Matar Musaki Hausa Novel Complete
MATAR MUSAKI
(nakashashe)
Oum mufeedah✍🏽
Paid book
Page 1 to 4
Bissimillahi rahamani rahim
“Dan Allah Dady kada ka hukuntani akan laifin da bani na aika ta ba Wallahi Dady bani bace Wallahi kayarda Dani Dady kada ka aura minshi Dan Allah”
Na karashe maganar da kuka Mai tsuma zuciya Ina Jin zafin shiga tsakanina da mahaifina da akayi
“Aure na nawa kuma ai dazu bayan sallah jummu’a na bada ke gareshi ga sadakinki ma dubu biyar ne ” Dady ya watsomin kudi ihun kuka nasaka tare da Dora hannuna aka dai-dai lokacin Umma tafito daga part dinta tashigo parlour na Dady da gudu na Isa gareta tare da rugumeta cikin gunjin kuka har Ina Jin nufashina na sama-sama nace”Ummm..umma.umma Dan Allah..”
Hannuta tadoramin abakina tare da rugumeni sosai ajikinta ta dago idon ta jajir ta kalli Dady dake kallonta cikin mamakin ganin karon farko tun haihuwata Umma ta nuna kulawarta gareni jikinshi ne yayi Dan sanyi ganin kallon da take mashi kafin ta ja hannuna munufi kofar fita dai-dai lokacin momy tashigo fuskarta dauke da murmushi kallo daya Umma tayi ma ta taja hannuna mukashige sashenta rufe kofa tayi har da key kafin ta zaunar Dani a daya daga kujerarun falon nata ruwa tamikomin masu sanyi nasha kafin nashiga sauke ajiyar zuciya,
Kusana tadawo ta zauna har lokacin bata cemin kanzil ba ta yanjoni ta Dora kaina a cinyarta ahankali nakejin wata natsuwa da ban taba ji ba kasancewar ban taba rabar Umma tunda nafara girma Sai de Momy kasancewata yar fari ga Ummata,tana matukar nuna alkunyarta agareni Amma yau rana daya nassmu kulawarta,
Umma”Duk Wanda kikaga yana rayuwa a doron kasa da kaddararshi ki karbi kaddararki hannu biyu kiyima mahaifinki biyayya kada ki kullaci mahaifinki shi bashi yakar zomon ba rataya aka bashi kinunawa duniya mahaifinki ya Isa dake ki nunamusu cewa kedin jinina ce biyayya hakuri kawaici ajininki yake yawo kidena kuka kidena ihu da hargowa ki natsu ki karbi aurenki Allah zai dubeki zai kawomiki dauki inde kin bar komai gareshi bazaki taba tabewa”,
“Umma musaki ne NAKASHASHE ido daya ne fa dashi Umma kuma ba asan asalinshi ba Dan Allah Umma kada kubarni nayi rayuwa dashi”
Na karashe da wani irin kuka
“Asiya! Dago kikaleni”
Afirgice na dago Jin Umma takira sunana karon farko arayuwata
“Inde ni nahaifeki kuma na Isa dake kada kisake zubar da hawayenki akan aurenki ki tashi keje ki gayawa Ubangiji kukanki ki kuma shirya tafiya gidan mijinki da biyayyar aure”
Ta ture kaina tare da tashi tashige bedroom dinta tana goge hawayen idonta
Rainon Soja Hausa Novel Complete
Chak hawayen idona suka tsaya naji zanyi abinda Umma tace din tashi nayi nashige bedroom Dina nashiga toilet wanka nafara yi kafin na dauro alwala nafito
Dai-dai lokacin momy tashigo dakin fuskarta washe tace”Amarya ki shirya inji Dady ki yanzu zaki wuce gidanki” tasake kallona tare da wata siririyar dariya tace”Matar musaki Mai ido daya yi sauri fa”.
