Littafan Hausa Novels

Gawurtattu Uku 2024 Hausa Novel

Gawurtattu Uku 2024 Hausa Novel

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

_Gawurtattu uku 2024_

 

 

WANKA DA GARI…

 

 

FATIMA SUNUSI RABIU

Ummu Affan

 

 

*Book 1 Page 3-4*

 

Tana kammala faɗar hakan tayi wucewarta, daman saboda yaranta za tayi girkin kuma sun fita da Abbansu faƙat.

Zaliha kuwa taji haushin kalaman Sakinaa don haka ta ɗau alƙawarin sai ta yi wa Sakinaa sharrin da sai tayi da na sanin abinda ta faɗa mata.

Ko da su Abban Yusra suka dawo Sakinaa ko leƙowa ba tayi ba, yaranta suna shugowa tayi sauri ta musu shirin islamiyya ganin lokaci ya kusan ƙurewa sannan ta rakasu har gurin Direban da ke kai su makaranta.

Tana dawowa daga rakasu ta iske Abban Yusra da Zaliha a farlour, za ta wuce bedroom taji yana kiranta. Tsayawa tayi ba tare da ta juyo ba, bai damu da yadda tayin ba ya ce,

Humaira Hausa Novel Complete

“Tun da kin hana Zaliha ta dun ga shigar miki kitchen sai ka ce ke ki ka gina sa? To daga yau ke zaki din ga mata girki duk abinda take so za ki dafa.

Da sauri ta juyo ta kalli Zaliha cike da mamakin jin irin sharrin da ta mata.

“Haba Abban Yusra yan zun ni ce zan zama mai girkin Zaliha sai ka ce wata ‘yar aiki, ai ba abin da ka ɗauke ni kenan ba.”

“To da me ki ka dace? Ai wallahi yafi kyau ma a ki raki da ‘yar aikin don matsayinku guda ne yanzu a wajena.” Ya faɗa yana wani hura hanci.

“Shi ke nan.” Tana faɗa ta wuce ba tare da ta kuma cewa komai ba.

Tun daga ranar Sakinaa ba tayi ƙasa a gwiwa ba ta zamo ita ke yin komai na gidan duk Zaliha tasa ya kori ‘yan aikin gidan Baba Maigadi kawai aka bari sai Direbansu Yusra, hatta wanki da guga ita ce. Daman tana wanki idan ta so, haka ba ko wanne kaya take bayarwa ba, guga kam tana ci mata rai.

Yaranta Yusra da Fahat Zaliha ta ɗau ɗawainiyarsu sosai take kula da yaran, shirinsu zuwa School da islamiyya haka fannin abincinsu ba ta wasa, ko a da can Zaliha me ƙaunar yaran ce.

Hajiya kuwa kusan kullum sai tazo gidan tayi tawa Fatima tujara da habaice-habaice, tayi ta tsine mata ita da iyayenta, wani sa’in ma su ukun suke haɗuwa suyi ta mata rashin mutumci da tujara, maƙaƙen maganganu kuwa tana shan su da gori.

Fatima ba ta da kwanciyar hankali wuni kuka, tayi duhi ta jeme tayi baƙi sosai ta rame kullum cikin kuka take saboda tsabar wahala da baƙin ciki.

Wata rana tana zaune a kitchen tana aiki ta jiyo muryar Hajiya na kiranta, tashi tayi da sauri har tana tuntuɓe ta zube a gabanta.

“Hajiya ashe kin zo barka da zuwa.”

Hajiya ta daka mata tsawa, “Ya isa haka, yau dai zamanki yazo ƙarshe a gidan nan.” Sakinaa ta kalli Hajiyar da sauri ta ce, “Me nayi kuma Hajiya? Ki rufa mini asiri na mutu maza su kai ni, don Allah kar ki tozarta ni, idan ba ki kalle ni ki duba su Fahat.”

Zaliha ta taɓe baki, “Ƙwarƙwasa raka kishiya biki, yau dai ƙarya ta ƙare sai a koma gida aci gaba da cin tuwon dawa miyar kuka daman da shi aka raine ki.”

