Ko Da So Hausa Novel Complete
Ko Da So…*
Bismillahir rahmanir raheem
*1*
Idon ta cike da hawaye take kallon sa, fuskar ta ɗauke da mamaki gami da tsoron yadda lokaci guda ya birkice kamar ba masoyin ta abin alfaharinta ba.
Anya shi dinne kuwa?
Hannu tasa ta goge hawayen da ke famar zarya a kuncin ta, don tafi ganinsa da kyau, duk da tasan gogen su bawai shi zai sa zafafan hawayen nata su tsaya ba.
Warware manyan idanunwanta akan sa.
Shi dinne dai, Mukhtar. Mukhtar dinta. Mijinta, uban yayanta. Sanye yake da farar shadda kamar ko wacce ranar juma’a. Farin kaya ba karamin ƙara masa kwarjini da kyau da haiba yake ba.
Ta sake goge wasu hawayen dake zuba daga kwarmin idonta ta kalle shi.
“Kar kayi mana haka Abban Abdallah… dan Allah…” ta faɗa cikin karaya. Bata san me zata ce masa ba amma abunda yake bukata daga gareta yafi girman tunaninta. Ba zata iya ba.Shima yafi kowa sani.
Kamar ba zaice komai, kamar yanayin nata ya bashi tausayi sai dai ɗan guntun tunanin da ya yi yasa shi kauda kai daga kallon, saitin da ya juya ta matsa ta ko yi nasarar jefa kwayar idanun ta cikin nasa.
Ta sa ni Muktar ɗin ta na son ta domin tana iya ganin zallar tausayin ta gami da madarar son ta a idanun sa, ta sani soyayyar Muktar gare ta bata gushewa a zuciyar sa. Takan gane haka ne a Idaniyar sa da basa taɓa iya boye zallar ƙaunar ta, duk kuwa da tsananin bacin ran da yake ciki. Take taji hawayen idonta sun fara ƙafewa, saboda wani hope da taji ya ziyarci zuciyar ta.
Karkarwar da take yi tuni ta tsaya, hawayen ma kamar an ce su tsaya. Cike da kwarin gwiwa ta matsa kusa dashi, murmushin kwarin gwiwa tuni ya mamaye fuskar ta, kallon sa take tana neman irin nata murmushin a fuskarsa. A hankali ta kamo hannun sa tana tsara mai zata ce a ranta da zai sa ya sauko daga fushin nan, sai dai yadda ya juyo a fusace ya sata sakin sa da sauri kamar wadda ta taɓa wuta.
Cikin daƙiƙu idanunsa suka gauraye jajir kamar garwashi cikin kausasasshiyar murya mara amo yafara magana wadda inda ace Hafsa tasan abinda zai furta kenan da tuni ta toshe masa baki tahau magiyar kar ya furta.
“Na sake ki Hafsa. Na sake ki saki daya. Ki bar mun gida yanzun nan…”
Kalmomin da bata taɓa koda da wasa tsanmanin jin su daga bakin Muktar ba, kallmomin da suka saka dukkan wata gaba jikinta ta sage. Kalaman da ta jisu tamkar saukar dalma a zuciyarta.
“Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un… Muktar ka sake ni fa kace?” Sam sam idaniyar ta sun dena gane komai yayin da ɗakin ya hau juyawa da ita tamkar fanka.
Yaraf ta zube a gurin, a ruɗe ya yi kanta yana Faɗin, “Ummu Abdallah…”
Yadda ya yi maganar yasa yaran su da basu san mai ke wakana ba suka yo falon da sauri, kamar wata ƙaramar ɗiyar sa haka ya ɗauke ta ya yi waje yaran suka bi shi yuuu…
A karo na farko kenan a rayuwarsu. Tun tasowar su da suka taɓa ganin Mamin ta su a irin wannan yanayin. Tuni jikin su yayi mugun sanyi. Mami mace ce mai kuzari gami da jarumtar ɓoye ciyo, duk runtsi tana daurewa ta farantawa yaranta sun shaƙu da ita ita ce koman su, kamar yadda suke koman ta. Ko kadan basu san menene rashinta ba a rayuwar su. Ko wannen su yana samun lokaci daga gareta dai-dai gwargwado. Wasu lokutan in suna hira takan ce musu su zama masu dogaro da kansu domin wataran zasu tashi babu ita a duniyar ma gaba daya.
