙarya cikin idanunta sannan ta fito, a hankali tace

 

“Abba sannu da zuwa” ta faɗa da muryarta da ta sake yin rawa fiye da yadda take. Cikin tausayawa yace

 

“Yawwah. Bari na ɗakko miki magani ki sha se ku wuce” Tun da dai ta san makaranta ce dole se taje tun da Abba ya saka baki ya sanyata faɗin

 

“A’ah Abba ai na sha, ciwon kai ne dama kuma ya warke”

 

“Toh madallah. Se kun dawo Allah ya tsare.” Didi da Little kaɗai suka iya amsawa ita kuwa Lulu ta kasa faɗin komai dan gaba ɗaya hankalinta ya tafi kan yadda zasu ƙarke ne da Gwani bayan ba tayi hadda ba, duk da yadda hankalinta ke a kwance da rashin yin haddarta ta amma yanzu se da ta ji wani tsoro tsoro na neman kamata tayi saurin basarwa tana sake cika tana batsewa. Ita kuwa Didi dariya kawai take yi a ɓoye dan kada Lulun ta gani yanzu se ta sake fusata.

 

“Yau ba zaki biyawa Masoyiyarta ki ba?” Didi ta faɗa tana kallan Lulu sanda suke dab da wuce gidansu ƙawar Lulun. Hararar gidan tayi kamar shi ne ya mata laifi sannan tace

 

“Ehh ɗin..” ta faɗa tana wuce gidan ma da sauri. Ba tace komai ba Didi se bin bayanta da tayi suka cigaba da tafiya. Sakin hannun Didi Little yayi ya koma kusa da Lulu yace

 

“Ki riƙeni kin ji!”

 

“Ba za a riƙe ba” ta faɗa tana maka masa wata uwar harara, dan yau ɗin gaba ɗaya haushin kowa take ji, musamman ma Little ɗin da kamar shi ne ya janyo mata, da yace bacci take da yanzu tana can a matsayin mara lafiya tana bacci hankalinta kwance. A yanzu kam dariya Didi tayi sosai ta cikin niƙab ɗinta, ta janyo hannun Little suka cigaba da tafiya. A haka har suka ƙarasa makarantar..

 

 

 

*** ***

Gida ne da ya amsa sunansa gida, ƙato wanda idan baka sani ba daga kallan farko zaka iya kiransa da ƙatuwar plaza. Haɗaɗɗen gida ne wanda tsayawa faɗar irin haɗuwar da yayi ɓata baki ne, dan kuwa anyi ɓarin kuɗi kamar me, an gina shi cikin tsari da ƙwarewa kamar ba a Nigeria ba. Ko daga Compound ɗin gidan kaɗai se an tashi kanka saboda yadda ta matuƙar ƙawatu da abubuwa kala kala se dai marasa hayaniya. Idan kuwa tun farko dama a cikin Compound ɗin ka tsinci kanka to fa ba zaka taɓa cewa a Nigeria kake ba. Ƙaton parlour ne da ya lamushe kujeru saiti uku a gefe guda na cikinsa, wanda anan ne aka zuba kayan ado da ƙawa aka ƙawata haɗaɗɗen parlourn da ko na shugaban ƙasa albarka, parlour ne da ya amsa sunansa parlour, parlour ne da a karan farko zaka iya kiransa da aljannar duniya saboda matuƙar haɗuwar da yayi. Akan ƙaramar kujera wani kyakkyawan babban mutum ne dake sanye cikin wata dakakkiyar shadda da kallan farko zaka mata ka san ta lamushe kuɗi na musamman, fuskarsa kuwa a kallan farko baka isa ka ƙayyade adadin shekarunsa ba, saboda yadda jin daɗi da kuma hutu suka lamushe kaso masu yawa daga cikin shekarunsa. Kyakkyawan babban mutum wanda aƙalla ya bawa 50 baya, idanunsa saye suke cikin glass me matuƙar kyau da tsada, wanda yake amfani da shi idan ze yi wani aikin da ya shafi Computer ko waya. A yanzu ma idanunsa na kan hamshaƙiyar waya ne yana dannawa cikin ƙwarewa. A nutse take takowa cikin parlourn, duk da yanayin shekarunta da suka tura hakan be hanata cin kwalliya kamar yarinya er shekara 20 ba, ƙafarta saye cikin wani hill shoe, sanye kuma cikin rantststiyar atamfa me shegen kyau da tsada, ta sha ɗauri irin wanda ake kira da ture kaga tsiya. A haka take takowa zuwa cikin ƙaton parlourn da kafin ƙarasowarta inda mutumin nan ke zaune ta ɗauki sakanni masu yawa. A nutse ta nemi waje ta zauna cikin kissa da kisisina tace