Hajiya ta ce, “Hakkun kuwa sai a gaida me dattin hula, da mai baƙin ɗanƙwali.” Zaliha ta saka dariyar mugunta tare da buga cinya, “A koma can idan ma ya amsheki idan kuma ya ce abi duniya ne to ai gaki gata maraba take da waɗanda ma suka fiki, ke duniya wanda bai zo ba ma jiransa take.”

Tuni ruwan hawaye suka tsinke a fuskar Sakinaa Hajiya ta ce, “Wannan yaron inaso ka sallame ta, idan kuma zaka ci gaba da zama da ita to, ni dai naga rabuwarku tafi.”

“Hajiya duk abin da ki ke so haka za a yi.” Numfasawa tayi “A’a kar ka ce na shiga haƙƙinka.”

Takarda da biro ya ɗauko ya yi rubutu ya cillawa Sakinaa yana faɗin, “Ko ɗaya Hajiya ai na yadda ƙwallon mangwaro ne na huta da ƙuda.” Ɗauka Sakunaa tayi ta buɗe a hankali saki ɗaya ta gani.

Hawaye ne suka wanke fuskarta kallonsu tayi, sai kuma ta miƙe tsaye ta wuce.

Beedroom ɗinta ta shiga, ta faɗa toilet wanka tayi sannan ta fito, ta shirya cikin wasu riga da siket na atamfa sannan ta sauke ƙaton akwatinta ta zuba kayanta da duk wani abu mai muhimmanci nata, ta zuba takardun makarantarta a ƙaramar jakarta da kuɗaɗenta waɗanda Abban Yusra ke bata kafin su fara samun wannan matsalar, ta sagala jakarta ta jawo a kwatinta ta fito.

Har zuwa lokacin suna Parlour, suka kalleta ta kallesu gyara tsayuwa tayi ta kalli Hajiya da Zaliha ta ce,

“Na gode da abinda ku kai mini ba zan ce komai ba domin nasan ni najawa kaina.” Kallon Abban Yusra tayi.

“Kai kuma tsakanin ni da kai wanda ya cutar da wani Allah ya saka ma shi.”

Sannan taja akwatinta tana kuka tabar gidan, bata tsaya tambayar yaranta ba domin tasan yadda Hajiya ke ƙaunarsu ba zata ba ta su ba.

Tana fita ta samu a daidaita sahu ta tsayar tahau bayan ta sanar da shi inda zai kaita, suna zuwa ta biya shi kuɗinsa sannan taja akwatinta zuwa cikin gidansu wanda ginin ƙasa ne ɗan madaidaici, irin na malam Shehu.

Da sallama ta shiga cikin gidan jiki a sanyaye, daga can cikin ƙuryar ɗaki taji ana amsa mata sallama, wata mata ta fito wacce ba Ummanta ba ce, ta gaishe da matar tare da tambayarta,

“Umma ba ta nan ne?” Matar ta ce,

“Wacece Umma kuma?”

Sakinaa ji tayi kamar an buga mata guduma a ka, ta ƙarewa gidan kallo tabbas nan ne gidan iyayenta gidan da tayi ƙuruciyarta a ciki ta dawo da kallonta ga matar.

“Ba nan ba ne gidan Malam Abdullahi Bakanike ba?”

“Gaskiya ba nan ba ne sai dai ban sani ba ko waɗanda suka tashi ne ki ke nufi, kuma shekararmu uku a gidan nan mijina saya.”

HAwaye ne ke bin fuskar Sakinaa ta ce, “Don Allah ko kin san inda suka koma?” Matar ta ce “Wallahi ban sani ba.” Cikin shassheƙa Sakinaa tayi wa matar godiya tare da fita jikinta na ƙyarma, mummanan tsoro ya shigeta ga tsananin tashin hankaki.

Jan akwatinta tayi gaba tana tafe tana kuka, kai tsaye garejin da Abbanta ke aiki ta nufa bayan sun gaggaisa da mutanan da ke wajen waɗanda ba ta san su ba take tambayar ɗaya daga ciki. “Don Allah Malam Abdullahi nake nema.” Wani mutumi ya ce, “Wane ne kuma haka?” Tayi masu kwatancen kamaninsa yadda zasu gane, wani dattaju ya ce, “Ai ya daɗe da barin garejin nan kusan shekaru uku kenan.”