Sai gashi yau rashin lafiya ta kwantar da ita ji suke tamkar duniyar ta tsaya musu. Ko da yake a wajensu duniyar ce ta tsaya domin Mami ita ce rayuwar su.
Tun jiya kawo ta ba wani bacci suka samu ba, Aiman ɗan ƙaramin cikin su ne ke ta faman zarya lokaci lokaci yana leƙa ƙofa da alamu mahaifin su yake tsanmanin gani wanda tun jiya da ya zo ya tabbatar an kwantar da ita bai dawo ba. Jiƙin yayan sa matsa, Yaya wai Yaushe Abie zai dawo.
Abdullahi ɗan kimanin shekaru goma sha biyu da kana kallon sa kasan idanuwan sa basu samu runtsawa ba, wanda har kuka sai da yayi. Shine dan ta na biyu kuma yafi kowa jinta a zuciyarsa kamar yadda uwar take dukkan kokarin ta ita ma ta boye yadda take jin sa daban a cikin yaranta. Ya dubi ƙanin nasa a hankali ya ce anjima kaɗan sam yaron bai cika som magana ba, bare yanzu ga tashin hankalin Umman su.
Juyawa Aiman ya yi ya cigaba da zaryar sa tamkar wani banban mutun, haka duk yaran Hafsa suke a nutse domin ita ɗim jajir tacciya ce wurin ganin yaran ta sun taso abin kwatance.
Azal Hausa Novel Complete
Kallonta suke yi dukkan su, alokacin da numfashin ta ke sama da kasa. Bacci take yi amma a baccin ma mutum in ya nutsu zaiga yadda take fusga da firgita kadan kadan. Sosai suka kura mata ido dukkan su suna jira suga kawai ta tashi.
Aiman ne ya matsa kusa da Babban wan su Faruk “Yaya wai Mami yau she zata tashi ne? Ni yunwa nake ji.” Ya faɗa yana tura baki. Kursum dake kusa dashi ta kwadeshi. Da gani itace a saman sa.
“Kai dallah malam waye yake ta abinci? baka ga Mami a kwance ba, Silly boy kawai.” Tayi tsaki tana sake mayar da taguminta kamar dazu.
Babban yana ta kallonsu bai ce komai ba kuma sai aka yi sa’a karamin baiyi kuka ba.
Suna zaune sunyi jugum jugum baban nasu ya fado dakin da gudu Aiman ya faɗa jikin sa, yawwa Abie tun jiya nake jira kazo ka tashi Mami. Kallo daya babban ya ma su yana shafa kan Aiman sannan ya dauke kan sa.
Tsai Abdallah yake kallon mahaifin na su babu wanda ya faɗa masa kuma babu ma alama a tattare da mahaifin nasu amma yasan shine silar kwanciyar mami. An yi kwana biyu yana lura da irin yadda suke mu’amala kamar makiyan junan su.
“Ya me jikin?” Abie ya sake tambaya bayan sun gaishe shi amma sai aka rasa wanda zai bashi amsa kamar sun haɗa baki gaba ɗaya.
“Mami will be fine. Kuzo in kai ku gida ku shirya ku yafi islamiyya…” ya faɗi yana so su tafi don baya son ta farfaɗo akan idansu domin bai san yadda zaiyi ba.
