Baqeer Hausa Novel Complete
BAQEER
NA
AYUSHER MUHD
DA
UMM ASGHAR
DADANO DAGA RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA ƊAYA
*RUBUTUN ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU.*
*TAFIYAR BIYU TAFI ƊAYA*
*KIN TABBATA KIN CIKA MACE? BABBAR MACE DAKE JI DA KANTA? KINA CIKIN MATAN DA SUKA SAN KANSU? WANDA SUKA SAN MUTUNCI DA DARAJAR KANSU? KO KUWA KEMA KINA CIKI SAHUN SU O’O?*
*INA KUKE MANYAN MATA? WAƊANDA SUKA SHIRYA DAN GYARA JIKINSU? AURANSU? DA KUMA FARINCIKINSU?”
*KUYI MAZA KU GARZAYA GUN FITACIYGA KUMA INGANTACIYAR MAI MAGANIN MATA DA MAZA DAN AMSAR NAKU KU GYARA DA KANKU WATO MEERAH HERBS WACCE TAI FICE GUN KAWO MUKU INGANTATTUN MAGUNGUNA BA TARE DA ALGUS BA.*
Mun gwada mun gani 💯
Mun gani mun shaida 💯
Anyi mun gani 💯
MAGANIN SANYI
MAGANIN NONO
MAGANIN HIPS
MAGANIN SLIMMING
MAGANIN NANKARWA
GYARAN AMARE
GYARAN MAIJEGO
MALLAKAR MIJI KO MATA
SUBULU DA SCRUB
MAYUKA NA GYARAN JIKI
TURAREN WUTA
MATSI
MAGANIN NI’IMA
MAGANIN TSUMI
INFECTION FLUSHER DA DAI SAURANSU…..Uwar gida, Amarya, Budurwa, Saurayi, Ango, Mai gida? Duk mai kuke jira? Kuyi maza ku garzaya Meerah herbs maganin dake ingantace 💯
08142800199
07068558096
[1]
Tafe yake a gefen titi hannunshi na dama na riƙe da waya wacce ke saitin kunenshi, yanayin shi kaɗai zaka kalla kasan yana cikin ɓacin rai wanda ke nuni da abinda ake faɗa a cikin wayar ba abu ne mai daɗi ba. Magana yake yi a nutse sai dai kuma ranshi a ɓace yake matuƙa saboda rainin hankalin da mutumin yazo mishi dashi, taya zai sa yayi mishi aiki akan bayan kwana biyu zai biya shi kuɗin aikin shi amma gashi har yanzu da ake neman yin watanni biyar bai gama biyanshi kuɗin shi ba? Sai ma tsitsinka mishi kuɗin da yayi ta yadda babu wani ƙwaƙƙwaran abu da zai iya yi da kuɗin tunda ba a dunƙule ya bashi ba. Cike da takaicin abinda yake ji ya ɗan sauke ajiyar zuciya yana ƙoƙarin yin magana, abinda yaji ne yasa ya kasa tantance a wace duniyar yake, wani abu yaji yayi sama dashi, idanunshi ne suka sauka akan sararin samaniya yaji kwakwalwarshi ta ɗauke dif na wucin gadi, sam ya kasa gane abinda ke faruwa dashi, kafin yai auni ya dawo da kwakwalwarshi tai wani aiki yaji ya faɗo kan wani abu, kanshi ne ya ji ya bugi gaban mota sannan ya sulale ya faɗi ƙasa, dishi-dishi ya shiga gani a hankali yake ƙoƙarin buɗe idanunshi yana son sanin meke faruwa dashi, sai dai idanunshi mai makon su buɗe sai ma kullewa da suke, karar kiɗa kawai yake ji a kunuwanshi, nan idanunshi suka rufe wanda daga nan bai sake sanin inda kanshi yake ba.
Daga cikin motar kuwa wani saurayi ne wanda kallo ɗaya zaka yi mishi kasan ɗan gayu ne wanda ke ji da kanshi. “Goddamn it! This bastard is gonna make me late.” Matuƙin motar ya faɗa haɗe da dukan stearing wheel na motar da ɗan ƙarfi, burki ya taka sannan ya rage sautin kiɗan dake tashi cikin motarshi, bai ko kashe motar ba ya fito a fusace yana duba gaban motar, ganin da yayi babu abinda ya sameta yasa shi komawa cikin motar yayi reverse ya kaucewa saurayin dake yashe a ƙasa wanda kana ganinshi zaka ga babu alamun rai a tattare dashi, yaja motarshi da wani irin mugun gudu ya bar wurin yana mitar ‘duk Daddy ne ya janyo musu ya rasa unguwar da zai yi gini sai cikin talakawa wai shi a dole yana protecting political image ɗin shi, gashi nan abinda ya janyo musu mingling da ƴaƴan matsiyata da basu san komai ba sai gidadanci.’