 

“Barka da wannan lokaci Yallaɓai.” Se da ya ƙarasa abin da yake yi cikin waya kamin ya ɗago ya kalleta bayan ya ɗan zame glass ɗin fuskarsa yace

 

“Barka kadai..”

 

“Aiki ake yi ne?” Ta tambaya tana gyara zama akan haɗaɗɗiyar kujerar da ke kusa da tasa.

 

“Ƙwarae kuwa. Kin je kin duba abokiyar zaman naki? Bata ji daɗi ba.” Se da ta taɓe baki sannan tace bayan ta yamutsa fuska

 

“Zan dai shiga, amma yanzu magana ce ta kawoni akan Boy.” Ƙarasa cire glass ɗin yayi ya ajje a gefe kamin ya juya ya kalleta sannan yace

 

“Yaya muka yi da ke?” Girgiza kai Hajiya Salma tayi kana tace

 

“A’ah fa Yallaɓae, ka sake kwantar da hankalinka ba wani abun yayi ba. Akwai manufofi da dama da suka saka na takura se ya tafi ƙasar waje karatu, misali raba shi da Abokansa na nan ɗin waɗanda yake biye musu, acan kuwa idan babu su na san dole ze rage wasu abubuwan. Kawai dai zuwa nayi in ji ko zaka tura a ɗakko shi ne?” Sauke ajiyar zuciya yayi, bayan yayi murmushi sannan yace

 

“Kamar na faɗa miki zan cire hannuna daga wannan maganar koh? Babu yanda ban yi dake akan fitar AREEF ƙasar waje ba kika dage, yanzu ma se kiyi komai da kanki.”

 

“Haba kai kuwa me yasa za kace haka? Ta yaya zan yadda Boy yayi karatu anan bayan ga ‘ya’yan manyan mutane na ta fita waje suna karatu wasu ma sun koma da zama acan. Se nawa ɗan ƙwalli ɗaya takk, ace yayi karatu a cikin ƙasar nan. Yanzu yallaɓae mu ba abin kunya ba ne a garemu ace ɗan gidan ALHAJI MATAWALLE guda yana karatu a cikin ƙasar nan bayan babu sa’anninsa? Wannan ma ai salon raini ya shiga tsakaninsa da ‘ya’yan talakawa ne.!” Ta ƙare tana yatsina fuska kamar wadda ta ga kashi..

 

 

 

A JINI TAKE

*(IZZATA)*

 

 

By

_*ZARAH MAITAMA (Mhiz Innocent)*_

 

 

*CHAPTER ONE*

 

Page_02

 

__Kallanta Alhaji Matawalle ke yi har ta ƙare zancenta. Ya girgiza kai yana ɗaukar juice me sanyi cikin tambulan ya kai bakinsa ya ɗan kurɓa kana ya sauke. Baya son zancen nasu yayi nisa dan be ƙarasa aikin da yake yi ba, ya kuma san idan har be amsa mata ba ba zata tafi ta bar maganar ba, shi kuma ya riga da ya tsara mutanen da zasu je taho da Areef ɗin. Se dai a kodayaushe baya nuna mata yana bin bayan yadda take shagwaɓa Areef ɗin, take so ta dinga nuna yafi kowa a cikin garin saboda kasancewarsa ɗan wanda yafi kowa kuɗi a garin a wannan lokacin.