Kamar wanda ya faɗi wani abun tashin hankali Abdallah ya zuba masa ido kafin ya maida kallonsa zuwa ga Mamin yace, “hutu mukeyi ai Abba ka manta kuma in mun tafi waye zai zauna gun…” bai ƙarasa ba yaga kamar hannunta yana motsi. Ba shiri ya bar maganar tasa ya miƙe yayi kanta. Dukkan yaran suka mata rumfa suna kallon yadda take motsa yatsun ta a hankali gami da ƙoƙarin buɗe idanun ta.
A nata bangaren kuwa ji take kamar an ɗora mata dutsen Dala a kanta. Wani irin nauyi da ciwo ya mamaye gaba daya jikinta. A sannu a hankali take binsu da idanuwa.
Kamar a tare suka fara jero mata sannu sai dai babu wanda ta tanka.
“Alhamdulillah.” Mukhtar ɗin ya furta ganin ta farka, da dan damuwa a muryarsa sannan ya matsa kusa da ita. Daidai sanda idonta ya kama nasa, sannan ta fara zubar kwalla. Kamar wasa sai hawayen ɓakin ciki ya fara zirya akan kumatun ta.
“Mami, jikin ki ciwo?” Dan Aiman ya tambaya, su kuwa manyan sun ma rasa me zasuyi. Ba ma zasu iya tambayar ta mene matsalar ba musamman yadda suka ga ta kafe mahaifin su da ido.
“Mami please ki mana magana…”
“Mami sannu kinji, a kira miki doctor?”
“Mami sannu, dan Allah ki daina hawaye, yana min ciwo…”
Haka muryoyin yaran nata suke tashi a cikin ɗakin amma kamar ba da ita suke ba. Shi take so yayi magana. Har yanzu tana da kwarin gwiwa akan makomar su. Har yanzu tana son shi. Har yanzu shi din, shine farin cikinta. Kalamai uku kawai take so taji daga gare shi.
“Na maida ki.” Shi yasa ta zuba masa idanuwanta ba tare da kula da cewa yaran suna sane da su ba.
Sai dai Mukhtar ma ba tare da la’akari da yaran ba kawai ya juya ya fice daga dakin sam ci gaba da kallon masoyiyar tasa a haka zai iya sawa ya canja hukuncin da ya yanke, hukuncin da sam baya fatan janyewa.
Ko sannu bai ce mun ba.
Ko murmushin nan nasa kai sani farin ciki bai min ba, anya ba mafarki nake ba?
Hawayen da suka fi na ɗazu zafi suka ziraro zuwa kuncin ta lokacin da ta ɗora idanun ta bisa kofar da ya ja ya rufe.
A hankali ta rufe idanuwanta. Daga nesa nesa take jin yaran suna rokarta ta tashi sai dai tayi nisa daga duniyar da take yanzu. So take ta koma duniyar soyyayar su da Mukhtar don taga a ina ne ta kuskure. Ta san ko wanne labari yana da tushe, ko wanne labari yana da asali. Yana da mafari…
Nasu Mafarin ya fara ne a birnin Kano dake Najeriya.
****
Dala, Kano.
Sauri yake ya kammala cin tuwon dake gaban sa duk da yaji daɗin dumamen sosai zai so ace a hankali zai cinye shi sai dai baya so ya makara.
Daga gefe kuwa Inna ce ta ke ta faman jan ruwa daga rijiyar dake tsakar gidan tana cika bokitan dake gefenta. Mace ce ba zata haura shekara hamsin da biyar ba. Yar karamar mace ba tsawo babu kiba a tattare da ita. Fuskarta doguwa ce, hancinta madaidaici ne, leben ta ma mai tudu ne baka ce wuluk sai dai kaf yaranta babu wanda yayi bakinta. Gaba ɗaya su hasken mai gidanta suka ɗauko, farin bafulatani, Malam Adamu Mujeili. Duk da a Kano ya tashi amma yan asalin Yola ne. A nan Kanon suka hadu sukayi aure har suka haifi yara shida kafin Allah yayi masa rasuwa.
