Mulki Hausa Novel Complete
𝐌𝐔𝐋𝐊𝐈
By
Ashanty Love.
(M Afnan)
ASHANTY©AREWABOOKS.COM
✯D͟A͟Z͟Z͟L͟I͟N͟G͟ S͟✯T͟✯R͟’✯W͟R͟I͟T͟E͟R͟S͟✯
P 9/10.
Yau tsawon kwana biyu kenan da zuwan Halliru da sakon soyayyar daya kawo. Malam Hallirun ma na daina cewa sai Halliru dan yasan bazai samu damar da yake buri ba. Harta islamiya a kwana biyun nan Kin zuwa na yi da niya nake janyo wani aike da lokacin makarantar ya yi saboda kawai kar naje. Ita kanta Baba mamaki take yanda nake rawar jiki idan ta aike ni. Baffa kuwa bai tab’a tambaya ba dan yasan bana fashin makaranta dole sai da kwakkwaran dalili, shi yasa yanzun ma ya sawa ransa haka ne.
Yau da kaina nakai markad’en awara can bayan layin mu sabida almajirin da yake kaiwa ya tafi garin su noma dan muna cikin lokacin rani ne. Bansan me yasa ba amma tunda na fito sai nake ji kaman ana kallo na. Na juya gabas,kudu,arewa amma banga alamun hakan ba kowa sabgar gabansa yake. Yo ma ina abun kallan ni dai nasan ba wani kyau ne da ni ba sannan abun da ke jan hankalin mazan ma suke kallan matan ni bani dashi. Har naje nakai markad’en na dawo jikina bai daina bani haka haba. Gabda zan shiga gida naji sallamar Halliru kusa dani. Chak na tsaya ina kallan sa gefe na sanye cikin shadda fara yau babu hula a kansa gashin kan nasa yana ta zuba shek’i yasha gyara. Babu laifi ya yi kyau kam dan baza ka kirashi da mummunan ba yana da kyau daidai misali. Baki ne shi dan na fishi haske ga wani gemu daya tara yasha gyara. Sannan bashi da tsayi sosai kusan zan iya cewa da kad’an ya fini.
“Sahla, slma nayi sallama baki amsa ba”
Sanin darajar sallama yasa na amsa masa a cunkushe na cigaba da tafiya yana bina.
“Markad’e ki kai ne?,kawo na riƙe miƙi mana”
“A’a ka barshi na gode”
“Sahla, don Allah kar mu tsaya muna ja-inja a kan titi ki kawo na riƙe, ai ni nace ki kawo”
Badan naso ba na miƙa masa dan nima bana san maganan tayi tsayi tsakanin mu. Har muka k’arasa kofar gida magana yake cikin Jan hankalin da nutsuwa duk da ba bashi amsa nake ba sai naji yau haushin nasa da bnke ji ya ragu. A kofar gida naja tunga na miƙa hannu zan karb’i markad’en ya riƙe.
Yar Mulki Hausa Novel Complete
“Baki bani Amsa taba Sahla, kin amince min na fito? ”
Rasa abunda zance masa nayi kawai na d’aga masa kai dan na kagu ya bani kayan na shige gida. Dan in muka cigaba da tsayuwa anan tsaf zan kwarfe shi wlh. Wani irin murmushi ya sakarmin ya miƙo min bokitin na karb’a na shige gida da sauri.
“Ke da waye nake jin maganan ku a kofar gida”
“Malam Halliru ne”
“Waye kuma wani malam Halliru? Halliru ne ko jafaru? Wato kin fara jaye-jayen maza ko?,bari ma…”
Bilkisu ta yi saurin katse ta “Baba shi ne fa Malamin nasu da naji Baffa yana miki magana ranan ”
“La’ilaha illallahu Muhammadu rasulullahi (S.A.W), wato labe ki ke mana kenan idan muna magana ko?”
“Nifa Baba ba labe nayi ba kin manta a tsakar gida ya yi maganan ranan ”
Tayi maganan tana kunkuni alamun taji haushin kalman da Baban ta furta.
“Au toh yi hak’uri y’ar lele na manta ne ai shi yasa daina fushi ”
Kai kawai na girgiza na shige d’aki na barsu nan tana ta faman lallashi. Tun ranan da Baffa ya yi magana kan saurayin Bilkisun ya fito wata sabuwar tarairaya ta tashi. Wani irin kulawa Baban ke bawa Bilkisu saboda burin ta ya cika Bilkisun ta ta samo attajirin mai kuɗi dake yi musu b’arin dukiya ba kad’an ba. Kullum da irin abunda Bilkisun ke shigowa dasu. Da Baffa ya gani ranshi ya masifar b’aci ya dinga fad’a ta inda ya shiga bata nan yake fita ba. Sai ya zama yanzu duk abunda ya bata sai a shigo dashi a boye ba’a barin Baffa ya gani a yanzu haka ma ya chanza mata Babbar waya babu abinda bata yi cikin ta. Ni dama basa bi ta kaina tunda sunsan ba fad’a zanyi ba.