Akwai Sirri Hausa Novel Complete
Majalisar samari ce zaune a kan kujerar dake ƙarƙashin bishiyar darbejiya, daga gefensu kuma mai shago ne yana ta saye da sayarwar shi, idan ka kalli can nesa dasu kuma zaka ga gungu-gungu ne na yara suna wasanni kowanne na daidai shekarun su. Idan ka buɗe ido ka kalli yanayin gidajen unguwar sosai zaka gane cewa kowa ta haɗa wato daga masu hannu da shuni har zuwa matsakaita masu rufin asiri bakin gwargwado da kuma talakawa, a taƙaice dai unguwa ce ta kowa da kowa. Musu ne ya kaure a wannan majalisar inda samarin unguwa ke taruwa su zauna yawanci da yamma bayan sun taso daga wuraren sana’o’in su ko makaranta. Musu ne akan siyasar ƙasar nan don haka wurin ya kaure da hayaniya har wani baya jin abinda ɗan uwanshi yake cewa, wani daga cikin samarin ne idanunsa suka kai kan abinda ya faru daga gaba dasu kaɗan, ihu ya saki da ƙarfi wanda ya sakasu kallon wurin suma, hankali a tashe suka rugo inda saurayin nan yake a yashe.
Suna ƙarasowa hankalinsu ya sake tashi ganin halin da yake ciki. A guje Bello ɗaya daga cikinsu ya ƙarasa wurin hankalinshi a mugun tashe, jiki na rawa ya kai hannu saitin hancin saurayin dake kwance akasa dan ya tabbatar yana numfashi, wata nannauyiyar ajiyar zuciya ya sauƙe jin yana numfashi a hankali, kafin ya nemi taimakon sauran jama’ar da ke wurin akan su taimaka akai shi asibiti. Cicciɓarshi aka yi za’a saka shi cikin motar ɗaya daga cikin mutanen da suka taru a wurin, hankalinsu ya sake tashi ne ganin jini ta bayan inda aka ɗaga shi, haka su Bello da wani daga cikin abokansu suka sakashi a mota, duba wayarshi Bello yayi sai dai sam babu alamar ta, ya sani sarai a cikin mutanen wurin ne wani har ya sace dan yanzu in aka yi hatsari wasu sata ce kawai a gabansu ba wai ceton rai ba.
Accident and emergency (A&E) na asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano suka isa dashi, a gaggauce aka karɓeshi aka yi ciki dashi domin kuwa ba ƙaramin jigata yayi ba, kuma har yanzu bai san inda kanshi yake ba, sai numfashi da yake fitarwa shima a hankali.
Nurse ce ta kawo musu takarda akan su cike sannan tace “Ya sunanshi?”
Bello cikin sanyin jiki yace “Muhammad Baqeer!”
“Kai ne guardian ɗinshi?” Kalaman da yaji nurse ɗin tayi mishi kenan, kafin yayi magana tace “In kasan ba kai bane please ka ƙira su yanzu dan muna son su saka hannu cikin gaggawa.” Tana kaiwa nan ta juya ciki da alama sauri take yi, Bello idanunshi duk sun yi jaaa, wayarshi ya ɗauko yana ƙoƙarin ƙiran mahaifin Baqeer, mamaki ne ya kamashi ganin ƙiran wayar mahaifin nashi, nan ya daure ya ɗauka “Aka ce Baqeer yayi hatsari?” Kalaman da yaji ya dake shi da ita kenan, cikin rawar murya yace “Eh muna asibitin Aminu Kano!”
“Ni nasan wannan abotar taku ba abinda zata jawo mana sai ɓacin rai, don na sha faɗa maka ka daina zuwa kana kiranshi in yana aiki amma da yake kai ba mai jin magana bane kai kenan da ziryar janshi ku tafi majalisa.”
A hankali Bello yace “Wallahi yau Baba bama ni na ƙirashi ba sannan yana zuwa ko zama bai yi ba ya tafi.”
Jin alamun an kashe wayar yasa ya shafi saman goshinshi yana sauƙe wata nannauyar ajiyar zuciya.
Baba daga can ɓangaren ranshi ne ya sake tunzura a fusace ya fara ƙoƙarin fitowa daga gidan, hannu tasa ta rikeshi tace “Kai ma Alhaji ka kwantar da hankalinka, na tabbatar ba sosai bane da sukace yaji ciwo sosai, kasan zancen yara su dama sun iya zuzuta abu.”