Malam Adamu mutum ne me zuciyar nema duk da bashi da wadata amma ba’a taba kwana da yunwa a gidansa. Yaran sa kuma suna zuwa makaranta har zuwa lokacin da Allah Ya dauke shi. Mukhtar shine dan shi na fari sai mata hudu reras a kasan sa. Mai bin Mukhtar tun bata shekara ba ta rasu sakamakon cutar kyanda da tayi.
Tun bayan rasuwar malam Adamu a lokacin Mukhtar yana gab da kammala sakandire, sauran yaran basu cigaba da karatu ba. Mukhtar haka zai fita yayi buge bugensa a kasuwa ya samo musu na abinci.
Ganin wahalar tayi wa Mukhtar yawa yasa mahaifiyar tasa ta fara sana’ar saida abinci wadda dama shi ta tashi taga mahaifiyarta tana yi sai dai bayan ta auri malam Adamu sai ya nuna sam baya so tayi sana’a. A yanzu kuwa dole ta kama sai tayi.
Haka dai sukayi ta faman ciyar da gidan har suka aurar da Rashida inda sauran yaran kuma suka koma makarantar gomnati. Zuwa yanzu kuma Mukhtar ya kammala jami’a inda ya karanci civil engineering don ya kasance yana da fasaha da kokari. Yanayin rayuwa da halin da kasarmu ke ciki ya sa yanzu shekarar su hudu da gamawa amma bai samu aiki ba.
Satin da ya gabata ne Inna Kulu taji wata sanarwa a rediyo na wata makaranta da take neman malamai. Sai da ta tabbatar ta haddace bayanan da aka yi. Bayan Mukhtar ya dawo daga kasuwa ne take sanar dashi abunda taji ta kuma karfafa masa gwiwa ya gwada ko za’a dace. Duk da ya na ganin kamar bata lokaci ne zaiyi, haka yaje ya gabatar da takardunsa a makarantar. Jiya kuma aka kira shi yazo yau a musu gwaji.
“Ashe Muntari ba zaka yi sauri ka tafi ba?” Ta fada tana juyowa taga me yake yi.
Murmushi yayi. “Tuwon yayi dadi inna. Yanzu zan tashi.”
Ba tare da tace komai ba, ta dauki murfin rijiyar ta rufe sannan ta samu gefe taja kwanon nata tuwon.
“Allah dai yasa a dace.” Ta faɗa cike da damuwa tana kai loma bakinta.
“Amin Inna.” Ya amsa mata a gajarce yana mikewa. Bakin inda take wanke wanke ya nufa ya tarar duk ta dauraye komai saboda haka shima a take ya wanke kwanon nasa.
A hankali ya dubi tsakar gidan da shi kadai ne abunda mahaifinsu ya bari. Idonsa ya fara kan katangar dakinsa da ta fara zubowa daminar da ta wuce. Sannan ya kalli gefen dakin inna wanda babu ko fitila balle fanka cikinsa. Kafin wannan ma yana bukatar gyara. In sha Allahu da albashinsa na farko zai gyarawa Inna dakinta da yake yoyo.
Yana yarfe hannunsa ya nufa inda ya ajiye jakar sa a kofar dakin su Hajara yana tabe baki.
“Sai yaushe zaki tashi wadancan magunan Inna? Wallabi ki dena shagwaba su.” Ya fada yana shan kunu alamun abun yana bata masa rai.
Dan murmushi Innar tayi sannan tace, “maza maza Allah ya kiyaye ya bada nasara.” Ya san ba zata tanka shi ba shiyasa kawai shima yayi mata murmushin yana mata sallama.
****
Harabar makarantar cike yake da jama’a kamar haɗin baki yau iyaye masu biyan kudi sun cika makil ga kuma mutanen da aka gayyata suzo gwaji. Dukkan su a tsaye suke masu hira nayi masu korafi nayi. Wasu daga iyayen kuma suna ofishin admin suna abunda ya kawo su.
