Matar Mutum Hausa Novel Dandano
DANDANO DAGA LITTAFIN *MATAR MUTUM*
Mallakar Maryam Farouk (Ummu-Maheer)
Marubuciyar
2-WATA KISHIYAR
3-HALIN KISHI AND NOW
4-MATAR MUTUM
A qarqashin qungiyar FIKRA WRITERS ASSOCIATION
BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM
Shiru falon ya dauka banda qarar Ac bakajin komai se salallamin da Hajiya Binta takeyi murya a sama tamkar wadda aka aikowa da mutuwar iyayenta dare daya, seka rantse da Allah yanzu ta fara jin maganar ba wai ita ta assasa yin taron ba dan qaddamar da wani shiri nata. Can kuma ta zabura ta miqe tsaye idonta akan Ahmad daya sunkuyar da kai qasa, abinda yake ji a zuciyarsa baze misaltu ba, wai duk akanme? A ina aka taba haka?
“Amadu ashe baka da hankali ban sani ba? Wayonka da nake gani na banza da wofi ne baka san komai ba se neman kudi kamar barawo?” Hajiya Bintan ta fada, Momy ta dago a karon farko tun zamanta a falon ta kalleta jin kalmar data jibanci gudan jinin nata da ita wai Barawo,ita kuwa Hajiya bata dakata ba fusace taci gaba da cewa
Ummu Amanih 2 Hausa Novel Complete
“Wallahi tallahi ko sama da qasa zata hade banga uban daya isa ya qulla auran nan ba yar Bakanike Amadu? Mu zamu hada surukuta da Yar Bakanike kuma Sadaka yallah mayu? to idan ita uwarka sallamammiya ce komai aka ce bata musawa ni bazan lamunta ba, iyakar irin tsiyar da aka dakko mana sun isa BA’s an hado mana da wanda zasu zo suna mana dauki daidai suna ciyayya ba”
“Duk wannan a ganina ba wani abun azo ana tayar da jijiyar wuya akai bane, magana ce ta aure kuma shi ma’auri yace yaji ya gani sannan ni da kaina nayi binciken iyayenta kuma ban samu wani abun qi da ze saka a hana shi auranta ba” Alhaji Audu dake kishingide kan kujera ya fada. Momy da Anty Amarya suka kalleshi kamar yanda da yawan yayayensa dake zaune duk suka kalleshin. Harara Hajiya Binta ta maka masa kamar wani danta tace
“Lallai Alhaji, ya kake nema ka canza magana koda yake kwanakin nan ka zama me fuska biyu daman”
Mamaki kamar ya shaqesu jin abinda Hajiyar ta fada masa, baki da hanci duk suka zuba suna jiran suga matakin da ze dauka amma sukaji muqus sema Hajiya data ci gaba da sababi tana cewa
“Da zakace bakaga wani aibu da ze hanashi auranta ba ai kuwa ita keda babban aibu, Talaka yar talaka kuma Mayya”.
“Amma Hajiya talauci baya cikin sharuddan da suke hana aure, sannan maita da kike jifanta da ita kinsan cewar ba qaramin abu bane idan sukaji zasu iya yin qararki akan hakan” tsautsayi ya saka Anty Amarya magana tamkar kuwa Hajiyan na jiranta daman tace
“Babu shakka Rabi dole kice talauci baya cikin abinda ze hana aure saboda kinji zaki samu qarin yar uwa ko Ahalul fuqara’u za’a qara yawaita? Koda yake ma a hakan ita ai ta fiki tunda nata uban ance yana da tartibiyar sa’ar da yake samun abun kaiwa bakin salati ba irin naki tsohon ba se an bi gidaje anyi yawon maula kafin a tattara a kaiwa Iyali ya isa be isa ba a yayyafa aci shi kansa Alhajin daya kwaso wa kansa qaya gashi nan kullum cikin nadama da dana sanin auranki yake, jiya farar safiya gari ko gama haske beyi ba me dattin hula ya buga mana gida wai katangarku ta fadi daka fita ka bashi kudin ina dawowa kayi kana mitar daka saba duk sanda yazo maka maula irin rayuwar da kake so shima Amadun ka jefa shi a ciki kenan ya qare yana nema dangin Sadaka Yalla su dabaibayeshi su cinye sannan subi dan naman jikin nasa ma da ba auki ne dashi ba su lashe ni daman kwanakin nan zugewar tasa ta zarce misali ashe da walakin yaje an zarge kurwa tab” Hajiya Binta ta fada tana tsaida idonta akan Alhaji
Baqin cikin maganganunta suka saina Anty Amarya barin falon babu shiri saboda kukan daya taso mata, shekaru goma sha tara kenan babu ranar Allah da zata fito ta koma ba tareda ta goranta mata talauchin da ba ita ko iyayenta suka siyawa kansu ba, dukda tabbas Mahaifinta shi yake qara zubar mata da mutunchi saboda ya kasa wadata da dan Abinda Allah ya hore mata take taimakonsu dashi haka shima Alhajin ta sani iyakar qoqari yanayi cikin su uku ita kadaice duk watan duniya seya saukewa iyayenta buhunhunan Abinci da kudin cefane duk a son Baban nata ya dena banzar dabi’arsa ta yawon maula gidajen Masu kudi anci sa’a ya dena amma fa kullum yana take gidan Alhaji Audu, sabulun wanka wannan se yazo ya roqa an bashi.
