Kurman Baki Hausa Novel Na Hugumah
Kurman Baki Hausa Novel Na Hugumah
*_Bismillahir rahmanir rahim_*
*_KURMAN BAK’I_*
*H U G U M A*
PAGE 01
_Akwai saqonni masu tarin yawa a ciki,saidai kuma KURMAN BAQI ne me wuyar fassaruwa,ga duk me nisan zangon hankali da tunani zai tsinkayi hakan,DAN JAGORA NE ga mata,musamman masu KISHIYA,kuma hannunka me sanda ne ga masu sana’a data shafi labarin dake cikin littafin_
*NOTE:qirqirarren labari ne wanda ya dace da matsalolin da mata ke fuskanta a yanzu,komai dake ciki qirqirarre ne,idan ya dace da zahirin rayuwar wata to arashi aka samu*
Zaune take zaman farar stool din dake ajjiye gaban dressing table din dakin. K’afarta daya kan daya tana kuma karkadasu da wani irin sauri. Kallo daya tak zaka yiwa fuskarta ka fahimci akwai zallar bacin rai mai mugun yawa shinfide a saman fuskarta,bacin ran da ko shakka babu yana yiwa zuciyarta wani irin fusga da kud’a me ciwo.
Hatta da launin idanunta zuwa fuskarta sun sauya,abinda zai alamta maka kuka tasha bana wasa ba,da alamu kuma ba wani lokaci me tsaho ta dauka da gama kukan ba.
Har cikin zuciyarta takejin wani irin masifa da tashin hankali suna sadakarta. Qoqari take tayi ta taushi zuciyarta amma kuma kamar hakan yana neman gagararta.
Ita din tana cikin jerin sahun matan da basu iya cinye fushi da bacin rai ba tare da zukatansu sun furta ko sun furzar da shi ga dukka wanda yayi silar afkwarsu a wannan yanayin ba.
“Idan ba damuwa don Allah zan dan fita yau din,amma bazan wuce awanni biyu ba zan dawo in sha Allah” Sautin muryar dake tashi sama sama ya ratso ta cikin windows dinta,ya kuma keta labulayenta ya isa ga kunnuwanta.
Isar sautin muryar kadai ga kunnuwanta amma sai taji kamar an sakar mata guduma cikin tsakiyar zuciyarta. Tana da muradin jin amsar da wanda akayi maganar dominsa zai bayar,wannan ya sanyata miqewa zumbur ta kuma kai ga labulen ta yaye a zafafe.
Fes take iya hango mutum biyun wanda ke magana cikin wata irin nutsuwa a tsakaninsu. Tsayayyen namiji ne wanda ke tafe da tsaho da kuma qibarsa gaba daya,wanda hakan ya bashi wani irin kyakkyawan murjajjen jiki da ya qara masa kyau da cikar zatin da kai tsaye ya isa ya amsa sunan NAMIJI. Duk kuwa da cewa shi din ba wani mugun kyakkyawa bane,amma sam sam bai hada koda hanya da kalmar MUNI BA. Baqi ne da bahaushe kan kira da wankan tarwada,wanda yayi wani irin kyau me cike da nutsuwa cikin wani lallausan yadi ruwan sararin samaniya a jikinsa. Ganinka na farko da shi zaka tabbatar da cewa shi din gwanine wajen iya murza hula da sanya sutura ta zauna a jikinsa,hakanan telansa ya qware qwarai da gaske gurin baiwa dinki haqqinsa,dukka wadannan abubuwa suna da cikin abubuwan da suka hadu suka qarawa SALEEM kwarjini da cikae kamala da kuma siffa.
Matar Mutum Hausa Novel Dandano
Matar dake a gefansa kuwa duka duka shekarunta ba zasu haura ashirin da takwas ba,idan tayi nisa da yawa ashirin da Tara zuwa talatin. Ita dinma baqa ce kamarsa,saidai nata baqin har yafi nashi gogewa,chocolate color ce sosai,mai matsakaicin tsaho,ba gajeriya bace,saidai kuma bata kai tsahonsa ba sam sam. Tana da manyan idanu masu matsaikatan girma,hakanan hancinta yana da tsaho da tudu. Komai nata matsakaici ne,itama tana da wani kyau na daban,wanda baiyi yawa ba.