Dai-dai lokacin da Mukhtar ya shiga harabar makarantar yaji zuciyarsa ta harba. Bai san dalili ba, kafin ya ankara kuma sai yaji nutsuwa ta saukar masa. Nan ya sami inuwa ya rakube kusa da wata matashiya ita ma rungume da jakar takardunta ta sha gilas amma fuskarta babu kwalliya. Sallama yayi mata ta amsa da fara’arta sannan suka yi shiru.
Suna wannan jiran ne motar me makarantar ta faka a kofar makarantar. Alhaji Muhammad mutum ne mai karamci da sanin ya kamata. Mutum ne da ya bude makaranta don amfanin jama’a sama da neman kudi domin dan kasuwa ne da yake da rufin asirin sa ba laifi kuma ya kasance likitan ilimi ne.
Kamar ko yaushe sanye yake cikin babbar riga. A hankali ya futo daga motarsa, mai gadi ya taho da sauri duk da ko yaushe sai Alhajin ya dakatar dashi.
“Abba ka jira ni mana…” wata murya ta faɗa a shagwabe.
“Hafsah kenan, kin makarar dani ina sake gaya miki.” Ba shiri ta fisgo jakarta tare haƙura da shan shayin da taso ta shanye kafin ta fito.
Kyakkyawa ce. Duk wanda ya kalle ta haka zai fara cewa game da ita. Ba doguwa bace can can amma ba gajera bace. Sanye take a abaya kalar ruwan goro wadda tayi bala’in yi mata kyau.
Da sauri take tafiya ta kamo babannata da har ya shige ciki. Ba tada kiba shi yasa ma saurin nata yayi kamar gudu take. Kallon lokaci tayi taga takwas dinma bata cika ba Baba yake ta wannan saurin.
Sanda ta kamo shi har ya fara gaisawa da mutanen wajen ya kuma tsawarar akan barin su da akayi ba’a bude musu aji sun zauna ba. Nan take aka bude ajin da za’a musu interview din.
Alhaji Muhammad office dinsa ya nufa tana binshi a baya.
“Ni fa ba zama nazo yi ba Abba. Nima so nake naga yadda kakeyin komai.”
“Hafsah kenan.” Abunda yace kawai sannan yayi magana da principal da wasu malamai da suka shigo suka nufi ajin da za’a yi gwajin.
Lokaci na tafiya, Hafsah tana hammar gajiya don ba ita kadai ba har su Baban sun gaji saboda yadda mutanen suke ta wahalar dasu basu san komai ba balle su cancanta. Ko ita da yanzu ta fara jami’a tafi wasun su.
Ganin saura mutum biyu yasa tayi hakuri ta zauna. Ita ma biron ta a hannu bata yadda ba sai grading take.
Wata macece me gilas ta fara magana. Kaf cikin jama’ar babu me kwazon ta. Anan take Hafsah ta sa a ranta an samu malamar wannan subject din. Ganin ita kamar ta gama nata aikin yasa ta jawo wayarta ta fara dannawa tana dora selfie din da tayi a snapchat.
Tunda ya fara magana abu ɗaya Hafsah taji duniyar ta dakata.
“Sunana Mukhtar Adam.” Duk wani abu da yace bayan nan bata ji shi domin ta faɗa wata duniyar daban, ta shagala da kallonsa tana yabonsa a ranta. Ta nutse a duniyar da ya kaga ba tare da ya sani ba, da muryarsa.
Wannan shine mafarin labarin su. Kafin ta fahimci hazakarsa, haibarsa ta fahimta. Kafin ta gane me kokari ne, sai da ta gane me kyau ne. Kafin ta gane ya hadu, sai da ta rasa hankalinta, sainda zuciyarta ta fara kitsa mata wani abu akansa. Wani abu da a lokacin bata san menene shi ba.
Ta so ace, zamanta tayi a gida a wannan ranar!