Ta fice dakin zubewa nayi awajen Zan fasa ihun kuka
“Kada ki zubar da hawayenki shiii! Tashi ki shirya aniyarta zata bita ko bada de ko bajima Allah baya kyale hakin wani”Umma dake shigowa dakin ta fada ita takama min nashirya cikin wata dark blue shadda da mayafina ta shirya min akwatina na biyu muna cikin Shirin Dady yashigo dakin kallo daya Umma tayi mashi ta dauke Kai shima haka cikin daure fuska ya mikomin wata yar madai-daiciyar jaka yace”karbi yan uwan mijinki sun zo daukarki kuma kisani gidana ba’a yaji kisani banason ma kitako kafarki gidanan nan kusa kiyi zamanki acan duk wani Abu da a sakamaki Momy sunje sun saka ki yi biyayya ga mijinki domin shine gatanki yanzu”
Ina ji kuma Ina gani aka fito Dani gidanmu idan ko wace amarya a mota ake kaita gidanta ni Asiya a keke-nape naje gidan aure tunda muka shiga gidan banyi wa kowa magana ba inajinsu suna maganarsu har suka danganani ga dakina suka fice to kodama ba dangina ni kadai nazo,wani kuka ne yazomin bayan ficewarsu haka nayita yin abina Ina kara tsinewa kishiyar uwa domin nasani duk abinda yafaru Dani da dalili Momy ne,
____________________
Tun da aka shigo da ita layin nasu abokinshi Umari gurgu yafara yi mashi shakiyanci yana tsokanarshi “ango ango Ali yaufa ango kake inji Allah”
Ahankali yadago kanshi dake duke ya kali Umari gurgu Masha Allah farine tas Mai matsakaici tsayi kyakyawa ne sosai Sai idonshi daya dake da wani Abu tamkar yanar gizogizo aciki yayi da dayar take normal duk dahaka bazaka kirashi da Muni ba,
Cikin sanyin muryarshi yace”Kacika tsokana Umari nifa haryanzu gani nake tamkar mafarki zuciyata ta kasa aminta da al-amarinan”
Umari yace”kasan de wani baya Auren Matar wani saboda haka kacire komai a rayuwar duk da nasan zaka fuskanci matsaloli musaman wajen yarinyar Amma Kayi hakuri ka jure insha Allahu komai zai wuce, kaga dare na karayi katashi kashiga gida nima Zan shige Sai da safe in mun hadu mu karasa”
Gyada Kai Ali yayi tare da cewa”Ok yayi Allah yatashe mu lafiya” yakarashe da tashi tsaye nan sukayi sallama tunda yanufo gidan nasu yakejin jikinshi nak’ara sanyi har yashigo tsakar gidan kallon kofar Iya yayi yaganta asakaye Sai da yarufe gida kafin yanufi d’akin Iya da sallama yashiga ta amsa tana cewa”yanzu nakecewa bari natashi na nemoka tun dazu su Hafsi suka kawota konan dasukace su shigo da ita nace aa saboda dare yayi abarta harda safe ma gaisa saboda haka jeka da safe mayi magana anbar yarinya tun dazu ita daya”.
Kasancewarshi ba ma’aboci magana ba yasa ya gyara rigar farin yadin jikinshi dinkin ta zarce yace”Sai da safe”
Iya Tace”Allah yatashe mu lafiya”
Tunda yashigo sashen nasu da yar karamar Gina ce ta rabasu da Iya kasancewar gidan daki biyu rak Sai Kuching dake daf dashigowa gidan da toilet Sai akaja gini aka raba dakunan Amma duk toilet daya ne,
Gabanshi wani irin buga yayi lokacin da yashiga dakin yana kallon dukiyar da aka zuba can ya hangota da idonshi daya kwance take tun tana kuka har barci wahala ya dauketa,
Yafi mint biyar tsaye yarasa yazaiyi kallonta kawai yake zuciyarshi na bugawa da karfi
“Yau shi Ali shine yake da wannan kyakyawar halitar amatsayin mata?”