“Ina zuwa kenan?” Ya tambayeta yana duban fuskarta da murmushi ya subuce mata
“Gidan aunty khadija mana” kai ya jinjina yana murmushi
“A dawo lafiya Allah ya tsare” ya fada yana same fadada murmushinsa. Qaramar dariya ce ta qwace mata
“Da sauri haka?,saboda kaji gidan aunty deeja ne?” Ido ya fiddo yana sakin wani murmushin
“Ta yaya zan hanaki zuwa nan?,ai nasan ta samu ne” ya fadi qasa qasa. Siririyar dariyar da ta ajjiyeta musamman saboda shi ta saki,cikin salon nuna jin kunya tace
“Ni bance ba,amma dai sirri ne”
“I know,bance sai naji ba nima,Karki jima please” ya fada cikin tausasawa yana takawa zuwa muhallin ajiyar mota na gidan dake dauke da motoci gida uku kamar yadda iya adadin abinda zai iya dauka din kenan
“Nasan ba ka son yin dare a waje daddynsu,ba zan kuma saba ba in sha Allah” dakatawa yayi da tafiyar ya waiwayo yana dubanta. Wani murmushi ne saman fuskarsa wanda ya sani bai isa ya hanashi fita daga fuskar tasa ba. Tattausan murmushin itama ta saki sannan tadan rausaya kanta cikin alamun jin nauyin kallon da yake matan. Tamkar an saya hannu an finciko zuciyarta daga qirjinta haka ZAINAB taji. Taji na zata iya qara koda second daya a tsaye tana kallon wannan abun ba. Sai ta saki labulen da sauri ta kuma juya da sassarfa tana rufar qofa zuciyarta na sake soyewa da wani irin zafi da radadi.
Ya za’a yi mutumin da tun daren jiya ta rasa ganin walwala koda qanqani saman fuskarsa?,hatta da abincin darensa ma bai samu ci ba,ya kuma gaya mata baijin dadi ne a haka suka kwana amma shine yake rausaya da idanu da wani irin shu’umin kallo irin haka?. Bayan ko yau da safe a tsaitsaye ya shirya,ko fuskantarta suyi magana ya kasa yi,sai baya da ya juya mata,ya gama shirinsa a gaggauce ya fice?. Ta dauka ya jima da barin gidan ma,ashe yana tare da wannan makirar baqar matar tasa.
“Allah ya bada sa’a,ya tsare mana kai,ya baka ikon nemo halak ka ciyar damu da ita,a dawo lafiya” idanunsa ya lumshe kadan,addu’arta tana masa tasiri har tsakiyar zuciyarsa. Wanann addu’ar na cikin jerin abubuwan dake faranta zuciyarsa duk safiya,ta kuma yi masa rakiya har zuwa shagonsa na kasuwa.
Da fara’ar shimfide akan fuskarsa ya bude idanunsa yana motsa labbansa. Sai idanun nasa suka sauka akan zainab wadda ke tsaye tana numfarfashi nata idanun itama a kansa. Janye dubansa yayi daga kanta ya mayar ga RUQAYYA yana cewa
“Ameen ameen,na gode qwarai,Allah yayi albarka”
“Ameen” ta amsa masa tana shafa tafukan hannuwanta dukka biyun saman fuskarta,sannan tayi taku biyu taja baya daga kusa da zainab din,ba tare data dubeta ba saboda sanin cewa ko meye zata gani saman fuska da idanunta ba alkhairi bane,sai ta saka kai cikin gidan tana zarcewa sashenta.
“Har ka warke kenan?” Zainab ta jefa masa tambayar kai tsaye tana ci gaba da dubansa, tambayar da tazo da salo ma titsiye da kuma son qure mutum
“Dama ai ba ciwo nakeyi ba,nace dai miki bana jin dadi ne kawai,kuma kowa yana tsintar kansa a irin wannan yanayin”Ya fada yana janye dubansa daga kanta,baqinciki na lasar zuciyarsa. Ita sam kwata kwata ma kamar bata kishin kanta?,bata taba damuwa da ta sauya wasu abubuwa ba ko don ruqayya. Ruqayya din bata taba zamar mata abar kwatance ba,tafi bawa abu guda daya muhimmanci,sannan wannan abu dayan tafi bashi himma kima da darajar data zarce ace an bashi din.