*Rubutawa*
*AeshaKabir*
*Fadimafayau*
*Ko da so…*
*2*
Jiki ba kwari Hafsa ta bi shi da kallo lokacin da ya bar ajin,idanunta ta maida kan takardar da sunayen masu neman aikin ke kai Muktar ta kuma mai-maitamana, murmushi ta yi kafin ta ja biro jikin sunan nasa kamar yadda ta yiwa matashiyar matar ɗazu alamar ya ci interview ɗin.
Ahankali ta miƙe tana duba agogo kafin ta miƙawa Malamin da suke interview ɗin tare, wanda ke kusa da ita bari in je gun Abba, karɓa kawai ya yi ba tare da ya ce komai ba, bata damu da rashin maganar tasa ba ta bar ofishin.
Har ta wuce ta dawo, fuskar ta ɗauke da murmushi “lah Anti ina kwana?” ta faɗa cikin har shen turanci matar ma murmushi ta mayar mata, “kyace ina kwana mana, anya Hafsa? ace tunda kukai candy ko a ɗan leƙowa a gaisa,” matar ta mayar cikin turanci.
“Kai Anti wallahi abububuwa sukai yawa, kuma gani na na yi in nazo ai duk kuna aji zan ɗauke muku hankali, anma ai ina cewa Abba ya gaisar mun da ku.”
“Eh fa ya na faɗe wataran, bari in je sauri nake Hafsa ta faɗa”
” nima kin ga aji zan shiga” matar ta fada kafin ta yi gaba.
Abba na zaune yana duba takardu Hafsa ta shigo da Sallamar ta, ɗagowa ya yi yana kallon ta kafin ya ce “to sarkin rikici badai nufin ki anan zaki zauna ba?,” girgizar kai ta yi a’a tafiya ma zan yanzun nan naga an mana fixing class 2-4 gwanda in je.
“Towo class kuma gashi ni yanzu ina som mu tattaunawa da team ɗin da sukai interview ɗin, dan mu samu mu a turawa waɗan da suka samu nasara sakon kar ta kwana zuwa gobe su fara zuwa, musanman wanda zai ɗauki Physics ɗin nan.”
“Tom shikenan kawai bani kuɗin ɗan sahu da na ƙara masa 200 a kan normal price zai kaini, dan innace sai driver ya zo kaini zan makara.”
Dubu Uku Abba muƙo mata “Allah ya bada sa’a,” murmushi ta yi “Amin sunma yi yawa ai, Allah ya saka da alkairi” ta faɗa kafin ta wuce.
A nitse Muktar yake tafiya tun da ya baro ɗakin gwajin ya kasa tunanin hukuncin da mutanen zasu yanke tsaf ya tsaya dan naƙaltar su sai dai fuskokinsu ba su nuna sun yi maraba ko akasin haka da jawabin da ya gudanar ba, duda cewa shi a ransa yana jin kwarin gwiwar ya yi abin da ya da ce ko da bai samu Malamin senior ba to su ɗauke shi a matsayin malamin primary.
Har ya wuce mai lemon ya dawo soyayyar Umman sa da lemo mai ɓawo yasan ya bazai iya ganin lemo ya wuce bai sai mata ba, Ɗari biyun sa kenan, “na ɗari za’a bani” ya faɗa a takaice, Baba Yakubu ne ya yi miƙo masa bakar ledar kai dai Muntari kana son siyan lemon ɗari naga randa zaka sai na du ɗari biyun.
Dariya Muktar ya yi, ” adai ci gaba da tayamu da addu’a wataran na dubu zan siya,” Allah dai yasa ai nima zan so haka.
A kishin giɗe Innan take tana jin radiyo ganin shigowar Muktar ya sata gyara zama, yanayin fuskar ta ya nuna ɗoƙi da son jin labari mai daɗi na an ɗauke shi aikin, ajiyar zuciya ya yi kafin ya zauna kusa da ita ledar lemon ya miƙo mata kafun ya ce “wanne shirin suke?”