Gawurtattu Uku 2024 Hausa Novel

“Ki je zamu yi maganar.!” Ya faɗa bayan ya kalleta fuskarsa a ɗan cunkushe, baya ma so yayi mata magana akan irin maganganunta marasa daɗi da kullum basa ƙarewa alan talaka, yayi maganar, yayi faɗan har ya gaji.

 

“Amma Yallaɓae da gaske ka damƙa komai a hannuna?” Girgiza kai yayi kafin yace

 

“Na ɗauki wannan aikin, ke dai kawai ki shiryawa dawowarsa.” Murmushi me ƙayatarwa ta saki har cikin ranta tana jin daɗi, musamman idan ta tuna yadda tilon ɗan nata ze dawo bayan tsawon shekarun da ya ɗauka a harvey Mudd College da ke California U.S. Ba ta kai ga cewa komai ba Alhaji Matawallen ya sake faɗin

 

“Ki saka a gyara masa part ɗinsa.” Da sauri ta soma faɗin

 

“Yallaɓae halin Boy ɗin ka manta? Ni da kaina zan gyara masa, idan ba haka ba yanzu zaka ji yace ɗakin yana warin ‘yan aiki.” A wannan karon ma se ta ƙare maganar tana yamutsa fuska.

 

“Allah ya taimaka” yayi gaggawar katseta.

 

“Ameen. A huta lafiya.” Tayi maganar tana miƙewa ta fice daga ɗakin. Bin ta da kallo yayi kafin ya dawo da dubansa cikin ɗakin yana girgiza kai, a kodayaushe al’amuran Hajiya Salman ƙara ƙaimi suke yi, shi har mamaki take ba shi da ta yadda ya cire hannunsa akan tafiyar Areef ƙasar waje. Bayan ta manta waye shi wajen kula da tarbiyyar Areef ɗin, shi ne take tunanin ze bar shi sakaka haka a can wata ƙasar ba tare da yana sakawa ana duba shi ba? Ya sake girgiza kai kawai yana maida glass ɗinsa ya cigaba da abin da yake yi cikin wayar.

 

.. Wayarta da tayi ƙara ta kalla, ganin kiran wadda ya shigo wayar ya sanyata ɗagawa tana cigaba da taku ɗai_ɗai.

 

“Hello Auntyn Areef” shi ne abin da Hajiya Salma ta faɗa. Murmushi wadda aka kira da Auntyn Areef tayi kana tace

 

“Na’am, toh ya ake ciki?”

 

“Cikin satin nan Boy ze dawo!”

 

“Woww!! Amma gaskiya na ji daɗi ki ce na kira a daidai.”

 

“Aikam dai. Bari zan kiraki akwai abin da zan yi yanzun.” Babu ɓata lokaci suka yi sallama da ƙanwarta ta daidai lokacin da ta ƙaraso bakin ƙaton part ɗin abokiyar zamanta. Se da ta ɗan tsaya kamar me son ganin wani abu, se kuma ta ɗan saki ƙaramin tsaki kana ta cigaba da takawa zuwa cikin ɗakin. Haɗaɗɗen ɗaki ne da ya ƙawatu da Furniture masu kyau da tsada, komai kuma na cikin ɗakin milk da coffee ne irin masu ɗaukar idon nan. Ƙaton parlour ne se dai duk girmansa be kai na Alhaji Matawalle ba. Daidai lokacin da ta shiga ɗakin ta tsinci muryar Atine (Er aikin kishiyarta) na faɗin

 