Hannunshi ya fincike daga hannun matar dake tausasar sa da kalaman nan, yana ji kamar zuciyarshi zata fito, yana fitowa daga ɗakin yaga Fatima wacce itace mahaifiya ga Baqeer ɗin, tana ƙoƙarin shiga da kwanukan da ta wanke cikin ɗakin ta, fita kawai yayi ranshi na sake ɓaci, da gudu kanin Baqeer wanda saurayi ne bai wuce shekaru 24 ba shine ya fito daga ciki gidan ya biyoshi tare da buɗe ƙofar mota ya shiga gefenshi ya zauna.
Baba bai musa ba ya ja motar don ko magana baya son yi.
Tuƙi kawai yake yi amma gabaki ɗaya ya rasa nutsuwarshi, hukuncin Allah ne kawai ya kai su asibitin lafiya amma ba don yayi nutsatsen tuƙi ba. Suna shiga accident and emergency Bello wanda dukkanin nutsuwarahi tana wajen ƙofar da aka shiga dashi ya taso ya taresu. Durƙusawa yayi yana gaida mahaifin Baqeer sai dai bai iya ya amsa shi ba saboda halin da yake ciki sai ma tambayar shi da yake yi yanayin jikin na Baqeer ɗin “Tunda muka zo aka shiga dashi ciki basu fito ba sai dai an buƙaci sa hannu wanda ganin baku zo ba yasa nayi, sun bukaci za’a ƙara mishi jini nida Salim daya kawo mu mun je an gwada namu ko yazo ɗaya da nashi sai dai anyi rashin sa’a basu yi matching ba, to bayan nan dai har yanzu basu ƙara fitowa ba sai dai ko muje mu tuntuɓi waɗancan nurses ɗin muji yadda ake ciki.”
Hannu Baba ya ɗaga mishi alamun ya kyaleshi sannan ya nufi wurin Nurses ɗin, Salim dake fitowa yana gaisheshi ko amsa wa baiba saboda hankalinshi baya jikinshi, Nurses ɗin har sun fara tafiya sai ga ɗaya daga cikin likitocin da suka karɓe shi nan ya fito hakan yasa Bello dake biye dasu a baya ya nunawa Baban Dr ɗin yace “Yauwa gama likitan dake duba shi nan ya fito” Baba yi yayi kamar bai jishi ba har suka ƙarasa wurin shi.
“Sannu likita.”
“Yauwa sannu Baba,” yace yana mai gyara tsayuwarshi.
“Yarona ne aka kawo mota ta buge shi ance ku kuka dubashi, ya jikin nashi dai? Ina fatan babu wata matsala?”
“Hmm..” kawai kanin Baqeer yace yana taɓe baki don a ganinshi da ace ɗaya daga cikin shi ko ƴan uwanshi ne hakan ta faru dasu ba lallai ne ya nuna damuwarshi har haka ba amma da yake ɗan gwal ne baya da lafiya duk yabi ya ruɗe tun ma bai ga a halin da yake ciki ba,”Allah yasa ma kada ya tashi” ya samu kanshi da yiwa ɗan uwan nashi mummunar addu’a babu tausayin halin da ya samu kanshi a ciki.
Ɗan kallon shi likitan yayi yana tunanin ta yadda zai fara faɗa mishi halin da ɗan nashi yake ciki ganin yadda hankalinshi yake a tashe “A yanzu dai ba zance komai ba, sai abinda gwaje-gwajen da aka yi mishi suka nuna, mun dai yi ƙoƙarin tsayar da zubar jinin da yake yi sai dai muna buƙatar wanda za’a ƙara mishi ina fata kun zo da wanda zai bashi jinin, sannan akwai karaya a hannunshi na dama da ƙafarshi ta hagu”.
“Innalillahi wa inna ilaihi rajiun, Allahumma ajirni fi musibati wa akhlif li khairan minha” Kawai Baba ke nanatawa. Cikin wata irin kasalalliyar murya irinta wanda abun duniya ya taru yayi wa yawa yace “Ko nawa jinin za’a iya ɗiba matukar jininmu ɗaya ai, Allah ya sauƙaƙa mishi ya tashi kafaɗunshi.” Ya ƙarasa maganar cikin murya mai karkarwa.
Dukkansu suka amsa da ‘Ameen’ banda kaninshi da yake tsaye a gefe sai faman cika yake yi yana batsewa shi a dole bai so zuwa asibitin ba ya biyoshi ne kawai dan mahaifiyarshi ta turo shi akan yazo yaga meke faruwa ya kai mata labari.
