Akanshi Hausa Novel Complete

Akanshi Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

AKANSHI

BY

*KADIDJA BASHIR*

daga alqalamin

*Maman Abdallah*

 

Marubuciyar Littafin

 

*MUGUNTA FITSARIN FAKO*

And new

 

*AKANSHI*

 

PAID BOOK

 

 

*PERFECT ESSENTIAL WRITER’S ASSOCIATION*

*P.E.W.A*

*Home of perfect writer’s* *together we stand

 

*ESSENTIAL WRITER’S*

 

*Pen is mightier than* *the sword*

 

 

_Bismillahir rahamanir rahim

 

Pree

Page *1&2*

 

Shuru kake ji kamar babu wani mai rai a cikin wajan, baka jin komai sai Saukar Nunfashin Mutanan dake zaune .

Yadda tsarin wajan yake shi ya tabbatar mini da kotu ne , gyara tsayuwa ta nayi na fuskanci inda nake Tunanin nan ne aka tanada dan zaman Alƙali, wani Babban mutun nagani mai cikar kamala da haiba, sanye da Manyan Kaya na Alfarma, da Hirami akan shi, ya sanya farin glass a Idanunsa, wanda yake ƙara masa ƙarfin gani, Sakamakon yana fama da lalurar Idanu, ga kuma Shekaru da suka fara ja.

 

 

Dattijo dan kimanin shekaru sattin da uku Duniya, Malam Inuwa Masa’ud kenan, Alƙali mai Gaskiya a cikin jerin Alƙalan da da jama’a suke alfaharin dasu.a wannan Gari, ɗan gani Kashenin Gaskiya ne komai Ɗacinta, akan riƙon Gaskiyar sa, dayin Hukunci kamar yadda ya sauka daga sama , aka yi masa sanadin duka Iyalan sa har lahira.

 

Matar Musaki Hausa Novel Complete

Ameen ameen naji suna faɗa duka wajan , sai yanzu na lura ashe tun Shigowa ta wajan adu’ar buɗe taro ake, tare da yin salati ga Ma’aikin Allah .

yana daga cikin ƙa’idar Malam Inuwa komai ayi shi akan sunnar Ma’aiki s.a.w , shi ya Umar cemu da mu ƙawata wajan zaman mu , da yin Salati a gareshi, dan haskene a garemu ranar tashin Alƙiyama.

Ubangiji da kansa yayi alƙawarin duk wani abun da aka ɓudasa da sunan Habibin sa, to yanajin ƙunya maido da wannan abu ba tare da an duba kuma an karɓe sa ba.

Jama’a nace Annabi Muhammadu ………..

Duk wanda bai ce S.A.W ba to shine babban marowaci a wannan Duniyar, haka ya faɗa s.a.w.

 

Wajan zama nima na nema na zauna a kusa da wata Mata, kukan da take ne a hankali yasa na kalli sashen da take zaune, Farar Mace ce amma ba fara cancan ba, tanada tsago guda biyu a gefe da gefen Fuskar ta, Fuskar nan duk ta Kumbura alamar kodai tasha kuka ko kuma batada Cikakkiyar Lafiya, Atamfa ce a jikin ta mai Mafaidaitan kuɗi wajan saya, da alama matar tana da tsabta sosai dan ko takalman da ke ƙat’farta a wanke yake tas kamar ba ƙasa ta tako kafin ta iso kotun ba.

Juyowa tayi Sashen da nake, ganin zata kamani ina kallon ta yasa na maida Hankali na wajan Alƙali.

 

Gam, gam, gam ya buga Teburin da yake gabansa da Gudumar Hannun sa, nan waje ya sake yin tsit kamar ba kowa, cikin Daddaɗan Muryar shi mai Cikar kamala yace ” maga takarda muna sauraron ka” , wani dan Matashi ya mike daga inda yake a Zaune, ya miƙa wa alƙali takardun da yake Hannunsa ta ƴar kantar da take tsakanin su kafin ya daidaita tsayuwar sa yace ” yau muna biyar ga watan Rabi’ul Auwal , wanda yayi daidai da Bakwai ga september, ya dauko wata Takardar da take ajiye akan sauran takardun da yake gaban sa , ya cigaba da cewa yau za’aci gaba da sauran Shari’ar da ake yiwa Hasiya Ibrahim, ana zargin ta kashe Mijin Auren ta Mukhtar, bayan basu fi watanni Biyu da Kasancewa Ma’aurata ba ” yana faɗin hakan ya zauna a Mazaunin sa .