♥︎♥︎♥︎
K’aramar motace kirar BMW fake chan gefen titi bak’a mai bak’in titi. Amin dake zaune mazaunin direba ya juya yana kallan AJ dake kwance bayar motar ya zuba mata ido yana zukar had’addiyar walking stick dake hannunsa gold colour (taba).
“What are we doing here ne AJ?, Akwai wanda za ka gani ne? Almost 1hr kenan munanan baka cemin komai ba”
“I need to know”
Shi ne kawai kalma da ya furta masa. Kan Amin ya k’ara d’aurewa da wannan maganan tashi. Juyawa ya yi shima inda yaga ya maida hankali. Ido ya d’an zare yana kallan yarinyar nan data musu rashin kunya kwana ki. Tabbas ita ce. Tafiya take amma sai waige-waige take kafin ta shige wani lungu riƙe da katon bokiti. K’are mata kallo ya yi bata da wani abu da zata ja hankalin AJ kanta ya .yaga irin y’an matan da suke bibiyar AJ kaf dinsu mata ne da suka amsa sunan Mace. Mata ne da suke so Booby da Assy amma ita wannan gatanan baiga alamun tana dasu ba duk da cewa ta zurma wani uban hijabi ne dake Jan k’asa. Yes a fuska kam tabarakalla dan tana da kyau zaice yasha ganin mata kyawawa na bibiyar AJ da har kyan nasu da ya yi yawa yasa duk kyan ki yake ganin ki saffa-saffa.
Abun tambayar anan shi ne me yasa AJ yau da kansa ya d’auko sa suka zo nan ba tare da matakan tsaron sa ba?. Sunzo kuma sun b’uge da kallon wata yarinya? . Shi yasan tun ranan data yiwa AJ wannan rashin kunyar bai d’auki mata ki a kanta ba akwai lauje cikin nad’i ,tabbas kuma zai gano koma mene. Sunanan zaune sai gata ta dawo still dai riƙe da bokitin kafin ta kauracewa idan su kuma wani ya tare ta suka jera suka tafi tare.
Wani irin mugun smirk AJ ya yi yana zuk’ar tabar sa idanshi a kanta har ta shige gida.
“Let’s go”
Amin bai musa ba ya tada motar suka bar gurin ba tare da yace komai ba.
♥︎♥︎♥︎
Ni kaina ina mamakin yanda duk na zubar da maka maina a kan Halliru. Yanda naci burin wulaƙan tashi sai abun ya juye yanzu ina matuƙar ganin girmsa da jin kunyar sa. Bazan iya cewa ga takamaiman abunda nake ji akan sa ba amma nasan kasancewa ta dashi yana sani farin ciki. Ya iya kalamai ne ga kulawa bansan ta yarda zan kwatanta ba. Ana cewa malamai basu soyayya, ni kuma sai nake ganin sunfi samarin ma iya zuba kalamai na love dan gashi cikin dan k’ank’anin lokaci ya chanza min tunani. A yanzu maganan mu tayi nisa dan har iyaye sun shiga ciki sati mai zuwa nake tunanin za’a kawo kayan sa rana da lefe. Bilkisu ita saurayin nata wai ya fita amruka sai ya dawo Baffa yaso a had’a amma daya ga sunfi so s𝐮yi nata bidirin daban sai ya kyale su kawai.
Hira muke nida Sahiba bayan mun taso daga makaranta. Babu irin tsokanan da basuyi min ba bayan sunji labarin soyayya ta da malam Halliru gashi abu ya yi nisa. Tun ina fushi muna fad’a har na hak’ura. Daidai layin su muka yi sallama ta wuce gida nima sai na karya hanya nabi ta lungu ina ganin zanfi sauri ina kuma da suyar awara. Dankareriyar motace bak’a wuluk tasha gabana kaman zata bugeni. Da sauri na matsa gefe na d’ura uban ashar.kam bala’i ai kuwa da an tab’a ni da yau anga bala’i wlh. Bud’e motar a kayi gabana ya yanke ya fad’i. Wannan face d’in da har sallan dare nake Allah karya k’ara had’a ni da ita yau gashi a gabana sanye cikin kananan kaya gajeren wando da riga mai yankakken hannu. Wani salo har ta gashin kansa a tufke yake a tsakiyar kansa dama maza na tufke gashi ne?. Zikiri na fara ina kallansa tsoron sa fal cikin zuciyata amma fuska ta tamke. Ya kara wani irin girma kaman wani bijimi .rigar ita kanta duk da ba mai kamawa bace amma ta kamashi dam kaman kirjinsa zai yaga ta. Da wata irin tafiyar izza ya tako gabana sai dana d’aga kai na kall𝐞 sa.
Add Comment