Kwantan Bauna Hausa Novel 2023
KWANTAN ƁAUNA
FitattuBiyar 2023.
©️ *Nana Haleema.*
*Book 1*
*007.*
Bayan sallar juma’a aka samu kiran gaggawa daga mai martaba duka iyalan gidan hatta matan da suke gidan mazajen su sai da aka kira su aka taru a fadar cikin gida duk wani da ya kasan jini a gidan sai da aka kira shi. Dukkan su suna zaune ana sauraren abinda mai martaba zaice kowa yayi mamakin kiran.
Gidan Uncle Hausa Novel Complete
A kamalance da k’asaita da zallar nutsuwa da hikima ya fara fad’in, “kamar yarda na saka a kira ku nasan da yawan ku kuna tunanin lafiya akayi kiran gaggawa haka kasancewar bai tab’a faruwa ba. Ba wani abun bane an kira ku ne akan murabus da nace zanyi a d’ora Asad.” Kallon kallo aka shiga yi dukka mutanen wajan gaban su na fad’uwa matuk’a burin kowa yaji k’arshen maganar.
“Babu batun ta a yanzu mu janye, amma nan da wasu kwanaki maganar zata dawo matuk’ar ina raye kuma abinda nace baza’a canja shi ba, in kunga abinda na fad’a bai faru ba ku tabbatar k’asa ta rufe fuska ta.” Shiru fadar take ko masu kirari babu kasancewar magana ce ta cikin gida su kad’ai babu damar magana kuma sai ya bada dama. Fuskokin mutanen dake wajan zaka kalla zaka hango zallan farin ciki akan abinda yace, fuskar Mama ce kawai a d’aure cikin akasin farin ciki amma bata ce komai ba.
“Bana son na sake jin wata magana akan wannan na yiwa tufkar hanci, in lokaci yayi komai zai bayyana amma banda yanzu.” Nan ma shiru suka kuma yi kafin yace, “Akwai wanda yake da magana a cikin kuz?.” Shiru akayi babu wanda yace komai sai daga baya babar y’a kaf gidan mai Maimuna wacce taci sunan mahaifiyar mai martaba ake kiran ta da Mummy tace, “Allah yaja da zamanin mahaifin mu, Allah ya kare mahaifin mu a duk inda yake. Hukuncin mai martaba shine hukunci a ko wanne lokaci, babu mai magana a cikin mu.”
Kai ya girgiza kafin yace, “Kowa zai iya tafiya.” Kai k’asa sukayi da kansu a tare dukkan su suka furta, “A tashi lafiya.” Dukkan su suka fita kowa ya nufi b’angaren sa zuciyar kowa fari kar sab’anin Mama da take cikin mayuwacin hali.
Tunda ta shiga b’angaren ta take zagaye hankalin ta a tashe ta matuk’a ta kasa zama sai kai kawo take, ta d’auki waya hannu na rawa ta kira Sadiya tana d’auka tace, “Sadiya akwai matsala babba.”
Daga can b’angaren tace, “Ranki ya dad’e me ya faru?.”
“Mai martaba ya janye batun murabus d’in sa haka kawai babu wani dalili.”
“Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un, Ranki ya dad’e munyi sake gaskiya, duk yadda akayi wani abun aka yiwa mai martaba kuma ya shiga jikin sa. In fulani zata tuna akwai wanda zasu shiga su fita wajan ganin an tarwatsa mana abinda muka saka a gaba.”
“Shiyasa nace miki ina buk’atar zuwa Kano, dole ne na shiga garin Kano a kwanakin nan, babu wanda ya isa ya shiga tsakanina da mulkin Asad, babu shi ko waye” tana fad’a ta yanke wayar hannun ta na rawa ta kira Asad.
Yana zaune yaga kiran ta daman yasan sai Mama ta neme shi ya d’auki wayar baiyi magana ba ya sauke daga kunnen sa ya tashi ya tafi b’angaren nata, can ciki ya shiga inda ya kasance babu mai shiga sai su yana shiga kafin ma yayi magana tace, “a tafiyar da kuka yi dashi me kuka tattauna har ya canja shawara lokaci guda?.” Ya d’ago ido kamar zaiyi magana sai ya fasa ganin hakan sai ranta ya sake ya b’aci tace, “bazan lamunci wannan shirun naka ba Asad! Ka fad’a min kaine kace masa baka ra’ayi?.”