“Kaji dai tsoron Allah kada ranar qiyama ka tashi da shanyayyen barin jiki wallahi…..koda yake ba laifinka bane,kaci ka sha,duk da shima asirin ai yana tadda hali ne” ta fada a zafafe sannan ta juya abinta tana komawa cikin gidan da sauri saurinta.
Bai dakata da kallonta ba har ta bacewa ganinsa,ya sauke numfashi mai nauyi ya zura key yana qoqarin bude motarsa yana girgiza kai hadi da jan wani qaramin tsaki. Ba abinda ke yawo a idanunsa sai rigar baccin jikinta wadda duk dalli dallin maiqo ne a jikinta,abinka da abu silk jirwaye da maiqo bashi da wuyar nunawa a tattare dashi. Iya tsaiwarta a wajen,qamshin jikin ruqayya ya baje ya koma inda ya fito,ba komai a wajen sai wani yanayi dake nuni da lokaci yayi da gangar jikin mutum ta fara buqatuwa zuwa ga wanka,wankan da yayi imanin koda za’a yishi to saifa idan ya dawo ko kuma yana dab da dawowa idan an tafka sa’a a ranar.
Zuciyarsa cike da qiyasce qiyasce da juya al’amuran zainab ya tashi motarsa sannan ya sulale ya fice a gidan yana son daidaita nutsuwarsa kota halin qaqa.
A nutse ta tura qofar parlor din nata da bata gama rufewa ba saboda tana sauri ta cimmasa ta gaya masa zata fita din a yau. Ko ina a gyare yake tsaf a killace,sai ka rantse bata da yaro ko guda ko kuma amarya ce,saboda sassanyan qamshin turaren wuta da burner din dake kunne take bayarwa. Gurin burner din ta isa ta kasheta,ta gama bata qamshin da takeso ta kuma biya mata buqatarta. Sassanyan qamshin da tasan saleem din yafiso a ko yaushe bata taba yarda ta rabu dashi,bata damu ba da ranar girkinta ne ko ba ita ke da girki ba,itadai burinta a ko yaushe wannan qamshin ya zamana shine abu na qarshe da ya shaqa dag wajenta don ya zama abokin tayashi tunata tsahon yinin da zaiyi gurin neman halal dinsa.
A nutse ta buda daya daga cikin qofofin dake parlor din. Madaidaicin dakin yara ne me dauke da qananun gadaje guda uku,cikin dayan gadon yarinya ce ke kwance tana bacci. Sai data leqata ta tabbatar babu wata matsala sanann ta dawo a nutse ta rufe qofar,ta isa ga madaidaicin dining dinta me kujera hudu tana tattare plates din da ta gama breakfast. Yau duka tayi abincin karin tare da yara ta diba nata saboda tanason fita din,batason tsaiwa hada wani lokaci ya qurace mata.
Tsaf ta gama hada plates din da cups din,zata debe ta wuce kitchen taji an banko qofar babu zato ba tsammani,abinda ya sanyata waiwayowa da sauri tana fadin
“Hasbunallahu wani’imal wakil,waye haka?”
Kanta tsaye ba tare da shakka ko tsoro ba ta ratso cikin falon tana kallon ruqayya. Kallo na tsantsar qiyayya da tsana muraran. A kaf fadin duniya batajin akwai wata halitta da zuciyarta ta tsana bayan ita. Idanunta ta kuma saukewa akan plates da cups din dake riqe a hannun ruqayya,wannan ya sake bata tabbacin eh lallai,bayan ya tsallake breakfast din data shirya masa a nan yazo yayi karin kumallo?.
Ta hadiye wani abu me tauri da ya tsaye mata a wuya me mugun radadi,sannan ta watsawa ruqayya wani mummunan kallo.