Nan take tashin hankalinta ya nunku har ya gaza ɓoyuwa a fuskarta. Ta fito garejin tana kuka sosai bayan sun tabbatar mata ba su san inda ya koma ba.

Can nesa da garejin ta samu guri ta zauna bis a wani ɗan dandamali tana kuka, ina iyayenta suka je? Meke faruwa da su a halin yanzu? ta sake sakin wani rikitaccen kuka nan take rayuwarta ta baya ta fara dawo mata, tagumi tayi tana hawaye ta fara tariyo rayuwarta ta baya.

 

TUSHEN LABARIN

 

Malam Abdullahi talaka ne sosai sana’arsa Kanukanci wato gyaran moto babura har da kekuna. Malam Abdullahi mutum ne me wadatar zuci duk da shi talaka ne bai hana ya wadata gidansa da abinci da sutura ba domin gidansa ba anemi komai an rasa ba daidai gwargwado yana da ƙoƙarin neman na kansa.

Matarsa ɗaya Hadiza, asalinsu ‘yan Bakori ne ƙaramar hukumar jahar Katsina, domin daga shi har Hadizan ‘yan can ne, ya je garin Kaduna ne domin neman kuɗi shida abokinsa Saminu, abu kamar wasa har ya dawo da Hadiza nan, tun suna gidan haya har Allah ya buɗa masa ya fara gini don mutum ne me ƙoƙarin neman na kai.

Bayan ya kammala suka dawo garin gidansa, ɗakuna biyu ne a madaidaicin gidan ɗaya ciki da falo sai ɗaya guda sai kuma kitchen da bayi na wanka dana bahaya a waje, ginin ƙasa ne amma ya yi masa fulistar na suminti haka tsakar gidan shafe yake da suminti tas.

Sun daɗe ba su sami haihuwa ba, sai da suka shekara takwas da aure, aikuwa da Hadiza ta samu ciki sun yi murna da farin ciki mara musaltuwa, nan aka dun ga renon ciki da tattalinsa har ya isa haihuwa, ta haifi kyakkyawar ɗiyarta mace.

Sosai suka yi murna da farin ciki da samun ƙaruwar nan, inda ranar suna yarinya ta amsa NANA Sakinaa. Yarinya kyakkyawa wanka tarwaɗa, anyi bidiri don ‘yan Bakori sun zo a ka sha bikin suna daga baya suka koma gida.

Sakinaa ta taso cikin so da ƙaunar iyayenta suna ji da ita sosai musamman Abbanta. Abba akwai sanyi ko laifi tayi baya bugunta sai dai nasiha, garama Umma tasha bugunta idan tayi ba daidai ba

Ummanta mace ce mai natsuwa da kamala ga son addini da son mutane, haka Abbanta kowa a unguwarsu yana yabonsa ya samu shaida ta mutane kam.

Shekarar Sakinaa uku Abbanta ya sata boko da islamiyya don yarinya ce mai kazar-kazar ga surutu, ai kuwa ana sata baki ya ƙara buɗewa gata da ƙoƙari sosai.

Abbanta ke kaita boko da safe biyu na rana ya ɗaukota, idan yaci abinci ya koma wajen aiki daman da ya kai ta da safe yake wucewa aikin, idan yaci abinci ya koma huɗu na yamma yazo ya kai ta islamiyya, ƙarfe shidda ya ɗaukota su dawo gida shi ma daga lokacin ya dawo aiki kenan sai ya yi wanka ya fita masallaci sai anyi isha’i ya ke dawo wa daga nan kuma su zauna baranda su ci abincin dare sai ya yi wa Sakinaa tatsuniya da haka har tayi bacci sannan su je su kwanta. Haka rayuwarsu ta ke har zuwa lokacin da ta iya zuwa makaranta da kan ta.

Lokacin shekarunta goma, har abinci ita ke kai wa Abbanta gareji.