Kamar wace aka tsikara na tashi daga barcin da ya figeni inuwar mutum nagani tsaye da sauri na k’ara kallon kofar dai-dai lokacin shima yadago karaf muka hada ido gabana ne yafadi bana bukatar tambaya ganin idonshi daya ya tabbatar min shine de mijin da aka auramin,wani abune ya tokaremin Zuciya har lokacin nakasa dauke idona akanshi ganin haka yasa ya ida shigowa cikin sanyin muryarshi yayi sallama
Sai alokacin na dauke idona akanshi domin haushi da takaicinshi danaji lokaci daya cikin haka yayi ta takowa har ya iso tsakiyar dakin cikin sanyin muryarshi yace”kiyi hakuri ban shigo Miki da komai ba insha Allahu gobe Zan shigomiki da ita”
Wani kululun bakin-cikine yatasomin narasa mezanyi ko mizance gashi ya kafeni da kallo Dan karamin tsaki nayi nace”wannan Kai yadama” na juyarda kaina,
Ganin haka yasanya yasamu gefen cafet ya zauna,
Yace”to kitashi mu yi sallah mu godewa Ubangiji”
Ina nunashi da yatsa nace”mu godewa Ubangiji da me? Aurenka Allah ya kiyasheni Kai kaje Kayi ”
Juyar da kanshi yayi tare da yunkuwara yayi hanyar waje na bishi da kallo inajin tamkar in tashi in shakeshi,
Har wani baccin ya daukeni bai dawo dakin ba,
Kiran asubah yatayar Dani har lokacin akwai neppa Sai alokacin nakarewa d’akin kallo Dan madaidaicin gadona da wadrop dinshi duk Ash color Sai plasma Tv Dina daga gefe Sai freezer lg gefe da kureru 3st da 1st ,
Tashi nayi na fito waje ganinshi nayi kwance akan tabarma, tsam nayi jikina na mutuwa inajin tamkar kuma ban kyauta ba,
“Ga toilet can” haka naji yafada sake kallonshi nayi ganin har yatashi zaune rankina Dana gani na nufa akusa dashi naga butoci daya nacika da ruwa kafin na nufi inda yanunamin amatsayin toilet, inashiga naji yabude gidan yafita dakyar na iya futsari a toilet din domin irin bayan gidan na ne Mai salanga cike da kyankami nafito alwala nayi Ina batun shiga d’akin naji an bude dayan dakin da gini ya raba ban tsaya ba nashige ,
Wannan litaffin na kudi ne 500 Norma gruop vip 1k
[10/24, 12:05 PM] Ayaya:
MATAR MUSAKI
(nakashashe)
Oum mufeedah✍🏽
Paid book
Page 2
Ina idar da sallah yana shigowa gefen kujera yasamu ya zauna tare da kallona yace”Ina kwana”
“Da ban kwana ba ai da baka ganin ba ” na bashi amsa da zafina shiru yayi kafin yace”Manzon Allah sallalahu alaihi wassalam yace”magana Mai dadi ma sadaka ce Amma kiyi hakuri”
Yana k’ara sa maganar yatashi tare da ficewarshi
Jikina yayi sanyi koba komai bashi da laifi idan Zan yi adalci a yadda Dady yagaya min tallata ma akayi mashi kuma ya taimaka ya amsa wani kukan bakin-ciki ne yazo mun inajin bazan taba iya yafewa Momy domin ta cutar da rayuwata wayata dake cikin handbag dina tun jiya naji ta na ring hannu nasaka na janyo handbag din na ciro wayar number kanwata ce da muke uba daya wato Surayya daga wayar nayi
“Hello Anti Asiya ”
Ita ma Sai na tsici kaina da Jin haushinta na kashe wayar gabadaya hadi da yin jifa da ita kan gado
Kuka nakeyi sosai fiye da awa uku takai jijiyoyin kaina har suna amshi kaina na Sara min sosai
“Assalamu alaikum”
Dakyar na iya dago kaina na sauke a fuskar datijuwar matar dake tsaye jikin kofa tasaka hannunta daya ta yaye labulen d’akin kallona take fuskarta na bayanar da wani boyayen sirri da ke kasan zuciyarta
Nima din jajaye idona na kafeta dasu batare da ko sallamar ta na amsa ba haka kawai naji tshowar ba ta kwanta min azuciya ba,me tagani ko ta hanga ta washe fuskarta tare da shigo gabadaya d’akin tana cewa”sannu yata ya kwanan bakunta kiyi hakuri har yanzu bakawomiki kari ba Ali nacan yatahi sawowa,uhmm baki sanni ba nice mahaifiyar mijinki yana kirana da Iya Ali shi kadai ne dana ” kallonta nayi Ina karajin rashin yardata agareta inaji ajikina tamkar karya takemin ba itace mahaifiyarshi ba, ko a kamanceniya basu da ita din bakace wulul yayi da shi yakasance fari tas
Murmushi na aro nayafawa fuskata kafin na Dan sauko Ina gaida ta da sauri ta amsa min dai-dai lokacin yashigo d’akin kallo daya na mashi Ina amsa sallamarshi kasa-kasa na dauke kaina,
“Ah iya kina nan nikam nashiga d’akin ki banganki ba”
“Ina nan nashigo ganin yata”
Yace”gashi na amso” yakarashe da mikamata ledar hannunshi,
Amsa tayi tanacewa”bari inje in hadamiki yata kisamu ki karya kumalo”