“Nice nan,zuwa nayi na gaya miki abinda kika kasa ganewa,tunda baki da tsoron Allahn da zai ganar dake hakan,inason ki sani ke din baki isa komai ba kamar yadda baki isa ki rabani da saleem ba,duk yadda kike ganin bokanki tsafinki da tsubbace tsubbancenki sunayin tasiri,wallahi baki isa ki raba alaqar da Allaj ya hada ba,kuma a juri zuwa rafi da tulu da diban ruwa,dole wataran zai fashe” tana kaiwa nan ta juya a zafafe tana jin inama zai yiwu ta rufe ruqayyan da mummunan dukan da zai sanya a rasa gane ainihin halitattarta. Duk kuwa da tayi imanin babu wani kyau dake rudar saleem tattare da ruqayyan,face zallar tsafi da tsubbace tsubbace,tunda dai indai ana batu na kyan fuska da hasken farar fata,ko kusa ko alama ruqayya bata isa ta matso koda gefanta ba,wannan abun shi yake sake bata tabbaci a ko yaushe iyawa da gogewa a bun malamai da ‘yan bori suke sanyawa ruqayyan ke shan gabanta a zuciyar saleem,wanda dukkan me dogon nazari da tsinkaye koda ba’a gaya masa hakan ba shi da kansa zai fahimta.
Kasa ce mata komai ruqayya tayi face binta da kallo data ci gaba da yi har ta bacewa ganinta. Taja numfashi sosai sannan kuma ta sauke tana rausayar da kai. Koda sau daya bata taba tsaiwa ta biyewa shirmen zainab ba,amma a yau abun yayi ta’azzarar da har ta samu qwarin gwiwar shigo mata sashe?.
Karamin tsaki taja ganin qananun tunane tunanen matsalolin Zainab da basu taba qarewa cikin gidan ba suna neman bata mata lokaci,saita juya zuwa kitchen zuciyarta na sake fadada da tunani da mamakin halayen Zainab din. Me yasa har yanzu IDON ZUCIYARTA ya kasa budewa?,ta gaza fahimtar abinda ke gabanta a bayyane?.
Da irin wadannan tunane tunanen ta kammala dauraye plates da cups din da wanke kowanne kwano da aka bata da abinci ya zame mata jiki a duk sanda aka gama cin abincin,ta goge ko ina da kitchen towel ta sakayo qofar.
Tsaftataccen killataccen bedroom dinta ta buda ta shiga,ta kalli agogo,sai ta bude wardrobe dinta ta ciro mayafinta daya dace da da A shape din atamfar dake jikinta a dan gaggauce ganin lokaci ya fara ja,tanason taje ta dawo da wuri kafin yaran su dawo daga makaranta,don ta dade da yiwa kanta alwashin muddin ba wani babban uzuri ba ta daina barwa zainab su saboda wani dalili.
Ta dakin yaran ta biya ta dauki baby fatima dake barci ta sakata a kafada sannan ta maida lallausan mini blanket din yariyar ya lullubeta ta fito.
*_FOLLOW MY AREWABOOKS ACCOUNT_*
*HUGUMA*👑
*_KURMAN BAƘI_*
*H U G U M A*
PAGE 02
Muhallin da ta tashi dazun a dakin shi ta koma ta zauna,har yanzu babu wani sassauci data samu ko qanqani,duk da cewa daga ruqayya har saleem ta barwa kowa a cikinsu saqo. Sam bata damu da tarin qazantar dake a sashen nata ba bare hankalinta ya dauku wajen ganin ta tsaftace shi,duk kuwa da cewa rana ta fara yi,kuma lokaci ne da ya kamata ace gurin ya kasance cikin kintsi da gyara. Ba abinda yafi damunta irin uban kudadenta data kashe,ta siya magunguna masu tarin yawa na mata,magungunan da aka bata tabbacin sunansu KAFI MALLAKA. Kuma muddin tayi amfani dasu ba saleem ba,duk wani wanda yake rayuwa da saleem ma zaya zama qarqashinta ikonta da zabinta ne. Sai gashi gaba daya daga kudin har maganin babu abinda ta amfana dashi,maganin da yake na kwana biyu ne,tayi asarar dare daya,saura dare daya ya rage mata,wanda bata da wani hope a kanshi,saboda bahaushe ma ya fadi juma’ar da zatayi kyau tun daga laraba ake ganeta. Irin rabuwar da sukayi da saleem a yau bata tunanin zai nema wani abu daga wajenta a daren yau din,ita kuma batajin koda zatayi asarar kudin data zuba zata iya saukar da kanta ta nemeshi,muddin ba shine akayi katari ya saukar da kanshi ba. Koda bai bata haquri ba tana iya sallamawa,saboda kaf kudaden da ya basu ne saboda siyayyar sallah tasu data yara ta narka a ciki cike da yaqini da imanin zata maida mafiyinsu muddin tayi amfani da maganin.