Kai ya girgiza alamun a’a kafin yace, “wallahil azim Mama bamuyi magana irin wannan dashi ba, ki amince dani bazan yi k’arya dan na kare kaina ba” ya fad’a a sanyaye yana kallon k’asa. remote ta d’auka tayi jifa dashi ya tarwatse a wajan tana wuci tace, “koma dai meye Asad baka isa kak’i karb’ar mulkin nan ba indai ina da rai, Asad kaine zaka mulki garin nan babu wanda ya isa ya shiga tsakanin ku da mulkin nan, dole ka cika min burin.” tana fad’in hakan ta wuce zuwa d’akin ta tana fad’in, “A shirya min tafiya gobe zan wuce Kano.” Kai ya girgiza sai da ta shiga ciki sannan ya juya ya fita zuciyar sa gabad’aya babu dad’i ko kad’an.
A falon Hajiya iyalan ta zagaye suke da ita maza da mata y’ay’an ta kowa ka kalla zaka hango zallar farin ciki a tare dashi barin ma ita da take ta murmushi ita kad’ai alamun hak’ar ta ta cimma ruwa. Wayar ta da taji tana k’ara ya sakata ta mik’e ta shiga d’aki ta barsu a wajan ta amsa wayar tace, “Abu kamar wasa yana ta zama gaske, sai ga mai martaba da kansa ya janye batun nan.”
Waziri yace, “Na sha fad’a miki ki kwantar da hankalin ki komai fa a hannun mu yake amma duk sai ki bi damu kan ki.”
Murmushi tayi mai sauti tace, “yanzu meye abu na gaba?.”
“Master planer tace mu had’u dake waje d’aya zamu tattauna.”
“Yaushe zaka shigo to?.”
“Zan shigo zuwa dare.” Murmushi tayi tace, “Allah ya kai mu” tana fad’ar hakan ta yanke wayar zuciyar ta cike da farin ciki a bayyane.
*◇*
Amaryar Sarki Hajiya Rukayya wacce ake kira da Ammi a gidan itama tana zaune da nata iyalan babban d’an ta namiji mai suna Nazif a shekaru bazai wuce shekara sha hud’u ba ya kalle ta yace, “Ammi ni na rasa ganewa kamar kina goyan bayan sarautar Asad?.” Murmushi tayi ta kalle su dukkan su tace, “To meye nawa da zanki goyan baya Nazif? Kai dai a musulunce baka kai minzalin jan ragamar al’umma ba to meye abin tayar da jijiyoyin wuya akan hakan?.”
Babbar y’ar ta mace mai suna Zainab wacce ake kira Yaya Zainab tace, “kin huta Ammi, koma waye zai mulki garin nan mudai burin mu ya kasance alkahiri a gare mu da kuma garin.” Wacce take bin ta tace, “Shine kawai fatan mu amma ni banga abin tayar da hankali a lamarin nan ba. Asad kuma kaf gidan nan babu mai kirkin sa kawai shi rashin maganar sa ce illa amma kowa yasan halin sa ga san y’an uwan sa baya lakari da yanayin gidan namu kowa na sa ne. Duk da Mama bata son yana sauraren mu amma shi ko a jikin sa, ga ilimi da kud’i a hannun sa.”
Ammi tace, “Allah ya kyauta” duk suka amsa da amin suka cigaba da hirar su gabad’aya maganar mulkin katagum bata gaban su su kam.
Hydar da Aliyu da kuma Asad ne a zaune a b’angaren su babu wanda yake yiwa d’an uwan sa magana dukkan su waya ce a hannun su suna dannawa hankalin su a kwance, waya Hydar ya d’auka ya kira Dr ya sake tambayar sa jikin Rauda ya tabbatar masa da komai daidai. Asad ya dafe kansa da yake mugun ciwo yana yatsine fuskar sa. Hydar ya kalle shi yace, “Deaf ya dai?.” Yatsine fuska yayi yace, “nothing” yana fad’a kawai ya tashi ya shiga d’akin sa ya kulle k’ofar ya zaga baya ya bud’e varanda yana kallon harabar gidan ana ta hidima da shige da fice.
Allah ya sani baya k’aunar mulkin da ake son k’ak’aba masa ga jifa da yake sha tun daga fara maganar sarautar nan yake ganin mutane da yawa wanda baiyi tunani ba a mafarkin sa ina ga an bashi sarautar?. Burin sa kasancewa a madina ba’a Nigeria ba a can yake burin yin aiki kuma burin sa ya cika amma Mama ta hana.