Jikin Baba a mugun sanyaye ya shiga cikin ɗakin, ja yayi ya tsaya yana jin kafafuwanshi nayi mishi nauyi ganin ɗan lelen ɗan nashi a kwance wanda duk wani mai imani in ya ganshi sai ya zubar mishi da ƙwalla saboda gaba ɗaya kamanninshi sun sauya don ba ƙaramin buguwa yayi ba, Bello da Salim a gefe suka tsaya kawai dukansu hawaye sukeyi shi da Salim, don abun akwai ban tausayi ace awa biyu baya kana cikin koshin lafiya yanzu banda numfashi ba abinda kakeyi, hancinsa ɗauke yake da na’urar taimakawa gun yin numfashi na oxygen, a hankali Baba ya ƙarasa wurin har a lokacin bai dawo hayacinsa ba ya kalli Bello cike da tausayin ɗan nashi yace “Garin yaya hakan ta kasance?” Jiki a sanyaye Bello yake faɗa mishi iya abinda ya sani sannan yaran daya mai motar a yanda ya musu kwatance suna zargin yaran gidan Alhaji Sunusi Karaye ne shine wanda ya bugeshi, da yadda yaja motarshi ya bar wurin ba tare da yabi takan Baqeer ɗin ba wanda hakan yasa basu gane ko tabbas shi ɗin bane.
Nan da nan Baba ya sake fusata, yana ji ranshi na sake soyuwa, tabbas zai je har gida ya samu ubanshi don ba zai yarda da ganganci a cutar mishi da yaro ba. Baba ne ya fito aka gwada jininshi ganin girma ya kamashi suka bukaci a gwada na kanin nashi, kallan Bashir yayi yace “Wuce a gwadaka.” Ji yayi kamar zai yi ihu haka ya wuce dan tabbas suna tsoron mahaifinsu sosai, dawowa yayi ɗakin yana jin kwalla na sake taso ma idanunsa, zubawa Baqeer ido yayi kaf cikin ƴaƴanshi yafi ji da Baqeer sannan ya kwallafa rai a kank Baqeer ɗin ne zai samu abinda shi bai samu ba.
Hannunsa yasa ya riƙo hannunshi yana sake bin fuskarshi da jikinshi da kallo zuciyarsa na sake karyewa, ya daɗe riƙe dashi kafin yace “Allah ka dubeni ka tashi kafaɗn yaran nan, Allah ka dube ni da idan rahama….” nurse ce ta shigo ta ƙara sa mishi wani jinin wanda aka ɗebe daga jikin Bashir.
Baba kallon Salim yayi shida Bello da suke tsaye carlo-carko a gefe yace “Please ku tafi mun gode da kulawa.”
Jiki a sanyaye suka juya, Baba ya saƙe riƙe Baqeer bayan fitarsu kawai hawaye ne yaji sun zubo mishi, tabbas in har wani abu ya samu Baqeer ba zai yafema Alhaji Sunusi Karaye ba, idanunshi ne suka sauka kan bandage ɗin da ke naɗe a wutsiyar hannunshi na dama, hankali a tashe ya ƙarasa ɓangaren daman ya ɗan ɗaga hannun, nan danan ya fito cikin sauri yana neman nurse ɗin data fito daga ɗakin, a gaban wani ɗakin ya hangota cikin sauri ya ƙarasa yace “Nurse me ya samu hannun daman yarona?”
Kallonshi tayi sannan tace “Muje na duba.” Tare suka shigo ta nufi ɓangaren dama tana dubawa ta kalleshi tace “Karaya ce a wurin…….”
“Karaya? Kinsan me yake yi da hanun da zaku ce karaya?”
Cike da rashin fahimta tace “An mai ɗori insha Allahu zai warke.”
Cike da faɗa yace “Kina tunanin dan kun mai ɗori hanunshi zai dawo yanda yake ne? In ya kasa amfani da hannun fa ko ya kasa yin aikin painting ɗin da ya saba? Gasar da zai shiga ta zane da za ayi a karshen watan nan fa?”
Bashir ne ya ƙara so da sauri dan ance ma ya kwanta ya huta yace a’a ahi gida zaije, nan ya wa nurse alamar ta tafi, tana fita ya zabgawa Bashir wani kallo yace “Baka da hankali ne? Ko ka ɗauka ban ganka bane?”
“Baba ita me nene laifinta? Kula dashi fa kawai suka yi? Sannan shi me yasa kowa na zaune agida amma shi yana yawo a titi da majalisa?”
“Kana sake magana zaka ga ɓacin raina, shashashan banza kawai.”
Bashir bakinshi yaja yayi shiru, Baba kallon hannun yayi yana ji ya zai yi idan yaron nan bai warke ba? Shikenan rayuwarshi ta shiga garari, duk wani buri nashi ya tarwatse.
Hmmmm…
#Baqeer
#Shalele
# RayuwadaKaddara
#Hawayena
#UMMASGHAR
#AYUSHERMUHD
*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar
*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu
*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce
*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari
*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan
Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500