“Ranki ya daɗe cikin satin nan Yallaɓae Areef ze dawo.” Kafin Hajiya Sa’adah ta bada amsa, Atine suka yi 4 eyes da Hajiya Salma, duk se ta duburburce, ta miƙe a sukwane, a hankali ta zo ta gifta ta gefen Hajiya Salman ta fice daga ɗakin. Wata banzar harara Hajiya Salman ta bita da shi kafin ta ja ƙwafa ta ƙarasa shigowa ɗakin. Kyakkyawar farar bafulatanar da ke zaune kan kujera sanye cikin wata haɗaɗɗiyar atamfa me mugun kyau ɗinkin doguwar riga, ta juya ta kalli inda Hajiya Salma ke tsaye dan ganin abin da ya saka Atine fita haka babu faɗar dalili, se taga Hajiya Salma na cigaba da takowa zuwa cikin ɗakin. Murmushi ta saki duk da na ƙarfin hali ne kasancewar ta ɗan kwana biyu bata ji daɗi ba.

 

“Ki ƙaraso mana” Ƙarasawar tayi ciki se dai bata nemi waje ta zauna ba, ta ɗan ajje numfashi kafin tace.

 

“Har an kawo miki gulmar yarona ze dawo kenan?” Ta tambaya tana kallanta. Ɗan murmushi Hajiya Sa’adah tayi kana tace

 

“Ba gulma ba ce, kawai dai ta faɗa min ne ko da ban sani ba” Jinjina kai Hajiya Salma tayi tana ɗan taɓe baki

 

“Eyyah, don Allah Sa’adah ki fita a harkar ɗana, ban san wannan ɗin wane irin abu ne ba. Ka da kice zaki shirya masa wani abu, dan yana da uwar da zata shirya masa, baya buƙatar na shishshigi. Don Allah ki kama kanki ki bari idan kika haifa se kiyi rawar kan akansa.” Tun da ta soma magana Hajiya Sa’adah ke kallanta, ba tayi mamakin soma maganar da tayi ba dan dama ba yau ne karon farko da ta ke faɗa mata makamancin waɗannan maganganun ba, se dai yau ɗin mamakin yafi kamata sosai musamman da har se da ta shigo ɗakinta sannan take jifanta da waɗannan kalaman. A nutse ta buɗe baki duk da yadda take jin wani irin ɗaci a cikin bakinta, maganganun Hajiya Salman tabbas sun daketa sun kuma taɓata sosai

 

“In Sha Allah.” Shi ne abin da ta iya furta wa sannan ta ɗauki wayarta tayi stairs ɗin da ke cikin ɗakin nata. Tsaki Hajiya Salma ta ja tana bin ta da kallo, a ranta tana fata da addu’ar Allah yasa ta bar mata ɗanta, ta dena wannan shishshigin ta bari idan ta haifi na ta se ta yi duk abin da za ta yi.

 

 

 

 

… A ɓangaren Twins kuwa ko da suka isa makaranta kai tsaye aji suka nufa, lokacin babu wanda ya shigo ajin, da yake ajin ba baya ba wajen sanin ya kamata se kowaccensu ta ɗauki Qur’an ta soma bitar haddar da za a karɓa yau ɗin. Kallan Lulu Didi tayi tace a hankali saboda karatun da ake yi

 

“Ki maimaita karatun mana” ta faɗa ganin ta ɗauki wani hadith tana dubawa.

 

“Didi na iya fa, ba se na maimaita ba.” Sanin Lulun na da kaifin hadda ne ya sanyata yadda da hakan, ta rabu da ita, ita kuma ta cigaba da karatunta. Duk da yadda idanun Lulu ke kan hadith ɗin da take karantawa amma gaba ɗaya hankalinta ba ya kai, duk taurin kanta se take ji kamar ta ɗauki Qur’an ta yi haddar, amma se ta ji zuciyarta ta ƙeƙashe, hakan ne ya sanyata jan tsaki da siririyar muryarta ta cigaba da karatunta. Dukan da aka ɗaka mata a kafaɗarta ne ya sanyata saurin juyawa bayan ta ɗan saki ƙara saboda yadda dukan ya shigeta.