“Kaji dai shirin Muda likita nake son ji, ta yau ƴan siyasa sun siye filin shine nake saurara, ya aikin kuma fatan an dace.,?” Iska ya ɗan furzar “to gashi nan dai sunce zuwa dare zasu turo mana sako,” ya faɗa jiki ba kwari.
“To Ai shikenan, ai mutun baya wuce ƙaddarar sa in ba’a dace ba sai mu cigaba da jarrabawa” Umman ta faɗa ga. Shiru kawai sukai kowa da abin da ke zarya a ransa yayin da sautin Radio ke ta shi a tsakar gidan.
***********
Sam Hafsa ta gaji da ajin na farko ba son Physics take ba sabida bata ganewa, na biyu malamin da ke koya musun yada ya wani haɗe rai yasa duk haushi ya cikata, ga kuma haushin kanta da take ji tun ɗazu da take tawowa idanun ta sun gaza goge mata hoton mutumin ɗazun ita a yanzu ba zata iya faɗin asalin mai take tunani akan sa ba.
Kamar jira take Malamin ya fi ce zumbur ta miƙe, riko tan da ta ji an yi yasa ta juyowa Bilki su ce, tare sukai secondry school yanzu kuma suke aji guda a Jami’a, “Hajiya ina zuwa haka cikin gaggawa Bilkisun ta tambaya tana kallon ta.?”
Ɗan wawwaigawa Hafsa ta yi taso mu tafi kar” yamma ta yi,” dariya Bilkisun ta yi “wato da ace ban ruƙo ki ba kina nufin tafiya zakiyi ki barni ko me.?”
Dariya Hafsa ta yi “no da ba tafiya zan ba kawai zan ɗan fita ne in shaƙi fresh iska,”
“ok jeki ki shaƙa bari in nuna ma Ummi wannan abun”
“ok” kawai Hafsa ta ce har ta kusa bakin ƙofa ta ce “dan Allah karki barni ina ta jira waya ta babu caji nasan da Abba yaga biyar ta yi tunda na ce masa four ne zai ta kira in bai same ni ba hankalin sa zai ta shi.”
Tana tsaye jikin karfen benen tana bin bishiyun gun da kallo tare da tsuntsayen da ke kai kawo daga wannan bishiya zuwa waccan ji take tamkar kar ta bar gun wannan ya sa ma bata kuma leƙawa ta dan cewa Bilkisun ta fito ba.
Kafaɗar ta Bilkisun ta taɓa “zo mu tafi” kamar jela ta bi bayan bilkisun, sai da suka fara zuwa Masallaci sukai sallah kafin su nufi wurin da zasu shiga mota.
Har ƙofar gida aka kai Hafsa in da ta sauka tana ɗagawa Bilkisu hannu kafin ta fara kwankwasa kofar gidan su, minti kaɗan Baba mai gadi ya ta so ya buɗe ganin ta ya saki washe baki “a’a Hajiya karama a dawo?” dariya ta yi “eh walllahi na dawo ya aiki?” ta tamtabaya.
“Aiki Alhamdulillah ai tun ɗazu da naga Alhaji ya dawo shi kaɗai na ce araina yau bani da abokiyar hira sai kim kai yamma,”
” ka bari kawai Baba ai Malaman nan basa kyautawa bamu san da aijin ba ɗazu aka sanya da nasan da shi ai da ban bi Abba ba duk na gaji.”
“Assha sannu, Allah dai ya sawa karatun albarka,” “amin” ta ce kafin ta yi gaba, gaban ta ne ya hau faɗuwa lokacin da ta ɗora idanun ta kan Momin su wadda ke saman bene tana faman watso mata harara, tasan ba komai bane fa ce dan kawai ta ga tana magana da Baba, a hankali jiki ba kwari ta nufi kofar da zata datar da kai asalin falon gidan.