Hajiya ta bita da Harara taja tsaki ganin Mu’allim yabi bayan mahaifiyar tasa bayan daya bi Hajiyar da wani kallon Tsana idanunsa sun tara kwallar baqin ciki
“Umma ta gaida Ashsha, dama banga tsegumin daya kawo ku ba Alhalin baku da abin fadi” Hajiyar ta fada tana buga cinya kamar wata yarinya. Alhaji Babangida ne yayi gyaran murya, daga jin yanda yake magana kasan a tunzure yake yace
“Amma Hajiya Binta ni banga ta inda zancen Auran Ahmad ko wadda yake son aure ya shafeki ba, ko da ace mahaifin yarinyar nan yafi kowa talauci a duniya wannan ba hujjar ace ba za’a auri yarsa ba tunda talauci ba fasadi bane”
“Nima abinda na gani kenan Yaya, duk ma ba wannan ba a gidan wa aka taba titsiyewa akan matar da yake son aure? Ina har yar rawar Tiktok aka auro mana gashi nan ta fitini kowa tana koyawa yayanmu shaidanci amma waya daga kai yace wani abu kan hakan kodan saboda shi shafaffe ne da mai shiyasa ba’aga aibun abinda yayi ba se Ahmad da an san idan aka ce kar yayi ze haqura ai biyayya ba hauka bace” Alhaji Hassan ya fada cikin qunar rai.
Hajiya tayi kasaqe tana kallonsa Naziru ya zaburo masa yana cewa
“Ka kira sunana kai tsaye kuma na auri yar Tiktok din ai dai ba me farar qafa na auro ba”
“Yi shiru da bakinka Naziru barni dashi, yanzu kai Hassan tsabar baka da kunya ana maganar matar aure me Asali da tushe daga babban gida har ka saka baki? Koda yake kana da hujjar bin bayan Al’amarin, tunda uwarku ta auru a matsayinta na Tubabbiyar Karuwa…”
Tsawar da Hussaini ya daka mata me kama da saukar Aradu ta saka sauran maganganun bakinta maqalewa. Cikin yanayin da yake nuna qololuwar bacin ransa dan hatta da jijiyoyin kansa daya sha askin Skin sun fido rudu rudu haka idonsa ya rikida yayi jajir ya nuna ta yana cewa
“Akul Binta duk abinda kike ji dashi ya tsaya kan wadanda kika raina karkiyi kuskuren sako mahaifiyarmu a shirginki idan ba haka ba….”
“Idan ba hKa ba me zakayi?” Alhaji Zakariyya ya diro gabansa kamar wanda aka harbo da kwari da baka yana huci, Hajiya da tsoron Hussainin ya cikata ta ja hannunsa tana cewa
“Barshi Ubana dan hau ne”
“Ki qyaleni Hajiya ku kuke nuna kuna tsoronsa a gidan nan idan zafin kai da kwaya yake ji dasu shi qaramin kwarone kansa baze dauki ko rabin chajin da nakeyi ba an fada din ance Yayan Tubabbiyar Karuwa kayi abinda zak….”