 

“Masoyiya!” Ta faɗa tana buɗa baki. Galla mata harara wadda ta kira da Masoyiyar tayi kana tace

 

“Ni zaki wa rashin mutunci koh? Ya miki kyau” ta faɗa tana neman waje ta zauna kusa da ita ta haɗe rai.

 

“Ke dallah makara fa muka yi, na ɗauka kin tafi” Lulu ta faɗa tana kallan Fateema Kabeer wadda ta kasance babbar ƙawarta a Islamiyyar ta su.

 

.. Sanye cikin wata lallausar brown ɗin jallabiya, sumar kansa saye cikin irin wannan naɗin da larabawa ke yi a wajen goshi zuwa bayan kansu. Kyakkyawa ajin farko, fari me ɗauke da wasu idanu masu mugun kyau, manya masu ɗauke da baƙar ƙwayar ido me shegen kyau, wata irin gira ce da shi wadda take a jere kamar wadda aka saita ta ta zauna akan fuskarsa ta matuƙar ƙawata ta, hakan ya sa har haɗewa da junansu se da suka yi, saboda se da suka bada wani irin shahararren kyau a tsakiyar goshinsa. Bakinsa ɗan ƙarami ne kamar na mace, kuma ja kamar wanda yake shafawa jan baki ko wani abun makamancinsa, se dai sam ba haka bane. Hannunsa ɗauke da wasu littattafai na Addini kasancewarsa ɗaya daga cikin manyan Malaman Addini a makarantar, ba ma a makarantar kaɗai ba hatta a yankin yana ɗaya daga cikin manyan Malamai, duk da ƙarancin shekarunsa da ba zasu wuce 25 ba amma da yake gada yayi daga wajen mahaifinsa da ya kasance Babban Malamin Addini a garin. Se hakan ya sake siyo masa soyayya daga wajen mutane da dama, ba ga mata ba ba ga maza ba, kowa ƙaunarsa yake. Se dai kuma shi ɗin mutum ne me matuƙar bauɗaɗɗen hali, idan dai har ka fahimce shi a bai_bai ba zaku taɓa zauna wa lafiya ba, zamanku baze taɓa daɗi ba, se dai kuma idan har ka fahimce shi shi ɗin mutum ne me matuƙar kirki da sanin darajar ɗan adam. Abu ɗaya ne yake sakawa a kasa fahimtar inda ya dosa kasancewarsa miskili na ƙin ƙarawa, hatta da magana bata dame shi ba, za a iya masa wani abun ko kuma ayi abu a gabansa amma ba ze ta tanka ba. Sam baya ɗaukar raini, ba ya ma bada fuskar da za a raina shin shi yasa ba a taɓa jinsa da wata ɗaliba ko ɗalibi ba, dan idan dai har ze shiga aji abin da ya kai shi ne kaɗai yake yi, daga nan ba lallai ma wata magana ta shiga tsakaninsa da wani ba. Sallamarsa da muryarsa me amo da daɗin sauraro yayi cikin ajin, se dai kasancewarsa mutum mara fara’a a halitta ya sa fuskarsa a cunkushe take, dan kuwa za a iya kiran Gwani Affan da “Sad Man” Gaba ɗaya ajin suka haɗa baki wajen amsawa, se ya sako kansa cikin ajin cikin nutsuwarsa da tayi matuƙar haɗuwa da tsarin halittarsa. Ɗan lumshe manyan idanunta Lulu tayi tana jin yanda ƙirjinta ya buga sanda ya shigo cikin ajin, tsoron da ya lafa mata tun ɗazun yanzu ya dawo sabo, amma saboda ƙeƙashashshiyar zuciya irinta ta se ta sauke ajiyar zuciyar tana tsara abin da zata faɗa idan ya zo kanta a karɓar haddar.