Da sauri ta yi ƙoƙarin shigewa ɗaki dan karma Momin ta sassko ta mata faɗa, sai dai saurin nata bai idda ita ga shiga ɗakin ba ta ji Muryar Momin, “sannu issasshiya wato zaki iya cewa wancan mutumin kin dawo ni ban isa ki zo ki ce mun kin dawo ba?.”
Ajiyar zuciya ta yi a hankali kafin ta jiyo, “No momy kawai ina san aje jakata ne sai in hauro saman,” taɓe baki Momin ta yi, yanzu fisabilillahi Kalle ki, kin kyautawa mahaifin ki kenan?” kallon kanta Hafsa ta hau yi, tana son gano aibun ta gaza gano hakan yasa ta cewa Momy “mai nayi?”
“Eh kyace mai kikai zaku je makaranta inda mahaifin ki keda alfarma ace duk kayan ki ki rasa wanda zaka sa sai wannan jemammiyar rigar..?”
Dariya Hafsa ta yi “kai Momy wannan fa sabuwa ce last week na saya 17k fa” tsaki Momin ta ja, “ai walllahi lefin Abban naku ne ni ai bazan ta fi da ke a haka ba,” dariya kawai Hafsa tace “shikenan Mum karki damu in zamu fita tare sai abinda kika zaɓar min zan sa but banda takalmi mai tudu.”
“Ni in tafiya da ke a’a kawai kije ki bada ni cikin manyan mutane,” dariya Hafsa ta yi “mai aka dafa? yunwa na ke ji” ta faɗa tana shiga ciki.
“in sai na faɗa miki zaki ci ki kwana da yunwa,” Momin ta faɗa tana ƙokarin zama, Hafsan bata dena dariya ba ta nufi in da kwanunakan abin cin suke.
*******
Muktar na zaune cikin abokan sa kamar kullum bayan sun yi mangariba zuwa isha kafin ya wuce gida wayar sa ta yi ƙara alamar saƙo ya shigo, tun ɗazu yake duba wayar shiru ba kira ba saƙo wannan yasa har ya banzatar da wayar sai kuma ya ɗauko ya duba _”muna ta ya ka murnan samun aiki na koyar da Physics bisa gwajin da kazo ɗazu, zaka iya fara zuwa aiki daga gobe, gaza zuwa cikin wannan satin na nufin baka amshi aikin ba, Mun gode Hukumar Makaranta” _
Zumbur ya miƙe bayan kammala karatun saƙon Umman sa kawai ya tuna ita ya dace ta fara jin labarin nan, “ina zaka ne?, ai 8:30 batai ba” ɗaya cikin abokan sa ya faɗa cikin ɗaga murya.
Shima cikin ɗaga murya ya ce “mu haɗu gobe kawai, zan ma bayani,” gudu gudu sauri- sauri yake har ya ƙarasa gida sallamar ma tare da kiran Umma ya haɗa ta, cikin sauri ta fito “kiran da yake mata yasa ta kasa amsa sallamar lafiya dai kake mun wannan kira?”
Wayar sa ya hau nuna mata kallon sa ta yi ” yo banda abin Muntari ni me zan gane a waya mai ya faru?’ sun ɗauke ni aikin ya faɗa cike da murna ɗo.
“Kai Alhamdulillah, Allah ya ƙarawa annabi daraja yasa a fara asa’a, ayiriri!” ta sa buɗa, daɗi ya kuma rufe Muktar a duniya yana son ganin farin cikin Innan sa, “yau she kuma zaku fara zuwa ta tambaye shi?.”
“Go be in sha Allah” ya ce
“Allah ya sa muna da rai” ta faɗa
“amin Inna, bari in amso Omo gun Musa in zo in wanke kayan da zan sa gobe, gwanda in fara zuwa a mutunce,” dariya ta yi “tom sai ka shigo” ya fice…
*Aeshakhabir*
*Faɗimafayau*