Kamar wadda aka tsunkula ta miqe da sauri,ta sanya hannu tana jawo locker din madubinta. Tarin ledoji ne da tarkacen da zakayi tsammanin qaramar bolar mahaukata ce dake cunkushe da karikice,wasu a leda,wasu a kwalaye,wasu a takarda,wasu ma saboda rashin gyara da kintsin gurin sun fashe sun barbade a cikin locker din.
Da kallo tabi locker wani takaici yana sake ninkuwa a zuciyarta
“Wai dame na gaza da har yau na kasa ture wannan baqar matar tasa?,dame ruqayya ta fini ne?” Ta tambayi kanta tana qarewa locker din kallo,tako ina bata wasa da gyaran HQ dinta,duk wami magani da zata gani ana tallatawa,ko taji labarin kyan ingancinsa da aikinsa a gurin qawaye saita tabbatar ta mallakeshi hankalinta yake kwanciya,amma har yanzu ta gaza samun nasarar da take hangowa kanta.
Hannu ta saka ta dauko baqar ledar dake ajjiye daga gefe tana jan tsaki,kunceta tayi saman madubi,wasu qullukan garurruka ne da dunqulallun wasu abubuwa guda hudu. Daya brown daya baqi daya fari tas dayan kuma kore. Tsaki ta sake ja
“Fiye da rabin ma da akace nayi inserting nasu ashe nayi,banajin wadan nan ragowar zasu samar min da abinda nakeso” ta qarashe maganar tana maida ledar ta qulle. Gwara ta samo wani abun da zai cikashe mata gibin da zata samu.
Saman hautsinannen gadonta ta miqa hannunta,ta cusa shi qasan pillow dinta ta ciro wayarta. Kai tsaye data dinta ta kunna,sannan ta hau watsapp dinta.
Tarin saqwanni ne suka shiga shigowa,duk da jiyan raba dare tayi tana chart kafin ta rufe tabi saleem din bedroom dinsa.
Fitsarin da ya cika mata mara ya sanyata ajjiye wayar a gefan gadonta,sannan ta miqe da sauri ta tura qofar toilet dinta ta shige.
Saman tiles din toilet din ta tsugunna ta kwata fitsarin. Sai ta dinga bin fitsarin da kallo saboda wasu launika da ya fito dasu da wani birtsi birtsi. Tsaki ta saki tana jin wani sabon bacin ran
“Kalli yadda damshina da aikin maganin ke bi ta rariya a banza,haba,dole a yiwa saleem uzuri,akwai abinda ke shan kansa” ta fada a zuciyarta.
Ko digewa fitsarin bata jirayi ya gama yi ta miqa hannu ta tari ruwan famfon dake kwarara ta yafawa wajen,ta sake miqa hannu ta tara ta yafawa gurin ba tare da ta sanya hannu ta wanke ba,ta miqe tana qoqarin maida pant dinta da uban danshin dake maqale a sumar dake mararta damqam,wadda a qalla kusan watanni biyu kenan cikin ta uku ba tare da ta samu aski ba.
Sai a sannan ta lura da pant dinta da ya canza launi saboda kalolin magungunan matsi da taketa inserting tun yammacin jiya. Tsaki taja,ta fasa sakawa,sai ta zareshi ta jefa cikin bathtub dinta wanda ke dauke da kalolin pants da Braziers dinta da bata samu wankewa ba,ta tsartar da yawun bakinta dalilin rashin brush tana sakayo qofar toilet din cikin hanzari saboda kiran da taji ya shigo wayarta tana gudun kada ya tsinke bata daga ba.
