Magani A Gonar Yaro Yanda Ake Gyaran Jiki
*MAGANI A GONAR YARO*
*YANDDA AKE GYARAN JIKI DA GARIN BAWON LEMU*
GYARAN JIKI______HASKEN FATA
garin bawon lemu
madarar kwakwa
Nikakken tumatir
Sai ki gamesu wuri daya bayan kinyi wanka sai ki daukosu ki goge jikinki dashi ki dirje jikinki da kyau da kyau har tsawun minti 15__30 sai ki samu ruwan dumi ki dauraye jikinki dasu,bayan kin dauraye jikinki sai ki samu organic production na mai ammah na lotion mai kyau ki shafa
TAUSHIN FATA
Magani A Gonar Yaro
garin bawon lemu
furen rose
Oatmeal
Sai ki hadesu ki niqa,bayan kin niqa sai ki samu yogot,Zuma,da kuma man piya(avocado)
Bayan kinyi wanka sai ki shata a jiki ki darje jikinki da kyau da kyau, bayan minti 15_30sai ki wanke da ruwan dumi
Sai a kula wurin GYARAN jiki da fuska,gaba daya kada ayi su wuce sau biyu ko sau uku a sati.
Domin bawon lemu yana da karfi sosai a jiki Dan haka kada muyi amfani dashi na wuce misali
Add Comment