Alƙali inuwa ya kalli securityn da yake kusa da kanshi a tsaye yace ”a shigo da wacce ake zargi ” , cikin Girmamawa ya Amsa tare da barin wajan.

Wannan tsarin Malam Inuwa ne , killace wanda ake kan Shari’a dashi daga wajan Mutane, dan kar yawan zantuttukansu ya giɓi tashi ya kasa bada Amsar Tambaya yayin da ake masa, ƙarfe bakwai daidai Motar ƴan’sanda ta kawo ta Kotun tare da Rakiyar jami’an da zasu tsare ta har a gama Shari’ar a ga Sakamakon da ta bada, shine aka fice da ita can Cikin kafin lokacin Shari’a yayi.

 

 

Shigowa akayi da ita kanta a kasa , Matashiyar da za’a iya kiranta Budurwa a inda ba’asan anyi mata Aure ba, sanye take da baƙar abata ajikinta, da kuma baƙin hijaɓi, Hannun ta a cikin ancor haka securitys guda biyu mata suka shigo da ita, bisa jagorancin wannan securityn ɗan aike.

Har wajan da aka saba sakata ta tsaya suka kaita, kafin daya ta tsaya daga dama ɗaya kuma daga hagu, har yanzu kanta a kasa .

Gyaran murya Malam Inuwa yayi yace ” Masha Allah, Allah ya kuma nuna mana yau a Matsayin Rana ta ƙarshe da za’a gama wannan Shari’a, Hasiya ” ya ambaci sunan ta .

 

 

Ɗago da kanta ta tayi , masha Allah babu wanda zai ga Fuskar Hasiya bai yaba da kyawun ta, ba fata bace, ba kuma za’a kirata da baƙa ba, rashin walwalar da yake kan Fuskar ta shi ya bayyanar da Tsananin Tashin Hankalin da take ciki, a da yarinya ce mai yawon raha , amma yanzu ƙunci shine abokin rayuwar ta.

Sashen da mutane suke zaune ta kallo, karaf suka haɗa ido da Mahaifiyar ta, wacce har ta sauya kamanni a kamar data santa a da, da sauri ta kauda kanta zuwa wani gefen, dan bata san ɗan ƙwarin gwiwar data samu ya ƙoranye Sanadiyar ganin rauni a tare da Mahaifiyar Tata.

” Hasiya ” ya kuma kiranta a karo na biyu, cikin Muryar ta data gaji da kuka har ta dashe ta amsa da ” na’am ” , ” yau ne rana ta ƙarshe dan gane da zaman da muke akan Mutuwar mai gidan ki Mukhtar, shin sami lauyan da zai kare ki ” alƙali ya tambaye ta cikin Mutuntawa. ” a’a Ni har yanzu banida lauya ” ta faɗi kanta a ƙasa , ”shin Lauyan wa’yanda suke ƙara yana kusa ?” yayi Tambaya yana kallon sashen da Lauyoyi suke zaune, ” eh ina nan Allah ya Gafarta Malam ” cewar Barister Lawali Ɗalha tare da mekewa daga inda yake zaune , ya fito dan filin dakeTsakanin su da inda Hasiya take , ya kuma cewa ” Allah ya Gafarta Malam wannan abu a bayyane yake cewa Hasiya ita ta kashe Mukhtar bisa La’akari da Hujjoji dana bayar tun a Zaman farko, saboda haka ina neman Alfarmar wannan kotun Muslunci mai albarka data Hukunta wannan baiwar Allah daidai da Hukuncin da Ubangiji ya zartas akan duk wanda ya kashe rai ba akan hakkin Shari’a ba ” ya kara da cewa idan har ba ita ta kashe shiba ai da tuni sun nemi Lauyan da zai kare ta, ranka ya daɗe tsawan lokaci ana ta ɗaga wannan Shari’ar a wannan karon ina neman Alfarma da ayi Gaggawar yanke Hukunci Nagode ” ya karasa maganar da risinawa alamar Girmamawa kafin ya komawa wajan zaman sa ya zauna.