Ƙawarta wacce suka shaƙu sosai da ita itace Zaliha ɗiyar baƙotansu ce, kaf unguwarsu da ita aka san ta, kullum tare suke zuwa makaranta boko da islamiyya ajinsu guda ne.

Shekarun Fatima sha biyu ne lokacin tana Jss one, ɗin ƙaramar Secondary ta dawo kai wa Abbanta Abinci ne a gareji, tafiya take a hankali cikin natsuwa kamar wata babbar mace.

Shi kuwa yana cikin moto yana kallonta yanayinta ya burge shi, yasha haɗuwa da manyan mata ‘yan ƙasar nan da wajenta amma bai ga yarinyar da ta burgesa ba irin wannan ƙaramar yarinyar.

Bin ta yake a hankali cikin mota, ganin ta shiga wani lungu da mota bazata iya shiga ba, sai ya fito ya din ga bin ta a baya, ganin za ta ɓace masa ya sa ya yi saurin ƙara takun sawunsa yana kiran “Ƙanwata! Ƙanwata!!”

Ji tayi kamar daga sama ana kiran ƙanwata sai ba ta wai ga ba, domin a tunaninta ba ita ake kira ba ganin bata da yaya ita ɗaya iyayenta suka haifa.

Jin ana ƙara kusanto ta ana kiran, “Ƙanwata ji mana ko baki son sabon Yaya?” Hakan ne yasa ta tsaya chak tare da juyowa.

Wani kyakkyawan saurayi dogo taga ni yana zu ba mata murmushi, sanye yake cikin ƙananun kaya Jeanse da t-shirt ya yi kyau sosai sumar kan nan nasa baƙ wuluk sai shinning take, hannusa ɗauke da wani agwogwo daga gani zaka gane na gold ne saboda ƙyallin da yake, kana ganin takalmin ƙafarsa zaka ga ne na manya ne domin daga yanayinsa ka san komi na shi na musamman ne.

Ƙaraso wa Ya yi hannayensa zube cikin aljihu ya ce, “Ni suna na UMAR FARUUƘ.”

A zuciyarta ta furta.

‘Kuji mutum kamar na tambaye shi sunansa, amma fa sunan ga daɗi kuma suna manya ne, hakan ma na musamman ne.’

“Ke mene ne sunanki?” Ya katse mata tunani da tambaya.

“Ni?” Ta tambaya tana nuna kanta, cike da ƙuruciya. Abin ya ba shi dariya ya ce, “Yes ke ni ba kiji na faɗ miki nawa sunan ba?”

“Sakinaa!” Ta faɗa kai tsaye domin ita ba ta iya ƙarya ba.

“Wow nice name, suna me daɗi kuma babban suna.” Murmushi kawai tayi.

“Ni zan wuce kar Ummana ta ji ni shuru.” Bin bakinta ya yi da kallo yadda take magana cikin natsuwa. Murmushi ya yi. “Ummanki ko dai Ummanmu? don haka wuce muje gidan tare.”

Cike da mamaki take dubansa za tayi magana ya rigata, “Ko baki son inje incewa Umma tayi sabon ɗa kuma yayan Princess?” Kallonsa tayi “Wace ce kuma Princess?” Cike da yarinta tayi tambayar.

“Ke ce mana, sunanki yana da girma a wajena.”

Rufe fuska tayi cike da kunya, murmushi ya yi “Mu je ko?”

A can gida kuwa Umma taji Sakinaa shuru, saɓa hijab tayi zata fito kenan sukaci karo da Abba ya ce, “Lafiya ina zuwa kuma Hadiza?”

“Garejin daman za ni naji Sakinaa shuru.”

“Shuru kumakina nufin bata dawo ba? Ai tuntuni ta tafo gida.” Dukansu sai hankalinsu ya tashi za su fita nemanta kenan sai ga su.

Kallon-kallo suka fara Umar ya ce, “Sannunku da gida.” Ya duƙa har ƙasa ya gaishesu, suka amsa cike da mamaki. Abba ya ce, “Lafiya dai ko yaro? Sam ban waye ka ba?”