Lumshe idanun sa yayi mafarkin da yayi a jiya ya dawo masa kansa ya wara idanun sa yana k’ok’arin tuno fuskar yarinyar da ya gani ta taimake sa a mafarkin amma ya kasa, furzar da iska yake yi jikin sa na kyarma hankalin sa ya tashi ji yake gidan gabad’aya yana juya masa sam baya son zama a cikin sa, duk yadda yaso daurewa kasawa yayi ya fito ya d’auki makullin mota ya fita har lokacin Hydar da Ali suna zaune.
Hydar ma fita yayi aka bar Aliyu a zaune yana ganin fitar su ya mik’e ya shiga d’akin Asad yana k’arewa d’akin kallo kamar yana neman wani abun a ciki. Babba ne d’akin sosai komai fari ne a d’akin hatta tiles d’in d’akin fari ne labulaye carpet komai fari ne a d’akin, fari kuma tass babu alamun daud’a a tare da ko ina sai khamshi da yake yi. tab’e baki yake yana girgiza kai yana hasahen abinda ya kamata yayi a d’akin kafin ya fita daga d’akin.
Hydar yana fita asibitin ya koma a lokacin Umma ce kawai a ciki ya shiga da sallama ta amsa tana kallon sa yace, “Sannu Mama, ya mai jikin?.”
“Da sauk’i gata bata farka ba har yanzu.” Kallon ta yake yi ya runtse idanu ya rasa dalilin da ya saka gaban sa yake fad’uwa in ya kalli fuskar ta sai yaji wani abun yana shigar sa ya rasa meye.
“Allah zai bata lafiya.”
“In sha Allah, ban san sunan ka ba.”
Murmushi yayi kad’an yace, “Aliyu suna na” ya fad’a yana ajjiye kud’i a gefen gadon ta ya fita bai kuma cewa komai ba. Kallon kud’in take yi ganin su da yawa a zahiri bata tab’a ganin mai yawan su ba balle kuma ta rik’e ta yunk’ura zata d’auka kenan Baba ya shigo.
Idanun sa akan kud’in suka fad’a ya k’araso yana fad’in, “Ikon Allah wannan abin arzukin fa” ya fad’a yana k’arasowa wajan ya d’auki kud’in yana kallo.
Kallon sa Umma tayi lokacin da yake juya kud’in tace, “Wanda ya buge Rauda ne yanzu ya fita shine ya ajjiye kud’in.”
“Tooo!” Ya fad’a da murmushi a kan fuskar sa yana sake kallon kud’in.
Tab’e baki tayi tana kallon sa ya zuba kud’in a aljihu yace, “To shi wanne irin mai kud’i ne haka?.”
“Ban sani ba” ta bashi amsa a tak’aice tana kallon wani wajan daban.
“Allah sarki daman in arzuk’i zai same ka sai Allah ya kawo silar faruwar sa, sai gashi silar arzuk’ina yazo ta hanyar hatsari” ya fad’a yana cigaba da murmushi ya saka hannu ya dafe kud’in.
Shiru tayi kawai bata ce komai ba tayi tagumi tana kallon Rauda da take bacci har lokacin bata farka ba. Fita yayi yana ta dariya ta bishi da kallo kawai tana girgiza kai har ya b’acewa ganin ta.
Fitar sa ba jimawa sosai Rauda ta farka rad’ad’in azaba ya kawo mata ziyara ta runtse idanun ta muryar ta bata fita tace, “Wayyo Allah!” Abinda tace kenan tana hawaye.
Jin hakan ya saka Umma tasowa da sauri tana fad’in, “Rauda sannu kin tashi?.” Kai take juyawa tana fad’in, “Umma k’afana!, k’afa Ummana!!, zafi take min zata cire” ta fad’a tana kuka sosai ga kanta na mugun ciwo.
“Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un, sannu Rauda, Allah ya baki lafiya.” Kuka take sosai Umman ma sai ta fara hawaye tana rik’e hannun ta tana fad’in, “kiyi hak’uri Rauda, kiyi hak’uri.” Bud’e k’ofar akayi aka shigo Umma ta kalli wanda suka shigo taga likita ne da Hydar likitan ya kalli Umma yace, “yaushe ta farka Mama?.”
Sai da ta goge idanu tace, “yanzun nan.”
“Rauda sannu, me yake miki ciwo yanzu?” Dr ya fad’a yana kallon ta.