LIKITAR AURE sunan da ya fito kenan baro baro,wani mahaukacin tsaki da yafi dukka na baya ta saki
“Ku******mar uba,aikin banza” ta fadi a fili takaicinta yana kasheta,sai tayi rejecting kiran ta shiga watsapp abinta.
Shamsiyya ta fara lalubawa cikin jerin chats din dake dashboard dinta
“Yauwa” ta fada da sauri tana gyara zamanta saman gadon ganin ta sameta a online cikin sa’a. Sallama ta danna mata,yana shiga yayi ticking blue
“Ina kika shiga likita tana ta kiranki?” Saqon shamsiyya ya shigo. Ji zainab tayi ba zata iya jurewa typing ba,sai ta fara yi mata voice note
“Yo me zanyi mata?,bayan asara tana dab da fadamin?,nayi amfani da komai da tace amma babu abinda ya faru tsakanina da saleem,hasalima tunda ya dawo daga kasuwa ya shiga dakinsa ya ajjiye jakarsa ya dawo parlor ya hau wasa da ‘yan biyu,haka kawai naga kamar ya shigo ne da wani irin fushi,ana kiran sallahr magariba kuma tunda ya fita sallah bai dawo ba sai bayan isha’i,da na kawo abinci ma baici ba ya shige wanka abinsa,da ya fito kuma yace bayajin dadin jikinsa ne gaba daya,na juya yaqi cin komai,da na gaji nima sai na qyaleshi don ba wannan ne yafi damuna ba,kinsan wani rainin wayo?,na tafi naje na kwantar dasu hassana kafin na dawo sai zuwa nayi na tarar yayi bacci?,ya duqunqune a blanket,juyin duniya ya tashi ina da buqata wallahi ko juyowa baiyi ba”. Zaman jiran shamsiyya ta gama ji ta bata amsa sai taga yayi mata tsaho,don haka ta fice daga inbox dinta ta fara duba charts.
Saqon wani group dinsu da take masifar so mai suna MATAN NI’IMA shi yafi kowanne shigowa, group din yana matuqar sakata nishadi don tana qaruwa dashi sosai ta fannin magungunan mata,musamamman na turawa,wanda ita kanta ta sissiya wasu tayi amfani dasu,hakanan a boye ta siyawa saleem ta sassaka masa abun sha ba tare da ya sani ba. Tayi hakanne saboda sanin da tayi masa,baya qaunar ire iren wadan nan magungunan sam,duk abinda za’a ce masa magani ne na irin wannan fannin to baya ciki,ita kuma yadda matan keta comment a kansa ya sakata sha’awar gwada amfani dashi.
Saqonnin ta fara bi a hankali,tun tana jin hirar na gundurarta kamar ta fice har ta soma daukan hankalinta
_Maman mahbuba ya daren?,ya kikaji aikin maganin?_
_a fito mata a bamu feedback mana_
_hmmma ai abun ba’a magana,wadda bata gwada ba gaskiya an sha da ita_
Ire iren maganganun da suka sanyata zaquwa kenan,ta soma bin saqonnin da sauri sauri har ta gano bakin zaren hirar.
Kai tsaye ta yiwa matar data fahimci a gurinta akaci kasuwar maganin magana ta private,sai taga ma jiranta ta karanta saqon bata lokaci ne,don haka ta sauka ta kirata direct call.
Tana dagawa taji ta ambaci sunanta,abinda ya dad’ad’awa zainab rai. Wato tayi shaharar da sunanta ya tambara a group din kenan har ake iya kama sunanta kai tsaye?.
Sama sama suka gaisa,zainab ta nema qari bayani akan magananin. Bayanin da matar tayi mata yasa taji ta gamsu d’ari bisa d’ari
“Nawa ne kudinsa?,idan na turo kuma zan samu a yau?”