Marin da Hussanin ya daukeshi da shi irin me jirkita kwakwalwar nan ya sakashi wuntsilawa gefe dafe da fuska yana raba idon, Hajiya Binta ta fasa ihu tayi kanta, a fusace Naziru ya cakumi kwalar Hussanin ya kai masa naushi a fuska yana cewa
“Wlh baka mari banza ba sena rana mana” nana dambe ya sarqe a tsakaninsu kowanne ya shiga kaiwa dan uwansa mugun hari da yake jikinsu iri daya ne, dukkaninsu dogayene masu qirar qarfi shiya qarawa Damben armashi dan kowa ya gagara kai dan uwansa qasa amma dai Hussainin yafi kai hari a zuciye. Ahmad, Momy da Hassan ne suka shiga qoqarin raba su sauran jama’ar falon kuwa seka rantse a Tv suke kallon wannan Al’amari babu wanda ma ya motsa balle ya kai agaji sema tattare qafafunsu da sukayi dan kar a fado musu. Hajiya na gefe sa Alhaji Zakariyya dake kururuwa kamar mace sakamakon yanda Marin ya shammaceshi ga haqorinsa daya daya turgude a qasa, ihu take itama tana Zagin Hassan da Hussaini, jafa’in duniya babu wanda bata janyo musu na se wanda ta manta.
Momy ta kalli Alhaji Audu dake zaune akan kujera tamkar gunki cikin kuka tace
“Kana kallo Alhaji, jira kake se daya ya kashe daya kafin ka tsawatar musu? Anya kuwa Alhaji ka shiryi tarar da ubangijinka cikin salama kamar yanda kowanne musulmi yake fata?” Cikin kuka ta fice daga falon, a bakin qofa taci karo da yayansu Mata a tsaitsaye cikin tashin hankali. Hajiya qarama datafi kusa da ita tacewa
“Kira Babanku Alqali ki gaya masa yazo babu lafiya a gidan nan” tana fadar haka ta shige cikin gida tabar Hajiya qarama na qoqarin kiran Baba Alqali amma sau biyu wayar na subuce mata saboda yanda jikinta yake rawa dakyar ta iya dannan kiran.
Momy kuwa harta isa dakinta hawaye be tsaya mata ba, ba kuma tasan ranar da zata dena zubar dasu ba hawayen baqin ciki, takaici da dana sanin auran wannan mutumin da sam bata san me zata kirashi ba. Son zuciyane ko kuwa tsabar qin Allah ya saka Alhajin yin abubuwan da yakeyi bata sani ba amma koma menene ta tabbata muddin be tuba ya gyara alaqarsa da Ahalinsa ba ya mutu a haka tabbas baze kwanta cikin salama a Kabarinsa ba.
A can falon kuwa Hussaini ya mazge Hassan dinsa daya cukumi cikinsa yana qoqarin janyeshi kafin ya kaiwa Ahmad qafa amma ya goce ba shiri suka matsa suka barsu zuwa sannan Hussainin keda nasara dan ya kai Naziru qasa ya masa lilis har ya kai baya iya maida martani se qoqarin kare kansa kawai yake amma be haqura ba yaci gaba da jibgarsa kamar Allah ya aiko shi. sannan kuma Alhaji Audu ya samu qarfin yunqurawa daga zaunen da yake tamkar wanda ya tafi hutu wata duniyar na wucin gadi ya dawo haka ya shiga jan numfashi kamar me Asthma. Ahmad yayi kansa yana cewa
“kun gani ko ku bari idan ba kashe shi kuke so kuyi ba”.
Hussaini ya tsugunna ya dauki Agogon Azurfarsa daya tsinke a garin dambe bayan daya gaji da jibgar Naziru ya kalli Ahmad din yace
“Toh ya mutu mana, wa rayuwarsa ta dama bare idan ya mutu ya damu? Sedai ko su daya dauka Yaya ya fifitasu akan kowa sune zasu shiga uku duk ranar da aka ce babu shi” sannan ya kalli Hajiya Binta da idanunsa da suka koma abin tsoro yace
“Nan gaba idan wani daga cikin marasa kunyar Yayanki yayi niyyar tsoma baki a sabgata ki gargadeshi dan zanci gaba da nuna muku abun da dan Tubabbiyar karuwa ze iya aikatawa” yana gama fadar haka ya fice daga falon kamar kububuwa.