“K’afana, k’afa na zai cire, kaina zai fashe ku taimaka min” ta fad’a cikin tsananin azaba tana juya kanta. Gaban Hydar fad’uwa yake jin yadda maganar ta take fita tausayin ta ya sake kama shi jikin sa yayi sanyi matuk’a ganin duk fa da bai buge ta ba da hakan bata faru ba.
Allura likita yayi mata ya d’aura mata ruwa har lokacin juya kanta take yi sabida ciwo. likitan ya kalli Umma yace, “Kiyi hak’uri Mama zata daina jin ciwo in sha Allah, sai a hankali zaki ga kamar batayi ba” Kai ta d’aga kai daga nan suka fita Hydar ya kalli Dr yace, “tana cikin ciwo sosai babu wani taimako da za’a yi mata?.”
“Prince daman ai sai a hankali zata samu sauk’i, yanzu farkawar ta kenan dole taji ciwo a jikin ta amma yanzu zai lafa.”
Hydar yace, “Dr ayi abinda ya dace please.”
“In sha Allah prince zata dawo kamar batayi ba.”
“Thanks” yana fad’a ya bar wajan da sauri shi kuma ya koma office.
Haka Hydar ya koma gida gabad’aya jikin sa ya gama mutuwa tausayin Rauda yake ji na shiga jikin sa sosai, da ya kulle ido sai yaga yadda take kuka tana kiran k’afar ta sai hakan ya sake tayar masa da hankali sosai, muryar ta da kukan ta kawai yake ji a kansa da kunnuwan sa hakan ya sake saka jikin sa yin sanyi yana ji kamar yayi mata kuka.
Lokacin da ya shiga b’angaren su Asad baya nan sai Aliyu yana zaune yana tauna chewing gum ganin yadda Hydar ya shigo ya saka yace, “lafiya kai kuma?.”
Hydar ya zauna yace, “yarinyar dana kad’e ce tana cikin ciwo abin tausayi.”
“Mtswww and so? I think y’ar talakawa ce ko?.”
“Ita y’ar talakawar ba mutum bace?.”
“Bata da banbanci da matattaciya.”
“Ban san me yake damun ku ba, shi d’an talaka ba mutum bane ba ko me?, ko kuma kai ka zab’i taka rayuwar a haka?.”
Aliyu ya tab’e baki yayi masa banza bai kuma kula shi da dan a ganin sa bashi da hankali in shine ya buge ta ko k’afar sa zasu gani ne balle ya dinga zarya haka akan kanta. Shima Hydar d’in banza yayi masa dan ya lura Aliyu da Mama halin su guda ne.
A b’angaren waziri da Hajiya suna zaune kamar yadda suka saba a inda suka zaba had’uwa a sirrance waya na hannun waziri an saka speaker muryar mace babba mai cike da kamala tana fita daga cikin ta, Waziri yace, “kamar yadda na fad’a miki anyi komai an gama gashi har mai martaba yana cewa an jinkirta komai.” Murmushi tayi mai sauti tace, “na raina wayon ka da kai da ita kanta Sa’adatun, yanzu ku har kun amince da abinda yace?. Wasa yake muku da hankali ya d’auke hankulan ku daga kan sarautar gabad’aya rana tsaka sai dai kuji sanarwa Asad ya zama sarkin ku dole ku duk’a ku gaishe sa. Kun manta tare suka fita ne a jiya?.”
Kallon juna sukayi kafin Waziri yace, “Haka ne, amma bakya ganin kamar wannan karon da gaske yake?.”
“Ina baka kana mik’o min hannu. Kai kasan babu wanda ya san sirrin mai martaba sama da Asad sai kuma Mubarak k’anin ka, ko lokacin da suka je Kano da shi Mubarak d’in suka tafi tare aka tattauna aka cimma matsaya ku baku san komai ba. Ku a ganin ku mai martaba zai bada dama kayi sarauta ne? Kuyi tunani dakyau zaku gano kwantan b’auna ne.”