“Eh akwai available,zaki samu,dubu ashirin da biyar,to amma tunda kece ansan saba da juna,ki tura ashirin,naki ne da na megidan duka zaku sha,na tabbatar saikin kawo wata ma”. Nauyi taji kudin sunyi mata,saboda sosai tayi barnar kudin wajen likitar aure. Tun daga fallen zanin daurawa na magani data siya a wajenta da tarkacen kayan matsi a qalla ta barnatar da kusan dubu dari da talatin,abinda ya rage mata a hannun nata yanzun dubu ashirin ce,kuma zubin adashi takeso ta fara dashi,to amma hausawa sukace ranar biyan buqata rai ba’a bakin komai yake ba,don haka tace
“Ba damuwa zan baki address,a kawomin sai na bada cash”
“Shikenan ba damuwa”.
Ranta fes taji kamar an sauke mata wani nauyi da yahau saman zuciyarta. Sai ta koma ma ta kwanta tana sake bin feedback na matan da sukayi amfani da maganin.
Murmushi sosai ta dinga saki,tana jin cewa daren yau lallai zai zama na musamman,tana jin ma su hassana gurin ruqayya zata turasu,kuma ko taqi ko taso dole ta karbesu don ta samu ta sake sosai.
Wannan kwanciyar ta kaita har azahar bata sani ba tana group din ana maida yadda akayi tana biye dasu,har ji tayi ya qagu maganin ya iso. Bata ankara ba sai kiran sallar azahar din taji ana qwalawa. Ta rafka salati tana miqewa hadi da bin dakin da kallo.
Tun safe tana fama da qunci,ko brush batayi ba bare ta sakawa cikinta wani abu,bare kuma ayi batun gyara gidan da dakin saleem,ga yara suna kan hanya sun kusa tasowa a makaranta,bata dafa musu abincin da zasuci su wuce islamiyya ba.
A gaggauce ta sauko ta fara da kwashe tarkace kayan dake warwatse a qasan bedroom din,tana yi tana qiyasta rashin mutuncin da zata tsiyaya a yau idan maganin ta ya iso.
Bata jin zata dagawa ruqayya qafa ko diss,tabbas sai ta cusa mata kwatankwacin abinda take gani da ji a duk sanda take da saleem. Wani irin sabon riritawa kulawa tare da kuma tattali take gani a idanu da fuskarsa a duk sanda ya kwana sassan ruqayyan. Tayi imanin babu wani abu dake siyawa mace irin wannan soyayyar illa abu biyu. Kula da HQ da magungunan da zasu matseki gam ta yadda zai kiyayeki tare da dasawa zuciyarsa babu macen da zata kai darajarki ta wanann bangaren. Sai kuma hanya ta biyu da ba zata jurewa zirga zirgar wahalarta ba bayan ga wadda ta fita sauqi wato asiri. Imaninta yafi tafiya ga cewa asirinne,domin itadai bata taba ganun ruqayya ta siya wani abu waishi maganin mata ba,ko labari bata taba ji ba,to ta yaya macen dake zaune haka saket ba tare da kayan aiki ba zata samu irin wanann soyayya da kulawar indai ba ta hanyar tsubbu da asiri ba?.
Ko kafin ta gama gyara dakin ta gaji tubus,ta watsar da tsintsiyar ta zauna gefan gadon tana jan wani tsakin wanda bata gajiya da yinsa. Ba abinda ta tsana a duniya irin aiki,a yadda ta hasaso rayuwar aurenta ta kuma tsarata shine taci ta kwanta kawai,komai saidai a miqo mata. Saidai ga tarin rashin sa’a sai gashi tayi katari da mutumin da sam sam bashi da ra’ayin aje me aiki cikin gidansa.
“Duka duka ma me akayi?,yaran biyu rak?idan akwai buqatarta nan gaba sai a dauka din” wanann itace amsar da saleem ya bata lokacin da tazo masa da batun.
Cikin tarin qailula,zallar son jiki da rashin son morawa kai komai sai gashi takai gefin la’asar bata gama komai ba. A dai dai lokacin driver ya dawo da yara daga makaranta,suka shigo fici fici dasu kamar kullum cikin nau’in jigatuwar da duk dalibi yake tsintsar kansa.
*HUGUMA