 

Tsayawa nayi ina kallan ikon Allah sanda na ji bakinsa ya furta

 

“Ina Hafsa Abba?” Dan ban taɓa tunanin za a iya yi masa Hausa ya ji ba ballantana ya furta da bakinsa saboda daga yanayin halittarsa har shigarsa da larabawa yayi kama, se dai maganar da yayi ce ta sanyani fahimtar tabbas bahaushe ne, se dai a cikin hausawan irin na daban ɗin nan ne, wanda za a iya cewa sun samu komai, musamman ma dai a wajen Gwani Affan da aka ba shi kyau, da kuma ilimin Addini, se dai kamar kowanne ɗan adam ba za a rasa wani abun da ya rasa ba, ban san a wajen Gwani Affan ko akwai abin da ya rasa ba dan ni dai a fili ban gan shi ba. Zumbur Hafsa Abba ta tashi bayan maganar da Gwani yayi, tace a hankali

 

“Malam ga ni!” Ba tare da ya kalleta ba ya jinjina kai sannan ya fita daga ajin, bin bayansa tayi zuwa wajen tana ɗan gyara tsayuwarta.

 

“Se gobe idan Allah ya kai mu zan kar6i hadda! Ki sanar da en ajin”

 

“Toh Malam” Daga haka ya juya ya soma takawa dan barin wajen cike da nutsuwa, se da ya ɓacewa ganinta sannan ta juya ta koma ajin ta sanar da su saƙon shi. Lulu kaɗai tayi farin ciki da hakan, dan kuwa gaba ɗaya en ajin farin ciki suke da dawowar Gwanin ajinsu. Haka dai ba dan sun so ba suka haƙura. Yau ɗin sosai take cikin farin cikin tun da suka fito daga makarantar murmushi yaƙi barin baby face ɗinta. Didi na lura da ita kuma ta san dalili amma bata kulata ba. Maganar da Fatima Kabeer ta yi ne ya sanyata kallanta

 

“Masoyiya baƙuwa na miki magana tun ɗazu.” Juyawa Lulu tayi ta kalli wadda Masoyiyar ke magana a kanta, itama ita take kalla tana murmushi, yaƙe tayi kana tace

 

“Sannu!” Daga haka bata sake cewa komai ba. Daidai lokacin da suka zo zasu rabu, se suka yi sallama da yake ita baƙuwar zuwan makociyarsu Fatima Kabeer ne ya sa suka yi hanyarsu.

 

“Wallahi ƙawar nan ta ki ta min Fatima, kyakkyawa da ita kamar ita tayi kanta” Murmushi Fatima tayi tace

 

“Allah koh?” Ba tare da tunanin komai ba Abida tace

 

“Wallahi kuwa dama zaki haɗani da ita!” Kallanta Fatima tayi cikin er rashin fahimta da maganar ta ta sannan tace

 

“Ban gane ba?” Dariya Abida tayi kana tace

 

“Mu yi ƙawance mana”

 

“Uhmm ai ga ki ga ta, dan in dai Masoyiya ce wallahi dizgaki za ta yi” Se da Abida ta tsaya ta kalli Fatima har se da Fatiman ta tsargu sannan tace

 

“Shi kenan!” Daga haka babu wadda ta sake cewa komai suka cigaba da tafiya.

 

 

 

_Claremont California U.S

Tunnel Rd Berkeley

East Bay Hotel_

 

 