Hajiya tace, “duk abinda kika ce haka ne tabbas tunani na bai kawo haka ba sai yanzu, tabbas kwantan b’auna mai martaba yayi mana yana so hankalin mu ya d’auke daga kan Asad ne shiyasa yace haka. Ya fahimci akwai masu nufi irin namu shiyasa yayi saurin dakatar damu.” Murmushi tayi mai kyau tace, “Dad’ina dake kina da saurin fahimta. Ku nutsu ku kuma dawo hankalin ku in ba haka ba kuna ji kuna gani komai zai lalace muku. Suhail kuma tabbas ya sakawa Asad layar nan dana baka kuma ta fara shiga jikin sa zancen da nake muku yanzu ma zaman gidan ya fara neman gagarar sa, ciwon Hydar zai tashi a cikin kwanakin nan, ga Aliyu kuma daman ba zaman gidan yake ba. Matuk’ar bamu d’auke hankalin Rabi’atu ba to tabbas shirin mu bazai tab’a tafiya yadda muke so ba, rashin lafiyar Hydar da barin Asad gida ya isa ta fasa tafiyar da tace zatayi, dan matuk’ar taje Kano sai komai ya lalace.”
Waziri ya girgiza kai yace, “Wannan shine shirin mu na gaba kenan?.”
“Shiri na gaba a kan Asad ne ya zama dole ya bar gidan nan kota halin k’ak’a, ko kuma ya bar duniyar gabad’aya barin sa da numfashi barazana ne ga namu numfashin.”
Hajiya tace, “Abinda nake nuna masa kenan tun farko amma ya kasa ganewa, a kawar da Asad shine abu mafi mahimmaci a wajan mu.”
Tace, “kwantar da hankalin ki Hajiya baza mu gaggawa ba, a hankali zamu tafi da lamarin in muka ba bar Asad da Aliyu ma komai zai tafi yadda muke so, zakuyi mamaki idan nace Aliyu yana neman hanyar da zai bi wajan ganin ya zama sarki a garin nan, tabbas Ali zai iya kashe Asad abu ne mai sauk’i a wajan sa indai burin sa zai cika wannan ba komai bane ba. mu jira muga yadda wasan zai kaya.”
“Abinda nake so dake Sa’adatu ki cigaba da nuna k’aunar Asad a gaban mahaifin sa, ki jawo sa jikin ki yadda baya sakewa da uwar sa ke ya sake dake, kiyi duk abinda zakiyi ya fara cin abin hannun ki ana zuwa wannan gab’ar mun kamo wuyan sa, na bar ku lafiya” tana fad’a ta datse kiran wayar. Hajiya tace, “kirata naji ta yaya zan jawo shi jiki na, dan Allah ka kira ta.”
Waziri yace, “Bana tab’a samun ta a waya sai dai in ina taso zata kira ni sai ta bani lokacin da zamuyi magana.”
“Gaskiya ta cika babbar master planer, amma wacece ita? Naso na gane maganar ta amma na kasa ganewa, na santa kuwa?.”
“Ba lallai kin santa kedai kiyi abinda tace ta kai k’arshe wajan iya tsara plan. Ta wacce hanya zaki bi Asad ya zo hannun ki?.”
Numfashi ta sauke tana girgiza kai kafin tace, “Salad, zogale, lansir, wad’annan shine abinda Asad yafi so yaci tun mai babban d’aki tana raye, duk juma’a sai ta aiko masa da d’aya daga cikin su an masa lafiyayyen had’i zai ci kuma hankali a kwance. Bayan shi sai kunun tsamiya mai lemon tsami, sai kuma shayi ko coffee ko kuma chips Asad yana son wannan abubuwan dasu zanyi amfani na meye gurbin mai babban d’aki wajan aika masa dashi duk juma’a, babbar matsalar ita Rabi’atu kana ganin zata bada damar da zan jawo Asad jikina?.”
“Tabbas kinyi tunani mai kyau Asad yana matuk’ar son abubuwan da kika lissafa kuma shi halinsa daban ne dan kin bashi karb’a zaiyi yaci bazai kawo komai ba, yadda zuciyar sa take fara gani yake ta kowa fara ce, yarda baya nufin kowa da sharri gani yake kowa ma haka ne. Matsalar dai ita uwar sa kamar yadda kika ce.”
Ta daki kujerar da take kai tace, “Amma bar ni da ita nasan abinda zanyi zan biyo mata ta k’ark’ashin k’asa sai burin mu ya cika.”
“Ki dai yi a sannu kin san tana da wayo kuma ta dafu da magani ne tun tana yarinya ta kuma dafa y’ay’an ta, ki duba wahalar da muke ta sha tun suna k’ananu har yanzu akan abu guda muke, amma zamu kamo bakin zaren in Allah ya yarda.”
Hajiya ta mik’e tsaye tace, “ni na koma zaka ji bayani daga baya” tana fad’a ta fita shima bai jima sosai ba ya tashi ya tafi…….
*ni kaina na shiga confuse fa, wacece Master planer kuma?.
Add Comment