Nace”bari inzo intayi”nakarashe da bin bayanta ko kallonshi banyi ba,
Tunda nafito naga har tanufi kitchen cimata nayi na amsa endomie ce da kayan tea cikin kankani lokaci zance na kammala hadawa domin nahana Iya samin hannu nace tabari kawai nayi duk da tanace Wai amarya nake yan- yan surutunta har yafara bani haushi kasancewar gawayine sai aikin yamin sauki Dan danan nagama ita tasaka na dibarmashi a plet da hadaden tea din na nufi d’akin badan Raina naso ba Sai Dan ba tarbiyata bace musu da babba, Ina shiga naganshi zaune tsakiyar d’akin saman capet ya zurfafa tunani har nashigo bai sani ba
“Gashi” nafada Ina duguwara mashi abincin firgigi yayi nikuwa ko kallonshi bansake yi ba na wuce na dauko kayan wankana da Umma ta hadamin waje daya na dauki tewul da dogon hijab na fice Sai da nafara juye ruwan zafin da na Dora akan wuta cikin boket na surkasu da nasanyi na shiga toilet din ko yanzu dakyar nayi wanka na dauro tewul dina nasaka hijab Dina har kasa nafito hannuna daya rike da kayan da na cire,
Tunda nashiga d’akin bayanan saboda haka a natse na shirya cikin doguwar abaya ta pink color ,na shafa yar powder inajin wata yar karaman natsuwa na shigata
Na nufi kofa da nufin zuwa wajen Iya na bude labule kofar dai-dai shima ya bud’e zai shigo karaf mukayi nayi ba zuuu!! Zan fadi wani lallausan hannu naji akan kwankwaso na an taroni na fado akan faffadan kirjinshi wani lallausan kamshi naji yadaki hancina da yasani karayi luff,can natuno a kirjin da nake ai da sauri na wullitse shikuwa bakon yanayi da yashigeshi yasa ya koma tamka photo har na janye jikina kallona kawai yake nikuwa harara na dalla mashi Ina Jan karamin tsaki, na bi ta genshi Zan wuce naji ya tasgoni ya matsani da jikin bango “wakikewa tsaki? Dan kinga nasaka maki ido daga jiya zuwa yau bahakan na nufin nidin walakanta ce ne ba kuma ko kinki ko kin so ni mijinki ne a gida ba akarantar da ke darajar miji bane?” Yakarashe yana kallona da one eye dinshi “sakeni” cikin sanyin muryarshi yace”me zai Hana kisaka karfinki ki kwaci kanki,” cizo na gantsara mashi a hannu da sauri yasakeni yana “washh!” da gudu na fice na nufi d’akin Iya
“Eh jiya aka daura” shine abinda naji Iya na fada daf da zanshi d’akin da sallama da’alamu waya takeyi ne tanajin sallamar tawa naji tayi wani yare ta katse tana kokarin boyewa nashigo d’akin…
Shedar biya ta wannan 0907 355 6632
[10/24, 12:05 PM] Ayaya: https://chat.whatsapp.com/LIlyhIanMqA0v3H7i8zqGv
👨🏾🦯MATAR MUSAKI👨🦯
(nakashashe)
Oum mufeedah✍🏽
Paid book
Page 3
Murmushi Rashi gaskiya ta shiga yi tana cewa”ah yata kece” yi nayi tamkar Banga me take ba nace”eh nashigo ne nak’ara gaidaki”
Murmushi tasakeyi har sautinshi na fitowa tace Allah sarki ai kuwa na gode shi Ali har yafita ne?”
Nace”aa yana can d’akin”nakarashi maganar Ina karewa d’akin kallo,gefen katifarta ta nunamin tanacewa” zauna yata”
Zama nayi Ina kara nazarina akan Iya duk yadda akayi akwai abinda take boyewa tou ni meye ruwa na can ta matsemata duk azuciya nake wannan maganar,
Duk shiru mukayi ni kodama can ba ma’abociya magana bace muna cikin zaman kuramen yashigo d’akin da sallama har yayi wanka ya canza kaya zuwa wani tsohon dogon jens dinshi da yar riga Black color itama duk taji jiki,
Cikin sanyin muryarshi yace”Iya Zan fita yanzu Bashar yakirani zamuyi wani aikin gini”
Dagowa nayi da sauri na kalleshi “aikin gini?” Na maimata azuciyata Ina kallo Iya ta yi mashi addu’a har ya fice ko kallonshi bansake yi ba shima ko gefena bai kallah ba har yafice,Ina nan d’akin Iya har 12:35 tashi nayi Ina ma ta sallama na nufi d’akin tsintsiya nadauko na share d’akin tare moping na kunna turaren tsinke da Air-freshener na zauna nayi beark Dina Ina gamawa nafito da kayan na wanke har wadanda yaci abincin na komawata d’akin,har lokacin iya na cikin d’akin ta
Ina shiga d’akin naji sallama a hankali na amsa Ina ida shigewata Jin Iya ma ta amsa,
Ina shigowa naga an maido da neppa kayan kallona na kunna kasancewar naga an hada komai tashar mbc Bollywood,
Hasken waje naga yashigomin sanadin da yasaka na daga kaina domin ganin Wanda ya budemin labulen d’akin, wani ihun murna nayi Ina wutsulowa kan kujera da gudu na rugumeta Ina cewa”Anti Salma!”