Maganganun Hussaini sun daki qirjin Alhajin kamar shigar bullet, ya yunqura cikin wani yanayi ya tashi tsaye dan bakinsa kamar an liqe masa shi da glue yake ji yana tsayuwa akan qafafunsa jiri ya kwasheshi ya koma kan kujerar Yaraf kamar wata gingimemiyar giwa ta fadi Ahmad da Hassan suka rufu akansa, Hassan din ya kalli Ahmad yace
“Riqeshi bari na dakko Kit dina a mota mu gani idan kuma babu hali mu wuce Asibiti dashi kawai” yana gama fadar haka ya fice da gudu kamar yaro ya nufi motarsa.
Da wani irin yanayi Alhajin ya ringa kallon Yayansa Maza da suka fara miqewa daddaya suna barin falon harda masu sakin qananun tsaki dalilin bata musu lokaci da akayi da wannan wasan kwaikwayo da suka rigada suka saba dashi babu Wanda ya nuna damuwar cewa wai Mahaifinsa ne a wani yanayi da ko ba’a fada ba sunsan Hawan Jininsa ne ya tashi Allah ma ya taqaita ba Paralysis ya samu ba irin wannan komawa da yayi ya fadi akan kujera, wani abu ya tokarewa Alhaji Audu maqoshi, hawaye ya ziraro a idanunsa abinda ya sake rikita Ahmad kenan a shekarunsa Talatin a Duniya sau daya ya taba ganin kwalla a idon Mahaifinsa lokacin da aka kawo gawar qaninsa Baballiya daya rasu a wani hatsarin jirgin sojoji daya rutsa dashi se yanzu kuma hawaye yake dagaske tabbas Al’amarin dake zuciyarsa ba qarami bane
Uhmmmmmm
Bakuji komai ba cikin cakwakiyar dake damfare cikin wannan Ahali masu ban sha’awa daga Nesa, BECHI FAMILY kenan wanda sukayi wa kansu take da MARMARI DAGA NESA tabbas kuwa su amsa sunansu hakan idan akayi la’akari da kalar bahaguwar rayuwar da suke gudanarwa wadda ALHAJI AUDU BECHI ya assasa a cikin rashin sanin abinda hakan ze haifar masa a gaba. A lokacin da girma ya cimmasa yake buqatar hutu da nutsuwar zuciya a sannan ne kuma muguwar dabi’ar daya dabbaqa tsakanin Ahalinsa ta fara farautarsa ku biyoni cikin wannan Tafiyar me taken MATAR MUTUM dan jin yanda zata kasa.
Ban cika baki ba amma dayardar Allah nasan ba zakuyi dana sanin bin tafiyarba, kamar yanda na saba fitar daku kunya a wannan karon ma na shirya tsaf kafin muka hau wannan mota
Yi Maza ki sanya 500 a Asusun
*7061838488*
*Maryam Farouk*
*Opay Digital service*
Sannan ki tura da shaidar biya akan layin
*07061838488*
Idan katin wayane zaki dauki hotonsa ki turomun, idan kuma VTU ne ki saka a *08142548705*
Yan Niger ku tuntubi
Akwai tsarin special posting ma’ana wanda suke so a tura musu ta PC 1k ne
Masu ta’ammali da Arewabooks a sauqaqe ku karanta abunku a can babu hayaniya babu rikicewar Pages kudai kuyi following dina
*@Maryamfarouk01*
Sannan kusha karatu lafiya ga sauri ku kerewa yan Whatsapp
Qawayen Ma’u na Amana nasan a shirye kuke, ga kuma Jama’ar Umaimah yar Daba kuma nasan tsaf zaku taho kuyiwa AFEEYA kara, ku kadai kun isa gayya ku tayata kwatar yancinta cikin wannan rayuwa me sarqaqiya data tsintsi kanta.
*MATAR MUTUM ZE FARA ZUWAR MUKU A RANAR 01/12/2023 DA YARDAR ALLAH*
KU DANNA
https://whatsapp.com/channel/0029VaDQ4O44o7qPA0yV9x26
Domin shiga WhatsApp Channel dina ku karanta free pages
Sannan ku danna wannan don shiga comment section
Nagode
Add Comment