Murmushi ya yi “Lafiya ƙalau kawai mun haɗu a hanya ne.” Nan Sakinaa take sanar musu abin da ya faru.

Abba ya ce, “A’a shugo daga ciki a shumfiɗa maka tafarma.” Ya miƙe yabi bayansu, Umma ta shimfiɗa musu tafarma a barandar gidan.

Umar ya ƙara gaishe da su Abba, suka amsa masa cikin sakin fuska. Ya ɗaura da cewa. “Suna na Umar Alƙasim Inuwa mun haɗu da Sakinaa a hanya shi ne na tsayar da ita muka gaisa har na biyota gida in gaisheku.”

Abba ya ce, “Babu komai Ummaru da fatan dai lafiya, ba wani abin tayi maka ba? domin ba a shaidar ɗan yau haihuwarsu ake ba a haifi halinsu ba.”

“Babu komai Abba kawai dai haka nake jinta kamar Ƙanwata.” Gaba ɗaya sukayi dariya. Abba ya sake cewa, “Ai haka Allah ke ikonSa baka san mutum ba sai kaji ya kwanta maka, kamar yarda nima kallo ɗaya na maka naji kashi ga raina daga ganinka gidan mutunci ka fito.”

Umar ya yi murmushi “Na gode Abba ƙwarai nima jinku nake kamar iyayena.”

Umar ya daɗe gidan sai da yaci tuwan daren Umma sannan ya bar gidan, yadda suke sai ka ɗauka daman sun daɗe da sanin juna. Wanda wannan ne kuma silar faruwar ko wacce zanen ƙaddara daga rayuwar Sakinaa..

**** **** ****

Da sallama ya shiga katafaran Parlourn gidan. Daddy ne ya miƙ da sauri ya ruƙo shi.

“Faruuƙ daga ina ka ke? Har ka iya kai wa irin wannan lokacin?”

Mummy ta ce, “Ka ta da mana hankali ko abinci mun kasaci Faruuƙ ina ka je?”

Murmushi ya yi.

“Dad an Mum me kuka mayar da ni ne?”

Da sauri Daddy furta “Ƙaramin yaro.”

Mummy ta ce, “Jaririma zaka ce Daddyn Faruuƙ.”

Ɓata fuska ya yi cike da shagwaɓa ya ce “Duk girman nan nawa amma kuke cewa haka ko aure fa aka mini lafiya ƙalau zamu zauna da matata ”

Mummy ta fara tafa hannu ya yin da Daddy ya riƙe baki.

“Faruuƙ aure! Karatun kuma fa?” Murmushi ya yi “To ai naji kuna ce mini ƙaramin yaro ne. Dundu Mummy ta kai masa ta ce, “Kaci gidanku daga ina ka ke, sai fa ka faɗa mini ko dai taɗin kaje don mu ga ne ka isa auren?”

Zama ya yi kusa da ita ya ce, “Daga gidansu Sakinaa nake.” Nan ya sanar musu komai ya ɗaura da cewa “Wallahi suna da ƙyirki sosai.”

Mummy ta ce, “Faruuk ba dai saurin yarda ba, kar fa ka ɗauko mana abin da wataran zai saka mu kuka.”

“Haba Mummy don Allah ki yi mana fata na gari.” Shafa kan sa tayi “Is ok my son tunda kana son su muma dole mu so su.” Daddy ya ce, “Wannan haka yake.”

Washe gari ya dauki iyayensa sai gidansu Sakinaa, ƙwarai sun yi mamakin ganin gidan, ba su taɓa tunanin talakawa ba ne, haka suka shiga sun ga karramawa gurin Abba da Umma, haka ma Sakinaa

Kallo ɗaya Mummy tayi wa Sakinaa taji yarinyar ta shiga ranta shima Daddy haka.

Tun daga wannan rana zuminci mai ƙarfi ya kullu tsakanin iyalan gidan su Sakinaa da Umar kai ka ɗauka daman ‘yan uwa ne su tun usul….

08104335144

 

 

#WankaDaGari

#UmmuAffan

#GawurtattUku

#LabarinSakinaa

Add Comment

Click here to post a comment