Itama murmushi tayi ganin farin-ciki a tattare da ni,rikota naji har muka zauna saman kujera tana karewa d’akin kallo,
Anti Salma kanwar Umma ta ce uwar su daya ubansu daya itace Auta d’akin su tana aure birni-kebbi ya’yanta biyu Arifa da Arif,
Ta kalleni bayan na kawomata ruwan sha tace”Ummanki tace tayita kiranki switch off?” Sai alokacin na tuna da wayata na bata fuska”Wallahi kasheta nayi ban zaci kiranta ba bari naje na kunna”
Tace”aa zo nan muyi magana ba jimawa zanyi ba “,
Matsowa nayi nasamu waje gefen ta na zauna “Asiya! Asiya!! sau nawa nakiraki” nace”sau biyu”
Tacigaba da cewa”Asiya Zaman Aure haƙuri ne,kar kiga yadda aurenki yazo kice za ki bijirewa miji kisani ayanzu duk wani nauyi da haki na wuyan mijinki wajibine biyayya agareshi duk yadda yake inde kinason shiga al-jannah kisani duk wanda ba zai yi haƙuri na wani lokaci ba, zai sha wahala a kowane lokaci kiyi hakuri ki rugumi mijinki hannu biyu ki saka aranki ibada ce zakiyi ,cikin Zaman aurenki kafun ki aikata wani Abu yi kokari kiyi dubi akan auren daasuka gabaceki. Domin Dole akwai Wanda tashiga Halin dakike ciki, takuma dauki mataki kan halin datake ciki. Kuma daga karshe meya haifar Mata? Kidiga tsayawa kiyi dogon tunani kafin ki yanke hukunci a komai na rayuwar gidan aurenki
Kiyi
Haƙuri,kiyi haƙuri ki ɗauki aure matsayin ibadah,kar ki biye ma ƙawaye,ban da yaɗa sirrin miji,ki zama mai yawan haƙuri kiyi koyi da halayen Rabi’atul Adawiyya wajen yima mijin ki biyayya zaki ji daɗi a ranar lahira,ki bi mijinki kiyi koyi da matayen masoyin mu Habiby Rasulullah صلى الله عليه وسلم Dan Allah Asiya kinga yadda komai yazo ki daure ki jajirce sa’anan Abin da yafi komai kuma a cikin zaman Aure shi ne ki kama Allah gam babu mai iya miki sai shi,ko da wasa kar ki je wani guri domin Kai wata bukata taki kaiwa Ubangiji yana sane da duk lamarinki Kinji”
Na gyada kaina Ina goge hawayen da suka zubomin tacigaba da cewa”ga kayan garaki can Ummanki taha tace akawo domin shi Dadyn ku yace ba ruwanshi Asiya Dan Allah ki natsu gidan mijinki ki riki mijinki sau dayawa wani abun muna kallonshi ba alkairi ba Sai yakasance kuma shine alkairin agaremu” ta bud’e jakar hannunta ta ciro kudi tana riko hannuna tasaka min tace”ki dena kuka Asiya ita rayuwa komai Mai wucewa ne waddanan kudi dubu dari ne ki ajiye a hannunki in kuma za ki bawa mijinki ya ja jari walillahil hammdu domin an gayamin sanar gini ce yake ko ita din za’a iya wata daya ko sati biyu bai samu ba ki karbi kaddararki hannu biyu kiyi hakuri watara sai labari da yarda Ubangiji”
Rugumeta nayi ina cewa”nagode Anti Salma Insha Allahu zan baku mamaki zan jure”
Tace”yawwa ko kefa Allah shi Miki albarka”
Nace “Amin ”
Tashi tayi na rakota har wajen Iya suka k’ara gaisawa muka yi sallama Ina kallo motarsu ta tashi suka wuce ni kuma nadawo nasamu Iya tsaye tana kallon buhuhunan da kayan abinci da Anti Salma ta kawo inajinta tana ta godiya ko amsawa banyi ba nashige d’aki domin ni kadai nasan yanayin da nake ciki…
Wannan litaffin na kudi ne 500 Norma gruop vip 1k
Turo tanan👇🏼
0907 355 6632
Oum mufeedah✍🏽
Add Comment