Malam Inuwa ya fara wasu ƴan rubuce rubuce a takardar dake gaban sa.

 

Kukan Maman Hasiya ne ya cika ilahirin kotun , da gudu tazo wajan da tarin Lauyoyin da zasu kai takwas wasunsu suna jiran lokacin da za’a gabatar da Shari’ar da suke Jagoranta, kusa da ƙafafuwan su ta zube tana kuka mai tsuma rai, Nunfashin kamar zai bar Gangar jikin ta, tabbas wannan Jarabawar Hasiya ce amma ita tafi ta jin zafi da raɗaɗin wannan Intila’in daya tunkaro su Bagtatan ba Tsammani, cikin kuka mai Tsuma rai tace ” dan Allah ku taimaka mana , kamar yadda Allah ya taimake ku ya baku dama, wallahi bata aikata abinda ake zargin ta dashi ba, ta ƙaƙa zata kashe mutumin datafi so sama da Rayuwar ta, *AKANSHI* bata ji , kuma bata gani, wallahi ba ita bace, dan Allah ka taimake Ni ka tsaya wa ƴata dan Allah” Mama Kuburah ta ƙarasa Maganar leka riƙe ƙafar Lauya Lawali wanda ya gama zuba zance da bada Hujjoji akan Lallai Hasiyar ita ta kashe Mijin ta Mukhtar, cike da Dubara ya janye ƙafar sa daga riƙon da tayi masa, yayi wani Murmushi mai sauti, wanda sai da ya Hankalin jama’ar dake Kotun, wanda kowa yake faɗin albarkacin bakin sa game da Shari’ar .

Cikin Kissa, Makirci da iya ɗaure Mutun yayi kalar tausayi yace ” haba Mama wannan ai ba Girman ki bane, koma miye ai bai kai har ki dafa Ƙafafuwa naba, wannan abu dai anriga da anyi shi, ina mai baki Shawara ɗazu maiƙa wuya ku faɗi Gaskiya, ta yiyu ta sami Sassauci wajan yanke mata Hukunci, koda dai kowa yasan Hukuncin wanda ya kashe Mutun a Shari’ar Muslunci ” ya ci gaba da cewa nidai abinda nake gani kenan, amma idan har kina Tunanin zaki samu wanda zai kare ta shikenan, sai Ku Gabatar dashi a Matsayin Lauyan da zai kare ta , wannan Shawara ce ” ya faɗa yana ɗaga kafaɗa alamar ya rage nata.

 

Malam Inuwa ya kuma buga Guduma a karo na uku, jin duka kotun ta Hargice da Cecekucen jama’a , nan kuwa waje yayi tsit , kowa ya haɗi sauran zancen da yake bakin sa, bakajin komai sai kukan Mama da Ajiyar Zuciyar Hasiya, cikin ɗaga Murya Alƙali yace ” Malama Kuburah a karo na karshe zan ɗaga wannan Shari’a a karo na huɗu kenan, jiya iyau, babu abinda ya canja a Tsakanin kwanakin da muka baku akan ku sami Lauyan da zai kare ku, baki shike yanka wuya, idan zaki tuna akwai Lokacin da ita kanta Hasiyar ta amsa cewa *AKANSHI* ne , bazamu san ma’anar wannan kalma ba , sai dai idan ita ce ta faɗa da bakin ta, ko kuma munji daga bakin Lauyan ta, saboda haka , na daga wannan Shari’ar har zuwa Ashirin ga wata, zuwa wannan Lokaci ina fatan zaku sami Mafita da yardar Ubangiji, sannan kuma za’a cigaba da tsare Hasiya a Gidan Yari har Lokacin da muka ɗauka ya ƙaraso, abu na biyu a wannan karon za’a iya Ziyartar ta, kama daga Iyayenta, kodai wasu Makusantan ta” Malam Inuwa ya faɗa haka tare da yin Rubutu a Takardar dake gaban sa .

 

” Ninan zan Tsaya mata ” suka ji Magana daga Bakin ƙofar shigowa Kotun…………….

 

 

Ayi Haƙuri ba yawa.

Post a Comment

Previous Post Next Post