.. Haɗaɗɗen ɗaki ne da ke cikin East Bay Hotel wanda ya amsa sunansa ɗaki me kyau, ado da ƙawa, ya matuƙar ƙawatu da wasu Furniture ‘yan ubansu. Kiɗa ke ta shi a cikin ɗakin cikin wata ƙatuwar speaker da ke gefe guda, sosai waƙar ke tashi da ƙarfi kamar ba mutum ɗaya ke ji ba. Babu kowa cikin ɗakin bayan speaker da ke cigaba da aikinta. Taɓa ƙofar toilet da na ji anyi ne ya sanyani saurin kai idona wajen. Farar ƙafarsa da ke cikin wani takalmin wanka itace na fara hangowa lokacin da yake zame takalmin kafin ya kai ga fitowa gaba ɗayansa. Singlet ce a jikinsa se towel ɗin da ke ɗaure daga ƙugunsa yayin da ya ɗora wani akan kafaɗarsa. Yanayin rigar da ke jikinsa itace ta fallasa halittar ƙaƙƙarfan jikinsa da ke ɗauke da wasu lafiyayyun kwantattun gargasa baƙa wuluk, wadda ta zauna ɗass akan farar fatarsa da ta gaji da gyara, hutu gami da jin daɗi. Ƙarasawa yayi gaban mudubi yana ɗan kaɗa kansa dake ɗauke da tulin suma wadda aka yiwa gyara na musamman, hakan ne ya bani damar ganin kyakkyawar fuskarsa da ke ɗauke da wasu shu’uman idanu, wanda kallo ɗaya idan yayi wa mutum ze iya rikicewa, ba ga mace ba hatta ga maza idanunsa kan firgita wasu mazan, idan kuwa mace ta bari ya ɗora shu’uman idanunsa akanta idan dai har bata rikice ta faɗa ƙaunarsa ba toh ba za ta bari ta sake iya haɗa idanu da shi ba saboda yadda idanun nasa suke kamar suna ɗauke da wani maganaɗisu ne, a iya idanunsa kaɗae an ƙure kyau, dan kuwa idanunsa na ɗaya daga cikin abin da ya kwashe kaso masu yawa daga cikin kyawun da Allah ya bashi, se kuma dogon siririn hanci da ke zaune akan fuskarsa kamar an zana. Duk da yanayin yadda kiɗan ke tashi da ƙarfi hakan be hana shi rage sautin ba se ma buɗe baki da yayi ya shiga bin sautin waƙar da se ka rantse shi yayi ta saboda yanda yake bin kowanne waje cike da ƙwarewa da muryarsa me daɗin sauraro. Ya ɗauki wajen rabin awa yana shiryawa sannan ya gama cikin wata haɗaɗɗiyar riga da crazy jeans da suka matuƙar yi masa kyau. Wata er ƙaramar abin hannu me kyau da tsada ya ɗauka ya saka a hannunsa da shi kansa yake ɗauke da kwantacciyar suma me matuƙar kyau. Wayarsa da ke ajje kan gado ta shiga ruri, se a lokacin ya ƙarasa ya rage sautin kiɗan da ke tashi, wanda da alama ba dan kiran da aka masa ba ba ze rage sautin ba. A nutse ya koma ya jingina da jikin mirror shu’uman idanunsa a ɗan lumshe kamar yadda suke a halitta, shi ba irin manyan idanun nan gare shi ba, basu da girma can kuma ba ƙanana ba ne se dai tasirinsu da kuma kyansu na musamman ne kamar yadda shi ɗin ya kasance na musamman.

 

“Bad!” Shi ne abin da Lucky da ya kira wayar ya faɗa bayan ɗaga kiran da Areef yayi.

 

“Yeah Lucky, What’s going on?” Yayi maganar da muryarsa da ita kanta ta daban ce, me daɗin sauraro gami da wani amo da ke ɗauke da ita.

 

“Amm ka jirani harkar nan ta samu zan kawo maka har ɗaki.”

 

“Nop, Let’s meet at school couz mutanen Dad na nan.” Da mamaki Lucky yace

 

“A’ah Bad kada kace min tsoro kake ji?” Ya tambaya dan ya san halin Bad boy ɗin. Wani murmushi Areef ya saki kamar ba zece komai ba se kuma yace

 

“Lucky! Just let’s meet there” ya faɗa yana taune lips ɗinsa na ƙasa idanunsa a lumshe..

 

 

 

 

 

Me son karanta A JINI TAKE (IZZATA) har ƙarshe ze tura ₦300 ta 8124818273 Zahra’u Yusuf Ishaq Opay. Shedar biya ta 08124818273.

Post a Comment

Previous Post Next Post